Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 20

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 20

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 20: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 20. .........Hajiya Nimrah kam dai koda ta bar wajen gidan sayen…

4,332 words

.........Hajiya Nimrah kam dai koda ta bar wajen gidan sayen awara ta nufa, koda ta sayo yaran gidansu data samu acan gidan awarar sunzo saye suka janye ra'ayinta suka tafi tare ta cikin gari bata dawo ta bayan gidan ba. Ta samu Umma na murza taliya, dan wannan itace sana'arta. Tuni Bana ya sayo mata wata fulawar ta murza a maimakon wadda Nimrah ta zubar, wannan ma ta wasu ce take murzawa a yanzu. Nimrah ta zauna kusa da ita tana shan majina da buɗe kwanon awararta. "Umma kalla, Baba Zinai ta zubo min da yawa". Batare da Umma ta kalleta ba ta ce, "Kin gode. Sai ki tashi ki cire wannan majinar da kike faman sha ki wanke hannu sannan kizo kici dan nasan a fitarki kaf tarkacen garin nan sai da kika taɓa". "To". Ta faɗa cike da abin arziƙi ta tashi tayi duk yanda Umma tace. Harda ɗebo ruwa a moɗa cikin randarsu. Tazo ta ajiye ta kaiwa zaune. Kamar wadda aka tsikara ta ce, "Umma kinga ko, da zanje ta bayan gida nabi, a gonar Baban Zakiru naga wasu mutane da yawa zaune, idanunsu jajaye kamar na fatalwa. Hadda jakunkuna manya sun ajiye, wai sukace min ƙauyen Garjalle zasu je......" Kallonta Umma tai a karo na farko, sai kuma ta ɗauke kai cikin rashin ɗaukar zancen da muhimmanci ta ce, "To uwar soki burutsu zaki fara baƙin surutun naki ba. A gidan uwarwa ake ganin wata fatalwa da rana. Ɗauki awararki kici bana son magana". Baki ta tura sosai, kamar zatayi kuka ta ce, "Na rantse da gaske nake Umma. Kuma har wajensu naje ma, har naga wani mai irin kayan......" "ALLAH idan baki min shiru ba sai na fasa maki baki, koki tashi ki wace wajen Inna in damuna zakiyi." "Mi kuma tayi za'a fasa mata baki? Bayan ɗazu kika gama dukanta". Baba dake shigowa ya faɗa. Sannu Umma tai masa sannan ta ce, "Ta isheni da surutu ne. Wai taga fatalwa ko a gidan uwarwa ake ganin wata fatalwa". Shi abin ma dariya ya bashi, ya kaɗa kai kawai yana ƴar dariyar da faɗin, "Uwa sarkin magana, Zakanyar Kawu Tanimu, in dai zance ne a bar miki abinki". "Baba banyi ƙarya ba fa, kuma harda mai irin kayan......" Murfin kwano da Umma ta jawo ya sakata saurin dafe bakinta dan tasan kaɗan daga aikinta ta kwafɗeta da shi. Shima Baba sai ya shige kawai yana murmurshi.. koda Nimrah taga Umma da Baba sun ƙi sauraren labarinta na fatalwoyi sai ta surare ta koma sashen kakarta Inna. Acan ta fara bata labari, sai dai anyi rashin sa'a itama Inna ta kwaɓeta batare data maida hankali a zancen ba ta ɗauka soki burutsinta ne kawai data saba. Daga ƙarshe ma korota tayi daga sashen akan ta tafi ta bata waje barcin zatayi. Daga haka Nimrah ta fice cikin yara suka kama wasa. Can kamar an tsikareta taba yaran labari suma, abinka da ƙuruciya sukace ƙarya ne, sai ta dage akan suje ta nuna musu. Aiko haka suka haɗa gayya suka fita bada sanin iyayen ba bayan gidan. Tafiya takanas babu ko gargada ta kaisu har wajen mangwaron nan dake cikin gonar Baban Zakiru kamar yanda ta faɗs, sai dai a yanzu babu kowa wajen mutanen sun tashi sai robobin ruwa da suka sha da takardun nama, wata ledar ma ba'a cinye naman ba. Haka sukaita tsincewa suna ci, suka tattaro robobin ruwan dana lemo suka dawo gida. Yawancin iyayen sun gansu da waɗan nan robobin ruwa dana lemo, amma sai basu tambayesu daga ina ba saboda a wasu lokutan kawunsu Tanimu kan raba musu dan su dinga zuba ruwan zuwa makaranta, shima kuma yana zuwa dasu ne daga birni. Da yamma gab da magriba Umma ta gama aikin tuwon dare. Ruwan data ɗumama ta ɗiba taima Nimrah dake ta damunta da surutu tana cin gyaɗa wanka. Ta shafa mata mai ta saka mata kaya. Tuwon Inna data zuba a langa ta saka a botiki ta tura gaban Nimrah ɗin. "Ki ɗauki tuwon Inna kikai mata, sai ki dawo ga miyar nan itama zan saka miki a wannan botikin ki ɗauka ni zan shiga wanka bana son a kira magriba, saura kuma dan ALLAH kiyi abinda ban saki ba, ALLAH bazaki bini gidan Malam ba in har kikai min wata ɓar nan". "To Umma, ALLAH ba abinda zanyi, dan ALLAH kada kice bazaki je dani ba, ina son na gaida Malam da Iya". Nimrah ta faɗa cikin tsalle-tsalle tana daukar botiki. Ita kuma Umma ta ɗauki ruwan wankanta ta shige bayi tana faɗin, "In da kinso ganinsu ai ƙafarki tasan inda suke". Nimrah da bataji mi Umman ta faɗa ba ta ɗauki tuwon Inna ta fita cike da murna zasu gidan Malam, (Malam dai shine mahaifin Umma, babban malami ne a yankin kuma dattijon arziƙi da kowa ke girmamawa) koda Nimrah ta shiga sashen Inna babu kowa, dan dama ita kaɗaice a sashenta tunda kishiyarta ta rasu sai dabbobinta. Ɗaki ta shiga ta ajiye mata kwanon tuwon ta fito, ta sake komawa sashensu ta ɗakko miyar ma ta kawo. Harta juya zata tafi ta hango ƙwayayen kazar Inna dake akurkin jikin katanga gab da fita a sashen. Kwana tayi ta koma wajen akurkin ta duƙunna ta ɗauki ƙwai ɗaya ta saka a botikin hannunta, sai kuma tayi ɗan tsai kamar mai lissafin sauran ƙwayayen, hannu tasa ta ƙara ɗaukar ɗaya, ta ce, "Ni ɗaya Umma ɗaya. To Baba fa, shima bari na ɗaukar masa, idan Inna taji harda shi akaci ai bazata dake shi ba tunda yayi babba sosai." tana maganar tana leƙa cikin akurkin duba wasu ƙwan. Sai dai maimakon ganin ƙwari taci karo da wata jaka. Hannu tasa ta jawo jakar. Tare da faɗin, "Lah Inna har cikin jaka take ɓoye ƙwai, aiko saina ɗibawa Babana da Kawu". Tana maganar tana kici-kicin buɗe jakar, sai dai ta kasa. Abinka da yaro tana jiyo maganar Inna ta yayimi jakar ta jefa a botikin ta ɗauka da gudu ta shige bayi, sai da Inna ta shigo ta shiga ɗakinta Nimrah ta fito da gudu nan ma ta fice zuwa sashensu da wannan ƴar jaka da zato ta ke ita ƙwai ne Inna ta ɓoye a ciki. Lokacin da take shigowa sashensu Umma ta shige ɗaki dan anata kiran sallar magriba. Anan tsakar gida ta ajiye botikin da jakar duka ta nufi ɗakin gayama Umma takai wa Innar tuwon. Koda ta faɗa mata sai tace taje tayo alwala suyi salla su tafi. Cikin farin ciki ta fito, dan tasan koba komai zatayi wasa da ruwa ai. Sai da ta gama facaccalinta kuwa sannan ta tafi ɗakin tayi sallar. Ta mance da batun ƙwai taci tuwo suka tafi gidan Malam. Kafin su dawo ta ɓingire barci, sai goyota Umma tayi ma. Sanda Baba ke shigowa gidan ta jima da yin barci. Misalin sha ɗaya na dare Umma da Baba sun gama cin abinci da hira Umma ta fito kaye-kaye tsakar gida sai ga Tanimu ya shigo sashen da sallama. Amsa masa tayi, tana murmurshi da faɗin, "A'a kawun Nimrah baka kwanta ba?". "Wlhy kuwa ban kwanta ba Yaya, nace bari nazo nai muku sallama dan in sha ALLAHU gobe zan koma birni. Amma sai yamma zan wuce da safe dai zanje hayi wani ɗaurin aure, daga can nake son nabi wasu abokanmu da zasu zo ɗaurin auren suma daga birni." "Kai kawun Nimrah da wuri haka, wannan karon ai baka daɗe mana ba, kwata-kwata bakafi sati biyu ba". "Wlhy naso yin sati uku ne fa, to ganin mota a sauƙaƙe yasa zan wuce kawai. Amma bazan jima ba nanda ƙarshen wata zan dawo yin dashen albasar nan." "Ato da gaskiyarka, ALLAH to ya kaimu. Ka shiga Yayan naka na ciki ai, bari nima na ƙarasa kaye-kaye dan karnuka na shigo mana da dare". Amsawa yay da to yana shigewa, ita kuma ta cigaba da tattare kayan tsakar gidan. Ciki harda botikin nan da Nimrah ta sakawa jaka a ciki. Batare da Umma ta damu da miye cikinsa ba ta rufe shi da murfinsa dan dama tana kwaɓin fulawar taliya ne a ciki idan zata murza. Ɗaki ta shiga da su ta ajiye, daga haka ta zauna suka cigaba da hira da Baba da Tanimu....

★>>>>>★<<<<<★

Tunda ragamar jejin ta koma hannunsa a daren jiya duk ya kasance a tsarguwa. Ko barcin kirki baiyi ba, dan haka kawai yake jin wani abu mai nauyin gaske a zuciyarsa. Ga yawan faɗuwar gaba dake samunsa. Bafa yau ne karo na farko da Zak-Shadow ke barin jejin shugabanci ya koma hannunsa ba, amma sai yake jin na wannan karon da girma sosai. Wajen misalin ƙarfe uku na dare barci ya gagaresa gaba ɗaya, sai kawai ya tashi. Wayar sadarwa ya ɗauka, yay kira kai tsaye ga dukan Captains dake cikin rundunar, cikin bada umarni ya buƙaci ganinsu. Basu ko ɓata lokaci ba, dan kafin ƙarfe huɗu na asuba sun tattaru a sansanin nasu. Meeting Major Imran yay da su na minti talatin kawai, kafin biyar na asuba ya sallamesu kowa ya nufi komawa sansaninsa....

★A lokacin da Major Imran Abbas ke zaman wannan meeting da Captains ne yaran ƙungiyar duhu suka samu damar kutsa kai cikin wasu sansani kamar yanda suke iso tun farkon dare. Mataki na farko da suka fara amfani da shi shine datse na'urorin sadarwa dake cikin sansani uku. Cikin bazata ƙarfe biyar dai-dai na asuba matasan jaruman sojojin na ƙoƙarin gabatar da al'awalar shiga sallar asubahi, wanda basa sallar na ƙoƙarin amsar duty kawai sukaji saukar harbin kan mai uwa da wabi. Tabbas duk wanda bai zama jami'in tsaro ba bai san minene tashin hankali da ainahin jarumtar mazan ƙwarai ba. Cikin abinda baifi minti biyu ba sojojin nan sun rikiɗe maida raddi, hatta waɗanda suka sami harbi bata ciwon suke ba sam balle zubar jinin da suke yi. Lokacin da Captains ɗinsu suke dawowa wajen ƙarfe biyar da wasu mintina wasa yayi wasa, domin kuwa waje ya hargitse hargitsewa irin ta MAZAJEN FAMA. Cikin tashin hankali Captains ɗin sukai ƙoƙarin kai rahoto ga sauran sansani ta hanyar wayoyin sadarwa, amma abin mamaki duk basa aiki. Makircin masu makirci yayi tasiri kenan bisa ƙaddarar UBANGIJI. Ba wannan bane hari na farko da suka taɓa fuskanta, amma wannan kam ya girgiza hazo sakamakon tsahon shekaru uku kenan babu wani damuwa har suna jin sun gama nasara akan azzalumai, domin kuwa shiri suke na barin jejin a cikin wannan shekarar ganin zaman lafiya ya samu a yankin fiye ma da yanda ake fata..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

40

........Gari ya ɗan fara hasken dake bayyana safiya, Major Imran daya kasa zaune ya kasa tsaye na a bakin ruwa yana zubama tsuntsayen nan dawa tamkar yanda sukeyi shi da Zak-Shadow wani irin nishi ya fara tasiri a cikin kunnen sa. Kowane yanayi soja mai ankarewa ne akan aikinsa. Cikin sauri ya ajiye robar dawar yana waige-waige da ƙara buɗe kunne saitin inda yake jin nishin. Tabbatar da wajen ya sashi zabura tare da ciro bindiga a jikinsa yaja ya ɗana, cikin sanɗa da jarumta ya tunkari wajen. Dai-dai yana isowa gab aka ƙara jan nishin da ƙarfi tare da hankaɗa ciyayin wajen. Soja ne ya bayyana jikinsa kace-kace da jini, da ƙyar yake iya ambaton, "Commandos, help us! We need you here! Where are you?.". Ai Major Imran baima San ya zabura kansa ba. Cikin tashin hankali yakai duƙe gabansa yana mai kamashi gaba ɗaya... "Soldier! What happened? Report now! Are you okay?.". "Sir! Hari, hari aka kai mana a kusurwar ƙofar kudanci, sun mana ɓarna, sun datse na'urar sadarwa, shiyasa muka kasa isar da sanarwa......" Ya kasa ƙarasawa saboda aman jini da yake yi. Bayyana tashin hankalin da Major Imran Abbas yake ciki ɓata lokaci ne. Sai dai da yake soja-soja ne babu alamar rawar jiki ko ɗimuwar zahiri. Da kansa ya ɗauki sojan nan a hannunsa ya juya nasu sansanin....

Zamu iya cewa wannan shine mafari, mafarin tashin hankali na bazata da masu makirci suka ɗauki kwanaki suna shiryawa da daidaita wannan gaɓar domin aiwatarwa ya tabbata. Ba ƙaramar ɓarna akaima sansani ukun nan da aka kaima hari ba. Gashi an yanke musu na'urorin sadarwa ta yanda har Headquarter sun gagara kai rahoto balle sanar da Zak-Shadow halin da ake ciki. Sai misalin ƙarfe goma sha ɗaya aka samu damar fita da waɗanda suka jikata, sai mutane shida da tun asubahin ma sun rasu, sojoji huɗu ƴan ta'addan biyu......

>>>•>•>•<•<•<<<

Tunda ya fita sallar magriba sai ƙarfe tara saura suka shigo gidan shi da Ammar dake maƙale da shi, dan shima gab da magriba ya iso daga Zaria inda yake karatu. Bai haɗu da Dadan nasu ba sai a masallaci bayan sun fito sallar magriba. Sosai suke so da ƙaunar Zak-Shadow, dan shi suka buɗe ido suka gani kuma suke kallo a matsayin uba. Ba sunan Dada da suke kiran shi ne kawai girmamawar da suke masa ba. Hatta umarni idan ya basu ko saka doka akan abu ko hanasu yin wani abu duk son da sukema abunnan sun barshi kenan har abada. Dan sunyi imanin bazai hanasu abinda zai amfane su ba, ba kuma zai sakasu yin abinda zai cutar da su ba. Komai na hidimar rayuwarsu: ci, sha, ilimi, lafiyarsu da duk wani abu da akema ɗa ɗan gata shi da Mammah ne sukai musu a rayuwa. Taya zasu gagara masa biyayya su zama butulu. Sun tabbatar soyayyar da Dada ke musu soyayya ce irin ta ƴaƴa da mahaifi. Babu abinda zasu biya shi da shi sai addu'a da fatan shima ALLAH ya bashi tashi zuri'ar, dan rashin haihuwar nan tasu na damun kowa kawai dai basa magana ne... Tunda suka baro gidan su Imran surutu kawai yake zuba masa. Shi ko Zak-Shadow nashi murmurshi, sai lokaci-lokaci yake jefa magana a taƙaice. Hakan baya damunsu, dan duk wanda yasan Dadan su yasan bamai yawan magana bane. Sam ba miskili bane, amma bai da yawan surutu ko dariya. Idan yaso hirarsa kuwa zakaji yanayi da Mammah sosai kamar bashi ba. To suma sukan ɗan samu kanshi wani lokacin ya biye musu idan yana jin nishaɗi.. Gaba ɗaya kowa na falon har matarsa da ƙannenta. Dama Aunty Ummi da Aunty Mommy da tun ɗazun suna gidan tare da shi. Aunty Mimi ce sai yanzu ta iso, ɗazun sanda Biebah ta kirata sun fita da mijinta anguwa. Suna yin sallama kuwa ta taso a guje cike da farin ciki tana faɗin, "Oyoyo Dada ta rungumeshi". Kansa ya girgiza kawai tare da ɗan bubbuga bayanta. "Ke dai baƙya girma ko". Ɗagowa tai tana dariya da kamo hannunsa cikin nata ta riƙe. "Dada in dai a gabanka ne ina nan ƴar yarinyata Autarka, dan ma wannan ɗan buƙulun yazo ya ragen farashin autar ne da waccan yarinyar". Tai maganar tana hararar Ammar da Biebah. Ramawa Ammar ɗin yayi shima, "Sai ki haɗiyi ƙwallon mangwaro ki suma, dole dai a ce da mijin iya baba ai. Muma autocin nan dai ne ko Auta". "Yes Yayana". Biebah ta amsa masa tana ma Mimi gwalo. "Dada ka gansu ko, shiyasa idan baka nan bana son zuwa gidan nan na daɗe". Murmushi yayi kaɗan shi dai, sai kuma ya shafa kanta da faɗin, "Ki daina lulasu, ke yanzu ai kin girmi ƙuruciyarsu. Kalleki fa da yara har biyu". Fuskata ta ɓoye a jikin hannunsa, dan ita kunya take ji ma ace ta haihu. Shima bai sake cewa komai ba yaja hannunta suka ƙarasa cikin falon. Tashi Yaya Bilal yay ya bashi kujera da yake, ya koma kusa da Mammah, dan shi dama ɗan shagwaɓar Mammah ne, ya girma amma bai san ya girma ba. A ƙasa Ammar da Mimi suka zauna kusa da ƙafafunsa, duk sun riƙe masa hannaye kamar wasu ƙananun yara ko zai gudu ya barsu. Biebah tai ƙwaɓa-ƙwaɓa da fuska kamar zatai kuka ganin sun tsare ko ina bata samu wajen zama kusa da Dada ba. Gefensa ya nuna mata da ido, basa iya zama a kujera idan yana kan kujera har su Ja'afar kuma, amma bazata iya kuma ƙin bin umarninsa ba, dan haka ya taho saɗaf-saɗaf kamar munafuka ta zauna a hannun kujerar da yaken. Dai-dai nan Mommy ta fito a kitchen ɗauke da kofi akan tray ƙarami. "Oh ni, duk kunzo kun wani dabaibayeshi kamar ku kaɗaine da Dadan." "Kema dai ƙya faɗa Mommy". Cewar Aunty Ummi tana harararsu. Murmurshi Mammah tayi, yayinda matarsa dake cike fam da kishi da takaici kamar ba ƴan uwansa ba ta ɗan taɓe baki. Mugun haushin wannan soyayyar da yake nunawa ƴan uwansa take. Ta taɓa suɓutar bakin nuna masa abin yayi yawa, daya zuba mata wani mummunan kallo ai bata sake kwatantawa ba. Bilal ya ce, "Dada dan ALLAH sati biyu zakai mana ko? ALLAH muna missing ɗinka muna son muyita kallonka, idan kana nan gidan yafi daɗi". Sai da ya amshi mug ɗin shayin da Mommy ta kawo masa ya kai baki kaɗan sannan ya amsa Bilal ɗin. "Kuyi haƙuri Bilal, lokaci na zuwa da zan zo na zauna tare da ku na baku dukkan lokaci na. Nima ina jin farin ciki a duk sanda nake tare da ku". Sosai maganarsa ta shige su da saka su jin ƙaunarsa na ratsasu. Naneeha data ɗan zuba masa ido ya kalla, sai kuma ya kauda kansa. Falon ya ɗanbi da kallo tare da faɗin, "Ina Mu'azz!". Biebah ta ce, "Dada yayi barci, ya gaji da jiranka ya ɓingire". "Da wuri haka". Ya faɗa a taƙaice. Mammah dake duba wani littafin addini ta ce, "Wannan ɗan naka ai ruwa-ruwa ne. Ina ga dai sojan zaka maidashi ko zai canja." Dariya sukayi su duka. Banda shi daya ɗan murmusa kawai. Haka suka cigaba da hira cike da nishaɗi, duk da shi tashi maganar bamai yawa bace, sai dai sun sha murmushi dan su kam yana musu murmushi ba kamar a waje ba. Kasancewar duk anan su Aunty Ummi ma zasu kwana wannan hira bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗayan dare. A hakan ma sai da Mammah tace su barshi yaje ya kwanta, dan su basu ƙi a kwana ana hira suna ganin Dada ba. Tuni Nabeeha da ƙannenta dama sun koma can sashen nasu tun wajen 11. Dan haka ya fito, sai Ammar da Bilal da sukai masa rakkiya har ƙofar sashen nasa sai da ya shiga sannan suka koma...

Ganin haske alamar batai barci ba kai tsaye ɗakinta ya nufa a karo na farko tun isowarsa gidan. Zaune kuwa ya sameta tana waya, ta canja kayanta zuwa na barci da sukai mata ƙyau sosai. Idanunsa a kanta yay sallama cike da nutsuwarsa. Idanu ta ɗago a hankali ta kalleshi, sai kuma ta kawar tana yin sallama da wanda suke wayar. Dai-dai tana ajiye wayar yakai zaune kusa da ita, kasancewa a sofa take zaune. Ganin kallon daya zuba mata cike da tsarguwa ta ce, "Mummy na gaishe ka". "Na gode". Ya faɗa a taƙaice. Kanta ta jinjina masa itama, sai kuma ta matso kaɗan ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hannunsa ta kamo ta saka nata a ciki. Mintuna kusan biyu suna a haka shiru, sannin hirarsa sai ya gadama ya sata ɗaga kai tana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskarsa, idanunsa a lumshe suke tamkar mai barci, amma tasan ba barcin yake yi ba. Dan haka ta ɗan matsa hannunsa tare da faɗin, "My Cool". "Uhhmm". "Kayi barci ne". Maimakon amsa mata sai ya buɗe idon kawai yana kallonta. Kasa jurewa tai ta ɗan risinar da nata tana sauke numfashi. Cikin jin shakkar faɗar abinda ke bakinta ta cigaba da matsa yatsun hanun nasa, kafin a ɗarare ta ce, "Dan ALLAH wannan karon ka yarda muje muga likitan nan mana. Ta hakanne zamu fahimci idan wata matsala ce a tare damu mu tashi mu nema magani. Shekara goma sha fa ba kwana goma sha bace My D. Dan ALLAH kai baka jin wani abu a ranka idan ka kalla ƙannenka da yaransu? Ga su Ja'afar suma zasuyi nasu auren, nan da shekara ɗaya sai kaga duk suma da yaransu. Haka kake son suma matansu suzo a bayan bayana su haihu ina kallo...." Shiru ya mata yaƙi tankawa. Sai hakan ya ƙara ƙular mata da zuciya, dan haka yake mata a duk sanda ta kawo masa batun zuwa ganin likita. Kuka ta fashe masa da shi mai ratsa zuciya. Kafin ta yunƙura fuu ta miƙe da nufin bar masa wajen, batare daya kalleta ba shima ya riƙo hannunta, tare da fisgota ta faɗo jikinsa gaba ɗayanta. Kici-kici ta fara nason tashi tana ƙara ƙarfin kukanta, amma riƙon da yay mata da hannu ɗayan nan kawai ta gagara tashin. Ganin ba iya ƙwatar kan nata zatai ba da gaske sai kawai ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta cigaba da raira masa kukan.Tsawon lokaci suna a hakan idanunsa a rufe tamkar bai san tanayi ba, ganin ba dainawa zatai ba ya ɗagata a jikin nasa ya miƙe da nufin bar mata ɗakin gaba ɗaya.........✍🏼

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 41_

__________________

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LkEgiP5qOEo9YDYjaeZLLc?mode=ems_wa_t✍️✍️ Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed yar mutan Chadian traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products at home my people bazamafa a kwai zafafan promo damukeyi in Sha allahu zuwa on 15 zamugama sannan gareku Yan Kano free ne kayanki zasuzo miki amma fa karyazo bayan mungama promo kuce kyauta ne aa zakibiya kudi nagode takuce yar mutan Chadian mai gyaran ciki dawaje 💃💃 please banda maza,❌maza❌ In kinada matsala wadda zamu iya taimaka miki 09065504546 Ga PRODUCTS DINMU KAMAR HAKA MAGANIN SANYI TSUMIN BOM MADARAR TABAJE GORON TULA SYRUP ZUMAR SHADAMATSIN GARIN YAUKAYAUKA EMERGENCY GARIN KINFI KAZA DADI SIRRIN MALLAKAR KASA SIRRAN GIDANKI DAHUWAR KAZA DAHUWAR CICCIBI DAHUWAR YAN SHILA HMM BAZASU IRGUBA INA GODIYA SOSAI MY PEOPLE 🥰🥰

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Zaram tasha gabansa, sai dai ta gagara kallonsa kamar yanda shi yake kallonta. Zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗi, shawarwarin mahaifiyarta na bata ƙwarin gwiwa ta ce, "Haysam kana saka min shakku a zuciyata da jin yarda akan maganganun mutane. Kodai baka son haihuwa ne kamar yanda kowa ke faɗa?". Ya daɗe bai ji abinda ya sokar masa zuciya kamar kalamanta ba. Cikin wani irin yanayi mai girman gaske ya zuba mata idanu yana mata wani irin kallo mai zafin gaske. Zuciyarsa kuwa tuni ta yinƙuro ta tokare maƙoshinsa. Ya tabbata in dai ya buɗe baki akan bata amsar kalamanta zai iya gaya mata mai zafin gaske da zata ninka wadda ta gaya masa sau dubu. Dan haka sai kawai ya zagayeta ya fice a ɗakin gaba ɗaya. Fashewa tai da wani irin kuka tana kaiwa ƙasa ta zube. Jifa ta fara yi da duk abinda ya tare mata gaba. Babu abinda ke ƙara ingiza fushinta sai kalaman mahaifiyarta. Tabbas ta yarda gaskiya Momy ke faɗa akan mijinta. Dan ita kanta a wasu lokutan takan zauna taita tunani game da al'amarinsa. Yanda yake mutum mai yawan buƙatar iyali miyasa idan ya tafi wajen aikinsa in ba ita ta takura masa da magiyar yazo tana missing ɗinsa ba dan kansa baya shiryowa yazo dan yin hakan. Sannan ko zuwan yayi idan ba ita da kanta ta kawo masa kanta ba bazai nema ba. Da tana ɗauka tsabar girman kansa ne ke sashi yin hakan. Sai da mahaifiyarta ta fara fargar da ita ne akan kodai yana neman mata ne sannan ya ɗan fara taba tunaninta, sai dai zuciyarta bata amince ba tana wasi-wasi dan tasan sa da ƙyanƙyami. Amma zuwa yau zuciyarta kamar ta fara jin aminci da wannan zance, musamman idan ta tuna maganar wasu ƙawayenta da kance ta tashi tsaye akan mijinta dan wasu sojojin akwai son matan tsiya, shiyasa ma basu cika son haihuwa ba dan kar aima ƴaƴansu abinda sukema wasu. Waɗan nan tunane-tunane Nabeeha ta cigaba da tasirantarwa a wannan dare suna ƙara tunzurata da rikita mata sissafi. Koda ta sake kiran mahaifiyarta ta gaya mata yanda sukayi da mijin nata sai ita kuma ta sake tabbatar mata hasashensu ya zama gaskiya dai, Zak-Shadow baya san haihuwa a gaske. Kuma tabbas dole ta miƙe tsaye da bincikensa dan ta tabbatar shin baya neman mata. Ai ko haka ta ƙara hawa ta zauna. Da safe har ya shirya ya fito bata leƙashi ba. Sai shine ya shigo ɗakin nata. Yanda ta faffasa abubuwa kawai ya tsaya yana kallo, kafin ya maida idanun kanta. Tana kwance a kan gado da waya a hannunta. Sarai kuma ta ji shigowar tasa amma tai biris. Uffan baice mata ba ya juya ya fice a ɗakin. Sai ta raka bayansa da harara tare da jan tsakin daya shiga kunnensa a bazata, dan ya juyone da nufin dawowa ɗakin ya mata magana. Cak ya tsaya tamkar wanda akai ma tsawa, sosai fuskarsa tayi masifar sake haɗewa fiye da yanda take, idanunsa sun wani juye alamar zuciyar ƴan maza ta motsa, dan ni kaina na tsorata addu'a kawai nake kar yace zai koma ɗakin. Ganin ya bar wajen ya sani sauke ajiyar zuciya. Sashen Mammah ya nufa, a kallo ɗaya kuma ta fahimci ransa a ɓace yake. Sai dai batayi magana ba saboda ƙannensa. Shima cikin dannewa da haƙuri da ALLAH ya bashi ya fuskanci ƴan uwansa ya ajiye batun Nabeeha gefe.....

>>>>>★<<<<<

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull