Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 23
Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 23: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 23. Kandala matar Tanimu dake laɓe tun shigowar su Zak-Shadow a…
3,755 words
Kandala matar Tanimu dake laɓe tun shigowar su Zak-Shadow a bayan katangarta data raba sashensu dana su Umman Nimrah na ganin su Imran sun fita itama tabar wajen saɗaf-saɗaf. Sai faman tafa hannaye take da riƙe haɓa irin na gulma. Magana ce ke tsikarar mata uwawu gashi babu damar fita kai gulma maƙwafta, ta gagara zaune ta gagara tsaiwa. Zuwa can dabara ta faɗo mata, wata ƴar dusa data shanya akan rumfar dabbobinta ta ɗauka ta juye a roba. Sashen ɗayar facalarsu da mijinta da su Tanimu ke uba ɗaya ta nufa. Tun daga farkon shiga ta ce, "Ramma ga dusa, naji kina jaje ɗazun na gagara tashi ne na miƙo muki ita tun ɗazun ina fama da ciwon kai". Ramma da tasan batai jajen dusa ba ita dai ta buɗe baki zatai magana. Da sauri Kande ta ƙyafta mata ido alamar tai shiru. Sai ko ta wayance itama ta ce, "Kai aiko na gode. Tun ɗazun dabbobina ke kuka na rasa tudun dafawa". Ƙasa-ƙasa Kande tace, "Ramma akwai matsalafa a gidan nan". "Matsala ai dama cikinta muke Kande. Yau kwana biyu mazanmu na can a hannun sojoji". "Ai inaga gaskiya ta kusa bayyana, ALLAH ya kusa ƙwato mana su. Tun ɗazun wannan bahagon sojan da kallon fuskarsa kawai tashin hankali ce yazo gidan nan. Naga ya ɗauki waccan yarinyar ƴar gori ya fita da ita, tunda kuma suka dawo suka tsare uwarta da tambayoyi tana basu amsa, har kayan sakawar Yaya mai kifin aka sakata ta ɗakko suka zazzage, naga sun fiddo kuɗi sabbi fil ƴan ɗari biyar, da layin waya. Kin kuma san bashi da waya ai. Gashi can sun sake fita dai...." Ramma dake zazzare ido ta ce, "Mun shiga uku Kande, kar dai ana zaton wuta a maƙera a ganta a masaƙa". "To aiko da alama can ɗin take. Yo ai biri yayi kama da mutum, ki kula a kwanakin nan basa shan koko kullum sai shayi da burodi, ranar ƴar naba su Laminu labari wai sunci tsire da daddare babanta ya sayo. Ke dama ki kiyayi mutum sumu-sumu wlhy abin tsoro ne. Randa Tanimu zaiyi tafiyar nan da daddare yake gaya min ya ranci kuɗi a wajensa har dubu arba'in, naita mamaki har ina jin haushi, ashe-ashe kuɗin bana ALLAH bane". "Kande ni abinda ban gane ba anan. Kenan dai shine ya kawo mana wannan masifar da aka samu shekaran jiya cikin gidan nan?". "A to ke da mi kike tunani, shine mana. Dan bala'i ya rasa inda zaije ya ajiye sai ɗakin tsohuwarsa, yanzu da wannan abun daya kashe mutane a Gangare ne a ciki tunda ance fashewa yake shi ai kinga shike nan ya kasheta ko yama ɗiyanta asara. Maganinta itama, badai tafi sonshi da ƴarsa ba kamar shi kaɗai ta haifa, mai mata wahala daban wanda take riritawa daban". Salati kawai Ramma take tana ƙarawa, dan maganar ta girgizata matuƙa. Kasancewar ita babu wani jin haushin su Umman Nimrah a ranta ita tausayinta ne ma ya kamata wlhy. Ka daɗe baka haihu da mutum ba sanda kuma ALLAH ya fara baku ace ga wannan masifa mutum nayi, ga yarinya mace, idan wannan magana ta fita wazai aureta a wannan garin basu da ba'a manta abin gori....
<<<<<•>>>>>
A ɓangaren su Imran mintuna talatin ba'ai ba Captain Musa ya iso da wata tawagar soji, da karnuka. Sai da suka miƙa gaisuwa ga Zak-Shadow dake a ƙofar gida har yanzu yana waya sannan suka shiga cikin gidan. Kamar yanda ya bada umarni haka sojojin nan keyi, bincike ake mai zafi da yafi na farko har a jikin bango da ramin ɓeraye ba'a bari ba. Kai saida takai hatta ledar ƙasan ɗakin Umman Nimrah sai da aka kwaye gaba ɗaya, da ledar sama da akai kamar silin. Cikin filos ba'a bari ba. A ɗayan ɗakinsu da take ajiye-ajiyen kayan aiki da icce sai randunan ruwa sai da aka fidda komai. Wani guri ne ya nuna kamar an tona aka maida ƙasa aka rufe Zak-Shadow yace a tone shi shima. Haka suka shiga tonawa kuwa, abin mamaki sai ga tunkunyar ƙasa, ana buɗe murfinta sai ga kuɗi masu yawa a ciki kusan cike. Nan fa aka shiga fiddosu bandir-bandir sabbi ƙal. Hakama a cikin ɗakin Umma an ƙara samo kuɗi cikin katifar rimi ta gadon da yake kwana, harda wayoyi har biyu. ALLAH sarki Umma zuwa yanzu kuka take sosai, hakama Inna sai surutai take kamar wadda ta zautu. Tana son baban Nimrah sosai fiye da sauran yaranta musamman yanda bashi da yara sosai ɗin nan. Duk da kuwa Tanimu yafi ƙyautata mata da yi mata hidima a rayuwa, shi baƙin halin matarsa ne yasa bata sakewa da shi, itako Umman Nimrah tana mata abu kamar ƴarta. Idan ma ta nema abu Baban Nimrah ɗin bai mata ba ita takanyi a madadinsa batare da Innar tasan ba shine yayi ɗin ba. Bincike na biyu shine gidan abokinsa mai rasuwa Abashe, inda su Zak-Shadow suka gane shine gidan matar nan mai yara marayu da suka fara samun abubuwa tace ita kuma bata san da su ba. Ashe kuwa da gaske bata sani ɗin ba. Dan sai yanzu ne da zance ya kai ya kawo akan lamarin Baban Nimrah ɗin ta tuna ya kawo musu hatsi kusan sati ɗaya kenan, da yake tunda mijinta ya rasu haka yaketa ɗawainiya da ita da yaran babu gajiyawa, randa ya kawo hatsin yace babban yaronta da yaci sunansa suke kira da Aboki yaje ya amso musu kifi. Tabbas taga yaron nata da bako bayan ledar kifi, koda ta tambayesa sai yace mata Baba ne ya bashi ajiya yace zai amsa ranar kasuwar Gamau. Itako bata maida hankalin sanin minene a ciki ba yaron ya shiga da bakko ɗin ɗakinta ya ajiye. Bako ta sake tunawa ba sai yanzu ma. Gari fa ya ɗauki sabon tashin hankali. Dan duk wanda keda alaƙa da Baban Nimrah sai da aka kamashi a wannan yinin, hatta wajen kifinsa da inda yake zuwa sari a can cikin local government ɗinsu sai da aka bibiya. Zuwa dare sai ga ƴan uwansa na nan gidansu duk an sakko, sai dai banda Tanimu dan basu gama bincike a kansa ba. ALLAH sarki Umman Nimrah idan ka ganta abin tausayi, wuni ɗaya duk ta susuce ta fita a hayyacinta. Dan zuwa dare ma zance ya gama baje gari dan ma akwai sojoji da sukai musu takunkumin hana yawo barkatai ƴan uwanta sukazo suka tafi da ita harda Nimrah bisa umarnin mahaifinta dattijon arziƙi, babban malami ne a yankin ma ba garin kawai ba, dan bazasu so abin kunyar da mijinta ya aikata ya shafeta ba, musamman da matan gidan suka fara mata habaice-habaice da yada magana a kai-kai ce bisa jagorancin Kande matar Tanimu data fara yaɗa maganar, dan ma dawowar mazan gidan ya sata komawa tai laƙwas ganin babu nata mijin itama....
>>>>>><<<<<<<
A sansanin su Zak-Shadow cikin tantin Imran da bai cika zama ba ake tsare da su Baban Nimrah, zuwa safiya ake son fita da su daga jejin zuwa birni, ana ƙara tantance wanda basu da alaƙa da al'amarin ne musamman waɗanda aka tattaro yau da rana. Kwanaki na uku kenan bayin ALLAHn nan su Zak-Shadow basuyi barcin rabin awa ba. Yaransu da manyansu tsaye suke akan ƙafafunsu. Kai ko abincin kirki basa ci sai ƴaƴan itatuwa. Duk mai imani ya gansu sai ya tausaya musu. Amma a haka muda muke kwance a gidajenmu muci mu ƙoshi mu kunna tv muyi kallo, mu hau gado muyi barci har muke iya zagin jami'anmu da kallonsu muce basa aiki. Musani ganin jami'an dake ofisoshi zaune, da wanda ke yawo akan hanya suna nuna wasu halayya mara ƙyau bashike nufin mun rasa zakaƙuran jarumanmu dake cijin jeji daban-daban suna gumiruzu akanmu ba. Akwai irinsu Zak-Shadow da su Imran da yawa da bamu san da su ba, sai dai ALLAH ya saka musu da alkairi kawai zamuce.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 46_
__________________
https://wa.me/+23408067422528 Kina son rage kiba ba tare da kin daina cin abunda kike so sannan ba tare da kinyi gudawa ba? To kimin magana domin samun hanyoyi da zaki rage kiba ba tare da kinsa wahala ba. Ko kuma matsalar gashi ce ke damunki, ko rashin tsahon gashi ne, shima muna da solution dinsa. Ko kuma fatar ki tana lalacewa ne a sanyin? Muna da ingantaccen man da zai gyara miki kafafunki ko kuma kamar ta jarirai. Ko kuma kafarki ce take kaushi a sanyin nan muna da ingantaccen mayuka Ko kuma man gyaran fata kike so da zai gyara miki jikinki a sanyin Nan ?duk muna dasu ba tare da kinsa wahala ba sannan 100% natural ne. Yar uwa idan ma bangaren samun kudi shima kike nema shima duk zamu koya miki. Kedai kawai ki mana magana domin karin bayani.
https://wa.me/+23408067422528 "Shin Ke uwa ce, kina son samun kuɗi ba tare da kin fita kin bar 'ya'yanki a gida ba?" ko kuwa ke student ce kina son samun karin kudin shiga ko kuma ma dai kawai kison karin side hustle ne Tare da Oriflame, za ki iya yin kasuwanci daga wayarki a gida. Ba tare da kin fita ba. Mata da yawa sun riga sun farga da wannan Kasuwanci kuma suna moriya dashi sosai, suna making kudi daga gida, kuma ke ma za ki iya sannan bayan ribar ki zaa biyaki salary a karshen wata. ko kuma kina son yin siyayya for personal use ne ba tare da anci riba dake ba ga link nan a kasa zaki iya register da kanki it's free👇
https://shop.oriflame.com/NG-salmaibrahimismail/3M3HmQWe __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........*_01:am_*
Zama a duhu tamkar ɗabi'a ce ta wannan ƙungiya, musamman a lokacin yin meeting. A yau ɗin ma da zaman nasu ya kasance na gaggawa ba kowa da kowa bane a falon. Ogansu ne kawai sai Black Spider da yaronsu Dagger. Dagger bawani muhimmanci ne da shi a wajensu ba face KAREN FARAUTA. Dan kuwa suna kwance ne yana musu yaƙi da horar da yaran mutane a tafarkin hatsabibanci. Shike da yaran dake musu haƙar ma'adanan yankin Bankaura da sauran ƙauyukan wajen da adalinsu suka samar da ƙungiyar ga'addaci da zata janye hankalin mutane daga ma'adanan saboda kafawa da tsarewar jaruman jami'an ƙasar sukayi irin Zak-Shadow. Kuɗi kam suna sakarma Dagger ta yanda yake sake ruɗuwa da zama a rufewar idon sai da ƙasarsa da yankinsa hankali kwance batare da jin yana aikata kuskure ba ma. Shima kuma yana amfani da kuɗin wajen ɗibar ƴaƴa a cikin tafiyar cikin sauƙi saboda ƙarancin tallafi daga matasan ta hanyar ayyukan yi akoda yaushe. Ogan nasu daya kasance bamai yawan magana ba sai baƙar mugunta taf cikinsa ya wani zuƙi ƙaton sigarinsa yana ma Dagger wani kallo mai kama da raini ƙo ƙasƙanci ne ma oho masa. Amma kasancewar eyeglass ne a idonsa shi Dagger ba gani yake ba. Cikin harshen da suke magana da shi cike da isa da ƙasaita ya ce, "Kana nufin kazo gaya mana bazaka iya ba saboda banzan can ya kama maka yara?". "Ko ɗaya sir! Ai ko kura ta rame tafi ƙarfin wawason namun jeji. Waye wani Zak-Shadow ballantana yaransa. Ina son naji ne ko akwai hanyar fitar da su a hannunsa? Ko kuma mu kashe su kawai kafin ya kaisu cikin birni kamar yanda yake shiri, amma ku sani dukansu da aka kama sunada matuƙar amfani a tafiyar mu, musamman ma mutumin nan na Bankaura, dan mutumin nan yanada manyan sirrikanmu da bani da tabbacin idan yaji wuya bazai tona ba kamar yanda yay sakacin da ƴar iskar matarsa ta buɗe mana aiki. Na matar tasa ma bai ɓata min rai ba, wannan shegiyar yarinyar mai kama da ƴar aljanu, tun randa ya haɗu da su Ganuwa ashe ƴarsa ce ya ɓoye musu......" "Kaga hakan na nufin da saninsa tazo wajen...." Black Spider ya faɗa cikin fushi da ɓacin rai. "Bana jin haka oga, domin kuwa Ganuwa ya tabbatar a bazata yarinyar tazo musu. Kuma yana ganinta ya rufe fuska. Sai dai ina yin zargi ɗaya, uwarta ce ta turota danta tabbatar mata shine, dan bana raba ɗayan biyu tare yarinyar take da uwarta ita ta laɓe." "Idan ko haka ne baka buƙatar wani umarni anan. A kashe matar tasa da ƴar gaba ɗaya. Shima bama buƙatarsa ya gama aikinsa". "An gama Sir! Dama wannan umarnin kawai nake jira. Sai dai a majiya mai ƙarfi na samu labarin ɗazun iyayenta sunzo sun ɗauketa a gidan. Tana gidansu. Babanta kuma shine hatsabibin malamin nan daya hana mu rawar gaban hantsi a farko." "Duka ahalin nata a kashe su. Dan bamu zo ƙasarku dan wasa ba, buƙatarmu ta lokaci ce muna kammala ɗiba zamuyi gaba. Duk wanda yace kuma zai tari gabanmu koda uban waye sai mun kawar da shi ya koma ƙasar takawarmu a hanyar samun cikar wannan burin. Kar su wuce gobe..." Yay maganar ƙarshe da umarni yana barin falon gaba ɗaya, ba kowa bane face oga kwata-kwata. Shima miƙewa Black Spider yayi yabi bayan oga, hakan ya tabbatar ma da Dagger sun gama da shi. Ji yay kamar ya harari bayansu, amma ya kanne. Sai dai ƙasan zuciyarsa yana jin wani nauyi da shi kansa yakan kasa tantancewa. Shin ɗan sauran ɓurɓushin kishin ƙasar ne a wajen kokuwa takaicin dukiyar da mutanen ke samu ne su ana ɗan tsakura musu ke son saka masa jin hassadarsu...
<<•>>•<<>>•<<•>>
Asubar fari wani irin hayaƙine ya turniƙe illahirin garin Bankaura da in kai wasa ganin gabanka ma zai iya maka wahala. Ga wani irin rigugi da ke tashi mai matuƙar saka razani a zukata duk wani mai rai. Kai da kaji amon kasan sautine dake fita daga bindigogi ko wasu nau'in makamai masu fashewa. Kasancewar asubahi ce barcin da mafi yawan mutane basa samu saboda tsoro a farkon dare yanzu gabanin asuba duk ya kadasu sun ɓingire. Hakan yasa shiru yayi yawa tako ina gaba ɗaya jejin ya ɗauki sautin da har saƙon ya isa cikin kunnuwan su Zak-Shadow. Ai ko shine ya fara fitowa a tantin da ake tsare da su Baban Nimrah sakamakon tuhumar da ya saka ake musu tun daren jiya, dan yafi son samun dukkan bayanan da yake buƙata kafin ya miƙasu hannun hukumar bincike gudun samun matsala. Jin fa al'amarin na gasken-gaske ne dan har wani jijjiga jejin keyi saboda azabar fashewar gurneti ya zabura cikin wani irin rawar jikin jarumta. Kafin cikin gigitacciyar muryarsa ya furta, "Are you soldiers or a bunch of jokers?!!?". Gaba ɗaya sansanin ya amsa da faɗin, "No, Sir! We are Soldiers, Sir!!". Cikin ƙanƙanin lokaci wajen ya rikice da ƙarar gudunsu ta yanda suke rige-rigen shigewa motocin yaƙi, wasu dokuna, wasu mashina. Wasu kuma suka ƙara zagaye tantin da su Baban Nimrah suke dan kar ya zaman irin takun ranar ake son maimaita musu. A janye hankalinsu can gaba ɗaya nan kuma aka musu kwaf ɗaya. Saboda sun kula koma wace ƙungiyace wannan da ƙarfinta take. Sojojin na isa garin ya ƙara hargitsewa da musayar wuta, tsawon awa ɗaya a wannan yanayin kafin sautin ya fara lafawa sai kukan yara da mata ya fara fitowa.. A dai-dai lokacin jirage masu saukar angulu na soji suka fara isowa suma. Cikin ƙanƙanin lokaci suka zagaye ƙauyen musamman ta yankin da abin yafi ƙarfi. Sosai tsakkiyar gidan Malam Hamisu mahaifin Umman Nimrah yayi kaca-kaca da jini, yayinda gawarwaki kusan biyar na maza ke kwance. Ta gefe kaɗan ƙyaƙyƙyawan dattijo ne mai cikar kamala ma'abocin furfura da dogon gemu durƙushe a ƙasa da Handcuffs a hannunsa da aka maida ta baya wani soja na ƙoƙarin kunce masa amma da alama al'amarin yaci tura dan kamar an kulle handcuffs ɗin da wani kwaɗon sirri. Idanu kawai kyakkyawan tsohon ya zubama gawarwakin ƴaƴansa da su Dagger suka kashe yana kallo hawaye na bin kamilalliyar fuskarsa ta girma da kwarjini. Ta gefe kaɗan matane da yara da zasu iya kaiwa adadin talatin da ɗoriya. Suma dai kukan suke sosai wasu har sunayi tamkar zasu shiɗe. Fitowar Zak-Shadow daga cikin ƙaton gidan na ƙasa mai sassan da yawan gaske da zai tabbatar maka family house ne na waɗan nan mutane ya saka sojin dake zagaye da mutanen shiga sara masa cikin nuna girmamawa a garesa. Kansa kawai ya jinjina musu yana yamutse fuskarsa da tai kaca-kaca da jini ta yanda ko iya gane ainahinsa ba'ayi sosai. Hakama farar rigarsa da wandonsa na sojoji duk sun ɓaci. Cikin bada umarni yay nuni da gawarwakin dake a yashe a ƙasa tare da tsohon nan. Da sauri ɗaya daga cikin yaran nasa ya furta, "Sir za'a fara gaba da su ne?". Maimakon yin magana yanzun ma kansa kawai ya jinjina. Basu damu ba, domin sun san shi mutum ne mara son yawan magana. Sai da suka gama kwashe gawarwakin da aka saka a cikin wasu ledoji sannan aka samu nasarar kunce handcuffs ɗin hannun dattijon nan. An kama shi da nufin miƙarwa dan jikinsa rawa yake a bazata kawai ruwan harsasai suka fara sauka a jikinsa. Gaba ɗaya wajen ya rikice, Zak-Shadow da yaransa suka fara dube-duben ta ina harsasan ke fitowa, yayinda wasu sukai kansa akai ƙoƙarin riƙoshi da hanashi kaiwa ƙasa daya tafi zai zube. Kukan yaran nan da mata ne ya ƙara ƙarfi. Yayinda wasu a cikinsu suka miƙe da gudu zasu nufesa, amma sai sojojin suka hana hakan ta hanyar shan gabansu. Dai-dai nan wani taƙadari cikin yaran Dagger ya buɗe ƙaton dirom ɗin dake tsakar gidan ya fito yana dariya. A take sojoji suka ɗana bindugu, masu tunanin yin fata-fata da namasa har sun ɗana kunamin bindugun nasu ya turo Umman Nimrah gabansa bindiga a kanta daya ɗora mata. Sai lokacin su Zak-Shadow suka fahimci shine yayi harbin ta cikin drom ɗin kenan. Cikin bada umarni da kaushin harshe Major Imran ya furta, "Idan kana son tsira da sauran abinda ya rage maka na numfashi ka ajiye bindigarka". Dariyar shaƙiyanci yayi, ga fuska ya shafe da baƙin abu ko gane kalar fatarsa balle kamaninsa ba'a iya yi. Da yanayin shaƙiyanci ya amsa ma Imran da, "An gaya maka goro na kasa a duniyar da har nake son ya ƙare na ƙirga riba da jari balle na damu da rayuwata. Kama bar wahalar da kanka, jinin wannan matar halattacene a wajena dan koba komai zanyi jihadi kashe mata mai tona asirin mijinta." Ya faɗa yana ƙara danna kan bindigar a kan Umma dake hawaye tana kallon Zak-Shadow da zuciya ta kume ƙirjinsa, yanda kawai zai fasa kan tsinanne yake yi. Aiko tamkar wani abin siddabaru babu ma wanda ya kula da sanda ya ja kumar bindigar hannunsa ƴar mitsitsiya balle ɗagawar hannunsa sai saukar Bullet akan shegen, dan shi ɗin ƙwarraren maharbi ne kowa ya sani kuma. Kasancewar shi kuma ɗan iskan ya riga ya ɗana kunamar bindigar hannunsa a wuyan Umman Nimrah tun ɗazun harbin da akai masa ya tafi baya sai kawai yatsarsa ya motsa harsashin ya fita ya shige jikinta. Kusan tare Zak-Shadow da Imran suka zabura kanta. Sai dai kafin su dire ma ita ta dire a ƙasa rikica. Cikin matsanancin gigita Imran ya riƙota yana jijjigata da gwala kiran sunan Captain Musa. Murmurshi tayi mai ɗaci da ciwo hawaye na zubowa ta gefen idanunta dai-dai da malalowar jini a hannun Zak-Shadow da ya kai hannu shima zai riƙota Imran ya rigashi, sai ya kasa ƙarasawa da hannun kuma ya kasa janyewa. Da ƙyar ta iya sake yin wani murmushin tana juya idannunta da ƙyar akan Zak-Shadow... A dai-dai nan shima munafukin nan mafi kusanci da Zak-Shadow ya katse videon daya ɗauka a wayarsa yana ɗan sakin munafukin murmurshi nasara guda biyu..........✍🏼
_Wato a duniyar nan ALLAH ka rabamu da maƙiyi mai fuska biyu. Kunga wanda zai nuna maka soyayya a gaban idonka a bayan idonka yafi kowa ɓataka da aibantaka ba ƙaramin azzaluminka bane. Wannan shegen na tsaneshi tun kan aje ko ina. Duk wanda yake tare damu a zahirin rayuwa da baɗini da wata manufa ya rabbi ka rusashi kafin shi ya ruguza mu😭😭🙏._
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 47_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________