Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 27

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 27

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 27: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 27. .........Hinde kawai ya samu a falon tana gyara, cike da…

4,199 words

.........Hinde kawai ya samu a falon tana gyara, cike da girmamawa ta duƙa har ƙasa tana gaishe shi. Amsa mata yay a taƙaice yana wucewa ɗakinsa kai tsaye. Fitowa Amima dake laɓe tayi daga kitchen, dan har zata fito taji ƙamshin turarensa ta koma baya da sauri tana leƙe, sai ko taga shi ɗin ne dan haka ta maƙe har sai da ya shige ta fito. Hinde ta watsama harara, tare da jan tsaki sannan ta wuce bedroom ɗin Auntyn su, dan sauran ƴan uwanta duk suna can harda Mamansu data kwana a gida. "K yanzu kawo tea ɗin ne tun ɗazun sai yanzu Amima?". Sai da ta ballama mai maganar harara, duk da kuwa yayarta ce dan itace ma ke bima Auntynsu Nabeeha gaba ɗaya. Sannan ta ce, "To dan ALLAH ya kike so nayi Aunty Jiddah, ba nazo zan fito ba Dada ya shigo, ke komai mutum yayi bai iya ba". "Okay rashin kunya zaki min dan na miki magana". "Aunty Jidda ba ɗazun na gama gaya muku ba kina kareta ke da Momy, to har Auntyn ma rashin kunya take mata wlhy ko Aunty Ismat". "To fitinannu miya faru kuma?". Dattijuwar matar dake fitowa daga bathroom riƙe da hannun Nabeeha dake ɗaure da towel alamar wanka tai mata ne kome oho musu ta faɗa. A tare duk suka juya suna kallonta, kafin ɗayar budurwar da batace komai ba tun ɗazun ta ajiye wayar hannunta tana bata amsa, "Amima ce kema Aunty Jiddah rashin kunya Momy". "ALLAH dai ya shiryeki Amima, ni ban san yanda zanyi da wannan halin naki ba. Shiyasa ma yaron nan ke ɗaukarku marasa tarbiyya har yana iƙirarin ku bar masa gida, sai kace wani gidan gold.." "Momy dan ALLAH ki daina faɗar haka a gabansu. Ni banga laifin Yaya Haysam ba wlhy, iya ƙoƙari yayi akan yaran nan, shekara nawa kusan nauyinsu a kansa yake, shike nan kuma idan sunyi kuskure bazai tsawatar musu ba..." "Kafin ya ɗauki nauyin su naga ubanku ya ɗauki har nauyin nashi uban ai ko. Sannan shi kansa a yanzu da uwarsa da ubanwa suke taƙamar bada ubanku ba..." "Humm Momy kenan, mudaiyi magana ta gaskiya. Amma ko tarihin Baban Bauchi da Abba ya bamu babu ta inda yake ɗaukar nauyinsa, ya dai ce yana zuwa gidansu yay weekend saboda yana koyon ɗinki a wajen Uncle Zubair. Idan ma bam manta ba Abba yace kaf hidimar aurenku shi yayi har gidansa na kano Baban Bauchi ne ya saya masa shi. Sannan idan ance dan alaƙar dake tsakanin baban bauchi da Abbanmu ne yake musu zai ce Ismat kawai zai riƙe a gidan nan banda Raihana da Amima tunda yasan baida alaƙar komai da su ko...." Takai ƙarshen maganar ranta a ɓace. Dan ita dama bata ƙaunar irin waɗan nan abubuwan, gaba ɗaya halayyarta irin ta Uncle Nasiru ce. Shiyasa ma Momyn bata sonta sosai, dan ko bayan auren Nabeeha da Dada data kwashesu ita komawa tai gida taƙi zama wajenta sai Ismat kawai. Raihana da Amima kuwa ƴaƴan ƙanwar Momy ɗin ne da take can yawon galgal ɗinta bariki ita kuma take riƙo, shine ta tattaro su ta maidoma gidan Nabeeha ɗin dan itama ba zaman ƙasar take ba sosai, kullum tana yawon zuwa Dubai da Chaina ne harkar business acewarta. Cikin ɓacin rai itama Momyn ta buɗe baki zata fara zazzagama Jiddah masifa sallamar Hinde ta katseta, Jiddah da Ismat ne kawai suka amsa, tana rakuɓe daga ƙofa a ɗarare ta ce, "Dada ne yace a faɗa muku zai shigo". "Anji bar nan munafuka". Cewar Amima tana watsa mata harara. Da sauri kuwa ta juya ta tafi. Karo na farko Nabeeha dake zaune shiru a bakin gado da Momyn ta zaunar da ita idannunta sunyi luhu-luhu alamar taci kuka bana wasa ba cikin rawar murya ta ce, "Momy ni dai kar ya shigo, ALLAH bana son ganinsa, kije kawai ki sameshi a falon, dan bazanyi magana da shi ba har sai ya sanar miki alaƙarsa da yarinyar nan, sannan in har bashi da alaƙa da ita sai ya yarda ya maidata inda ya ɗakkota....." Kai Jiddah ta girgiza cike da takaici tana miƙewa idonta akan Nabeeha dake uban kuka kamar ranta zai fita. "Aunty na fahimci wata fitina kawai kike son haddasawa a rayuwar aurenki. Amma ki dinga tuna abinda Abbah ya gaya miki a jiya dai, ki kuma kiyaye biyema sharrin zuciya dan wlhy zata kaiki ta baroki ne a tashar dana sani. Yanzu dan kawai ɗorawa kai masifa daga ganin yarinya kika ɗauki wannan bala'in kika azama kanki? Kota bakinsa bazaki bari kiji ba ma sai kace an faɗa miki yana da alaƙa da ita ne..." "Ke dama ai na jima da sanin ba ƙaunarmu kike da kishin mu ba Jiddah, amma in banda munafuncinki har wani dogon ƙarin bayani ake buƙatar ji, ki kalla baƙar fatar yarinyar irin ta ƴan uwansa ce babu wani banbanci a ciki...." "Ikon ALLAH, to daga fatarta tayi kalar ta ƴan uwansa sai kuma akai mi? Anya kuwa Aunty Nabeeha? Wai ko dai zargi kike son juya al'amarin nan ne ga Yaya Haysam?". "Idan ta zarge shi laifi ne? Kinga Jiddah ki kiyaye ni. Yanzu dan ubanki ko kece mijinki yazo miki da yarinya zuciyarki bazata ɗarsa miki wani abu ba wannan rayuwar da maza suka lalace suka gama maida matansu na gida wawaye? Balle ma sojoji mayun mata.." "Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kai Momy, kema goyon bayan wannan son zuciyar tata zakiyi kenan? Mizai sa ni kuwa dan mijina yazo da yarinya bamma zauna naji ta bakinsa ba na kama zarginsa, ai idan nai hakan na zalunceshi na zalunci kaina. Wlhy ina baku shawara kada ku bari wani ma yaji wannan maganar, idan ba haka ba ke Nabeeha ke zatama ruwa, dan wlhy kinfi kowa sanin waye Yaya Haysam". Daga haka tai ficewata ta bar musu ɗakin zuciyarta na mata zafi matuƙa.

Hango Dada a falon zaune ya sata tsayawa da sauri a ƙofar ɗakin ta share hawayenta sannan ta ƙarasa. Zaune yake cikin kujera zama irin na girma da kamewa. Ganin waya yake sai ta wuce kitchen, babu jimawa ta dawo ɗauke da ruwa da kofi a ƙaramin tray, a coffee table ɗin gefen kujerar da yake ta ajiye, ta duƙa ta buɗe murfin robar ruwan ta zuba a kofin. Zata ajiye a tray ɗin ya miƙo mata hannu alamar ta bashi. Cike da girmamawa ta miƙa masa, yay mata alamar thanks yana cigaba da magana a wayar. Gaba ɗaya sai Jiddah taji zuciyarta tayi nauyi, bawan ALLAH shi da gidansa amma ruwa ma bashi da ƴancin daya shigo azo a bashi. Tana zaune a ƙasan carpet ɗin zuciyarta nata tunane-tunane harya kammala wayar data fahimci akan aiki ne. Sai lokacin ya ƙarasa shanye ruwan data bashin ya ajiye kofin, karo na farko ya ɗan kalleta, "Jidda dama kina ƙasar nan?". Sosai kunya ta kamata, ta ƙara ƙasa da kai tana murmushi. "Ina nan Yaya, dan ALLAH kayi haƙuri nasan ni mai laifi ce, amma wlhy bana sanin sanda kake zuwa ne wani lokacin ma sai ka tafi sannan". "Yanzu dai tun kafin na faɗi laifin har kin kare kanki? To shike nan na haƙura". "Na gode Yaya. Ina yini?". "Lafiya lau. Y kike ya yara da mai gidan naki?". "Duk suna nan lafiya ƙalau Yaya, anjima ma zai zo tare da su su gaisheka". "To ALLAH ya kawo su lafiya". Kafin ta amsa su Ismat suka fito. Sum-sum kamar na ALLAH suka zo kusa da ita suka zauna suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu. Dan haka cikin rawar murya Raihana ta ce, "Dada Momy tace ka shiga". A taƙaice ya ce, "Uhmm". Bai tashi ba bai kuma sake magana ba. Dan haka Jiddah ta miƙe tana faɗin, "Yaya bari naje na gaida Mammah, nima shigowata gidan kenan, na fara zuwa can na samu kana ciki shiyasa ban shiga ba". Guntun murmushi yay mata yana jinjina kansa. Sosai yarinyar halayenta ke burgesa, dan komanta irin na Uncle Nasiru ne. Su Ismat na ganin ta miƙe suma zaram suka miƙe, dama tamkar akan ƙaya suke...

Sai da suka fice da fin mintuna biyar sannan ya tashi. Cikin nutsuwarsa ya isa ƙofar ɗakin Nabeeha, yay sallama suka amsa, koma muce Momy ta amsa tare da bashi izinin shiga sannan ya shigan. Kallo ɗaya yay ma Nabeeha dake zaune a gado da plait a cinyarta tana tsakurar hanta da aka gasa mata. Kauda idanun nasa yay yana kaiwa zaune a kujerar ɗakin, dan Momyn tasu ma na zaune ne a bakin gadon ta ɗayan gefen, kamar gaske ta wani zabga lulluɓi. Danne ɓacin ransa yay ya gaida Momy, ta amsa tana faman sinne kai da jajanta masa tare da taya murnar cin nasara. Shi dai a taƙaice ya amsa mata da ya gode. Bai ce ya mai jiki ba bai kuma yima Nabeeha magana ba. Dan haka Momy ta zungureta kaɗan da mata alamar ta gaisheshi. Ita ko sai ta wani tura baki gaba da ɓata fuska kamar zata saki kuka. Sake zungurinta Momy tayi, sannan tana cika baki da iska ta ce, "Ina yini". "Lafiya". Ya amsa a taƙaice. Wani irin ƙona mata rai yanda ya amsa ɗin yayi, hakama Momy taji haushi, a ranta tace, shegen yaro mai girman kan tsiya. A fili kam cike da bariki tai murmushi. Ta ce, "Ai tun jiya muke saka ran shigowar ka gidan dan nima da yamma nazo saboda yanda jikin nata yayi tsanani. Amma yau dai Alhamdullahi tunda gashi har ana cin abinci". "Waye ba lafiya?". A yanda yay tambayar kansa tsaye sai da Momy da Nabeeha suka kalla juna. Baki sake Momyn ta ce, "Haysam Nabeeha mana. Shin baka san bata da lafiya bane? Shekaran jiya tunda suka baro wajenka a asibiti da ƙyar ta iya kawo kanta gida". Maimakon ya nuna jimami da tambayar miya faru sai cewa yay, "ALLAH ya ƙara lafiya". Daga haka ya miƙe abinsa. Batare daya sake kallon kowannensu ba ya fice abinsa. "Babbar bala'i, amma yau na ƙara yarda yaron nan tantirin riƙaƙƙen ɗan iska ne...." Kuka Nabeeha ta fashe da shi tana mai yin jifa da plate ɗin abincinta, zata fara haukan faffasa abubuwan nata Momyn ta riƙeta, sai kawai ta faɗa jikinta ta fashe da kuka.........✍🏼

🤣Gaskiya nima nace baka da M Zak...🏃🏼‍♀️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 54_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃. __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Cikin kuka Nabeeha ta ce, "Ni wlhy Momy bazan zauna a gidan nan ba. Dama na gaya miki zai iya aikata fiye da haka dan kar a tuhumesa kan yarinyar nan. Ni kawai ki tashi mu tafi bazan zauna ba". "Ke matsalata da ke sakarai ce. Idan kin tafi ina zaki je? Miye kuma amfanin tafiyar muda muke fatan jin gaskiya. Tashi zakiyi ki bishi can tunda ita uwar tasa tsoron tambayarsa wacece yarinyar take ai dole ke ki tambaya ya faɗa miki idan yana son zaman lafiya a gidansa. Yanzun ma ai munafunci ya hanata kiransa tun yana can ta sanar masa baki da lafiya". "Momy wlh...." "Bana son jin komai tashi ki wuce kar ma ya koma can a hure masa kunne. Duk da shima shegen kansa ne". Badan taso ba ta miƙe, sai dai itama zuciyarta a ƙagauce take da son jin wacece yarinyar, dan tasan shi ɗin ɗan kai tsaye ne baya ƙarya, ba kuma ya shakkar faɗar abinda ke ransa game da ko miye a gaban ko waye. Dan ko Mammah tasan ko abu baida daɗin faɗa in dai gaskiya ce baya fasa faɗa a gabanta sai dai zai tausasa harshe wajen faɗar kawai. Babu ko kunyar tunawa da ƙanenta dake gidan da ƴar rigar jikinta mara nauyi iya gwiwa ta fita a ɗakin, kanta ko ɗan kwali babu sai slippers a ƙafarta da wayarta kawai...

<<°>><<°>><<°>>

"Miyasa kuka buƙaci gani na anan? Su waye ku?". Mutumin ya faɗa fuska a kumbure yana kallon mutanen dake baƙin fuska a idanunsa, hasali ma basa kama da ƴan ƙasarsa tako ina. Murmurshi makirci Raven yayi tare da kallon Scythe da Viper, kai suka jinjina masa alamar yayi magana. Shima nasa kan ya jinjina musu sai kuma ya sake maida dubansa ga mutumin. Cikin harshen turanci ya ce, "Sir! Munzo gareka ne domin girmamawa da wani aiki na musamman da muke da tabbacin zai taimakawa tafiyarka. Ni dai sunan Scythe, abokaina Viper da Raven. Kamar yanda na faɗa maka muna tafe da tallar haja mai girma da zata amfane ka ƙwarai da gaske". Ya kai ƙarshen maganar yana ma Raven nuni da akwatin kusa da shi. Turo masa akwatin yayi, yasa hannu ya ƙarasa matsoshi gabansa tare da buɗewa bayan ya saka wasu lambobin sirri da zasu iya kaiwa goma. Koda ya buɗe sai ya ɗan zubawa abinda ke ciki ido ya saki murmurshi, kafin ya juya akwatin yana kallon mutumin. Shima akwatin ya zuba ma ido na sakanni, sai kuma ya kalli Scythe ɗin cikin waro idanu sosai waje. Janyewa yay a lokaci guda, tare da kai hannu cikin akwatin Scythe ya janye da sauri yana murmurshin mugunta. "Ranka ya daɗe ita haja ai ba'a taɓata sai da yarjejeniyar ciniki. Kar kayi gaggawa, idan ka bada haɗin kai wannan shaidar gani da ido ce kawai akwai babbar ganima a ƙasa". Yawu sosai ya haɗiya, idanunsa har yanzu a waje ya furta, "Kar kaga laifina, wannan kayan alatun ba'a sakacin yi musu abari ya huce saboda gujema rabon wani". Dariya sukayi a tare, Raven da Viper suka tafa. Shi ko Scythe ya ce, "Haba harda ku manyan ƙasa kuma sir!". Kai tsaye cikin watsa hannu da sakewa ya ce, "Ai mune mukafi buƙatarsu ma abokina, dan sune ƙarfin namu kuma barazanarmu ga talaka. Daga ina wannan tagomashin arziƙin ya fito". "Kwantar da hankalinka komai mai sauƙi ne sir, wannan dai lagwadar a wannan ƙasar taku ne, sai dai ba a wannan yankin naku ba. Mun kuma jima muna hutawa da wannan hajar, zuwa yanzu ma yaci ace mun ƙoshi, sai dai kasan ita ɗanyar fata bata fashewa, sannan babba da jaka baya rasa filin sakawa koda a zahiri ya ƙoshi. Bari na taƙaita maka bayanin, wannan kayan dai da kake gani daga wancan yankin da aketa bata kashi ake samo su, na baka a buɗe kawai akansu ne ma akewa ƙasa fenti da jini..." "What!". "Magana ta gaskiya kenan sir! Yarda da kai kuma yasa mu tunanin dakkoka dama ire-iren ka dan aci tagomashin arziƙin da ku. Hakan kuma bazai yiwu ba sai kun bamu haɗin kan sakace guntun naman daya tsaya mana a tsakankanin haƙora ya hanamu cigaba da tauna sauran tsokoki balle muje ga tauna ƙashi. Ina fatan ka fahimce ni". "Da dai zaka ƙara bani a buɗe dana fahimta ɗin". Raven ne ya amshe da faɗin, "Yana magana ne akan Iliya ɗan mai ƙarfin ku, dan duk ƙoƙarin ruwa na bin hanyar wucewarsa ya kafa ya tsare da ganuwar dutsina data ƙarfe ya tilasta shi bin katanga ya tsaya cak. Kaga kuwa idan har ana son ya wuce kar yay hanƙoron da zai iya shafe ganuwar yabi ta sama dole a kada ganuwar tun yana a iya rabinta a bashi hanyarsa, sai kaga kowa ya zauna lafiya batare da ambaliyar da zata iya cinye ƙasa baki ɗaya ba." Cikin jinjina kai da murmurshi ya ce, "Babbar magana. Anya kun san ƙarfin da ILIYA ƊAN MAI ƘARFIN nan keda shi a ƙasa da saman ƙasar nan kuwa? Musamman a wannan gaɓar da kowa ke kallonsa kamar commandor ɗin yaƙin duniya na biyu". "Idan har ƙarfin sama zai raunana akan bashi garkuwa hura masa kai na ƙasa ai tamkar ƴan tsaki suke, maybe ma da an biya wasu da kuɗaɗe zasu koma masa aturen ƙasa da jifar dutse tamkar sunga sheɗan". "Eh kaima kazo da magana. Sai dai matsalar taya za'ai yekuwar saman ta dunƙule a waje ɗaya dan in har zata yiwu tafiya sai an taɓa kowane kashi a tsakanin kayan haɗin miya in har ana son miyar tai zaƙi da daɗin da za'a iya cin kowane abinci da ita". "Wanan mai sauƙi ne, dan mun shirya takardun gayyata kamar irin takan nan, sannan muna barar jagora daga gareka zuwa wasu". "In dai haka ne muna buƙatar gaggawa, dan wannan gaɓa ce da zamu iya kama zaki a tsakiyar farautarsa. In ba haka ba samun wata damar zai iya yin wuya. Amma a wannan wasan da ko huce gajiya bai gama yi ba zamu iya amfani da SAWUN GIWA SAI YA ƁADDA NA RAƘUMI batare da duniya ta fahimta ba". "Wannan shine shirin mu dama, shiyyasa muka yunƙuro da wuri ba sanya. Dan kuwa hatta bayanan sirri da guntayen videos munada a hannu da zamu iya ƙulla gadar zaren da in dai shi ba aljani bane dole ya faɗa ciki. Albishir na ƙarshe da zamu maka shine har a cikin gidansa muna da babban harsashin da ake kira tsinka jini. Kuma Senior ɗinsa ne tun a makaranta, na tabbatar ya masa irin sanin da muke buƙata". "Eh lallai na yarda yanzu kam tafiyar ta gaske ce. Dan mutumin nan da kuke gani hatsabibancinsa ya wuce tunani. Ni shaida ne a zaman meeting da muka taɓa yi da shi". "Mune zamu baka labari sir, amma zuwa yanzu zai gane SARKIN YAWA YAFI SARKIN ƘARFI AI". "Wannan gaskiya ne".

>•<%>•<%>•<%>•<

Tunda ya baro ɗakin nata bedroom ɗinsa ya dawo, aikin dake ransa ya baje takardu da laptop yana cigaba da yi a study table ɗin bedroom ɗinsa. Sai waya da Imran yay kiransa ya ajiye a table ɗin ya saka a hansfree. Badan sanin halinsa ba ko sallama bazatai ba zata shigo. Amma dai ta daure tayin. Duk da ya jita bai amsa ba bai kuma juya ba yana cigaba da maganarsa da Imran ne da yin typing a laptop, da alama maganar tasu yake rubutawa. Dan dai-dai tana isowa inda yaken yake faɗin, "Lallai akwai banbanci tsakanin hotunan biyu, dan shi yafi na farkon duhun fata". Daga can Imran ya amsa da, "To kenan twins ne ko mi? Idan kuma har hakan ne taya za'ai su canja kansu na tsawon shekaru batare da an gane ba, tunda dole ɗaya ne a cikinsu sojan". Iska mai zafi Zak-Shadow ya furzar, sai kuma ya cije baki da ƙarfi, kai tsaye ya ce, "Ka kira Dabo yanzun nan, daga nan zuwa 24h ina son cikakken bayani akan family ɗinsa." "Amma ba Dabo ɗin bane ke bibiyar motsinsa?". "No. Yusuf ne". "Okay tom ba damuwa. Zuwa anjima nima zan shigo gidan." "Sai ka zo". Ya faɗa yana yanke kiran. Ganin ya matsar da wayar gefe ya jawo wasu takardu zai cigaba da abinda yake kamar ma bai ganta ba ta matsa da sauri gabansa tai ƙoƙarin tsayawa jikin table ɗin duk da wajen ya mata kaɗan. Shiru yayi kamar bazai kulata ba, sai kuma ya ɗago idanunsa da babu wasa a cikinsu ya zuba mata fuska a tsuke. Ganin kallon da yake mata yasa zuciyarta fara rawa, sai hawaye shar-shar suka fara tsiyaya. Kauda idanun yayi, cikin halin ko'in kula ya ce, "Tashi min anan". Maimakon matsawar kamar yanda ya bata umarni sai kawai ta sake ɓarkewa da kuka. "Ai dama nasan ba ƙaunata kake ba, su Abbane suka cusa maka ni, dan kaga ina sonka shiyasa kake min duk wannan wulaƙancin kuma. Duk randa baƙin cikinka ya kashe ni sai ka huta, koma ka kasheni ka huta ɗin yanzu". Haɓarsa ya tallafe kawai yana kallonta, yanda yay mata zuru sai ta sake jin tunzura. Juyawa tai a fusace zata watsar masa da kayan study table ɗin karo na farko a tsawace ya furta, "Karma ki fara wannan shashancin naki anan. Ga ƙofar da kika fito nan, koma can kije kiyi a ɗakin ki stupid kawai". Sosai ta gama firgicewa dan tasan halinsa idan yay fushi baida sauƙi. A hakan ma yaya lafiyar giwa. Ƙasa ta zube kawai ta sake ƙarfin kukanta sai kace wata mai aljanu, nan ko ƙalau take abinda Momynta ta shirya mata tayi kenan. Tsam ya miƙe da nufin bar mata ɗakin kuwa, caraf ta kama ƙafafunsa ta riƙe. "Dan ALLAH ka tausaya min ka gaya min alaƙarka da yarinyar nan, kace min ba ƴarka bace baka da alaƙa da ita, in ba hakaba wlhy mutuwa zanyi......" Dummm kan Zak-Shadow ya bayar a karo na farko. Zuciyarsa tai wani irin tsayawar sakan biyu kafin ta harba da ƙarfi a ƙirjinsa. (Ƴarsa kuma) Ya ambata a ƙasan zuciyar tasa yana kallon Nabeeha dake cigaba da kuka. Da ƙyar ya iya furta, "Nabeeha kina da hankali kuwa? Wace irin magana ce wannan?". Zata sake magana yay wani irin hankaɗeta gefe, tare da nuna mata ƙofa ya ce, "Get out of my room, before I lose my control". Cikin nuna ƙarfin hali ta buɗe baki zatatai magana. A mutuƙar tsawace data saka jikinta fara rawa ya ce, "I said get out....." Da sauri ta miƙe, dan idanunsa sun fara birkicewar tasu irin yanda take matuƙar tsoron ganinsa da zargin ma wani lokacin yana shan ƙwaya. Gudu-gudu sauri-sauri ta nufi ƙofa har tana neman faɗuwa. Shi ko dake binta da kallo wani irin runtse idanu yayi da masifar ƙarfi. Dan bai taɓa jin abinda ya kaɗa masa zuciya a tashin farko ba irin furucinta. Shi yarinyar nan zata kalla tsakkiyar idanunsa ta dangantashi da zina zai ce komi ma take nufi? Tunda ai tasan dai bayan ita baida wata matar a wannan duniyar da har zata ce wai yarinyar ƴarsa ce, ƴa fa? To ana sayo ƴaƴa a kasuwa ne?. Gorar ruwa dake a saman table ɗin ya fisga tare da ɓalle murfin ya hau kwankwaɗa, sai da ya shanye gaba ɗaya yay wurgi da gorar ya maida bayansa da kansa jikin kujerar ya kwantar yana mai lumshe ido. Wannan fa shine abu goma da ashirin...........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 55_

__________________

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LkEgiP5qOEo9YDYjaeZLLc?mode=ems_wa_t✍️✍️ Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed yar mutan Chadian traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products at home my people bazamafa a kwai zafafan promo damukeyi in Sha allahu zuwa on 15 zamugama sannan gareku Yan Kano free ne kayanki zasuzo miki amma fa karyazo bayan mungama promo kuce kyauta ne aa zakibiya kudi nagode takuce yar mutan Chadian mai gyaran ciki dawaje 💃💃 please banda maza,❌maza❌ In kinada matsala wadda zamu iya taimaka miki 09065504546 Ga PRODUCTS DINMU KAMAR HAKA MAGANIN SANYI TSUMIN BOM MADARAR TABAJE GORON TULA SYRUP ZUMAR SHADAMATSIN GARIN YAUKAYAUKA EMERGENCY GARIN KINFI KAZA DADI SIRRIN MALLAKAR KASA SIRRAN GIDANKI DAHUWAR KAZA DAHUWAR CICCIBI DAHUWAR YAN SHILA HMM BAZASU IRGUBA INA GODIYA SOSAI MY PEOPLE 🥰🥰

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull