Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 10

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 10

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 10: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 10. ..........Ranar 10 ga Oktoba, shekara ta 1972, garin Kobi na…

4,478 words

..........Ranar 10 ga Oktoba, shekara ta 1972, garin Kobi na cikin Bauchi ya tashi da sanyi mai ɗauke da ƙamshin ƙasa na ruwan da aka sha da asubahi. Saukar ruwan data kasance kusan dai-dai da farkawar A'isha dake gidan su Abdul-rasheed ɗakin Inna tashi a gigice da ciwon mara. Inna ma dai dama ta farka, dan haka tai kanta tana salati, tunfa lokacin aka fara gumirzun naƙuda, makwafciyarsu Inna Salame dake unguwar zoma tuni ta shigo suna kanta ita da Innar, baba nata addu'a a cikin ruwa Inna na amsowa ana bata da sauran saƙe-saƙin ruwan magani da Inna Salame tazo da su. Dama kuma tunda cikin ya shiga watanni bakwai take shansu kala-kala, duk da Abdul-rasheed baya so dole ya haƙura, amma yana ɗaukarta a ɓoye ya kaita asibiti gudun kar su Inna suyi faɗa dan basa so. Shi kuma yana son lafiyar matarsa da kulawa mai tsafta. Har gari ya waye tangaran, matan yayun Abdul-rasheed ma da maƙwafta suka shigo A'isha bata haihu ba, sai zuwa can hanci ya ɗaga kaɗan, rana ta leƙo kaɗan da yanayin ɗuminta mai daɗi da armashi dake ma mutane daɗi. A cikin ɗakin Inna kukan jariri baƙon duniya ya ratsa kunnen duk wanda ke cikin gidan Baba a wannan hantsi. A take farin ciki ya mamaye fuskokin kowa, dan kuwa dai A'isha ta sauka kenan, UBANGIJI ya kawo iyaka. "Alhamdulillah!" in ji tsohuwa Inna Salame mai karɓar haihuwa, ta share gumi tana murmushi bayan kammala yanke cibiya. Cikin ɗan hasken ranar daya hudo tagar ɗakin ta Inna ta ɗagashi da ƙyau tana faɗin, "Barka-Barka yar nan kinji, yaro ne, kuma lafiyyayen gaske masha ALLAHU." A'isha, sabuwar uwa, ta saki hawayen farin ciki tana kallon yaron ta gefen ido daketa motsi a cikin hannun Inna Salame tana gogeshi zata naɗeshi a farin mayafi na auduga na ɗaukar jariri da Inna ta kawo. Addu'a ta shiga jera masa a zuciyarta, kamar yanda take yi masa tun tana a gaɓar ɗanɗana zafin naƙuda, hakan a gareta koyarwar Abdul-rasheed ce, dan tunda ta samu cikin nan ya ƙara ƙaimi wajen koya mata rainon ciki da fara masa tarbiyya irin ta musulinci tun a ciki, addu'oi yanayi itama tanayi. Inna Salame ce ta shiga gyarata bayan ta mikama Inna baƙon duniya daketa callara kukansa tamkar yana shelantawa ƴan Kobi da garin Bauchi baki ɗaya zuwansa duniya. Sosai wannan haihuwa ta saka mutane da yawa a farin ciki, yaro yasha addu'a kala-kala ga iyaye da kakanni. Yayinda bakin Abdul-rasheed ya kasa rufuwa dan ana haihuwa yara suka je suka sanar masa a ƙofar gida shi da su baba. Dan bayan idar da sallar asuba ya rako Baba gida kamar yanda ya saba, ga ɗan yaf-yaf na ruwa da ake yi har lokacin, shine sukaci karo da Inna a ruɗe zata fita kiran Inna Salame take sanar musu A'isha ce ke naƙuda, tun daga lokacin bai iya barin gidan ba yana nan tare da Baba yana mata addu'a a zuciya. Bayan ɗan lafawar hayaniyar gidan da saukar garwar ruwan wankan maijego aka kwashe mata zuwa bayi, aka ɗiba na jariri shi kuma zuwa ɗakin Inna. Saura kuma nata ƙoƙarin ɗaura kunu da za'a dama na jego a wuta. Gefe ga kawunan akuyoyi masu ƙyau da Abdul-rasheed ya shigo da su yanzun nan babu jimawa. Ransa fal yake da son ganin A'isha, amma ya daure bai takura ba kada ace ya cika rashin ta ido. Sai ma wajen Baba dake ɗaki daya shiga kamar yanda Inna ta bashi umarni dan a kawo masa abinci ya karya. A lokacin ne aka kawo baƙon duniya daya sha wankan ruwan zafi yay luff a cikin showal yana barcin huce gajiya. Baba ya amsheshi fuska da murmurshi yana faɗin, "Baƙon hantsi ne zance kona asubahi". Cikin dariya Inna tace, "Mai tada mutane da asuba dai baƙon hantsi". Dariya Baba yayi kaɗan da faɗin, Kinga yaci suna biyu kenan, KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DODO". Abdul-rasheed dake saurarensu ma na ɗan murmushi da cin abincinsa sai dai yana satar kallon ƙyautar da ALLAH ya bashi ta gefen ido. Baba ya furta, "Masha ALLAH, wannan dai gida ka ɗakko abinka baka tafi kalar dangi Kano ba. Gashi nan kamar ranar aka haifi ubansa kwabo-da-kwabo sai hasken fata na ɗaukar magana na kanawa". Inna ta ce, "A gida kam ya ɗakko, ni kaina tun kan ma a gogeshi nace wannan Abdul-rasheed sak. ALLAH yasa yayo halinsa shima ɗan albarka". "Amin ya rabbi". Baba ya amsa mata yana masa addu'a. Sai da ya kammala ya miƙama Abdul-rasheed shi. Kasa amsarshi yayi saboda kunya. Sai da Baba ya ce, "Ka jimin ja'irin kaya, amsheshi mana ka masa addu'a ka sanya masa albarka. Ga dabino ka tauna ka bashi". Hannu biyu Abdul-rasheed ya saka ya amshi gudan jinin nashi, kuma tsokar jikinsa daya fito daga masoyiyarsa A'ishatul-humairah. Ƙasa-ƙasa ya saki ajiyar zuciya yana kallonsa. Lallai kamaninsa da yaron a bayyane take, Banbanci kawai shi jinkiri ne ɗan a wanni a duniya kuma mai hasken fata irin ta A'isha, shi kuma uba daya fara nisa a gwagwarmayar rayuwa zuwa yanzun. A cikin zuciyarsa yake faɗin (Zakina kazo duniya a ranar da ƙasarsa ke murnar cika shekaru goma da kwana goma da samun ƴanci, jarumin da aka haifa cikin sabuwar ƙasa mai sabuwar fata. A zahiri ƙasa bata san tana buƙatarka ba, amma ina sha ALLAHU sai ka zama wani ginshiƙin riƙeta a yayin girma da ƙarfin ikon ALLAH. ALLAH yay maka albarka, yasa ka zama mahaddacin Alkur'ani da sauran ilimomin littatafan addini, ka zama mai aiki da su bamai karatu kawai da shagala ba. UBANGIJI ya wadata zuciyarka da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) UBANGIJI ya soka damu gaba ɗaya ya yarda da mu. ALLAH yasa ka zama mai jin ƙan iyaye da al'umma, ALLAH ya ɗora nasarar ka akan ta maƙiyanka, ALLAH ya rayaka rayuwa mai tsaho da nagarta, ya shimfiɗa tausayin al'umma a zuciyarka, ya baka zuciyar nema daga halak ya saka maka ƙyamar haramun). Yana kammala wannan addu'a a zuciyarsa ya tauna dabino kamar yanda Baba ya bashi umarni ya sakamasa a baki. Da farko fuska ya yamutse, sai kuma ya fara motsa ɗan bakin nashi a hankali. Inna dake kallonsu cike da tsokana tace, "Anya wannan mai gidan bazai fini kwaɗayi ba". Dariya Baba da Abdul-rasheed suka sanya suma. Inna ta sake faɗin, "To jifa yanda ya lamushe abinsa tsaf." Nan ma dariyar dai sukayi, kafin baba ya saka Abdul-rasheed yayma yaron huɗuba da sunan da yake da ra'ayin saka masa. Nan ma yayi sannan Inna ta amsheshi ta koma da shi. Abdul-rasheed ya sanarma Baba sunan da yay masa huɗubar da shi, Baba ya sanya albarka tare da tambayar ma'anar sunan. Daganan suka cigaba da hirarsu. Duk yanda Abdul-rasheed yaso ganin maijego a yinin ranar bai yiwu masa ba, sai dare bayan sallar isha'i Inna tana ɗakin Baba kai masa abinci ya samu wuff ya shige, dan kuwa zuwa yanzu babu kowa duk matan yayunsa sun koma gidanjesu da maƙwafta sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai ƙannensa biyu ƴammata Nana da Alawiyya. Yana shiga ɗakin ya aike su dan kawai ya musu wayo, a bazata A'isha taji ya rungumeta. Kunya ya sakata fara mutsu-mutsun janyewa. Cikin raɗa ya ce, "Haba Shatuna matar Abdul-rasheed ki barni naji ɗuminki, na samu tubarrakin jego mana. Na rage kewarki ta kwana da kwanaki. Sannu-sannu kinji baiwar ALLAH, ALLAH yay miki albarka, lallai yau UBANGIJI ya azurtani da babbar ƙyauta ta hanyarki, ke mace ce mai daraja da kimar da bata da misali a wajena. Ina fatan kina lafiya babu inda ke miki ciwo ko?". Kanta ta jinjina masa alamar eh. Ya ce, "Alhamdullahi, zuwa safe zan roƙi baba ya bari na kaiku asibiti a ƙara dubaku kinji. Goben kuma in sha ALLAHU saƙo zai isa gasu Inna suma na samun jika mai kama da Babansa, yanzu kin yarda na fiki ƙarfin jini ba". "Ni ban yarda ba, kawai dan ya ɗanyi kama da kai kaɗan kake cika baki". Abdul-rasheed ya yi dariya, yana kallon jaririn da idonsa cike da jin daɗi. "Indo kiji tsoron ALLAH, wato kamar ma kaɗan yayi dani ashe, wannan dai kishi ne kawai kike dani. Amma kowa yaga Zakina yasan photo copy ɗinane ai. Za mu sa masa suna *Haysam*." Karon farko ta ɗan kallesa, "Wannan wane irin suna ne? Karfa ace ka sama ɗanka sunan aljanu". Murmushi yayi da ja mata hanci kaɗan, "Sunane kamar kowane suna, kuma yana da nashi tarihi shima. Fassararsa na nufin (Zaki). Ina fatan nawa Zakin ya tashi da ƙarfin zuciya da jarumta irin ta baradan Zakuna. Yayi nagarta irin ta mutane masu dattako da tsaftataciyar zuciya, mai jinƙai gana ƙasa da shi, mai ƙyautatawa da girmamawa gana sama da shi. Mai kishin ƙasa da son cigabanta, da haka ina fatan ki bani gudunmawa wajen gina tarbiyyarsa da waɗan nan jimlolin, amma ginshiƙinsu ya zama ilimin addini dana zamani ne". Cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, "In sha ALLAHU zaka sameni mai biyayya a gareka. ALLAH ya bamu tsahon rayuwa mu da shi mai albarka". "Amin ya rabbi Matar Abdul-rasheed, sannan Maman *_Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi_*". "Niba mamarsa bace, ga iyayensa nan cike da gida". Ta faɗa tana kauda kai irin na kunya. Dariya yayi shima da sake rungumeta, kafin sallamar su Nana ta sakashi mata sallama ya fito kamar ba shi ba..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 20_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau'in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006

TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun rikiɗe zuwa kwanaki, kwanaki sun haɗu sun zama sati, satittika sun dunƙule zuwa wata, wattani suka haɗa shekara. Shekaru sun cigaba da shuɗawa. Har amarya Yakura ta cika shekara uku a gidan Abdul-rasheed. Bata samu ciki ba har yanzu, hakama A'isha tunda ta yaye Haysam shekara biyu kenan bata samu wani cikin ba. Abdul-rasheed kuwa nata sake samun ɗaukaka a wajen aiki da kasuwancinsa na ɗinki, dan zuwa yanzu ya koyar da yara da yawa aikin tela, kuma Alhamdullah suma suna cin gashin kansu, ga shagon saida kayan ɗinki ya buɗe duk sati Nasiru na aiko masa da kaya daga kano. Wani lokacin kuma yaje da kansa yayo daga nan yayo zumunci ya siyama Inna kayan abinci ya dawo. Zuwa yanzu kusan duk ɗawainiyar zuri'arsa ta dawo kansa ne. Yayima su Baba yayima yayunsa da ƙannensa, yayi ma dangin mahaifiyarsa, yayima dangin matansa. Sannan ya sauke hakkin gidansa. Haysam yaro ɗan shekaru huɗu a duniya, ya tasa abinsa masha ALLAH, kyakkyawa mai lafiyar jiki ga gatan iyaye dana kakanni, ya tashi yaro mai shiru, mai son karatu da tambaya. Wayonsa ya girmi shekarunsa, damma baida surutu ne. Yana da shekara biyar a duniya kwatsam a ɗan tsakanin sai ga A'isha da ciki, ya salam zo kaga murna wajen Abdul-rasheed da Yakura dama su Baba, cikin A'isha nada wata biyu itama Yakura ta fara nata laulayin, ya rabbi, rasa ina Abdul-rasheed zai saka kansa yayi dan farin ciki, dan harga ALLAH yana matuƙar son yara. Kamar yanda A'isha ta fara samun ciki itace ta fara haihuwa, santalelen yaro namiji a wannan karon ma, mai kammani da Abdul-rasheed shima. Ansha shagali yaro yaci suna Ja'afar. Ja'afar nada wata biyu da kwanaki itama Yakura ta sauka, itama dai ta santalo nata namijin mai kama da Abdul-rasheed, shima dai yaci suna Ma'aruff. Haysam cike yake da farin cikin samun ƙanne da suka tashi tamkar tagwaye, dan kuwa ma tagwayen ake kiransu. Su Ja'afar nada shekara ɗaɗɗaya aka saka Haysam makaranta, dan kuwa ya cika shekaru shida a duniya cif. Duk da kuwa kafin ma sakashi makarantar tuni ya fara ɗaukar karatu a wajen mahaifinsa da ma A'isha da Yakura. Dan Abdul-rasheed tsaye yake akan tarbiyyar Haysam, sannan akwai shaƙuwa a tsakaninsu mai girman gaske. Akoda yaushe zaka sameshi zaune a gefen mahaifinsa yana sauraron karatun Alƙur'ani ko labaran tarihi na Annabawa da jarumai. Hakama sauran litattafai dai-dai fahimtar yaro mai irin shekarunsa. Duk lokacin da mahaifinsa ya karanta masa tarihin jarumtar Annabawa data sahabban MANZON ALLAH (S.A.W) irinsu Abubakar As-Siddiq (RA). Abokin ANNABI mafi kusa kuma khalifa na farko, mai haƙuri da sanyin hali Umar Ibn Khattab (RA). Khalifa na biyu, adalin shugaba jarumi kaifi ɗaya. Usman ibn Affan (RA). Khalifa na uku, ya tattara Al-Qur'ani cikin littafi, mai yawan ƙyauta kuma mai sadaukarwa ga bayin ALLAH mabuƙata. Aliyu ibn Abi Talib (RA). Khalifa na huɗu, kuma ɗan'uwan ANNABI, jarumi da baya tsoro sai dai kafirai suji tsoronsa, dan ya basu wuta iya wuta a filin daga, Mijin Nana Fateema ƴar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga su Abdulr-rahaman ibn Awf (RA). Irinsu Sa'ad ibn Abi Waqqas (RA). Talha ibn Ubaidullah (RA). Zubair ibn Al-Awwam (RA) ɗan uwan Ummul Muminin Khadija. Bilal ibn Rabah (RA), mai kiran salla na farko jarumi na gaske. Salmanul-farisi (RA) da ire-iren su da yawa da in lissafosu zamuyi da irin rawar da suka taka a musulunci da tsayawa kusa da MANZON ALLAH mu kammu mun san jarumai ne abin koyi da ba Haysam kawai ba ƴaƴanmu ma ya kamata ace muna basu tarihinsu domin su tashi da burin koyi da su ba zindiƙan wannan zamanin ba da yaranmu ke koyi da su koyi mara amfani da amfanarwa. A ɓangaren hikayoyi yana bashi irin nasu Iliya ɗan Mai Ƙarfi, Jatau Ɗan Mariya, Sarkin Zamani, da makamantansu. Dan a wancan lokacin, ana yaɗasu a gidajen rediyo kamar su rediyo Nigeria da jaridu irinsu Gaskiya tafi Kwabo da sauransu. Irin waɗan nan tarihi da hikayoyi sunyi tasiri matuƙa a zuciyar Haysam, dan har yana ji a ransa yana son yayi koyi da su wajen hidimtawa addini. Sai dai abinda ke saka lissafinsa ruɗewa shine zamanin da yake saɓanin nasu ne, tunda shi bai zo zamanin yaƙe-yaƙe ba. Dan haka sai yayta jerama Babansa tambaya. Abdul-rasheed kuwa baya gajiya da bashi amsa, tare da kawo masa misalai akan idan su anyi yaƙe-yaƙe a zamaninsu shi kuma zai iya zama Ɗan sanda, ko SOJA ko wani dai aikin kaki domin bama ƙasarsa gudummawa. Ba wani fahimta Haysam yake da ƙyau ba, amma hakan na sashi jin eh lallai zai iya hakan. A haka ya fara makaranta sai abubuwansa suka sake faɗaɗa. Bayan yaye ƙannensa Ja'afar da Ma'aruff iyayensa sun sake samun ciki kusan a tare, amma Yakura ma ta riga A'isha a wannan karon, dan haka ta rigata haihuwar ɗa namiji mai kama da ƴan uwansa. Shima dai yaci suna Bilal, bayan wata uku da kwanaki itama A'isha ta haihu mace. A karo na farko Abdul-rasheed ya samu mace, dan haka taci suna Halimatu mahaifiyarsa Iya kenan suna mata alkunya da (Ummie). Itama dai akasha shagalin sunanta. A wannan lokacin ma Yakura ta sa sake yin gwanne kuma, dan Bilal nada shekara ɗaya ta sake samun ciki, dole A'isha ta cigaba da shayar da Bilal da Ummie a tare, aka bar Yakura da laulayin sabon cikinta har ALLAH ya kaishi haihuwa ta haifi mace itama da taci sunan Inna wato Karimatu suna mata alkunya da (Mommy). Bayan haihuwar Mommy babu jimawa UBANGIJI ya amshi ran Baba, jiyyar kwanaki biyu rak. Wannan rasuwa ta girgiza wannan zuri'a, barema Inna data koma kamar ta ruɗe. Haka dai akasha kuka da kai-kawo kowa ya haƙura a ƙarshe. Ashe wata na tafe, dan Inna na cikin takaba itama dai ciwo yay mata tsanani, ta matuƙar sakama kanta damuwar rashin baba, ashe itama ciwo ne na tafiya, itama dai a cikar wata na shida da rasa baba tabi bayansa. Su Abdul-rasheed suka sake gigicewa da ƴaƴanta. Nan ma akasha kuka kowa kuma ya haƙura, shike nan gida ya faɗi, an bar su Abdul-rasheed daga su sai dangi. A lokacin Haysam nada shekara goma sha ɗaya a duniya. Yana primary 5, yana shirin gamawa kenan ma, tunda aji 5 ce a lokacin 1983. An gama kukan rasuwar su Baba da Inna babu jimawa itama mahaifiyar Yakura ta rasu, haka suka kwasa sai Maiduguri. Satinsu guda suka dawo ko muce A'isha da Abdul-rasheed suka dawo tare da yara. Yakura sai data ƙara kusan sati biyu ma sannan ya dawo. A lokacin A'isha ta sake samun ciki, cikin daya dinga bata matuƙar wahala, daga ƙarshe ma ta haifeshi a bakwaini, har sai da aka sakashi cikin kwalba na wasu watanni, ita kuma tasha jiyya tamkar bazata rayu ba, mafi yawan mutane idan suka je dubata gani suke kafin su ƙaraso gida za'ace A'isha ta rasu. Abin birgewa kuma Yakura ke jiyyarta kai bakace kishi bace ba sam. Haka dai tasha fama tsahon watanni kafin ALLAH ya bata lafiya ta miƙe tamkar ba'ayi ba, dan kafin cikar wata biyu jikinta ya murje sarai harta fara dawo da ƙibarta. Kamar jira sai ita kuma Yakura ta shiga nata sabon laulayin cikin. A yanzu dai Abdul-rasheed nada ƴaƴa bakwai a duniya. Haysam, Ja'afar, Ma'aruff, Bilal, Ummie, Mommy, sai autan A'isha Ammar. Family ya haɗu sai dai Alhamdullah. Ga kuɗaɗe Abdul-rasheed na samu na ban mamaki, sai dai baya tarawa kullum cikin hidimar ƴan uwa yake da ƴaƴansu, kai hatta maƙwafta da abokai cin arziƙinsa suke yi, dan mutum ne mai ƙyauta da hidima. Ga dai kuɗi ana wasa da su, amma idan ka cire gidan da yake rayuwa bai ajiye kaddarar komai ba. Hakan kuma bai taɓa damunsa ba bai taɓa kuma damun matansa ba. Ba shi kawai ba su kansu sun koya daga alkairinsa, ko baya kusa sukan yi a madadinsa da ɗan abinda yake basu da sana'o'in su duk da kuwa ƙananu ne. Abdul-rasheed bai taɓa sayen kaddara koda ta fili ya ajiye ba balle gona idan ka cire ta mahaifinsu da yake nomawa, bayan rasuwarsa kuma aka raba musu gado, daya tashi sai ya barma ƙannensa da suke ɗaki ɗaya ma kason sa. Dan a lokacin ne autan ɗakinsu ke shirin yin aure, shima dai ya gado Abdul-rasheed duk tsawon lokacin nan yana yawon karatu ne, daga ƙarshe dai zaiyi aure a yanzu cikin wannan satin. Auren daya taka rawar gani mai ban tsoro da razanin zuciya a zukatan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi dama al'ummar anguwa, kai harma duk wanda yasan wannan sunan wannan aure ya kawo masa tarihin da bazai manta da shi ba.........✍🏼

Shin miya faru ne a wannan aure daya zame ma wannan zuri'a tambari da bazasu manta ba? Wane ajiyayyen tarihi wannan aure zai bari haka?🥲. Kudai kumuje zuwa dan har yanzu a shinfiɗa muke. Cakwakiyar da shagulgula na gaba🏃🏼‍♀️.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 21_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.......Tabbas an ɗauro auren Umaru lafiya a garin Barno, dan kuwa shi a can ya ɗakko tashi matar da suka haɗu a wajen karatu a Zaria. Su Abdul-rasheed sunyi gangami sun halarci wannan aure a sabbin motocin daya saya musu shi da yayunsa biyu, akan suma sauran zuwa ƙarshen shekara in sha ALLAHU zai saya musu nasu, sannan ya biya hajji zasuje shi da Babban yayansu. Amma rayuwa bata da tabbas, a yayin dawowarsu Bauchi motar Abdul-rasheed tayi haɗari, a ciki kuma shine da yayansa na uku a ciki, sai abokansa biyu da Haysam. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, haɗari ne mai gigitarwa da tada hankalin wanda ya gani, dan kuwa babbar mota ce ta hayesu tsaf. A take ɗaya a abokan Abdul-rasheed da Yayansa suka rasu, dan kuwa sune a gaban motar, abokinsa driver, yayansa a gefensa. Sai Abdul-rasheed da ɗayan abokin da Haysam dake tsakkiyarsu a baya. Wani hikima ta UBANGIJI sai akai kamar anyi wurgi da Haysam ta tagar motar, dan can waje gefe aka tsuntoshi babu rai, yayinda nan su Abdul-rasheed mota ya danne su, shi rabin jikinsa a waje ƙafafunsa zuwa ƙugu na ciki ƙarfen mota ya rabasu kaɗan ya rage ƙugunsa ya rabu da gangar jikin. Yana kuka da kiran sunan ALLAH yana kuma ambatar sunan Haysam da roƙon mutane su taimkesa su duba masa yaronsa karya mutu. (ALLAH sarki ɗa da mahaifi kenan😭, yana cikin azabtuwa amma bata kansa yake ba. Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭 🙏🏼, ka yafe musu laifukansu ya rabbi😭😭). Da ƙyar aka iya zaro su Abdul-rasheed a wannan mota, akai asibiti da su. Kafin ma a isa ɗayan abokinsa shima ya cika. Shi ko sai da yay kusan awa guda ma likitoci nata kai-kawo a kansa kafin ALLAH ya amshi abinsa. Wannan rana dole ya zama ranar ruɗani da ahalin Abdul-rasheed bazasu manta da ita ba a rayuwarsu. Ranar da ta raba su Haysam da mahaifinsu, ta zo cikin rashin shiri. (Wato mutuwa! Mutuwa! Mutuwa nada tashin hankali ƴan uwana, mutuwa nada gigita ƙwarai da gaske, wlhy bazamu gane wacece mutuwa ba sai randa tazo kammu. Wane shiri kai mata, wane shiri kake mata? Ka kammala baka kammala ba ko bakama fara ba wlhy sai tazo, zuwan da babu ɗaga ƙafa balle jiranka koda na sakan ɗaya danka kammala abinda ka fara😭😭).

Mata ƴan biki nata kai-kawo anan Bauchi, sai dai jikin A'isha dana Yakura duk a sanyaye kamar marasa lafiya. Ga yawan faɗuwar gaba da suke samu da nauyin zuciya. Ita Yakura sai kowa ke ɗauka ciki ne. Itako A'isha ganin tasha jiyya bata ko jima da miƙewa ba sai kowa ke mata uzirin da sauran nauyin jiki. Sai dai ba haka bane ba, mutane kuma basu gane ba haka bane sai lokacin da labari ya iso cikin Bauchi, tun anayi ƙasa-ƙasa kada su A'isha su fahimta lokacin ma da ran Abdul-rasheed har dai ta fasu bayan rasuwarsa. Dan dole aka kwaso gawarwakinsu huɗu reras idan ka cire Haysam ɗan shekara goma sha ɗaya dake gadon asibiti likitoci na ƙoƙarin ganin sun ceto tashi rayuwar. Hakama matar Ayuba Yayan Abdul-rasheed dake fama da tsohon ciki duk tayi sukuku. A lokacin da aka shigo da gawar Abdul-rasheed data Ayuba rawa jikin A'isha da ƙus-ƙus ɗin mutane ya fara shiga kunnenta ya fara. Cikin ɗimuwa ta fito daga ɗakinta batare data fahimci inama take ajiye ƙafa da ɗaukewa ba ta durƙushe a gaban gawar mijinta da aka shimfiɗar a ƙofar ɗakin nata, hawaye na zuba kamar ruwan sama da ba ya ƙarewa. Hannunta na karkarwa ta kaishi kan babbar rigarsa da aka rufa masa dake jiƙe da jini ta yaye a hankali, fuskarsa dake da ƴan ƙananun raunuka ce ta bayyana, sai kawai ta tafi luuuu ta kife akan fuskar tashi ta sume musu. Dai-dai faɗuwar Yakura itama data fito daga ɗakinta a guje, ita kam jini ne ya ɓalle mata abinka da mai ciki. Ga matar Ayuba can ma ƙudar dole ta sameta. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ya rabbi ya rabbi mun tuba, mun tuba ya ALLAH 😭😭. Gida ya ɗauki koke-koke da ƙyar ake tsawatama mutane. Yayinda aka zubama A'isha ruwa a jiki ta farfaɗo, Yakura kam dole Inna Salame ce a kanta ana ƙoƙarin tsaida jinin daya ɓalle mata. Haka aka shigar da Abdul-rasheed ɗakin A'isha da Ayuba cikin jini babban Yayansu da mai bi masa sukai musu wanka aka shiryasu a tufafinsu na gaskiya. Tufafin da kai da ni suke jiran mu ma. Duk yawan kaya masu tsadar man da kika tara bango guda na drawer da wanda ka tara duk nan za'a barsu dama anan muka samesu. A naɗemu a wannan yankin farin ƙyalle tal kamar yanda a yau akama Abdul-rasheed da Ayuba. Haka ma sauran abokansa biyu an kaisu nasu gidajen ana musu nasu shirin suma...

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull