Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 8
Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 8: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 8. .........Abdul-rasheed bai dawo ba sai bayan sallar isha'i.…
4,153 words
.........Abdul-rasheed bai dawo ba sai bayan sallar isha'i. Yana shigowa Khadijah tai musu sallama ta wuce. Shi kuma ya zauna yana zolayar A'isha akan yau dami-dami tayi da baya nan?. Sai da ta ajiye masa abincin da aka kawo daga gidansu gabanshi sannan ta zauna tana bashi labari cike da farin cikin tabbacin yau ɗin ya mata daɗi. Shima sai yaji nashi farin cikin ya sake girma, da jin damuwar yanda zai tafi ya barta nan da kwanaki kaɗan dan zai koma Kano makaranta. Dole dai ya ture tunanin a ƙarshe ya lallaɓata sukaci abincin tare, daga nan suna hira yaga ta fara hamma yace taje ta kwanta. Shi kuma ya ɗakko kayan karatunsa ya fara nazari. Daga baya shima ya kwanta a nashi gado batare da yau ma yama A'isha komai ba. Kwanakin da suka biyo baya sun cigaba da gudana ne cike da shaƙuwa a tsakanin Abdul-rasheed da A'isha. Domin kuwa cikin hikima irin ta masu ilimi yanata jan ra'ayinta da janta a jiki kamar aboki tana sake sakin jiki da shi. Gayyar yaranta kuwa na anguwa kullum tare da su take yini, a haka suka cika kwanaki goma Abdul-rasheed ya shirya komawa Kano dan kwanakin hutunsa sun ƙare. Gashi yana ƙarshen zango baya buƙatar wasa da karatunsa. A'isha taci kuka sosai har ya dinga jin kamar shima ya tayata, daga ƙarshe dai da ƙyar ya lallasheta ya tafi ya barta zukatansu cike da ɗaci. A'isha ta koma sukuku da ita, kuma yanzu tana yini ne kawai a gidanta, amma da daddare can gidan su Abdul-rasheed take zuwa ta kwana. Da safe sai ta dawo gidanta sai kuma dare taje can. Tun tana tsangwamar kanta harta saki jiki saboda ƙannensa biyu da suke kusan sa'anni ƴammata. Ga Inna ba ruwanta, faɗanta kawai dai idan anyi ba daidai ba. Sosai A'isha take saka hannu suyi aikin gida tare da su Alawiyya, idan zasu fita ne dai Inna ke hanata binsu, ko in zasu tafi makarantar allo. Tun abin na sakata kuka harta fahimci hakan fa shine ƙa'ida da doka, tunda sauran matan yayunsa bataga suna fita ko'ina ba sai da dalili, dan haka sai ta saki jiki. Tun A'isha na ƙirga kwanakin tafiyar Abdul-rasheed harta bari, kwanci tashi sai gashi da watanni har huɗu. A lokacin ne Baba ya aika masa wasiƙar tunatarwar yazo gida ko kwana biyu yayi, koya manta yana da iyali ne yanzu. Ya kamata ya dinga sara yana duban bakin gatari. Wasiƙa ta isa ga Abdul-rasheed. Kuma ya gamsu da tunatarwar Baba, sai dai baya son zuwa gida ne saboda kaucewa abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke raya masa akan A'isha. Yana son ya bata damar ƙara fahimtar kanta har gaɓar kammala karatunsa daya rage watanni biyu rak. Dan haka ya maida saƙon wasiƙar baba da amsar ban haƙuri data neman uzirin bashi damar kaiwa zuwa watannin da suka rage masa. Acewarsa karatunsu ya ɗauki zafi a yanzu kuma suna gab da fara jarabawa. Bayan an kawo wa baba amsar Abdul-rasheed dole ya haƙura ya bishi da addu'a, dan ya fahimci manufarshi kai tsaye. Haka kuwa aka ci gaba da rarrafawa har watanni biyun Abdul-rasheed na karatu suka cika. A lokacin ya shirya baro Kanon dabo zuwa Bauchin Yakubu gida. Sun sha kuka sun sha ruɗani shi da amini kuma ɗan uwa Nasiru da ogansa Yaya Zubairu. Daga ƙarshe dai dole suka sallamawa tunda mai rabawa ta raba, sai dai ance sabo turken wawa ne, a wannan gaɓar wannan turke ne kafe da zukatan su Abdul-rasheed. Yaje yayma Innar A'isha sallama, dan dama yana zuwa duk kwanakin mako da yake yi a anguwar kullum safiya gaisheta, hakan yasa abincinsa daga gidansu A'isha kullum kwano ukun nan babu fashi a kwanakin ƙarshen makon. Shiko baya gajiya da godiya da yin kuma cefane ya kai ma Inna. Ya kuma yi ƙoƙari ya lallaɓata ta yarda ya saka Bashir da Tasi'u a makarantar primary da ƴaƴan gidan su Nasiru ne kawai ke zuwa a layin. Inna ta haɗa tsaraba mai yawa sai ƴar sana'ar da amarya kanyi irinta ƙulle-ƙullen kayan lwaɗayi. Haka Nasiru yay masa rakkiya har tasha tare da su Bashir, basu dawo gida ba sai da motar su Abdul-rasheed ɗin ta ɗaga zuwa Bauchi....
_________________
BAUCHI
A bisa al'adar wannan zamanin zaman mace babu ƙunshi a ƙafa da hannu kamar wani zunubi ne. Kahama kitso ƙa'idane wani na tsufa kina sake wani akai-akai. Wannan wajibi ne ga mace mai aure a kowane yare na arewacin ƙasar. Dan haka koda Abdul-rasheed baya nan a duk sanda ya dace A'isha tayi ƙunshi da kitso Inna na sakata tsefe kai cikin matan yayun Abdul-rasheed wata tai mata kitso. Hakama tana yin ƙunshi tare da su dan sukan shirya yinsa ne a tare. Dan haka da wahala ka samu A'isha babu irin wannan tsaftar. Kamar dai yau a jiya Inna ta sakata yin sabon kitso, inda Magajiya ta zuba mata ƙanana masu ƙyau harda na gaba sak dai irin na barebari. Yau kuma suka shirya yin lalle a ƙafafunsu tun safe. Haka kuwa suka sakashi har yamma yana jikinsu. Sai la'asar suka kunce, A'isha batai niyyar zuwa gidanta ba yau sam dan haka ta ɓararraje suna hira da sauran facalolinta dan a gidan ɗaya daga cikinsu akai ƙunshin. A dai-dai kuma wannan lokaci Abdul-rasheed ya iso. A gidansu ya sauka kamar yanda ya saba, dan haka Inna ta tareshi tarba mai girma. Cike da hikima irin ta manya yana zaman gaisawa da Baba ta aika akai mata kiran babbar surukarta, a soro suka tsaya, bayan ta gaisheta ta shaida mata Abdul-rasheed ne ya dawo, maza su saka A'isha ta koma gida ta gyara jikinta. Sannan su taimaka mata sauri-sauri su tayata gyara gidan shima kafin ya iso. Ta amsa da ladabi ta fice. Tana zuwa ta gwargwaɗama sauran ƴan uwanta dan haka suka tasa A'isha a gaba. Tana son jin ba'asi babu wanda ya bayyana mata, sai dai sunce umarnin Inna ne hakan. Girman suruka koda matsayin kishiyar uwar miji take girma gareshi a wannan lokacin, dan haka A'isha bata sake tari ba ta bisu, dan yanda Innarta zatai mata magana ko bata umarni ta bi haka Inna itama zatayi tabi dole dan matsayin uwar miji take a garesu. Dan danan suka taimaka mata da dukkan abinda ya dace, ruwan wankanta kanshi yasha turare kala-kala a cikinsa. Hakama ɗakin suna kammala gyara mata suka baɗesa da turaren wuta. Basu taɓa mata gadon miji ba suka barta ta gyara da kanta suka fice zuwa nasu gidajen lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Hakan yasa cike da mamaki A'isha ta fara kici-kicin gyaran baban gado dake matsayin na mijinta Abdul-rasheed, zuciyarta kuwa cike da wasi-wasi akan mike faruwa ne wai? Gashi kafin su tafi sai da sukai mata kashedi akan ta zauna a gida karta ce zata biyosu ta jira. Bata fahimci mi suke nufi ba sai da Abdul-rasheed yay sallama yara biye da shi da kaya niƙi-niƙi. Ita jitai ma kamar ta firgita, dan haka ta fito wuff da fitilar ƙwai a hannu domin haskawa, hakan ya bama Abdul-rasheed damar ganinta fes a cikin sirritaccen hasken mai cike da ƙayatar da mai kallo. Tayi ƙyau cikin atamfa mai tabarma sabon ɗinki ne daga cikin kayan lefenta da sai yau ta saka. Turus ta tsaya tana kallonsa itama kamar yanda yake kallonta, sai dai shi nashi kallon na shauƙi ne da kewa matsananciya. Itako na mamaki ne da ruɗanin bazatar tasa. Sun zubama juna ido harna fin minti ɗaya har yaran nan suka ajiye kayan suka fice abinsu suka barsu dan saurin komawa suci tsarabar daya bayar a basu a can wajen Inna. Sai da aka kabbara salla ne hankalin Abdul-rasheed ya dawo jikinsa. Numfashi ya furzar a hankali yana janye idanunsa daga cikin na A'isha da suka tara ƙwalla, cike da sanyin murya ya furta, "Bani buta kada na rasa salla gaba ɗaya". Sukuku ta koma ciki kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta ɗakko masa butarsa ta ƙarfe, tazo gabansa ta durƙusa ta miƙa masa. Amsa yay yana kallonta shi dai, dan harga ALLAH sai ya ga ta ƙara masa cika a ido da girma, shi yana can tunaninta na hanashi sukuni da isasshen barci, itako da alama ko'a jikinta daɗinta take ci, ƙaramin murmushi yayi kawai, kafin ya maida hankali yayi alwalar ya fice gudu-gudu sauri-sauri dan har anyi raka'ar farko ma. Sauƙin ma massalacin kusa ne da su gab. Koda aka idar da magriba bai dawo ba, A'isha ma data idar da tata sallar tana zaune shiru, tama rasa miya kamata tayi ita kam, a haka yaro yayi sallama, ta amsa tana miƙewa hannunta riƙe da fitila. Tire ne da kwanika akan yaron, dan haka ta ajiye fitilar tana faɗin, "A'a Salihu kayan nan basu maka nauyi ba?". "A'a basuyi ba. Inna ce tace na kawo miki. Tace tana gaisheki sai da safe". "To na gode Salihu, amma kace mata ai yanzu ma zan taho gidan nima". Shi dai Salihu ya amsa da to ya fice abinsa. Itama dai ta ɗauki turen ta shige da shi ciki. Tuwo ne da miya sai fura damammiya a kwanon sha, ta tabbatar furan Baba ne aka ɗibo, dan Abdul-rasheed akwai son fura kamar Baban. Baki ta kuskure tai sallar isha'i dan an fara. Bayan ta idar ta miƙe, tabarma dake matsayin ta miji dake can saman babban gadon a maƙale ta taka ƙaramin gado zata zaro. Sai dai hannunta yaƙi ya kai, dan dole sai ta hau gadon zaifi mata daɗi amma bata son hawa ta saɓa a ganinta laifi ne. A yanda take ta amsa masa sallamar da yayi, ta cigaba da ɗiɗɗishenta na son ɗakko tabarmar. Inda take ya ƙaraso, ya tsaya a bayanta gab sosai, cike da kulawa da tausasawa ya ce, "Mizaki ɗauka haka Matar Abdul-rasheed?". Da yanayin shagwaɓa na wahalar da take sha ta ce, "Tabarman can mana, amma kamar ance ta gudu min na kasa na jawo". Hannayensa ya harɗe a ƙirji yana kallonta, ya ce, "To banda abin A'ishatu ai ta miki nisa ne, ga hanya mai sauƙi ki taka gado ki hau ki ɗakko kawai, tanan inda kike baƙya tsoron ma ki faɗo". "A'a zan iya a haka, kuma fa na faɗa maka tun ranar hawan gadon nan babu ƙyau". "Okay na manta haka ne fa, amma ai nima nace ki hau na yafe miki tun a waccan ranar ko. Kinga nidai sakko na tayaki ni". Yay maganar yana kamata cak ya sauke ƙasa. Kafin ta ankara ya sakata a jikinsa ya rungume...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 15_
__________________
_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau'in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._
_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._
INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006
TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1
Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
........Zata fara mutsu-mutsu ya ce, "No Matar Abdul-rasheed relax mana, haka matan ƙwarai suke tarbar miji idan ya dawo daga tafiya. Shin bakiyi kewata bane? Wata shida ba kwana shida ba A'ishatul-humairah. I miss you fiye da yanda kike zato". "Shi miye A mis ɗin?". Ta faɗa cike da jin kunyar yanda ya dabaibaiyeta, gashi yaƙi bata damar fita a jikin nasa yanda take fata. Siririyar dariya yayi yana ɗago fuskarta ya lakace mata hanci. Sai kuma cikin raɗa ya furta, "Nayi kewarki buhu-buhu". Itama murmushin tayi kanta a ƙasa. Sai kuma tace, "To wane yare ne kayi?". "Turanci". Ya bata amsa muryarsa na ƙara shigewa cikin maƙoshi, dan zuwa yanzu ta nutsu ta daina masa mutsu-mutsun son ƙwacewar. Zata ƙara magana ya ce, "Adana tambayoyi nan duk zan amsa ma Matar Abdul-rasheed anjima. Yanzu dai banu ruwa da abinci yunwa nake ji". Zabura ta ɗanyi alamar tunawa, sai kuma ta janye jikinta a nashi ta durƙusa har ƙasa ta ce, "Kayi haƙuri ina yini, ka dawo lafiya ya hanya? Ya ka baro mutanen Kano?". Idanunsa a kanta yay murmushi, sai kuma ya duƙa batare da ya amsa ba ya kamo kafaɗunta duka da hannu biyu ya miƙar da ita. Sake rungumeta yayi sannan ya amsa mata gaisuwa. Kafin ya rufe da faɗin, "Mutanen Kano duk na gaisheki harda gidaje da motoci. Gaisuwar Inna da tasu Tasi'u kuwa tafi rabin buhu". Cike da farin ciki ta ce, "Na gode! Amma miyasa Inna bata biyoka ba dasu Tasi'u. ALLAH kullum sai nayi kuka idan na tuna su". "In sha ALLAHU daga yau bazan sake bari hawayen kewar su Inna su zuba ba, zan dinga share su da murmurshi da farin ciki. Su Tasi'u kuwa karki damu zasu zo, Nasiru yace zai kawo miki su. Inna ce dai ba lallai anan kusa ba, ƙila sai kin haihu". Ba ƙaramin kunya kalmar sai ta haihun nan ta sakata ba. Dan haka bakinta ya mutu bata sake magana ba daga nan tama zame jikinta daga nashi dake mata daɗi kanta a ƙasa. Tabarmar daya ɗakko mata ta amsa ta shimfiɗa masa, shiko yana faman binta da murmurshi ganin yanda take ta faman sinne fuska dan yace zata haihu. Tsaff ta shirya masa abincin a tabarmar, shima sai ya zauna yaci dan yunwa yake ji sosai. Yaci ya ƙoshi yasha fura. Itako daya mata tayi tace ta ƙoshi bai takurata ba. Yana kammalawa ta kauda kwanikan, shi kuma ya hau zame kaya yana faɗin, "Saura wanka. Bari nai amfani da ruwan drum ɗin can ƙila yafi ɗumi, tunda naga da alama amarya bata fara girki ba a gidan nan har yanzu". "Inna tace ba yanzu ba". Ta bashi amsa kanta tsaye. Ƴar dariya yayi da faɗin, "Ƴar gatan Inna kenan, wato ba yanzu ba". "Eh mana, sai na ƙara girma tace". "To Inna ta shirya kayan girki kam dan yau zaki girma". Sam A'isha bata wani gane mi yake nufi ba. Shima kuma bai ƙara cewa komai ba ya fita. Koda tace bari tazo ta kai ruwan sai yace ya hutar da ita ta zauna ta jira shi...
Koda Abdul-rasheed ya fito wanka samun A'isha yayi ta ɓingire barci, bai tadata ba ya saka babbar riga a jikinsa ya fita a gidan, bai wani jima ba ya dawo da ledar nama tsire sai ƙamshi yake. Tadata yayi cike da lallaɓawa, zata fara masa shagwaɓar ya barta ita barci take ji ya dai lallasheta taje ta wanko fuska. Naman ya bata yace taci. Da farko kunya ta hanata ci saboda shi. Ganin haka yasa shi fita ya bar mata ɗakin, sai ta samu taci kuwa sosai, ta ɗauki sauran ta ajiye gefe. Ta fito danta kuskure baki ta ganshi zaune a waje, miƙewa yay yana tambayarta mi take so? Tace zata wanke baki ne. Bakinta ta wanke da gawayi da gishiri kamar yanda Inna ta koya mata tun a gida safe da dare idan za'a kwanta. Shima sai ya amsa yayi duk da yana da brush shi kam, itama kuma ya sayo mata. Suna komawa ɗaki A'isha ta kama gadonta zata haye. Riƙo hannunta yayi, dan haka ta juyo, suna haɗa ido tai maza ta duƙar da kanta ƙasa. "Barci kike ji?". Ya tambaya cike da kulawa. Kanta a ƙasa ta jinjina masa. Ya ce, "Na baki gado na ki ɗana yau?". "A'a ga nawa nima zan kwanta anan, kaima sai ka kwanta a naka". "Miyasa baƙya so?". "Saboda kowa yana da nashi". "Toni nazo na ɗana naki?". "Ai bazai ishemu ba". "To shike nan ki hau nawa sai ki bani naki". Bai jira tayi magana ba ya ɗauketa camak ya dire a saman gadonsa bayan ya ɗago labulen. Wani daɗi ya ratsa A'isha, a ranta tace (Ashe gadon daɗi ne da shi haka, kai miyasa ban taɓa ɗanawa da baya nan ba) shi dai dake kallonta bai san abinda take ayyanawa ba ya ce, "To kwanta sai da safe". Ya zuge mata labulen mai suna zuge shige. Aiko tana ganin ya rufeta ruf ta wani baje a gadon tana murmushi, ALLAH a kwai daɗi, ga taushin katifa gana zanin gado. Ga filo sun zagaye gadon reras har sha biyu gwannin sha'awa, ai saiga hajjaju matar Abdul-rasheed cikin ƴan mintina barci yayi awon gaba da ita. Duk abinda take Abdul-rasheed na kallonta ta tsakanin labulen yana danne dariya. Sai da ya bari barcin ya mata ƙarfi yaje ya rufe gida ya dawo. Duk abinda ya dace tayi matsayin matar gida sai shine yayi. Ya kashe fitilar ƙwan su gaba ɗaya dan baya son kwanciya da haske shi kam sam, sai dai akwai Torchlight a kusa da shi koda yaushe. Labulen ya ɗaga kaɗan ya leƙasata, ganin yanda ta ɓararraje dole ya dara kaɗan yanzun kam. Dan da alama dai gadon nan ya lula da matar Abdul-rasheed ba ƙarya. A haka ya samu ya hau shima ya gyara mata kwanciya, sannan ya zuge labulen suka koma ruff. Haskata ya ɗanyi da fitila, da gaske barcinta take hankali kwance alamar bata da wata matsala, wato babu abinda yakai ƙuruciya daɗi, ita yanzu bata san mi yake ji ba, shiko tsahon watanni yana azabtuwa a kanta. Hora kan nasa kuwa ya zame masa alkairi, dan tabbas da ya taɓata kafin tafiyarsa da bazai iya sati biyu a Kano baizo Bauchi ba. Amma gashi Alhamdullah har ya cika watanni shida ciff ya dawo garinsa na haihuwa dawowa ta har abada, inma da abinda zai sake biyo baya da zai sa ya fita bazai kai kamar wanda yayi a baya ba, duk da yana da burin sake zurfafa iliminsa again. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, tare da kashe fitilar ya ajiyeta gefe ya gyara filo da ƙyau shima ya kai kwance.. Cikin barci A'isha ta fara jin saɓanin abinda bata taɓa ji ba tsayin rayuwarta. Wato hannun mutum a jikinta a firgice ta farka tare da zabura ta ƙwalla masa ƙara. Ƙarar data sashi saurin ɗora hannunsa a saman bakinta ya rufe shi ruff, tare da kamota ya riƙeta a jikinsa da ƙyar tana fisgewa. Babu shakka da ace akwai wani a gidan sai ya jita, ALLAH ya soshi su biyu ne. Da ƙyar ya tausata ta nutsu, bayan ya maimaita mata kalmar shine da Abdul-rasheed yafi sau goma kafin ta fahimta. A hakan ma bata nutsu ba ta saka masa kukan ita ta haƙura zata koma gadonta ta kwanta. Lallashinta yake da iya iyawa da kwantar da kai amma taƙi fahimta. Shi ko yana cikin wani hali, dan haka ya fara mata nasiha da son fahimtar da ita da yaren da zata gane. Ina hajjaju bata gane ɗin ba, daga ƙarshe dai dole ya barta ta sakko a wannan gado kuwa, dan neman shiɗe masa take alamar dai ta riga ta tsorata da shi.
A gurguje Please 🏃🏼♀️
>>>>>•<<<<<
Wasa fa farin girki tsakanin Abdul-rasheed da A'isha, dan tun yana ɗaukar al'amarin mai sauƙi harya fahimci baya samuwa cikin sauƙi. A washe gari wasan ɓuya ta sanya da shi. Zuwa wani daren yana fita sallar magriba ta sulale itama tabar masa gidan. Koda aka idar da salla bai dawo ba sai da akai isha'i. Nan ɗin ma Baba yabi gida duk dan ya bata dama ta yi barci cikin salama, dan ya fahimci yinin yau gaba ɗaya a ɗarare take da shi ko fara'a batayi ma har yara dake shigowa. Wajen ƙarfe tara baba yace ya tashi yaje gida dare nayi. Haka yay musu sallama shi da Inna ya taho, koda yazo gida ya shiga ɗaki wayam babu A'isha, sai yay tunanin taje bayi ne. Zaman jiranta yayi, duk da yayi mamakin ganin tiren abinci da aka aiko daga gidansu a ƙofar ɗaki, sai shine ma ya shigo da shi ciki. Shiru-shiru babu motsin Indo, dole fa ya miƙe ya fito tsakar gidan da Torchlight a hannu, ya gama haske-haskensa babu alamarta, ƙarshe dai har bayin ma ya leƙa nan ma babu ita. Hankalinsa ne ya tashi, babu shiri ya fito ya nufi gidansu, abinka da ba wani nisa ba, dan can hankalinsa kawai ya bashi zata iya zuwa. Inna da Baba na haramar shigewa suma su kwanta ya shigo, da mamaki suke tambayarsa lafiya?. A ruɗe yace, "A'isha. Naje gida ban sameta ba, na zata tana bayi ne sai dana ga daɗewan yayi yawa na leƙa babu alamarta, ashe ma ban lura bane buta na nan a ɗaki. Sosai hankalin Baba ya tashi shima, sai dai ita Inna abinka da mace sai ta tafi tunani. Ganin suna sallallami tace, "Ku dakata, nasan babu inda zataje tunda ba wani waje ta sani ba daga nan dai sai gidajen ƴan uwanka, kuma dai duk gamu a kusa. Bari mu fara duba nan gidan kota shigo". Inna ta amshi Torchlight ɗin baba ta fara leƙa ɗakuna tana haskawa. Ilai kuwa sai ga A'isha a cikin yara su Alawiyya ƙannensa da yaran maƙotansu da suke zuwa kwana gidan tana shaƙar barcinta hankalinta kwance. Inna ta ce, "Yau ga ja'ira, ai gata nan tsakkiyar su Nana kuwa tana barci. Bara na tasota". Lokaci ɗaya shima Baba tunaninsa ya harba, dan haka yace, "Kinga barta kada ki tasheta Karimatu." "A'a ya zakace kada a tasheta Malam. Miye amfanin kwanciyar anan?". "Barta ke dai, kai jeka sai da safe". Duk da ba haka Abdul-rasheed yaso ba bazai iya musawa ba, cike da ladabi yay godiya ya tafi ransa fal mamakin A'isha. Ya fahimci yarinyar nan so take ta ƙwaɓa masa aiki dai kawai. Ashe labarin da abokinsu ya basu akan tashi matar data dinga komawa gida ma ita ana maidota kasancewar garinsu ɗaya suna masa dariya ashe shima tashi Shatun jiransa take. Tirƙashi akwai aiki kenan dai...........✍🏼
🤣🤣🤣Babban yaƙi kam😂.
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 16_
__________________
https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6
*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*
*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*
*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*
*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*
_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃
*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 💃_*
20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k
*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. 💃 Ga sauƙi abaka tamkar ƙyauta 💃💃😀_*
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________