Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 19

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 19

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 19: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 19. .........Taron yara ne a filin da ake kira dandali a ƙauyen.…

4,496 words

.........Taron yara ne a filin da ake kira dandali a ƙauyen. A wannan dandali duk wani abun kwalam da maƙulashe ana saidawa, da daddare kuma nan ƴammata ke taruwa yin gaɗa da hira da samari. Yanda ƙura ke tashi da ihun yaran da suka taru zai baka tabbacin faɗa akeyi. Gashi hantsi ne maza duk suna gona, kusan duk ta inda ka zagaya yaran ne sai mata masu satar fita anguwa ganin mazan basa nan. Tafe take tana ƴan waƙe-waƙenta da ƙaramar galon fara mai cin kwalba uku ta mai an zuba man gyaɗa da zai iya kai kwalba ɗaya da rabi a ciki, sai leda baƙa a ƙulle. Yanda aka ɗaure bakin galon ɗin harda leda zaka gane anyi haka ne dan karta zubar. Harta kama hanyar da zata sadata da gidansu ta canja saboda hango ƙurar dake tashi a dandali da ihun yara irinta. Sauri-sauri gudu-gudu kuwa ta nufi can, dan a duniya babu abinda ke burge Nimrah irin damben tsiya, iyayen sunyi faɗa har sun gaji, ga kawunta Tanimu na ɗaure mata ƙugu, da anyi magana yace a barta dan ita *_Zakanya_* ce soja ma zata zama. Tsabar fitinar Nimrah idan nace kowa ya santa a ƙauyen nan banyi ƙarya ba. Cike da rigima ta fara kutsawa ta cikin yaran dan son ganin abinda ke faruwa, ko tsoron a zumar da man gyaɗan dake hannunta batayi. Bako ta tsaya ko'ina ba sai tsakkiyar filin faɗan. Tana shiga kuwa ta ajiye galon ɗin man da ledar ta cire ɗan hijjabinta taci ɗammara ta koma tsakkiyar masu faɗan ta tsaya. Cikin tsiwa da rawar kai ta ce, "Ke Abubu matsa na sayi faɗan nan, dama haushin wannan shegiyar Ɗaharen nake ji. Babu musu Abubu ta matsa ta bama Nimrah waje, dama ba ƙarfi gareta ba tun ɗazun Ɗahare ke jibgarta, dan kuwa ta girmeta har ita Nimrah ɗin ma. Ɗahare zata kai shekara tara ma. Ɗahare dake kallon Nimrah tana huttai ta nunata da yatsa tana faɗin, "Ke Nimrah wlhy ki fita a wannan faɗan ba ruwanki, dan sai na haɗa ke da Abubun naci uwarku a filin nan". "Sai dai kici uwarki". Cewar Nimrah cike da tsiwa tana girgije-girgijen jiki ita a dole mai ƙarfi, sai kuma ta duƙawa ta dimtsi ƙasa a hannu biyu, ta sake matsawa gaban Ɗahare sosai ta nuna mata. "Gata tsiya gata arziƙi ki zaɓa". Cikin takaici Ɗahare ta kaɓe ta tsiyar, ai ko sai kokawa ta kacame tsakaninta da Nimrah. Nan fa ihun yara ya ƙaru dan kamar wasa sai ga mutuniyar taku takai Ɗahare ƙasa ta dimbiji ƙasa ta cika mata baki da ita. Dambe yay dambe aka tambaɗar da man gyaɗar Nimrah, ledar ma dake ɗauke da ƙuli-ƙuli ciki tuni yara sun saka mata wawa. ALLAH ne ya kawo wata mata ta raba wannan tsiya da ƙyar bayan ta kori yaran wajen da bulala. Nimrah na huci tayi buɗu-buɗu da ƙasa har cikin gashin kanta ta fara neman galon ɗin mai da ledar ƙuli, yayinda Ɗahare ke kuka da zaginta da cewa sai ta rama. Da ƙyar matar nan ta janyeta ita kuma Nimrah ta ɗauki galon ɗin manta data kimbiɗe matar ta sakata a gaba suka wuce. Sai lokacin kuma kuka da tsoro sukazo mata. Amma taƙi bari kukan ya fito har matar ta rakata ƙofar gida tace ta shiga ita kuma ta wuce... Hassatu da a yanzu Nimrah ke kira Umma nata aiki da kallon yanda rana ke ƙarayi zuciyarta cike da tunanin ina Nimrah ta tsaya, ta ajiye iccen data ɗebo zata ƙarama wutar dambu da take yi. Gidansu gidan yawa ne mai sassa daban-daban dan haka ta shiga ƙwala kiran sunan ɗan facalarta da take jiyo suritunsa a sashensu. Daga can ya amsa yana fitowa, yazo gabanta yana faɗin, "Umman Nimrah gani". "Lawwali taimakeni dan ALLAH ka bimin sawun Ninrah gidan Inna Yalwa na aiketa sayen mai da ƙulli tun gama karin kummalo ga shi har sha biyu ta wuce bata ba labarinta, maza ka duba min ita kaji". "To". Ya faɗa yana nufar hanyar babbar ƙofarsu, sai ga Nimrah dake jin duk abinda ma ke faruwa rakuɓe a bango da galon a hannu. "Ke Nimrah kizo Ummanki na kira". Harararsa tayi, cikin son huce haushin faɗan da tayi a kansa ta ce, "Baza'azo ba ɗin, munafuki". "Kece munafuka dai, minai miki zaki ce min munafiki?". Duka takai masa da galon ɗin man, ya koma cikin gidan da gudu. "Lawwali ina aikar da nai maka kake shigowa da gudu?". Nimrah ce zata dakeni, tana zaure". Umma najin hakan tasan tayi tsiyar ne, in dai har ba'a zubar mata da mai ba to an zubar da kuɗin ne. Batace komai ba ta cigaba da aikinta. Sai da ta kammala ta shiga wanka ganin azhar ta gabato sannan Nimrah ta lallaɓo ta shigo cikin sanɗa ta ajiye galon ɗin. Ta juya zata koma da gudu Umma data fito a bayin ta manta sabulu ta kamata caraf. Wani ihu ta fasa mata kuwa. "Wayyo ALLAH na shiga uku Umma dan ALLAH kada ki dakeni, Inna ku kawo ɗauki Umma zata tumurmusa ni, wlhy kunkuru na da kafaɗata ciwo suke, na mutu na lalace a taimakeni." Tsayawa kawai Umma tai tana kallon yanda take ihun da dire-diren iskancin. Sai ko ga kakarta da wasu a matan gidan sun shigo. Dai-dai Umman ta kai hannu zata mangareta surukar tata ta dakatar da ita. "Karki sake ki taɓata Hassatu, ke wai baƙya tausayin yarinyar nan ne kullum duka dai duka dai, gata abu ba abuba ko jikin kirki ta gagara yi saboda masifarki". Ran Umma a ɓace ta ce, "Inna nagaji da al'amarin Nimrah a gidan nan, tun gama karin kummalonta fa na aiketa sayen mai gidan Inna Yalwa sai yanzu take dawo min da galon ɗin babu man babu kuɗin, dan iskanci kuma ta shigo ta faɗa min yanda akayi shine ta laɓe a zaure har tana shirin dukan Lawwali dana aika ya nemo min ita. Wannan wace irin rayuwa ce, jiba jikinta daga gani dambe taje tayi yarinya kamar wata namiji". "Koma dai miye dukan ai ba shine magani ba addu'a ce, sannan kowane yaro da irin ƙuruciyarsa". Inna tai maganar tana ƙwace Nimrah a hannun Umma. Dole ta sakar mata ita, tanaji tana gani ta wuce da ita sashensu aka barta da takaici, sai sake bada wasu kuɗin tayi aka sayo mata wani man. Ba kuma ta sake saka Nimrah a idonta ba sai dare da babanta ya dawo gidan....

>>>>>>★<<<<<<

Sai da suka je sallar azhar massalaci suka dawo sannan ya koma sashensu. Ƴammatan ɗazun kawai ne a falon, suna ma jin motsinsa suka shiga rige-rigen faɗawa bedroom ɗin kwanansu. Sai dai hakan bai hanashi fahimtar suna a gidan ba har yanzu. Sai da ya shige ɗakinsa ɗaya daga cikinsu ta fito cikin sanɗa ta shiga bedroom ɗin matar gidan. Tana zaune a bakin katafaren gadonta da yaji shinfiɗa ta alfarma kamar yanda jikinta ke cikin kwalliya. Ɗakin ya haɗu matuƙa, komai tsaf babu wani tarkace. Waya ce a kunnenta alamar magana take da wani, sai dai ganin yanda ƙanwar tata ke tsaye a bakin ƙofa fuska a marairaice ya sata ɗan kauda wayar a kunnenta ta rufe speaker ɗin da hannu. "Miya faru?". "Aunty ya dawo fa, dan ALLAH kije ki bashi haƙurin". Hararta ta ɗanyi da faɗin, "Naji. Fita ki bani waje." Sai da ta tura baki gaba sannan ta juya fuuu ta fita. Ita kuma tai ƙaramin tsaki tana janye hannunta. "Mommy Please ina zuwa, wai ya dawo sashen. Bari naje kin san shi da baƙar zuciyar tsiya, duk yanda mukai zan kiraki. Amma dan ALLAH ki kwantar da hankalinki babu inda zasuje". Banji mi akace mata daga can ba, ta dai yi ɗan shiru alamar saurare kafin ta yanke kiran ta ajiye wayar. Gaban ƙaton mirror ɗin ɗakin taje, ta ɗauka wasu turare ta ƙarama jikinta tare da mouch freshener sannan ta fito. Dining ta nufa ta ɗauki wani ƙyaƙyƙyawan basket ƙarami da aka shirya abinci a ciki ta nufi ɗakinsa. Shigowarta dai-dai da fitowarsa a bayi jikinsa na raɓar ruwa farar fatarsa tayi wani fayau sai towel ɗaure a ƙugunsa. Tabbas Zak-Shadow murɗaɗɗen mutum ne bana wasa ba, dan ko wasu ƴan wrestling ɗin albarka. Sarai yaji sallamarta da motsinta, amma yay biris ko kallon ƙofar baiyi ba yama wuce bakin gado abinsa yana ɗaukar wayarsa dake a bed side drawer tana vibration. Kiran ya ɗaga tare da kai wayar kunnensa. Dai-dai lokacin ta ƙaraso wajen itama bayan ta ajiye basket din acan saman table dake a tsakiyar kujerun ɗakin. A hankali ta manna jikinta da bayansa, ta zagayo da duka hannyenta biyu, ɗaya a ƙirjinsa ɗaya a saman shafaffen cikinsa mai manyan layukan six-pack. Sai ko daya ɗan lumshe ido saboda yanda ta fara zagaya hannun a jikin nasa, sai dai ya dake abinsa, yana cigaba da wayarsa hankali kwance. Bai kuma ajiye ba sai da ya kammala. Yana cireta a kunnensa yay ƙoƙarin janye jikin nasa daga riƙon datai masa, sake ƙanƙameshi tai cike da shagwaɓa ta furta, "Please my Cool one, I really miss you wlhy. I'm so sorry, dan ALLAH kada kaimin hukunci da laifin daba nawa ba. Bance kazo dan na ɓata maka rai ba". A hankali ya ɗan saki huci, batare da yayi maganar da take son yayin ba yasa hannu ya cire hannayenta dake a jikinsa. Da sauri ta dawo ta gabanshi ta rungume shi tsam-tsam, tare da sakar masa kuka. Karo na farko ya ɗan ciji gefen lips ɗinsa, shiru kamar bazai kulata ba sai kuma a hankali ya ɗaura duka hannayensa biyu akan bayanta shima ya zagayeta yana sake matseta. Cike da farin ciki ta sake ƙanƙameshi da bashi kissis masu zafi a saman ƙirji, kafin ta ɗago tai ɗiɗɗishe da ƙafafunta dan ya fita tsawo kawai ta haɗe lips ɗinsu waje guda. (Ehem-ehem nai gyaran murya dan ganin al'amarin babbane), dan kuwa tuni ya ɗagata cak ya ɗora a gadon ta yanda tsahonsu yay dai-dai, tun abun nasu na iya tsayen ana sumbatar juna har takai suka zube a gadon gaba ɗaya...........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 38_

__________________

🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

https://chat.whatsapp.com/DMCa4TXOqV712jNc1UBBRH?mode=ems_copy_t

*_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF 'YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_* 🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327

*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,

Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍

Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍

Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃

Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai , Mmn Yusuf likitar Mata💃😍

Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃

Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃

Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima

KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻

Kalolin gumba Kalolin matsi Kalolin gari Kalolin tsumi

Zumar dabino Zuma Mai rubutu Zumar goron Tula Zumar ridi

Dahuwar kaza Dahuwar zabo Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar tsoka Tara Dahuwar Yan shila Dahuwar kwai Mai rubutu

Turaren mallaka Turaren Mara Turaren tsugunno Turaren k'irji Shuumar humra HATSABIBI turare Hatsabibiyar humra

Matan gaske Maltinat Mata Shayin Mata Tsumin kankana Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a Akwai hadin farinjini na matar aure Akwai kwallin mallaka Zoben mallaka Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻

07069711327 call or Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________ ..........A wahale ta kalla agogon dake bangon ɗakin, ƙarfe shida saura fa na yamma. Wani irin ciwo ƙasusuwanta ke mata, tun kusan ɗaya da rabi bawan ALLAHn nan bai barta ta huta ba, sallar la'asar ma a ɗakin yayi ta, duk da yanda yaga tayi laushi tun ɗazun bai raga mata ba har sai da ta fara masa kuka da roƙo da magiya, a hankan ma sai da ya mula dan kansa... Fitowarsa a bayi ya katse mata tunani, ɗaure yake da towel yana tsane jiki da wani, suna haɗa ido ta tura masa baki. Nashi bakin ya ɗan taɓe yana ɗauke ido a kanta shima. Sai da yaje gaban mirror cikin muryarsa data koma can ƙasa ya furta, "Ki tashi ki gyara jikin ki raguwa kawai. Ki damu mutum yazo-yazo sai yazo kuma kiyita raki". Cikin sake tura baki ta ce, "Kai dama ai baka da tausayi wani lokacin, amma idan bani ɗinba ma wazai iya da kai. Kuma ni ALLAH bazan iya tashi ba, bakaji ƙasusuwana ba kamar ana sassarawa fa". "Da sauƙi ma tunda sarawa ce ba niƙawa ake ba". Ya bata amsa cike da gatse. Bata sake cewa komai ba, dan so take ya sauka a fushin nasa yabar ƙannenta su cigaba da zama a gidan. Shima bai sake magana ba ya gyara jikinsa tare da saka kaya. Ita dai tana binshi da kallo harya kammala. Zuciyarta kuwa wani ƙara cika take da soyayyar sa, tasan samun miji irinsa ba ƙaramin morewa bace. Gaban gadon yazo ya tsaya hannayensa a cikin aljihu yana kallon fuskarta dake a marairaice, ita ko ta kasa kallon cikin idonsa. Shekara ta goma sha suke da aure, amma har yanzu bata iya kallon tsakkiyar idon Zak-Shadow duk da wayewarta da matsanancin soyayyar da take masa, to ƙarshen wayewa ma tun tana shekara biyu a duniya aka tafi da ita UK, ba kuma ta taɓa zuwa Nigeria ba sai a shekarun girma kuma a lokacin sukai aure. Takan ji ya mata kwarjini da cika mata waje a duk sanda yake a gabanta, wani lokacin ma tafi sakewa da shi a waya fiye da kasancewa a face-to-face.... Ɗagatan da yay ne cak ya katse mata tunani, kamar wata babyn wasa duk da kuwa ita ba ramammiya bace jikinta a mulmule yake da ƴar ƙibarta sai dai bamai yawa ba. Hannayenta ta zagayo a wuyansa tana mai kwantar da kanta a ƙirjinsa. A haka ya shiga da ita cikin bayin ya dire cikin jacuzzi. Ƙasa-ƙasa cikin raɗa da wani salon soyayya irin ta manya yana wani kalar shinshinar wuyanta daya sakata lumshe idanunta tsam-tsam ya furta. "Kiyi amfani da ruwa mai zafi sosai zai daina taguwar Zak... Sarkin raki" dai-dai nan ya sakar mata ƴar sumba a cikin kunne data sakata zabura. Yanda ta ƙanƙame jikinta ya sashi sakin wani lallataccen murmushi na ganin dama, cike da takunsa na zarra da jarumta ya bar mata bathroom ɗin gaba ɗaya har lokacin da ƙaramin murmushin a lips ɗinsa, ƙyawawan idanunsa kuwa sun wani shige ciki sosai jan cikinsu yafi yanda suke akoda yaushe. Sai wani luuu yake da su yana buɗewa a gajiye... Gaban mirror ya koma ya saka turare kaɗan ya fice a ɗakin gaba ɗaya dan yana son zuwa gidan su Imran gaida iyayensa.....

<<★>><<★>><<★>>

ƘAUYEN BANKAURA

Rakwacammm!! Ɓarin bazata ya karaɗe kunnen Umma dake tsakar gida tana aiki. Da sauri ta kalla ƙofar ɗakin, tare da ƙwala kiran sunan Nimrah da tasan tana ciki. Shiru taƙi amsawa. Umma tai ƙwafa da faɗin, "Nice nake kiranki kina min shiru ko, shike nan ALLAH ya baki sa'a na shigo ɗakin nan jikinki ne zai gaya miki." Tsulum ta fito jikinta fututu da garin tuwo ko fulawa. Suna haɗa ido da Umma sai ta fashe da kuka tana ɗaga yatsa sama bayan ta lashesa akan harshe. "Umma na rantse bani nai miki ɓarin nan ba, ɓeran ɗakinki ne......" kuka ya ƙwace mata. Rasama abin cewa Umma tayi, kawai ta cigaba da kallonta. Itako tana ƙara ƙarfin kukanta da rantsuwar ba ita bace ɓera ne yay ɓarin nan. Dai-dai nan Babanta dake bayi ya fito. "Kaiya-kaiya lafiya dai kuwa? Uwa kin san bana son wannan shashancin kukan banzar fa. Mi akai miki?". Ran Umma a ɓace ta ce, "Sai anyi mata. Ko ita tayi ai ta iya kukan iskanci. Kuma wlhy yau babu mai hanani dukanki a nan gidan. Fulawar mutane kika ɓarar min daga kawowa ai musu mirjin taliya, bayan a sama na sakata saboda sanin halinki". "Na rantse ɓera ne, Baba kace karta dake ni, ai dai ɓeran yafi ta kamo ta daka". Nimrah ce ke maganar cikin uhun kuka bayan ta rugo tazo jikin Babanta ta ɓuya. Kansa kawai ya girgiza da faɗin, "ALLAH ya shiryeki Uwa, al'amarinki ya fara bani tsoro, yanzu kiyi laifi amma tsabar shaƙiyanci kice wai ɓera ne? Shekaran jiya fa haka kika ɓarar da mangyaɗa Inna ta hana a taɓaki da Kawunki Tanimu, yanzu kuma kayan mutane, sana'ar kike so uwar ki ta daina?". "Baba na rantse ɓera n....." Bummm!!! Abinda Umma ta jeho mata ya daki bakinta. Ai data buga wani tsallen ihu ta zube ƙasa saita fara birgima da faɗin wai Umma ta cire mata bakinta. Haushi ya ƙara turniƙe Umma tazo kanta da tsumagiya ta fara zuba mata a jiki, da ƙyar Baba ya kwaceta. Sai ga Inna ta shigo itama tana sababi, dan a duniya idan kana son ganin tujararta to ka taɓa Nimrah a gidan nan, shiyasa ma take wani iskancin da hujja. Maimakon taima Umma kaɗai faɗa sai ta haɗa harda Baba wai basa son Nimrah. Su dai haƙuri suka koma bata....

Da Nimrah Inna ta tafi sashenta, acan ta lallasheta ta bata nera ashirin wai ta sayo awara da kunu gidan Zinaru. Aiko da farin ciki ta ɗauki kwano ta tafi, gidan Zinaru mai awara da gidansu akwai ƴar tazara kaɗan, dan gidansu Nimrah yana cikin gidajen ƙarshen gari, sune na ƙarshe ma sai jeji babu gidaje a bayansu sai wasu ƙauyukan. Har tabi ta cikin gari ta canja hanya ta koma ta bayan gida tabi wai tafi sauri. Tafe take tana shan majina da doke-doken abubuwa da karan dake hannunta. Wani lokacin ma har yara ƴan uwanta idan ta gamu dasu sai dai kaji ta zuba maka duka, kafin ka rama ta zura da shegen gudu. Gata ƴar sirit babu ƙiba sai tsayi. Taje birtalin da zata fita a bayan gidan ta koma hanyar gari sosai ta hango wasu mutane zaune a ƙasan wata ƙatuwar bishiyar mangwaro dage wajen. Humm Nimrah neman magana ake gaya muku, sannan Nimrah faɗi ba'a tambayeka ba. Fasa tafiyar tai ta koma hanyar inda mutanen nan ke a mangwaro. Babu zato sukaji ƴar muryarta na faɗin, "Suwaye ku?". Da wani irin sauri duk suka juya suna kallonta, sai mutum ɗaya da bai juya ba sai ma runtse ido da yayi tare da jan hiraminsa dake kan wuya da sauri ya rufe fuskarsa alamar baya son ta ganshi, kuma tabbas ta sanshi ne shiyyasa yayi haka. A hasale wani zai mata magana na kusa da shi ya hanashi ta hanyar riƙe masa hannu ya matse. Murmushi yayi mata tare da faɗin, "Yarinya miya kawoki nan?, mu baƙi ne". Fuska a ya yamutsa, maimakon kula zancensa na farko sai catai, "Baƙi? A bayan gari". Sosai mamakin shegen wayonta ya bayyana a kan fuskokinsu. Wanda yay maganar dai ne ya sake mata murmushi. Ya ce, "Eh zamuje ƙauyen Garjalle ne". Batace komai ba, sai ma ido data zubama jakunkunan gabansu, sai kuma ta koma kallon wanda ya rufe fuskarsa. Ganin yanda ta zuba masa ido yasa wanda yay mata magana ɗazun ɗakko naira hamsin ya miƙa mata. "Kinga ƴar Baba amshi wannan ki wuce gida kada a nemeki". Kuɗin ta zubama ido, sai kuma ta girgiza kanta tana kamo gefen kallabinta da aka kulle ta nuna masa. "Bana so, nima Inna ta bani zanje sayen awara ne". "Yauwa to maza kije ki sayo kada ta ƙare". Harta juya zata wuce sai kuma ta dawo. Ta ce, "Kai Baba to miye a wannan ƙaton jakan da yawa? Wannan kuma miyasa ya rufe fuskarshi ko bashi da lafiya?". Babu wanda a cikinsu baiji kamar ya hamɓare yarinyar nan ba. Amma dai wanda ke amsata ya daure ya ce, "Eh baida lafiya. Jakun kuna kuwa mangwaro ne muka zuba". "Ai yanzu ba lokacin mangwaro ba ne". Ta amsa tana sake matsosu. Tsawa na ɗazun ya daka mata dan ya kasa haƙuri, "Ke wuce ki bar nan komu yanka ki mai shegen surutun tsiya, ƴar firit dake sai sa ido kamar aljana". Ganin ya ƙare maganar yana jawo wani ɗan icce a kusa da shi da gudu tabar wajen kuwa. Sai da tai nisa daga nesan tana hakki ta juyo ta ce, "Ku! In ALLAH ya yarda sai kura ta cinye ku masu jajayen ido irin na fatalwa". Daga haka ta sake zurawa a guje. Takaici ya saka wanda yay mata tsawar nan ciro wata ƴar mitsitsiyar bindiga ya saita ta. Cikin sauri wanda ya rufe kansa da hirami ya kaɓar da bindigar yana yaye hiramin da girgiza masa kai alamar karya aikata wannan kuskuren. "Mi kake nufi ko kana da alaƙa da ita ne?". "Babu ruwanka da koma ya nake da ita, ka duba mana yarinya ce ƙarama dududu bata wuce shekara bakwai da wani abu ba. Sannan a tsarinmu bamuyi haka da ku ba ai. Babu cutar da yara, babu cutar tsoffi". "Kai baƙauyen banza anƙi abi dokar taka, kodan kaga mun biyo ta hannunka ne kake tunanin bazamu iya aikin da kammu ba. Kada ka manta kuɗi muka biyaka kai mana komai. Sannan da kake kiranta yarinya ai a yarintar tata tasan rashin kunya ma manya ko. To na rantse maka duk inda naga yarinyar nan a garin nan sai na fasa mata kai kuwa". Da sauri mai hiramin nan ya kalla Ogan tawagar, kafin ma yayi magana ogan ya ce, "Kaga manta da shi, babu abinda zai mata kasan shi dai da zuciyar tsiya. Kamar yanda mukai alƙawari da kai tun farko babu canji, bazamu taɓa yara da tsoffi ba. Kai dai kaje ka fara mana aikin tantance yara mazan da muke so. Zuwa jibi ka tabbatar aikinka ya kammala zuwa dare zamubi gida-gida mu tattaresu waje guda. Ga kayan aikinka nan da kuɗaɗenka zaka iya tafiya". Kansa kawai ya jinjina, sai kuma ya miƙe. "Bazan tafi da waɗan nan kayan ba yanzu, sai magriba zan dawo ɗauka." "Baka da case Goga". Ogan ya faɗa yana bashi hannu. Daga haka ya gyara hiraminsa ya zagaya wata hanyar ɓadda kama ya koma cikin gari..........✍🏼

(Lallai cakwakiya, to wanene wannan 🤔? Yaya batun wanda yace sai ya kashe Nimrah? Kuna ganin zai ƙyaleta kuwa🤔🥲😳. Hummm kudai muje kawai, dan ba'a fara komai ba ma. Cakwakiya ce iya cakwakiya a cikin littafin nan🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️).

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 39_

__________________

*_Kuyi hakuri dani, ni kaina bana gane kai na saboda uzurirrika da suka zagayeni wlhy. Amma ina sha ALLAHU ina gab da kammalawa na dawo da hankalina gaba ɗaya kanku. Ina muku fatan alkairi gaba ɗaya 😘😘😘😘😀🙏_* __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull