Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 5

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 5

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 5: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 5. ......... Abdul-rasheed ya cigaba da karatunsa, yana kuma koyon…

3,974 words

......... Abdul-rasheed ya cigaba da karatunsa, yana kuma koyon ɗinki da zuwa yanzu ma zamu ce ya iya tunda yana yi ya samu taronsa da kwabo, yana iya ɗinka kowane ɗinki da hannu da kuma yi da keken ɗinki, tsakaninsa da A'isha kuwa sai Alhamdullah, dan zuwa yanzu mutane da yawa a layin sun san alaƙar tasu. Har ma takai ana kiransa da suna Abdul-rasheed ɗin A'isha, dan ko baka ganesa ba da ance maka haka kuwa zaka gane shi ake nufi. Sun sake samun hutu yay shirin zuwa gida Bauchi, zuwan daya samu rakkiyar Nasiru abokinsa, shima zaije yaga tushen Abdul-rasheed a wannan karon yay sati guda sai ya dawo. Hutun nashi kuwa ya haɗa da bikin ƴan uwansa mata biyu da suke uba ɗaya da za'ayi, da ƙanwarsa ɗaya da suke ɗaki ɗaya, sai ɗaya namiji da suke uba ɗaya shima. Hakanne ma yasa Nasirun zai bishi. Nasiru ya samu tarba ta mutuntawa a wajen mahaifin Abdul-rasheed dama ƙannensa, dan sun san sunanshi a bakin Abdul-rasheed. Kai hatta da abokan Abdul-rasheed tunna ƙuruciya dake anguwar kowa iya ƙoƙarin sa yake na ganin ya ƙyautatama Nasiru. Yanda gidan ya cika da mutane da dangi sai Abdul-rasheed ya samu kanshi da share hawaye, ga dai dangin mahaifiyarsu cike taf da gida amma ita babu ita a wannan duniyar. Asalin mahaifiyarsa ƴar Maiduguri ce, dan haka danginta duk daga can suka zo, ƙanwar tasa ma da zatai aure can za'a kaita auren zuminci ne. Bayan ɗaura aurarrakin maza suka fara shirin wucewa, dan sai zuwa gobe matan zasu tafi da amarya itama. Abdul-rasheed yana cikinsu yana godiya akan ƙoƙarin su duk da shima goben da shi za'aima ƙanwarsa rakkiya Maidugurin. Cike da kulawa wani dattijo da suke kira Baba Kalla ya dubi Abdul-rasheed ɗin tare da faɗin, "Kaima kuwa kaga da zaka zo cikinmu ai sai ka ɗauki mata. Hakan zai ƙara dawwamar da hankalinmu a kanku muma batare da mun shagaltu akan yin wani abu babu ku ba. Kasan dai shaiɗan ba rago bane, yanzu yanda babu mahaifiyar nan taku a raye sai gaka muna shagaltuwa da yin sakaci akan lamarinku, balle ma gashi ba gari ɗaya ba. Amma kaga idan ka aura a cikinmu, kamar yanda shima Gana ya auri Khadijah ai kaga koda yaushe babu batun manta juna. Dan lokacin rasuwar mahaifiyarku shima kamar wasa mukai irin wannan zaman da shi ikon ALLAH ashe ma suna tare da ita tuni. Bazamu so ku zauna a ware a cikinmu ba dan mahaifiyarku sanda tana raye mai ƙoƙarin bibiyar al'amarin dangi ce da don ƙyautata musu a kowane motsinta." Karaf wani a ciki yace, "Ai Baba bama sai an kaita da nisa ba, dan da zasu dai-daita da Yakura ni dai al'amarin su na min kamanni, itama yarinya ce mai sanyin hali da nutsuwa kamar shi. Gashi tana kama da mahaifiyarsu kamar ita ta haife ta. Abdul-rasheed ka fara gwadawa ka gani akan Yakura duk da nasan itama dai bazata ƙika ba." Tunfa da aka fara maganar nan gaban Abdul-rasheed sai faman faɗuwa yake da dukan uku-uku, dan haka yay shiru na tsawon lokaci har sai da mahaifinsa dake wajen yana lure da yanayinsa ya kira yi sunansa. Ɗan firgigit ya kallesa, sai kuma ya amsa kiran da yay masan. Baba ya zuba masa ido na sakanni, kafin ya furta, "Bakaji abinda ake gaya maka bane?". Ajiyar zuciya mai nauyi Abdul-rasheed ya sauke, kafin ya ce, "Baba duk naji". "Shine kuma kai shiru Abdul-rasheed. Sufa shawara suka baka bawai sunce dole bane. Kuma tun a ɗazun nima suka sameni da batun amma nace su maimaita a gabanka saboda gudun halin ɗan yau dana sani". "Kayi haƙuri Baba, ni mai karɓa ne ga dukkanin umarnin ku. Kawai dama......" Yayi shiru ya kasa ci-gaba. "Dama mi? Kayi magana mana. Dare keyi su suna son su ɗauki hanya ne ka sani". Yawu Abdul-rasheed ya sake haɗiyewa, ya muskuta zamansa kansa a ƙasa. "Baba dama akwai zancen wata yarinya ne da muka haɗu acan Kano kusan shekara ɗaya da rabi kenan, tun wancan zuwan naso samunka da batun sai rasuwar Inna ta gitta. Amma zan haƙura da batunta ɗin kawai. Sai dai damuwata ta yanda zan ma iyayenta bayani ne bayan su kuma sun riga sun bani yarda da aminci. Ban fara neman ta ba kuma sai da naje garesu suka amince min. Wannan ne kawai damuwata amma ba ƙin karɓar umarnin ku ba". Sosai zauren yay shiru. Baba ya zubama Abdul-rasheed ido kawai kamar mai nazari. Baba Kalla ne ya katse shirun da faɗin, "Tabbas maganarka abar a kalleta ne Abdul-rasheed, kuma bazamu saka ka zama ƙaramin mutum ba tunda har magana ta gitta haka. Zamu baka goyon baya kuma idan har ta kasance irin yarinyar da muke maka fata. ALLAH yasa haka shi yafi alkairi." Gaba ɗaya aka amsa da amin. Daga haka kuwa babu wanda ya sake motsa wannan zance har akai biki aka tashi lafiya. Koda yaje Maiduguri shi da Nasiru ma babu wanda yay masa maganar. Yaga kuma Yakura da akai masa magana a kanta. Itama dai yarinya ce ƙarama kamar Ai'sha, ko muce ma A'isha ta girmeta dan ita bazata ma wuce 12 ba da wasu watanni. Kwanansu biyu suka dawo, Nasiru ya koma Kano da shatara ta arziƙi daga dangin Abdul-rasheed, sai wasiƙa daya bashi ya kaima A'isha da kayan biki aba Inna da Gwaggon su Nasiru da Babansu da Yaya Zubairu suma. Abdul-rasheed ya cigaba da shan hutunsa daya rage harna sati biyu kafin ya fara shirin komawa Kano. Ana gobe zai wuce bayan sallar isha'i baba yasa aka kirashi. Dama dai yana da shirin zuwa wajensa, yana jira ne ya gama cin abinci, sai kuma ga kiranshi. Daga tsugunne ya gaishe da Baba, ya amsa masa yana masa nunin ya zauna. Inda ya nuna masan ya zauna. "Gobe ne tafiya ko?". "Eh Baba in sha ALLAHU". "To ALLAH ya taimaka, ya kuma bada sa'a, sai a ƙara dagewa da karatu, bani da haufi akan ka Abdul-rasheed, sannan na yarda da tarbiyyar dana baku ku dukanku. A kowane motsina kuma ina bin ku da addu'a ne musamman kai dake nesa da ni a yanzu. Dan duk sauran ƴan uwanka ina tare da su idan ka cire Hadiza da aure ya ɗauke min yanzu itama. Nasa an min bincike akan batun yarinyar dakai magana...." Karo na farko Abdul-rasheed ya ɗago a firgice yana kallon Baba. Cike da rawar murya yace, "Baba A'isha!?". Murmushi Baba yayi kaɗan shima yana kallonsa, sai Abdul-rasheed yay saurin yin ƙasa da kansa. "Kwarai kuwa A'ishatu Abdul-rasheed, dan na fahimci kana sonta sosai. Shiyyasa banyi ƙasa a gwiwa ba na tada ɗan aike takanas yayo min bincike. Kuma Alhamdullah dukkan abinda ka faɗa min shi aka dawo aka sanar min babu ƙarya a ciki. Harma da wanda baka sani ba game da halayyar mahaifinta da mahaifiyarta da ita kanta. Abdul-rasheed na amince ka auri A'isha. ALLAH ya sanya albarka a cikin tarayyarku. Idan kaje sai ka sanar musu nan da sabon wata idan yayi kwana biyu iyayenka zasuzo garesu. Babanka Kalla zaizo su haɗu da iyayenku na nan su Nuhu sai suje, tunda karatunka saura shekara ɗaya kaga sai a tsaida magana kawai su tabbatar da gaske muke ko". Sosai wani irin farin ciki mai girma ya baibaiye rayuwa da zuciyar Abdul-rasheed, sai dai kunya ta hanashi bayyanawa, murmushi dai yake ta faman yi haƙoransa a buɗe. A zuciyarsa kuwa ji yake kamar ya tashi yayta rawa dan daɗi. Baba ne ya katse masa murmushin da faɗin, "Sai dai ina da wata shawara a gareka guda ɗaya". Cikin nutsuwarsa ya koma sosai. Ya ce, "To Baba". "A kan maganar da su Babanku Kalla sukayi ranar auren ƴan uwanka. Mizai hana ka auri itama tasun ka haɗa biyu tunda namiji na mata huɗu ne. Koba komai ka sake samun kusanci da ƴan uwan mahaifiyarku, ka kuma samu abinda kake so. Yarinyar da suke faɗa yarinya ce nutsatstsiya sosai, dan kasan da ita akai jiyyar mahaifiyarku gaba ɗaya da uwarta. Nidai a ɗan zaman da tayi na kusan watanni biyar damu banga wani abin ashsha a tare da ita ba sam. Ga yarinyar kasan itama mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama, inda uwar ke aure yanzu sam mijin bashi da halin kwarai, nuna mata yake kullum ya gaji da yarinyar bayan kuma kafin ya aureta yay alƙawarin riƙeta shiyyasa ma su Kallan suka barta taje da ita. Kaga idan akai hakan itama an taimaketa ai ko? Amma shawara ce dai kamar yanda na faɗa maka ba tilastawa ko umarni ba. Dan ko ƴaƴana mata bazan ma auren dole ba balle ku maza. Kaje kayi tunani ka yanke hukunci da kanka. Duk kuma wanda ka zaɓa ni mai goya maka bayane a ciki". Daga haka Baba yay masa doguwar addu'a tare da ɗaukar kuɗi ya bashi. Amma sai yaƙi amsa, ya sanar masa yanzu ɗinkin da yake yi na kawo masa kuɗin amfani harma dana asusu da yake yi. Ko gudunmawar daya bama ƴan uwansa ta aure duk da kuɗin ɗinkin ne. Baba ya ƙara jin daɗi sosai, ya ƙara saka masa albarka. Ya bashi kuɗin kuma yace yaje dai dasu, dan wannan hakkine a kansa. Dole badan Abdul-rasheed yaso ba ya amsa yay godiya tare da addu'a sosai shima. Washe gari ya ɗauki kuma hanyar Kanon dabo, mai mata mai mota, mai dala da gwauron ɗutse, garin da ba Kano ba dajin ALLAH, hankaka maida ɗan wani naka, duk wanda ya shigo ƙasar kanon mu ya zama namu, jalla babbar Hausa yaro ko dami kazo an fika.

★Alhamdullahi Abdul-rasheed dai ya dawo Kano, ya kuma isar da saƙon Baba ga mahaifin su Nasiru, shi kuma ya samu Inna da kawun A'isha da maganar. Sunyi farin ciki sosai dan har zuci suke son Abdul-rasheed. Kamar yanda kuma baba yasa akai masa bincike akansu suma batare da sun sani ba sun aika har garin Bauchi an yi musu bincike akan Abdul-rasheed da ahalinsa. Kuma Alhamdullahi suma basu sami wani abin ashsha ko aibu ba sai nagarta. Ba iyayen A'isha kawai ba, hatta itama A'isha tayi farin ciki sosai, dan tunda ya gaya mata take ta faman murmushi tana ɓoye fuska..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 9_

__________________

*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*

*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*

*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*

*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*

_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Ahalin Abdul-rasheed sun cika alƙawari, dan kuwa a karo na farko suka iso garin Kano biyu ga sabon wata kamar yanda suka faɗa. Abdul-rasheed da kansa yaje tasha ya taho dasu. Ya fara kaisu makarantar su sannan suka nufo Ƙofar mata anguwar su Nasiru. A gidan su Nasirun suka fara yada zango. Bayan anyi gaisuwa da godiya bisa ga ɗawainiyar ahalin Nasiru. Suma sunyi godiya da hidimar da akai da Nasiru da yaje. Daga haka sukaci suka sha sannan mahaifin Nasiru ya shiga cikinsu aka wuce gidan kawun A'isha. Acan akai komai cike da mutunta juna da karamci. Abinka da mutanen da, ba alfahari babu fariyya babu ƙyale-ƙyale mara amfani, an bada kuɗin da hatsi har buhu uku na nagani ina so dana gaisuwar iyaye, a take akai baiko. Da za'a rabu an rabu cike da dattako da godiya ma juna. Nasiru da Abdul-rasheed suka rakasu tasha suka wuce. Dan sunce bazasu kwana a Kano ba. Abinka kuma da duniya na kwance ba'a tsoron komai.. Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI. Karatun Abdul-rasheed nata miƙawa, an kuma sake kawo kuɗi na biyu gidan su A'isha, tare da kayan sa rana. Huhun goro, farar alewa, sai cakuleti, sai cingam bazuka, sai alewa daima. Sai kuma tabarma karauni guda biyar, sai katifa da botikin ƙarfe da butar ƙarfe, sai zanin gado da barguna guda huɗu rigis abinsu. Kayan sarana dai sambarka dan duk wanda ya gani yasan dangin Abdul-rasheed sunyi ƙoƙari. Dan haka aka saka ranar aure watanni huɗu.

____________

Bayan wucewar baƙi dangin Abdul-rasheed iyayen A'isha ɓangaren dangin uwa dana uba suka baje kayan sa rana aka raba. Aka bama Inna nata da danginta, dangin mahaifinta suka ɗauki nasu. Sosai A'isha take a cikin farin ciki, sai dai wani ɓangare kuma jikinta duk yayi sanyi. Ko lokacin da ƙanwar Inna da suke kira Inna Haule tai kiranta akan ta faɗi suwa zata zaɓa matsayin ƙawaye da baranya akai musu kayan saka ranar kasa magana tayi, daga ƙarshe akace taje abinta ta sanar ma da Bashir ko Tasi'u su suzo su faɗa. Haka kuwa akayi, ta gayama Tasi'u ƙawayenta biyu da take son ɗauka matsayin babbar ƙawa Lantana da Jummai, sai baranya kuma, dan haka aka ƙulla kayan sa rana aka kai gidajen iyayensu kamar yanda ake ta rabo gidan sauran dangi da abokai da makwafta. A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI, kwanakin aurensa da A'isha nata gabatowa. Domin kuwa sai anyi bikinsu da watanni bakwai ma zai kammala karatunsa. Gabatowar abubuwa dole ya shirya yaje gida Bauchi. Dan ya samu saƙon wasiƙa daga drivern da ake yo masa aiken kayan abinci. Baba ne kuma ya rubuto ta da Ajami.

ٱلسَّلَامُ عَلَيْكُمْ

إِنَا فَاتَن كَانَا فِي قُشِي لَافِيَّا عَبْدُ الرَّشِيدْ. يَا كَرَاتُنْكُو يَا جَمَاعَار دَا كَكَيْ تَرَّة سُو. تَوْ دَنْ ٱللَّهْ دُكْ أَغَايْدَا مِنْ دَا كُوَا.

إِنْ بَا زَنْ تَابَا مَاكَا كَرَاتُو بَا كَيْي قُوكَارِي أَ سَاتِينْ سَمَا كَازُو غِيدَا كُونَا كْوَنَا بِي يَنْ سَا كَا كُوْمَا. دَنْ إِنَا سُون مُي يِ مَاجَنْغَا، كَاغَا كُوْمَا نِي بَا إِي يَا زُو كَانُونْ نَنْ تَاكُو زَنْ بَا إِنَا فَمَا دَا شِكَرُونَا.

نَا بَرْكَا لَافِيَّا. دَاغَا مَهَافِفِنْكُو. شَيْخُ إِيسَا كُوبِي بَوَتْشِي.

Assalamu alaikum.

Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya Abdul-rasheed. Ya karatunka ya jama'ar da kake tare da su. To dan ALLAH duk a gaida min da kowa. Idan ba zan taɓa maka karatu ba kayi ƙoƙari a satin sama kazo gida kona kwana biyu ne sai ka koma. Dan ina son muyi magana, kaga kuma ni ba iya zuwa Kanon nan taku zan ba ina fama da shekaruna.

Na barka lafiya. Daga Mahaifinka. Shehu Isa Kobi Bauchi.

Abdul-rasheed na gama karanta wannan wasiƙa baiyi ƙasa a gwiwa ba sati na zagayowa yayima garinsa na Baushi tsinke tare da asusunsa daya jima yana tarin kuɗin ɗinki a ciki. Sosai kuwa Baba ya nuna jin daɗinsa da zuwan nan. Dan a matse yake da son ganinsa. Bayan ya huta sun taɓa hira da Inna da ƙannensa ya fita gidajen yayunsa duk suka gaisa da matansu da su suma. Daga nan ya leƙa abokansa, sai bayan sallar isha'i ya dawo kasancewar yasan zuwa lokacin Baba ya shigo gida cin abinci. Hakan kuwa akayi, ya sameshi zaune a ƙofar ɗakinsa kan tabarmar karauni yana cin abincinsa a akushinsa. Sannu yay masa ya nema waje ya zauna, bai ƙara magana ba har sai da Baba ya kammala ya fuskanceshi dan kansa. Sun tattauna sosai akan batun bikinsa dake tunkarowa nan da wata ɗaya, sai batun gida da aka gina masa kamar sauran ƴan uwansa anan jikin gidansu, gini ne dai irin na wannan zamanin, wato ginin laka (ƙasa) kamar yanda aka sani ga talaka, an shafeshi da farar ƙasa ƴar aliya daga cikin ɗakunan, a waje an yarfa abin gwanin ƙyau. Abdul-rasheed yayi godiya sosai ga mahaifinsa harda hawaye, yay masa addu'ar tsahon rai da lafiya mai ɗorewa. Bayan ya lafa Baba ya ɗora masa da batun kayan lefe da dangin mahaifiyarsu suka kawo daga Maiduguri. Akwatin ƙarfe ne da irin na mutan da guda ɗaya ƙaton gaske, akwai kaya a ciki wato atamfofi irin na mutanen da sai takalma da kayan shafa kamar dai yanda ake haɗa lefe a wancan zamani. Baba ya sake da nuna masa kwalla guda biyu daga wajensa shima kuma kayan lefen ne dai a ciki, kamar yanda yayma sauran ƴan uwansa shima yayi masa tunda na dangin mahaifiyarsa daban nashi daban matsayin uba. Rasama tacewa Abdul-rasheed yayi sai hawaye kawai yake sharewa da godiya. Daga ƙarshe ya ɗakko asusun nan gaba ɗaya ya dire a gaban Baba. Baba ya ɗan zubama asusu ido sannan ya kalli Abdul-rasheed a nutse. "Wannan asusun fa Abdul-rasheed?". "Baba kuɗaɗen da nake tarawa ne na ɗinki a ciki daman". "Masha ALLAH, ALLAH yayi maka albarka, amma ai naka ne, miyyasa zaka kawo min nan?". "Baba naka ne, kai amfani da shi domin rage nauyin abubuwa sun maka yawa. Nasan dai bazasuyi maka komai ba, amma dai za'a rage wani abu". Murmushi Baba yayi a karo na farko, ya sake saka masa albarka sannan ya ɗauki asusun ya miƙa mishi. "Abdul-rasheed bazanƙi amsar ƙyauta daga hannunku ba. Domin hakan ba nufin jinƙai da neman albarka. Kuma hakan da kai min ya sakani jin daɗi ƙwarai da gaske. ALLAH yayi maka albarka da sauran ƴan uwanka duka. Amma kaje da asusun nan ka cigaba da tara abinda kake samu, bayan ka kammala karatunka ka dawo gida akwai abinda zamuyi da kuɗin ni da kai. Dan haka ka cigaba da ajiye min su a hannunka kaji". Batare da Abdul-rasheed yay tunanin komai ba ya ce, "To Baba. In sha ALLAHU yanda kace haka za'ayi". Daga haka suka cigaba da hira har lokacin barci..

>>>>>>>•<<<<<<<

Kwanakin Abdul-rasheed biyu ya dawo Kano makaranta, bai shiga anguwar su A'isha ba sai da sati ya zagayo kamar yanda ya saba. Sai dai suna tare da Nasiru a makaranta kullum. Shi ya bama tsaraba ma da ƙanwarsa ta bada a kawoma A'isha ya kai mata shi kuma sai ƙarshen sati ya shiga suka gaisa.. Rayuwa ta cigaba da tafiya bikin Abdul-rasheed da A'isha nata ƙara matsowa, ana shirye-shirye shi kuma hankalinsa nakan jarabawar da suka fara, wadda bai kammalata ba kuwa sai ana saura kwana huɗu ɗaurin aure. Zuwa lokacin gidan su A'isha ya gama cika da danginsu na nesa, har ma am sakata a lalle a safiyar yau ko muce da hantsi, wato an saka mata turare irin na al'ada matsayin kamu. Wannan yasa shima Abdul-rasheed bai ganta ba, dan a wannan zamani idan aka saka amarya a lalle keda ango kuma sai a ɗakin aurenku. Sam Abdul-rasheed bai so haka ba, dan tunda ya fara jarabawar nan basa wani samun zama da A'isha, zai iya cewa rabonsa da ita ma tun mako uku da suka wuce randa sukai hira harda Nasiru suka bata kuɗin ƙarshen zance da ake bama budurwa sule na gugar sule har sule biyar cif. To gashi kuma yau da yake son ganinta bamai yiwuwa bane, dole ya haƙura ya kama hanyar Bauchi tare da Nasiru ɗan amanarsa. Sai ana gobe ɗaurin aure zasu dawo Kano su sake komawa tare da amarya. Koda su Abdul-rasheed suka isa Bauchi a can ma sai ya tadda gidansu taf da dangin mahaifiyarsa dana Baba, kai har ma da dangin Inna duk da ta kasance kishiyar uwa. Tuni an baje buhu-buhu na masara dana gero anata faman daka domin samar da garin tuwo harma dana MASA ƳAR BAUCHI, sai fura dama sauran nau'in abinci irin na wannan ƙarni da su shinkafa. Sun sami tarba ta farin ciki, inda abokan wasa dake dakon isowar ango dama suka lulluɓeshi aka fara zazzage masa kwalaben turare masu ƙamshi irin su ɗan duwala ana guɗa, hakan kuwa na nufin shima an saka shi a lalle kamar amarya.

*_KANO_*

A nan Kano ma dai ɓangaren amarya bari muɗan dawo baya kaɗan miji a yanda aka sakata a lalle da yanda suke shagalinsu da ƙawayenta. Zamuce amarya da ƙawayenta sun fara shagali tun a ranar data kasance saura kwanaki bakwai ɗaurin aure. Amma an sakata a lalle ana saura kwana uku. Ranar litinin Inna Zainabu ta bata umarnin tsefe kanta kamar yanda yake a al'ada, da taimakon ƙawarta Jummala ta samu ta tsefe shi. Daga haka suka cigaba da sabgarsu. Washe garin ranar laraba da mutanen Bauchi suka iso da lefen A'ishatu a washe garin randa su Abdul-rasheed suka tafi kenan, akwatin ƙarfe da kwalla biyu sai tabarmi karauni guda huɗu. Gidan ya cika sosai da maƙwafta, bayan an cika baƙi da shatara ta arziƙi na abinci, anyi gaisuwa irin ta mutunta juna, dama gidan su Nasiru suka sauka, dan haka suna kammala bada lefe suka koma can abinsu, kasancewar nisa dama su huɗu ne kawai suka kawo kayan, zasu zauna kuma har a ɗaura aure sannan. Masha ALLAHU kaya sai sambarka. Dan kuwa dai amarya tayi goshi. Atamfofi ne nagartattu irinsu mai tabarma, mai barewa, akwai oni-ƴasu, sai joji da ƴalle gwaggwaro, sai t-shirt masu ƙyau, sai sufa gwaldin, sufa shadda, akori-kura, kai kaya dai sai sambarka. Kayan kwalliya da sabulai suma dai tsaf, sai turaren alwalar uwar ɗiya ƙatuwar kwalba sosai, sai ƴarduwala, miski da sauran irin yan feshi. Sai kuma gyale da su takalma kaya dai rigijib-jib komai ka taɓa akwai irin na wannan zamanin..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 10_

__________________

*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana 💃 fulanin asali ke nan 😘._*

*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*

_Maza kuzo ku sha labari da ɗumi-ɗuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buɗe muku gidan gyara da ƙalƙale jikin mata ƴan kwalisa a kusa da ku gabb._

*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na👇_*

*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*

_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_

*_Zaku same mu a wannan numbers ɗin kamar haka👇_* *07068210505* *09133081313*

_DEALER IN all kind of skin care products such as:_

moisturizer Sun screen Face Toner Eye cream Face serum Face wash Face scrub Face cream Face marsk Body lotion Body cream Shower gel Body scrub Tube Body oil Body spray Perfume Hair crm Hair spray and many more

*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne 💃_*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull