Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 22

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 22

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 22: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 22. ........Kaf gidan sai da kowa ya fito tsakar gida suka fara…

4,368 words

........Kaf gidan sai da kowa ya fito tsakar gida suka fara bincike a kowane sashe. Nimrah uwar magana sai son sakin zance take yi Umma ta toshe mata baki da hannu. Sojan dake bincike a sashensu ne ya fara fitowa hannunsa ɗauke da botiki, gaban shugaban su ya ƙaraso dake tsaye inda kowa na gidan yake... "Mun samu bullets da yawa a nan ɓangaren". Yay maganar dai-dai yana ajiye bitikin gaban ogan ya fiddo jakar dake ciki. Wani irin bugawar zukata Baba da Umma suka samu a tare. Musamman da Captain Musa ya buga tsawa da faɗin, "Suwaye masu wannan sashen?". Rikicewa Umma da Baba suka sake yi, a take suka fara rantsuwar su basu san da jakar bama a sashen nasu. Zaram Nimrah dake kallon jakar ta ce, "Umma kwai ne a ciki fa". Sai kuma ta zabura gaban sojan tana cigaba da faɗin, "Kai Baba ɗan sanda ƙwan Inna ne a ciki ka ɓoye kada ta gani ta dake ni". Yanda tai maganar ƙasa-ƙasa cikin raɗa tana cacumar jakar ta maida a botikin yasa sojojin zuba mata ido, sai kuma Captain Musa ya kai duƙe gabanta ya riƙo hannunta, jikin ƙafarsa dake tsugunne ya jingina ta, fuskarsa da murmurshi ya ce, "Ƴata miye sunanki?". Kai tsaye ta ce, "Zakanyar Kawu Tanimu". Kaɗan ya rage yay dariya, dan yanda tai maganar, amma sai ya danne ya ce, "Bayan Zakanyar Kawu Tanimu sai wane suna kuma?". Ta ce, "Naja'atu. Nimrah. Uwa. Sunana da yawa". Murmushi Captain Musa yayi yana jinjina kansa da shafa kanta. "Sunayen kuwa masu daɗi, kamar yanda kike mai ƙyau kema. Kince ƙwayayen Inna ne a cikin wannan jakar? Ya akai ke kika sani?". Inda mutanen gidansu suke ta kalla, ganin duk ita suke kallo ta kauda kanta da kai ɗan bakinta wajen kunnen Captain Musa cikin raɗa ta ce, "Jiya da Umma ta aikeni kai mata tuwo naga ƙwanta a akurkuki shine na ɗauka nasa a botikin, to sai ban ɗaukama Baba ba shima da Kawu ta dawo, shine na ɗakko duka jakar dan karta kamani, kaga ai zata iya zaneni ni kuma bana son duka". Kanta ya ƙara shafawa yana murmurshi, sai kuma ya miƙama sojan dake kusa da shi hannu. Da sauri ya miƙa masa waya. Danne-danne yay ya kai kunnensa yana miƙewa tsaye, hannunsa ɗaya riƙe da nata. Sai da ya ƙame kamar yana a gaban ogan da ya kira sannan ya ce, "Sir mun sake samun harsasai da adadinsu zai kai dubu biyu a wani gida". Banji mi akace masa daga can ba, yanda dai ya ɗan buga ƙafa da sake ƙamewa ya ce, "Yes Sir!". Zai baka tabbacin umarni aka bashi. Daga haka ya sauke wayar ya miƙama yaran nasa. Idonsa ya maida ga mutanen gidan da sukai tsuru-tsuru cikin matsanancin tashin hankali. "Wacece Inna? Tare da iyayen yarinyar nan?". ALLAH sarki su Umma duk sun ƙara gigicewa, musamman Inna da al'amarin ya haɗa da tsufa, tuni ta jiƙe jikinta da fitsari, jikin sai rawa yake yi sai da Umma ta kamata. Gefe aka maida su, babu jimawa Zak-Shadow ya shigo gidan baradan sojoji kusan huɗu biye da shi. Ƙamewa sojojin sukai a tare, suka sara masa. Hannunsa dake dunƙule kawai ya ɗan miƙar alamar amsa girmamawarsu. Fuskar nan kam ba sauƙi babu sassauci. Dan su kansu mutanen gidan su Nimrah shigowar tasa sake gogitasu tayi, kai da gani kasan BARADAN MAZA ne da kansu ba saƙo ba. Duk rashin tsoron Nimrah tana haɗa ido da shi da sauri ta koma bayan Captain Musa ta ɓuya tana ɗan leƙosa kaɗan da ido ɗaya. Zak-Shadow ya bi duk mutanen gidan da kallo irin na nazari, kafin ya ɗauke kansa ya maida ga sojojinsa, a nan ne ya hangi Nimrah dake ɓoye jikin ƙafafun Captain Musa. Da sauri Captain Musa ya shiga yima Zak-Shadow bayanin tattaunawar sa da Nimrah cikin harshen turanci. Sai da ya gama tsaf yana saurarensa sannan ya maida dubansa ga Nimrah. Abin mamaki a karo na farko yay mata wani ɗan murmushi, sai kuma ya muƙa mata hannu da muryar lallashi ya ce, "Zo Baby girl". Kalmar Zo ɗin kawai ta fahimta, ta kuma san kiranta yake, dan haka ta maƙe kafaɗa alamar a'a, dan bata taɓa cin karo da mutumin daya bata tsoro da cika mata waje irinsa ba, ko babanta mutum ne mai sanyi hali da rashin hayaniya, bai taɓa dukanta ba, idan yaga Umma ma zata daketa shike cetonta. Haka ma Kawu Tanimu da kowa ke ɗaukarsa masifaffe a gidan, ita sangartata yake ko laifi tai baya dukanta. Risinawa Captain Musa yayi ya gwargwaɗa mata magana a kunne kamar yanda tai masa ɗazun. Karo na farko ta ɗago tana kallon Zak-Shadow. Sai kuma cike da ƙuruciya tace ma Captain Musa, "Da gaske baba ɗan sanda?". Kai Captain Musa ya jinjina mata yana murmurshi. Kallon Zak-Shadow Nimrah ta sake yi, ganin har yanzu yana murmurshi sai ta nufesa da sauri. Hannu ya saka ya ɗauketa gaba ɗayanta, ɗaukar da ta saka Umma kallonsa hankali tashe. Wani mugun waro idanu tayi a kansa, jikinta da bakinta na ɗan rawa cikin suɓucewar harshe ta ce, "Bawan ALLAH kai ne?". Ganin wanda take kallo take maganar yaran sojin suka daka mata tsawa, sai lokacin shi Zak-Shadow ma fahimci da shi take, karo na farko ya dubeta, kai tsaye kuwa ya gane ta, dan dama tunda ya kalla Nimrah zuciyarsa ke yi kamar yasan fuskarta, ashe kamanin mahaifiyarta ne. Hannu ya ɗagama sojan da ke mata tsawa, ita kuma duk ta firgice dan gani take harbeta sojan zaiyi. Zak-Shadow baiyi magana ba sai kallonsa daya maida kan Nimrah Ummanta kamar zatayi kuka. Cikin son kawar mata da hankali ƙasa-ƙasa ya ce, "Muje ki nuna min inda ƙwan Inna yake mu kwaso sauran ma, duka zan baku shi ke da mamanki". Hawayen da take riƙewa na zubo mata ta ce, "To kace Kada Baba ɗan sandan can ya bugar min Umma na". "Bazai bugeta ba ai". Captain Musa ya faɗa cike da lallashinta shima. Sun motsa zasu tafi tace ita sai da Ummanta, babu yanda suka iya da wannan mulkin mallaka na Nimrah dole akabi yanda take so. Umma ce ta kaisu har sashen Inna, Zak-Shadow kam na ɗauke da Nimrah har yanzu. Sai da suka isa sashen ne ya sauketa ya riƙe hannunta, babu ko gargada ta kaisu inda akurkukin Inna suke jere da yawa dan tana kiwon kaji, zabbi sosai har ma da agwagi. Cikin bada umarni Captain Musa ya dubi yaransu uku dake biye da su, ai cikin sauri suka shiga bincike akurkayen ɗaya bayan ɗaya. Aiko abin mamaki daban tsoro sai ga abubuwa ana zaƙulowa. Ai tuni an shiga fancake komai dake sashen Inna, itama kuma an taso ƙeyarta. Baiwar ALLAH kuka take tana ƙari da rantsuwar bata san da wannan ajiya ba sam. Hasali ma bata san Nimrah ta ɗauki waccan jakar ba, ta dai ga an ɗiba mata ƙwai biyu, ta kuma san itace ke mata haka, wani lokacin ta kai cikin kajinsu wani lokacin tace zata soya taci. Ba ɓangaren Inna kawai ba gidan gaba ɗaya aka shiga masa filla-filla, yayinda aka tattare mazan kaf waje ɗaya, aiko mata da yara nata kuka. Bincike yay bincike har cikin rijiyar gidan da rumbuna ba'a bari ba, an ko samu abubuwa da yawa da sukafi na sauran gidaje da aka samu, kuma abin mamaki an rarrabasu a ɓangarori da dama ta yanda baka isa cewa tunda a sashen wane aka gani ba shine ya ajiyesu. Dole dai aka tattara su Baba da ƙanensa da yayunsa duka su kusan goma sha shida mazan gidan, idan ka cire Tanimu da yay tafiya a jiya da safe kowa yana nan. An bar wasu sojoji a gidan dan tabbas suna buƙatar tsaro, dan dole ne akwai mai alaƙa da su Dagger a gidan, idan kuma suka ji an samu kayan da ke gidan zasu biyo sahu na ganin sun ɓadda mai alaƙar da su ko ɗaukar wani mataki...

<<•>><<•>>•<<•>>

Kwanaki biyu kenan su Baban Nimrah na hannun su Zak-Shadow. Hatta Kawu Tanimu daya wuce birni anje an taho da shi. An kuma samu wasu tsirarun yara cikin waɗanda aka kwasa a garin a wani gida, sauran kuwa da alama an riga an fita da su. Har yanzu waɗan nan ƙauyukan suna zagaye ne da sojoji, musamman gidan su Nimrah dake cikin haɗari fiye da kowane gida a ƙauyen Bankaura, sai gidaje huɗu da suma aka samu makamai da yara tara cikin wanda aka sata. Tun waccan ranar Zak-Shadow bai sake shigowa ƙauyen ba dan yayi busy sosai, bincike suke babu wasa shi da su Imran da sabbin jami'ai da aka ƙaro musu. Yayinda su Captain Musa da sauran Captains ke aikinsu bisa jajircewarsu da yaran soji tako ina a cikin jejin. Yanzu ma sunzo yin wani sabon bincike ne a nan cikin gidan su Nimrah ɗin ta hanyar zanen hannun kowa, suma mazan gidan dake hannunsu duk an ɗauka acan sansani. Sun sami Nimrah na darzar kuka da birgima ita bazataci garin kwaki da Umma ta jiƙa ba shinkafa zataci. Umma kuwa ta zuba mata ido kawai tana kallo dan tashin hankalinta yafi ƙarfin rigimar Nimrah. Ba ita kawai ba duk macen dake gidan tana cikin tashin hankalin tafiya da mazansu da sojoji sukayi, ga yara babu su babu labarinsu dan har yanzu ba'a samo su ba. Imran sarkin son yara da tausayi ne ya zo har inda Nimrah take bori ya ɗagata cak batare daya damu da yanda tai buɗu-buɗu cikin ƙasa ba. Shi dai Zak-Shadow kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, sai da tai wani furuci ma Umma ya juyo a karo na biyu ya ɗan kalleta. Cikin kuka Nimrah ta sake maimaita, "Kuma sai naje na kira fatalwoyin bayan gida masu jan ido su saka ki a jakarsu su tafi dake tunda bazaki dafa shinkafa ba". Mutane irin su Zak-Shadow nada wata baiwa ta tsarta da saurin tsarguwa. Sannan inda suna a gaɓar aiki basa raina abu komai ƙanƙantarsa koda ga waye yazo. Imran nama Nimrah murmushi da faɗin, "Yi haƙuri Baby kada ki kira ma Mama fatalwa in dai shinkafa ce ina da ita zan baki...." Zak-Shadow daya ƙaraso inda suke idonsa akan Nimrah da tunda ta hango yana tahowa ta ƙanƙame Imran da lafewa a jikinsa dan tsoronsa take ji. Yana isowa ta sake ɓoye fuskarta sosai a jikin Imran ɗin. Kai kawai Zak-Shadow ya ɗan girgiza, kafin ya saka hannu a aljihu ya ciro Dabino da yake yawan ci dan yana matuƙar son shi, zai iya ci miki dabino yasha ruwa matsayin abinci. Ɗan hannunta ya kamo ya saka mata, a karo na farko ta ɗan ɗago cike da shakka ta kallesa tare da hannun nata. Murmushi ya mata kamar ranar, sai ta tashi da ƙyau tana dariya cike da farin ciki.........✍🏼

Tunda aka ba Nimrah dabino aiko za'a sha labarin fatalwoyin bayan gida kenan, yau zamu san mai ɓoye fuska.🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️😂

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 44_

__________________

*🔥 RASH BEAUTY WORLD 🔥 duniyar kayan mata masu kyau da arha ,Ina masu son kaya na kyan gani, amma basu son tsada? To, *ki daina nema!* Rash Beauty World ta zo miki da komai:

*👗 Abaya masu kyau na zamani Egypt/dubai* 👜 *Bags masu kyau* *👠 Takalma masu ɗaukar ido* 💍 *Jewelry masu ƙyalli kamar na sarauta* 🍽️ *Kayan Kitchen masu amfani da kyau*

*Koma da Naira kaɗan za ki yi shopping kamar sarauniya!* 👑💃

✅ Farashi mai sauƙi ✅ Kayamasu quality ✅ Fast delivery

*Shiga group dinmu yanzu kiga sabbin kaya ,Kayanmu masu kyau ne kuma farashi mai sauƙi! Kar ki bari a baki labari don samun kayayyaki masu inganci* 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/GzcU1TcAem21oJedkisrhj?mode=wwt

*RASH BEAUTY WORLD - Inda kyawu da araha suka haɗu!* __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Hannu ya miƙa mata shima yana cigaba da murmushin nasa dai, babu musu ta tafi wajensa. Cikin wayo da dabara ya tambayeta miye fatalwa? Yaushe ta ganta kuma?. Yo har a gayama Nimrah zance, ba'a tambayeta ba ma faɗa take balle wannan harda cin hanci aka bata. Ai tsaf ta shiga bama Zak-Shadow labarin fatalwoyin bayan gida. Koda yace zata kaishi ya gani? Sai ta bashi amsa da, "Ai sun gudu tun ranar, koda na raka su Fatsima ma da sukace zasu gani babu kowa sai dai mun samo jarkoki harda nama". (Anzo wajen) Cewar Zak-Shadow a zuciya. Dabino ya sake cirowa a aljihu ya bama Nimrah, sannan ya fita da ita su Imran biye da shi ransu fal mamakin al'amarin wannan yarinya. Ranar fa da taimakon ALLAH da wayon nan nata suka gano makamai na ban mamaki a gidan, yau kuma ga wata sabuwar magana da tabbas tunda sukaga oga ya maida hankali akai tana da muhimmanci. Tsaf Nimrah ta dinga nuna musu hanya har cikin gonar nan da taga mutanen ranar da take kira fatalwoyi. A kallon farko kuwa sojojin suka fahimci gaskiyar zancenta. Dan har yanzu akwai alamar mutane sun zauna. Sauran takardun nama da yaran basu ɗauka ba saboda an cinye suna wajen duk da iska ta ɗan ɗaukesu sun matsa, sai kashi a gefe dake nuna alamar na gardawane da kufan fitsari da akayi, ɓawon ƙwai da akaci da sauran sigari da akasha. Nimrah na cin dabinonta ta nuna wani waje tana kallon Zak-Shadow. "Baba ɗan sanda, kuma anan naga wani mai irin kayan Babana zaune shima ya rufe fuskarsa saboda tsoron fatalwoyin". "Babanki?". "Eh mana". ta faɗa cikin shiririta tana cin dabinonta. Kallon kallo akai tsakanin Zak-Shadow da Imran. Imran ya maida hankalinsa kan Nimrah, cike da wayo ya ce, "Shine kuma baki masa magana ba?". "Ai tsoro naji na fatalwoyin, kuma ya rufe fuska fa, shima kaga ai tsoron su yake ji ko baba ɗan sanda?". "Miyasa baki faɗama mamanki ba?". "Na faɗa mata ita da Inna sukace na cika surutu, shine na gayawa su Fatsima sukace ƙarya nake, niko na rakosu harnan fatalwoyin kuma har sun gudu". Wani irin cije baki Zak-Shadow yayi, zuciyarsa na hasaso masa tabbas akwai ɓoyayyen al'amari akan mahaifin yarinyar nan. Barin wajen sukai suka koma can gidan su Nimrah. A karo na farko Zak-Shadow ya buƙaci zama da Umma dake cikin tashin hankali tunda suka fita da Nimrah, sai dai ganin sun dawo ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Dan haka ma koda Zak-Shadow ɗin ya nema suyi magana bata musa ba. Tabarma ta ɗakko ta kawo ƙarƙashin inuwar ceɗiya dake a sashen nata. Dan haka kawai take jin girman mutumin nan a ranta tun randa suka fara haɗuwa shekarun baya. Bai musa ba ya zauna shi da Imran. Ita kuma zata zauna ƙasa yace ta ɗakko wata tabarmar. Ɗaki ta koma ta ɗakko tabarma ta shinfiɗa itama ta zauna. Shiru wajen ya ɗauka kafin ta motsa baki cike da ƙarfin hali ta ce, "Kayi haƙuri da abinda nayi ranar, ban san kuskure bane ba. Wlhy farin ciki ne kawai ya kamani na ganinka saboda tun wancan shekarun da muka haɗu nai maka alƙawarin baka abinda na haifa sai nake yawaita mafarkinku a barci na. Kullum kuma cikin addu'ar ganin ba haifi namijin da zan baka ba nake, amma har yanzu ALLAH bai cika min burina na ba". Karo na farko Zak-Shadow ya kalleta, kai tsaye ya furta, "Ina abinda kika haifa wancan karon?". Cikin sauke ajiyar zuciya ta kalla Nimrah dake wasa da ƙasa gefensu kaɗan, "Itace waccan da kuka fita da ita ɗazun". Daga shi har Imran kallon Nimrah sukai suma. Imran dake murmushi ya ce, "Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarta. Minene sunanta?". "Naja'atu, amma muna kiranta Nimrah saboda sunan mahaifiyar maigidana ce." Ɗan huci Zak-Shadow yayi kaɗan, ƙasa-ƙasa ya ce, "ALLAH ya rayata". Sai kuma ya cigaba da faɗin, "Ranar tace miki taga fatalwa a bayan gida, miyasa baki saurareta ba?". "Nimrah nada surutu sosai, shiyasa nakan ƙwaɓeta da irin waɗan nan abubuwan saboda tarbiyyarta matsayinta na mace". "Hakan ba laifi bane, amma yana da ƙyau idan yaranmu sukazo mana da maganar abinda ba kasafai ake zancen sa a cikin al'umma ba mu basu lokacinmu, idan na gyara ne mu gyara musu, ko muyi musu ƙarin bayani ta yanda zasu fahimci abin a yanda yake. Idan ba haka ba zasuje su faɗa a inda bai dace su faɗa ɗin ba, maybe ya cutar da su, ko kuma ya zama na cutarwa ga kowa. Yanzu kamar ita zancen fatalwa data kawo miki mutanen da sukai muku ɓarna da ɗibar yaranku ta gani a wannan ranar, da kin saurareta da kin fahimci abinda take magana akai, koda bazaki iya ɗaukar mataki ba zaki iya faɗawa maigari, kinga kin taimaki garinki da al'ummar garin. Saɓanin haka kuma kinga sakamakon daya kawo." Ba ƙaramin tashi hankalin Umma yay da bayanin Imran ba. Ta zubama Nimrah ido da har yanzu ke wasa hawaye na silalo mata. Imran ya sake katseta da faɗin, "Minene sana'ar mahaifinta?". "Manomi ne kamar sauran mazan garin, sai sana'ar kifi da yake yi kuma". "Ɗanye?". "Eh, harda soyayye, a can yara yake zama, duk zagayen ƙauyukan nan shi kaɗai ne ke wannan sana'ar shiyasa yake samun kuɗi sosai dan wajensa ake zuwa a saya ƙauye-ƙauye dake kusa damu". "Ƙarfe nawa yake fita da kayan sana'ar tasa?". "Sai da yamma bayan la'asar. Dan haka yake jimawa bai shigo gida ba sai irin sha biyu haka, wani lokacin kuma baya kaiwa musamman idan Tanimu ƙaninsa na gari, dan yakan amsheshi shi kuma ya dawo gida". "Shi Tanimun miye sana'arsa?". "Shima yana noman ne, amma yana fita balaguro cikin birni. Yaro ne mai ƙoƙari sosai, dan kusan cigaban dake yankin ƙauyukan nan namu duk da taimakonsa da tsayawarsa aka samesu." "Kamar mi da mi?". "Kamar makarantu, asibiti, wutar lantarki. Shi ne yayta wayar da kammu har muka saka yara a makaranta musamman mata da mukaƙi da farko." "Idan yaje birni yakan daɗe ne?". "Baya wuce wata uku yake zuwa gida yay kamar sati biyu ko uku sai ya koma". "Shida mijinki waye yafi wani kuɗi?". "To bana ce ba, dan shi samun namiji ba kai tsaye mu muke iya ganewa ba anan. Amma su duka kowa na samu gwargwadon iko, sai dai shi Tanimu mutum ne mai hidima ga ƴan uwansa gaskiya. Shi ko mai gidana in banda mu da Innarsa babu nauyin kowa a kansa". "A wannan zuwan da Tanimu yayi gida kwanansa nawa a garin?". "Bai wuce sati ɗaya ba". "Yana taya maigidanki zama wajen kifinsa kamar yanda ya saba?". "Eh yana taya shi". "Kwana huɗu da suka wuce ina maigidanki ya je?". "Yaje Gangare ɗaurin auren ƴar wani abokinsa". "Ƙarfe nawa ya dawo?". "Da daddare ne sosai gaskiya dan har munyi barci ma?". "Tunda kika aureshi, kin taɓa kama shi da wani laifi?". "A'a gaskiya, shi mutum ne mai haƙuri da rashin son magana. Tun a rayuwar samartaka ma ban taɓa jin ance ga abokin faɗansa ba. Koni aka ɓatawa rai na tashi da nufin yin faɗa ko ramawa yakan zauna yayta bani haƙuri da hanani." "Kasancewar sana'ar dare yake yi yana zama a gida tare da ku ya yini?". "A'a gaskiya, yin haka zai iya zama abin magana mu anan balle gidan yawa, yakan fita kamar kowa amma yana shigowa gida musamman lokacin cin ɗumame da kuma in an gama abincin rana". "Zamu iya ganin kayan sakawarsa?". Ɗan shiru tayi a karo na farko ta kasa amsa Imran a wannan karon, sai da Zak-Shadow ya ce, "Karki damu ba wani abu bane". Ajiyar zuciya ta ɗan sauke. Kafin ya miƙe ta shiga ɗaki, babu jimawa ta fito da akwatin ƙarfe babba. A gabansu ta ajiye sa, Imran ya ce ta buɗe da kanta. Buɗewar tayi tana fiddo kayan ɗaya bayan ɗaya, gaba ɗayansu basufi kala bakwai ba, duk yadi ne irin na mai ƙaramin ƙarfi. Bayan ta gama gaba ɗaya yace ta maida, ta kawo masu datti suma. Haka ta miƙe ta ɗebo su, suna ɗaure a cikin zaninta, harda nata dana Nimrah. Nashi suka saka ta ware, nata ma haka, sai na Nimrah da sukafi duk nasun yawa. "Zaki iya lissafa min ranakun da duk kuka saka waɗan nan kayan?". Da yake basu da yawa sai tace zata iya. Da nata ta fara, sai nashi. Ta ɗakko kala na huɗu tai ɗan shiru tana kallon kayan, a karo na farko ta kallesu, sai kuma tai ƙoƙarin ajiye kayan batare da tayi magana ba". "Miyasa zaki ajiye?". "Na manta ranar daya saka waɗan nan gaskiya, shiyyasa zan ajiye gefe kozan tuna kafin na gama". "Ya yi cigaba". Cigaba da lissafa sauran kala ukun da suka rage tayi. Imran zai yi magana Zak-Shadow ya katsesa ta hanyar yi mata nunin ta ɗauki kayan ta koma da su. Ƙoƙarin kwasa tai harda wanda ya ware ɗin nan yace ta barsu. Haka ta barsu ya kwashe sauran. Tana barin wajen Zak-Shadow yay kiran Nimrah. Da gudu kuwa tazo, ya kama hannunta ya zaunar a kusa da shi, sai kuma ya jawo kayan baban nata gabansu ya ajiye. "Kalla wannan kayan na waye?". Cikin wasa tace, "Babana". "Yaushe ya saka su a jikinsa?". "Na manta". "Tuna dai, kamar na ranar da kikaga fatalwoyi ne a bayan gida fa". Kayan ta zubama ido kamar mai son tuno haka. Sai kuma ta kalli Zak-Shadow. "Eh-eh irinsu ne wanda ya rufe fuska ya saka". "Dami ya rufe fuskar?". "Bansan sunan abin ba, amma Babana na saka irin shi shima". "Jeki ɗakko min na gani". Da gudu ta tashi zuwa ɗakinsu. Umma dake tsaye tana kallon su hankalinta ya fara tashi, zata bi bayan Nimrah Imran ya hanata. Kusan mintuna uku kuwa sai ga Nimrah da hiramin Babanta ta dawo. Karɓa Imran yayi, ya ce, "Kin tabbatar shine wannan?". Kai ta jinjina musu kawai. Imran ya kalla Zak-Shadow, kai ya jinjina masa. Shima sai ya jinjina nashi yana ɗaukar kayan ya fara bincikar aljihunnan jikin wando da rigar. Ana farko ya ciro kuɗi ƴan ɗari biyar bandir biyu sabbi, ɗayan ya ciro wata takarda ƙarama a nannaɗe. Gaban Zak-Shadow ya ajiye kuɗin, sannan ya warware takardar.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 45_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Layukan waya ne a ciki har huɗu. Suma ajiyesu Imran yayi, sai kuma ya juya yana kallon Umman Nimrah dake kallon kuɗin da mamaki, dan ita kam bata san da su ba sam, kai kayan ma ta kasa tuna randa mijin nata ya sakasu a jikinsa.... "Ko zamu iya ganin wayarki?". Ajiyar zuciya ta ɗan sauke na katsewar tunaninta, ta girgiza masa kanta. "Banda waya". "Mijinki fa?". "Shima baida ita, sai dai ranar yake cemin yana son ya saya mana ni da shi, zai ba Tanimu ƙaninsa idan zai dawo sai yazo mana da ita. To ban sani ba ko ya ba Tanimu sautin a randa zai tafi". "Kota wani baki taɓa gani a hannunsa ba?". "Eh to sai ta matar Tanimu, itama kuma sai in Tanimun ya kira dan suyi magana take kawo mana, ta kuma kaima Inna. Daga ba wannan ba ban taɓa ganinsa data kowa ba, kai gidan nan ma duka daga Tanimu sai matarsa keda salula". Zaki iya faɗa mana abokan mijinki da kike yawan ganinsu tare, har suke zuwa gidan nan". "Abashe ne kawai abokinsa. Kuma ALLAH yay masa rasuwa watanni goma sha ɗaya kenan. Kowa da shi kawai ya sanshi tun yana saurayi". "Ina ne gidan Abashen?". "Da nan makwaftanmu ne, amma yayi sabon gida sun koma can farkon gari shekara uku kenan?". Kai kawai Imran ya jinjina mata, sai kuma ya juya yana kallon Zak-Shadow da duk ke nazartar tambayoyin da Imran kema Umman Nimrah da amsar da take bashi. Canja harshe Zak-Shadow yayi, cikin harshen turanci yace, "Dole a sake sabon bincike a gidan nan. Kayi kiran Captain Musa yanzun nan". Daga haka ya miƙe ya fita yana latsa wayar hannunsa alamar zai yi magana da wuni...

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull