Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 31

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 31

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 31: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 31. ........Imran da Uncle Jamilu dai suka lallaɓa Uncle Nasiru…

3,860 words

........Imran da Uncle Jamilu dai suka lallaɓa Uncle Nasiru suka fice. Shima Zak-Shadow da baice komai ba sai ya ajiye flowers base ɗin yabi bayansu. Sunyi alwala ran Uncle Nasiru a ɓace matuƙa, sai da suka fita wajen gidan Zak-Shadow yay musu bayanin hukuncin daya yanke kawai. Abin mamaki su duka babu wanda bai sauke ajiyar zuciya ba, sannan fuskokinsu suka washe da farin ciki, barema Uncle Nasiru albarka ya dinga zubama Zak-Shadow da faɗin, "Hakan da kai shine dai-dai Haysam, ALLAH yay maka albarka ɗan halak. Babu isashen lokacin magana suka wuce massalacin dan za'a fara salla. An idar mutane zasu fice Imran ya dakatar da su, Uncle Nasiru da Uncle Jamilu kuma suka matsa kusa da liman suna magana. Abin mamaki, abin al'ajabi da girgiza zuciya kawai sai ji su Ma'aruff dake massalacin harda Bilal daya dawo shi da Ammar suka tsaya yin salla kafin su shiga gida Nimrah kawai suka tura ta shiga sukaji ana batun ɗaura auren mai sunan Dadan su Haysam da wata wai Naja'atu Nimrah. Abinda ya sake ɗaure kansu kuwa Dada da kansa yay wakilcin auren Naja'atu, shi kuma Uncle Nasiru yay wakilcin Haysam Abdul-rasheed Shehu da suka sake tabbatar da Dadan nasu ne dai ake nufi, sai dai sun gagara kamo lissafin wacece Naja'atu. An ɗaura aure akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Dubu ɗari biyu mai daraja da kima a wannan lokacin na 2013, dan kuwa itace miliyan biyun wannan ƙarnin saboda taɓarɓarewar kuɗaɗen ƙasarmu. Ana gama shafa addu'a Zak-Shadow ya dinga jin kamar an zare masa jinin jiki da jijiyoyi a lokaci guda, sai yaji wani irin sanyi na shigarsa kamar wanda yake a cikin dusar ƙanƙara. Sai da takai har kowa ya fita a massalacin shi ya kasa motsawa. Aka barsu shi da Imran kawai dake kallonsa yana shu'umin murmurshi mai ƙayatarwa. Sai da yaga da gaske ba motsawa zai yi ba sannan ya kai hannun ya taɓa kafaɗarsa. "ALLAH ya sanya albarka a wannan aure, ya bamu tsawon rayuwar ganin girman Nimrah matsayin MATAR ZAKI NA." Ɗago idanunsa da suka kaɗe sosai yay yana kallon Imran a karo na farko, sai kuma ya lumshesu ya sake buɗewa akan Imran ɗin cikin yanayin damuwa da motsa lips kaɗan, "Imran kada kai wannan tunanin, dan ni banyi dan hakan ba, nayi ne dan waccan shashashar ta dawo a hayyacinta ta fahimci gaskiya kafin lokaci ya ƙure mata. Amma a yau ɗin nan zan yanke wannan igiy......" Hannu Imran ya ɗaura masa a baki yana girgiza kansa. "Karka ce haka Haysam, kada kai irin wannan tunanin. Idan ka aikata tamkar ka zalunci Nimrah ne, ka kuma ci amanar da mahaifiyarta ta baka. Wlhy ko babu wannan rikicin kai ne yafi cancanta ka auri yarinyar nan, dan ina da tabbacin zaka zame mata garkuwa kuma bargon rufin asirin da bazata samu a wajen kowa ba koda kuwa nine..." "Imran baka da hankali ne?, yarinya ƴar shekara bakwai kake cewa na zauna da aurenta a wannan shekarun nawa? Yin hakan ma ai shine zalunci a gareta, sanda zata gama sanin kanta ma ai na gama tsofewa". "A'a yagalgalewa ka gama yi ba tsofewa ba, girman yaran shekara nawa ne. Bata wata shekara bakwai ɗin nan gaba kaga ikon ALLAH, sannan shi namiji har yanama nace tsufa ne?, in dai da lafiya ai ko tamanin garai ya ɗau Sweet 16. Balle kai na tabbata sanda zata kai girman baka ko cika hamsin ba. A yanzu waye zai ce ma ka cika talatin ɗin balle ace ka ɗara. Malam ajiye huɗubar shaiɗan riƙe auren nan gam in sha ALLAHU na yin alfahari ne har cikin aljanna. Fatan mu dai ALLAH ya bamu tsahon rai da lafiyar jiki". Rasa ma abin cewa Zak-Shadow yayi, kallonsa kawai yake da wani irin yanayi har ya kai ƙarshen zancen. Cikin girgiza kai ya ce, "Imran bazan iya ba, ko ƙannena bana ma fatan suji wannan abun kunyar ai....." "Hhhhh sai dai kuma wani, dan wannan kam a gaban su aka ɗaura tun daga Ma'aruff, Ja'afar, Bilal har Ammar". "What!?". "Wlhy suna massalacin nan su duka akai komai. Kana kuma bazaka iya ba, to miye abin kunya bayan koyi kayi da sunnar MANZON ALLAH mai girma ma kuwa. Dan karka manta MANZON MU ya auri Uwar Muminai Nana A'isha (RA) tana da shekara shida a duniya, ta tare gidansa tana da shekara tara, a lokacin shi kuwa yana da shekara kusan 53, to sai kuma kai ne yanzu zaka kira abin ko kallonsa da abin kunya, bayan UBANGIJI ne ya baka batare da kai kanka ka taɓa saka hakan a lissafinka ba. Wannan wata hikima ce ta UBANGIJI dan haka babu batun yin wasa da ita a gareka, kai dai kawai yi addu'a lokacin shan gara yazo". Imran ya faɗa yana dariya da miƙewa. Sai Zak-Shadow yaji ma jikinsa ya sake zama sanyi ƙalau. Babu yanda zai yi dole ya tashi yabi Imran ɗin suka fita zuwa gida. Shigarsu kuwa ya tabbatar da cewar ƙanen nasa sunji, dan a tsakar gida ya samu su Ja'afar tsabar iskanci sun fito da speakers ɗin ɗakinsu suna kwasar rawa su duka huɗun. Abin takaici abin haushi Nimrah a tsakiyarsu ta ware itama tana rawar. Yo dama amara Nimrah da son nanaye. Yayi kansu a fusace ya hango Mammah, Uncle Nasiru da Uncle Jamilu tsaye suna musu dariya cike da farin ciki. Sai su Nabeeha dake tsaye daga ƙofar sashensu suna kallonsu kallo irin na mamaki alamar basu san mike faruwa ba sukam. Ita Nabeeha ma hankalinta akan Nimrah yake, ji take kamar ta kashe yarinyar kowama ya huta. Dan a yanzu ɗin wani sake ganin ƙyawunta tayi alamar yarinyar ta fara washewa da cima mai ƙyau da sutura, idan kuwa takai nan gaba hummm... Yanzu ma dariya Imran yayi da faɗin, "Zakina ka sallama kawai kaji, ka barsu suyi farin cikinsu kaga ma harda tsuntsuwar taka ake cashewa." Rasama abin cewa Zak-Shadow yayi, sai yay ƙoƙarin juyawa da tunanin barin gidan Uncle Nasiru ya dakatar da shi. Sai lokacin ne kuma su Bilal suka gasa ma. Da gudu kuwa suka shige ɗakinsu da yake ƙofar ta wajen compound ɗin take bata falon Mammah ba. Har Nimrah zata bisu Imran yay kiranta. Tsayawa tai kuwa cak, ganin Imran sai ta taho cike da farin ciki dan kowa sai da taba labarin makarantar da aka kaita sune bata gani ba. Imran na ganin zata zo jikinsa ya nuna mata Zak-Shadow, sai ko ta juya wajensa, caraf ta riƙo hannunsa tana faɗin, "Dada!". Dan yau Bilal ya gaya mata yanda zata dinga kiran kowa a gidan, tare da mata faɗan ta daina cema Zak-Shadow da Imran Baba ɗan sanda. Imran tace masa Uncle, Zak-Shadow tace Dada. Shine fa yanzu tace Dada ɗin. Kallon ta yake bai ce komai ba. Bata damuba ta fara bashi labarin makarantar kuwa hankalinta a kwance, kai daga ganin yanda take farin ciki da ɗan tsalle-tsallenta kasan abin ya kai mata har ƙuryar ranta.....

<><><><><>

A lokacin da can aure ya ɗauru tsakanin Zak-Shadow da Nimrah kamar a mafarki anan Headquarter zaman meeting Janar ya sake yi a yau shi da wasu manya da kwamitin da aka naɗa zasu yi bincike akan wannan taƙaddama ta Zak-Shadow dake tsakkiyar son kaɗa musu hankali. Meeting room ɗin yayi shiru baka jin komai sai kaɗawar fankoki da takardun da Janar ke motsawa yana a gabansa alamar yana karanta wani abu mai muhimmanci a ciki, dan fuskarsa cike take da damuwa. Gefe ya ture takardun yana ɗan furzar da iska. Sai kuma yay ma Colonel Haydar nunin yayi magana. Zama Colonel Haydar ya gyara, cike da girmamawa ya ce, "Sir, mun tattara dukkan bayanan da suka shafi Shadow Recon tun shekaru hudu zuwa yanzu. Ga jerin ayyukansu, bayanan waɗanda suka halarta, da kuma rahoton da ya kawo tarin matsala, wato Operation Silent Echo da a yanzu ake son yin amfani da shi akan Zak-Shadow ɗin". Karɓar file ɗin General yayi, cikin nutsuwarsa ya buɗe shi a hankali. Hoton aiki, sunaye, jerin lokuta. Batare daya ɗago ba ya ce, "Colonel shekara uku da suka wuce, wane irin aiki ne ya jawo rufewar su a hukumance?". "Sir akwai zabuka uku. Amma abin da muka fi samun tabbaci a kai shi ne haɗarin da ya faru a lokacin Operation Silent Echo, an samu mutuwar fararen hula kamar a wannan lokacin, rahoto ya haifar da tsokana a wasu kafofin yaɗa labarai, sannan aka umarci a dakatar da unit ɗin don a gudanar da bincike. A lokacin an kwance wasu membobi, wasu kuma an jefa su a ayyukan waje." General ya ja numfashi mai ƙarfi da ɗan furzar da iska. "Shin akwai waɗanda suka je kotu ne?". A yanzu kam wani dake gefen Colonel Haydar ne ya amsa da "A zahiri an yi bincike a cikin gida, amma an dakatar da duk wani shari'a saboda political interference. Wasu bayanai sun ɓace daga files na asali kuma tun a lokacin." Idanu General ya rufe na ɗan lokaci, alamar damuwa da fushi. Amma ya haɗiye abinka da mazan fama, cikin sauƙaƙa lafazi ya furta, "Hakan na nufin idan an ɓoye bayanai har kamar haka a wancan lokacin, to kuwa wannan maganar tana nuna akwai masu ƙoƙarin kare wasu marasa gaskiya kenan. Na san Haysam, mutum ne da baya ji daɗin cutar fararen hula. Idan akwai shaida mai ƙarfi da ke nuna akasin haka mugani". Yanzun kam Captain Akon ne ya miƙa wata USB ƙarama, cikin girmamawa ya ce, "Ga wasu kwafin da aka samu daga tsohon kwamandan unit, sai dai ba cikakke bane, amma akwai abubuwa masu amfani da zasu taimaka. Sannan akwai sunan wani Moly Kaithan a cikin waɗanda suka amfana daga ayyukan da suka farun". Cikin takaici General ya ture files ɗin kaɗan, sai kuma ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya. "Kada mu yarda a rarrabe mu da siyasa. Wannan bincike zai gudana cikin sirri. Zai fito ne daga ofishin mu, daga cikin runduna kuma. Kar a bari kowa ya san matakan mu. Ina sake gargaɗin kowa ya kula, dan duk wanda yay amfani da wata matsala dake tsakaninsa da Zak-Shadow yay abinda ba shine gaskiya ba zan bashi mamaki. Colonel Haydar kai ne shugaban wannan comitin a ɓangarenmu, Brigadier General ya zama Chairman na kwamitin tuhuma da bincike, koda su daga can gidan Gwamnatin sun bada nasu"..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 62_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........."Yes sir. A yanzu haka na shirya team guda uku, legal liaison, intelligence analysis, da forensics document review. Amma sir, idan har an taba goge wasu takardun fa, ba abune mai sauki ba a garemu, dan za'a iya amfani da hakan a cimmana" "No Colonel kada mu fara da zarge-zarge. Muna bukatar gaskiya. Ka kawo mini jerin sunayen waɗanda suka yi aiki tare da Shadow Recon, waɗanda suka zauna a gida da waɗanda aka tura waje. Zan fara da hira da su." Cikin gamsuwa Colonel Haydar ya yi ƙasa da kai na girmamawa, "Sir, zan kawo jerin nan gobe in sha ALLAHU. Amma fa akwai ƴar matsala a waje, wasu daga cikin waɗanda aka rufe sun riga sun shiga harkar siyasa wasu kasuwanci. Wasu kuma sun yi murabus ne kawai dan kansu sun koma gefe." Kai General ya jinjina kawai batare da yace komai ba, sai kuma ya ɗauki fayel ɗin dake ɗauke da hoton Zak-Shadow ya zubama hoton ido ba wasu sakanni. "Zan sanar da Ministan Tsaro cewa wannan bincike zai cigaba da tafiyar a karkashinmu har zuwa wani lokaci kafin nasu ɓangaren kwamitin su shigo ciki. Dan gaskiya muna bukatar hujja a hannuwan mu kafin mu kira ko mun gayyaci kowa. Sai kuyi ƙoƙarin tattara komai daya shafi shi wannan harin na kwanaki goma tun daga farkonsa har zuwa fitowarsu a jejin. Dan zamu iya gayyatar Haysam nan da 2 to 3 days. Ina ƙara gargaɗinku ku kula". A tare suka amsa da "Yes Sir". Daga haka ya fice ADC ɗinsa biye da shi.....

<<•>><<•>><<•>>

Tunda Uncle Nasiru ya fara bayanin sa jikin Nabeeha ya fara rawa, bata ma bari ya kai ƙarshe ba cikin ɗimuwa ta ce, "Abba nifa ban gane ba. Wai wane Haysam kake magana ya auri wanene...?" Sai da Uncle Nasiru ya zuba mata harara, cikin sake tsaurara harshe ya ce, "Hausar ce kika daina fahimta kenna ko? Bayan Haysam mijinki akwai wani Haysam ɗin ne anan? Ba kince ke baƙya ji ba, uwarki kuma itace limamiyarki mai ɗoraki akan keken ɓera. Kinga yanzu ke da ita bakwa buƙatar sake gwajin likita ko ƙaryatawa tunda dai UBA baya auren ƳARSA....." "Amma Nasiru kai azzalumi ne? Ƴar taka za'a haɗa kai da kai a wulaƙanta?". Momyn tace tai maganar cikin huci da miƙewa kamar zata rufe Uncle Nasiru da duka. Dan sai wani girgiza jiki take, hakan yasa kowa zuba mata ido banda Zak-Shadow dake danna waya kamar ma ba'a kansa ake bala'in ba. Dai-dai nan ihun Nimrah ya karaɗe kunnuwansu. Kusan lokaci guda Mammah da Zak-Shadow suka miƙe, hakama Imran da Uncle Jamilu. A tare su huɗun suka nufi kitchen inda suke jiyo ihun nata, shima Uncle Nasiru ya take musu baya. Babu wanda bai razana da ganin Nabeeha a kitchen ɗin ba da wuƙa a hannu, yayinda Nimrah ke can saman kitchen cabinet ta maƙale Nabeeha dake ƙoƙarin jawota na kuka da faɗin, "Wlhy sai na kasheki, shegiyar yarinya annoba mai kama da arnan jeji baƙa mummuna". Nimrah dake kuka cike da ihu da cika kunne ta ce, "Niba shegiya bace ba, kuma ba arniya bace muguwa mai yanka mutane. Wayyo Ummana zata yankani kizo Umma, Kawu Tanimu na...." numfashinta ya wani jaaa alamar ɗaukewa saboda kafta da Nabeeha ta sake kai mata da wuƙar cikin rufewar idanu. Hakan kuma yayi dai-dai da isowar Zak-Shadow gabanta yay ƙoƙarin janyeta amma ina UBANGIJI ya riga ya ƙaddara sai ta sami Nimrah sai ko ta shata mata wuƙa a cinya. Ya rabbi, wani irin gigitaccen ihu da Nimrah ta saki Zak-Shadow bai ma san ya wanke fuskar Nabeeha da wani wawan mari guda biyu ba a lokaci ɗaya, wajen yin taga-taga zatai baya saboda gigita shima ta sharɓeshi a hannu, saboda kaifin wuƙar sai da ta fasa rigar shaddar jikinsa ta ratsa fatarsa. Amma bawon ALLAH bata kansa yake ba, ƙoƙarin zaro Nimrah data maƙale a lungu yake yi dan yarinyar tayi ɗif alamar ta suma. Ga jini tuni ya wanke rigarta ta dai-dai cinya inda Nabeeha ta yanke ta. Gaba ɗaya hankalin su Mammah ya gama tashi, Zak-Shadow dake rungume da Nimrah yana gama sauketa Mammah ta ɗaga rigar, ai a rikice tace, "Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un" dan yanka ne babba sosai damma jini ya jiƙe ƴar cinyar tata ba'a iya ganin girmansa da zurfinsa. "Muhammad karka sauketa muje asibiti". Mammah ta faɗa cikin tashin hankali. Suma su Uncle Jamilu gaba ɗaya sun gama rikicewa. Hatta Momyn Nabeeha rawa jikinta yake yi, tama kasa zuwa inda Nabeehar ta kife kan kitchen cabinet itama alamar taji marin maza. Sai da suka fice Uncle Nasiru da gaba ɗaya yay sumar tsaye ya tafi taga-taga zai faɗi, da ƙyar ya iya laluben bango ya dafe. A haka ya fice a kitchen ɗin shima yabar Momyn Nabeeha da jikinta ke rawa zuciyarta kamar zata fashe. Dan kasancewar a ƙarshe tazo sai idonta ke nuna mata akan ciki Nabeeha ta yanki yarinyar, kai tsaye ta kasheta... Acan compound ma su Ja'afar gaba ɗaya sun gigice saboda a yanda Dadansu ya fito da Nimrah shaddar jikinsa duk ta ɓaci da jini abinka da fara kawai sun ɗauka ta mutu ne. Hankali a tashe suke tambayar miya faru? Basu sami amsar kowa ba, sai kawai suma suka fara rige-rigen shiga mota....

★ Duk da raɗaɗin da hannunsa ke masa bata kansa yake ba, yana riƙe da Nimrah har aka gama mata ɗinki bayan an tsaida jinin da ƙyar dan anyi allura takai uku kafin aci nasara. Ya rabbi, duk mai imani dole yaji tausayin yarinyar, dan kuwa yankane bana wasa ba, gashi ya shiga sosai har ana iya ganin ƙashin ta. Su kansu asibitin da farko tsoron taɓata sukai sai da Zak-Shadow ya nema gigitasu da ihu. Dole suka dawo hayyacinsu sukai abinda ya dace. Tana sume akai komai aka gama, sannan suka farfaɗo da ita da dabarunsu. Allurar barci suka sake mata dan da ihu ta farka. Imran ya maida Zak-Shadow dake neman miƙewa ya zaunar yana ma nurse ɗin nuni da hannunsa. Ƙoƙarin nuna shi baya buƙata yayi, dan haka Imran ɗin ya ɗaure fuska ya kafa ya tsare kuma. Dole ya haƙura ya tsaya. Nashi ma da sauƙi amma fa ya yanku shima babu laifi, sai dai bai kai ko kwatar na Nimrah ba. Amma shima duk da haka sun masa ɗinki a wajen. Sun so riƙe Nimrah yace kawai a sallamesu za'a kula da ita a gida. Dole aka basu sallama da magunguna da dokar kawota ana dubawa suka wuce gida. Yanzu ɗin ma shine ya ɗauketa, ko'a mota tana riƙe a jikinsa har gida. Anan kuma suka tarar da tashin hankalin Uncle Nasiru, su Ismat da Biebah data dawo makaranta zagaye da shi suna kuka, sauƙin ma Biebah tai hankalin kiran matarsa, shine fa ta iso a rikice da likitansu datai kira a waya. Shine yaketa ƙoƙarin ganin nunfahsinsa ya daidaita sanda suke shigowa. Kai sukam dai wannan family sai dai suce Alhamdullah a wannan tsakani. Ganin al'amarin zai ƙwaɓe dole aka ɗauki Uncle Nasiru zuwa asibiti. Ga kuma Nabeeha can ta kulle kanta a ɗaki tana ihun kuka da rantsuwar idan Zak-Shadow bai saki Nimrah ba sai ta kashe kanta itama. Takaici ya saka babu wanda yabi takan haukan nata sai uwarta dake magiya da lallashinta su Amima na tayata. Da ƙyar da ƙyar dai suka samu ta buɗe. Uwar ta wani rungumeta tana kuka itama wai miyasa zatai mata haka. Miye-miye dai nan sukaita surutasu.....

"Tunda barci take kaje ka raba kayan nan da jikinka Muhammad, sam basu da ƙyan gani duk jini abinka da farin abu ƙara tada hankali yake". Mammah ce mai maganar cikin damuwa da sanyi, dan kuwa babu abinda ke mata kai-kawo idan ta kallesa sai lokacin da Abdul-rasheed ke shinfiɗe a ƙasa an lulluɓa masa babbar rigar shaddarsa data jiƙe da jini. Dama su kaɗai ne a ɗakin nata, daga ita sai shi sai Nimrah daya shinfiɗar a gado. Kansa ya jinjina yana miƙewa. Har ya fara tafiya ta sake dakatar da shi. "Dan ALLAH na roƙeka kada kace musu komai?". A karo na farko ya zubama Mammah hargitsatstsun idanunsa da suka mugun kaɗewa kamar wanda ya busa cocaine. Ita kanta Mammah sai da taji zuciyarta ta motsa saboda yanda idanun nasa suka koma. Magana yake son yi amma zuciyar ƴan maza tazo wuya ya ma kasa, sai kawai ta ce, "Dawo ka zauna".. Bata jira amsawarsa ba ta taso ta kama hannunsa ta maidoshi inda ya tashi. Baya iya bijire umarninta, dan haka ya koma ya zauna kawai kamar yanda ta buƙata. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya ita ta fita a ɗakin. Babu jimawa Ma'aruff yay sallama a ƙofar ɗakin cikin rawar murya alamar shima tsoron shigowa yake, dan sun san wanene Dadansu idan yana fushi, ya subahanallah abin babu ƙyau sam. Sum-sum ya shigo kansa a ƙasa kamar munafuki, kaɗan ya saci kallonsa yaga idanunsa a rufe suke, ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke tare da ajiye kayan a kusa da shi kaɗan. Idanunsa cike da hawaye miryarsa na rawa kamar wani ƙaramin yaro, ba komai ya kawo hakan ba kuma sai tausayin Dada, dan duniya basa ƙaunar abinda zai taɓa musu shi. "Kayi haƙuri Dada, ga kaya ka canja inji Mammah".. sanin ya jishi, yasan bazaiyi magana ba kuma yasa shi fita yana share hawayen da suka sakko masa. Wlhy badan Mammah ta hana su ba yau sai sunma Nabeeha dukan mutuwa a gidan nan, kuma da bazata kwanar musu a gida ba. Amma babu yanda suka iya Mammah ta kafa ta tsare. A falo ma sauran ƴan uwansa na zaune jigum-jigum, dan har su Ummi ma sun zo gidan tuni..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 63_

__________________

https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt

https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite

https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝 Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.

Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull