Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 33
Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 33: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 33. ........Yanda hankalin su Janar ya tashi a wannan gaɓar har…
4,260 words
........Yanda hankalin su Janar ya tashi a wannan gaɓar har ba'a magana. Dan gaba ɗaya komai ya juye a yanda basa fata kuma basa zato da tsammani. Ga takurawa da suke samu daga gidan gwamnatin. Dole a karo na farko kwamitin bincike ya aikama Imran takardar gayyata. Wannan takarda kuma ta riskeshi a dai-dai lokacin da yake fitowa zai zo gidan su Zak-Shadow domin dubashi da duba jikin Nimrah. Harda matarsa, sai Ruƙayya da bataje makaranta ba jiya ta kwana da zazzaɓin mura. Ai ko tanata murna zata ga sabuwar ƙawar da Dada yace ya kawo mata. Komai Imran bai kawo ba game da wannan takarda ta gayyata, dan tunaninsa ma ai ana kan bincike ne game da su Dagger, yasan kuma za'a iya nemansu akan hakan. Suna shigowa gidan Zak-Shadow na fitowa daga sashen Mammah a zuciye, kallo ɗaya yay ma motar Imran ya ɗauke kai zai wuce. Imran ya san Zak-Shadow sani bana wasa ba, dan haka shima a kallo ɗaya da yay masa ya fahimci akwai matsala, ko gama kashe motar baiyi ba ya ɓalle murfin ya fito, cikin hanzari da ƙarfin jini irin na masu ɗammara ya sha gaban Zak-Shadow dake gab da shiga sashensa. Kallon kallo suka zubama juna shi da Imran ɗin. Cikin fushi Zak-Shadow ya ce, "Bani hanya". "Mi kake shirin yi?". "Zan bigeka na wuce". "Sai dai ka bugeni ɗin, amma in dai sai na matsa ka wuce bazaka shiga sashen nan ba. Sannan ina roƙonka ka ƙara haƙuri akan wanda kayi jiya. Nasan an maka ba dai-dai ba Haysam, amma ka dubi Uncle Nasiru ko dan nagartarsa ka ƙyale yarinyar nan da halinta." "Kasan mita sake min ne?". "Kayi haƙuri indai ba wani raunin ta sake jima wani ba. Haysam Please ina ƙara roƙonka kada ka biye mata ku zama ɗaya. Ka barta ita da kanta zatai dana sani wataran". "Bazan iya cigaba da zama da ita ba". "Dan girman ALLAH kar kace haka, dan dama abinda nafi tsoro kenan fiye da komai. Kai jigo ne ga wannan gida, abinda kayi zai zama mai sauƙi wajen koyi gasu Ja'afar. A wasu lokutan idan mata suka kuskure mana, ba rabuwa da su bane mafita horasu a cikin gidan ne mafita. Karka manta kaine kake min wannan huɗubar fa. Miyasa yanzu idanunka zai rufe? Ita dai bata isa sakaka sakin Nimrah ba, ta dinga kallon yarinyar kawai a matsayin matarka duk da ƙarancin shekarunta ya isheta hukunci mai zafi da zai fi kowanne. Amma dan ka rabu da ita ai tamaci nasara kenan". Kallonsa kawai Zak-Shadow yake yi, amma ya gagara sake cewa komai. Sai dai har yanzu zuciyar na'a maƙoshi, bai kuma gama tantance amsar kalaman Imran ɗin ba ko ƙin amsar. Dai-dai nan Ruƙayya da basu san da zuwanta ba ta kama hannunsa cike da farin ciki tana faɗin, "Dadana nazo". Idanu ya lumshe a hankali, sai kuma ya juyo yana kallonta, yanda yarinyar ke masa murmushi cike da farin ciki sai shima bai san ya mata murmushi kaɗan ba, sai kuma ya ɗauketa gaba ɗaya yana sauke ajiyar zuciya. Batare daya sake kallon Imran ba ya juya sashen Mammah. Imran ya girgiza kai yana murmurshin shima. Dan ya tabbatar badan zuwan Ruƙayyan ba da wahala ya fasa shigar. Shima bayansu yabi, dama matarsa harta shige. Ba ƙaramin farin ciki Mammah tayi da ganin Zak-Shadow ya dawo ba, ta sauke ajiyar zuciya idonta akan Imran. Dan ta tabbatar badan zuwan nashi ba za'ayi mara daɗi ne yau a gidan. Murmurshi Imran yayi shima, cikin girmamawa yay mata nunin ta kwantar da hankalinta. Cikin jinjina kai tace, "ALLAH yay muku albarka". Da Amin ya amsa yana hararar su Ma'aruff da suka tuttura baki alamar basu so ba, sun so yau Dadansu yaci ƙaniyar Nabeeha ne wlhy, amma Yaya Imran ya hana. Gargaɗi ya shiga musu da ido, dan haka suka haɗe hannaye alamar ban haƙuri. Daga nan suka maida hankali akan Aunty Hafsat matarsa dan ƴan gidanta ne sosai. Hasalima shi Ja'afar ƙanwarta zai aura mai suna Shariffa. Ma'aruff kuma ƙanwar su Imran ce sunanta Lailah. Dada kam tunda ya shigo bai kula kowa ba dama, kai tsaye inda Nimrah take ya nufa, itama hankalinta nakan Ruƙayya tunda suka shigo. Itama Ruƙayyan hankalinta akan Nimrah yake. Dada na ajiyeta kuwa ta koma kusa da ita ta zauna, cike da farin ciki ta ce, "Dada itace wannan?". Kansa ya ɗaga mata yana kallonsu su duka, dan daga gani hali zai zo ɗaya. Sai Ruƙayya ta rungume Nimrah, cikin raɗa ta ce, "Daga yau ke ƙawata ce inji Dada". Cike da farin ciki Nimrah tace. Eh. Ruƙayya ta ƙara rungumeta, sai kuma ta kalla ƙafarta ta ce, "Kinji ciwo ne?". "Ƴar daba ce a gidan nan ta yankani da wuƙa ni da Dada". Furucin Nimrah ya shiga kunnen kowa a ɗakin, hakan yasa Aunty Hafsat da Imran da Mammah da sai yanzu sukaji sunan da Nimrah ke kiran Nabeeha da shi duk suka kalleta. Su Bilal kam kwashewa sukai da dariya. Imran ya ce, "Nimrah ƴar daba kuma?". "Eh Yaya" tace da Imran kasancewar haka taji su Ja'afar na kiransa. Caraf Ruƙayya ta ce, "K ba yaya ba Dady". Kallonta Nimrah tayi itama, ta ce, "Ai su Uncle Ammar Yaya suke cewa". Mammah tai murmurshi a karo na farko, cikin katse taƙaddamar tasu ta ce, "Nimrah su Yayansu ne, ke kuma Daddy zakice keda ƙawarki Ruƙayya ko?". Kanta ta jinjinama Mammah tana murmushi, sai kuma ta kalla Ruƙayya ta ce, "Shike nan nace Daddy". Ruƙayya tai dariya itama. Sai shirmen nasu ya burge kowa, ciki harda Dada dake sauke ajiyar zuciya kawai. Ƙarshe ma ya fice a ɗakin, Imran ya tashi ya bishi.....
(())★(())★(())★(())
Bayan sallar Azhar Imran ya amsa kiran kwamiti dan dama ƙarfe biyu suka buƙaci ganinsa. Bai gayama Zak-Shadow ba ya baro gidan akan zai je wani waje ya dawo. Shima Zak-Shadow bai tambayesa ina zai je ba ya wuce cikin gida dan akwai aikin da yake so ya kammala. Zuwa gobe da safe yake so ya zauna da Ojo.
★★★
Sojoji huɗu ne a matsakaicin ɗakin binciken da aka shiga da Major Imran Abbas, duk da kuwa yasan ɗakin ba baƙonsa bane. Cikin nutsuwarsa ya kai zaune bayan ya miƙa gaisuwar girmamawa a garesu, sai dai a zuciyarsa ya fara wasi-wasi amma ya danne.. Brigadier General Abraham Yohana ne ya fara magana. "Major Imran Abbas ka sani wannan zamane na sirri. We expect full honesty from you". Ya ɗan ja numfashi yana jujjuya biro a yatsansa, kafin ya ɗan matsa kusa da teburin da takardun ke kai. "Before we proceed Major," ya sake faɗa cikin murya mai sanyi sai dai cike da iko, "this is an official military inquiry. Anything you say here will be part of the record. Are you willing to cooperate fully with this Board?" Cikin girmamawa Imran ya ce, "Yes, sir! I'll cooperate fully". Takardar gabansa ya ɗan duba, sai kuma ya ɗago yana sake kallon sauran jami'an da ke gefe, kafin ya dawo da idanunsa kan Imran. "Good. Let's start simple. A ranar 17 ga watan jiya May a ina Zak-Shadow ya kwana?". Ba ƙaramin dukan zuciyar Imran wannan tambaya ta bazata tai ba. Sai kawai ya samu kansa da zubama Brigadier General idanu na sakanni. A zuciyarsa hasashen miya kawo wannan tambayar yake? Brigadier General ya sake katse masa tunani da maimaita tambayar. Ajiyar zuciya Imran ya sauke. Kai tsaye ya ce, "Sir yana sansani tare damu". "Washe gari 18 fa?". Gaba ɗaya Imran ji yake kamar zai rikice, amma ya ce "Itama haka...." "Ka tabbatar?". Shiru yay ya kasa cewa komai. Brigadier General ya cigaba da faɗin, "To amma miyasa kuma anan bayanansa ya saɓa da abinda ka faɗa yanzu?". Yay maganar yana yin nuni da projector daya bada umarnin a kunna. Ana kunnawa kuwa videon ranar da Zak-Shadow ya koma jejin bayan an kai hari na biyu garin Marke da Gangare ya bayyana. Tun daga isowarsa sansani a mashin da shigarsa mota shi da karnukansa har isowarsu Gangare da bayanin da yayi cikin ɓacin rai kan abinda ya faru, inda yace baya nan cikin kwana biyu kacal sun bari an musu irin wannan illar ya maimaita kansa yafi sau huɗu dan a sake tabbatar da ƙaryata abinda Imran ɗin ya faɗa ma. "Har yanzu kana akan bakan ka na cewar yana nan ɗin komai ya fara faruwa?". Lt. Col. Peter Okon ya faɗa yana tsatstsare Imran da idanu. Shiru Imran yayi zuciyarsa na wani irin dokawa, zuwa yanzu ya fara hasaso al'amari mai girma, dan kuwa ba rami miya kawo rami. Babu dalili miya kawo ɗaukar video sirri akan su a lokacin da suke kan aiki. Imran nada haƙuri da sanyin hali, amma akan Zak-Shadow bashi da haƙuri da kawaici. Dan haka cikin tsaurara harshe a karo na farko ya ce, "Sir! Akwai makirci a wannan al'amarin kwarai da gaske. Eh naji kai tsaye zance Haysam baya cikin sansani tun daga ranar farko da aka kaima sojojinmu hari. Domin kuwa yazo ziyartar gida akan abinda ya shafesa, hakan kuma bawani abu bane a hukunce mun sani, musamman da idan mukai dubi da dalili mai ƙarfi ne ke iya saka Haysam motsawa daga sansani, sai kuma ya tabbatar babu wata matsa sannan baya iya wuce kwana biyu duk tsanani". "Eh muma bamuce laifi yayi ba na zuwa gidan, sai dai miyasa ba'a kai harin ba sai bayan ya tafi? Kuma yanayin harin yay dai-dai da abinda ya faru shekaru uku da suka wuce." Aka sake kunna wani video da aka ɗauka daga rikicin shekara uku da ta wuce, lokacin da Special Recon Unit ta jagoranci farmaki a yankin Gulmadu. Hoton ya nuna Zak-Shadow yana magana da sojoji, sai kuma a nan gaba aka ga wuta ta tashi, kamar umarnin harin daga gare shi ne. Wani kalar rinewa idanun Imran sukayi, sai dai kafin yay magana Colonel Galadima ya ce,........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*66
.........."Major Abbas, wannan fa, dukansu dai gasu da idonka ka gani. Ka tabbatar nan ma shi ne Lt Colonel Haysam Abdul-rasheed". "Eh shi ne sir! Amma wannan video ba irin wanda muka sani bane shima, tunda shi muna da copys muma". "Me kake nufi Major Imran?". Ji Imran yay kamar ya zagi mai maganar, amma ya dake. "Wannan footage an canza shi. Ba haka abin ya faru ba shima wancan lokacin. Lokacin da muka samu umarnin komawa kan yaƙi waccan ranar, ba daga Lt. Colonel Haysam ya fito ba. Communication link ɗin mu ya yanke tun kafin wuta ta tashi". "Are you suggesting falsification of evidence, Major?". "Sir! Duk wanda yasan wanene Lt Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu da kwazo da sadaukarwarsa yasan hakane kuma zai bada tabbaci irin nawa kai tsaye. Wlhy a kishin ƙasa da jajircewar aiki irin ta Haysam ansan wannan tatsuniyar kuskurene dangantashi da irin wannan zargin. Duk da kuwa bansan ma'anar yin hakan ba." Yanda yay maganar cikin zurfin lafazi dake nuna ɗaci yasa ɗakin ya ɗan yi shiru na wani lokaci. Kafin zuwa can Chairman ya ɗan kalli sauran mambobin, ɗan ɗaga kafaɗa ɗaya daga cikinsu yayi, cikin nuna halin ko'in kula ya ce. "Major Imran zargi ko bincike ga aikin soja ba laifi bane ba ka sani, karka canja mana manufa mu muna akan aikinmu ne kawai. Abu na gaba kalli wannan". Aka sake kunna tv. Yanzu kam sune a cikin gidan Malam Hamisu mahaifin Umman Nimrah, a lokacin da aka harbesa ga handcuffs a hannunsa. Sai fitowa da Umma a dirom da wani yayi, sai dai abin mamaki saɓanin yanda suka sani yanzu babu bindiga a hannun yaron, sannan sai da aka fito da Umman ne aka harbi mahaifinta, kai tsaye kuma harbin nan daga Zak-Shadow yake, sannan itama Umman harbin da Zak-Shadow yayima yaron dake riƙe da ita kai tsaye sai ya koma kanta, hakan na nufin nan ma Zak-Shadow ne ya kashe ta. Na ƙarshe umarnin Zak-Shadow akan yaran nan da aka ɗorama bindiga, maimakon sakinsu da ya saka akayi sai ya nuna harbinsu akayi, sannan shi da Zak-Shadow ɗin da Captain Musa suka fito a gidan, suna fitowar ne Kuma bomb ya tashi da sojojin da abun ya faru a gabansu duka da mutanen gidan...." Ai Imran ma bai san ya furta, "Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wlhy Sir wannan duk ƙarya ne, tayaya ma Zak-Shadow zai kashe wanda ya kuɓutar da kansa...." nan fa ya warware ainahin komai daya faru a wajen, amma suka nuna su basu da hujjar yarda tunda bada su akai ba, sannan komai daya faru gashi sun gani a video. Abu na ƙarshe a duk sojojin dake wajen da zasu iya bada shaida an kashe su ta hanyar bomb, shi da Zak-Shadow kawai suka rage shima Captain Musa an kashe shi a cikin rububin yaƙi, kuma bullets ɗin jikinsa na sojoji ne bana ƴan ta'addar ba. "Mutum na ƙarshe da muka tabbatar yana wajen tare daku shine yaron Zak-Shadow Lieutenant Ojo. Kuma a yanzu an rasa inda Ojo yake kwana biyu kenan. A bincike kuma an gano ka san komai a kansa, dan kai ne ma kukayi wayar ƙarshe da abokin Ojon ya sanar maka inda yake". Imran ya cije lips da ƙarfin gaske, ransa na ƙuna ya ce, "Tabbas Ojo yaron Haysam ne na amana, ya kuma san abubuwa a kansa matuƙa, sai dai bayan operation ɗin nan mun gano yana aika bayanan sirri ga wani waje, shine dalilin ɓoyesa da nayi". "Mi yasa baku kai rahoto ba?". "Sir bamu kai rahoto ba saboda muna son tabbatar da hujja kafin mu kawo. Hasalima Zak-Shadow bai san na kama Ojo ba sai a washe garin jiya". "Kana dai nufin kai da Lt. Col. Haysam Abdul-rasheed kuka ɓoye bayanin?". "Sir! Mu ba mu ɓoye bayani ba kamar yanda na faɗa. Muna kokarin tabbatarwa ne kafin mu fallasa". "Shike nan zamu riƙeka anan. Wannan magana kuma duk ka rubuta a takarda Major Abbas. We'll need a full written statement from you by 1800 hours. Kuma har inda Ojo yake a yanzu". A maƙoshi Imran ya ce, "Yes, sir." Sai kuma ya miƙe domin fita, yana jin zuciyarsa na bugawa, dan kuwa yasan abubuwa sun riga sun ƙwaɓe, sun kafa dokar zamansa anan dan kar ya fargar da Zak-Shadow. Bayan an kaishi wani sabon ɗakin binciken sirrin ɗaya daga cikin jami'an da suke tare da shi wanda harda Col Faro ya ɗan kalle shi gefe cikin raɗa ya ce cikin muryar da ba kowa zai ji ba. "Be careful, Major. This is deeper than you think." Daga haka ya ajiye masa takarda da pen ya juya shima ya fita bayan ɗayan ya sake gyara camara dake ɗakin ta yanda duk wani motsin Imran za'a gani. Sai kuma ga wani sojan ya kawo masa ruwa da kofi ya ajiye shima ya juya ya fita aka rufe ɗakin. Maimakon fara rubutun kwantar da kai kawai Imran yayi a jikin kujerar ya wani lumshe idanu yana furzar da iska mai azabar nauyi ta bakinsa....
Wato mutane na al'amarin nan sai addu'a fa kawai, ga shi Zak-Shadow bai san ina Imran ya tafi ba balle yay wani ɗan hasashe😭.
><><><><><><><><
Tun aunty Hafsa na kallon agogo da tsammanin dawowar Imran akan lokaci ya maidasu gida kodan yara da suke dawowa ƙarfe biyar daga makaranta har ta fara magana. Aunty Ummi ta ce, "Inaga dai yayi nisa ne, amma nasan shima ai hankalinsa na nan ɗin. Nayi mamaki ma da naga Dada yanzu a gida duk tunani na ɗazun tare suka fita wlhy". "Ni kaina na zata suna tare, ashe shi kaɗai ya fita. Damuwata ma yaran ne, dan mai aiki na bata nan taje ganin gida. Nasan kuma nan da ƴan mintuna driver zai ɗakko su". "To ko dai kiranshi zakiyi ya kawo su nan". "Kuma da gaskiyarki bari na taɓashi muga". Tai maganar tana ɗaukar wayar ta. Dai-dai nan Ammar ya shigo yana faman ɓata fuska da jaka goye a bayansa. Cikin son ƙular da shi Mimi dake fitowa a kitchen ta hau dariya da faɗin, "Wai da gaske fushin komawa makarantar kake Ya Ammar?". Harararta yayi, cike da haushi ya ce, "Ƴar sa ido ina ruwanki da ni to". "Niko nake da ruwa da kai, amma tunda kace haka shike nan bara na koma da dambun nama na". Da sauri ya nufota yana faɗin, "Yi haƙuri, haba mu tagwaini". Dariya duk falon aka saka masa. Shi dai bai kulasu ba yaje yana lallaɓa Mimi. Sai ko gashi bayan ta gama ja masa rai ta ɗakko masa wata ƴar jaka mai ƙyau, amsa yay cike da farin ciki, dan yasan kayan daɗi ne kala-kala ba dambun naman kawai ba. Saboda haka take masa wannan gatan duk da kuwa bata da abokin faɗa sama da shi a gidan kullum saboda sakonta ne. A lokacin ne suma su Yaya Ma'aruff suka shigo gidan, suka kuma zagayeshi wai sai ya basu sun gani. Shi ko ya ƙanƙame jaka yaƙi basu.... "Kasan Ammar idan ka bari Magriba tai maka a gidan nan sai ranka ya ɓaci, ka zauna karkazo ka wuce". Tsitt falon yay duk suka juyo dan kuwa Dada ne a bazata ya shigo kuma yake maganar ga Ammar cike da gargaɗi. Ammar kamar zai yi kuka ya ce, "Dada dan ALLAH ka bari sai da safe, ALLAH na maka alƙawarin bazan wuce gobe ba". Harara ya zuba masa kawai ya juya zai fita abinsa. Ganin zai koma Mammah dake bama Nimrah abinci a baki ita da Ruƙayya ta ce, "Muhammad wai Imran fa? Tun ɗazun Hafsat na jiransa ga yara zasu dawo daga makaranta amma shiru. Nazata ma tare kuka fita ashe kai kana gida". Tsayawa yayi, sai kuma ya juyo bayan ya kalla agogon hannunsa. "Shi kaɗai ya fita Mammah, nima banyi zaton zai jima haka ba. Amma kin kira shi ne?". Yay maganar ƙarshe yana maida kallonsa ga Aunty Hafsat. Cike da girmamawa ta ce, "A'a tun dai kiran farko dana masa bai ɗaga ba. Nayi zaton ko wani uzuri yake yi". Bai sake cewa komai ba ya ciro wayarsa a aljihu ya daddana sannan ya kai kunne. Sai dai batama shiga ba. Mamaki ya kama shi ya sake kira. Nan ma taƙi. Fuska ya ɗan yamutsa kaɗan, idonsa akan wayar ya ce, "Wayar ma yaƙi zuwa, maybe yana a inda ba network. Ki shirya Bilal ya kaiki kawai". Amsa masa tayi da to. Har ya sake juyawa zai fitan ya sake juyowa. Idonsa akan su Aunty Momy ya ce, "Kuma ku tashi ku tafi gida. Karna dawo na samu kowa tunda ku ƙafarku bata gajiya da yawo". Kafin ma su fara masa magiya ya fice abinsa. Aiko kamar zasuyi kuka. Sai dai sun san tunda ya faɗa dole haka za'ayi. Su Yaya Ma'aruff kuwa suka tasasu gaba da tsokana abinka da kowa nada nashi sakon. Koda suka koma roƙon Mammah tasa baki tace ita babu ruwanta. Ammar kawai zata roƙama alfarma shima saboda yamma ce bata son yabi hanya daga nan har Zaria. Cike da farin ciki Ammar yazo ya zauna yana rungumeta.. Caraf Nimrah da bata gani ta ƙyale ta ce, "Uncle Ammar kuma baka jin kunya". Cikin ɗan waro ido ya ce, "Nimrah kunyar mi kuma". "Rungume Mammah, kuma naga kayi ƙatoto". Mi za'ai inba dariya ba. Itako ko a jikinta tama cigaba da wasanta ita da Ruky....
★★
Duk wannan abun da ake su Nabeeha na ƙunshe a sashenta. Wai ashe bata da lafiya har likita suka kira mata. Su su Mammah basu sani ba. Amma shi Zak-Shadow yana sane tunda yana sashen a ɗakinsa tun ɗazun. Yanzu ma bayan ya fita a sashen Mammah Momynta ke shigowa ita da wata mata suka shige sashen. Ko a kwallar rigarsa ya koma can ƙasan rumfar bunu dake a gidan ya zauna, hankalinsa da tunaninsa duk suna kan ina Imran ya shiga..........✍🏼*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 67_
__________________
https://chat.whatsapp.com/DMVSa4G3a9sDd8Jjgm0mzs?mode=ems_copy_t
Kin Dade kina Neman group din dazaki tallata kayanki kyauta Baki samuba to ki hanzarta shiga free advert group na EASHAS BITES AND BEAUTY domin tallata Kayanki kuyi saving number dinta domin samun shiga group dinnan akwai members Sama da 500+ aciki💃💃💃💃👇👇👇👇
wa.me/ +2348064705686
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........10:30pm
Aunty Hafsat ta kira wayar Biebah tana tambayarta ko Imran ya dawo nan gidan. Biebah ta ce, "A'a gaskiya Aunty, ni dai banga Yaya Imran ba, dan sanda na dawo islamiyya ma Dada kawai na tarar a compound zaune. Kuma Mammah tace baku jima da wucewa ba lokacin." "Har yanzu Dada na gidan?". "Eh yana nan, gashi ma tare da Mammah na bashi?". Kafin ma Aunty Hafsat tayi magana Dada yay ma Biebah alamar ta bashi wayar. Cikin girmamawa ta kawo masa. Sallamar da yayi ta saka Aunty Hafsat saurin gaisheshi. Ya amsa a taƙaice da tambayarta "Har yanzu bai dawo ba?". "Eh wlhy Yaya har yanzu, ni tsoro ma ya fara kamani. Dan sanda muke fitowa gida zamu taho nan gidan dama wasu mutane kamar jami'anku sunzo sun bashi wata takarda. Sai dai ban san ta micece ba amma naji yana ce musu zuwa 2 ɗin zai je. Daga haka ya shigo mota kuma bai sake min zancen komai ba". Cike da mamaki Zak-Shadow ya ce, "Takarda? kuma jami'an mu?". "Eh, dan ɗaya akwai wandon sojoji a jikinsa". "Okay ina zuwa to. Kada ki damu babu abinda zai faru". Yanke kiran yayi batare da ya jira amsarta ba. Mammah da ke kallonsa ta ce, "Lafiya kuwa?". "Babu komai Mammah ina zuwa". Yay maganar yana miƙewa ya fita. Duk da kallo suka bishi har su Bilal. Dan suna zaune ne dama ana hira.
A waje Zak-Shadow yay ɗan tsai cikin nazari. Zancen Col Faro ne ya shiga dawo masa na jiya. Dan haka ya zaro waya a aljihu yana jinjina kai da cije lips yay kiran wata number. Ana ɗagawa daga can aka gaishe shi, a taƙaice ya amsa. Kafin ya ɗora da gaɗin, "Kaga Imran ya shigo Headquarter yau?". "Eh tabbas Sir! Na fito salla ni da Faruk naga motarsa ta shigo, sai dai banga fitarsa ba dan na koma office ina wani aiki". "Bincika min ƙarfe nawa ya fito, sannan office ya shiga ko mi?". "Okay sir!". Wayar ya katse ya gyara tsaiwa, ko mintuna huɗu ba'ai ba wancan ya sake kiransa. Koda ya ɗaga sai ya fara masa bayanin daya sakashi yin cak. "Sir! Na duba har yanzu motarsa na nan. Yanzu kuma nake jin ƙus-ƙus ɗin wai zama akai da shi na musamman, a yanzu haka ma yana a ɗakin bincike". Shiru Zak-Shadow bai ce komai ba tsahon sakanni, sai kuma ya katse kiran yana mai furzar da huci. Yanzu kam ya fahimci komai. Dan haka yay kiran Col Faro, dan ya tabbatar a wajensa ne kawai zai ji abinda yake so. Sai da ta kusan tsinkewa ya ɗaga. Baima jira ko gaisuwa sunyi ba kai tsaye ya ce, "Imran na tare da ku?". Sai da Col Faro yay ɗan jim sannan cikin tsantseni ya ce, "Kada ka tada hankalinka. Na tabbatar zuwa safiya zasu barshi ya fita". "Bazai yiwu ba, gani nan zuwa". "Kayi haƙuri dan ALLAH kar kazo, dan zuwanka haɗari ne babba ga Major Imran. Ka bari muga abinda safiya zatayi. Ni kaina yanzu ina ƙoƙarin son sanin mi suka tattauna da shi ne dama zan kiraka na gaya maka. Amma zuwanka yanzu zai iya sake ɓata komai". Da wani irin zafin rai Zak-Shadow ya kaima motar da yake jingine a jiki naushi, batare da yace komai ba ya yanke kiran. Ya jima zuciyarsa na hanƙoro a cikin ƙirji, kafin daga ƙarshe ya danne komai ya koma wajensu Mammah. Wayar Biebah ya amsa yay kiran Aunty Hafsat. Ya ce ta kwantar da hankalinta akwai aikin da Imran keyi amma zuwa safiya in sha ALLAHU zai dawo gida. Bai jira amsarta ba kuma ya yanke. Koda Mammah ta sake masa tambaya amsar daya sake bata kenan itama. Daga nan ya musu sallama ya wuce. Tun daga nan ta sake fahimtar akwai matsala, sai dai tasan bazai faɗa ba...
Sam Zak-Shadow baiyi wani barci ba a wannan daren. Ya kwana ne akan ƙafafunsa yana salla da kuma zaman lissafe-lissafen abubuwa a taƙaice. Dan ya gama auna komai ya kuma fahimta gwargwadon hangensa. Ya auna hanyoyin kuɓuta da tsaida gaskiya yaga duk wadda yabi zai iya saka Imran a haɗari, sai kawai yay murmushi yana mai tabbatar ma kansa amsar hanyar ƙarshe kawai. Duk da ya san zai saka Mammah da ƴan uwansa a tashin hankali. Amma zai samu abinda yake so a ƙarshe koda kuwa sunci nasara a kansa shi Imran zai ƙarasa abinda yake fata kuma shi zai ci nasarar sannan zai kuɓuta. Sai kawai ya sake yarda zai sadaukar, dan ransa fansa ne ga Imran balle ma wannan harin kai tsaye nashi ne. Da wannan hukuncin ya kwana a ransa, dan haka duk wani abinsa mai muhimmanci ya killacesa waje guda a ɗakin ya kuma ajiye wasu domin Imran........
<<%>><<%>><<%>>
WASHE GARI.... 7/6/2013.
8:30am