Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 21

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 21

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 21: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 21. Gaba ɗaya wannan yinin su Major Imran sun yishi ne akan…

3,482 words

Gaba ɗaya wannan yinin su Major Imran sun yishi ne akan ƙafafunsu wajen binciken son sanin su wanene suka kawo musu wannan harin, ta wani ɓangare kuma hankalinsa a tashe yake matuƙa akan son samun Zak-Shadow kafin zancen harin da aka kai musu ya kai Headquarter asan baya jejin tunda yayi fita ne irin ta sirri. Amma har wani daren bai samu mafita ba. Sai dai sun sake shiri na musamman akan kowane sansani dama jejin gaba ɗaya. Dama haka wannan munafukai ke buƙata, wato karkatar da hankalin su Imran ɗin, sun ko samu nasara zamuce, dan ana cikin sallar isha'i suka sami nasarar kai hari a ƙauyuka uku. Bankaura dake babban ƙauye na wannan yankin, sai wani ƙauye da ake kira Gangare, sai kauyen Marke. Wannan sabon tashin hankali ne da waɗan nan ƙauyuka basu taɓa fuskanta ba a baya, dan rikicin shekarun baya daya faru a sauran ƙauyukan ne banda nasu. Ruwan fitar harsasai da ƙarar tashin nakiya ce ta fara jan hankalin wasu a yaran su Imran. Cikin gaggawa wani haziƙin matashin soja ya silalo yabaro inda suke da bayi da nisa da ƙauyukan ya sanar da Imran. Ai babu ɓata lokaci ya zabura da wasu tawaga suka nufi wannan waje. Ƙauyen Gangare suka fara shiga kasancewar shine farko. Tun a farkon shiga suka fara cin karo da gawarwakin mutane. Hankalinsu ya tashi dan sun fahimci al'amarin da lallai babba ne. Ai babu wani maganar ɗaga ƙafa suka buɗe ma yaran su Dagger wuta, nan fa sabon wasa ya koma tsakaninsu, mutanen gari kuwa tashin hankali yasa sun watse cikin jejin, wasu kuma a cikin gidajensu suka samu wajen ɓuya. Matuƙar bata kashi akasha a wannan dare, kowane ɓangare sun gama jigata musamman mutanen gari da sukafi fuskantar ƙalubale, an kashe mutane da yawa, a wannan ƙauye. Ba'a samu lafawar wannan hargitsi ba sai zuwa ƙarfe shida da rabi na asuba gari ya fara haske, daga ƙarshe dai su Dagger suka gudu, an kashe wasu a cikinsu suma, an kama mutane biyu kuma, kamar yadda wasu a cikin yaran su Imran suma aka ji musu ciwo, sai dai soja ko ɗaya bai mutu ba. Sojoji na tattara mutanen da suka jikkata Imran ya samu waya ta wani da aka kashe, gefe ya koma ya shiga neman layin Zak-Shadow, a lokacin kusan ƙarfe tara na safiya. A kuma dai-dai wannan time ɗin ne Zak-Shadow yake a sashen Mammah tare da ƴan uwansa bayan ya baro nashi sashen da ɓacin ran matarsa.

★ Bilal ne yaga wayarsa na haske, dan shi hankalinsa ya tafi kan magana da Mammah. "Dada kamar ana kiran wayarka". Bilal ɗin ya kalla, sai kuma ya juya yana kallon wayar dake a gefensa. Baƙuwar number ce, shi kuma baya ɗaga baƙuwar number. Dai-dai nan kiran ya katse, har zai ɗauke kansa sai kuma wani kiran ya sake shigowa a karo na biyu, cikin takaici ya ɗauki wayar zai kashe gaba ɗaya dan zuciyarsa sam babu daɗi... "Ya kamata dai ka ɗauka kasan waye". Maganar Mammah ta dakatar da shi daga kashe wayar, cikin bin umarni ya ɗaga tare da sakawa a hansfree. Jigatacciyar muryar Imran ta daki kunnensa, "Imran ne Sir!........." Wayar ya ɗauka yana miƙewa tare da cireta daga hansfree ɗin gaba ɗaya. Cikin wata irin razananniyar murya ya ce, "What! Shine sai yanzu kuke sanar dani. Imrannn!!!". Yanda ɗakin ke amsawa da amon muryarsa yay matuƙar tada hankalin ƴan uwansa, a zafafe ya yanke kiran yana mai isowa gaban Mammah. Kai tsaye ya ce, "Mammah zan wuce akwai matsala". "Ya rabbi, miyake faruwa?". "Ba lafiya Mammah, hari aka kai mana. Kiyi haƙuri zamuyi waya". Daga haka ya fice daga falon kamar wani yunwataccen zaki. Hankalinsu a tashe duk suka miƙe suna kallon juna, sai kuma duk sukayo waje suma. Dai-dai nan yake fitowa daga sashensa da jaka a hannu, sai hular mashin ɗinsa. Gaban Mammah yazo ya ɗan rungumeta, ta shafa kansa tana mai masa addu'a, dan yanayinsa kawai ya tabbatar mata al'amarin babba ne sosai. Hakama ƙannensa a tare suka zo suka rungumesa tare da masa addu'a. Da sauri yabar wajen ganin su dukansu suna faman sharar hawaye, har Mammah duk jarumtarta sai da ta kauda kai gefe, yana hawa ƙaton mashin ɗinsa da in yana tafiya baka jin ƙara Bilal ya zabura ya nufi gate da gudu ya buɗe masa. Ai ko a guje ya fice daga gidan shima, dan ji yake kamar ya rufe ido ya gansa a jejin...

Ganin kowa ya fito babu Nabeeha ƙanwarta ta tafi da gudu tana buga mata ɗaki da kiranta. "Aunty!. Aunty! Ki buɗe dan ALLAH Dada fa zai tafi". Wani irin dukan zuciyar Nabeeha kalmar zai tafin tai a karo na farko. Cikin sauri ta diro a gadon da take kwance. Yanzu fa taji yana buga mata ƙofa da kiran sunanta tai banza da shi, a zatonta kan maganar jiya ne yazo ko fitinarsa ce ta motsa, duk da tasan kome yake ji idan yana fushi zai iya danne abinsa ya haƙura, shiyasa taƙi buɗewa. Tana buɗe ƙofar ƙanwarta taja hannunta kawai suka fito, sai dai rashin sa'a suna fitowa tsakar gidan ana rufe gate alamar harya wuce. Sharrr hawayen da suka cika mata ido suka shiga rige-rigen zubowa, sai kawai jikinta ya kama rawa har tana neman faɗi sai da ƙanwarta ta riƙeta. Ciki suka koma, dan su ma su Mammah sun shige nasu sashen. Bedroom Nabeeha ta shige tana mai fashewa da kuka, dan ita duk tunaninta abinda tayi jiya ne da ƙin buɗe masa ƙofa a yanzu ya fusata shi. "Aunty dan ALLAH ki daina kukan nan, kimasa addu'a kamar yanda sauran ƴan uwansa ke masa. Dan ita yafi buƙata a garemu baki ɗaya". "Ismat bazaki gane ba, laifina ne, nasan nina fusatashi ya tafi. Miyasa daya buga ban buɗe masa ƙofar ba...." "Anya haka ne kuwa Aunty. Kamar fa kiransa akai daga wajen aiki inaga wani abu ne ya faru". "Wajen aiki?". "Tabbas haka ne Aunty, amma ki bincika wajen su Mammah". Hawayenta ta shiga sharewa da sauri. Sai kuma ta jawo wayarta ta shiga kiran number ɗinsa. Amma harta katse bai ɗaga ba. Ta jera masa fin kira goma no answer, sai ta sake fashewa da kuka tana yin jifa da wayar, ALLAH ma ya sota bata faɗi ƙasa ba Ismat ta cafe..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 42_

__________________

https://wa.me/+23408067422528 Kina son rage kiba ba tare da kin daina cin abunda kike so sannan ba tare da kinyi gudawa ba? To kimin magana domin samun hanyoyi da zaki rage kiba ba tare da kinsa wahala ba. Ko kuma matsalar gashi ce ke damunki, ko rashin tsahon gashi ne, shima muna da solution dinsa. Ko kuma fatar ki tana lalacewa ne a sanyin? Muna da ingantaccen man da zai gyara miki kafafunki ko kuma kamar ta jarirai. Ko kuma kafarki ce take kaushi a sanyin nan muna da ingantaccen mayuka Ko kuma man gyaran fata kike so da zai gyara miki jikinki a sanyin Nan ?duk muna dasu ba tare da kinsa wahala ba sannan 100% natural ne. Yar uwa idan ma bangaren samun kudi shima kike nema shima duk zamu koya miki. Kedai kawai ki mana magana domin karin bayani.

https://wa.me/+23408067422528 "Shin Ke uwa ce, kina son samun kuɗi ba tare da kin fita kin bar 'ya'yanki a gida ba?" ko kuwa ke student ce kina son samun karin kudin shiga ko kuma ma dai kawai kison karin side hustle ne Tare da Oriflame, za ki iya yin kasuwanci daga wayarki a gida. Ba tare da kin fita ba. Mata da yawa sun riga sun farga da wannan Kasuwanci kuma suna moriya dashi sosai, suna making kudi daga gida, kuma ke ma za ki iya sannan bayan ribar ki zaa biyaki salary a karshen wata. ko kuma kina son yin siyayya for personal use ne ba tare da anci riba dake ba ga link nan a kasa zaki iya register da kanki it's free👇

https://shop.oriflame.com/NG-salmaibrahimismail/3M3HmQWe

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Mahaukacin gudun da yay a hanya, wanda UBANGIJI ne kawai ya tsaresa kusan ƙarfe biyu na rana ya iso cikin jejin. Tun daga sansanin farko da aka kaima hari a daren shekaran jiya ya fara cin karo da tashin hankali, dan gaba ɗaya sansanin a hargitse yake, an fasa tantunan da harsasai tako ina huji ne, ga karnuka nan kusan huɗu kwance a mace an harbesu. Shiru babu kowa alamar mazaje nakan aiki. Sansaninsu ya ƙarasa da sauri, tuni ƴan tsirarun sojojin da ke a sansanin suka tareshi tare da miƙa gaisuwa. Ajiye mashin ɗinsa yay a wajen da yake ɓoyewa, tare da canja kayansa zuwa uniform ya zubama bindugu biyu bullets sannan ya fice. Kai tsaye inda baradan karnukansa suke yaje ya buɗesu. Ai ko suna ganinsa suka fara wani mahaukacin haushi. Bayan mota dake fake irin ta sojoji dake shiga kowane kwazazzabo saboda ƙarfin tayoyi ya buɗe musu duk suka shiga, shima ya zagaya gaba inda aka buɗe masa kusa da mazaunin driver, cikin sauri wanda zai tuƙa shin ya fice a wajen a guje zuwa ƙauyen Gangare inda su Imran suke. Da tarin gawarwakin mutanen garin fin arba'in ya fara cin karo su Imran sun taresu a waje guda. Sai sojojin da suka samu raunuka ana duba su da wasu a jama'ar gari da suma suka sami raunukan. Garin tsit mutane duk sun ɓuya, sai su sojojin kawai da kallo guda zai tabbatar maka duk a jikace suke, wasu suna gyara bindiga, wasu kuma suna ta duba ƙananun raunikan jikinsu. Motar na tsayawa duk suka miƙe. Tare da ƙamewa suka sara masa. Yayinda Captains ɗinsa suka iso gabansa da sauri, ilahirin fuskokinsu suma na nuna gajiyawa da damuwa. Zak-Shadow da idanunsa sukayi ja, muryarsa cike da ƙarfi da zafi idonsa akan Major Imran Abbas ya furta, "Na bar sansani na kwanaki biyu kawai, amma ku kai sakacin da komai ya rushe haka? What the hell is this?! Are you ladies or soldiers?!". Yanda yay maganar idanunsa na sake rikiɗewa kamar garwashin wuta yay matuƙar hargitsasu. Kowa ya kasa magana, dan babu ma mai wannan zarran bare gigin, garama Major Imran, dan haka a yanzu ma shine yay magana. Cikin matuƙar girmamawa Major Imran dake tsaye a kusa da shi jikinsa da kura, ya ce, "I'm sorry sir. Mun yi iya ƙoƙarinmu. Amma mun ji kamar makiyan suna sanin duk motsinmu ne kafin mu yi. Kamar ana gaya musu abin da muke shiryawa ne kai tsaye. Sannan hari ne na bazata. Mun rasa haɗin sadarwa tun daren shekaran jiya. An kai hari biyu lokaci guda a Arewa da Yamma. Sojojinmu sun watse, mun rasa mutane da yawa. Wannan dalilin ne ya janye hankalinmu da sansanin mu, ashe shiri ne na musamman, hari ne na kauda hankali aka kaima sansanin nan shine ainahin target ɗinsu". Sosai zuciyar Zak-Shadow ke hanƙoro a cikin ƙirjinsa, wani irin raɗaɗi da zafi mai ƙuna yake ji a ransa. Dan ya fahimci bayanin Imran fiye da yanda yayi masa shi, tabbas yaji a ransa dole ne harin ya kasance shiryayye, sannan an tsarasa ne ta hanyar amfani da fitarsa a jejin. Sanin fitarsa kuwa dole tana da nasaba da munafiki a cikinsu. Dan Imran bazai taɓa aikata wannan kuskuren a gareshi ba. Da rinannun idanunsa masu saka tsinkewar zuciya ya juya yana ƙarema sojojin da duk suka nutsu kallo. Nazarinsu yake ɗaya bayan ɗaya. Ya daka tsawa yana zagaya tsakaninsu, yana kallonsu kamar zai cinye su da idanun. Wasu daga cikin sojojin suka sunkuyar da kai, wasu suka tsaya cak saboda tsoro. "Wanda ya ɗauki nauyin ƙasarmu ba zai yi wasa da jinin mutanenmu ba!, dan kuwa duk soja na gaskiya ɗan ƙwarai ne kuma ɗan jalak ne. Yanda ya shiga da ƙarfin zuciya, haka yake karɓa da ƙarfin imani, sannan ya sadaukar da dukkan gaskiya. Ku sani duk wanda na gano yana fitar da wani sirri namu komai ƙanƙantarsa wlhy sai ya ɗanɗana kuɗarsa da mafi girman hukunci. Zan gano shi, ko da kuwa yana tsakanin ku kuma mafi kusa da ni. Dan haka tun kafin guri ya ƙure masa stand up! Fix this mess now!". Shiru kake jin wajen ya ɗauka kowanne yana kallon kasa. Har kana iya jin bugun zuciyoyinsu dake kai kawo a ƙirazansu. Ya ɗan ja numfashi mai zafi shima, yana kallon garin da ya rikice. Sai ya sake daka musu tsawa cikin murya mai zurfi, wacce ke cike da takaici da iko, "You call this a village? Pathetic!" Janye idanunsa yay daga kansu ya fara taku a hankali yana kallon gawarwakin bayin ALLAH da basu taka ma kowa ba balle zubarwa amma aka musu irin wannan kisan zalunci. A wannan lokaci Zak-Shadow ya fahimci cewa ba kawai yaƙi da makiya yake yi ba, akwai wani babban yaƙin da munafukan cikin gida da haɗarinsu yafi na waje. Cike da zafin zuciya ya juyar da kallonsa zuwa sama, inda hayaƙi ke hargitsewa cikin iska. Ya rufe idonsa na ɗan lokaci, a saman lips ya furta, (Wannan ba yaƙi da bindiga bane kaɗai. Babban yaƙi ne duhu). Idanun ya sake buɗewa a kansu ya sake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, yanzu kam cikin ɗan sauƙaƙa zafinsa amma da ɗaga murya da ƙarfin soja ya cigaba da faɗin, "Kun bar harin bazata guda ɗaya ya rikita ku haka? Kuna nunama shashashu masu dattin kai su masu ƙarfi ne akan karfinku why?! Why? My Soldiers! Why?". Suma ji sukai gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi, kalamansa na ratsasu da sake ƙarfafasu da zaburar dasu. A tare suka sara masa tare da faɗin, "I'm sorry Sir!". Iska ya ɗan furzar, cikin tsawa da sake zaburarwa ya ce, "Ku tattara mutane a bama ƴan uwansu su musu wanka ayi jana'iza, zamu mayar da martani kafin gari ya waye!" A tare suka amsa cikin murya mai rawar tsoro da ƙwarin gwiwa: "Yes, sir!" Shima cikin ƙara ƙarfafawar ya ce, "Move! Let's show them what real soldiers look like!" Nan masa suka sake faɗin "Yes sir!" a tare.

★ Zak-Shadow baifi mintuna goma sha biyar ba jiragen sama na soji masu saukar angulu suka fara sauka a kauyen, yayinda sojoji ke shiga gida-gida suna fito da mutane kamar yanda ya bada umarni, a wannan fitowar kuwa sai gashi an zaƙulo yaran Dagger har uku da suka ji rauni suka ɓuya cikin wasu gidaje. "You see! Kuna nan zagaye da gawarwaki maƙiyanku na fake a cikin al'ummar da kuke bawa garkuwa. Abin takaici abin a kamaku da duka. Ƙasa duk sukai da kawunansu musamman Captains da Major Imran. Yayinda shi kuma ke ƙara hasala, ji yake kamar ya dawo da hannun agogo baya ya goge wannan zuwa gida nashi. Duk da ya san zamansa a jejin bazai hana komai ba matsayinsa na mutum kamarsu, amma yana jin kamar shine sanadin komai, kamar anyi amfani da tafiyar tasa ne aka tsara komai. An kwashe sojojin da suka raunata da wasu a mutanen gari da suma suka ji raunuka. Gawarwakin kuwa aka shiga gidaje da su akai musu wanka aka shiryasu cikin likafanin da su Zak-Shadow suka bayar. Haka aka jera su reras abin tashin hankali akai musu salla su arba'in da uku. Harda su Zak-Shadow akai sallar, sannan aka haɗasu a babban rami guda ɗaya da aka haƙa. Tuni rahotanni sun fara fita ga jama'ar gari, dan har sallar da sojojin sukama gawarwakin sai da aka nuna. Hankali ya matuƙar tashi, zantuka suka fara kai-kawo barkatai, dana gaskiya dana ƙirƙira. Yayinda anan cikin jeji su Zak-Shadow suke sabon shiri. Dan sun bar ƙauyen Gangare bayan an zuba sojoji tako ina suka shiga ƙauyen marke da shi ma aka kaima harin duk a daren jiya. Anan ɗin ma akwai sojojin, sannan harin baiyi tsamari kamar na Gangare ba, dan ba'a rasa rai ko ɗaya ba. Wanda suka jikata kuwa an kwashe su zuwa asibiti cikin birni kamar na Gangare. Suna cikin ƙauyen Marke suka sami rahoton gaggawa daga sojojinsu cewar a ƙauyen Bankaura an rasa yara matasa har guda hamsin da wani abu maza da mata. Cikin tashin hankali Major Imran da Zak-Shadow suka ɗauki hanyar ƙauyen Bankaura tare da wasu sojoji. Suna shigowa ana kiran sallar magriba. Sun sami garin a hargitse, iyayen ƴaƴa nata koke-koke cikin matsanancin tashin hankali. Tun ba'aje da nisa ba Zak-Shadow ya fahimci koma yaya ne ba'akai ga fita da yaran a garin ba sai dai wasu a ciki. Sannan dole-dole akwai bakin wasu a garin, dan wannan tarko ne na da ɗan gari akanci gari. Tuni yasa sojoji suka zagaye duka ƙofofin shiga da fita na garin. Tun a daren suka fara bincika wasu gidaje daki-daki. Binciken daya sa aka fara zaƙulo wasu makamai a wani gida an ajiye ƙarƙashin gadon matar gidan. Ta kuma rantse akan bata san wanda ya ajiyesu ba, kuma ko miji bata da shi ALLAH yay masa rasuwa sai yaranta huɗu duk bama masu wani girma ba. Amma babban an haɗa da shi a yaran da aka sace dudu kuma bai wuce shekara sha biyar ba. Kasancewar an sake haɗa musu na'urar sadarwa a yammacin yau cike da bada umarni Zak-Shadow yasa a kawo musu wasu na'urorin, dan tabbas akwai magana a cikin wannan ƙauyen na Bankaura ƙwarai da gaske. Sojoji sun cigaba da shiga gidaje, inda bincike ya ƙara tsauri matuƙa hatta inda bakai zato ba a gidan ka sai an bincika kuwa. Wannan kuma umarni ne daga oga kwata-kwata, wato Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu (Zak-Shadow), ba kuma sojojin ne kaɗai keyi ba harda baradan karnukansa da suka samu training mai wahalar gaske dako su sojojin bazasu nuna musu komai ba....

<<<<★><★>>>>

Duk wanda ya kwana ya tashi a garin bankaura in dai ya kai shekarun banbance rayuwa da mutuwa barci sai dai ɓarawo ya ɗaukesa amma bana zahiri ba. Waɗanda ma aka ɗaukewa yara sun kwana ne suna kukan tashin hankali. Da asubahi sai sojoji ne sukai kiran salla, dan babu wani mai kiran salla daya fita balle liman ko mamu. Kai sallar ma a cikin gidaje wasu basuyita ba sai da rana ta haska. Anan kuwa mituniyarku Nimrah sarkin rikici da ire-irenta dama barcinsu suka sha hankali kwance. Tana farkawa ma ta fito tsakar gida abinta wai zata wanke ido, sai da Umma ta kamata da ƙyar ta maida ɗaki. Kuka ta fara da tirje-tirjen ita yunwa take ji, "Umma ki barni naje gidan Iya mai koko na sayo". Baba ne ya kamata ya zaunar kusa da shi, cikin lallashi ya ce, "Uwa kiyi haƙiri, idan yunwa kike ji a saka miki fura kisha da ƙuli, yau iya mai koko bata koko dan garin namu ba lafiya". Cikin rashin fahimta Nimrah tace, "Baba zazzaɓi akeyi?". Kafin ya bata amsa sojoji suka shigo gidan. Dan sai yanzu ne aka iso ta bangaren gidajen su. Gida ne gidan yawa, dole sojojin suka kasu kowane ɓangare.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_ *_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 43_

__________________

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JuUwr2QU7XMEYXZ7L7 Mmn surayya me kayan kamshi Ina amaran da uwayan gidan tou kumatso kusa Mmn surayya ta gwangwaje ku da kayan kamshi munada Turaran wuta na danal banat Kajiji Turaran kaya watau abbasiyya Kabbasa spray Humra Kwallacca Uwa uba Ina kuyarda yadda xaki hadasu Zaku iya samuna ta wannan number wayar kamar haka👇 08103143517 Ina katsina Ina aika kaya ko ina. __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull