Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 32

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 32

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 32: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 32. ..........Washe gari da fitinar Nimrah suka tashi a gidan.…

4,061 words

..........Washe gari da fitinar Nimrah suka tashi a gidan. Dan tunda ta farka da asuba take ta kuka ƙafarta-ƙafarta. Haka suke zagaye da ita kowa na ƙoƙarin lallashinta. Yayinda Mu'azz ke tayata kukan shima. Sai kusan bakwai Zak-Shadow da bai san abinda ke faruwa ba ya shigo. Dan rashin samun isasshen barci a daren jiya shima yau makara yay ko sallar asuba a gida yayi ta. Dan haka sai yanzu yake fitowa daga sashensa, batare da ya ko kalla hanyar ɗakin Nabeeha ba, hasalima yayi zaton basa gidan, dan tunda suka dawo asibiti jiya baiga kowa ba tsakanin ita da uwar tasu da ƙannen nata, sai Jiddah ce ma da daddare ita da mijinta suka zo duba su tanata kuka da bashi haƙuri akan abinda ƴar uwar tata tayi. Tun shigowarsa falon yake jin kukan Nimrah. Kai tsaye ɗakin Mammahn ya nufa shima, inda ya tadda duk ƙannensa a ciki. Kowa kuma ƙoƙarin lallashin Nimrah dake kwance jikin Mammah yake yi, amma yarinyar nan taƙi sauraren kowa sai kwarara ihu take yi. Babu wanda yaji sallamarsa sai da ƙamshin turarensa ya shiga hancinansu da gyaran muryar da yayi sannan duk suka juyo, idonsa akan ƙafar Nimrah ya amsa gaisuwarsu, suko hankulansu na'a kan hannunsa shima. Cikin girmamawa da tsantseni ya gaida Mammah shima, tare da tambayarta jikin Nimrah data ɗan sassauta kukanta. "Alhamdulillah, sai dai inaga dole mu koma asibiti yanzu dan tunda asuba take kukan ƙafar, inaga tana mata ciwo ne, kaima yaya naka hannun?". Hannun nasa ya ɗan kalla, sai kuma ya kalla ƙafar Nimrah ɗin itama. "Ni kam babu wani damuwa Mammah, itama harda rigima dai". "Rigima kam ai dole ce, dan tana da hujjar yinta. Wannan ciwon ba ƙarami bane ga babba ma bare ita. Babbar damuwar ma taƙi cin komai ga tea nan har ya huce taƙi sha". Hannu ya miƙama Biebah dake riƙe da kofin batare da yace komai ba, ganin haka sai kawai Mammah ta miƙe tana faɗin, "To Biebah tashi ki nema na mutane abincin kari. Mu'azz tashi kaima muje kai shirin makaranta." Kamar zai yi kuka ya ce, "Mammah ni bazanje ba, zan zauna tare da Nina". Kallon da Zak-Shadow ya watso masa ya sashi sauka a gadon da sauri, sai dai idanunsa cike da ƙwalla. Murmurshi kawai Mammah tayi ta kama hannunsa suka fice. Caraf Nimrah ta ce, "Mammah ni dai ki dawo naki nake so...." Mammah na ƙoƙarin juyowa Zak-Shadow ya watsama Nimrah harara, sai ta sake taɓe baki zatai kuka. "Kika bari wannan hawayen suka zubo zaneki zanyi. Maza karɓa kisha. Kin zauna kinama mutane kukan banza amma bakinki baya mutuwa". "Ni dai dan ALLAH ka bita a hankali Muhammad, idan bazaka iya ba na dawo na bata". Ƙaramin murmushi yayi. "Shike nan Mammah zan bata". Suma su Bilal duk murmushin sukayi dan sunji daɗin ganin murmushin nashi. Shima zamansa ya gyara ya fara kai mata kofin bakinta, sai ko ta fara amsa babu musu. Sha kamar uku ta yatsine fuska tana kallonsa, ta ce, "Dada". "Uhhhm". Ya amsa mata a maƙoshi. "Kaima ƴar dabar ce ta jimaka ciwo a hannu?". Da mamaki ya zuba mata ido, a zuciyarsa yana ayyana (sai shegen surutu). Suko su Ja'afar dariya zancen nata ya basu, jira suke suji amsar da Dadan zai bata amma yayi shiru. Cikin kasa haƙuri Ammar ya ce, "Nimrah ƴar daba kuma?". "Eh Uncle Ammar". Ta faɗa kamar yanda taji Mu'azz na kiran kowansu da Uncle ɗin. Batare da jiran cewar kowa ba ta cigaba da faɗin, "Ummana tace ƴan daba ke riƙe wuƙa da yanka mutane ai. Kaga itama ta riƙe wuƙa ta yankamu ni da Dada, Dada kaima kayi kuka data yanka ka?". Ta ƙare maganar tana tsatstsareshi da idanu. Rasama abin cewa yay, sai kawai ya samu kansa da girgiza mata kai. Idanu ta waro masa sosai, sai kuma ta yamutsa fuska alamar motsin da tai taji zafi. Amma bata haƙura ba sake cewa, "Kenan kai baka yi kuka ba? Kuma baya maka zafi kamar nawa?". Nan ma kai kawai ya jinjina mata yana kai mata kofin shayin a baki dan ta ƙyaleshi da wannan surutun nata, gashi ta wani tsatstsareshi da idannunta. Kauda kanta tai gefe, dan in surutu nacin Nimrah itafa sai ta fetsar take jin daɗi, dan yanzu ma kai tsaye ta ce, "Dada jira na gama. Kai miyasa baka jin zafin ko kaima ɗan daba ne? Dan Lawwali yace min suna ƴan daba dake yankar mutum idan aka yanke su basa jin zafi kuma basa yin kuka". Anya shi kam ya taɓa gamuwa da magananniyar yarinya irin wannan? A zuciyarsa yake ayyanawa, yayinda su Ma'aruff ke ƙunshe dariyar dake cinsu. Dai-dai Nimrah ta kai hannu tana taɓa hannun Zak-Shadow dake kallonta kawai Momyn Nabeeha tai sallama, kafin su amsa ta shigo Nabeeha biye da ita sai su Ismat a ƙarshe, dan ita da kanta ta tattaro su wai su duba Nimrah su bama su Mammah haƙuri. Ai a bazata Nimrah tai wani uban tsalle ta haye jikin Zak-Shadow ta ƙanƙamesa tana fasa ihu da faɗin, "Wayyo Dada ƴar daba ta sake zuwa, ɓoyeni kada ta yankamu. Wayyo Dada wayyo zata ƙara yankamu shike nan ƴar daba mai wuƙa". Idan kunji ana sumar tsaye to ita Nabeeha da uwarta sukayi. Dan har tsakiyar kai kalmar (ƴar daba) ɗin nan ta dakesu. Yayinda su Bilal suka kasa haƙuri shi da Ammar suka shiga kwasar dariya. Suko su Amima yanda Nimrah tai uban tsalle ne da firgita ya basu dariya. Ita ko baiwar ALLAH da gaske tsorata tayi, dan tai bala'in shigewa cikin jikinsa, ƙarshe ma rigarsa ta ɗaga ta tura kanta ciki ta duƙunƙune, ALLAH ya sota ma tun a daka tsallen farko ya riƙe ƙafar tata mai ciwo a hannunsa, da ba ƙaramin fami zatayi ba kam, maybe ma ɗinkin ya farke tunda jikin ba wani ƙwari gareshi ba fatar ƙuruciya. Ihun Nimrah ya shigo da Mammah da Biebah, sai Mu'azz da har an masa shirin makaranta. A tsorace Mammah ta ce, "Wai mike faruwa?". Da ƙarfi Nimrah dake cikin rigar Zak-Shadow ta ce, "Ƴar daba ce mai wuƙa Mammah ta dawo zata yankamu ni da Dada, ku yankata Mammah kuma ku yayyankata kamar akuya". Duk yanda Yaya Ma'aruff da Yays Ja'afar ke dauriya a wannan gaɓar suma sai da suka dara. Sai Mu'azz ne abinka da yarinta ya hau gadon yana kamo hannunta da faɗin, "Ke Nina bafa ƴar daba bace su Aunty ne fa". Cikin kuka Nimrah ta ce, "Ƙarya kakeyi Ƴar daba ce, ranar ita ta yankamu ni da Dada, kuma tace saita kasheni bata sona. Muguwa! Muguwa in ALLAH ya yarda sai kin mutu yau kin haɗu da fatalwar kabari da walakiri mai ƙaton sanda". Cikin matsanancin ɓacin rai da kishin ganin yanda Nimrah ta shige rigar Dada, shi kuma ya wani zauna kamar gunki yana riƙe da ƙafarta kawai sai zuciya ta tokare ƙirjin Nabeeha. A zafafe ta ce, "Ubanki ne mugu ɗan daba shegiyar yarinya mayya, Momy ga abinda nake gaya miki nan kinƙi yarda kina wani muzo mu ganta..." tai maganar tana kai hannu zata damƙo ƙafar Nimrah dake hannun Dada. Abinda kuwa bata taɓa zato bane ya faru, dan kuwa caraf aka riƙe hannun nata, tana ƙoƙarin fisgewa cikin rufewar idanu Mammah ta ɗauke fuskarta da mari. Lokaci guda ɗakin yay tsitt, dan bama ita data ɗago a birkice taga Mammah ce mai marin ba hatta Zak-Shadow kansa ya girgiza, dan kowa yasan wacece Mammah akan kawaici.... Katse tunaninsu Mammah tayi, cikin faɗa ta ce, "Shin haka kike dama Nabeeha ko yanzu ne wannan halayyar banzar take neman shigarki? Wane shirme ne wannan kike yi akan yarinya ƙarama ƴar cikin ki, wadda da ALLAH ya baku haihuwa kin haifi wadda ma ta fita......" Hannun Nabeeha Momynta ta kwace daga wajen Mammah, itama a fusace ta ce, "Haba Hajiya A'isha yada haka da girmanki? Bakiga laifin Haysam shi da ya auri ƴar cikinsa ba sai laifinta, kishiya ko jaririyace ai yin kishinta ba haramun bane balle wannan hatsabibiyar yarinyar mai kama da an haifeta a tsakiyar tasha....." "K! Ya isheki haka Malama!!". Ma'aruff ya faɗa a zafafe tamkar zai kaima Momy duka. Cikin zazzaro idanu dan shima akwai zuciya kamar Dada ya cigaba da faɗin. "K har kina da bakin cema wata ƴar tasha bayan ga ƴar tasha nan kin haifa mai yankar mutane da wuƙa, ai gaskiya Nimrah ta faɗa ƴar daba kika haifa, sannan Wlhy mahaifiyarmu ta fita cikin idanunki idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki, dan akan Mammah da Dada komai zamu iya yi ciki harda koya muku tarbiyya dan naga tayi ƙaranci anan. Ku mi yasa baku san kawaici bane ba, idan badan Mammah ɗin ba wlhy da tun jiya mun yagalgala ku sai buzinku.". "Iyeee!!! Ma'aruff ni zakama rashin kunya?". "Anyi miki ɗin, in har zaki taɓa mana uwa duka ma zaki iya ci a hannunmu. Anata muku kawaici amma bakwa ganewa, damma kin samu ana gayawa ƴar taki gaskiya da gyara tarbiyyarta tunda ke kin kasa. Nimrah kuma ta zama matar Dada sai dai duk mai mutuwa ya mutu da baƙin ciki babu canji, wani wasan ma sai nan da shekarun girma....." Hannun Ma'aruff Mammah ta riƙo dan yi yake kamar zai kwashe Momyn Nabeeha da mari. "Ya isa haka". Cewar Mammah tana janye Ma'aruff baya. Kafin ta maida dubanta gasu Nabeeha, babu alamar wasa ko sassauci a tare da ita ta nuna musu hanyar fita, "Ga hanya Hajiya Hasiba, idan kuma kuka kaini bango to zan barku da Muhammad, kun san kuma abin bazaiyi ƙyau ba. Dan na fara gajiya da tausarsa akan wannan haukar na Nabeeha. Dan ALLAH ku barmu muji da abinda ya dame mu." Cikin ɓacin rai itama Momyn ta buɗe baki zatai magana Mammah ta sake ɗaga mata hannu tana girgiza kanta.... "Idan bazasu fita da arziƙi ba Mammah ki barmu mu fitar da su, dan mu nan munma ishesu Dada yafi ƙarfinsu, su ɗin banza ya tanka haukarsu". Yanzun kam Ja'afar ne mai maganar. Jiki a sanyaye Ismat tazo ta kama hannun Momynsu dana Nabeeha, shiyyasa tacema Momy kada aje bada haƙurin nan yanzu dan tasan nacin Nabeeha da mitar tsiya, sun kuma san wanene Dada a gidan. To gashi nan shi baima ko kallesu ba su Yaya Ma'aruff na neman lakaɗa musu duka. Duk haƙurin Mammah yau an sakata tayi abinda ko da kwatance basu taɓa gani ba a tsawon rayuwar zamansu gidan kusan shekara uku..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 64_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t

UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1FEkjc/

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Duk wannan bidiri da ake fa Nimrah na cikin rigar Zak-Shadow har lokacin, sai dai ta ɗan ɗaga tana kallon komai. Sai da taga su Nabeeha sun fita ta wani sauke ajiyar zuciya kamar babba tana fitowa, hawaye shaɓe-shaɓe a fuska ta kama dariya da faɗin, "Yauwa Uncle Ma'aruff kun kori ƴan daba. Ai dama kun zaneta. Kuma in ALLAH ya yarda sai ta mutu kuraye da fatalwoyi sun cinyeta ko ɗan ƙashi bazasu bar mata ba." shirmenta ya sakasu yin murmushi gaba ɗaya. Banda Zak-Shadow dake zaune shiru har yanzu. Sai dai Nimrah na gama fita a jikinsa ya ƙarasa ajiyeta kawai ya miƙe. Da sauri Mammah ta ce, "Muhammad ina zaka?". "Kiyi haƙuri Mammah". Abinda kawai ya iya faɗa kenan yay waje tamkar mayunwacin zaki. Kiransa Mammah keyi, dan indai yace tayi haƙuri zai aikata ba daidai bane amma ina. Daɗi ne ya kama su Bilal, dan sun san Dada aiki ne gamai ƙare ka. Mammah na yunƙurawa zata bishi su Ma'aruff suka riƙeta cike da makirci suna bata haƙuri, nan ko so suke Dada yaje yay abinda suke so kada ta hana....

(Sai daku ƙanen Dada 😂💃🏼)

>>><<★>><<<

"Aiki ya faɗa". Cewar Mr Specter yana wata dariyar mugunta cike da nishaɗi. Suma sauran dariyar suke har oga Jush duk da kuwa shi mutum ne bamai yawan dariya ba. Scythe ya ajiye kofin giyar daya kwankwaɗa, cike da izza ya ce, "Ka faɗi wasan Zak-Shadow". "Faɗuwa kan faɗuwa ma kuwa". Black Spider ya karɓe yana ƙyalƙyala dariya. Viper ya cigaba da faɗin, "Ai ban taɓa zaton shegen nan zai faɗi haka cikin sauƙi ba, babu ƙarya ya wahalar da mu." "Ni kaina ban zato ba Viper, ashe tun da can da haka mukai da tuni labarin wani ake bashi ba. Ashema fankamar banza yake shege zagaye yake da maƙiya yana tunanin mayaƙa ne. Na rasa miyasa suka kasa kaishi ƙasa tuntuni bayan ya gama shige musu hanci tun tuni." "Humm bakaji mi Garba nan yace ba, Janar ɗin nasu ne ya tsaya masa ai shiyyasa, dan ko yanzu yace ya kafa ya tsare akan bayanan cikin gida da ake haɗawa wai karsu fitar." "Ɗan wahala, yayi ya gama shima ta kujerarsa yake yi. Hatta Ministan nan sai mun ɓarar da shi a kujerarsa". "Wannan dole ne ai, shi kansa uban gayyar tasu dolene mu ɓarar da shi dan na fahimci badan wannan matakin da muka ɗauka ba bazai bamu haɗin kai ba." "Karku wani damu kanku, duk wanda yay mana kan kara sai mun masa na itace." Raven ya ce, "Ni bama duk wannan ba, ɗazun fa mutum nan ke sanar dani ya rasa kowane bayani daga ɓangaren cikin yaronmu. Kuma yaro mafi kwazo dake kusa da Zak-Shadow". Cikin zabura Oga Jush ya ce, "Kana da hankali kuwa Raven, amma shine baka sanar ba?". "Kayi haƙuri sir, nima yanzu zamu shigo nan nake ganin saƙonsa. Shiyyasa ma na ɗan dakata nai kiransa a waya kafin na shigo. Amma na bashi awanni uku akan ya tabbatar yazo da labarin da kai zai iya ɗauka". Lokaci guda sukai ɗif, kusan mintuna biyu oga Jush ya ɗauka waya. Kai tsaye yay kiran number Garba. Aiko sai gashi ya ɗaga yana magana ƙasa-ƙasa daga can. Cikin rufewar ido Oga Jush yace, "Ina son ganinka idan ba damuwa". A gadarance Garba ya ce, "Bazai yiwu ba dan ina kan aiki. Ka faɗi koma miye a haka ina jinka". Duk da Oga Jush yaji haushi sai ya danne, a ransa yana tabbatar da zai yi maganin Garba ɗin, ya dai gama musu aikin nan. "Okay ba damuwa, na samu rahoto ne mai ƙarfi yanzu cewar cikin yaran Zak-Shadow babu wani, kuma makusancinmu ne." "Miye rank ɗinsa?". "Lieutenant." Jimmm Garba yay alamar tunani, zuwa can ya nisa, cike da son nuna gwaninta ya ce, "Ka tura hotonsa. Duk da ina da tabbacin Ojo ne ko Rufa'i". Oga Jush bawani yasan sunan yaron bane ba, dan haka yace, "Okay yanzun nan za'a tura maka". Daga haka ya ajiye wayar yana kallon Raven. "Ka kira shi yanzun nan ya tura maka hotonsa a tura masa". "Okay Sir". Raven ya faɗa yana ƙoƙarin kiran Nanu. Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, cike da girmamawa daga can ya ce, "Ayi haƙuri sir ina kan bincike yanzu haka". "Babu damuwa, zamu samu hotonsa ne?". "Eh za'a samu sir". "Tura min". Cikin sakanni hoton Ojo ya shigo wayar Raven. Babu ɓata lokaci kuma aka turama Garba.....

<<<<<<>>>>>>>

Dariya sosai Lt Col. Garba keyi yana kallon hoton Ojo. Lallai yanzu ne wasa zai ƙara zafi kamar yanda yake so. Domin kuwa kowa yasan Ojo yaro ne makusancin Zak-Shadow matuƙa gaya. Yaransa biyu amintattu ya saka a sirri su bincika masa ina Ojo yake daga lokacin zuwa dare. Da girmamawa suka amsa masa kuwa. Ai ko awa ɗaya basu cika ba sukazo masa da bayanin tafiyar Ojo gida. Sai dai a labari mai ƙarfi ga wani abokin Ojo shine Ojo na wani hotel ne zaune da budurwarsa bai je gida ba. Hakan yay ma Garba daɗi, da kansa ya nufi hotel ɗin neman Ojo ɗin, bayan ya saka abokin na Ojo bashi number ɗin budurwar. Dan sun gwada kiran layin Ojo a kashe. Koda ya kirata ta sanar masa inda zasu haɗu ya sameta cikin damuwa da jin haushi. Dan a amsoshin da take bashi ya fahimci haka. Jin cewar daga fita sayo mata abu a mall ɗin kusa da hotel ɗin shine bai dawo ba yay shiru yana nazari. Kafin cikin jinjina kai yace ta bashi wayarsa. "Da wayar ya fita ai". Nan ma shiru Lt. Garba yayi, sai kuma ya miƙe ya mata sallama. Bai zame ko ina ba sai ofishin ogansa, ya labarta masa komai daya samo. Murmurshi Ogan yayi da girgiza kansa, ya ce, "Baka da dama Garba, ka dai dage da kai za'a kai Zak-Shadow ƙasa". "Na tsaneshi ne Sir! Tun tuni da na samu dama ma da wannan hannun nawa zan kashe banza wlhy. A wannan gaɓar kam idan na bari aka ƙara masa girman da ake shirin yi zan shiga uku ne kawai, Junior ɗina ne fa a makaranta ake shirin maidawa Senior ɗina akan aiki, haba impossible nabar Haysam ya koma samana, a yanzu ma da muke mate a aiki ba ƙaramin zafin hakan nake ji ba, shiyyasa akan wannan al'amarin sai inda ƙarfina ya ƙare". "Zan kuwa taimaka maka kodan kwatanta alkairin da kai min nima a baya. Yanzu kaje ka samu abokin shi yaron ya kai report ma ogansu kan basu san inda yake ba, kuma gidansu an kira ance baije ba zan ƙarasa sauran aikin." "Okay Sir!". Lt. Col. Garba ya faɗa cike da farin ciki yana miƙewa. Sai da ya ƙame ya sara masa sannan ya fita. Yana zuwa kuwa abokin Ojo ɗin ya nema, ya tsara masa komai. Shi ko aboki najin zai samu tagomashin arziƙi babu wani tunani yaje ya kaima ogansu report kamar yanda Lt Garba ya tsara masa. Oga yay shiru cikin nazari, dan kuwa Ojo yana ƙarƙashin Zak-Shadow ne, shi kuma ya kamata a kaima report ɗin rashin ganin Ojon, sai dai kuma a yanzu Zak-Shadow baya kan aiki yana hutu, a gefe kuma ga tataɓurzar da ake yi a kansa ma. Daya lissafa yaga lissafin bazai dai-daita ba sai kawai ya tura report ɗin shima sama. Tura report ɗin rashin Ojo anyi rashin sa'a ya faɗa a hannun ɗaya daga cikin membobin kwamitin bincike, wanda kuma shima sam baya ra'ayin Zak-Shadow. Aiko baiyi ƙasa a gwiwa ba ya kai ga kwamiti tare da tsatstsara zantukan da suka ja hankalinsu har suka maida hankali akan batun, tunda dama a wannan gaɓar bai kamata suyi sakaci da abu komai ƙanƙantarsa ba...

★ Bincike ya tabbata akan neman Ojo ta ɓangare biyu koma muce uku. Domin kuwa ga ƴan ƙungiyar duhu, ga Lt. Garba, ga kuma kwamitin bincike. Al'amarin kamar wasa aka girmamashi ya zama babba. Inda a karo na farko Nanu ya haɗu da shugabannin ƙungiyar duhu saɓanin da da bai san kowa ba sai Raven. Yau kam sai gashi ƙuru-ƙuru zaune a tsakkiyarsu sakamakon memory card daya bayar wanda sai daga baya ya tuna Ojo ya bashi tun a washe garin fitowarsu a jeji. Oga Jush dake kallon Nanu a karo na farko yayi maga cike da izzarsa. "Nanu kake ko?". "Eh Sir!". "Ka tabbatar wannan memory ɗin daga hannun Ojo ya fito?". "Kwarai da gaske. Dan kuwa a washe garin da suka fito a jeji kasancewar kasan shi bai samu wani rauni ba ya kirani ya sanarmin yayi videos sosai a wajen yaƙin, har naita mamaki shi taya ya iya yin hakan bayan suna ta ransu, shine yace shi mahaukaci ne zai shiga yaƙi, ai yana manne da Zak-Shadow dai. Dana fahimci da gaske yake sai nace mu haɗu to na amsa. Shine yace haɗuwa bazata yiwu ba na bari sai abubuwa sun lafa, idan kuma ya samu dama zai bada saƙo ta hannun budurwarsa. Ranar kuma muka haɗu da budurwar tasa ta bani saƙon da tambayata ko nasan inda yake, nace mata a'a gaskiya, shine ma dalilina na kiran oga Raven na shaida masa, dana duba saƙon kuma banga wani abu mai amfani ba sai jiya da dare dana zurfafa nazari na sake ɗakkosu na zazzage shine na samu wannan memory card ɗin". Cikin gamsuwa oga ke jinjina kai, kafin ya bada damar a saka memoryn kowa yaga mike ciki. Dandanan kuwa aka saita komai da magiji, sai ga komai daya faru a jeji tare da su Zak-Shadow dalla-dalla, duk da ba komai aka ɗauka ba, wani gurin ma bai ɗauku da ƙyau ba amma sun samu wurare masu muhimmanci da suka sakasu a farin ciki mara misali. Musamman inda Zak-Shadow ke dawowa jejin, da inda ake kashe mahaifin Umman Nimrah, da inda ake kashe Umman kanta, da inda bomb ya tada gidansu da yara da sojoji a ciki. Harda randa Zak-Shadow kema su Baban Nimrah tambayoyi a cikin tanti. Tsabar farin ciki oga da kansa yayma Nanu ƙyauta ta musamman. A take kuma suka turama wani ƙwararren masani dake wata ƙasa yay editing videon ta yanda duk iya son gano gaskiyarka baka isa tantance abinda ke ciki ba haka yake ba. Ana dawo da videon suka kalla suka sake maidashi a sabon memory card suka kira Lt. Col. Garba suka danƙa masa, akan suna son a saka memoryn a kayan Ojo. Hakan kuwa akayi, Lt. Garba ya danƙama abokin Ojo memory card ya mayar a kayansa dake cikin barrak, sannan ya koma ya kitsama ogansa batun binciken kayan Ojo, oga kuma ya ankarar da membobin kwamitin bincike. Suko dama yanzu basa wasa da abu komai ƙanƙantarsa akan wannan case, kodan matsin lambar da suke samu daga gwamnati........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 65_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull