Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 26

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 26

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 26: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 26. Zantukan Ojo kaf sunje kunnen oga Jush shugaban ƙungiyar…

3,647 words

Zantukan Ojo kaf sunje kunnen oga Jush shugaban ƙungiyar duhu. Dan haka ya tara meeting na gaggawa ga members ɗin ƙungiyar. Dama dukkan motsinsu a tsakanin nan a cikin meeting ɗin suke kala-kala. A duk sanda ya bada umarni babu mai wasa wajen amsa kiransa. Dan haka a yanzun ma cikin gaggawa suka gama hallara. Kowa da kowa yazo idan ka cire Dagger da dama ba akowane zama suke zama da shi ɗin ba sai suna buƙatar hakan saboda a wajensu sunan karen farauta kawai yake amsawa. Saɓanin kowanne zama yau oga ne ya fara magana kafin ma su tambayi dalilin zaman. Sai da ya fara kunna musu recording ɗin muryar Ojo da aka tura masa duk suka saurara. Batare da jiran cewar wani a cikinsu ba ya cigaba da faɗin, "Zamu rushe wasu ɓangarori na plan c". Gaba ɗayansu kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu, cikin alamar tambayar juna a yanayin kurame suke ɗan jujjuya hannayensu. Wasu ko na ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki irin na suma basu gane ba. Oga Jush dake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya yay ƙaramar gyaran murya daya dakatar da gungunan nasu dake tashi a ɗakin. Tsitt sukayi gaba ɗaya, tare da maida hankali kansa. Sai da yaja sakanni cike da shan ƙamshi sannan ya cigaba da magana. "Kamar yanda na faɗa bama buƙatar wasu ɓangarori na plan c kwata-kwata saboda na fahimci wani abu a yanzu". "Kamar mi kenan oga?". "Muna buƙatar su Dagger a raye. Dan haka Viper ka dakatar da plan ɗinmu na tura masu kashesu". "Yanda kace haka za'ai Sir. Amma miyasa kace hakan? Bayan kasan zaman mutanen nan a raye hannun sojojin nan komai zai iya faruwa, ciki kuwa harda sanin mu su wanene. Musamman haɗarin yafi girma akan Dagger da shi ya sammu. Gara ma sauran su Dagger ɗin suka sani". Tabbas zancenka a kan hanya yake kuma kana kan dai-dai Viper. Amma abinda nake son ku tuna ba ko yaushe ake iya kama tsuntsu ta baki ba, dan wani tsuntsu ba hatsi yake ci wajen ƙoto ba ababen cikin ruwa ne abincinsa. Ba kashe Dagger ne mafita ba, yin amfani da shi wajen kama mutumin nan ta wuya shine ya dace". Sake kallon kallo suka shiga yi, dan su sam basu wani fahimci komai ba. Cike da izza Mr Specter sarkin ƴan girman kai tamkar ogan nasu ya furta, "Na fahimci abinda kake nufi Oga, kuma nayi na'am da wannan tsarin. Kai tsaye ma ni har wani ƙyaƙyƙyawan tunani yazo min". Karo na farko Oga Jush ya saki murmurshi idonsa akan Mr Specter, shiyyasa yake matuƙar son shi, dan shima akwai kwanya. Yana wani jinjina kai da lumshe idanu da buɗewa a lokaci guda ya ce, "Yes Mr Specter muna saurarenka, wane tunani kayi?". Wani ƙarin girman kai Mr Specter yaji, dan haka ya gyara zamansa yana ajiye ƙatuwar sigarin hannunsa a ɗan bowl ɗin da yake tara tokar. "Sir ina ganin wannan sabon shirin zai dace da yin jifa da karan farautarmu a jikin fatsar da zata kamo mana wannan babban kifin. Ina nufin wannan yaron Ojo, dan aikinsa na ƙyau sosai, sai dai gaggawa zata hana masa yin doguwar tafiya dan Zak-Shadow ba sakarai bane". Murmurshi mai faɗi Oga Jush ya sake saki, sai kuma ya shiga tafama Mr Specter, dole suma sauran suka zama ƴan bin yarima akasha kiɗa kawai. Sai da sukai na fin sakan goma sha biyar sannan suka sarara. Oga Jush ya ce, "Lallai ka gane mi nake nufi a sabon shirin mu na ɓangaren haggu. Na ɓangaren dama kuwa lokaci yayi da tafiyarmu zata gayyato manyan babba da jaka na ƙasar nan, hakan ne kawai zai bamu damar farauto kifin cikin ruwa dake gadarar shi ISHA'U DUTSE NA RIMI ne BAKA FARGABA, to amma a ƙarshe shima ai yace SAI NA RUWA ko". A karo na farko saura ma suka fahimci darasin Ogan nasu, dan a tare suka kece da dariyar mugunta da na hango nasara. Sun sake tattauna abinda ya dace musamman akan fara horar da sabbin yara da maye gurbin Dagger a cikin yaransa da su Zak-Shadow basu kama ba da gaggawa, sai al'amarin Ojo da shima dole su gaggauta, daga haka taron ya watse zukatansu fes.....

<><><><><><><>

Tun shigowarsu harabar gidan Zak-Shadow ya zubama baƙuwar motar dake fake a dai-dai ƙofar sashensu idanu. Koda Ja'afar ya kammala parking a inda ya dace har Ma'aruff ya fita ya buɗe masa sashen da yake hankalinsa nakan motar dai, a karo na farko shima Ma'aruff ɗin ya juya ya kalla motar, sai kuma ya juyo batare da jiran tambaya ba ya ce, "Dada motar Momyn su Ismat ce, jiya tazo da yamma itama". Kauda idanun nasa yay daga kan motar, batare da yace komai ba ya miƙama Ma'aruff ɗin wayoyinsa biyu. Ja'afar ma daya riga ya fito can gefen ya buɗe ya ɗauki briefcase ɗinsa. A tare suka rufe motar, sai kuma suka kalli juna suna murmushi ganin ya nufi sashen Mammah. Da sauri sukabi bayansa sun ɗan tafa kowa ya janye hannunsa yana yarfarwa da ƙoƙarin danne dariya duk a lokaci guda, sai kuma akai sa'a Dadan ya juyo zai kallesu ganin basu biyo shi ba. Da sauri suka gimtse fuskoki tare da zabura inda yake. Shaƙiyancin Ja'afar da Ma'aruff babu wanda bai sani ba, dan haka ma ya juya abinsa ya cigaba da tafiya suna take masa baya. Sallamar su ta saka Mu'azz dirowa a kujera da gudu yayo ƙofa, cike da farin ciki yake faɗin, "Oyoyo Dada na". Guntun murmushi Zak-Shadow yayi, tare da tsayawa cak har Mu'azz ɗin ya ƙaraso inda yake ya rungumeshi. Kan yaron ya shafa, dai-dai shima Ja'afar na kai masa rankwashi da faɗin, "Ɗan iya kenan, wato Dadanka ma kai kaɗai, ai mu riƙo aka kawomu gidan naga". "Ai rankwashin da yafi wannan ya kamata kai masa". Cewar Ma'aruff yana harar Mu'azz shima. Baki Mu'azz ya tura yana sake maƙale Zak-Shadow, dan in dai muguntar Uncle ɗin nasa biyu ne ya saba da ita a gidan. (Mu'azz ɗan Aunty Ummi ne, mahaifinsa ya rasu tun yana a ciki, dan watan Aunty Ummi ɗin bakwai da aure mijin nata ya rasu, ba kowa bane face yayan Imran, rasuwar ta gigitata dama ahalinsa da su su Zak-Shadow ɗin, har takai ta shiga wani yanayi na ciwo dole aka dawo da ita gida, a haka ta ƙarasa rainon cikin ta haifeshi. Ko bayan haihuwar tasa ma ansha fama da ita kafin ALLAH yasa ta koma dai-dai ta cigaba da shayar da shi, sai dai rainonsa gaba ɗaya Mammah da Mimi ne sukayi shi, har ya kai yaye. Ta jima a gida bata sake wani auren ba kusan shekara biyar dan tama koma karatu, sai da Zak-Shadow yay mata jan ido sannan. Ƴan gidan su Imran basu taɓa nuna kwace Mu'azz ba a hannunsu, sun san yana samun dukkan gata anan gidan, sai dai kuma suma hakan baya hana suyi masa nasu gatan. Dan haka Mu'azz shine jika na farko a gidan tunda har yanzu matar Dada Nabeeha bata haihu ba duk da kuwa tare akai bikinsu da Ummi ɗin a lokacin. Gashi a gidan sabon aurenta har ta sake yara biyu). "Dada! Nima kaga Mammah ta kawo min sabuwar ƙanwa. Sunanta Nimrah". Mu'azz yay maganar yana raba jikinsa dana Dada. Bai jira amsarsa ba ya bar wajen da ɗan gudu. Inda Nimrah take maƙure a tsakanin kujera tunda sukai sallama ta tashi ta buƴa a wajen dan har yanzu bayan Mammah da Mu'azz ɗin taƙi sakin jiki da kowa a gidan. Hannunta ya kamo cike da farin ciki ya ce, "Nina taso ga Dadana da nake baki labari yazo". Kafaɗa Nimrah ta maƙe alamar bazataje ba. Da damuwa a fuskar Mu'azz ya juya inda su Dada suke tsaye har yanzu yana kallon su. "Dada kaji wai bazata zo ba". Maimakon Zak-Shadow ya basu amsa sai ya shiga takawa a nutse har inda suke..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 52_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Dai-dai Nimrah na ƙara matse kanta da kujera ita a dole bata son ganin koma waye. Su dai su Ma'aruff na tsaye suna kallonsu. Zaune ya kai a kujerar hannun dama, ya harɗe ƙafafu cike da ƙasaita ɗaya kan ɗaya, idonsa akan Mu'azz da duk damuwa ta bayyana masa a fuska. "Hy Baby Bird! fito a wajen". Buɗaɗɗoyar muryarsa ta baradan maza dake komai kai tsaye ta saka Nimrah zabura tsaye a lokaci ɗaya, sai dai jikinta rawa yake mata, tana kallonsa ta sake maida kanta ƙasa ta risinar dan bata manta tsawar da yay mata ranar a asibiti ba harta sakata barcin dole, bata tashi farkawa ba sai a gadon ɗakin Mammah. "Fito nan nace". Ya sake faɗa babu wasa. Ganin yanda jikinta ke ƙara ƙarfin rawa Mu'azz ya kama hannunta ya fito da ita yana raɗa mata magana ƙasa-ƙasa. "Nimrah ki daina jin tsoro Dadana ba dukanki zai yi ba". Ita dai batace komai ba, sannan taƙi kallon kowa har Mu'azz ya kawota gaban Dada ya tsayar. Idanu ya ɗan zuba mata, dan harta canja a kwana biyu idanunsa ke gani, kodan kayan da aka saka mata masu ƙyau da tsada ne oho. Wando ne dogo pink mai faɗi kamar falazo, sai ƴar farar t-shirt a ciki an ɗora jacket kalar wandon a sama, kasancewar jacket ɗin a buɗe take daga gaba ya sashi ganin farar ta cikin, daga ganin kayan kasan sabbi ne fil. Ga kanta a tsefe an ɗaure da ribbons, da yake tana da gashi sai yanda Biebah ta raba mata shi biyu yay mata matuƙar ƙyau. Da ƴan ƙauyen Bankaura zasu ganta ba lallai su iya ganeta ba.... Shashshekar kukan data fara ya katse tunaninsa na ƴan sakanni, har Ja'afar ya nufo inda suken domin lallashinta duk da yasan ba lallai ta yarda da shi ba sai ya tsaya cak saboda kamo hannunta da Dada yayi ya matsar kusa da shi sosai. Furucin da yayi cikin sauƙaƙa murya ya saka Mammah dake fitowa daga kitchen dakatawa.. "Ni ne baki son gani a gidan Nimrah?". Kai ta girgiza masa alamar a'a, dan tana da wayonta ras. "To mi kike ma kuka?". "Ni wajen Umma zani". "Miyasa baƙya son nan? Bayan gashi har kin fara zama ƴar gayu." Shiru tayi taƙi magana, shima sai ya zuba mata idanunsa masu tsorata manyan ma balle ita kawai. Ganin haka yasa Mammah ƙarasowa falon tana faɗin, "Dole ne ai haƙuri da wannan yanayin nata dan sai a hankali ne zai barta tunda tayi wayon sanin waɗanda ta baro. Sai kuma kun haɗa da tausasawa idan kuna son ta sake da ku". Dukansu sun gamsu da furucin Mammah ɗin, dan haka Dadan ma ya saki ajiyar zuciya kawai. Sai kuma ya kai hannu ya shafa kan Nimrah cikin sake kwantar da murya fiye da ɗazun ya ce, "Zaki sha alawa?". Kai ta girgiza alamar a'a nan ma. "To mi kike so?". Ma'aruff daya kai gabanta durƙushe ya faɗa shima cike da lallashi. Juyawa tai ta kalleshi, a mamakin kowa kamar jira take cikin sauri ta janye jikinta a kusa da Dada ta koma jikin Ma'aruff ɗin. Baki ta motsa kaɗan alamar akwai abinda take son faɗa. Ganin haka sai Ma'aruff ya kai kunnensa saitin bakin nata alamar ta gaya masa anan. Aiko cikin ɗan rawar murya da raɗa ta ce, "Awara". Murmushi Ma'aruff yay mata, "Kin tabbatar kafi autar Mammah?". Kanta ya jinjina kuwa. Ya sake sakin ƙaramar dariya yana bata hannu alamar su tafa. Ɗan ƙaramin natan ta miƙa masa, yako tafa ɗin. Dariya Mu'azz da Ja'afar keyi, Mammah ma sai tayi murmushi. Shima uban gayyar kauda idanunsa yayi a kansu yana wani ɗan mitsilin smile da in ba kana kallonsa kallon ma na ƙurilla ba bazaka san yayi kayansa ba. Dai-dai nan Ma'aruff ke kama hannun Nimrah suna nufar ƙofa, ya ce, "Mammah, Dada mu mun tafi sayen awara". "Muma ba'a barmu a baya ba". Cewar Ja'afar yana kama hannun Mu'azz shima sukabi bayansu. Mammah ta ce, "To adawo lafiya". Shi dai Zak-Shadow bai tanka ba, suna gama ficewa ma ya zamo a kujerar ya zauna ƙasan lallausan carpet ɗin falon ya fara gaida Mammah ɗin. Amsa masa tayi da kulawa, tare da tambayarsa yaya jikinsa? Yace Alhamdullah baya jin ciwon komai. Dama normal yake sune suka matsa sai sun riƙeshi. Mammah da ke murmurshi ta ce, "Ai na gode musu da suka riƙe kan kuwa. Yanzu dai hankali ya kwanta ko komai ya lafa babu wata matsala acan ko?". "Eh Alhamdullahi babu wata damuwa kam, dan an ƙara ma ninka tsaron jejin gaba ɗaya dama jihar. An kai sabbin sojoji har dubu biyar". "Kai Alhamdullah ai hakan shine dai-dai kam. ALLAH ya ƙara kiyaye gaba. Ya ƙara zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar tamu baki ɗaya. Dan wannan tashin hankalin sam bashi da wani amfani, ko su waye suka ƙirƙireshi basu ƙyauta ba". "Hummm ai Mammah sai ma kinga irin yanda suka kassara ƙauyukan, ga mutane sun tsorata anyi-anyi sunce bazasu cigaba da zama ba. Wasu kuwa bama asan inda suke ba, dan har a jiya da muka shiga jejin ana kan cigaba da zaƙulo mutane da gawarwaki." " Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ALLAH kai mana maganin wannan masifa. ALLAH ya saka musu da gaggawa. Ku kuma UBANGIJI ya cigaba da kare mana ku". "Amin Mammah". Shiru ne ya ɗan biyo baya, kafin ta sauke ajiyar zuciya da cigaba da faɗin, "Kamata yay na barka kaje ka huta, na kuma baka damar yimin bayani akan yarinyar nan da kanka. Sai dai bazan iya wannan dauriyar ba dan tun jiya na gama ƙagauta ka shigo gidan nan dama Saboda yanda matarka ta ɗaga hankalinta. Tunda muka baro wajenka asibiti take rusar kuka lallashin duniya taƙi sauraren kowa. Ƙarshe ma sai da Asthma ɗinta ya tashi aka kira Dr Kulu ta dubata, ban san yaya akai ba kuma sai ga ita Hajiya Nana tazo gidan, ban sani ba ko ƴan uwan nata ne suka kirata anan ta kwana. Ɗazun da safe na shiga na sake duba Nsbeeha ɗin kuma naga jikin nata dai sai a hankali, dan ta saka ma kanta damuwar yarinyar nan da yawa harma na rasa mi hakan ke nufi". "Mammah mi take nufi kuwa banda rashin hankali. Ku ƙyaleta kawai idan ta kashe kanta ba ita ta huta ba". "A'a bama fatan hakan sam. Yanzu dai miye bayani akan yarinya? Ƴar waye?". Bai ɓoye ma Mammah komai ba duk da kuwa akwai abinda sirrika ne na aikinsa. Kafin ya kai ƙarshen labarin fuskar Mammah tayi sharkaf da hawaye tana ta faman sharesu sun gagara tsayawa. Haka shima idanun ƴan mazan sun juye tare da kaɗewa jazur. Cikin share hawaye Mammah tace, "Lallai wannan yarinya abar a tausayama ce. In sha ALLAHU zamu kula da ita za kuma mu tayaka riƙe amana Muhammad. ALLAH ya rayata ya bata ilimi mai albarka da tsahon rayuwa". "Amin Mammah. Wai naji gidan shiru ƴaƴan naki sun koma gidajensu ne halan?". Yay maganar ƙarshe da son kauda mata yanayin da take ciki. Murmurshi kuwa tayi tana sake goge fuskar tata. "Na dai korasu, dan su aka biye musu basuƙi idan kana gidan nan suma su dawo su tare ba. Ammar kuma yana barci wai kansa ke ciwo. Biebah na makaranta". "Shi baya ce jarabawa zasu fara ba shine ya ƙara share wajen zama. Anya Ammar na karatun nan Mammah?". Dariya Mammah tayi har haƙoranta farare tas kamar bana tsohuwa ba na bayyana. Ta ce, "Ni kam ina zan san ko bayayi Muhammad, amma dai nasan magajin Abiy bazai zama rago ba ai". Murmurshi yayi shima mai yalwa. "Shike nan Mammah ai dama ba son laifinsa kike ba. Ni bamma san miyasa aka saka masa sunan nan ba? Ai ni ya kamata a sakawa". Dariya sosai yanzun kam Mammah keyi, ta ce, "Oh kishin ne ya motsa ashe. To duk ya muku wayo dai ya ƙwace ai". "Mun bar masa ya muka iya". Zak-Shadow ya faɗa har yanzu fuskarsa da murmurshi yana shafa kai. Haka yake idan yana a gaban Mammah sai ka ɗauka bashi bane. Zai saki baki sosai suyi hira yana zuba murmurshi. Ita kuma hakan ke sakata nishaɗi dan bata son ta ganshi shiru-shirun nan, sai taga kamar yana a cikin damuwa ne. Tashi tai tana cemasa yaje yay wanka ga abinci ta haɗa masa da kanta, dan taga duk yayi rama". Murmurshi yayi zuciyarsa na sake cika da so da ƙaunar Mammah. Sai kawai ya miƙe yana amsa mata da, "Ai Mammah bari kawai naci tunda lokacin Asr da saura. Dama da yunwa ta na taho coffee ne a ciki na tun safe". "Wannan wasan cin abincin naka na nan har yanzu dai. Bismilah sai ka zauna kaci, amma daka fara zuwa ka duba jikin Nabeeha sannan". Cike da ƴar shagwaɓar da Mammah kawai yake yima a duniyar nan itama sai lokaci-lokaci ya ce, "Please Mammah ki bari dai nacin dan ALLAH". Kanta kawai ta ɗan girgiza tana murmushi. Sannan ta zauna a kujerar daning ɗin daya ja mata baya shima ya ja ya zauna. Ta ɗauki saving spoon danta zuba masa ya amshe da sauri. Dama tasan ba bari zai yi ba, dan shi haka yake, ko tafiya da yana da dama ɗaukarta zai dinga yi da kansa dan karta wahala. Kaɗan ya zuba abincin ya tura gabanta alamar ita yake son ta bashi. Nan ma murmushi kawai tai ta wanke hannunta ta fara ɗiba da hannun tana bashi kamar yanda tasan yafi buƙata. Ai ko sai gashi yaci sosai, duk da dama ta dafa masa abinda tasan yana ci ne domin inganta ƙaƙƙarfan jikinsa da lafiyarsa. Sai da yaci yay nak yasha ruwa yana godema UBANGIJI daya azurtashi da cin sannan itama ya zuba wanda yasan tana ci ya fara bata. A haka masu sayen awara suka dawo suka samesu. Zasu juya su fita dan bama Dadansu damar sakewa da Mammah yace su dawo dan Mammah ɗin ma ta ƙoshi. Bai wani zauna ba ya tattara kayansa Mu'azz ya amsa ya riƙe domin masa rakiya sashensa. Kallon Nimrah da hankalinta ke akan awara yayi lokacin da yake gittasu zai fice, yanda ta duƙufa zai baka tabbacin tana son awaran ne sosai. Bai ce komai ba dai ya fice abinsa kawai..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 53_

__________________

Ina mata ma'abota ado da kwalliya maryam's all-in-one emporium ta tanadar muku Mayafai masu kyau da aminci kama daga plain chiffon veils masu kyau kamar daga Egypt suka sauko🥰 jersey scarfs , beaded and stoning veils, Chantilly, 2D to 10D Turkish veils Dubai d.s Kuma abun farinciki muna bada sari da siyan dai dai ina Kano Ina tura kaya ko'ina cikin Aminci da yardar Allah ga number ta 09064960666

https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt

A cikin duniya ta gayu da burgewa mayafi shine ya ke daukaka ado da aji

Maryam's all-in-one emporium 09064960666 Kano Anan ne gayu yake tarar da qawa.

Ki more hadaddun Mayafan mu da suka hada da Plain chiffon veils (soft & flowy) Italian Chantilly veils (pure elegance Jersey Veils (comfort meets class) Lafaya and many more.

Each piece tells a story of grace, crafted for women who understand beautyin simplicity.🤍

🖤 Premium quality 💛 Affordable luxury 🖤 Available in elegant shades 💛 Delivery 🚚 duk inda kike a fadin duniya

Ba mayafi kawaii kike bukata ba you deserve a statement of class.👑

Wholesale group https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull