Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 30
Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 30: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 30. ★Anan ɓangaren ma Momyn Nabeeha da Nabeeha ɗinne a ɗakinta…
3,580 words
★Anan ɓangaren ma Momyn Nabeeha da Nabeeha ɗinne a ɗakinta sun kulle kansu suna sake tattaunawa. Dan suma tunda suka dawo gidan Momyn keta sake tunzura Nabeeha, hakan ne yasa Jiddah yin fushi tabar musu gidan ko jiran zuwan mijin nata ma batai ba. Dan ta riga ta fahimci al'amarin Momynsu a wannan karon yayi babban tasiri a zuciyar ƴar uwarta Nabeeha. Tana tafiya Momyn ta koma zaginta, sai hakan ya ƙara tunzura zuciyar Nabeeha ta ƙullaci ƴar uwar tata da sake tabbatar da ba sonta da ƙaunarta take ba daman, tunda bata kishinta bata tayata baƙin cikin abinda ke faruwa da ita. Hasalima goyon bayan mijin nata take saboda neman duwawun zama. Sai hakan ya sake jagorantarta shagaltuwa da huɗubar Momy da dake jin zafin Zak-Shadow matuƙa..
★Zak-Shadow kam tun bayan wucewar Imran daya koma sashen ɗakinsa kawai ya shige ya rufe kansa. Shi sam ba wani shirmen Nabeeha ko abinda ke faruwa a gidan ke damunsa ba. Hasalima bai ɗauki wannan serious ba dan yama gama tsara abinda zaiyi. Damuwarsa tana ga aiki ne musamman akan al'amarin Ojo da binciken da yake yi na musamman akan ainihin son sanin shuganin ƙungiyar duhu. A yanzu ma yana tsaye a bakin tagar ɗakinsa ne, yana sanye da kayan barci farare masu sauƙin nauyi, hannunsa riƙe da kofin shayi da bai gama sha ba. Sararin samaniya datai haske fayau na gangarawar ƙarewar wata ya zubama idanu kawai. A hankali tunaninsa yabar kan Ojo ya koma ga sojojin da suka barin a sansani a halin yanzu, yana jin kewar aiki, amma a lokaci guda yana jin daɗin hutunsa da ya tabbatar zai bashi damar binciken daya kafama alƙalami.. Vibration ɗin wayarsa ne ya katse tunaninsa, ya ɗan waiwaya yana kallonta a study table, kafin ya furzar da iska kaɗan tare da takawa zuwa study table ɗin. Ɗan zubama number ɗin ido yayi na sakani harta tsinke, ba suna, amma ya tabbatar duk wanda zai kira wannan layin nasa amintacce ne a garesa. Kiran ne ya sake shigowa a karo na biyu, bai jima ba yanzu kam ya ɗaga. Sallama akai daga can, ya amsa a taƙaice tare da faɗin, "Who's this?". Murmurshi akai mai sauti daga can, sai kuma a taƙaice aka furta, "Col. Faro". Karo na farko Zak-Shadow ya ɗan murmusa, sai kuma ya ajiye kofin hannunsa yana kaiwa zaune a kujerar study table ɗin tare da ɗan taɓe baki cikin mamaki. "Humm kai dai bazaka taɓa canjawa ba, shi kuma wannan layin fa?". Ƙaramar dariya Faro yayi daga can, sai kuma ya furzar da iska kaɗan shima tare da komawa serious, yace, "Zak-Shadow Ba zan iya yin wannan kiran da wata waya ta hukuma ba". "Humm hankaka...". Sai da yay ƴar dariyar batun Zak-Shadow ɗin da ƙarasa masa da ".....baka jewar banza ba" sai kuma cikin damuwa ya ce, "Zak... Ina cikin aiki yanzu, kuma lokaci bai ƙi min yakana ba. Amma akwai wani abu da ya kamata ka sani kafin lokaci ya ƙure." Ɗan shiru Zak-Shadow yayi na fin sakan biyu, kafin ya sake daidaita muryarsa ya ce, "Ina saurarenka". Ajiyar zuciya mai ƙarfi Faro ya saki, "Ka kula sosai Zak. Na ji ana motsi a sama. Sun buɗe fayil ɗin Shadow Recon Unit. Kuma sun haɗa sunanka da wani rahoto mai nauyi. Ban san gaskiyar sa ba, amma na ji suna cewa za a turo da Special Board daga Defence HQ domin bincike." Shiru ya biyo bayan maganar, sai ɗan cizar lips da Zak-Shadow keyi kaɗan-kaɗan da ƙaramin saukar numfashin Faro. Zak-Shadow ya saki murmurshi mai bala'in ƙayatarwa a hankali yana miƙewa hannunsa ɗaya a cikin aljihu, inda ya baro jikin window ɗin nan ya koma ya sake tsayawa kamar ɗazun. Kai tsaye ya furta, "Da alama ababen farauta sun fara tsallako gaɓar ruwa domin neman ceto, sai dai idan basuyi taka tsantsan ba za suyi gudun GABA KURA NE BAYA SAYAƘI. Wane ne ke da alhakin motsin?". "Ban sani ba, amma akwai liken tattabara a cikin runduna, Zak-Shadow naji a jikina wani na ciki ne ke aika bayanai. Ka kula sosai. Idan wani abu ya faru, kar ka bari su kama ka kai tsaye. Ka jira umarni na hukuma, amma ka sa idonka a kan mutanenka, musamman waɗanda ka fi yarda da su." Kai tsaye ya kamo bakin zaren, dan haka ya sake sakin murmushi mai sauti, "Faro…" Zak ya kira sunansa cikin murya mai nauyi, tare da dakewa ya cigaba da faɗin, "Karka kuskura ka tona asiri da yawa. Ka tsaya a gefe, ka bar sauran wasan a kaina". "Na riga na shiga Haysam, Imran kawai nake ji, dan yana da rauni akan ka. Kuma bana so a bar maka wannan wasan kai kaɗai, ko yin amfani da shi akan ka, dan girman filin da za'ayi shi ya wuce duk yanda kake tunani…" Daga haka Faro ya katse kiran daga can. Ji kawai Zak-Shadow yayi Beep… beep… line disconnected. Tsayawa yay kawai yana kallon wayar kamar yana son ta amsa masa sauran abin faɗar dake yawo a zuciyarsa da kanta. Sai dai yasan hakan bamai yiwu bane, yasan kuma iya batun da zai iya samu daga Faro kenan, wannan ma da yaji amintaka ce da yarda, amma duk tsanani soja baya auna wajen harbi da harsashi a gaɓar share fagen wasa. Wayar ya ajiye a hankali, yana tura labulen window ɗin da ƙyau saboda buƙatar shaƙar iska mai yawa, idanunsa ya tsayar kan sararin samaniya dake rikiɗewa zuwa duhun tsakkiyar dare. A ƙasan maƙoshi fuskarsa da murmushi mai wahalar fassara ya furta, "Da alama yanzu ne za'a dawo da wasan gaskiya. Wasan da zai rarrabe shiru da amsa kuwwar masu son a shelantawa".
((★))<>((★))
WASHE GARI....
A yau rana ce a gurin kowa kamar sauran ranaku da suka shuɗe. Sai dai ga Zak-Shadow rana ce da tazo da abubuwa kashi-kashi. Masu ban tsoro da ban mamaki har ma da ruɗani musamman ga ahalinsa dama duk wani masoyinsa. Rashin samun isasshen barci da daddare baisa ya kwanta da safe domin yin ramuwarsa ba. Dan ana idar da sallar asubahi ya fito a masallacin kenan su Ammar zagaye da shi kiran Imran ya shigo wayarsa. Dama ya fito da wayar ne shima dan nemansa, sai kuma akai sa'a shi ya fara kiransa. Barin inda ƙanen nasa suke yay ya koma gefe, duk suka bishi da kallo rayukansu babu daɗi, dan sun kwana da damuwa. Yanzu ma sun yanke shawarar tunkararshi da batun da aketa ɓoye musun duk da sunji komai, sai dai shakkarsa ta sakasu inda-inda har Imran ya kirashi. A tare suka saki ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna....
"Na kama yaron nan a daren jiya da kaina dan na kasa haƙuri". "Oh shittt! Imran miyasa kai hakan?". Zak-Shadow ya faɗa cikin runtse ido. Cikin rashin damuwa Imran ya ce, "Zak.. wannan abun dole muyisa da gaggawa, dan jiya Dabo ya sake kirana sakamakon abubuwan daya sake samu a gidan su Ojo. Shiyasa na fahimci jira har sai gobe yabar barrak mu kamashi zai iya zama matsala. Shiyasa kawai na tarfashi a wani hotel da ya je". "Hakan da kayi shine dai-dai, amma matsala zata iya biyo bayan hakan nayi da kanka da kayi". "Miyasa?". "Ba maganar waya bace. Yanzu dai ina ka ajiye shi?". "Yana cikin gidana, dan hakan ne kawai zai k......." "Imran!!!!! A are you madd!!!!". A yanda yay maganar ba Imran ba hatta su Ma'aruff sai da suka firgita. Kafin Imran ya iya cewa wani abu Zak-Shadow ya cigaba da magana cikin kaushin murya da zafafawa. "Maza ka kimtsa shi gani nan zuwa zan fiddashi. Wane irin mugun tunani da ganganci ne wannan zaka kaishi cikin gidanka? Wlhy idan ka bari wani abu ya biyo hakan da zai taɓaka sai na HUKUNTAKA Imran. Sai na HUKUNTAKA tabbas sai na HUKUNTAKA...." Kai da kaji yanda yake magana kasan tabbas Imran yana cikin babban lagonsa da yake matuƙar tsoro da gudun abinda zai iya taɓa rayuwarsu.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 60_
__________________
https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt
https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite
https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝 Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.
Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
..........Imran kuwa murmushi kawai yayi daga can, sai ma ya yanke wayar yana ɗan taɓe baki. Zak-Shadow nashi kenan, shi ya yarda ya shiga kowane irin haɗari dominsa, amma idan shine ya gwada yin wani abu koyaya yanzu Zak-Shadow ɗin zai tada hankalinsa. To an taɓa rayuwa haka, shi ya sadaukar da rayuwarsa a kansa shi kuma ya gagara yin hakan saboda son tashi rayuwar, bazai yiwu ba, sai dai akan koma minene ya yarda suyi mutuwar kasko. Amma bazai yarda shima Zak-Shadow ya shiga haɗari ba duk rintsi in dai yana da damar taimakonsa... Cikakken mintuna goma ba'ai ba kuwa Zak-Shadow ya ƙarasa gidan Imran, damma sai da ya koma gida ya ɗauki mota sannan. Wata muguwar harara ya zubama Imran ɗin dake compound zaune yana jiran isowarsa, dan yasan tunda yace zai zo to zai zo ɗin. Imran yayi dariya yana tasowa, koda ya iso jikin motar da har Zak-Shadow ya fito ya bashi hannu ƙin amsa yayi. Imran ya sake murmusawa yana kamo hannun nasa sukai musabaha. Cike da tsokana ya ce, "Haba Yayan Imran ayi haƙuri. Irin wannan tada hankali haka? Kada ka manta dai ƙanin naka soja ne fa". Harararsa Zak-Shadow ya sake yi, a ɗan fusace ya ce, "Kana saka kanka a haɗari da iyalanka kana ɗaukar abu wasa. Imran wai miyasa baka jin magana ne?..." "To bana ce ayi haƙuri ba dai, sannan baka bari na kai ƙarshen maganata bane ba fa. Ba wannan gidan nake nufin na kawo shi ba, sabon gidan can fa da babu kowa". ALLAH sarki Zak-Shadow, wata irin ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke yana runtse idanunsa da kifa kansa jikin motar. Imran ya sake yin murmushi, sai kawai yaji ƙananun ƙwalla sun taru masa a cikin ido. Shi ya sani ƙaunar da Zak-Shadow ke masa mai girma ce, shiyasa shima bai san yawan adadin da yake masa ba a rayuwa. Sunja lokaci a haka kafin su koma inda Imran ɗin ya taso suka zauna. Ba jimawa matarsa ta kawo musu coffee. Cikin girmamawa ta gaida Zak-Shadow dan Yaya ma take kiransa. Shima ya amsa mata da kulawa yana tambayar lafiyar yara, tace suna lafiya gasu nan ma zasu zo gaisheshi. Aiko babu jimawa suka fito, su huɗu abin sha'awa mata biyu maza biyu. Dukansu kama suke da Imran ɗin. Fuskarsa da murmurshi ya buɗe musu hannayensa, suma cike da farin ciki suka zo suka shige jikin nasa. Yanda yake suna musu soyayya irin ta mahaifi haka suke masa soyayya irin ta uba da ƴaƴa. Ya tambayesu makaranta kowa yace lafiya lau, kowa kuma na ƙoƙarin bashi labarin makarantar tasa. Shi ko yana zuba murmurshi da saurarensu. Yarinya ta uku, wadda daga ita sai auta da zasu iya zama sa'anni da Nimrah ta ce, "Dada zan bika wajen Mammah". Kanta ya shafa da faɗin, "Makarantar fa Ruƙayyan Dada?". "Ni na gaji da zuwa dama". Murmurshi yayi har haƙoransa na bayyana, ya ce, "Babbar magana, dama ana gajiya da neman ilimi Baby na. Kinga yanzu dai kije school, na miki alƙawarin weekend zan zo da kaina na ɗaukeki dama na kawo miki ƙawa". Wani tsalle Ruƙayya ta saka cike da farin ciki tana ma sauran ƴan uwanta gwalo. Suma sai suka fara ƙorafi, sai da Imran ya ga zasu damesu yace su wuce su ƙarasa shiri lokaci zai ƙure ga driver na jiransu. Badan sun so ba suka wuce ciki. Shi kuma suka cigaba da tattauna abinda ya dace. Sun tsayar da shawarar bazasu kula Ojo ba sai nan da kwana uku, zuwa lokacin ya jigata yayi laushi. Dole anan Zak-Shadow yay breakfast, dan basu baro gidan ba sai 11:30, suna zuwa ya wuce sashensa yin wanka. Shi kuma Imran ya shiga wajen Mammah, in da ya samu Uncle Nasiru da Uncle Jamilu da yazo daga Bauchi, kasancewar kuɗin jirgi Zak-Shadow ya tura masa shine ya iso da wuri. Itama Mammah ganinsa kawai tayi, har ma abin ya bata mamaki, bata samu damar tambayarsa komai ba bayan gaisuwa sai ga Uncle Nasiru yazo. Suna zaune suna hira harda su Yaya Ma'aruff da ganin Uncle Jamilu ya hanasu fita kasuwa, dan sammakon nasa da zuwan bazata ya tabbatar musu akwai dalili. Suna nan zaunen Dada ya shigo, basu ba hatta Mammah sai da ta zuba masa ido. Shi ko kamar baiga kallon da suke masan ba ya sake fiskewa abinsa. Ja'afar daya kasa haƙuri cikin ɗan sosa ƙeya ya ce, "Humm wlhy Dada manyan kaya na maka ƙyau, ka ganka kuwa kamar sabon ango..." ya ƙarasa faɗar angon a hankali. Hararar da Dadan ya watso masa ta saka Ma'aruff rufe baki yana danne dariya, Ja'afar kam sai yay saurin haɗe hannayensa alamar ban haƙuri, su ko su Mammah duk murmurshi sukayi. Mammah ya fara gaidawa, sannan cikin girmamawa ya gaida Uncle Nasiru da Uncle Jamilu, suma su Ja'afar suka gaisheshi. Dai-dai nan kira ke shigowa a wayar Imran, ganin likitan jiya ne mai kiran yasa shi ɗagawa a wajen batare daya tashi ba, sun gaisa yay masa bayanin ga result ya fito ya za'ayi? Sai yace masa ya jirashi gashi nan zai zo ya amsa. Yana yanke wayar ya sanar musu doctor ne. Uncle Nasiru yace, "Ai sai muje kenan?". "A'a Uncle bara kawai naje na amso kuyi zamanku". Su Ma'aruff najin haka suka miƙe wai bari su rakashi, shi ko yace suje. Daɗi ne ya kamasu, tunda dama neman hanyar jin komai sukeyi. Bayan fitarsu ne Mammah da Uncle Nasiru da Uncle Jamilu suka sake tattauna abinda ke faruwar, dan shi dama Zak-Shadow bai ma Uncle Jamilu bayanin komai ba. Sosai Uncle Jamilu ya girgiza, tare da jin tausayin yarinyar, dan yanzun kam Mammah ta buɗema Uncle Nasiru da Uncle Jamilu komai game da mahaifin Nimrah ɗin matsayinsu na iyaye. Sai lokacin ma Zak-Shadow ke tambayar tana ina?. Mammah ta ce, "Bilal ya tafi kaita makarantar su Mu'azz, nayi mamakin ma har yanzu bai dawo ba dan tun goma suka tafi". Shima agogon hannunsa ya kalla dan gab ake da kiran sallar azhar, sha biyu kusan da ashirin ne. Zai yi magana sallamar su Imran ta katseshi, kowa juyawa yay yana kallonsu banda shi. Imran ya zauna, Mammah tace Ja'afar yay kiran su Momyn Nabeeha daga nan su wuce kasuwa ta sallamesu. Baki suka tura gaba su duka alamar basu so hakan ba, dan su so suke ai komai a gabansu. Amma an koresu bayan daga Dadan sai su a gidan. Babu yanda zasuyi suka fitan, shi Ja'afar yaje ya sanar ma da su Nabeeha batun kira. Dan suna falo suna breakfast da sai yanzu suke yinsa. Daga ƙofa ya tsaya ya sanar musu, bai jira amsarsu ba ya juya abinsa. Harara Momyn tasu da Nabeehar suka rakashi da ita, yayinda Ismat ke jin kamar taje ta rungumeshi, tana matuƙar son Ja'afar, amma shi ko kallo bata isheshi ba, randa aka saka ranar aurensu tasha kuka, amma sai ta ƙara ƙarfafa kanta akan kota biyu taje. Sai da suka gama abinda suke fin minti ashirin sannan suka tafi, a zatonsu wai haƙuri Zak-Shadow zai bada ya faɗi gaskiya tunda su basu san likita ya kira ba, duk kuma Kusancinsa da Momyn bai kirata ya sanar mata komai ba saboda hargaɗin Imran. Yanda Momy ke cika da batsewa haka Nabeeha keyi, da ƙyar ta gaida Ubanta da Mammah. Momy kam babu wanda ta gaisar, sai Mammah ita ta gaidata, ta amsa kuma da ƙyar. Shima Uncle Jamilu da yake bamai damuwa bane sai ya gaisheta. Imran da Zak-Shadow kam yi sukai kamar ma basu san da shigowarsu ba, sai hakan kuma ya ƙona mata rai, a ganinta ko Imran bazai gaisheta ba ai shi ya dace Zak-Shadow ya gaisheta kodan ƴarta da yake aure. Cikin danne takaici Uncle Nasiru yay gyaran murya tare da yin sallama. Kowa ya amsa sannan ya amshi takardar da Imran ya miƙo masa. "Ga result ya fita, doctor ya kira Imran yaje ya amso. Zamu duba sai muga mike cik....." A wani irin zabure Momyn Nabeeha ta ce, "Kamar ya result ya fito anje an amsa? Ke nan wani abun aka ƙulla daban, yo inba wani abu aka ƙulla ba ai banga dalilin zuwa a amso result bada saninmu ba, kuma ai can ya kamata muje asibitin shi likitan ya mana bayani idan ba wani munafunci bane kuma ko an siyesa ne banda labari". Babu wanda ya tanka mata, shima Uncle Nasiru baki kawai ya ɗan taɓe yana girgiza kansa. Ya kuma buɗe takarda ya fara bayanin da kowa zai gane, sannan ya ajiyeta a kan table yace duk mai buƙata zai iya ɗauka ya sake dubawa. Caraf Nabeeha ta ɗauki takardar ta duba kuwa, tunkan takai ƙarshe ta fashe da kuka wai ita wlhy bata yarda ba, sai dai in anje ansayi likitan nan ne, dan haka sai dai a sake zuwa wani asibitin a sake sabon gwaji. Yanda Momynta ke sake zugata da faɗan maganganu sai zuciyar Uncle Nasiru data Zak-Shadow ta sake hasala. Hatta Mammah dannewa kawai take tana murmushin mamaki, shi kansa Imran sai faman cizar lips yake. Sai Uncle Jamilu ne ke magana cikin lallashi da son fahimtar da Nabeeha da uwarta. Amma da alama ma ko saurarensa ma basayi. Gani sukai kawai Zak-Shadow ya miƙe abinsa yana kallon agogo, sai kuma ya kalla Mammah da girmamawa ya ce, "Kiyi haƙuri da hukuncin dazan yanke". Cikin matuƙar tsoro Mammah ke kallonsa. "Wane irin hukunci kuma Muhammad? Kar ma kayi tunanin abinda zuciyata ke hasaso min". "Mammah wanda ya dace ne, na san kuma kema zai gamsar dake in sha ALLAHU. In dai abinda nake tunanin zakiyi hasashe ne kuma bashi bane". Daga haka ya kalla su Uncle's ɗin. "Lokacin salla yayi Uncle's". Uncle Nasiru daya gama kaiwa wuya yana kallon Nabeeha data cika kunnen mutane da ihu kawai ya fisgi flowers base dake saman Centre table ya wurga kanta. Da hannu ɗaya Zak-Shadow ya cafe, yayinda kowa a falon ya waro idon tsorata, dan gilas ne flowers base ɗin, sun tabbatar idan ya sauka akan Nabeeha sai taji ciwo in ma bai fasa mata kan gaba ɗaya ba. Haƙuri Mammah da Uncle Jamilu suka hau bashi, yayinda Momyn Nabeeha ta kacame da tsiya Nabeehar na tayata da ihun kukan iskanci..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 61_
__________________
Ina mata ma'abota ado da kwalliya maryam's all-in-one emporium ta tanadar muku Mayafai masu kyau da aminci kama daga plain chiffon veils masu kyau kamar daga Egypt suka sauko🥰 jersey scarfs , beaded and stoning veils, Chantilly, 2D to 10D Turkish veils Dubai d.s Kuma abun farinciki muna bada sari da siyan dai dai ina Kano Ina tura kaya ko'ina cikin Aminci da yardar Allah ga number ta 09064960666
https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt
A cikin duniya ta gayu da burgewa mayafi shine ya ke daukaka ado da aji
Maryam's all-in-one emporium 09064960666 Kano Anan ne gayu yake tarar da qawa.
Ki more hadaddun Mayafan mu da suka hada da Plain chiffon veils (soft & flowy) Italian Chantilly veils (pure elegance Jersey Veils (comfort meets class) Lafaya and many more.
Each piece tells a story of grace, crafted for women who understand beautyin simplicity.🤍
🖤 Premium quality 💛 Affordable luxury 🖤 Available in elegant shades 💛 Delivery 🚚 duk inda kike a fadin duniya
Ba mayafi kawaii kike bukata ba you deserve a statement of class.👑
Wholesale group https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________