Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 25
Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 25: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 25. .........Cike da girmamawa da soyayyar da suke masa suka…
4,463 words
.........Cike da girmamawa da soyayyar da suke masa suka zagaye gadon kowanne idanu cike da hawaye, shi ko ya zuba musu ido kawai daga zaunen da yake bayansa jingine da fillo. Sanye yake da wando da riga masu taushi kalar army green na barci. Duk da fatarsa tayi duhu sosai saboda wahalar yaƙi ga raunikan jikinsa hakan bai hana kamilar fuskarsa fitar da hasken kwarjini da bayannanniyar nutsuwarsa da kamun kai ba. Karo na farko ya sakar musu ƙaramin murmushi. "Miye haka kunzo kun zagaye ni kamar masu shirin min tambayoyin kabari?". A tare suka saki murmushi suma suna share hawayensu, sai kuma suka shiga rungumeshi abin sha'awa su takwas ɗin duka sukai masa runfa. Yayinda kukan Mimi da Biebah ya ƙara ƙarfi. Kansa kawai ya girgiza, tare da ɗan buga bayan Ammar da Ummi da sukafi kusa da shi. Cikin lallashi ya furta, "It's okay guys! I'm here. Kun san dai bana son kuka. Ina Mammah?". Kamar jira suke ya nema Mammah ɗin suka wani dare daga jikinsa Mammah dake tsaye a farkon shigowa ɗakin ta bayyana cikin idanunsa. Yunƙurawa yay zai sauka ta girgiza masa kai. Shi mutum ne mai tsananin girmama iyaye da basu darajarsu koda a gaban waye. Baya wasa da al'amarin Mammah a rayuwarsa ako wane yanayi.... "Kaida ke fama da kanka ina zaka sauka". Cewar Mammah tana ƙarasa shigowa ɗakin idanunta akansa. Ƙasa-ƙasa ya ɗan murmusa, koda ta kai zaune a gefen gadon kusa da ƙafafunsa sai yay salute ɗinta. Ƙaramar harara tayi masa, harar data saka murmurshinsa ƙara faɗaɗa ƴan uwansa kuwa na dariya. Da ido yay ma ƙanen nasa alamar suma suyi, ai ko sai suka wani ƙame tare da sara mata a tare. Mammah dake girgiza kai ta ce, "ALLAH ya shiryeku to. Da alama na fara zama kakarku kuma". Ma'aruff ya ce, "Mammah ba haka bane, kin san masu iya magana sunce UWAR RAGO akema JAJE, UWAR GWANI kuwa sai dai ai mata SAMBARKA." "Wannan zance haka yake Yaya M." Cewar Bilal yana kashe masa ido ɗaya. "ALLAH ya shuryeku". Mammah ta sake faɗa tana sake maida hankalinta kan Zak-Shadow daya risinar da kai yana gaisheta. "Yaya jikin naka?". "Alhamdullahi Mammah bana jin ciwon komai, kawai dai sun so riƙeni anan ɗin ne suma". "Yin hakan shine dai-dai ai. Ga jiki duk raunika ace ba'a jin komai kuma." Ɗan murmurshi kawai yayi, ta gefen yana kallon yanda Nabeeha ta haɗe fuska, dan tunda ƙannen nasa suka zagaye shi ta koma gefe. Sai su Ismat ƙannenta suka koma gefenta suma duk suka maƙale. Idanunsa ya ta janye, zuciyarsa na masa babu daɗi. Ya jima da fahimtar matar tasa bata son ƙyaƙyƙyawar alaƙarsa da ƙanensa, kai wani lokacin ko tare da Mammah ta ganshi suna hira sai fuskarta ta canja, ya rasa gane ma'anar hakan da take yi. Bayan ita bai taɓa nuna damuwar zaman ƙanenta tare da su ba, dan ko babu ita zai riƙe zuri'ar Uncle Nasiru a duniyar nan duk da kuwa Ismat ce kasai tashi biyun ƴaƴan ƙanwar mamarta ne... Shigowar Uncle Nasiru da Baban su Imran da Hajiyarsu, sai matar Uncle Nasiru ɗin da yaranta, dan itama dai yaranta biyar da shi a gidan yanzu, kuma suma duk sun tasa ba laifi. Idan aka haɗa dasu Nabeeha da ƙanenta biyu yaransa takwas shima a duniya. Cikin girmamawa Zak-Shadow ya gaida su, dan kallon iyaye yake musu su duka. Yana kallon Uncle Nasiru tamkar Abiy a gefensa, iyayen Imran kuwa suma sun zama iyaye a gareshi, dan suma suna masa abu irin na ɗan da suka haifa, shiyyasa zuminci ne mai ƙarfi a tsakanin waɗan nan zuri'a uku a yanzu. Sun jajanta masa, tare da jinjina da addu'a bisa ga namijin ƙoƙarin da sukayi da jarumtar murƙushe waɗan nan mutane da bayyanar ta'addancinsu ke tada hankalin al'umma. A wannan yanayin Imran da zuwa yanzu shi ya fara takawa dan kwanansa na takwas kenan shi a barrak ɗin tun randa aka harbesa aka kawosu ya shigo tare da wasu soja biyu. Sai Nimrah riƙe a hannunsa tayi fes da ita, sai dai tayi zuru-zuru alamar rashin sakewa da damuwa bayyane akan ƴar fuskarta. Kamar yanda Zak-Shadow ya zuba mata ido haka kowa a ɗakin ita yake kallo, yaran sojin suka ƙame cike da girmamawa ga Zak-Shadow, sannan sukai gaisuwa da tambayar jikinsa. Kai ya jinjina musu kawai. Imran ma ɗan ƙamewa yay alamar nuna girmamawar, kawai Zak-Shadow ɗin ya balla masa harara. Bakuna su Ma'aruff suka gumtse suna dariya ƙasa-ƙasa, suko su Mammah murmushi duk sukayi. Imran ya gaishesu, suka tambayi nasa jikin shima duk da kuwa kullum suna shigowa dubashi tun ma kafin a kawo su Zak-Shadow. A karo na farko Zak-Shadow dake kallon ƙafar Imran ɗin ya ce, "Yaya kafar taka?". "Alhamdullah saura kaɗan ya rage, dan shekaran jiya na fara takawa sosai. Yaya jikinka kaima?". "Ni lafiyata Lau, kawai anso takura min ne anan". Ƴar dariya Imran yayi, sai kuma ya jawo hannun Nimrah data noƙe gefe tayi kicin-kicin da fuska kamar zata fashe da kuka. Kusa da Zak-Shadow ya matso da ita yana faɗin, "Yanzu su Yusuf suka kawota, itama yau aka sallameta a asibiti". Hannu ya miƙa mata a karo na farko, sai kuma ya ɗaga kai yana kallon su Yusuf ɗin yaran sojin dake tare da Imran. Cikin girmamawa suka ƙara ƙamewa, sannan wanda aka kira Yusuf ya ce, "Sir! Yau da safe suka sallameta gaba ɗaya, bayan an tabbatar babu wata matsala a tare da ita a yanzu. Sai dai sunce lokaci-lokaci zata iya dinga tsintar kanta a yanayin tsorata ko firgici, dan haka za'a cigaba da kaita tana ganin likita da amsar magani". Kansa ya ɗan jinjina, "Sauran yaran fa?". "Duk suna cikin ƙoshin lafiya da kulawa ta musamman ga Captain Ayuba, dan tun ranar su aka miƙasu can hannun jami'an gwamnatin jiharsu. Da ita kaɗai muka taho nan Abuja bisa umarnin Major Imran". "Zaku iya tafiya". Kawai ya faɗa bayan ya jinjina kansa. Sai da suka ƙara Sara masa da salute shi da Imran ɗin duka sannan suka juya suka fita. Babu dai wanda yayi magana a ɗakin kowa yana kallon Nimrah da son jin ƙarin bayani a bakin Zak-Shadow ɗin ko Imran. Sai dai suma duk sunyi shiru. Sai da aka kusan mintuna biyu sannan Zak-Shadow yay ma Nimrah magana a karo na farko. Idanunta dake tara ƙwalla ta zuba masa batare data amsa ba, sai kuma ta fashe da kuka da faɗin, "Baba ɗan sanda nika kaini wajen Ummana. Bana son nan". Kallonta kawai yake yi shi dai, sai Imran ne cikin lallashi ya duƙo yana mata magana. Kafaɗa ta maƙe masa. "Ni dai bana son nan". Ta sake faɗa tana ɓarkewa da kuka harda fara buga ƙafa, ƙarshe ma ta zube ƙasa zata fara musu borin data saba yima Ummanta a Bankaura. Zak-Shadow bai ma san ya daka mata tsawa ba. "Kika mana bori anan sai na karya ƙafafunki, maza tashi". A mugun razane ta miƙe jikinta na rawa, ta gumtse baki domin hana kukan dake son kufce mata fita. Imran zai riƙota rawar jikinta ta ƙaru. A karo na farko Mammah dake kallonsu kamar kowa na ɗakin tai ƴar gyaran murya, sai kuma cikin lallashi ta miƙe ta ɗauki Nimrah cak ta ɗaura a saman cinyarta. Rungumeta tayi a jikinta. Kamar kuwa tana jira sai ta ƙanƙameta ta fashe da kuka. Cikin dabara irin ta uwa Mammah ta dinga shafa kan Nimrah da bayanta har barci ya ɗauke ta a haka. Dai-dai lokacin kuma likitan dake kula da Zak-Shadow ya shigo. Dole kowa ya miƙe domin tafiya. Mammah dake kallon ƙyaƙyƙyawar baƙar fuskar Nimrah dake barci ta ce, "Gashi tayi barci, ko nan kusa da kai za'a kwantar da ita ne?". "A'a Mammah ku tafi da ita gida, dama nan za'a kawota". Babu wanda a ɗakin bai kalla Zak-Shadow mai maganar ba, idan ka cire Imran dake normal. Tsulum Nabeeha ta ce, "Gida kuma D. A dalilin mi? Ina iyayenta da baza'a kaita wajensu ba sai gidan mu?". Bashi da niyyar bata amsar tambayoyinta. Dan haka Imran ya katse shirun da faɗin, "Kuyi haƙuri idan ya samu lafiya zakuji bayanin komai a kanta....." "Bayani kamar ya? Kai miyasa baza'a kaita naka gidan ba to? Ko dole shike da alaƙa da ita?". Naneeha ta sake maganar cikin rufewar idanu. Dan tana da matsanancin kishi na tashin hankali. Shiyasa ko ƴan uwan Zak-Shadow take jin kishi idan sun raɓe shi. Matar mahaifinsu Uncle Nasiru kanta saboda kishin uwarsu basa ko gaisheta, shiyasa da suka shigo ma ko kallonta basuyi ba balle ƴaƴanta duk da kuwa bata haɗa zama da uwarsu a gidan su ba, tunda sai da ta fita a dalilin auren Nabeeha da Zak-Shadow ɗin sannan ya aureta. Da aka sasanta su ta dawo tace bazata koma ba sai ya saki matar tasa, shiko yace tai zamanta, shi da matarsa mutu ka raba dan yana samun kwanciyar hankali a wajenta fiye da sanda yay rayuwa da ita. Hakan ya ƙara mata tsana a wajen su Nabeeha ɗin, ita ko ta kame kanta daga garesu sai dai su zageta a bayan idonta, agaban ta kam babu dama dan shakkarta ma suke yi... Ganin mugun kallon da Zak-Shadow ya watsama Nabeeha ɗin Mammah ta katse yunƙurin Imran na son sake magana. "Ya isa haka, kumuje kawai ga likita na jiranmu fa". Kowa yunƙurawa yay da niyyar tafiya banda Nabeeha data cika tai fam. Sai ma yunƙurowa tai zata sake magana Uncle Nasiru ya daka mata tsawa. "Ba'a isa dake ba kenan ko Nabeeha?". Hawayen da suka cika mata idanu ne suka silalo, ta ce, "Amma Abbah...." "Bana buƙatar ji, wuce muje". Yanda yay maganar babu wasa balle sassauci ya sakata raɓashi ta wuce tana waiwayen Zak-Shadow dako kallonta bayayi. Suna gama ficewa yaja tsaki mai ƙarfi yana mai zamewa ya kwanta. Ayyanawa yake a ransa Yaya zai yi da baƙin kishin Nabeeha shi kam? Dan yayi imanin tunda ta fara da haka ba ƙaramin badaƙala zaman yarinyar nan zai kawo ba a wajensu. Shi kuma babu gudu babu ja da baya akan yarinyar nan, yanda ya amshi amanarta a hannun mahaifiyarta in sha ALLAHU zai riƙe koda ransa zai zama fansa a wajen bata kariya........✍🏼
(🤔To babbar magana).
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 50_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
........Iska kaɗan Imran ya furzar yana kallon fuskar Zak-Shadow daya lumshe idanu. "Zak.. gaskiya akwai matsala, tunda har matarka ta fara nuna damuwa akan yarinyar nan". Shiru kamar bazai tanka ba, sai kuma ya buɗe idanunsa da har sun ɗan sake kaɗewa akan Imran ɗin. "Saboda itace mai aure na?". "Humm bazaka fahimta ba, kasan mata da kishi, bana son maimakon riƙe amanar da bani da haufi a kanka wajen riƙewa al'amarin ya koma wani abu daban. Taya kake tunanin zata riƙe yarinyar nan a wannan yanayin data fara nunawa?". "Sai ta kasheta ai, ince dai ƙarshen kishin nasu kenan ko. Mtsoww, ni kada ka ɓata min rai ma". Shiru Imran yay bai sake magana ba, amma tabbas shi yasan akwai rigima. Dan kishin Nabeeha ba ɓoyayye bane ga kowa. Tunda har akan ƴan uwansa da Mammah ba ɓoyewa take ba. A haka likita ya dawo ya duba Zak-Shadow ɗin, ganin ya ɗakko allurar barci ya dakatar da shi. "Ka sallame ni kawai". Cikin girmamawa sojan likitan ya ce, "Kayi haƙuri Sir ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ne, dan jikinka na buƙatar hutu sosai". Wani kallo ya watsa masa kawai. Da sauri likitan yace, "I'm sorry Sir". Murmurshi Imran yayi a karo na farko. Sai kuma ya kalla likitan. "Karka damu ka sallame shi kawai, idan baiji dai-dai ba sai ya dawo". "Okay Sir".
<<•>>°<<•>>°<<•>>
A ranar aka sallami Zak-Shadow daga asibiti. Shi mutum ne mai adalci da duba na ƙasa da shi akan komai daya dace. Dan haka maimakon tafiya gida ya samu hutun jiyya da aka basu sai ya koma jihar da ƙauyukan su Bankaura suke ƙarƙashinta ya duba sojojinsu da aka kwantar a asibiti. Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba da ganin irin ɓarnar da akai musu. Dan sojoji da yawa sun jikkata. Hakama ya shiga har inda aka killace gawarwakin waɗan da suka rasa ransu, ciki harda Captain Musa. Lokacin daya ɗora idanunsa akan Captain Musa sai da suka sake juyewa, Captain Musa jarumin soja ne ɗan amanarsa, ya taka rawar gani matuƙa akan wannan yaƙin, babu abinda zasu masa sai addu'a. Lokaci ɗaya aka harbesu da Major Imran, shi da yake kwana ya ƙare tun a jejin ya rasu, shi kuma Imran ya suma. Bayan ya gama zagaya su kaf daga asibitin cikin barrak inda sojojin suke su, babban asibitin jihar ya nufa itama. Nan ko mutanen ƙauyukan ne da suma suka samu raunuka. Kamar yanda yay fata suna samun kulawa ta musamman daga gwamnati, akwai kuma jami'an sojinsu a tare da su, da ƴan sandan farin kaya. Suma ya dubasu. Daga nan ya wuce sansanin da aka samawa waɗan da suka tsira. Ganin yanda aka barsu a wulaƙance sai a tsakar wajen suke kwana damma zafi ne ransa ya ɓaci. Dama akwai zaman da zasuyi da Gwamnan jihar da shi da wasu manyansu a washe gari. Ai gaba ɗaya ya tattara takaicinsa ya ajiye har zuwa lokacin zaman. Daga sansanin cikin jejin da nasu sansanin yake suka koma. Komai ya lalace, sai dai anata kafa sabbin tantuna an kuma kawo wasu rundunar sojojin dan bazai yiwu abar yankin a haka babu tsaro mai ƙarfi ba. Har dare suna a cikin jejin, dan har cikin ƙauyukan Bankaura, Gangare, da Marke sai da suka shiga. Anan dama abubuwan sukafi tsamari musamman Bankaura a ƙarshe-ƙarshe. Dan an musu ɓarna matuƙa da zasu daɗe basu maida gurbinta ba. Har a yau ana zaƙulo gawarwaki a cikin jejin da ƙauyen Bankaura irin na wanda suka ɓuya a wasu wajejajen suka kasa fita. A lokacin da suka wuce ta ƙofar gidan su Nimrah ya kwashe mintina uku yana kallon gidan da tuna abubuwan da suka faru tun daga farkon zuwan su Imran da sanda yay kiransu. Randa Nimrah tai musu zancen falawa har zaman da sukayi da Ummanta. Rayuwa kenan, cikin abinda baifi sati huɗu ba komai ya lalace, dan gidan ya rurrushe sosai sakamakon bomb da yaran Dagger suka tayar musu suma tamkar gidan iyayen Umman Nimrah. Shiyasa suma baya jin akwai wani sauran zuri'ar data rage, idan kuwa sun rage to ƙalilan za'a samu kuwa a ciki, suma yara ne ko wanda basa a garin al'amarin ya faru. Tunda suka baro jejin zuwa masaukin da aka bashi a cikin barrak na jihar wanka kawai ya iya yi ya zauna yana wasu rubuce-rubuce, bayan ya kammala kuma ya hau salloli. Bai kwanta ba sai da yay sallar asubahi. Zuwa ƙarfe goma dole ya farka dan suna da meeting da zasu zauna da Gwamna akan harkar tsaro. Amintaccen yaron nan nasa, kuma munafukinsa a bayan fage da tunda ya iso yake nane da shi ya kira a waya. Babu jimawa ya iso. Bayan miƙa gaisuwar girmamawa tamkar wani mutumin arziƙi kansa a ƙasa ya ce, "Sir! Akwai abinda kake buƙata ne?". Batare da Zak-Shadow ya dubashi ba ya miƙa masa wata ƙaramar takarda da ATM ɗinsa. "Kaje Boutique ka sama min kayan da zanyi amfani da shi. Saura ka ɓata min lokaci". Ya ƙarashe maganar ƙarshe cikin dakewarsa da rashin ɗaukar raini. "I'm sorry Sir, bazan daɗe ba in sha ALLAHU". Zak-Shadow bai sake tanka masa ba, hasalima ya ɗauke kansa ya koma gaban takardun da yay ta rubutu a daren jiya.
Koda Ojo ya fito sai ya harari ɗakin da Zak-Shadow yake, kafin ya kalla ATM ɗin daya bashi da takardar mai ɗauke da pin ɗinsa ya taɓe baki. Baiyi yunƙurin komai ba sai da ya fita a barrak ɗin gaba ɗaya. Nesa sosai ya samu waje ya tsaida mai mashin ɗin daya ɗakko shi. Sauka yayi ya bashi kuɗin, ya samu ƙasan wata bishiya ya zauna. Kamar yanda ya saba kai duk wani motsi da bayanan Zak-Shadow ga iyayen gidansa yanzun ma haka yay kira ya rattafa bayani. Tun daga dawowar Zak-Shadow a jiya har komawarsu jejin nan da ƙauyukan, da takardun da yaga ya baza a ɗakin daya kwana. Daga can wanda yake gayawar ya ce, "Su kayan daya aikeka ka saya na miye?". "Sakawa zai yi sir! Sai dai kamar akwai inda zasuje shi da wasu manyanmu dan jiya bayan mun dawo barrak ɗin sunyi wani ƙaramin meeting su uku". "Na baka daga nan zuwa awa ɗaya, nasan ina zai je. Idan ba haka ba kada ka kirani. Sannan ka sani, dolene a yanzu sanya idonka yafi na baya, dan mun rasa yara biyu a wannan tafiyar, an kashe ɗaya, ɗaya na cikin wanda aka jima rauni a asibiti". "Babu wata damuwa Sir, komai kuke buƙata zanyi fiye da hakan, kada ka manta na shiga rigar soja ne kawai saboda aikin ku badan zama soja ba. Shiyyasa ma a yaƙin nan ban yarda na cusa kaina a halaka ba". "Good! Da kake tuna hakan. Yaushe zai koma Abuja?". "Bani da cikakken bayani akan hakan shima, amma nasan bazai jima ba tunda yana ƙarƙashin hutun jiyya ne shi da aminin nashi dama sauran Captains ɗin mu. Dan shi kaɗai ma yazo jiyan alamar akwai abinda yazo yi, duk da dai nasan shi mutum ne azababbe akan aiki shiyyasa ake shan wahalar cimmas cikin sauƙi". "Mtsoww! Zai kuwa gane kuransa a wannan karon". Daga haka ya yanke kiran. Ojo dake dariyar mugunta zaram ya miƙe yana cire layin daya saka a wayar tasa yay kira, ya maida ainahin layinsa da kowa ya sani sannan ya sake tare mashin ya hau ya tafi aiken Zak-Shadow.
★Kai sojan da Zak-Shadow ya saka ya biyo bayansa ke ɗawa tamkar ƙadangare, sai da ya ga mashin ɗin da Ojo ya hau yayi ɗan nisa sannan ya tare wani shima ya hau. Bayan Ojon yasa suka bi, sai dai bai sauka a mashin ɗin ba lokacin da suka iso inda ya sauka a nashi mashin ɗin ya shige wani Boutique. Har yace mashin ɗin ya juya sai kuma yace ya dakata, suna nan kusan mintuna ashirin Ojo ya fito cikin sauri yana kallon agogon hannunsa. Mashin ya sake tarewa ya haye. Yanzun ma sakawa sojan yay suka cigaba da bin bayansa, sai dai ganin ya sauka a ƙofar gate ɗin barrak ɗin shi kuma sai ya sauka can nesa ya biya mai mashin ɗin ya ƙaraso da kafa. Bai nufi masaukin Zak-Shadow ba har sai da ya tabbatar Ojo ya kai masa kayan ya baro ɗakin sannan. Cike da girmamawa yayi knocking, Zak-Shadow ya bashi izinin shiga. Cikin ƙamewa da sarawa ya ce, "Sir! Duk inda yaje tare mukaje da shi ina biye......" tsaf ya labarta masa komai da ya gani ya kuma ji daga Ojo. Wani kalar zuba masa ido Zak-Shadow yayi, dan tabbas zuciyarsa ta girgiza. Saboda daga jiya zuwa yau ne kawai ya ɗarsa zarginsa akan Ojo, zargi kuma ba irin wanda ya samu bayani ba a yanzu. Dan kuwa shi zargin ma da yakema Ojon daban, abinda yaji a yanzu daban. A take wata ƴar zufa ta taru masa a goshi, idanun nan suka shiga juyewa. Da wata irin tsatstsaurar murya ya furta, "Ka tabbatar da abinda ka faɗa?". "Yes sir! Duk abinda na faɗa maka shine gaskiya, zaka iya saka wani binciken bayan ni ma domin tabbatar wa". Wani irin amsa kuwwa sunan Ojo ya shiga yi a kunnen Zak-Shadow da brain ɗinsa, har yana ma jin kamar wata juwa-juwa na neman ɗibarsa. Ojo fa, yaron daya bama yarda mai girma bayan Imran, dan ko sauran amintattun yaransa basu kai Ojo ɗin ba ciki kuwa harda shi wannan Yusuf ɗin daya kawo masa bayani akan Ojo ɗin yanzu. Lallai babbar magana, ashe kamar yanda yayi hasashen yaƙin nasa biyu ne na cikin gida dana waje hakan take.
>>•<>•<<>•<<>•<<
Har Zak-Shadow suka isa gidan gwamnati al'amarin yaronsa Ojo na masa kai-kawo a zuciya. Da ƙyar ya iya dannewa suka tattauna sosai akan abinda ya dace. Bai gusaba kuwa sai da ya sakko zancen ƴan gudun hijira da aka bari a wulaƙance. Babu wani tsoro ko shakka kuma ya nuna ma gwamna idan fa akai sakacin barinsu a wulaƙance to za'a iya fuskantar ƙalubale mai girma da yafi wanda ake kai a yanzu. Amma basu muhallin zama da tattara yaransu a saka a makarantu a samawa matan sana'ar yi da sauran mazan da suka rage shine babban gata garesu dama al'umma baki ɗaya.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 51_
__________________
https://vm.tiktok.com/ZSHcfQFhUuBVU-MpLRV/https://www.instagram.com/dijas_delicacy_?igsh=MWp3MThqcXlsZXB2eg==Wa.me/+2348140002981
https://www.instagram.com/dijas_delicacy_?igsh=MWp3MThqcXlsZXB2eg==
Assalamu alaykum mutanen Sokoto Da kewaye Shin Ko kunsan cewa DIJAS DELICACY ashirye take Domin faranta ranku a bukukuna Da kowani irin even? Kama Daga samosa, doghnut, spring rolls meat pie, birthday cakes Da sauransu Bata tsaya anan ba tana amsar orders koda yaushe. Inda samosa kike nema frozen Ko fried duka tana dasu akan 3k 10pcs and she bakes daily🥰 Bata tsaya anan ba GA masu son gyaran jikinsu wata skin care tana siyarda best skin care products Kama Daga face wash, face cream,body butter, shower gel dadae sauransu tana aeka Kaya a kowani gari cikin aminci Da yardar allah GA no. Dinta kiyi saving Domin samun naki was.me/+2348140002981 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Duk da yanda yake maganar kai tsaye ta sosa zuciyar gwamna haka ya danne, dan harga ALLAH wani irin kwarjini da cika waje Zak-Shadow ɗin yay masa. Ya jima yana jin labarinsa da jarumtarsa a wajen yaransa musamman kwamishinan tsaro a tsakanin wannan rikicin, amma bai taɓa tunanin mutumin fa ya wuce yanda ake labarin nasa ba. Cikin danne abinda ke ransa da nuna aminta da zancen Zak-Shadow ɗin ya tabbatar masa zai yi ƙoƙarin yin abinda ya dace in sha ALLAHU daga yau zuwa gobe ma. Dan ya fahimci hukumar sojin ma wani girma na musamman take bashi. Sun ƙara tattaunawa akan batun ƙara sojoji a cikin jejin kafin meeting ɗin ya tashi. A gidan Gwamnatin sukai sallar azhar, daga nan sukai zaman cin abinci da gwamna wanda Zak-Shadow yaƙi cin komai a wajen. Wannan ba sabon abu bane, dan duk wanda ya sanshi yasan ba'a ko'ina ake bashi abu yaci ba. Dan komai nashi da tsari. Kai da yawansu zasu iya ratsuwar basu taɓa ganin ya zauna cin abinci a gaban kowa ba. Idan zai ci abinci yakan killace kansa ne yaci a nutse. Hakan da yayi ma ya ƙara saka jin shakkarsa a zukatan jami'an gwamnatin da akai zaman hadda gwamnan kansa. Dan bayan barowar su Zak-Shadow gidan gwamnatin sai da sukai ƴar gulma akan girman kan Zak-Shadow yayi yawa. Acewarsu yana Lieutenant Colonel kawai yana wannan isar da izza inaga ya zama General watarana, ai kowama ya shiga uku. Acewarsu wannan tsaf zai iya assasa juyin mulki a ƙasa.
Oho shi baima san sunayi ba, dan daga gidan gwamnatin airport ya wuce zai wuce Abuja. Jirginsu yana gab da tashi ma. Acan ya samu Ojo na jiranshi, shi ya saka ya saya masa tickets harda shi. Bai tsara matakin ɗauka akan Ojon ba, amma ya ƙudira sake jansa a jikinsa fiye da da saboda wani dalili nashi. Mintina baifi goma da zuwansa airport ɗin ba jirginsu ya ɗaga. Tafiyar da bata gaza awa ɗaya ba suka sauka birnin tarayya. Anan airport suka rabu da Ojo, shi ya wuce barrak shi kuma ya samu su Ma'aruff sun zo ɗaukarshi. Cike da farin ciki suka rungumeshi kuwa. Ojo dake binsu da kallon ƙurilla ya miƙama Ja'afar ƴar briefcase ɗin Zak-Shadow ɗin dake hannunsa. Kafin ya ƙame tare da sara masa. Hannu kawai ya ɗaga masa batare daya kallesa ba, amma yana lure da kallon ƙurillar da yake ma su Ja'afar ɗin. Kaɗan ya cije lips ɗinsa, a ransa yana raya (Yaro tsaya matsayinka kada zancen ƴan duniya ya ruɗe ka. Dan in kace zaka tsalla gonar zuri'ata zan yanka maka kazar wahala ne kuma sai ka figeta da sili-silin gashi). A zahiri kam bayan mota da Ma'aruff ya buɗe masa ya shiga ya zauna. Suma duk gaba suka shiga Ja'afar yaja motar suka kama hanyar gida. Gaba ɗaya sun cika masa kunne da surutu kamar wasu ƙananun yara, shi dai yana jinsu da kunne kawai, wani lokacin kuma yakan yi murmurshi ko girgiza kai da faɗin, "ALLAH ya shiryeku" a taƙaice. A haka suka ƙaraso gidan....
(((★)))★(((★)))