Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 16

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 16

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 16: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 16. ........Kwanansa biyu ya huta Mammah ta zaunar da shi tai…

4,428 words

........Kwanansa biyu ya huta Mammah ta zaunar da shi tai masa bayani akan matsin lambar kawunanta game da aure. Abin mamaki sai taga Haysam yay kicin-kicin da fuska har idanunsa sun kaɗe. Cikin son kwantar masa da hankali dan ta fahimci kishin mahaifinsu yake ta ce, "Nima ba auren nan nake so ba, dan da ina da damar dazan bijire musu tabbas da nayi hakan. Bani da wani buri sai na ganin na tsaya a kan tarbiyyar ku, rayuwarku ta inganta kuma. Amma na rasa ta inda zan zamewa al'amarin su. Yanzu haka jiya-jiya Kawu Rayyanu ya kawo min wani mutumi wai makwafcinsu ne, yanata damunsu a kaina, shi da gaske yake ba wasa yazo da shi ba. Ban ɓoye masa akan ku ba yace yaji ya gani ya kuma yarda nai zamana anan shi zai dinga zuwa." Karo na farko Haysam ya ɗago yana kallonta, idanun nan sun kaɗe jazur. Cikin ɗacin murya ya ce, "Kuma kin yarda Mammah?". Rasama mi zatace masa tayi, dan gaba ɗaya ya juye mata tamkar Abdul-rasheed a gabanta. Sai kawai ta girgiza masa kai. "A'a ban amince ba". Ajiyar zuciya Haysam ya saki tare da furzar da huci, harma abin yaso mata dariya amma ta gimtse. Daga ranar bata yarda ta sake masa batun auren nan ba, har hutunsa ya ƙare ya shirya ya koma ya sake barinsu da kewa. Ya wuce da sati biyu aka ɗaura mata aure da Alhaji Nura. Harga ALLAH ba son auren nan A'isha take ba, amma haka ta daure ganin Alhaji Nura mutumin kirki ne, baida damuwa bai da hayaniya kuma. Kamar yanda yay alƙawari kuma ya riƙe mata marayu kamar ƴaƴansa. Bai rabata da sana'arta ba ya kuma shiga gyara mata gida. Matsalar abinci babu ita, haka ma ya shirya Malam Sulaiman ya rakashi har Kaduna ya duba Haysam. Shi Haysam bai fahimci komai ba, a tunaninsa abokin Malam Sulaiman ne kawai. Dan haka ya gaishesa da girmamawa tare da sakin jiki yana amsa masa tambayoyin daya dinga masa. Rayuwa ta cigaba da shuɗawa Mammah ta sake samun kwanciyar hankali da mijinta. Tayi ƙyau yaranta sunyi ƙyau suma sunata karatunsu. Duk da dai su Ja'afar da farko basu saki jiki da Alhaji Nura ba suma sai da Mammah ta dinga musu faɗa da nasiha. A haka Haysam ya sake zuwa hutu ya tarar da abinda bai masa ba. Amma da yake ya kwankwaɗi tarbiyya ya ƙoshi haka ya danne a ransa bai ko nunama Mammah ba har hutunsa ya ƙare ya koma. Tafiyarsa babu jimawa ciki ya bayyana a jikinta. Sosai Alhaji Nura ya nuna farin ciki mai tsanani da wannan ciki, dan matansa biyu babu wadda ta taɓa ko ɓatan wata shekaru fin goma-goma yana tare da su kuma sai Mammah a yanzu. Aifa kafin kace mi zance ya zagaye ko'ina, Mammah na samun gata iya gata a wajen mijinta kamar zai lasheta da wannan ciki, in dai kaga bata samu abu ba sai dai in batace tana so ba. Haka aka cigaba da rainon wannan ciki. Cikin Mammah nada wata bakwai abubuwa suka fara canjawa a yanda suke. Hidimar Alhaji Nura ta fara raguwa, hakama ɗokin wannan ciki, kai takai yanzu sai yay sati bai leƙo gidanta ba. Tun mutane basa fahimta har aka fara fahimta, wasu suka fara faɗin bai san haihuwa ne ai dama, wasu suce matansa ne sukai masa asiri, dan yaje ya tare a gidansu sai hidima yake musu. Al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta fara zama babba, takai Mammah tayi wata guda bata saka Alhaji Nura a idonta ba. Su Ammar da suka buɗi ido da shi suna kallonsa matsayin mahaifi sunci kukan har sun gaji sun haƙura. Inda ta godema ALLAH yanzu sana'arta ta zauna da ƙafafunta, dan tunda ta samu ya ƙara mata jari ta sake miƙewa da ƙafafunta. Ganin haihuwa ta kusa zuwa mata ta samu kawunta da batun abinda ke faruwa duk da tasan ya sani. Haƙuri ya bata da mata nasiha, ya tabbatar mata subi komai a hankali Alhaji Nura baya cikin hayyacinsa ne, dan al'amarin nasa akwai ƙamshin gaskiya game da asirin da ake faɗa matansa sun masa. Amma dai zai sameshi yaji mike faruwa. Jiki a sanyaye tace to ta koma gida.

________★

Kamar yanda Kawu ya faɗa zai samu Alhaji Nura ya same shin, amma mi abin mamaki sai Alhaji Nura ya murje ido ya fara tujara ma Kawu, daga ƙarshe ma yace shi ba cikin shi bane ba, A'isha taje ta nema wanda yay mata ciki. Idan kuma aka matsa zai kai kotu. Kai shi yama saki Mammah taje can ta nema uban cikinta. Wannan magana ta girgiza kawu matuƙa. Ya ce, "Haka kace?". "Eh haka nace, ku kaini duk inda zaku kaini, ina kan gaskiya ta ciki ba nawa bane ba. Kuma na saketa saki uku". "Babu inda zamu kaika, amma zamu zauna tare da waliyanka ka maimaita dukkan abinda ka faɗa kodan watarana kar kace sharri akai maka". Daga haka Kawu ya miƙe yayi gaba abinsa. Kamar yanda ya faɗa haka yaje ya samu waliyyin Alhaji Nura daya kasance mahaifinsa ya sanar masa. Shima kansa ya girgiza da wannan magana, babu ɓata lokaci ya nemo ɗan nashi akan batun, abinda kuma ya gayama Kawu shi ya maimaita ma mahaifinsa da waliyyan Mammah babu tsoro babu shakka. Sai kuma zancen yaso zama hayaniya a tsakani, dan kuwa ya sheganta cikin da cewar ba nashi ba, kamar wasa sai da aka dangana da mai-anguwa akai zama tsakanin Mammah da Alhaji Nura, anan ɗin ma bai canja ba daga batunsa na ciki ba nashi bane. Mammah taci kuka matuƙa da yin nadamar aurensa, daga ƙarshe akace sai a bari saita haihu aga mi zata haifa, idan gwaji ya kama sai aje ayi. Da wannan batu aka kashe magana, Mammah taje ta cigaba da rainon wannan ciki cikin matsanancin yanayi da ƙuncin zuciya da kewar Abdul-rasheed, har ALLAH ya kaita ga haihuwa aka samu mace. Abin mamaki yarinya kamar Alhaji Nura yayi kaki ya ajiye saboda kamanni, dan tun tana jinjirarta kamanin a bayyane suke. Mammah ta gode ma ALLAH mutane kuma sun tayata murna. Ita kuma daga nan ta hau kan nata dokin zuciyar, ta tabbatar ma Alhaji Nura bata buƙatar komai daga gareshi game da rainon ƴarta, kuma ko anan gaba kada yace yana da wata alaƙa da yarinyar. Babu ko musu yace ya amince tabbacin yana cikin mayen asiri har lokacin. ALLAH sarki sai mahaifinsa ne yay komai na sunan yarinya aka saka mata suna Habibah. Suna kiranta Biebah. Haysam yazo hutu lokacin yana shekara ta biyu a NDA ya tadda Biebah, yanda yake son sauran ƴan uwansa haka yake jin ƙaunar ta. Mammah bata gaya masa komai daya faru ba shi ma kuma bai tambaya ba duk da yaga Alhaji Nura baya zuwa gidan, a haka ya kammala hutunsa ya koma....

>>>>>>•<<<<<<<

Shekaru Sun shuɗa, Sabbin Jarumai Sun girma. Lokaci ya tafi kamar iska mai kaɗawa a zamanin rani da damuna. Shekaru uku sun shuɗe cikin gumi, jini, da hawaye ga matasan soji. A yau Haysam Abdul-rasheed Shehu, wanda aka fi sani da Zak-Shadow ya zama ɗaya daga cikin fitattun senior cadets na NDA. Yanzu idan ya wuce, sabbin cadets suna tashi tsaye domin girmamawa a garesa. A gefe kuwa Imran Abbas wanda a da yaro ne mai rauni ya zama ɗaya daga cikin masu kwarewa a sashen signals and intelligence unit. Ba wanda ya taɓa zato cewa shi ne sarkin kukan nan da ya shiga makaranta a shekarun uku da suka shuɗe. Duk inda suka shiga ana kiran jaruman biyu da suna (The two Shadows). Domin kuwa suna aiki tare tamkar gangar jiki ɗaya da zuciya biyu. Sunan Zak-Shadow da Imran ya sanya ma Haysam ya bishi, har takai Zak-Shadow ɗin yayi gaba fiye da sunansa na yanka. A yau suna aji ɗaukar darasi da Major Adetunji ke ɗaukarsu, wanda ya horar da su tun farkon shigowarsu NDA. Bayan ya kammala ya sallamesu su Zak-Shadow suka iso gaban allo ɗaukar masa kayansa domin yi masa rakkiya kamar yanda suka saba. Kallonsu ya tsaya yanayi cikin murmushi, "Haysam Abdul-rasheed Shehu, Imran Abbas the two Shadows". Murmushi sukayi a tare, duk da kuwa idan yana jin nishaɗi yakan kirasu da sunan ne daman. Batare daya jira amsawar su ba ya cigaba da faɗin, "Kuna cikin waɗanda suka fi nuna mana menene juriyar soja a wannan mate ɗin naku. Shiyasa kuke na daban a zuciyata yaran albarka, ina son a shekarar ƙarshen nan ku ƙara ƙwazo da jarumta fiye da shekaru uku da suka shuɗe, dan ina son ku zama misali ga duniya idan kuka fita ba cikin makarantar NDA kawai ba". Ƙaramin murmushi Haysam ya yi tare da salute ɗinsa, hakama Imran, a tare suka amsa da murya mai zurfi, "Yes, sir." Major Adetunji yay murmushi shima, dan har cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar Haysam da Imran. Yaran akwai tarbiyya da nutsuwa. Babu wanda zai ce yau ga wani laifinsu ko wani ya kawo ƙararsu ana faɗa dasu a cikin ɗalibai. Gasu da maida hankali akan komai. Duk wahalar da Haysam yaci a hannun Seniors bai taɓa kai ƙarar kowa ba, sai idan su sun gani su hukunta Seniors ɗin musamman idan muguntar tayi yawa. Sai gashi a yanzu komai yana neman zama tarihi, dan watanni kaɗan ta rage su shiga shekarar ƙarshe a NDA ɗin........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 32_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Komai ya cigaba da canzawa a kowane sakan zuwa minti da awoyi tamkar yanda kwanaki suka shuɗa zuwa watannin suka bada shekara uku data shuɗe. Su Senior Garba dake shekarar ƙarshe suna nan akan bigiren iska mai wahalar da kayan kara, domin kuwa har zuwa yanzu suna jin haushin yadda Haysam ya zama abin koyi, har officers ke yaba masa a bainar jama'a da yi musu misali da shi matsayin abin koyi. Sai dai kasancewar Haysam da kowa ke kira Zak-Shadow a yanzu ya zama jan wuya yasa su kansu shakkarsa suke basa iya yimasa abu kai tsaye kamar yanda sukeyi a shekarun baya na farkon shigowa. A yau ma ya fito massalaci da yay zaman yin azkar ɗin yamma bayan sallar la'asar Senior Garba ya kira shi gaban sabbin cadets da yake jagoranta. Harga ALLAH shi Zak-Shadow baiga ma Senior Garba ba, saboda hankalinsa yayi kan tunanin ina Imran ya shiga ne dan batare sukai sallar la'asar ba. Bayan an idar shi kuma ya zauna ɗaukar karatu kamar yanda ya saba a wajen malaminsu, daga nan yay azkar shine yake fitowa a yanzu. Yanayin yanda akai kiran nashi ya sashi dawowa daga duniyar tunaninsa akan Imran, cike da nutsuwarsa ya juyo sai sukai ido huɗu da Senior Garba ɗin, kamar zai shareshi ya wuce dan yasan shashasha ne sai ya fasa ya nufi inda yaken. Cike da son zubarma da Haysam ɗin mutunci a gaban yara Senior Garba ya furta, "Cadet Haysam! You think being praised makes you a soldier? We made you, remember that." Idanu Zak-Shadow kawai ya ɗan zuba masa kamar bazai tanka shi ba, hannuwansa a cikin aljihun wandonsa, har yay niyyar yaɓa masa baƙar magana dan ya iyata kwali-kwali, bashi da yawan magana, amma idan ya yaɓa maka baƙa ɗaya sai ka kwana ka yini tana cizon zuciyarka, amma miya tuna sai ya fasa, a taƙaice ya ce, "With all due respect, senior, the Academy made us all." Garba ya yi murmushi mai cike da baƙin ciki da tsana wanda ke ɓoye fushi, shifa duk sanda yaga yaron nan ji yake kamar ya shaƙeshi ya mutu ya huta ALLAH. Cikin kallon idon Haysam ɗin da shima ke kallonsa ƙyam ya ce, "Hmm.. perfect cadet. Zamu ga yadda zaka fuskanci Special Night Drill". Kai kawai Zak-Shadow ya girgiza yana barin wajen, dan lokuta da dama ɗaukar al'amarin Garba yake matsayin soki burutsu da motsuwar kai. Yasan night drill ba abune mai sauƙi garesu ba cadets, ana amfani da shi ne wajen gajiyar da mutum ta jiki da ta zuciya matuƙa, gudu cikin duhu, rarrafe cikin laka, da ɗaukar kaya masu nauyi har zuwa safe. Wasu ma daga cikin cadets suna jin tsoro idan aka ce "special night drill", amma shi bai taɓa ɗaukar hakan matsayin wani abun tsoro ko tashin hankali ba balle ya nuna damuwa. Ɗaki ya koma abinsa inda ya samu Imran ya dawo yana jiransa.

★ Da daddare kamar yanda Senior Garba ya faɗa ɗazun da yamma su Zak-Shadow suka fita Special night drill. Kasancewar akwai abinda Garban da abokansa suka shiryama Zak-Shadow yana gefe yana kallonsa cikin murmushin mugunta. John da shima ke kallon Zak-Shadow cikin taɓe baki da ƙwafa ya ce, "Wai shi yana jin kansa wani shege ko, zamu bashi banbancin kare da uban gida a yau, wannan karon sai mun karya shi". Ƙwafa kawai sauran sukai batare da sun tanka ba. Shima Zak-Shadow da bai san sunayi ba ma ya cigaba da motsawa cike da karsashi da ƙarfin jiki mai tafiya dana zuciya. Sam babu gajiyawa a tare da shi, sai ma taimakawa waɗanda suka faɗi a hanya yake yi. Sun dawo a zagaye na biyu wasu sun fadi ƙasa, wasu suna shashshekar wahala harda masu share hawaye, amma shi yana tsaye, yana kallon Garba kai tsaye cikin shirun daya saba kowa kuma ya sanshi da shi. Shiru ne mai zurfi dake ƙona zuciyar maƙiyansa. A zuciyarsa kuwa ayyanawa yake. (Yau zan nuna maka Ba ruwan jarumta da wanda ya fara zuwa duniya ko ajin karatun duniya Garba. Ba zan rushe ba, in sha ALLAHU har abada bazan faɗi a ƙasanka ba sai dai kabar NDA da takaici na a zuciyarka kuwa. In yaso ka ajiye aikin soja ka koma rawar ƙoroso). Yanda Zak-Shadow ke kallon Garba sai ya ɗan ji tsarguwa a zuciyarsa ga shakka da kwarjininsa na cizonsa a rai, amma sai ya dake saboda izza, shawarar da zuciyarsa dake gargaɗinsa yabi cike da gadara ya ce, "Dismissed!". Ba abinda Zak-Shadow da abokan Garba sukai tunanin ji zai fito a bakin Garba ɗin ba kenan. Dan haka ya bama abokansa haushi. Zak-Shadow kam ya wani bisu da kallo cikin ƙyaɓe baki ya bar wajen. Yana fara tafiya Imran ya ƙaraso suka jera yana goge laka daga fuskarsa. "Wallahi ba soja bane kai Zak… kai dutse ne. ALLAH tsoro ka bama Garba fa amma wata maganar banza yaso gaya maka da farko kamar yanda ya saba". Zak-Shadow ya murmusa cikin nutsuwa da kallon Imran ya ce, "Kaji tsoron rabbi Imran. Ai dama dutse baya jin zafi, ni kuwa mutum ne ina ji, kawai ban bari su gane ne dan har abada bazasu ga Haysam Abdul-rasheed a ƙasan takalmansu ba in sha ALLAHU". "In sha ALLAHU kuwa ƴan wahala."

__________★

KOMAI NISAN JIFA....

Alƙawarin ALLAH ya cika. Shekaru sun wuce cikin wahala da zafi, ƙura da ruwan sama harma da sanyi. Haysam Abdul-rasheed Shehu da abokinsa Imran Abbas sun girma a cikin NDA kamar ƙasar da take haifar da ƙarfin hali da gwagwarmayar neman ƴanci.. Tabbas zuwa yau an manta da lokacin da ake kiransu "new boys." Yanzu sune manya Seniors dake faɗa aji da shugabantar masu shigowa har ma da masu bi musu. Tabbas shekarar ƙarshe shekarar ƴanci amma shekara mafi tsaurin gwagwarmaya da karatu mai tabbatar da yaro soja. Haka su Zak-Shadow sukai juriya ƙwarai da gaske wajen tsallaketa tamkar yanda suka shallake na baya da suka shuɗe. Alhamdullah ga burin ƴan maza ya cika, NDA ta zama tarihi tamkar yanda primary da Secondary suka zama tarihi suma. A daren da suka karɓi takardar kammalawa, Zak-Shadow ya tsaya yana kallon harabar NDA, zuciyarsa cike da tunani. Wajen da ya sha ruwan sama, gudu a cikin laka, da azabar push-ups har yatsunsa suka kumbura, yau shi ne wurin da zai barwa tarihin da sai dai a tuna a bama ƙanne da ƴaƴa labari watarana. Imran ya matso kusa da shi murmushi na bayyana cikin fuskarsa mai tarin nutsuwa, "Zak-Shadow" ya kira sunansa da murya mai sanyi, bai jira amsawarsa ba ya cigaba da faɗin, "ka tuna ranar farko da muka shigo nan?". Juyowa yay yana kallonsa fuskarsa da murmushi mai nauyi, cikin buɗaɗɗoyar muryarsa mai fita da amon mazaje ya amsa masa da, "Idan zan mance da wannan ranar tabbas zan mance da kai My Imran. Yanzu kamar jiya ne... kai da kukan nan naka da yasa na tsaya ina kallonka tamkar Ma'aruff ko Ja'afar a gabana". A tare sukayi dariya, abinda Zak-Shadow bai cika son yi ba. To dama mai ganin suruntun nashi kamar hakan sai dai Imran ɗin ai.

★Alƙawarin ALLAH ya cika, Haysam ya samu cikar burinsa daya ginu bisa burin mahaifinsa. Ya kammala NDA bayan shekaru huɗu na wahala, gwagwarmaya, juriya da jarumta. A yau suke bikin Passing Out Parade ɗin su, musalta irin farin cikin da yake aciki abu ne mai wahala. Ba shi kaɗai ba, hatta Mammah da ƴan uwansa da malam Sulaiman da kawunsa da yazo daga Bauchi, da Innarsa Khadijah da Alawiyya suna cikin farin ciki. Domin kuwa sun halarci bikin passing out ɗin nasu su duka. Yanzu Haysam ba ɗan takara ba ne, soja ne cikakke, Second Lieutenant Haysam Abdul-rasheed Shehu (Zak-Shadow). Sun yi parade a gaban manyan jami'an soja da iyaye da ƴan uwa da abokan arziƙi. Ɗalibai da yawa da suka nuna ƙwazo a fannoni daban-daban sun samu ƙyautittuka na girmamawa, ciki kuwa harda Haysam. Lokacin da aka kira sunan Cadet Haysam Abdul-rasheed Shehu, sai dukan ɗakin ya amsa da ihun kiran sunansa daga mate ɗin nasa. "Sarki! Sarki! Zak-Shadow! Zak-Shadow!". Kai kace zasu fasa hall ɗin ne har iyaye da suka halarci taron najin ƙagara da mamakin wane yarone wannan mai farin jini ga yaransu haka?, sai da aka tsawatar musu saboda ihun kiran Haysam da ya kasa miƙewa sai da Imran ya kama shi ya miƙar tsaye. Cike da nutsuwarsa ya tako ya fito inda ake buƙatar ganinsa. Ba ƙaramin ƙyau kayan sukai masa ba, sun zauna a ginannen jikinsa na asalin zakin ga ƙƴawu ga nutsuwa ga addini, dan goshinsa kawai ya isa baka shaidar shi mai ibada ne kodan damɓareren tabon sallar da yake da shi. Ba tabon salla kawai ba a yanayin nutsuwar Haysam kawai zaka tabbatar da akwai ilimin addini sosai a tare da shi.. Zak-Shadow ya amshi lambar yabo ta Discipline and Endurance. Ya kuma samu ƙyautar girmamawa ta Best in Field Tactics & Discipline, abin da ya sa Mammah da ƙannensa suka yi kukan farin ciki a wajen kallon taron da suka halarta. A tare ƙannensa suka tashi mazansu da matansu sukaje suka rungumeshi. A karo na farko idonsa ya cika da ƙyallin hawaye, wannan ba kawai nasara bace, ƙarshen tafiyar jarumta ce da cika burin Abiy da samar da farin ciki a zukatan ƴan uwansa da Mammah, inama Abiy na raye ya cimma wannan rana.. isowar Imran daya ɗan buga kafaɗarsa da dariya ya sashi haɗiye hawayen nasa. Sai kuma ya juya yana kallonsa, suma ƙanensa sakinsa sukai suka koma wajen zamansu. Kashe masa ido ɗaya Imran yay da faɗin, "My Zak-Shadow yanzu zai koma gida a matsayin soja na gaskiya. kaga yanda Mammah take kukan murna ita da su Ma'aruff." Haysam ya murmusa, yana mai lumshe idanunsa ya sake buɗewa akan su Mammah sannan ya dawo da su kan Imran. "Tabbas Mammah tana kuka ne irin na farin ciki da cikar burin mijinta Imran, ba kukanta ita kaɗai take ba harda kukan Abiy da Umma duk a tare. Amma nima ba zan taɓa manta nan ba Imran. Wannan wuri ya juya ni daga maraya marar gata, zuwa mutum mai ƙarfi da damammaki da samun cikar burin mahaifi. Imran in sha ALLAHU sai na kaima Abiy wannan albishir har Bauchi a gobe-goben nan in dai ina da rayuwa". "ALLAH ya cika maka burinka, kuma ba kai kaɗai zaka Bauchi ba harda Imran Abbas ɗan Abiy da bai sani ba". Wani ɗan dukan basawa Zak-Shadow ya bama Imran a kafaɗa, sai kuma ya rungume shi hawayen da yake ta shanyewa suka samu damar ɗigowa. Shima Imran hawayen ne ke zubo masa. Yana ƙaunar Haysam, yana tausayinsa ƙwarai da gaske. Dan shi har yanzu bai san maraici ba, uwa da uba duk suna raye, kai shi tunda yasan kansa ba'a taɓa mutuwa a gidansu ba ma gaskiya. Sai dai a dangi haka sai kakarsu da ta rasu yana yaro sosai. Sannan gidansu su suna da kuɗi.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 33_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.......Zak-Shadow da su Mammah sun wuce Kano, zasuyi hutu na makwanni har shida. Ashe walima Mammah ta shirya masa. Dan haka suka iske gida cike da danginta anata girki. Ƴan Bauchi dai iya kawunsa ne kawai sai Khadijah da Alawiyya suka zo. Bai damu ba, wanda ya gani ɗin ma sun wadatar. Anci ansha an masa addu'oi kala-kala harda mutanen anguwa. Bayan kwanaki biyu gida ya koma sai su kaɗai, Zak-Shadow ya sake fahimtar rayuwa ta canja ga mahaifiyarsa, ta tabbata dai bata tare da sabon mijinta. Sai dai yanzun ma bai tambaya ba saboda girmamawa har sai da Mammah ta sanar masa komai a wannan karon da bakinta. Tabbas zuciyarsa ta hasala matuƙa, amma bai ce komai ba dai a zahiri. Itama Mammah data fahimci yanayin nasa sai tai masa nasiha da gargaɗinsa akan kar taji wani abu daga garesa. An riga anyi ya wuce sai a tari gaba. Badan yaso ba yay shiru kamar yanda ta gargaɗe san. A cikin wannan hutu ya samu damar bibiyar karatun ƙanensa, har zuciyarsa kuwa ya gamsu da yanda komai ke tafiya Alhamdullah. Musamman ma su Ja'afar ƴan Secondary. Ya ji daɗin kuma ganin yanda kasuwar Mammah tai tasiri a gida. Ya ziyarci Malam Zayyanu da abokinsa Malam Datti. Sun masa addu'a sosai da nuna jin daɗin nasarar da ya samu a NDA. Duk da yana cikin hutu bai daina yin motsa jiki da safe da yamma ba, kamar yadda suke yi a NDA. Wani lokacin idan yana fama Mammah har faɗa take masa ya huta. Yakan yi murmurshi ne kawai ya ce, "Mammah idan banyi ba jikina zai yi ciwo ne". Haka dole ta ƙyaleshi har hutunsu ya ƙare, kamar kuma yanda yay alƙawari yaje Bauchi tare da su Ma'aruff cikin weekend. Sun ziyarci kabarin mahaifinsu da Umma har ma da kakaninsu su Malam. Babu wanda yasan yaje a ƴan uwan mahaifinsu sai kawunsu Jamilu kawai, dan basu kwana ba a ranar suka juyo Kano. A watan Agusta ya koma Jaji, domin yin Young Officers Course, inda ya sake haɗewa da Imran, a wannan karon ma a ɗaki ɗaya suka zauna, dan sai da sukai duk yanda zasuyi aka haɗasu cikin amincewar UBANGIJI. Alhamdullahi sun kamalla course ɗin su a farkon shekarar 1999, daga nan kowa aka turashi inda zai fara aiki. sai dai an samu matsala dan anyi posting ɗinsu waje daban-daban shi da Imran, amma da yake suna da oganni tuni suka nema oga Adetunji suka sanar masa damuwarsu. Shine yay ta kai kawo har aka haɗasu waje ɗaya yanda suke fata, antura su aiki zuwa 82 Division Enugu, inda suka fara rayuwar soja ta zahiri. A can suka gane cewa aikin soja ba na jarumtaka kaɗai ba ne, aikin zuciya da sadaukarwa ne.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull