Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 24
Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 24: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 24. .........Kai Zak-Shadow ya shiga girgizama Umman Nimrah…
4,138 words
.........Kai Zak-Shadow ya shiga girgizama Umman Nimrah idanunsa na wani irin jirkicewa. Ya motsa lips zaiyi magana ta girgiza masa kai itama.. "Karka damu, a yanzu nafi buƙatar mutuwa akan rayuwar da zata cigaba da tunamin wanene mijin aurena. Rayuwar da zata cigaba da tunamin rasa ƴan uwa biyar da mahaifana a dalilin mijin aurena. Na godema ALLAH da ban koma gareshi ba sai da nasan wanene mijin aurena. Ba zan aibanta shi ba, amma ni da shi da ƴarmu tilo zamu haɗu gaban mai rarrabe ayyuka da gaskiya. Ban samu cikar burin haihuwar ɗa namiji da nai alƙawarin baka ba, amma zan damƙa maka AMANAR ƴata ɗaya tilo da kaf duniya dakai kaɗai na yarda. Dan ALLAH ka raineta tamkar yanda nake fata rainonta, ka bata ilimin addini dana zamani. Ka raini zuciyarta da jarumta irin taka da tausayi da hidima ga al'umma. Ko da wasa kada ka sanar mata ainahin halayyar mahaifinta, dan Alhamdullah Babana ya bata rubutun mantawa da shi a zuciyarta na har abada, ina kuma roƙon yay mata tasirin da bazata taɓa tunashi ɗin ba, amma ko ya cigaba da rayuwa har lokacin girmanta, ina son ta tashi da sanin shi mataccene tun tana da ƙuruciya, ma'ana ka sanar da ita ita ɗin marainiya ce gaba ɗaya ta rasa uwa da uba tun tana ƙarama. Sannan bana son tai amfani da sunansa a matsayin uba. Dan ALLAH ka riƙe min AMANAR NAJA'ATU NIMRAH, na yarda da kai bazakaci amanar dukkan alfarmata ba. Roƙo na ƙarshe har abada kada ka bar waɗanan mutanen suyi sukuni da walwala a wannan duniyar. Ka addabesu, ka zame musu KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DO...... D......" Ta kasa ƙarasawa saboda yanda numfashinta ke fisga. Da ƙyar ta sake jawo shi da furta, "N...Nimr... Na ɗakin Inn...nta a cikin kwalla Inn...a ta ɓoyeta. Dan ita suka fara ne... Nema su ka..she. ƙin... Nu nata da mukai yasa suka kashe Innata da ƴan uwan....a. Sunyi alƙawarin kuma sai sun kashe ta, ina tsoron kada su cigaba da bibiyar rayuwarta dan ALLAH ka kula da it.....a AMANA". Harshenta ya riƙe ta kasa cigaba da maganar. Ga Captain Musa ya ƙaraso da yaran soji zasu ɗauketa a saka cikin jirgi likita ya bata taimakon gaggawa. Amma ina wannan tafiyar mai girma ce, kuma ta har abada ce ga Umman Nimrah. Hannu Imran ya ɗaga musu da ƙyar, yayinda Zak-Shadow ya motsa lips ɗinsa da ƙyar ya shiga ambato mata kalmar shahada. Idanun kan sunyi wani irin masifar juyewa jajur. Cikin aminci UBANGIJI akan lips itama ta dinga maimaita duk abinda ya ambata ganinta na juyewa zuwa ga UBANGIJI, amma kuma har lokacin Zak-Shadow ɗin kawai take kallo. A haka idanun suka kafe alamar rai dai yayi halinsa. A mamakin kowa gefe Zak-Shadow ya maida kansa kawai. Kaudawar da kowa yafi zargin hawaye ne suka cika masa ido. Duk da kuwa kowa yasan kuka ba ɗabi'arsa bace. Musamman idan sukai dubi da kalolin tashin hankalin da suka gani a rayuwar aikin soja da tafi wannan har a ƙasashen ƙetare. Komai baice ba ya miƙe kawai, yayinda Imran yaja ɗankwalin kanta ta rufe mata fuska tare da shimfiɗeta a wajen. Koke-koken mata da yaran ya ƙaru sosai, matan sun kai su goma sha bakwai, dukansu kuma matan yayyen Umma ne da ƙanne, sai yaransu. Inda Zak-Shadow ya nufa Imran yabi da kallo, a ɗakin da suka sami nasarar fiddo tsohon nan ne, nan ne kuma Umma tai nuni da Nimrah na'a ciki. Captain Musa ne biye da shi. Basu fi mintuna uku da shiga ba kuwa suka fito Captain Musa ɗauke da ƙatuwar ƙwalla irin ta mutanen da mai hoton murtala. Da alama ɗakin da suka shigan da duhu dan harda fitila a hannunsa da suka haska. Murfin kwallar ya buɗe, sai ga Nimrah a ciki da alama ma a sune take. Riga ce doguwa a jikinta ƴar kanti, tayi face-face da jinin Inna dan sanda suka harbi Inna ɗin jinin ya fallatsawa Nimrah. Karon farko Zak-Shadow daya zubama cikin kwallar juyayyun idanunsa ya kauda kansa saboda isowar Imran wajen. Cikin girmamawa ya nuna matan da yaran dake wani irin kuka mai ban tausayi. "Sir! Suma za'a wuce da su ne?". Kansa ya jinjina masa da bin jejin da kallo. Sai kuma ya duƙa tare da saka hannu cikin kwallar ya ɗakko Nimrah gaba ɗayanta, kafin ya furta, "Alamu sun nuna basu kaɗai bane. Dan yara mata ne sukafi yawa anan, mazan basu wuce shekaru uku-uku ba. Dole ne akwai wata tawagar yara mazan gidan ɓoye a cikin jejin nan mutanen nan sun ɗiba". "Tabbas nima ina hasashen hakan Sir. Musamman idan mukai la'akari da furucin tsohon da yace adadin jikokinsa maza sunfi matan yawa". Shiru yay yana nazarin maganar Imran ɗin. Yayinda idanunsa ke bin mata da yaran da kallo a tsanake. Sosai kukan da suke ke taɓa masa ƙasan zuciya. Amma da yake ƴan mazan mazane na gaske babu alamar hakan a saman fuskarsa. Sai ma ɗauke idanunsa yay cikin bada umarni yace a sakasu a mota. Sosai ihunsu da karuruwa ta ƙara ƙarfi. Ɗauke kansa yay tare da yima Imran magana ƙasa-ƙasa. Kai Imran ya jinjina masa, shi kuma ya wuce jikin motar da yazo a kai ya saka Nimrah a baya ya kwantar. Imran dake bin matan da kallo nuni yay da yara kusan goma ya ce a fito da su. Bayan ya raɗama Captain Musa magana a kunne shima. Cikin gamsuwa Captain Musa ya matsa yayma sauran nasu magana shima. Aifa take suka ɗaura bindigu akan yaran. Ihun iyayen ne ya sake ƙarfi, yayinda suke roƙon kar a kashe musu yara dan ALLAH. A kausashe Imran ya furta "Idan har bakwa buƙatar rasasu suma ku sanar mana ina sauran ƴaƴanku suke? Barazanar mi sukai muku suka kwashe su?!!". Shiru sukai alamar matuƙar jin tsoron yin magana. Dan kuwa takunkumi akai musu ta ƙarƙashin ƙasa akan idan suka faɗa a bakin ransu su duka. Takaici da ɗacin daya mamaye maƙoshin Zak-Shadow ya daka musu tsawa. Yanda amon muryarsa mai matuƙar saka razani ta ratsa jejin ya saka su sake shiga razani. Tuni wata tsohuwa ta fara bayani jikinta na rawa. "Iya muke nan muka rage a gidan. Dan da yawan yaranmu maza suna birni neman kuɗi. Wasu kuma sun gudu bamu san inda suke ba". Shi ɗin jami'in tsaro ne na soji mai matuƙar fiƙrah da kaifin basira. Yayi matuƙar sanin aikinsa ta yanda ko'a furucin baki yakan iya tantance na gaskiya da akasinsa. Dan haka kai tsaye ga gane ya kuma fahimci tsohuwar a tsorace take. Batare da ta sake cewa komai ba yay nuni da a saki yaran. Ai a guje suka shiga komawa wajen iyayensu wasu har suna tintsirawa a ƙasa suna tashi. Fitowa su Zak-Shadow sukai ƙofar gida, aka bar yaran sojoji kusan goma sha a ciki tare da su. Mizai faru, mintuna goma su Imran basu ƙulla da fitowa a gidan ba dan suna tattaunawa ne kawai sukaji tarwatsawar abu mai ƙarfi ta yanda su kansu sai da suka zabura gefe dukansu. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ashe duk wannan abun dake faruwa bomb ne ɗaure a jikin ɗaya daga matan gidan, shiyyasa suka kasa faɗar inda sauran yaransu dasu Dagger suka ɗiba a jiyan suke. Gaba ɗaya kuma ya tarwatsa gidan da matan, da yaran, da sojojin da aka barsu da su su wajen ashirin. Wannan da shine tashin hankali ba'a sanya maka rana. Dan ba gidan ba hatta gidajen makwaftansu dake lafe a gida hankula a tashe tako wace kusurwa sun tarwatse. Sai dai kaga mutum yay sama an dawo da shi ƙasa a tarwatse, wasu ma sasan jikin duk a rarrabe. Wannan abu ya zafafi Zak-Shadow da fusatashi, dan kuwa tunda ya damƙa Nimrah a hannun Imran sai kawai yay sabuwar ɗammarar aiki da kansa ba umarni ba. Yaƙi da karan kansa ba jiran yara ba. Hankalin su Captain Musa ya tashi ganin yay wani hatsabibin tsalle ya shige motar yaƙi mai zazzage maƙiya da gurneti suka san ran ƴan maza ya ɓaci. Aiko da gasken ya ɓacin, kuma ranar yaran Dagger sun tabbatar ya ɓacin. Dan da karfin ikon ALLAH a maimakon Captains shi da kansa ya jagoranci runduna guda a cikin jejin suka dinga zaƙulo yaran daga. Wani mahaukacin kisa yake musu mai cike da fushi da baƙin ciki. Gaba ɗaya wannan yinin Zak-Shadow baiyi tsayuwar awa ɗaya ba da sunan hutu. Ga sojoji an sake ƙaro masa. Lungu da saƙo ya dinga zaƙulosu, dan kuwa bai gushe ba zai da ya gano sabon wajen haƙar ma'adanan daya sashi fahimtar dan su aka haddasa wannan sabon tashin hankalin na kwanakin nan. A take ya saka sojojinsa suka rufe wajen haba ɗaya... Zakusha mamaki idan nace muku duk wannan abun da ake munafukin nan bai gaji da ɗaukar video a wayarsa ba, dan cikin aljihun riga ta gaba ta sakata cike da dabara, duk kuma inda Zak-Shadow ya sanya ƙafa yana biye, hasalima shine ɗauke da wayar sadarwa a baya da jakar harsasai yana ɗurama Zak-Shadow a bindiga...
<<<<<>>>>>>
Kwanaki huɗu cir su Zak-Shadow na yaƙi a wannan yanki. Sun ci nasarar zubar da yaran su Dagger zubarwa mai muni, a ƙarshe kuma Zak-Shadow ya kama Dagger da hannunsa kamar yanda yay alƙawarin cikin awanni ɗari da yardar ALLAH. Sai ko UBANGIJIN ya yarje masa ya kuma tallafa masa kafin cikar a wannan ya cafke Dagger ɗin.. Ta ko ina ƙasa ta ɗauki labari akan kama Dagger da Zak-Shadow yayi da hannunsa. Da yanda ya jagoranci wannan yaƙi na tsawon kwanaki shida da kansa ba zaman bada umarni ba shi da Major Imran. Ta ko'ina gidajen tv dana rediyo zance su kawai kake ji. Dan kuwa sun nuna matuƙar jarumta da mazantaka na murƙushe ƙungiyar duhu da ƴan barandan data tara irinsu Dagger. Sai dai abinda Zak-Shadow da al'ummar ƙasa basu sani ba. Murƙushe su Dagger kashe maciji ne kawai batare da dare kansa ba. Saboda su Dagger sunan karnukan farauta kawai suke amsawa, manyan mafarutan na gefe suna kallon komai dake faruwa suma.
Duk da hankulan shugabannin ƙungiyar duhu a tashe yake da kama Dagger ɗin da daƙile aikinsu na haƙar ma'adanai a karo na biyu da duk Zak-Shadow ya taka rawar gani wajen cin nasa a kansu a gefe ɗaya suna jin nasarar mallakar yaran da suka saka aka satar musu dake a hannunsu. Duk da kuwa Zak-Shadow da kansa ya ƙwaci yara kusan talatin a wata maɓoya dake cikin jejin bayan ya tarwatse yaran Dagger da suma ke a wajen. A yanzu yaran dake hannunsu basu wuce ashirin ba, sai na ƙarshe da suka ɗiba a gidan iyayen Umman Nimrah da suma ɗin dai Zak-Shadow ya kafa ya tsare akan nemansu da fatan dawo da su...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 48_
__________________
*🔥 RASH BEAUTY WORLD 🔥 duniyar kayan mata masu kyau da arha ,Ina masu son kaya na kyan gani, amma basu son tsada? To, *ki daina nema!* Rash Beauty World ta zo miki da komai:
*👗 Abaya masu kyau na zamani Egypt/dubai* 👜 *Bags masu kyau* *👠 Takalma masu ɗaukar ido* 💍 *Jewelry masu ƙyalli kamar na sarauta* 🍽️ *Kayan Kitchen masu amfani da kyau*
*Koma da Naira kaɗan za ki yi shopping kamar sarauniya!* 👑💃
✅ Farashi mai sauƙi ✅ Kayamasu quality ✅ Fast delivery
*Shiga group dinmu yanzu kiga sabbin kaya ,Kayanmu masu kyau ne kuma farashi mai sauƙi! Kar ki bari a baki labari don samun kayayyaki masu inganci* 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/GzcU1TcAem21oJedkisrhj?mode=wwt
*RASH BEAUTY WORLD - Inda kyawu da araha suka haɗu!* __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
........."Wai wannan tsinannen mutumin aljani ko mutum?". Viper ya faɗa cikin yaren da suke amfani da shi, muryarsa na fita da ɗaci da zafin yanda yake jin tsabar tsanar Zak-Shadow. "Mutum ne Viper, sai dai uwarsa ta haifa mana bala'i da masifa ne kawai wlhy....." "Ni ma ta gaskiyar Viper ban yarda mutum bane ba sam. Duba fa yanda yake wajiga burukanmu, a karo na biyu ya sake rushe nasarar mu. Taya zamuce mutum ne? Idan ko har mutum ne shi ɗin shugaban matsafa ne matsiyac....." ya gagara ƙarasawa saboda hawayen da suka zubo masa sharr. Haka yake da baƙar zuciyar tsiya, shiyasa suke kiransa da suna Black Spider. Kukan nasa kuwa tamkar ya ƙara tunzurasu ne, musamman oga da har yanzu baice komai ba tun ɗazun. A karo na farko yayi gyaran murya, hakan yasa duk suka bashi hankalinsu, Black Spider mai kuka ya share hawayensa. Da kaushi murya oga Jush ya ce, "Silence. Plan c will begin now. Bana buƙatar Dagger da duka yaransa da aka kama a raye. Zamu sake sabon tsari daga yau. Shi ko tunda yace zai iya wasan zamu zuba. A yanzu ba wasan mutuwa bane ba, wasan gasa masa aya a tsakkiyar tafin hannu ne. Zai rayu, sai dai rayuwa mafi raɗaɗi da ƙasƙanci a idanun ƴan ƙasar tasa dake kambamashi da zuga jarumtarsa. Mu DODANNI ne da KIƊA A RUWA BAYA TADA HANKALIN MU. Zamu ɓoye shi a indanunsa da kunnuwansa zasu cigaba da jin kukan mutanen ƙasar tashi, ya cigaba da kallon gudanar jininsu a cikin ƙasa tamkar kwata ɗin yanka dabbobi. Zakuma mu ɗiba arziƙin ƙasar tasa, kuma ƴaƴan ƙasar tasa ne zasu zama bayinmu masu haƙa, masu kuma kashewa". Raff!! Raff!! Raff!! Kake jin tafi na tashi ga sauran members. Sun san waye ogansu, sun kuma yarda da shi ɗari bisa ɗari. Dan daga faro tafiyar nan zuwa yanzu bai taɓa faɗa bai cika musu ba. Matuƙar nutsuwa kuwa kalaman nashi suka basu, har suna ji a ransu Zak-Shadow tamkar sauro ne yanzu a dakin kwanansu da baya buƙatar magani sai net kawai domin killacewa. Ga damar shan jini ya samu, amma babu karfin fita domin tsira da rai... Sun rufe taronsu da zancen fara horar da sabbin yara da zasu maye gurbin Dagger. Yaran kuwa yaran nan ne da suka rage a hannunsu da suka sace. Daga haka taron ya tashi kowa ya kama gabansa rai fes..
<<•><•>><•><<•><•>>
A lokacin da can ƙungiyar duhu ke ƙoƙarin haɗa GUDU DA WAIWAYE... anan ɓangaren mazan fama bisa umarnin General ne aka turke Zak-Shadow domin duba lafiyarsa. Dan da farko ya dage akan baya buƙata, duk da kuwa ko'a zahiri jikinsa akwai ƙananun raunika na gumurzun da aka sha, banda cizon ƙwarin cikin jeji kala-kala da farar fatarsa ta kasa ɓoye wa. Shi kansa ba ganin likitan ne baya buƙata ba, hankalinsa da tunaninsa nakan Mammah da ƴan uwansa da matarsa ne gaba ɗaya. Dan ya tabbatar sunfi kowa shiga tashin hankali akan abinda ke faruwa, musamman daya kasance a kwana na uku da hargitsewar yaƙin har an sanar da mutuwarsa, mutuwar da ta ɗauki hankalin mutane sosai duk da kuwa ba daga bakin jami'an soji sukaji ba ko makusantansa, hasalima wani ɗan media daɗi ne ya zauna ya tsara labarin da komai, cikin sa'a kuwa ya samu karkatowar hankulan mutane a kansa har wasu gidajen jaridu wajen saurin son ace su suka fara kawo zancen suka fara yaɗawa. Da yake mutane jininsu a farce yake na son jin yaya Zak-Shadow ke ciki saboda randa ya saka sulken yaƙi da kansa kafafen yaɗa labarai masu girma da sanin yakamata sun sanar cike da alfahari. Shiyyasa fitar batun mutuwar tasa yaso yin tasiri sai da hukumar soji suka ƙaryata hankulan mutane ya kwanta aka cigaba da binsu da addu'ar samun nasara. Alhamdullahi UBANGIJI kuwa ya amsa wannan addu'oi tunda nasara ta samu. Duk da wasu sojojin sun rasa rayukansu wasu sun rasa wani sashe na jiki. Musamman Captains da aka rasa kusan guda uku da suka sha gwagwarmaya. Imran ma ya samu harbi a ƙafa, kamar yanda shima Zak-Shadow ɗin ya samu harbi a hannu ta gefen kafaɗa, sai dai da kansa ya cire harsashin ya kuma cigaba da gwagwarmaya, sai kuma a yau ne da komai ya lafa aka sake masa treating ɗin wajen yanda ya kamata...
<<<<<•>>>>>
Kamar kuwa yanda Zak-Shadow yay hasashe akan tashin hankalin su Mammah hakanne. Dan kuwa tun ranar da ya bar gidan ba kowa ya sake barci mai daɗi ba. Hatta su Ma'aruff dake ƙasar Chaina kawo kaya tunda Bilal ya sanar musu a ranar da Dadan ya ɗauki ɗammarar yin yaƙin da kansa suka tattara komai suka dawo gida cikin tashin hankali. Dan a duk sanda Dada yay irin wannan zuciyar ta saka sulken yaƙi ba ƙaramin ɗagawar hankali suke samu ba, gani suke kamar za'a kashe musu shi a tarnaƙin yaƙi. Sai dai Alhamdullah UBANGIJI na bashi kariya da nasara koda kuwa zai samu wani rauni mai girma, iyaka yayi jiyya ya miƙe ya koma filin daga. To amma wannan karon sai suka ji zukatansu sun karaya sosai. Mammah kanta mai ƙoƙarin ƙarfafasu da shanye tata damuwar a wannan karon itama a raunane take, amma maimakon zaman kuka da ɗaga hankali sai ta maida hankali ga addu'a da sadaka, hakan ya ƙarfafa zukatan su Bilal suma suka nutsu wajen gayama UBANGIJI kukansu da fatan nasara ga Dadansu. A randa kuwa akace an kashe shi ɗin nan yanke jiki Mimi tai ta faɗi, jini ya ɓalle mata abinka da mai ƙaramin ciki, hakama sauran babu wanda bai kusa suma ba saboda tarwatsawar zukata. Sai dai Alhamdullah abin bai nisa ba sukaji gaskiyar zance aka koma hawayen farin ciki. Yau kuwa suna jin fitowar su daga jejin kowa ya kasa zaune ya kasa tsaye. Tuni suka bar gida zuwa Headquarter tun ma kafin su Zak-Shadow ɗin su iso Abujan, dan an sanar zai wuce gida ya huta tare da yin jiyya. Suna a cikin barrak ɗin jirgin soji mai saukar angulu daya ɗakko su Zak-Shadow ya sauka, sai dai basu samu ganinsa ba aka shige dasu ciki saboda yanayin da yake ciki na ganin jiri a dalilin jinin daya zubar sosai. Su Imran kuwa dama yau kwanansu huɗu kenan a asibitin cikin barrak ɗin. Har bayan magriba basu ji sun gaji da zaman ba, zuwa lokacin ma Uncle Nasiru ya iso shima. Shi da mahaifin Imran ne suka samu ganawa da Gen. Dan son jin yaya Haysam ɗin na raye kuwa?. Cikin mutuntawa Gen yay musu bayanin da sukaji gamsuwa da kwanciyar hankali, ya kuma basu haƙuri da tabbatar musu in sha ALLAHU zuwa gobe za'a basu damar ganin shima Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu ɗin da muƙarrabansa dake a raye dan sunga Imran dama kullum ma suna zuwa dubashi, sannan a sanar da wanda suka rasa rayukansu... Wannan bayani ya saka su Uncle Nasiru lallaɓa su Mammah komawa gida, sai dai a gidan ma jigum-jigum sukayi babu mai wata walwalar kirki balle jira. Abinci kuwa babu wanda ya nema balle tunanin ci. Nabeeha matarsa kuwa data dinga kuka acan da dagewar acan zata kwana har sai ta ganshi koda suka dawo gidan Mammah bata barta komawa sashenta ba, sai ta taho da ita nan sashensu a bedroom ɗinta. Sosai take jin tausayin Nabeeha ɗin a ranta duk da kuwa ita ta haifi Haysam, ita tafi cancanta aji tausayi da yarda tafi kowa jinraɗaɗi da tashin hankali. To amma mata da miji sai ALLAH, musamman auren soyayya irin na Nabeeha da Haysam, dan tsantsar soyayyar da Nabeeha kema Zak-Shadow a bayyane take ƙwarai da gaske, bata iya ɓoyeta agaban kowa har da ita mahaifiyarsa ma. Shiyasa a wasu lokutan da Nabeeha kan nuna kishinta akan ƙannensa Mammah takanyi murmurshi ne kawai. Haka suma ƙannen nasa basa iya ɓoye kishinsu a kanta wani lokacin, musamman ma idan yazo gidan da nufin yin ƴan kwanaki kowanne najin shine yafi cancanta da samun lokacinsa fiye da ɗayan ɓangaren. Ita dai tana musu addu'a da fatan haɗin kai, dan koba komai itama Nabeeha tasu ce tunda jinin Uncle Nasiru ce, Uncle Nasiru kuwa ya cancanci kowace irin ƙauna da girmamawa a garesu baki ɗaya.
Washe gari ma basu sami damar ganin su Zak-Shadow ba. Dan allurar barci ake musu saboda su sami isasshen hutu na rashin wadataccen barcin kwana da kwanaki da suka sha. Musamman ma shi uban tafiya commandor ɗin yaƙin da ko bai faɗa ba a kallo ɗaya zaka fahimci a jigace yake da son barci, hasalima shine ya saka shi ganin jirin da har suka iso yana ciki. Kwanaki uku cir kuwa suka sami wadataccen barci da nutsuwa yanda ya kamata. Dan basa ganin kowa babu mai ganinsu sai likitoci da wasu manyan soji da ke ɗan zama da su a duk sanda suka ɗan farka musamman a lokacin salla. Suma basa wuce mintuna talatin suke fita su barsu. A kwana cikon na huɗu tunda safe iyalan Mammah kaf suka kammala shirin komawa cikin barrak da su Zak-Shadow ke kwance a asibiti. Mota uku sukayi dan babu wanda ya yarda aka barshi a gida har ƙannen Nabeeha. Ganin sammakon nasu ga ƴan jarida da suma suka matsu da son jin halin da su Zak-Shadow ke ciki dan su isar ma al'umma sai General da kansa ya bada umarnin a kaisu ɗakin da Zak-Shadow yake. Nabeeha ce gaba-gaba wajen shiga, cikin takaici Mommy ta balla mata harara da jan ƙaramin tsaki. Ja'afar dake gefenta da shima takaicin Raihana dake nuna kamar ta fisu son Dadan ya kume, ƙasa-ƙasa ya furta, "Itafa ji take kamar tama fimu sonshi mtsowww". "Kabar ƴar wahala Yaya J. Ai mu da ita kar tasan kar ce. Dan wannan da ace ta samu Dada yanda take so wlhy sai ta rabamu da shi ma". "Ita ɗin banza". Cewar Ma'aruff ƙasa-ƙasa shima. Dai-dai nan suka ƙarasa shigewa ɗakin. Shi kaɗai ne a ciki duk da kuwa babban ɗaki ne an kuma zuba komai a ciki na more rayuwa kamar ba ɗakin asibiti ba. Babu wanda zuciyarsa bata sosu a cikinsu da ganin yanda Nabeeha taje ta maƙalƙalesa ba. Haba wannan rashin kunya har ina bayan tasan Mammah na tare da su. Shi kansa Dadan da alama bai san harda su ba, tunda sai da ta shigo da fin minti ɗaya da rabi saboda gudun da tayi sannan suka ƙaraso. Suna yin sallama yay ƙoƙarin janyeta daga jikinsa, ita ko sai ƙara mannewa take har Momy da Ja'afar ɗin dake a gaba suka fara shigowa suka gansu. Magana yay mata data sakata sakinsa na dole, sai dai cike da takaici da baƙin ciki ta watsama su Mommy ɗin harara. Basu kulata ba, dan basa son koda wasa Dada ya fahimci suna TAKUN SAƘA da matarsa akan soyayyarsa.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 49_
__________________
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LkEgiP5qOEo9YDYjaeZLLc?mode=ems_wa_t✍️✍️ Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed yar mutan Chadian traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products at home my people bazamafa a kwai zafafan promo damukeyi in Sha allahu zuwa on 15 zamugama sannan gareku Yan Kano free ne kayanki zasuzo miki amma fa karyazo bayan mungama promo kuce kyauta ne aa zakibiya kudi nagode takuce yar mutan Chadian mai gyaran ciki dawaje 💃💃 please banda maza,❌maza❌ In kinada matsala wadda zamu iya taimaka miki 09065504546 Ga PRODUCTS DINMU KAMAR HAKA MAGANIN SANYI TSUMIN BOM MADARAR TABAJE GORON TULA SYRUP ZUMAR SHADAMATSIN GARIN YAUKAYAUKA EMERGENCY GARIN KINFI KAZA DADI SIRRIN MALLAKAR KASA SIRRAN GIDANKI DAHUWAR KAZA DAHUWAR CICCIBI DAHUWAR YAN SHILA HMM BAZASU IRGUBA INA GODIYA SOSAI MY PEOPLE 🥰🥰
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________