Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 34

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 34

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 34: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 34. Kamar yanda Zak-Shadow yay tsammani a wannan safiya ya samu…

4,326 words

Kamar yanda Zak-Shadow yay tsammani a wannan safiya ya samu baƙuncin ɗan aike daga kwamiti. Ya jima yana kallon takardar gayyatar mai tambarin Defence Headquarters a jiki. Sai kuma ya ɗan saki murmurshin ƙasaita. Gefe ya ajiyeta kawai ya cigaba da shan coffee ɗinsa, su Ja'afar dake kallon takardar cikin son sanin mike a ciki dan suna tare da shi ne a tsakar gida tunda suka dawo daga motsa jiki da suka bishi bayan sallar asuba. Basu koma ciki ba anan Biebah ta kawo musu coffee shine suke zaman sha har aka kawo takardar. Ƙasa-ƙasa Ma'aruff ya ce, "Dada badai aiki zaka koma ba tun yanzu? Wlhy bamu gaji da ganinka ba, dan ALLAH ka yi kamar wata uku". Cikin marairaicewa Ja'afar ma ya ce, "Eh dan ALLAH Dada. Kaga ma ko warkewa fa baka gama yi ba yankan hannunka." Rasama mizai ce musu yayi, suko sai sake shagwaɓe masa suke kamar wasu yara ƙanana. Sai kawai ya ce, "Tom naji, ku tashi kuyi shirin kasuwa nima zan fita ne". Badan sun so hakan ba suka amsa da to, dan su fa idan yana gida ko fita kasuwar basa son yi, tunda duk shagunan akwai yara, su matsayin oganni ne ko sunje zaman office ne. Sai da ya tabbatar sun shige ciki sannan ya ɗauki takardar ya duba. (Directive from the Board of Inquiry. Defence Headquarters, Abuja. Ana gayyatarka domin bayyana a gaban kwamitin bincike a yau 1:pm. Subject: Preliminary Inquiry concerning recent allegations on classified operations. Brig. Gen. Abraham Yohana, Secretary Board of Inquiry).

Ƙasaitaccen murmushi ya sake saki mai cike da ma'anoni, sai kuma ya maida takardar ya ninke ya ajiye. Daga ƙarshe ma ya miƙe ya nufi sashen Mammah. Kusan awarsa ɗaya a sashen Mammah ya koma nashi sashen, tun faruwar rikicin Nimrah bai kuma saka Nabeeha a idonsa ba, bai kuma nemeta ba sai dai yana ganin gilmawar ƙanenta da Mamansu da bai san mitake a gidan ba har yanzu. Shi kuma bashi da lokacin tambaya ko neman ba'asi, idan taso ta dawo gidan ma da zama matsalarsu ce wannan. Yana buɗe ƙofar ɗakin nasa akan Nabeeha ya fara sauke idanunsa, tana zaune a kujerar dake kallon kofar. Kwanaki kaɗan har ta rame, ga idanu a kumbure jajur alamar cikin kuka take har yanzu. Ɗauke idanunsa yay tamkar bai ganta ba, sai ma ya hau ƙoƙarin cire kayan jikinsa hankali kwance. Ai ko ta sake ƙuluwa, zuciyarta na ƙuna da rawar murya ta ce, "Saboda kayi sabon aure kake wulaƙanta ni?". Babu alamar ya jita ma, dan hanyar bayi ya nufa, da sauri ta tashi tasha gabansa, ya tsaya cak yana kallonta da birkitattun idanunsa, kasa jure kallonsa tayi ita kam, dole ta risinar da idannunta tana ƙara ƙarfafa kanta ta ce, "Haysam idan kana son zama dani ka ɗauki yarinyar can ka maidata inda ka ɗakkota, ka warware tatsuniyar gizo-gizon daka ƙulla kuma". Ƙirjinta dake sama da ƙasa alamar da ƙyar take tattaro maganar tana gaya masa ya zubama ido, yanda takai ƙarshen zancen nata da rumtse ido sai tama bashi dariya. Amma sai ya dake abinsa kai tsaye ya ce, "To Mama Nabeeha idan naƙi fa?". Kamar zatai kuka dan takaicin Mama daya kirata ta ce, "Zan koyi abinda bazai mana daɗi ba ni da kai". Maimakon amsata zagayeta kawai yay ya wuce bayi a binsa. Wayyo jitai kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu. Zuciyarta na bata shawarar ta jirashi wata na ingizata ta tafi kawai. Harta wuce fuuu zuwa kofa sai kuma ya dawo jikin ƙofar bayin, cikin fashewa da kuka da masifa ta ce, "Wlhy idan har baka yi abinda nake so ba nabarka har abada, mugu kawai azzalumi ALLAH ya isa ban yafe ba. Ga gidan nan na bar muku macuta". Daga haka ta fice fuuu. Duk abinda ya faɗa yaji, amma yay kamar bai jin ba ya cigaba da wankansa. Itako tana fita ɗakinta ta wuce, kai tsaye tace ma Momyn, "Momy muje kawai". Murmurshi Momy ta saki a karo na farko na cin nasara, kafin ta ce, "Yaƙi yarda kenan?".. Bata tanka zancen ba ta ce, "Momy ni dai muje". Ba ƙaramin tashi hankalin Ismat yayi ba jin gidan zasu bari, ita kam ai ita za'a shukama tsiyar sakata yin nisa da masoyinta Ja'afar. Sai kawai ta sanya musu kuka da magiyar ita dai kada su tafi. Abi komai a hankali. Ai wani mari mai lasisi Momy ta bata, daga haka bata sake iya magana ba suka tattara kayansu da dama sun haɗa tun jiya Hinde ta dinga fita da su wajen mota. Tana son zuwa ta sanar ma Mammah tana tsoro, dole ta haƙura a gaban idonta Momyn Nabeeha taja mota ita da Nabeeha a gaba su Amima a baya suka wuce. Sai a lokacin ta falla zuwa sashen Mammah ta sanar mata. Mammah zata tada hankalinta ƴaƴanta suka zagayeta da daɗin baki. Koda Zak-Shadow ya dawo sashen yin breakfast da tai masa maganar shima cikin rashin damuwa ya ce, "Mammah ba ita ta zaɓi haka ba. Ki saka musu ido kiga iya gudun ruwansu kawai yafi sauƙi. Yanda ta tafi da ƙafarta da ƙafartata zata dawo". Ba yanda zatai dole tai shiru.........✍🏼

Mu gayama ƴar Daba gaskiya ko muyi shiru duniya ta gaya mata 😂🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️?.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 69_

__________________

https://chat.whatsapp.com/DMVSa4G3a9sDd8Jjgm0mzs?mode=ems_copy_t

Kin Dade kina Neman group din dazaki tallata kayanki kyauta Baki samuba to ki hanzarta shiga free advert group na EASHAS BITES AND BEAUTY domin tallata Kayanki kuyi saving number dinta domin samun shiga group dinnan akwai members Sama da 500+ aciki💃💃💃💃👇👇👇👇

wa.me/ 2348064705686

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Motar shiru Zak-Shadow na murza siyarin a hankali tamkar baya so, a gefensa Imran ne zaune cikin alamu na tunani mai zurfi. A gabansu motar sojoji ce haka ma bayansu. Sai dai sukai tafiyar fin mintuna goma tsakaninsu da inda suka baro a karo na farko Zak-Shadow yay magana idanunsa akan titi. "Ina son su Ma'aruff su dawo kusa da Mammah". Kallonsa Imran yayi na sakanni, kafin cikin damuwa ya ce, "Saboda mi?". "Saboda bazai yiwu mu duka muyi nesa da ita ba." "Wace irin magana ce wannan? Kai ina zaka da har zakai mata nisa?". Murmushi mai yalwa Zak-Shadow yayi yana sake juya sitiyarin cike da ƙwarewa, sai kuma ya ɗan kalla Imran fisha ya maida idanunsa kan titin. Kamar bazai ce komai ba dan har Imran ya fidda rai da samun amsa, kafin ya ɗan furzar da iska. Cikin komawa serious ya ce, "Imran nasan ka san abinda nake hange, kuma bana jin akwai abinda zai hanashi faruwa sai wani ikon ALLAH. Mutanen nan sun gama shirya komai kafin su tunkaremu, kuma zaka tabbatar da hakan yanzu babu jimawa. Dan haka ina son a tsaida aikin gidansu ai musu gini anan cikin gidan tunda akwai fili ta baya. Idan zai yiwu kuma a canja tsarin gidan gaba ɗaya ma har Bilal da Ammar su samu nasu kowa ya zauna a ciki. Ka fara zama da su Ja'afar ɗin kasan abinda muke da shi a ƙasa, dan naso yin hakan dama sai dai nasan lokaci ya ƙure......" Cikin ɓacin rai Imran ya katseshi da faɗin, "Wai miye kake faɗa haka. Na gaya maka ka daina min irin wannan wasan." "Humm! Imran ba wasa nake ba". "To ka sani kuwa duk inda kake muna tare". "Bazai yiwu ba. Dan ina son a lokaci dana ɓuya kai ka cigaba da aiki. Na ajiye maka saƙo a ɗaki na.." Dai-dai nan suke isowa ƙofar gidan Imran inda aka ajiye Ojo. Tuni sojojin da suke tare duk sun dirga daga motocin da suke, dan haka Zak-Shadow bai kula kallon da Imran ke masa ba ya buɗe motar shima ya fita. Sai da ya ga Imran bashi da niyyar fitowa sannan ya leƙasa da faɗin, "Malam fito ka bada key mana". Shiru Imran ya kasa motsawa, dole Zak-Shadow ya zagaya ta inda yaken ya buɗe masa da kansa. Tamkar wanda juwa ke neman zubarwa haka Imran ya fito, yasan wanene Haysam, sani irin na ciki dabai ɗin nan. Tunda har ya ambata batun zai ɓuya akwai abinda ya gama shiryawa, wanda shi Imran yake gudu da son yaƙa. Ganin duk sojojin sunyi tsaye alamar shi suke jira da ƙyar ya iya ciro waya a aljihunsa ya shiga ƙoƙarin kiran mai kula da gidan, sai dai har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba. Ya sake na biyu ma haka, zai sake na uku Zak-Shadow yay ɗan murmurshi. Sai kawai ya dubi sojojin yace su ɓalle ƙofar. Hakan kuwa akai, sun tafi da nufin ɓalle ƙofa suka sameta a buɗe. Tun a anan aka tsaya kallon kallo, sai dai basu ce komai ba suka tura gate ɗin suka shiga. A tsakar gida suka tadda mai kula da gidan a yashe, ga wayarsa da Imran ke faman kira a gefe. Tattaɓashi ɗaya daga cikin sojojin yayi, cikin sauri ya ɗago ya ce, "Baya numfashi". Cikin tashin hankali Imran ya iso wajen, shima ya tattaɓashi amma da gaske baya numfashi. Suna ɗagoshi sukaga alamar an dakeshi ne ta ƙeya da wani abun. A take shugaban tawagar ya basu umarnin shiga gidan, shiko Imran sai jijjiga yaron yake yana ambaton sunansa amma babu alamar rai tare da shi. Zak-Shadow na gefe tsaye kawai ya zubama Imran ido...

Cikin abinda bai fi mintuna goma ba su Zak-Shadow suka fahimci babu Ojo a gidan an fita da shi. Dan a cikin gidan a ɗakin da Imran ya tabbatar ya ajiye Ojo duk ya aɓaci da jini har ta kan stairscase da falon. Dama gidan babu komai a cikinsa. Amma duk da haka sai da sojoji suka bincike ko wane lungu da saƙo nashi. Iyakar tashin hankali Imran ya shiga, amma abin mamaki Zak-Shadow ya dake a zahiri, koda akwai wata damuwa a tare da shi ya barma ransa. Tuni sojojin dake tare da su har sun isar da saƙo zuwa Headquarter. Ba'ai wani dogon lokaci ba aka zagaye anguwar da sojoji. Maƙwaftan dake jikin gidan duk an sakasu sun fito duk da ma sabuwar anguwa ce. Su akai taima tambayoyi suna bada amsar komai dalla-dalla. Sun tabbatar da wasu mutane ne suka zo gidan, hakan na nufin sune suka ɗauke Ojo kusan awani uku da suka shuɗe kenan, dan wasu sunga motar data shigo anguwar har cikin gidan, sannan duk sunji sanda mai kula da gidan keta ihun neman ɗauki amma tsoro ya hana su fita kasancewar su mata, ga shi kuma sunyi harbin bindiga har sau biyu. Cikin sa'a wani saurayin yaro ya bada siffar motar kaf da lambar jikinta, daga haka suka baro gidan shi kuma yaron Zak-Shadow da Imran ɗin suka wuce da shi asibiti. Sai dai me, suna isa asibitin sai ga sojoji an saka sun biyo bayansu wai kulawar yaron zata koma ƙarƙashin ikonsu. Tun daga nan Zak-Shadow ya fahimci anzo dai-dai wajen.....

<<%>><<%>><<%>>

Ɓatan Ojo ya sake hargitsa komai ta kowane ɓangare, dan hatta a cikin su jami'an sojin dake jin Zak-Shadow bazai iya aikata abinda ake zarginsa a kai ba zukatansu sun fara rawa da wasi-wasi. Sai dai a gefen zukatan nasu basa fata hakan ta kasance. Sai dai mizai faru kuma, ana kukan targaɗe kan batun Ojo sai kuma ga na karaya ya faru, dan kuwa misalin ƙarfe biyar na yammar wani mummunan labarin ya sake isowa hukumar sojoji. Wai an harbi jirgi mai saukar angulu na sojoji dake ɗauke da su Dagger a hanyar kawosu nan Abuja. Sabon zance kenan. Cikin gaggawa aka aika jami'ai inda abin ya faru. Kuma a cikin wani ƙauye abin ya faru, har an samu mutuwar fararen hula shida wasu sun jikata. Hakama sojojin dake tare da jirgin mutum biyu a cikinsu sun rasu, sauran sun raunana. Su Dagger su goma sha uku ne, an samu gawar biyar a cikinsu, sauran takwas ba'aga ko mutum ɗaya ba, hakan na nufin an ɗaukesu kenan. Duk da zancen bai gama bayyana ko a Headquarter ɗin ba, a yanayin nan duk wani masoyin Zak-Shadow dole ya kasance cikin jimami da fargabar abinda zai iya biyo baya, domin kuwa case ɗin su Dagger shine tushen case ɗin Ojo da ayanzu kai tsaye ake tuhumar Zak-Shadow akai.

_____________★

A Defence Headquarters kuwa, batun ɓacewar Ojo da batun su Dagger ya kai ga har gidan gwamnati. Abin mamaki, cikin ƙanƙanin lokaci aka kira taron gaggawa. (Emergency Security Council Meeting). Ba a ɓata lokaci ba, tuni manyan jami'an tsaro suka hallara cikin ɗakin taron, kowanne da fuska mai ɗauke da damuwa da jimamami, dan rashin su Dagger da Ojo kai tsaye na nuna tabbacin zargin da akema Zak-Shadow ne, duk masu bashi kariya basu da wani sauran abin faɗa. Bayan ƴan mintuna kaɗan da tattaunawa, an fito da hukunci mai nauyi. COAS ya samu umarni daga sama kai tsaye na kama Zak-Shadow. An kuma tabbatar masa a daren yau dan ba'a buƙatar wata hayaniya. Wannan shine saƙon umarni da COAS ya samu a dai-dai wannan lokaci da agogo ke neman buga ƙarfe shida na yammaci a ofishin ministan tsaro bayan fitowarsu daga meeting room. Shiru General Yusuf yana kallon ministan tsaro dake bada umarnin bai iya cewa komai ba na ƴan dakiku. Ya kasa ma kallon sauran takardar da ke gabansa. Sai da Ministan ya sake maimaita umarnin da baki cikin ɓacin rai, yana jaddada cewa umarnin daga shugaban ƙasa ne, sannan Janar ya furta, "Yes, sir". Ya faɗa yana sauke numfashi mai nauyi tare da miƙewa ya fito. Da sauri aka buɗe masa mota ya shiga, tunda suka baro ofishin minista ya faɗa duniyar tunani. A zuciyarsa kalmomin Minista ne kawai ke maimaituwa a kwalwarsa kamar amsawa kuwwa ne a cikin kunensa. Haysam Abdul-rasheed... to be apprehended. Hankalinsa a tashe yake matuƙa, zuciyarsa na masa zafi. Duk da cewa aikin soja ya koya masa ya bi umarni ba tare da tambaya ba, wannan karon zuciyarsa ta ƙi yarda. Amma ba shi da zaɓi. Suna isowa office shima yay kiran Director of Military Intelligence dake ƙoƙarin barin office. Amma dole shima ya yanke nasa hanzarin ya amsa kira. Tunda ya shigo office ɗin ya fahimci akwai matsala sosai, dan fuskar COAS ta nuna kai tsaye. Yayi gaisuwa cikin girmamawa. Amma COAS bai iya ya amsa da baki ba hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan sakanni biyu ya fara magana muryarsa cike da raɗaɗi, "Issue the arrest directive Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu quietly. No noise." Shima ba ƙaramin faɗuwa gabanshi yayi ba, ya ɗan zaro idanu waje zuciyarsa na girgiza. Sai dai kafin ma yace komai COAS ya miƙe abinsa alamar baya buƙatar wani zance. Rai a dagule ya fice daga ofis ɗin ba tare da ya tsaya da kowa ba ya bar Headquarters ɗin gaba ɗaya zuwa gidansa, kamar wanda yake guje wa wani abu da zuciyarsa ta kasa jurewa.

Bayan mintuna talatin, takardar Arrest Directive ta fita da cikakken sa hannun doka. An tura ƙungiyar jami'ai shida daga Military police da zasu kama Zak-Shadow bisa umarni, tare da amsar dukan abinda ya shafi matsayinsa.

(((*)))(((*)))

A ɓangaren Zak-Shadow da Imran sam basu sam mike faruwa ba, dan yanzu ma suke isowa gida daga asibiti bayan jam'an sojan nan sun tabbatar musu da komawar kulawar yaron a ƙarƙashinsu bisa umarni daga Headquarter kai tsaye gida suka nufa.. Sun yi ƙoƙarin kauda hankalinsu daga tashin hankali, kowa da tunanin da yake ƙoƙarin ɓoyewa, duk da shi Imran yaso su cigaba da tattauna maganar da suka fara ɗazun da Zak-Shadow ɗin, amma shi kuma yanata kaucewa sai kawai ya haƙura yay shiru shima har suka iso anguwarsu. Zak-Shadow sai da ya kai Imran har gida sannan shima ya shiga. Bilal ne ya buɗe masa gate, dan ya fito zai je massalaci sallar Magriba da aketa kira. Shima sai yana ajiye motar bai shiga ba ya fito domin gabatar da sallar kamar yadda ya saba. Bayan idar da sallar magriba ya fito Bilal tare da shi. Labarin rigimar Nimrah Bilal ke bashi har suka iso ƙofar gate ɗinsu, hakan kuma yay dai-dai da isowar motar data saka Zak-Shadow tsayawa. Shima sai Bilal ya tsaya yana kallon motar kawai........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 70_

__________________

https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt

https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite

https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝 Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.

Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Cikin nutsuwa jami'an Military Police suka fito a tsare. Babban cikinsu ya matsa kusa da Zak-Shadow cikin girmamawa da risinar da kai yayi gaisuwa. Amsa masa Zak-Shadow yayi cikin jinjina kai batare da yace komai ba. Sai kuma ya juya yana kallon Bilal yay masa alamar ya shiga gida. Bilal da bai fahimci komai ba face abokan aikin Dadan ne sukazo maybe zasuyi magana ne akan aiki sai ya shige gida abinsa kawai. Sai a lokacin Zak-Shadow daya sake binsu da kallo a taƙaice ya furta, "Akwai matsala ne?". Cikin sake risinar da kai ogan nasu ya ce, "I'm sorry Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed... by the order of the Defence Headquarters, you are under arrest. You're to come with us quietly." Zak-Shadow yay shiru kawai yana kallonsa na tsawon daƙiƙu, amma bai ce komai ba. Sai kuma a nutse ya koma kallon fuskokin sauran suma da duk suka risinar da kai alamar suna matuƙar jin nauyin kallonsa ma. Sai kawai yay wani ɗan murmushi yana sauke ajiyar zuciya. "Understood" ya furta cikin dakakkiyar murya, tare da miƙa musu hannunsa, alamar basu damar yi masa abin da suka zo yi. Wani daga cikin jami'an ya matso domin ɗora masa restraint band amma sai ya kasa. Sai ma cikin rawar murya ya ce, "I'm sorry Sir! wlhy bazan iya ba". Murmurshi Zak-Shadow yayi anan ma, batare da yace komai ba ya amsa da kansa ya saka....

★★★★

Motar su Ja'afar ta iso dai-dai Jami'an MP na barin ƙofar gidan. Sukabi motocin biyu da kallo, batare da sun kawo komai a ransu ba su ma Ma'aruff ya fita ya buɗe musu gate suka shiga ciki. Idan har suka shigo gida sukan fara zuwa su gaida Mammah ne kafin su wuce nasu ɗakunan yin wanka. Yau ma kamar kullum can ɗin suka nufa. Tun a farkon shigowa suke jin surutun Nimrah da Mu'azz da Ruƙayya da bata koma gida ba. Sunayin sallama Mu'azz da Ruky sukayo kansu suna musu oyoyo. Nimrah dai babu damar tashi saboda ƙafa. Gaishe su Bilal yayi, su ka amsa da kulawa suna tambayarsa ya aiki dan shi kam ma'aikaci ne. Fitowa Biebah dake kitchen itama tayi ta gaishesu, daga haka suka nufi ɗakin Mammah, dan in ta shiga sallar magriba bata sake fitowa sai tayi har isha'i. Har sun je ƙofa Ma'aruff ya juyo yana tambayar, "Dada fa? Ko yana sashensa?". Biebah ta ce, "Yaya tun ɗazun ya fita har yanzu bai dawo ba". Bilal ya ce, "A'a ya dawo Auta, tare ma mukayi sallar magriba. Zamu shigo gida yayi baƙi baku gansu a ƙofar gida ba?". Yanzu kam Ja'afar ne ya ce, "Eh muna isowa wata motar sojoji na barin ƙofar gidan, amma mu bamu ga Dada ba". "Maybe ya riga ya shigo ne". Duk sun gamsu da abinda Bilal ɗin ya faɗa, dan haka suka ƙarasa shiga wajen Mammah....

★Bayan idar da sallar isha'i su Ja'afar sun ta baza idon san ganin Dada ya fito a masallaci shima amma shiru. Kuma sun tabbatar idan yana gida jam'i baya wucesa. Sai da kowa ya shashshare suka tabbatar dai babu shi sannan suka koma gida. Kai tsaye sashensa suka nufa, tunda sun san shi kaɗai ne yanzu Nabeeha anyi yaji. Da knocking suka fara kafin su shiga. Sai dai ko ina shiru fitilu ma duk a rufe. Ma'aruff ya kunna fitilar falon haske ya gauraye ko ina. Sallama suka ƙara yi amma shiru babu alamar mutum. Sai kawai suka zauna a falon. Abin kamar wasa fin mintuna talatin babu motsin Dada, Bilal yaje yay masa knocking ƙofa amma shiru, dai-dai nan kiran Biebah ke shigowa wayar Bilal ɗin. Ma'aruff ya ɗaga. "Yaya Bilal Mammah tace wai ina kuka tsaya?". Miƙewa Ma'aruff yayi da wayar a kunne yana amsa mata da, "Gamu nan zuwa, muna sashen Dada ne kuma da alama baya gidan". Bai jira amsarta ba ya yanke kiran suka fito suka koma sashen Mammah. Duk sun sakankance Dada yaje wani waje ne har sunyi dinner sun dawo falo suna hira. Sai dai ganin Mammah tayi sukuku da yawa suka zagayeta da tambaya. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke, batare data amsa musu ba tace, "Biebah kwashe yaran nan su koma ɗaki kinga sun fara barci anan". Biebah ta ce, "To Mammah" tana miƙewa. Sai da ta tada Mu'azz ya wuce ɗakinsa sannan tazo ta ɗauki Nimrah takai ɗakin Mammahn ta ɗauki Ruky ma. Sai a lokacin Mammah ke amsa su Ja'afar. "Tun ɗazun nake jin zuciyata na rawa, sannan ina jina tamkar cikin tsoro-tsoro". Duk kallonta suke cikin tashin hankali suma a karo na farko. Jikin Bilal a sanyaye ya ce, "Mammah wani abu ya faru ne kuma?". "Babu abinda ya faru Bilal, kawai dai na fahimci bayan abinda ke faruwa a gidan nan na shirmen Nabeeha kamar Muhammad nada damuwa, sai dai yana ɓoyewa. Yau kuma gashi tunda ya fita har yanzu bai dawo gida ba, bai kira kowa a waya ba, kalla agogo ƙarfe goma saura. Sannan jiya na fahimci kamar Imran bai kwana a gidansa ba shima". "Tabbas Mammah maganarki na kan hanya, dan kinga ɗazun da safe wasu jami'an soja sun kawo ma Dada takarda, amma sai yaƙi ya buɗe a gabanmu yace muzo muyi shirin tafiya kasuwa". "Nima kuma yanzu kaga da yay baƙin nan Yaya Ma'aruff cayay fa na shigo gida, bai bari sunce komai a gabana ba." Shiru falon yay tunanin kowa ya fara dawowa jikinsa. Kamar an saita sai ga kiran Imran na shigowa a wayar Ja'afar. Ɗagawa yay cike da zumuɗi yana gaisheshi, Imran ya amsa da kulawa yana tambayarsa lafiyar kowa, sannan ya ɗora da tambayar Zak-Shadow. Ɗan jimm Ja'afar yayi, sai kuma cikin damuwa ya ce, "Dada baya gida, muma bamu sameshi ba." Da mamaki Imran yace, "Baya gida kuma?". "Eh wlhy Yaya. Mun zata ma kuna tare ai a wajen aiki. Dan Bilal yace bayan fitowarsu a massalaci sallar magriba yayi baƙi kuma kamar jami'anku ne". Imran ya ɗauki sakan biyu shiru kafin yace, "Ina Bilal ɗin?". Wayar Ja'afar ya miƙama Bilal. Koda ya amsa sai da ya fara gaisheshi, Imran ya amsa a taƙaice ya cigaba da jeho masa tambayoyi. Ba ƙaramin rikita Imran amsar Bilal tayi ba, dan yana faɗar motar da suka zo da ita ya gane jami'an MP ne. A dai-dai kuma lokacin yake canja channel daga tv da nufin kallon labarai aka nuna jirgin sojoji ya samu haɗari da yamma a wani ƙauye, kuma jirgin na ɗauke da wasu masu laifi ne da aka kama kwanan nan a rikicin daya auku na yammacin ƙasar. Ai cikin tashin hankali Imran ya yanke kiran batare da cigaba da tambayar Bilal ba, dan kai tsaye ya samu amsar tambayarsa ne.....

<<•>><<•>><<•>>

Duk da rufa-rufar da ake ta kama Zak-Shadow zuwa safiya dai zance ya gama fita cewar an kama shi ɗin. Abin mamaki kuma wata ɓoyayyar gidan jarida ta fara fidda bayanan kamashi a shafinta na X, tare da hoton lokacin da jami'an MP ke tare da shi, harda hoton dake da handcuffs a hannunsa. Kafin awa guda mutane miliyoyi sun zuba sharhi akan batun, manyan kafafen yaɗa labarai sun bazama binciken gaskiya. A gidan soji kuwa wasu hankalinsu a tashe matuƙa. Wasu ko na dariyar ALLAH ya ƙara da farin ciki mara misali. Nan fa wasu sabbin zantuka ma suka fara fita iri-iri masu ban mamaki. Kafin ƙarfe biyun rana ƙasa gaba ɗaya ta gama ɗauka. Babu wani labari dake trending sai batun kama Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu. A ɓangaren al'ummar ƙasa da yawa basu yarda zarge-zargen da akema Zak-Shadow ɗin ba, sun fi gaskata al'amarin da batun siyasa ce kawai ko wani abu daban. Su ko maƙiya na hura hanci da hanƙoron bada tabbacin zai iya fiye da haka....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull