Kenza eBookz

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 6

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull - Chapter 6

Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 6: Kida a ruwa book 1 by bilyn abdull Chapter 6. ........Bayan ƴan ganin lefe sun kammala kowa ya wuce an adana…

4,165 words

........Bayan ƴan ganin lefe sun kammala kowa ya wuce an adana kaya ma sannan A'isha ta dawo daga maɓoyarta. Ganin yanda aka ɓata gidan ta ɗauka tsintsiya ta hau shara kamar yanda ta saba, tana tsaka da sharar tsakar gida duk da baƙi sun fara cika gidan nasu ƴan biki matar yayansu ɗan ƙanin babansu ta shigo gidan. Cike da shammata ta shiga zazzage mata turare a jiki tana guɗa. Wani irin sakin tsitsiyar A'isha tayi a ƙasa, sai kuma ta fashe da kuka tana mai durƙaushewa a wajen. Kuka take sosai mai ban tausayi, har sai da akazo aka ɗagata a wajen. Abokan wasa kuwa sun samu nayi, sai binta suke da guɗa. An cire mata ƴan kunnenta da tsakiyarta ta wuya (Abin wuya, kamar sarƙa dai a yanzu). Hakama kayan jikinta ta cire an kawo mata tsohon zani da riga ta saka. Wannan alama itace amarya ta shiga lalle kenan, dan kuwa zuwa bayan sallar magriba wadda take matsayin Alwanka ɗinta tazo gidan, ƙawayenta dama tunda akai kamun sun cika gida abinsu domin zaman lalle ya fara kenan. Bayan gaishe-gaishe aka ɗakko ma alwanka tabarmin tirgeza guda uku ta kwashi amarya da ƙawayenta suka tafi gidanta. Da yake itama anan anguwar take da ƙafa suka taka abinsu. An zauna an ɗan taɓa hira kowa ya nema makwancinsa, makwancin kuwa wannan tabarmi ne da alwanka ta amso na turgeza (😂mutane na miye Turgeza? A amsa a comment akwai ƙyauta🤣, sannan miye Alwanka ma? Tambaya biyu kenan😂🙏). Biyu ƙawayenta suka kwanta, ɗaya aka bata ita kaɗai. Washe gari da safe aka dama musu koko aka sayo ƙosai aka basu sukai kari da shi. Daga haka suka koma ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake gidan suka zauna suna hirarsu, sai dai amarya daka ganta duk tayi sukuku, lokaci-lokaci ma takan share hawaye abinta. A ɓangaren Alwanka kuwa ta tanadi lallenta na ƙunshi har kwano ɗaya da rabi ta kwaɓa tunda safe na TURGEZA kenan, zuwa goma ta bama ƙawayen amarya lalle da zunguru sai ledoji su ƙunsa mata. Tsaf ƙawayen amarya suka ƙunsheta kuwa da ƙunshi na tsohuwa ta faɗa kwata (🤣ina fatan kun san ƙunshin dai?), hakama a hannunta sannan aka saka mata zunguru a ciki (Miye zunguru?😂 Wanda ya faɗa akwai ƙyauta shima🤣🙏). Bayan an gama sakama amarya lalle ƙawayen amarya suka fice zuwa gidan su Nasiru, dan kuwa ance duk abinda ake badawa na gidan anguna suje can su amsa. Bayan gaida Innar su Nasiru da baƙin Bauchi da suka samu a gidan aka danƙa musu shinkafa da manyan zakaru har huɗu, sai kayan miya da kayan magi da iccen girki da man gyaɗa, sai kuɗi wannan sune kayan kamu. Koda suka dawo gidan alwanka ɗanta Ibro ne ya yanka musu kajin, su kuma suka shiga hidimar girki amma dai Alwanka na duba musu da nuna musu yanda duk ya dace ace sunyi. Amarya kuwa na zaune da ƙunshinta har lokacin abinta. Zuwa azahar aka kammala abinci, shinkafa da miya da naman kaji zuɗu-zuɗu, mai kuwa. A ƙyallan har kana iya ganin fuskarka a ciki fes. Umarnin cire ƙunshi Alwanka ta bama amarya, dan haka ƙawayenta suka fara taimaka mata tai zaman cirewa kamar abin arziƙi, gefe kuwa manyan ƙawayen amarya sun shimfiɗa tabarma a tsakar gida, wanda suka taimaka mata ta cire ƙunshi suna gamawa ta miƙe da nufin barin wajen kawai taji an rufu a kanta, cak suka ɗagata sai kan tabarmar nan da aka shimfiɗa. A take ta birkice musu ta shiga bibbigesu da son ƙwace kanta, amma ina sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, tuni suka danneta a wajen, dama gashi daga ita sai zani ɗaurin ƙirji, dan sanda za'a saka ƙunshi sakata akai ta cire rigar. Tsaf ƙawayen amarya suka cire zanin nan kuwa daga jikinta aka barta zir sai ɗan kamfai (😂wato mutanen da anyi shagali da ɗanyen aiki gaskiya🤣). Sauran lallan da aka saka mata ya rage da wanda aka cire matan Alwanka ta kawo musu, nan fa ƙawayen amarya suka shiga ɗiba suna saka mata a jiki ana murjeta da shi. Itako tana kai musu duka da harbinsu ƙafa da hannu tana kuka. Har cikin gashin kanta ana raira waƙa, bari na ɗan raira muku💃🤣.

Ayye yara iye TURGEZA. Ga Turgeza yazo, Turgeza.

A wanketa da sauri, turgeza.

Lallen iya ƙamshi, turgeza.

Ayye yara amarya turgeza.

Sai da ni bilyn ku😂 (magana ta gaskiya ni na ƙirƙiro muku waƙar, amma ta gaskiyar ba haka take ba, baitin farko ne kawai na gaskiya kada kakanin mu suce na musu sharri😂🤣🤣).

Sosai amarya ta dirzu da lalle. Masha ALLAH kuma sai tayi ƙyau abinta, sai dai fa kowa ya daku gwargwadon iko cikin ƙawayenta. Itama kanta ta jigata da kuka da harbe-harben data sha. Ana sakinta taja zaninta ta ɗaura, data rarumi icce tai kan ƙawayen nan nata sai gudu Malam. Tuni fa kowa yay waje, masu neman wajen ɓuya suka nema, masu haura katanga nayi masu yin hanyar zaure nayi. Da ƙyar Alwanka ta kamata ta riƙe, sai da duk suka baje sannan ta saketa, babu batun wanka, wannan lalle na jikinta haka kuma zai cigaba da zama a jikin nata har sai gobe, gefe ta koma ta dasa sabon kuka. Babu wanda ya hanata har tayi mai isarta ta gaji dan kanta ta haƙura. Bayan komai ya lafa ƙawayen amarya suka daddawo sai kuma aka ɗakko abinci da miya aka baje kuma a tsakar gida da turirrika na rabo. Haka aka raba abincin ƙunshi da nama kowa ya samu har maƙwafta, aka baje kuma aka fara ci ana hira da wasa da dariya. Bayan sun kammala aka aiko baranya ɗakko igiyar shillo, babu jimawa ta dawo, amarya ta tashi ta saka rigarta da kallabi suka kwashi igiyar nan suka fice bayan gidan wajen wata bishiyar ɓaure ƙatuwar gaske. Anan aka ɗaura wannan igiya ta ɗauru kam sannan aka fara shillo, idan wannan ya sauka wannan ya hau, har yamma suna a wajen suna waƙe-waƙensu na ƴanmata cike da nishaɗi. Sai gab da magriba suka dawo gidan Alwanka. Washe gari alhamis ma haka suka sha shagalinsu aka ƙara yima amarya wankan lalle kamar jiya, dan kuwa yau ma zir akai mata sai ɗan kamfai aka shafeta da lalle har cikin kanta, tasha kukanta kamar jiya har yamma. Zuwa dare bayan sallar isha'i Alwanka ta tattarasu tai musu rakkiya aka maidasu gidan su A'isha. Gida kam ya gama cika da dangi tako ina. Bayan gaisuwa Alwanka tace "Ga aro na maido, ALLAH ya sanya alkairi ya fiddamu kunyar gobe. ALLAH Kuma yasa takai mutuncinta ɗakinta. Nagode, Nagode ALLAH yabar zuminci". Atare aka amsa mata da amin. Dangi sukai godiya suma sosai ta wuce. A ranar anan gidan su A'isha suka kwana, dan kuwa ɗaki guda aka ware musu ita da ƙawayenta. Washe gari juma'a ɗaurin aure, ta ko ina dangi maza sunata isowa, hakama tawagar ango da danginsa daga Bauchi, da abokansa na Bauchi dana Kano duk sun iso, zuwa ƙarfe sha ɗaya aka ɗaura auren A'isha da Abdul-rasheed akan kuɗi sule na gugar sule har sule goma cas. Lallai wannan yawan sadaki ya girgiza mutane, dan kuwa sule goma ba kuɗin wasan yaro bane a lokacin. Abinci kala-kala tako ina ƙamshin ke tashi na miyar taushe ga nama kamar a banza. Dangi kowa ka gani bakinsa a washe anatama juna sambarka, balle kuma ace Inna ai ba'a magana, tayi shar da ita cikin sabon ɗinki. Amarya kuwa na can tare da ƙawayenta a ɗaki, sai dai a miƙa musu abinci. Ƙawaye sunyi wanka da kwalliya, amarya kam dai tana nan ba wanka har yanzu dai tsoffin kayanta ne a jikinta na zaman lalle, sai bayan sallar azhar kuma aka shirya yima amarya wanka dan za'a shiryata domin tafiya Bauchi. An shirya ruwan wankan amarya a cikin ƙaton masaki da yasha addu'oi daga tsoffi, aka zuba lalle sai kuma ruwan turare kala uku masu ƙamshi sosai, sai sabulu shima mai shegen ƙamshin tsiya. Bayi aka kaishi sannan aka kira alwanka da zatai mata wanka. Aifa nan abokan wasa suka miƙe domin rakkiyar amarya bayi, tana kuka aka dannata ciki bayin, dama Alwanka an kiranta. Waƙa abokan wasan nan nata suka fara rairawa suna tafi yara na tayasu....

Tsohuwa iki wanke, kin saki Kwankwaso yeee a ƙofar soro💃....

(😂Ehem-ehem lamarin fa ba'a cewa komai, amma wannan waƙar ta gaskiya ce walle bani na ƙirƙira ba😎😂).

Kuka sosai itako amarya keyi, Alwanka kuwa na wanketa lungu da saƙo har gashinta dake danƙare da lalle. Duk wannan dattin ya fita da suke kira (Saiɓi), sai ga amarya na sheƙi da ƙyalli da ƙamshi kamar ka lasheta. Zani aka bata ta ɗauro aka rufeta da wani aka fito da ita sai ɗakin Inna. Acan aka shafa mata mai mai ƙamshin tsiya mai gurguwa, aka shafe ta da turarruka kala-kala Sannan aka bata sabon zani da riga na atamfar.... Ta saka daga cikin lefe yake, sai ɗan kwali disko da wani fallen zanin na lulluɓi. Aka shafa mata hoda aka saka mata jan baki amarya ta fito tsaf da ita masha ALLAH. To daga nan fa iyaye suka zagayeta aka shiga faɗa da nasiha, itako tana ƙunshe a zanin nan da take lulluɓe tana kuka sosai. Bayan sun gama akasa Inna tai mata addu'a tana kuka sosai, dan yau ne karo na farko da zatai nesa da ƴarta. Bayan ta kammala aka kamata aka fito da ita soro inda iyaye maza suke suma suna jira. Nan ma sabon faɗa da nasiha aka buɗe, gargaɗi dai kam amarya ta shashi gwargwadon iko kafin a kamata zuwa ƙofa gida inda motor da za'a ɗauki amarya take. Kanta ce guda biyu, sai ƙarama ɗaya da za'a saka amarya. Tuni masu zuwa sun cika kantar kuwa harda ƙawayen amarya, dan haka aka sakata cikin ƙaramar Innarta da Gwaggon na ɓangaren uwa da uba suka shiga kusa da ita, sai a gaba direba da Nasiru ne, ango da sauran abokai kuwa tuni sun ɗauki hanyar Bauchi su dama da iyaye ƴan ɗaurin aure. Motoci na ɗagawa ƴammatan amarya suka fara raira waƙa da yara....

Ayye yaraye dide, ayye yaraye naye, ayye yara iye naye yaraye!!.

Ƴammata kuzo roni, mi zamuyo roni? Aiko zaman lallen A'isha lale laya!.

Ke kikace kinayi da shi, shi yakace yanayi dake, har magana takai ga manya kibar mana koke-koken tsiya.

Babu mararraba ba rabawa, iccen wurma yasha harara, yasha rarraɓar masu ƴaƴa, tunda ya kada goɗiya.

Iye yaraye, ke kikace kinayi da shi, shi yakace yanayi dake!.

💃🏼💃🏼😂😂Iya nan za'a tsaya, (😎kuma itama ta gaskiya ce ehe😂).

Su suna raira waƙa amarya na kuka mai ban tausayi. Haka motoci suka wuce jama'ar anguwa na binta da addu'ar fatan zama lafiya na har abada. Ahaka aka ɗauki hanyar Bauchi. Tun masu waƙa nayi har suka gaji wasu ma suka fara barci, cikin amincin ALLAH bayan magariba suka iso Bauchi. Kai tsaye kuma gidan iyayen Abdul-rasheed aka wuce da amarya, inda suka samu tarba ta mutuntawa da girmamawa. Tarba dai kam dangin Abdul-rasheed sun yima amarya ta gata ita da danginta, yayinda take ƙunshe cikin gyauton zanin da aka lulluɓa mata na atamfarta mai barewa datai mata ƙyau. An kawo musu abincin maraba kala-kala sukaci suka ƙoshi, daga haka suka baje barci dan kowa ya gaji matuƙa, ita kanta amarya tuni ta ɓingire da ƙyar ma aka samu taci abincin.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 11_

__________________

*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana 💃 fulanin asali ke nan 😘._*

*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*

_Maza kuzo ku sha labari da ɗumi-ɗuminsa, domin kuma fa NAKUN ya buɗe muku gidan gyara da ƙalƙale jikin mata ƴan kwalisa a kusa da ku gabb._

*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na👇_*

*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*

_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_

*_Zaku same mu a wannan numbers ɗin kamar haka👇_* *07068210505* *09133081313*

_DEALER IN all kind of skin care products such as:_

moisturizer Sun screen Face Toner Eye cream Face serum Face wash Face scrub Face cream Face marsk Body lotion Body cream Shower gel Body scrub Tube Body oil Body spray Perfume Hair crm Hair spray and many more

*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne 💃_*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Washe gari an cigaba da shan biki a Bauchi, dan anyi wankan ango da ajo ɗinsa. Amarya kuwa babu wanda zai ce yaga fuskarta sam dan ko wajen wankan ango da ajo bata leƙo ba tana ɗaki ƙunshe. Hakan kuwa shine dai-dai kuma shine ɗa'a. A ranar kayan amarya suka iso dan su sai washe gari aka taho dasu. Gidanta dake nan jikin gidan sirukanta da sauran ƴan uwansa aka sauke, sauran kayan gara kuwa gidan su abdul-rasheed. A take danginta suka koma can aka hau jere, aka barta da ƙawayenta ita kuma anan gidan. Ɗakin amarya yayi ƙyau. Iyayenta sunyi ƙoƙari sosai. Gado ne guda biyu, babba mai rumfa na miji, sai ƙarami nata. Mai rumfa yasha ƙatuwar katifa da zanin gado harda rumfarsa ta sama da filo har goma sha biyu ciff, aka saka masa labule da ake kira (Zarge shige🤣). Dan haka gadon yay ɗas kamar ka zauna kaita kallo. Itama dai natan an saka katifa da zanin gado mai ƙyau, sai kabot da ya sha jeren fantekoki a sama da kwalloli, sai kanta a cike da tasoshi ƴar girke dake ta ƙyalli da ɗaukar ido na ƴar gata, sai tangarare suma na ƴar gata. Ga languna tuwo da miya kala-kala da kwanon sha. Sai kumbo manya anyi nasu dankin uwa ta raɓe suma a gefe masha ALLAH, ga uwa ta raɓe ta fantekoki masu murtala. Kowace kusurwa an buga darduma masu ƙyau, sai labule. Sai gansarwa na garar kaka da ƙoran fulani da suka sha tarde da ludaye a cikin an sakasu a ragaya aka rataye, ledar ƙasa ma an baza masha ALLAH. Kai abunfa ba'a magana, dan ɗakin amarya sai sambarka komai yaji, kaida ka gani kaga ɗakin ƴar gata. Abin dai masha ALLAH sai wanda ya gani. Dan duk hassadarka kai kana ganin wannan ɗaki kasan an zubama Ai'shatu kayan ƴar gata. Suna kammalawa zuwa dare aka dawo da amarya nan, suma dangin nata nan duk suka dawo aka cigaba da shagalin biki bayan an dire musu raguna manya guda biyu na jere. Washe gari buɗar kai, ranar kuma biki zai tashi, baƙi duk zasu wuce musamman ma ƴan kano. An dafa farar shinkafa, sannan amarya tayi wanka yau, dan tunda aka kawota ko kaya bata canja ba, batayi wanka ba kuma, idan kaga ruwa ya taɓa jikinta sai na alwala. Har yanzu bata saka Abdul-rasheed a idon taba shima haka bai ganta ba. Tunda safe aka fara mata kitso ƙana-ƙana masu ƙyau, sun jima sunayi dan har zuwa azhar sannan suka kammala aka haɗa mata ruwa da yaji turarruka da addu'oi ta shiga wanka da kanta. Bayan wani lokaci ta fito, an bata kaya ta canja, atamfa mai tabarma da akaima ɗinki mai ƙyau irin na wannan zamanin, yau dai gyale aka bata ta yafa ba zani ba, sabon takalmi sai tsakiyar wuya mai ƙyau tanata sheƙi. Sosai hankalinta a tashe yake, dan yan uwanta duk sun kammala shirin su, ana gama buɗar kai zasu wuce. Gida ya cika taf, dangin ango duk sun dawo nan suma. An fara yin rabo irin na al'ada ga dangin miji, bayan kammalawa ne aka fito da amarya dake lulluɓe cikin gyalenta, har yanzu dangin miji dama ƴan gari babu mai cewa ga kamaninta. Sabuwar tabarma aka shimfiɗa aka ɗora sabuwar kujerarta ƴar tsugunno a kai, ta zauna. Shinkafar nan da aka dafa fara sai gishiri kawai a cikinta, amma fa tasha mangaɗa ƙyallan aka juyo a ƙaton bangaji aka ajiye gabanta. Tana lulluɓen aka kamo hannunta biyu aka fito da su, ta haɗesu waje guda kamar mai addu'a aka cika mata shi da shinkafar nan taf. A baki ta saka, sai dai babu batun taunawa ta furzar a gefenta na dama, ta ƙara cika baki ta furzar a gefenta na haggu, ta karshe ta furza a gaba, sauran ta watsata baya. Daga nan ne fa aka shiga rangaɗa guɗa, masu kiɗan ƙwarya suka fara. Bayan an gama cashewa da kiɗan ƙwarya koma muce ana cikin cashewar iyaye a cikin dangin ango suka kwashi kayan da aka basu na baye suka koma gida, aka sake shirya amarya itama aka bisu da ita can hannunta riƙe da ƙwarya mai ƙyau. An fara kaita ɗakin Inna dake matsayin uwar mijinta a yanzu. Inna tayi addu'ar zaman lafiya, ta kawo kuɗi jaka biyu ta saka mata a ƙwaryar, danginta sukai godiya aka fito, daga nan sai ɗakin marigayiya mahaifiyar Abdul-rasheed, inda danginta suka fanshi nata, ba'a nan aka tsaya ba, sai da akabi iyaye kaf, dangin uban miji dana uwa. Kafin kace mi sai ga kuɗi shimili amarya ta tara a wannan ƙwarya, dan har makwaftansu da ake zumunci irin na mutuntawar mutanen da, makwata iyaye ne ba abokan gaba ba, nan ma sai da aka kai amarya, daga nan ne aka sake baidata gidanta inda yara da ƴammata ke cigaba da cashewa da kiɗan ƙwarya. An maidata ɗakinta, aka saka wasu cikin ƙannen ango suka zauna da ita, suko ƴan kano cikin hikima suka zare jikinsu duk suka gudu batare da amarya daketa kukanta ta farga ba. Balle kuma masu kiɗan ƙwarya na wasansu har magriba. Sai bayan sun tashi ne gida ya fara komawa tsit A'isha ta fahimci da kaf yan uwanta babu. Sosai ta ƙara ƙarfin kukanta, ƙannen ango dake tare da ita har lokacin na lallashinta. Zuwa bayan sallar isha'i an tafi an bar amarya ita kaɗai a ɗakinta tanata kuka, sai daga baya aka turo mata wasu ƴammata huɗu su zauna da ita saboda zuwan anguna. Babu jimawa kuwa ango da abokansa suka yo masa rakkiya cikin girma. Ƙawayen nan sune suka amsa, dan amarya na can ƙarshen bango ta rakuɓe ƙudundune cikin gyale. Anyi gaisuwa tsakanin ƙawayen amarya da abokan ango, ƙawayen amarya suka gabatar musu da abinci. Kwanika ne guda biyu dake a saman tire ɗin kwano da kwanon sha dake cike da ruwa an rufesu da tuma ƙasa (😂Azo gaya min minene tuma ƙasa akwai kyauta). Gefe suka koma su kuma abokan ango suka naɗe hannayen riga suka fara ɗibar girki, gefe kuma suna hira da ƙawayen amarya. Bayan sun kammala akai sayen baki, anyi ƴar jayayya akan kuɗi, daga ƙarshe dai suka ajiye musu jaka huɗu. Ita dai amarya na nan a gefe kamar ma bata san bikin da ake ba a ɗakin, kukanta take dai kawai. Abokan ango sunyi nasiharsu ga amarya da ango, tare da addu'a. Daga haka suka miƙe tare da ƙawayen amarya sukai musu sallama suka wuce. Abdul-rasheed ya miƙe dan rakasu Nasiru ya maida shi ya zaunar yana faɗin, "In dai mune mun huttasheka, zauna ka lallashi min ƙanwa sai munzo maka tausa". Daga haka suka fice suna dariyar kalmar shaƙiyancin Nasiru. Abdul-rasheed ya bisu da kallo kawai yana murmushi. Bayan fitar tasu ɗakin ya kasance shiru na fin mintuna uku, dan haka kawai shima Abdul-rasheed ɗin sai yake jin kansa wani iri tamkar ba shi ɗin ba. Yau ALLAH ya cika masa burinsa ga shi ga masoyiyarsa dai a tare da shi. Itako har yanzu kukanta take mai fita da sauti kaɗan da shashsheka. A hankali ya miƙe yana mai tattare babbar rigar jikinsa ya cire gaba ɗaya, saman gadon mai rumfa ya ɗaga labulensa ya ajiyeta sannan ya taka zuwa inda take zaune a maƙure tsakanin gado da bango. A nan ma ɗan tsayawa yay kanta yana kallo na sakkanni, kafin ya kai tsugunne gabanta ya ɗaura hannunsa kan nata dake riƙe da gyalen da take lulluɓe a ciki. Ɗan zabura tai na tsorata, dan haka ya saki hannun nata, sai kuma cike da tausasawa ya furta, "Ha Giwar mata, kukan ya isa haka mana. Yau fa rana ce irin ta farin ciki gaki ga Abdul-rasheed ɗinki, kwana da kwanaki an hana min ganinki kewa na neman kaini ƙasa. Bana son kukan nan yana ɗaga min hankali da sukar zuciyata, kiyi haƙuri ki daina yinsa. Ina sha ALLAHU na miki alƙawarin zan kwatanta daga ƙoƙari irin na Inna a gareke, bazan barki kiyi doguwar kewa ba ko yin kukan rashinta a kusa dake. Zan yi ƙoƙarin maye miki gurbin su Bashir, haka kuma zan maye miki gurbi na ƙawayenki. Zan zama adali mai ƙoƙarin sauke nauyin da ALLAH ya ɗora masa na maye gurbin damuwarki da farin ciki, kukan ki da dariya. Kin san ina sonki matuƙa A'ishatu, ba kuma zan daina ba har na koma ga UBANGIJI na in sha ALLAHU". Sosai kalamansa ke tasirantuwa a zuciya da gangar jikin ta, dan haka a hankali ya fara sassauta kukan nata. Da wannan damar yay amfani wajen bata umarnin miƙewa. Babu musu ta miƙe ɗin, dan a nasihar da tasha an tabbatar mata biyayya ga miji shine nasararta kuma wajib ne in har ba akan saɓon ALLAH ba. Sai dai fuskata na rufe a gyalen baya gani komai na jikinta sai hannu da ƙafafu ta ƙasa. "Je kiyi alwala muyi sallar godiya ga UBANGIJI". Nan ma bata musa ba akan umarninsa. Haka ta nufi hanyar fita waje ta ɗauki buta a ƙofar ɗaki, tsaidata yayi tare da takowa ya miƙa mata Torchlight ta ƙarfe da ake ma zubin batira. Ganin ba ganinsa take ba ya kamo hannunta ya saka mata a ciki, kamawar data sakata ƴar zabura kamar ɗazun. Har ma abin ya saka Abdul-rasheed sakin murmushi. Sai kuma cike da zolaya ya matsa jikinta sosai, cikin raɗa a saitin kunenta ya raɗa mata, "Ayi haƙuri a buɗe fuskar kar amarya ta ɓige da faɗuwa ko bige goshi a bango". Murmushi ta saki a karo na farko, sai dai bai gani ba dan ba ganin fuskata yake ba. Amma yanda ta juya da sassarfa yaji a ransa ta murmursa ɗin. Shima sai yay murmushin sosai yana binta da kallo. Kafin ya koma cikin ɗakin yana bin jeren da aka tsantsara musu da kallo daki-daki. Komai ya masa ƙyau, ya kuma ƙayatar da shi. Yana nan a haka harta dawo, baiyi magana ba ya amsa fitilar shima ya ɗauka butar ƙarfe ya fita domin yo alwalar..........✍🏼

*_Ayi haƙuri da jina shiru kwana biyu, an yi mana haihuwa ne bana samun zama shiyyasa. Naga kuma zan raba hankalina biyu sai kawai nace bara dai ayi suna sai mu dawo gaba ɗaya.😀🙏_*

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 12_

__________________

https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6

*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*

*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*

*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*

*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*

_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃

*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 💃_*

20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k

*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. 💃 Ga sauƙi abaka tamkar ƙyauta 💃💃😀_*

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull