Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 9

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 9

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 9: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 9. ......Aiko dai akwai aikin babba ma kuwa. Dan kuwa da asuba dai…

4,181 words

......Aiko dai akwai aikin babba ma kuwa. Dan kuwa da asuba dai koda Inna tasa su Alawiyya su rakota gida suna juyawa suka fita tai alwala sai ta shige ɗakin girkinsu dake a tsakar gidan, da yake ba girkin ta taɓa yi ba babu komai a ciki sai icce da aka tara da kayan ruwa da abubuwa da take kaiwa ciki ta aje, anan tayi sallar sai da gari ya waye sannan yaji motsinta zata fara shara. Fitowa yay daga ɗakinsu yana kallonta. Dan massalaci ma kasa zuwa yayi saboda ciwon daya kwana da shi na ciki. Tana ganinsa ta ajiye tsintsiyar zata gudu ya ce, "Kinga yi haƙiri tsaya. Cigaba da shararki in dai nine ma na koma". Ya koma cikin ɗakin ya ƙyaleta. Baki ta tura itama, ta ɗauki tsintsiyar ta cigaba da sharar. Haka yau ma sukai wannan yini tana masa wasan ɓuya. Da yaga ta takura a gidan sai ya lallaɓa ya fita ya koma tsohon ɗakinsu dake soron gidansu ya kwanta a can. Abinci ma aikowa yayi aka amsa aka kai masa can duk da kuwa daga gidansu aka aiko. Hajjaju amarya Indo ba jiya taji daɗin gudu ba, yau ma ana yin sallar magriba ganin ya shigo yace zaiyi wanka a lokacin dan bai samu yayi da rana ba, yasan kuma bazai iya barci ba in baiyi ba. A ɗarare takai masa ruwan bayi, yana shiga ta sulale zata gudu, sai dai ta samu ƙofa a rufe ta gidan. Kamar zatai kuka ta juyo ta dawo. Amma mi sai dabarar shigewa ƙasan gado tazo mata. Dan haka sauri-sauri ta shimfiɗa tabarma ta kawo wasu ƙorai da babu komai tasa a gaba-gaba ta yanda bazaka kawo da mutum a ƙarƙashin gadon ba ta shige abinta ta kwanta ko tsoro ma bata ji. ALLAH sarki bawan ALLAH Abdul-rasheed, hankalinsa kwance ya fito yasan dai bazata iya buɗe gidan ba, koda ya shigo ɗakin bai ganta ba yayi tunanin tana inda ta maƙale ɗazun da asuba. Sai ya ajiye kayan wankan yaje ya lallasota ta dawo, amma mi babu ko alamarta, da sauri ya nufi soro kofa a rufe yanda ya bari, ya sake dawowa ciki neman duniya ba A'isha. Mamaki da tsoro suka kama shi, to ta ina tabi ta fita? (Katanga), zuciyarsa ta ayyana masa. Zama yay yana dafe kansa kawai, dan wlhy kunya yake ji bazai iya zuwa gidansu ba yau kuma. Idan jiya basu gano shi ba ai yau sai su gane. Haka ya haƙura ya miƙe ya tafi massalaci sallar isha'i. Duk abinda yake tana jinsa, daya fita kuma bata kawo a ranta ya fito ba ta fice gidan ta cigaba da kwanciya a ƙarƙashin gadon har barci yay awon gaba da ita anan. Bayan sallar Isha'i Abdul-rasheed ya dawo, haka ya zauna shiru zuciyarsa na masa saƙe-saƙe, gefe yana ƙalubalantar kansa da rashin haƙurinsa, dan ƙila da bai mata abinda yay matan ba da hakan bata faru ba. Ga tsaraba ma ta kasa zama ta duba sam. In sha ALLAHU zai daure ya riƙe kansa ya bita a hankali. Da wannan tunanin ya ɓingire. Da asuba fitsari ya kama A'isha har yana neman zubowa, dan haka ta fito cike da sukur-sukur ɗin daya tada Abdul-rasheed, dan haka ya haska fitila da tunanin ko ɓera ne ya shigo musu. Amma yana kunnawa ya haske A'isha na fitowa a ƙasan gado. Mamakin duniya ya ishe sa, ya zuba mata ido kawai. Itako tayi tsuru-tsuru kanta a ƙasa tana matse ƙafafu dan fitsarin neman kufce mata yake. Fahimtar hakan da yayi ya saka shi sakin murmurshi, muryarsa a sauƙaƙe yace, "Amshi fitila kije kiyi". Da sauri ta amsa kuwa ta fice. Shima ya miƙe ya sauka a gadon yana sauke ajiyar zuciya. Amma lallai yarinyar nan ta cishi wasa jiya. Yanzu nan tana ƙasan gado dama duk bulayin daya dinga yi. Wato ita dai mace duk ƙanƙantarta akwai wayo da dabara. Da wannan tunanin ya fito da buta a hannu, baice mata komai ba ya ɗauki fitila data ajiye zata fara alwala ya wuce bayi, sanda ya fito ta gama zata wuce. Dan haka cike da lallashi ya ce, "Dan ALLAH ki zauna a gida to kada kije ko ina na dawo na baki tsarabarki da saƙon Inna, kada yazam akwai abin lalacewa a ciki kinga zai lalace". Kanta dake ƙasa ta jinjina masa. Sannan sum-sum ta shige ciki. Shima yay alwala ya fita. Koda ya dawo da wannan buɗe tsaraba yaja ra'ayinta, har hantsi ya fito ya fita ya sayo mata shayi, sai kuma ga kayan kari Inna ta aiko. Da lallaɓa, da lallashi da kwantar da kai ya samu wannan yini dai aka yi shi lafiya. Da dare kuma ya kafa ya tsare ya nuna mata shi tayi duk yanda take so. Ganin yaƙi kulata da abinda take gudun a yinin ma ko kusa da ita bai zauna ba balle ya taɓa mata hannu sai ta haƙura ta kwanta a gadonta, amma acewarta da ido ɗaya zatai wannan barci. Da yake shi barcin ya fita wayon bata ma san ya kwasheta ba har wanda take tsoron ya zauna a bakin gadon kusa da ita yay mata addu'ar barci sannan ya koma nashi gadon. Wannan sabon yin biris daya ɗauka ya kawo masalaha a tsakaninsu, itama ta sake jiki suka koma kamar da. Sai dai kwana kusan shida kuma yaji fa yana neman halaka, a daren ya kasa haƙuri ya sake maimaita na wancan daren, koma muce abinda yafi na wancan daren dan ya sameta fiye da waccan ranar, sai dai kuma ta fitgice masa dole ya barta batare da cimma buri ba. Daga nan ne fa ta sake birkice masa. A daren washe gari kuwa bata kwana a gidan ba, ta sake gudawa gidansu cikin su Nana ta kwana. Ita kanta Innar da su Nanar basu farga da ita ba sai da asuba da Inna ta tashesu suyi salla. Rasama abin faɗa tayi, yau ma sai tace su Alawiyya su rakata gida kawai. Kwanakin da suka biyo baya har huɗu A'isha bata daina yo tsere ba. Abdul-rasheed kuma ya zuba mata ido, hasalima ya koma maida hankalinsa batun buɗe wajen ɗinkinsa ya ƙyaleta. Hakama Baba yana sane A'isha a gidan take kwana, amma bai ce komai ba sai dai yayi murmushi kawai. Koda Inna tai masa magana a cikon kwana na huɗun sai cewa yay, "To mizance, tunda shi bashi da haƙuri da kawaicin barin yarinya ta sarara kaɗan ma kenan. Ke kuwa naga kema haka kika dinga yi min Karima, ƙarshe sai da Baba ya rakoki da tsumagiya gidan nan saboda can kike zuwa." "Ai kai ka jika Malam, ana maganar arziƙi saika dinga sakko wadda ba'a tambayeka ba. Amma ka bani dabara nima da tsumagiyar zan korata yau. Ina laifin yaron nan ai yayi kawaici ma. Aure wata shida haba ai a yaba masa. Abdul-rasheed da haƙuri da zurfin ciki. Su sauran ƴan uwansa wa yayi wannan haƙurin. Tijjani ma da yafi kowa rashin ta idonsa ko tsallake rana yayi". Haka ta fita tana sababi. Baba kuwa sai murmushi yake abinsa kawai...

Washe gari kuwa Inna ta shiryama A'isha tsaff, dan yanzu dai sune iyayen tunda babu wani nata a kusa. Kuma a wannan zamanin nasu na adalci ɗa na kowa ne. Babu wani surukutar mugunta ga matar ɗa da uwar miji, yanda suke ma ƴaƴansu haka suke ma matan ƴaƴansu saboda adalci da ƙyaƙyƙyawar zuciya, haka suma surukan suna ɗaukar iyayen miji iyayensu ba irin na yanzu ba da suke ganinsu kamar koshiyoyi. Kamar ko yanda ta saba ana cikin sallar isha'i sai gata ta shigo soron gidan da sanɗarta. Caraf Inna dake a soron ta dalleta da Torchlight, A'isha tai tsaye cak tsuru-tsuru da idanu, sai kuma ta duƙa tana gaida Inna dake tsaye kawai tana kallonta. Batare da Inna ta amsa mata ba ta ce, "Juya muje". Kallonta A'isha tayi kamar zata fasa kuka, Inna ta haɗe fuska kuwa ciɗin-ciɗin. Sum-sum ta nufi ƙofa dan tasan dai yau ruwa ya ƙarema ɗan kada kam. Haka Inna ta sata a gaba har gida da ƴar tsumagiyarta a hannu, badan ta daketa ba sai dan ta tsoratata. Karo na farko da Inna tazo gidan kenan, suna isa ƙofar ɗaki taci karo da buta, ɗauketa tai ta maida gefe suka shiga ɗakin. A mamakinta sai suka samu Abdul-rasheed a ciki kwance a tsakar ɗaki kan tabarma. Ashe ma yana gidan ta fita, baida lafiya, amma saboda wauta saita wayance da ɗaukar buta kamar zata fitsari daga nan ne ta sulale, butar ce Inna taci karo da ita yanzu da suna shigowa. Ganin Abdul-rasheed ɗin a ɗakin kuma yasata fahimtar ma'anar zaman butar a waje. Tashi yay da ƙyar cikin dauriya yana ma Inna sannu da zuwa. Inna dake binsa da kallo ta ce, "Lafiya kuwa ana salla kana gida Abdul-rasheed?". "Ba komai Inna kawai banjin daɗi ne, shiyyasa ma ban shigo gidan ba ɗazun da yamma". "Subahanallahi, amma shine ja'irar nan ta sulalo ta taho can. Nikam ya zanyi da A'isha jama'a. Mijinki na kwance a gida babu lafiya amma kina guduwa wani waje. A'isha wane haline wannan? Idan baki taimaki mijinki ba wa zaki taimaka. Kina son ki mutu a saki wuta ne? Ko kuwa na shirya naje Kano na gayawa Innarki halin nan da kike yi?". Cikin sauri A'isha dake kuka ta shiga girgiza kai. "Dan ALLAH Inna kiyi haƙuri bazan ƙara ba wlhy na tuba". "A'a nasan zaki ƙara A'isha. Wata nawa ana abu guda. Ai gara dai na tafi Kanon nan tunda mu baki ɗaukemu iyaye ba. Shima Abdul-rasheed ɗin ne ya ƙyaleki, sai kace wadda tafi ƙarfinka. Kafi son kaita fama da ciwo sai ka halaka kanka ne......" Inna dai nata sababi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Taima A'isha dake durƙushe tana kuka, taima Abdul-rasheed dake zaune kansa a ƙasa kunya da ciwo duk sun dabaibayesa. Sai da tai musu tas sannan ta wuce tana sake jaddama Ai'sha idan ta sake ganin ƙafarta a waje koda da rana ne ma zuwa can gidan saita zane ta, kuma sai ta tafi Kano ta sanarma Innarta. A'isha tasan aka sanarma Inna ai taga boni, dan haka ta sake rikicewa, dan Innarsu akwai zafi sosai tana da faɗa, duk da tana jansu a jikinta idan sukai ba daidaiba bata raga musu, balle ma ita ɗin nan da take kamar ƴar fari. Dan kafin ita Inna ta haifi yara kusan biyar suna rasuwa ne itace ta fara zama, a tsakanin ta da Bashir ma wani ya rasu shiyyasa ta bashi kusan shekara biyar........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 17_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau'in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006

TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Bayan ficewar Inna ɗakin yay shiru, sai shashshekar kukan A'isha daya cikashi, shi dai Abdul-rasheed yana zaune har yanzu kansa a ƙasa yana saurarenta. Sai da yaga ba dainawa zatai ba sannan ya ɗago cike da ƙarfin hali dan da gaske baida lafiya ya zuba mata idanunsa dake jajur irin na mai ciwo. Muryarsa da sanyi sosai ya ce, "Kibar kukan nan ya isa haka, ko kina son kanki yay ciwo ne?". Kanta ta girgiza masa alamar A'a. Ya ce, "To share hawayen ya isa. Kin daiji abinda Inna tace. Ke ko tsoro ma baƙyaji kiyita kai kawo a tsakanin dare. A'isha auren soyayya mukayi bana ƙiyayya ba. Mu da kanmu muka zaɓi juna muka kuma so mu zama ma'aurata ba haɗamu akai ba balle muce an mana auren dole ne. Kina da muhimmancin da bazan iya bari wani ya cutar dake ba balle ma ni kaina. Abinda kike gani yana faruwa tsakanina dake shi ne aure. Ina ga dole zamu fara karatu daga gobe, ba karatun Alkur'ani kawai kike buƙata ba a rayuwa da ibada, duk da Alkur'ani yazo mana da komai, amma dole sai mun haɗa da hadisi sannan zamu san su wanene mu da abinda ya kamata muyi. In sha ALLAHU hakan zai sa ki fahimci minene auren ma kansa". Kanta ta jinjina masa, sai kuma cikin rawar murya ta ce, "Kayi haƙuri bazan sake ba. Kuma dan ALLAH ka bama Inna haƙuri, sannan kace dan girman ALLAH kada taje Kano ta faɗama Innata, ALLAH idan ta gaya mata zata iya zane ni, kuma tayi fushi da ni". Ƙaramin murmushi yayi, a ransa yana ayyana ga tsoro ga rashin ji. A fili kam sai yace, "Shike nan zan bata haƙuri. Nikam baki min laifin komai ba. Tashi ma kije ki wanke idonki. Kinyi sallar isha'i kuwa?". "A'a". "To maza yo alwala kizo kiyi. Sai ki matsa min lemon tsamin can a ruwan zafi ai da saura a cikin flaks ɗin ko?". "Eh, tun wanda kasha shayi ɗazun ba'a ƙara ɗiba ba ai". Yauwa to yi sallar sai ki haɗa min wani shayin nasha kinji. ALLAH yay miki albarka ya shirya min ke ki daina haura katanga, dan nasan yanzu dai Shatuna ta girma, ta girmi haura katanga ta barma ƴan baya ko?". Kanta ta jinjina masa, sai kuma ta ce, "Nifa bana haura katanga ALLAH. Kullum ta ƙofa nake fita". Dariya yayi yanzu kam. Ya ce, "Oh oh matar Abdul-rasheed tafi Abdul-rasheed wayo". Dariya tayi itama tana rufe fuska da tafukan hannunta. A haka ta fita a ɗakin, shiko yana binta da kallo da murmushi...

Bayan A'isha tayi salla ta haɗa masa shayin lemon tsami ya sha. Ita kuma ta haɗa mai madara dan tace bazataci tuwo ba. Shi kuma bazai iya fita sayo mata nama ko kifin daya saba kullum ba. Dan bayi ma da ƙyar ya iya fita yaje. Hira ya dinga janta da shi yanda suka saba. A hankali ta saki jiki tanata masa dariya, dan labarin ƙannenta su Bashir yake ta bata da yaran gidan su Nasiru. Sai da yaga ta fara hamma sannan yace taje ta kwanta. Maimakon ita shi zaman lalubo litattafan da zai fara mata amfani da su ya shiga yi. Dan dama yana da burin hakan a kanta tuni. Sai da ya ajiye komai sannan yay tashi kwanciyar a ƙasa ma yau, dan bai hau gadon ba. Washe gari kamar yanda yay alƙawari hakan akai. Da hantsi bayan ta kammala aikin gida ya fita ya dawo sukai zaman karatu. A ɓangaren Alkur'ani kam A'isha Alhamdullah, sai gyara na abinda baza'a rasa ba dai. Dan haka ya fara mata da sauran littatafai. Abin nasu kamar wasa sai ya fahimci tana ɗokin karatun, cikin kwanaki kaɗan kuma ta maida hankali. Har takai yanzu karatun ma yafi cinye lokacinta fiye da biyema yara masu shigo mata da rana. Sun ja kwanaki suna karatun yana buɗe mata komai yanda zata fahimta da ƙyau, abinda yake na kunya taita sinne kai sai yayi kamar bai ganta ba ma, a dalilin wannan karatun ya fahimci A'isha ko jini bata fara ba ashe. Eh lallai aiki babba a gabansa, dole kam ta dinga masa gudun fanfalaƙe ashe. Ganin tana fahimta ya haɗa mata da karatun boko, sosai al'amarin ya fara bashi mamaki, dan gaskiya Alhamdullah tana da brain na fahimtar abu da wuri, gata kuma da nacin son karatun. Satin su uku da fara wannan karatu al'amarin UBANGIJI A'isha ta samu baƙuncin prioud ɗinta a bazata, babu ciwon mara babu komai. Da yake ya karantar da ita hakan sai bata ruɗe ba, sai ma matsananciyar kunya data sata ɓoye masa, ta shiga kici-kicin gyara kanta ita kaɗai. Sai dai ba'ai nisa ba tun a yinin ya ganota. Haka ya zaunar da ita ya sake mata dalla-dalla akan abinda ya shafi jinin haila, ya kuma sake koya mata yanda zata dinga tsaftace kanta da ƙyau. Wato ilimin addini duniya ne, dan kuwa babu mace ƴar gata kuma sarauniya irin mai ilimin addini, mata mu farka dan ALLAH musan kammu, ba'ace karki boko ba, amma ki tuna shifa bokon nan amfaninsa nada iyaka, shiko wannan da muke ɗauka ƙauyanci da shine za'a mori rayuwa mafi tsada dake can gaba garemu. Ba zaki gane wannan zancen ba sai randa mala'ikan mutuwa ya ƙwanƙwasa miki ƙofar amsa kiran ALLAH wlhy😭. Kwanaki uku A'ishatul-humairah tayi, a kwana na huɗu tai wanka abinta ta koma salla, sai da ta koma sallar ne ma Abdul-rasheed ya fahimci baƙo dai ya tafi, ya zaunar da ita ya mata tambayoyi akan yanda ta tsaftace kanta. Tana ɓoye-ɓoyen fuska ta sanar masa da komai. Shi dai nashi dariya ne. Fara ɗinkinsa da samuwar aikin koyarwa ta rage masa zaman gida, sai dai kuma a ɗan tsakanin ya gama shiryama tsuntsuwarsa. Dan kuwa a wani dare na juma'a ya maida Shatunsa cikakkiyar mace. Ya dai sha rigima mai saka ciwon kai da rakinta. Haka yayta lallashi da riritawa, dan sai da ya koma komai shike mata a wannan yinin. Ya kuma sanarma Inna cewar A'isha ta kawo mutuncinta, bawai da baki ko gatsal ba, a'a ya sayi abubuwa ne ya kai ma Innar, kansa a ƙasa ya furta, "Saƙo ne da za'a kai can gidansu A'isha, ai musu godiya da karamci". Wannan batu nashi kai tsaye ya fahimtar da Inna ina ya dosa, dan wannan al'adace mai girma da a wannan lokacin baka da dalilin ɓoyewa kodan mutunta matarka da kimanta iyayenta a idon naka iyayen. Sosai Inna ta nuna farin ciki tare da sanyawa A'isha albarka matuƙa itama. Shi dai Abdul-rasheed kansa a ƙasa yana amsawa a laɓɓa. Ƙanwar mahaifinsu da suke kira Gwaggo Gaji aka aika aka kira, itace taje can wajen A'isha domin bata kulawa. Anan kuma Inna ta shiga haɗa garar arziƙi itama bayan ta sanar da Baba wannan daddaɗan labari. Ba A'isha kawai aka shiryama garar arziƙi ba, harda mutanen Kanon dabo. Dan abubuwa sosai aka haɗa aka tada ɗan aike tun daga Bauchi har Kano gidansu A'isha shaidar ta kawo mutuncinta gidan aurenta, hakan kuma shine zai ƙarama iyayenta nutsuwa da farin ciki. Dan kuwa abin zai baka mamaki, sanda ɗan saƙo yaje da wannan albishir guɗe-guɗe aka dinga yi a gidan Inna. Daga ƙarshe aka raba kayan arziƙin da aka aiko aka dinga kaisu gidajen maƙwafta da abokan arziƙi. Suko sai gasu suna shigowa taya Inna murna da barka da arziƙi. Dan kuwa ashe anata ƴan ƙananun magana tun bayan auren A'isha cewar ba'aji komai daga dangin miji A'isha takai budurci ba, ashe-ashe angon mai kunya ne da kamun kai. Sai ko aka shiga yabonsa dan ya nuna dattako mai girma. Ita kanta Inna ranta fes, dan harda hawayenta tayi sosai a wannan gaɓar. A'isha ta gama biyanta, ita kaɗai ƙwalli ɗaya mace dama gareta.

________★

Anan Bauchi ma dai A'isha taga gata tako ina daga gidan su Abdul-rasheed dama dangin mahaifiyarsa. Dan labari har Maiduguri, haka suma kuwa suka haɗo garar arziƙi aka kawo mata har Bauchi. Bawai ana zancen bane haya-haya, a'a cikin hikima ne irin ta manya kawai. Kamar dai yanda Abdul-rasheed ya nuna alama ga Inna ta hanyar sayen abubuwa masu daraja yakai yace a aika su Kano gidan su Ai'sha ai musu godiya irin ta mutuntawa. Bayan ƴan kwanaki ta miƙe, sai dai ƴar kunya tsakaninta da Abdul-rasheed, shi dai nashi lallashi da lallaɓa. Gashi yanzu an bata girki, zata fara girki da kanta a gidanta an daina kawo mata daga gidan surukanta kuma. Wannan shine tushe kuma mafari, na fara gina sabuwar ƙyaƙyƙyawar rayuwa tsakanin A'isha da Abdul-rasheed data ninka ta farkon aure matuƙa. Kuɗi suka fara shigo masa ta ɓangaren albashinsa na aiki da harkar ɗinkinsa. Lokacin da suke cika shekara ɗaya da rabi da aure ya gyara gidan Baba sannan ya ƙara gyara nashi, ba wani gini ne sabo kona zamani ba, a'a buhunan siminti ya saya aka shafe ko'ina ginin laka ya ɓoye. Bai tsaya anan ba suma ƴan uwansa ya fara bin nasu gidajen yana gyarawa. Ya kuma dinga ƙara musu jari a harkar sana'o'in su. Bai tsaya anan ba ta kai har haihuwa idan anyi musu shine mai ɗawainiyar komai, yaransu kuwa ya ɗiba yakai makaranta. Baba kuwa ya hanashi yin komai hatta zuwa gidan Sarki yin hidima. A haka rayuwa ta shura suka cika shekara biyu cif da aure, sai kuma lokacin ne ALLAH ya bama A'isha ciki. Abdul-rasheed yayi farin ciki ƙwarai da gaske da wannan ciki, hakama A'isha da sauran dangi, sai dai kunya tanasa su ɓoye a gaban kowa sai sun keɓance. A shekarar 1972 data kasance shekarar cikar samun ƴancin ƙasa goma cif, auren A'isha da Abdul-rasheed cikin na uku cikin jikin A'isha ya fara haramar fitowa duniya, domin kuwa ya tsufa sosai, dan ma abinka da cikin fari ga ƙuruciya harkokinta take kai tsaye kamar bata jin nauyinsa, sai dai Abdul-rasheed shi yayta tausayinta da hanata wasu abubuwan musamman idan yana gidan, dan wani lokacin koya hana daya fita take tashi tayi, idan ya dawo yana faɗan ba yace ta bari ba, sai ta marairaice tace ba ita tayi ba su Alawiyya ne, dole zai haƙura yay shiru..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 18_

__________________

LADY'S BEAUTY PALACE

SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S BEAUTY PALACE

ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻

Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Lace Hijabs Supplements Kayan yara Saloon Kunshi na salatap Dana zane Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko Sari

Zamuyi promo din kayan mu na hijabs da Kuma zuma

Address bayan gidan drugs katsina State

Kayan mu masu inganci ne sosae

Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯

Whatsapp or call 08169307477

Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)

Instagram Hajara Rabiu

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull