Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 28

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 28

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 28: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 28. .........Da mugun ƙarfi Colonel ya buga desk ɗinsa yana mai…

4,284 words

.........Da mugun ƙarfi Colonel ya buga desk ɗinsa yana mai zazzaro idanu da ture takardun daya gama karantawa, cikin ƙaraji ya furta, "Lt. Col. Garba! Kana da hankali kuwa zaka kawoma mutane wannan maganar banzar. Ko gaskiya ne maganar da ake faɗa akan kana kishi da Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed ne?". "I'm sorry sir! Wannan shati faɗi na mutane ne kawai da son haddasa fitina. Dan kawai abinda ya faru tsakanina da shi a NDA na ƙuruciya sai a kalli abu mai muhimmanci irin wannan matsayin rashin jituwa. Sir nifa soja ne, yana da ƙyau na fargar da hukumata ɓarna idan naga zata afku balle ma irin wannan. Sannan ban kawo shi gareka kai tsaye ba sai da na tabbatar, ina kuma da shaidu sosai da suma suka gani kuma akayi a gabansu a cikin yaransa". Idanu kawai Colonel Galadima ya zubama Lt. Col Garba. Sai kuma ya sake jawo takardun yana sake dubawa ɗaya bayan ɗaya. Sosai zuciyar ke rawa, dan kuwa duk wanda ya kwana ya tashi yasan ƙwazo da gaskiyar Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu, sai dai isa cewa zai yi rejecting ɗin wannan report ɗin batare da bincike ba. Karo na farko ya zari tissue ya goge gumin daya tsatstsafo masa a goshi. Cikin bada umarni yace da Lt. Col. Garba, "Okay zaka iya tafiya". Ba haka Lt. Col. Garba yaso ba, amma sai ya miƙe cikin nuna jimami ya fita a office ɗin. Koda ya fita Colonel yafi minti sha biyar yana sake duba report ɗin kafin ya haƙura ya miƙe da takardun a hannu zuwa office ɗin Brigadier General, dan bashi da hurumin cigaba da riƙe report ɗin a wajensa dole ya kaisa sama saboda maganar babba ce sosai. Bayan an bashi izinin shiga ya ƙame tare da salute duk a lokaci guda. Brigadier General Abraham Yohana daketa rubuce-rubuce batare daya ɗago ba yay masa nuni da kujera. Zama Colonel yayi, cike da girmamawa ya ajiye file ɗin hannunsa gaban Brigadier General. "Sir wata babbar magana ce da ake buƙatar dubata da gaggawa". Karo na farko Brigadier General ya ɗago yana kallonsa, sai kuma ya maida kansa ga rubutunsa a taƙaice ya ce, "Mike faruwa Colonel Galadima?". "Report ne muka samu akan Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu game da wannan rikicin daya jagoranta." Batare daya ɗago ba ya ce, "Ba ɗazun aka gama meeting da ministan tsaro a fadar shugaban ƙasa ba akan karrama shi, shi da duk wanda akai yaƙi da bizne waɗanda aka rasa. Kuma harda kai ka sani". "Hakane sir! Amma fa al'amarin na neman canjawa ne. Dan wannan report ɗin na nuni da Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu da hannunsa akan shirya komai daya faru, hasalima shugaban ƴan ta'addan dake hannun jami'an bincike ya tabbatar da shima yana cikin ogans......" A fusace Brigadier General ya katse Colonel. "Wace kalar banzar magana ce wannan. Haysam!? Haysam! Dai? Za'ace yana tare da ƴan ta'adda?". "Wlhy sir nima abin ya girgizani matuƙa. Amma ka duba ka ga report ɗin dai. An kawo shi ne tun daga jihar da abin ya faru. Kuma banan kawai ba har gidan gwamnati ya isa". File ɗin Brigadier General ya ɗauka ya shiga dubawa. Cikin ɓacin rai yay wurgi da takardar yana faɗin, "Impossible. Har abada Haysam bazai taɓa koda ɗagama ƴan ta'adda ƙafa ba balle haɗa hannu da su. Wannan ma zancen banza ne, ba kuma Haysam ake son ɓatama suna ba hukumar mu ake son ɓatama suna". Shi kansa Colonel Galadima abinda zuciyarsa ke bashi kenan. Amma harga ALLAH zuciyarsa ta tsorata, dan ya fahimci wannan shiri ne mai ƙarfi da girma. Musamman idan akai dubi da yanda aka shirya report ɗin kansa..

Cikin ƙanƙanin lokaci takardar ta gama zagaye Headquarter ɗin. Babu shiri manyan suka haɗa meeting na gaggawa. Sai dai ko farawa basuyi ba kira ya samu General na kuma gaggawa daga ministan tsaro bisa umarnin shugaban ƙasa dake son ganinsa da gaggawa a gidan gwamnati cikin sa'oi biyu kawai. Dole yabar nasu meeting ɗin akan Lieutenant General ya jagoranta. Shi kuma ya wuce amsa kiran shugaban ƙasar......

<><><><><><><>

Yanda Nabeeha ke ribzar kuka ba ƙaramin sake zafafa zuciyar Mammah take ba. Amma ta danne cikin bada umarni tace ma Ma'aruff. "Kira min Dadan ku". Sai da ya watsama Nabeeha da Momynta harara sannan ya miƙe. Shima Ja'afar dake a wuya miƙewar yayi. Ammar kam da shigowar shi falon kenan baiji maganganun da Momyn Nabeeha ta faɗa ba tsaye yay daga bakin kofa kawai yana kallon Nabeeha ɗin. Har Ma'aruff na neman bugeshi. Kauce masa yay ya fita. Ja'afar ma ya shiga kitchen yana kai waya a kunnensa. Bayan gaisuwa ya zayyanema Uncle Nasiru daya kira komai dake shirin faruwa a gidan. Ba ƙaramin tashi hankalin Uncle Nasiru yayi ba da jin ɓacin rai, cikin sauri yace gashi nan zuwa gidan. (Shima dai Uncle Nasiru yanzu a nan Abuja yake, dan anan yake aiki, kuma anan cikin anguwar yake zaune dan da ƙoƙarin Zak-Shadow ma ya samu filin daya gina gidan, dan haka basu da nisa da su sosai). Ja'afar na yanke wayar ya kira Imran shima. Shima rai ɓace ya ce, "What! Yarinyar nan nada hankali kuwa?". "Yaya dama ai mahaukaciyar ce kune baku fahimta ba. Wlhy badan mutuncin Uncle Nasiru ba yau sai na fasa mata baki na karyar ƙafar uwar tata". "No. Ba wanda ya aikeka kai kuma. Gani nan zuwa gidan nima". Daga haka ya yanke kiran...

A lokacin da can zaman meetings ya ɓarke akan Zak-Shadow da alama nan wata sabuwar ƙurar ke shirin tashi saboda baƙin kishin matarsa Nabeeha da rashin hankalin uwarta dake bata goyon baya saboda wani burinta na banza da wofi. Kasancewar Ma'aruff ya iske Dadan su na wanka sai da ya jirashi, dan haka kusan lokaci ɗaya suka shigo falon Mammah da Uncle Nasiru. Suna zama Imran na shigowa. A can kuwa Biebah dake kitchen tana aiki taji komai tuni ta fice can baya tana kuka ta kira Aunty Ummi da Aunty Mommy da ma Aunty Mimi ta gaya musu abinda ke shirin faruwa. Ai tuni suma kowa ya ɗakko hanyar zuwa gidan. Yo ubanwa ya isa taɓa musu Dada a zauna lafiya ba'atada yaƙin duniya na uku ba. Ai wlhy Mammah ce kawai keda wannan isar, itama dan uwa ce babu yanda zasuyi da ita. Duk wannan abin dake faruwa Bilal baya gidan, ya tafi saka Nimrah a islamiyyar su Mu'azz, boko ma in sha ALLAHU gobe-gobe za'a kaita. Dan tunda Mammah ta gama jin komai a wajen Zak-Shadow ta yanke shawarar a yau ɗin nan za'a saka Nimrah islamiyya gobe boko ko hakan zai sa ta saki jikinta. Dama gashi anyi sa'a cikin satin nan aka koma hutu kuma zangon farko ne.

Tunda Zak-Shadow ya shigo falon yaji zuciyarsa ta sake zuwa wuya. Da ƙyar ya iya daurewa ya gaida Uncle Nasiru ya samu kujera ya zauna, tare da jingina bayansa ya lumshe idanunsa kawai yana sauraren zagin da Uncle Nasiru kema Nabeeha da ke neman komawa faɗa tsakaninsa da Momynta data saka baki. Sai da Mammah ta basu haƙuri da nuna musu kuskuren abin kunyar da suke neman yi agaban yara sannan sukai shiru kowa na huci. Dai-dai nan Imran ya shigo da sallama shima. Kai tsaye ya ƙaraso falon dan shima ɗan gida ne, har bedroom ɗin Mammah shiga yake. Yanzu ma sai da ya gaida su ita da Uncle Nasiru da Momyn Nabeeha su Ma'aruff suka gaisheshi shima. Da ido Mammah taima su Ma'aruff ɗin umarnin fita a falon. Badan sun so hakan ba suka fita. Amma sun san duk rintsi Mammah bata maganar data shafi Dada a gabansu in har bata farin ciki bace, amma a ganinsu wannan tasha banban ai, sai dai duk da haka an kora su waje. Bayan gama fitarsu da rufe ƙofa suka koma jikin windows suka maƙe, dan sun fi son jin komai yanda zasu ci ƙaniyar Nabeeha da lasisi. Mammah da bata san suna laɓe ba kai tsaye ta maida kallonta ga Zak-Shadow. "Muhammad". Ta kira sunansa kamar yanda ta saba. Idanunsa da suka rine ya buɗe, sai kuma ya gyara zamansa cike da girmamawa ya amsa mata. "Miya haɗaka da matarka haka da zafi har kake zaginta da korota daga ɗakinka cewar zaka daketa". A karo na biyu ya ɗan juya ya kalli sashen da Nabeeha take manne da Momynta, sai kuma ya dawo da kallonsa ga Mammah. Ƙaramin murmurshin takaici yayi, mamakin wannan ƙarya ta Nabeeha na cizonsa, amma sai ya danne, cike da girmamawa ya ce, "Tazo min da wata maganar banza ne akan yarinyar nan da kuka taho da ita daga asibiti Mammah". "A gani na ai bayani ya kamata kai mata ba kakkausan lafazi ba....." "Miye wani kakkausan lafazi zagi dai." Momyn Nabeeha ta katse Mammah a hasale. "ALLAH kika ƙara magana sai kin bar falon nan". Cewar Uncle Nasiru yana nuna Momyn Nabeeha. Itama a hasale ta ce, "To ubana". "Dan ALLAH kuyi haƙuri Yaya". Mammah ta faɗa cikin tausasawa, sai kuma ta cigaba da faɗin, "Muhammad ita yarinyar wacece a wajenka? Ƴar waye? Miyasa kazo da ita nan?". Ta jera masa tambayoyin duk da kuwa ita ya mata bayanin komai ɗazun.. Iska ya furzar mai ɗacin gaske, dan haka Imran yay saurin faɗin, "Mammah bara nai muku bayanin komai". "Ai bakai aka tambaya ba". Momyn Nabeeha ta faɗa tana hararar Imran. A hasale Uncle Nasiru ya ce, "Shine kuma zai bada amsa, kai Imrana faɗi muna jinka. Kai Imran ya jinjina ma Uncle Nasiru yana gyara zama. Yayin da a jikin Windows su Ja'afar kejin kamar su tsallako falon su daki bakin Momyn Nabeeha, dan zuwa yanzu suma su Aunty Ummi sun iso, tuni kuma su Ma'aruff sun musu bayanin komai dan haka suka nema wajen maƙewa suma ayi komai da su. "Wannan yarinya sunanta Naja'atu, amma iyayenta na kiranta Nimrah saboda sunan kakarta taci..........." tsaf Imran ya zayyane musu komai, sai dai banda ainahin halin da mahaifinta ke ciki, hasalima kamar yanda Umma ta roƙa sai ya sanar musu mahaifinta ya rasu a rikicin kamar mahaifiyar tata. Ba ƙaramin daɗin hakan da yayi Zak-Shadow da Mammah sukaji ba. Dan ita Mammah komai sai da Dadan ya sanar mata bai ɓoye ba. Cikin damuwa sosai Uncle Nasiru ke jimanta al'amarin, da tsakanin jin tausayin Nimrah a ransa. Amma a mamakin kowa sai ji sukai Nabeeha ta ce, "Wlhy ban yarda ba, Imran kai dama ai munafuki ne nasani, tun ba yau ba nasan ba ƙaunata kake yi ba. Banda ma rainin hankali in har da gaskene abinda ka faɗa ɗin ai ba ita kaɗai bace aka kashewa iyaye, miyasa su sauran yaran kuka barsu can ita kuka taho da ita nan. Ba sai ku barta acan camp ɗin ba kamar sauran. Ni wannan labarin ƙanzon kuregen bazan taɓa yarda da shi ba, dan dama na jima ina zargin ana cin amanata, idan har ana son na yarda ba ƴarsa bace sai dai muje asibiti ai musu gwaji shi da ita....." A matuƙar fusace Zak-Shadow ya miƙe, cikin buɗaɗɗiyar muryarsa dake fita da kaushi da ɗaci ya nuna Nabeeha, "Baki isa ba, kinyi kaɗan wlhy. Kije labarin ƙaryar aka baki, kuma ana cin amanar taki kiyi duk abinda zakiyi, dan ke baki isa sakani yin abinda banyi niyya ba wawiya kawai". A fusacen itama ta miƙe tana kuka, kai da ka ganta kasan kishi ne da zuga suka rufe idannunta, itama cikin ƙaraji ta ce, "To wlhy kuwa sai dai mu rabu, dan nima baka isa na cigaba da zama da kai ba. Jaka ka ɗauke ni ko dabba?, shekara da shekaru ina fama da kai muje muga likita akan matsalar haihuwa amma kaƙi saboda kasan mi kake shiryawa, kaje ka ajiye wata ƴar iska a jeji kana dadiro da ita ku haihu dan yanzu an kasheta ka ɗakko ƴar ka kawo gida mu shaƙi iska ɗaya da ita, mu kwanta muhalli ɗaya da it....." Tasss! Tasss!!! Kake jin saukar mari har biyu a kan fuskarta irin mai gigitarwar nan, ai ko ƙara ta ƙwalla, dai-dai da miƙewar Momyn ta ta riƙeta tana shiga tsakkaninta da Uncle Nasiru mai marin........✍🏼

Gaskiya ƙawata Nabeeha baki ƙyauta ba, ya zaki mana haka kuma😳😏.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 56_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t

UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1F __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........."Miyasa zaka mareta? Naga akan gaskiyata take dai ai? Sai a daki yarinya a hanata kuka. Idan yasan yana da gaskiyar mizai sa yaƙi yarda suje suyi gwajin?". Cikin kuka Nabeeha ta ce, "Momy ki barshi ya kasheni, Abba ka kasheni, dama mun san ai ba son mu kake ba yanzu, shi da yay laifin ka kasa yimasa magana saboda kana tsoronsa sai ni, sai ni da nake da gaskiyata za'a tauye ni......" Wani marin ya ƙara kawo mata, dan yama kasa magana saboda abinda ya tsaya masa a maƙoshi. Da sauri Momyn tata dai ta sake tarewa. "Wlhy bazaka sake dukanta ba". Mammah da al'amarin ya girmi kanta ma sai yanzu ta iya ɗaga baki da ƙyar tace ma Uncle Nasiru, "Dan ALLAH Yaya kayi haƙuri ya isa hakan, duka ba shine mafita ba, ku barta ta huta ta huce dan yanzu shaiɗan yayi tasiri a zuciyarta. Sannan kuma tunda gwajin take so ni zan masa magana zaije suyi, ba shike nan sai a zauna lafiya ko". A gatsine Momynta ta ce, "Da dai yafi kam". Taja hannunta suka nufi ƙofa. Gagara sake yin magana kowa yayi a falon, dama Zak-Shadow tunda ya gama yaɓa mata zancen farko ya koma can dining ya zauna, yaƙi fita ne dan kar ya ɓatama Mammah rai, Uncle Nasiru kuma yaga kamar ya raina shi, dan kallon uba yake masa. Amma ya tabbatar ya cigaba da zama inda Nabeeha take zai iya fara kai mata duka a karo na farko na rayuwarsu, shiyasa ya zaɓi komawa can ya zauna ɗin... Salatin da Mammah ta saki ita da Imran a lokaci guda ya sashi buɗe idanunsa ya kallo falon, ai baima San ya miƙe ba da sauri ganin Imran ya taro Uncle Nasiru alamar faɗuwa zai yi. Ganin Uncle Nasirun na neman sumewa ya ƙarɓi ruwan da Mammah ta miƙo da sauri, ɓalle murfin yay kawai ya zuba a hannu yana kaiwa duƙe shima ya shafa a fuskar Uncle Nasiru. Nannauyan numfashi ya kawo mai ƙarfi, sai kuma ga hawaye.... "Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, dan ALLAH Yaya ka kwantar da hankalinka. Wannan fa ba wani abun tashin hankali bane ba. Komai mai sauƙi ne, tunda ma ALLAH ya kawomu zamanin da ake gwaje-gwajen sai a godema UBANGIJI ko. A kuma je ayi dan itama ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali." "A'isha bazai je ba". "A'a dan ALLAH Yaya kada kace haka, ita masalaha a rayuwa babu abinda ya kaita daɗi da sauƙi balle ma a rayuwa irin ta aure, itama yana da ƙyau a bata hakkinta kodan cire zargi, kasan bazan iya bijirema umarninka ba, amma dan ALLAH ko sau ɗaya ne ka bani damar nan na roƙe ka". Yunƙurawa yay zai tashi, Zak-Shadow da Imran suka taimaka masa. A kujera suka maida shi, yay shiru tsawon lokaci, wata irin nadamar auren Momyn Nabeeha yake ji da zama da ita ba tsawon shekaru, wlhy badan ƴar uwarsa bace jininsa mafi kusa da har nadamar haɗa zuri'a yayi da ita. Matar nan itace babban ƙalubalensa na rayuwa, yasha wahala a hannunta a zamansu na turai, dan gaba ɗaya ta fanɗare masa ta saka yaransu fanɗare masa. Shiyasa ma ya yanke shawarar dawowa gida Nigeria. Ko batun saƙo da yake turama su Mammah ɗin da bai zuwa daga baya abokin nashi yazo ya gaya masa gaskiyar itace ta hana, ta dinga amsa tana rabawa uku ta bashi kaso ɗaya ta ɗauki biyu... Imran ne ya katse masa tunani da faɗin, "Uncle kayi haƙuri nima ina bayan Mammah, ka bari aje ai gwajin kawai kodan samun zaman lafiya da cire zargi, itama yarinyar kaga zata rayu cikin salama". "Imrana....." "Dan ALLAH Uncle". Imran ya sake katsesa. Kallon Zak-Shadow Uncle Nasiru ya ɗanyi, sai tausayinsa ya sake kama shi da kunyarsa mai tsanani, dan tabbas ya cutar da shi da har ya bari aka aura masa Nabeeha bayan yasan bata da isashiyar tarbiyya. Tabbas Haysam magajin Abdul-rasheed ne tako ina, dan ko a halayya da dattako da sanin ya kamata bai bar komai na mahaifinsa ba, kawai dai shi Abdul-rasheed mutum ne mai faranfaran da yawan magana, saɓanin Haysam mai shiru-shiru da ƙarancin fara'a a fuska idan ba shi yaso ba. Amma kowa ya shaida mutum ne mai haƙuri da kawaici.....

••><••><••><••

Da ƙyar Mammah da Imran suka ci ƙarfin Uncle Nasiru ya yarda da batun gwaji, shi dai gogan bai sake tankawa ba. Yayinda can ƙanensa ke cike tab a waje. Dan sanda Momyn Nabeeha ta fita da ita yanda suka zuba musu idanu a fusace sai da sukaji hantar cikunnansu ta motsa, shiyasa da sauri suka wuce su zuwa sashen su Nabeehan. Bayan sallar Magriba da aka kira Mammah tasa Biebah zuwa ta sanar musu su fito za'a asibitin. Koda suka fito a tsakar gida suka iske Mammah ta fito, Uncle Nasiru dama bai shiga ciki ba bayan dawowarsu massalacin. Hakama Imran da Zak-Shadow dake can gefe Imran ɗin na lallashinsa. Cike da gadara Momyn Nabeeha tace kuma sune zasu zaɓi asibitin da za'aje. Nan ma Uncle Nasiru zai yi magana Mammah tai saurin cewa sun amince ayi hakan. Takaici kamar zai kashe Uncle Nasiru da Zak-Shadow, amma dole sukai shiru aka tafi asibiti. Ita da ƴarta motar ta suka shiga. Su ko suka shiga mota ɗaya. Imran ke tuƙi, Uncle Nasiru a gefensa. Mammah da Zak-Shadow suka shiga baya Nimrah da Bilal ya dawo da ita tana barci a cinyarta, dan har yanzu barcin takeyi. Motar ta ce gaba tasu a baya. Cike da kulawa da lallashi Mammah ta kamo hanun Zak-Shadow a cikin nata, dan ta tabbatar zuciyar ƴan mazan na nan na tafasa a ƙirji, saboda umarninta ne kawai zai je gwajin nan. Aiko tabbacin a zuciyen yake ko motsi baiyi ba koda ta riƙe hannun nashi. Idanunsa kuma a rufe har suka iso asibitin daya kasance privete ne, babban asibiti ne kuma da akeji da shi a Abuja. Abinka da maganar kuɗi ko zaman mintina goma basuyi ba likitan da zasu gani ta basu izinin shiga. Nimrah da tun zamansu wajen ta farka tana lafe jikin Mammah Imran ya miƙama hannu. Mammah ta kalla, sai ta mata murmushi da faɗin, "Jeki kinji, ai yanzu zaku dawo ina nan ina jiranki". Kai ta jinjina Mammah, sannan ta miƙama Imran ɗin hannu ya sakko da ita. Da ƙafafunta ta taka har ƙofar Office ɗin, sai a lokacin kuma uban gayyar ya miƙe saboda maganar da Mammah tai masa. Nabeeha da itama sai yanzu uwarta ta kamata ta miƙar ta harari bayansa tana murguɗa baki, hakama Momynta da harara ta rakashi. Suna zuwa ƙofar ɗakin inda Imran ke tsaye tsagal Nimrah mai bakin magana da barci ya fara sakinta ta ce, "Baba ɗan sanda kanka ke ciwo ne?". Yanda tai maganar idonta akan Zak-Shadow ya saka Imran yin ƙaramin murmushi, shiko idanu kawai ya zuba mata ya ƙi magana. Yayinda Mammah da Uncle Nasiru ke murmurshin maganar tata, nan kuma Nabeeha da Momynta ji suke kamar su shaƙe shegiyar yarinyar. Nimrah bata haƙura ba ta matso kusa da Zak-Shadow, kamar zatai kuka tana kallon fuskar tasa dai ta kama hannunsa, "Baba ɗan sanda akwai zafi sosai ko? Kada kayi kuka kaj....." "Ke dan ubanki yima mutane shiru!!!". Nabeeha ta daka mata tsawa. A mamakinsu ko irin ma ta tsorata nan sai ma ƙuri datai mata da idanu ba shakka ba girgiza. Aiko ji Nabeeha tai ta sake hasala, ta fige hannunta tayi kan Nimrah zata daka, sai lokacin ta sake matsawa jikin Zak-Shadow sosai ta rungume ƙafafunsa tana ɓoye fuskata. "Wayyo Baba ɗan sanda kace Kada ta dakeni, bana son duka bana so...." Jin shiru ba'a daketan ba tai shiru, sai kuma ta ɗan leƙo fuskarta taga miya faru. Nabeeha ta gani tsaye cak tana huci kamar zakanya. Sai dai bata san miya tsaidata ba. Abinda kuwa bata sani ba wani shegen kallo Zak-Shadow kema Nabeeha ɗin daya sakata dakatawar. Imran shi ya katse yanayin da faɗin, "Bismillah ku shiga". Ƙwafa Nabeeha tayi da watsama Nimrah harara, ƙasa-ƙasa ta ce, "Sai na kasheki shegiyar yarinya ƴar zin....". Bata ƙarasaba Momynta taja hannunta suka shige. Shima cikin lallashi Imran yay masa magana da ido, bai tanka ba ya kama hannun Nimrah suka shiga, Imran biye da su. Da Imran kawai doctor ya gaisa, koda ya miƙama Zak-Shadow hannu yi yay kamar bai ma gansa ba. Shima doctor ɗin sai ya sake nutsuwa dan ya fahimci waɗan nan mazan bana wasan yara bane ba. A ɗarare ya juya ga Momyn Nabeeha yana tambayarta mike tafe da su. Ganin Momyn Nabeeha zata fara wani ƙalƙale-ƙalƙalen magana da iyayin ƴan bariki Imran ya katseta kai tsaye yay ma likitan bayanin abinda suke buƙata. Doctor yaga ba wajen wasa bane dandanan ya ɗauka waya yay kiran wani. Kafin kace mi an musu dukkan abinda ya dace anan cikin office ɗin nashi batare da sunje lab ba. Dukkan abinda ya kamata anyi musu, duk da dai ansha badaƙala da ihu lokacin yima hajja Nimrah nata gwaje-gwajen. Bayan an kammala komai doctor yace results sai nan da kwana biyu. "Bazai yiwu mu sameshi a gobe ba doctor. Abin na gaggawa ne Please". Momyn Nabeeha ce mai maganar, doctor yay ɗan jimm, sai kuma ya jinjina kai. "Okay ba damuwa hajjaju ai kece. Zuwa yamma zan kira ki". "Ai ni da zai yiwu ma zuwa 12 nake so, dan goben zuwa 1 inada meeting da first lady, kuma sai dare zamu fito". Bakin doctor a washe ya ce, "Shike nan yanda kike so haka za'ayi, zan yi ƙoƙarin hakan". "Na gode". Ta faɗa tana kama hannun Nabeeha suka fito, dama Zak-Shadow tuni ya fice da Nimrah. Sai Imran ne kawai aka bari, gama nazartar alaƙar dake tsakanin doctor da Momyn Nabeeha ya sashi tsayawar kuma. Sai da suka fice sannan doctor ya kallesa. "Ranka ya daɗe akwai sauran wani abu ne?". "Mai muhimmanci ma kuwa. Naga akwai alaƙa tsakaninka da su, to ka sani idan ɗigo ya canja a cikin result ɗin da muke buƙatar gani kayi kuka da kanka. Suna Major Imran Abbas." Daga haka Imran yay ficewarsa a office ɗin shima yabar likita da baki buɗe na firgici da mamaki. Dan a kwanakin nan babu sunayen dake amsa kuwwa a kafafen yaɗa labarai dana sada zumunta kamar Major Imran Abbas da Zak-Shadow da sauran Captains ɗin da akasha wancan gumurzun..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 57_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull