Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 11

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 11

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 11: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 11. Babu jimawa ta dawo tace yace gashi nan zuwa. Bata zauna cigaba da cin…

4,320 words

Babu jimawa ta dawo tace yace gashi nan zuwa. Bata zauna cigaba da cin abincin ba ta ɗauka plate ɗin takai kitchen. Koda ta dawo da ruwa a hannunta ƙoƙarin wucewa tai ɗaki. Dai-dai nan Uncle Tasi'u ya shigo falon da sallama. Duk amsawa sukai suna kallonsa. Sai dai zaram Uncle Nasiru ya miƙe yana kallonsa. Shi ko Imran bai san shi ba a zahiri sai labari a sanda wancan abin ya faru, dan haka babu wani alamun mamaki ko damuwa a tare da shi. Sai ma sannu da zuwa da yake jera masa. Sai dai ya gagara amsawa dan hankalinsa shima gaba ɗaya yana kan Uncle Nasiru ɗin ne. "Tasi'u!". Uncle Nasiru ya faɗa cikin matsanancin mamaki da al'ajabi. Karo na farko Tasi'u yay ƙasa da kansa, idanunsa na cika da ƙwalla. Fin sakan biyar kafin ya sake ɗagowa tare da takowa inda Uncle Nasiru yake ƙafafunsa nayi kamar suna rawa. Yana zuwa gaban Uncle Nasirun kawai sai ya zube akan gwiyawunsa. Imran ya zaro idanu waje sosai yana miƙewa, dan zuwa yanzu kam ya fahimci lallai akwai matsala, sannan baƙon yana tare da wani babban al'amari, yo dukda ba yaro bane babba da shi ya durƙusama Uncle Nasiru. Mammah ya kalla, ya ga ta duƙar da ƙai itama kamar mai kuka. Sai shima ya girgiza kansa. Muryarsa a raunane ya ce, "Mammah waye shi dan ALLAH? Naga kuna kama ba ɗan uwa bane ba shin?". Ɗagowa Mammah tayi ta kalla Imran tana ƙoƙarin maida hawayen da suka cika mata idanunta. Fuskarta da ɗan murmushi. Babu wani ko ɗar ta amsama Imran tambayarsa. Dan har cikin ranta kallon Imran take dai-dai da su Haysam. Jinsa take tamkar ɗan data ɗauki cikinsa ta haifa. "Imran Tasi'u ƙanina ne uwa ɗaya uba ɗaya. Baka san shi bane saboda wasu abubuwa da suka faru a baya. Amma sun riga sun wuce na yafe masa. Mun haɗu da shi a asibiti nd kwana huɗu kenan." Gaba ɗaya Imran sai yaji kamar ma yayi mutuwar tsaye. Ga kukan Uncle Tasi'u daya cika falon. Dan kuwa ya riƙe ƙafafun Uncle Nasiru ne yana raira kuka da kalmomin ban haƙuri kamar wani yaro. Yayin da shi Uncle Nasirun ya gagara sake iya cewa komai yana tsaye kawai shima idanun nasa sun kaɗe jazur. Kukan Uncle Tasi'u ne ya sakko da su Aunty Ummi. Ko muce Biebah taje ta kirasu dan komai dake faruwa tana kallo daga inda take laɓe. Ammar daya gama kaiwa wuya cikin fushi ya ce, "Ni wlhy wannan drama ɗin ta isheni haka nan." Duk juyawa su Mammah sukai suna kallonsu, dan basu san da sakkowar tasu ba. Sai dai kan wani yay magana Aunty Ummi ta ce, "Ba kai kaɗai drama ɗin nan ta isa ba Ammar harda mu ma. Shiyyasa ma su Yaya Ja'afar suka bar gidan, dama kuma jiran zuwan Uncle Nasiru kawai mukeyi muma. Idan Mammah nada zuciyar kawaici da haƙuri mu bamu san wannan ba, babu yanda za'ai maciji ya saremu a bakin rami mu sake maida ƙafarmu da tunanin bazai sake na biyu ba. Ai ko hausawa sunce sanin hali yafi sanin kama. Dan haka Uncle! Yaya kodai ku bashi shawarar ya koma inda ya fito, ko kuma ya nema masauki a wajen wannan gidan magana ta gaskiya". Tana gama faɗar haka ta juya zata bar falon tana hawaye. Take mata baya su Ammar sukai suma. Mammah zata dakatar da su Uncle Nasiru ya girgiza mata kai alamar ta barsu.... Dole Mammah tai shiru, shi kuma ya miƙe yana sake faɗin, "Tasi'u tashi muje can gidana, mu basu lokaci nan da kwana biyu." Daga shi har Mammah ɗin babu wanda yay jayayya, dan Uncle Nasiru yaya suke kallonsa uwa ɗaya uba ɗaya. Bayan wucewarsu shima Imran bai jima ba ya wuce gida abubuwa da yawa na masa kai-kawo a rai da zuciya......

(((★)))(((★)))(((★))) ★PRISON★

Yana komawa ɗakinsa ya zauna a gefen gadon sa yana kallon sojojin dake ƙoƙarin ɗaura tvn da suka kammala haɗawa a jikin bangon ɗakin. Baiyi musu magana ba, dan ko gaisuwar da sukai masa bai amsa ba a sanda ya shigo hannu kawai ya ɗaga musu. Suna kammalawa suka fice daga ɗakin tare da maida ƙofar suka rufe masa. Shima sai ya rufe idanu kamar yana barci amma ƙwaƙwalwarsa ce ta shiga aikin aunawa da lissafin abinda ya faru. "Facemask Analysis. Camara jikin agogo". Ya furta a saman lips yana wani ɗan gajeren murmushi har lokacin idanunsa a rufe. A zuciya ya cigaba da ayyana suffar mutumin dalla-dalla da irin ƙwaƙwalwar ma'aikacin daya san aikinsa. (Fuskar bogi, agogo, tsayayyun idanu na masu busashiyyar zuciya da shekarun girma na tantance gwagwarmayar rayuwa na tsawon lokaci. Yanayin motsin ƙwayoyin cikinsu na ƙwararren operatives. Hakan na nufin wani daga cikin manyansu ne. Ba sabon shiga ba. Barazanar da ya faɗa. Sun ce suna sarrafa shugabanni… hakan na nufin akwai infiltration a cikin gwamnati. Wannan na iya zama sashin da ke kai rahoton Board of Inquiry. Ya ambaci makusanta. Hakan na nufin da damar su Imran ya zo wurina shekaru biyar da suka wuce. Yanzu kuma sune suka saka aka dakatar da shi. In dai haka ne to akwai idanu dake zagaye da Imran cikin rundunar soji ko wajenta, lallai Imran zai iya shiga haɗari akoda yaushe dan ko zai mutu bazai bisu fuska da fuska ba. Ya furzar da iska mai nauyi yana runtse idanu, dan Imran wani sashe ne na jikinsa da taɓashi tamkar ruguza jarumtarsa ne. Abu na uku tambayar su (Me yasa suka barni da rai har yanzu? Nima wannan tambayar ta jima a raina. Tabbas da nine a matsayinsu, zan kashe wanda nake tsoro musamman in haɗarinsa zai zama babbar barazana ga ƙasata bawai a karan kaina ba. Amma su suna bukata na a raye. Me yasa?) yay shiru na tsawon lokaci, sai kuma ya tashi zaune da ƙyau ya ɗauki pen da takarda ya rubuta wannan tambayar. _"They need me?. For what? To watch me? To use me? Or to fear me?"_ Pen ɗin ya kai saman lips ɗinsa da suka ɗan bushe dan yau yana azumi. Abu na huɗu (Wasan da suke cewa ya fara… hakan yana nufin wani babban shiri da suke da shi a wannan tsakanin kenan? Wani sabon hari ne?. Ko wata rawar juyin siyasa?. To amma ai basa buƙatar mutum kamar ni wajen gane kosu su waye?, ko ina matsalar?. Wannan kuskurensu ne ko ni ne ban fahimta dai-dai ba?) ya sake yin shiru alamar dogon nazari. Tsohon lokaci yana kai kawo da tunaninsa, sai kuma ya kai dubansa kan television ɗin da aka saka a ɗakin. Karo na farko ya miƙe yana ajiye littafin hannunsa da pen ɗin, gaban tvn ya isa, sai da ya gama duba ko ina na jikinta ya tabbatar babu camara sannan ya ɗauka remote ya fara searching channels, tashoshin dake cikin decoder ɗin da aka haɗata da ita duk zaɓaɓɓune. Domin guda uku ne kacal ba'a komai a cikinsu kuma sai abinda ya shafi labarai. Labaran ma ba kowane labari ba. Dan a yanzu dai kusan harkokin siyasa ne da campaign da aka fara kusan wata uku kenan. Idanun ya janye a hankali cikin salon yin luuu da su ya maida gefe da sakin murmurshin nan nasa na ƙeta. Sai kuma ya maida remote ɗin ya ajiye inda ya ɗauka ya koma bakin gadon ta sake zama.. Gaɓar da tafi tsaya masa ce ta sake maimaita kanta a brain ɗinsa. (Sun ce suna sarrafa zuciyar manyan. Idan haka ne, bayanan da Imran ya kawo min game da janar mai ritaya… dole sai na sake nazari. Domin kuwa wani daga ciki yana iya zama mai sarrafa Janar a gefe, da wannan damar kuma kaɗai za'a iya cimma Imran. Dan tabbas tunda har suka faɗa ya fahimci cewa ziyara ta farko da ta biyu na Imran sun haifar da damuwa a ɓangaren kungiyar shaiɗanun nan, shiyyasa ma suka hana shi cigaba da zuwa. Ya ɗan murmusa kaɗan, dan ya fahimci abu mafi mahimmanci har yanzu suna tsoronsa. Shiyyasa suka hana a ziyarcesa, suka hana yay communication da kowa, suka saka aka killaceshi inda baya ganin kowa sai masu tsaronsa dake kawo abinci dama duk abinda yake buƙata. Ya jima da gane a jikin masu tsaronsa akwai camara dake isar da saƙon shigarsu da fitarsu wajensa. Zuwan baƙon nan ma ba saƙon da yazo faɗa bane kawai maƙasudin zuwansa nan, suna son suga ko ya raunata a zuciya zuwa yanzu. Suna son su gane ko ya ragargaje da raunin kaɗaici. Suna son su tabbatar ko har yanzu yana da ƙarfi daga irin ƙarfin da suke tsoro. Gaba ɗaya ma sai yaji ya sake raina wayonsu. Dan da da gaske, suna da ƙarfin ikon da suke faɗa, ba zasu zo su gaya min ba. Babu mai saƙon barazana da ikon cikakke sai wanda yake jin tsoron wanda aka aika wa saƙo. Yay ƙwafa, saboda wannan tunanin ya ƙara masa ƙarfin gwiwa, da fushi, da nunin ya sake tashi tsaye da shirye-shiryesa. Dole kuma ya aikama Imran saƙo batare da jinkiri ba...........✍️

[12/10/2025, 11:34 PM] Zeenaran 😘: 26

..........KWANA UKU da dawowar Mammah suka karɓi baƙuncin ƴan Bauchi da sukazo sunan Aunty Mommy. Gwaggo Khadijah, Gwaggo Alawiyya, da Gwaggo Nanah. Sai matar Uncle Jamilu da wannan ne karonta na farko da tazo. Dan tun abinda taima su Mammah ɗin a wancan shekarun take jin matsanancin kunyar zuwa inda suke. Sai dai har cikin ranta taji nadama. Musamman da ayanzu su Mammah ɗin ne riƙe da rayuwarsu tunda su Ja'afar ne suka buɗema Uncle Jamilu babban shago kayan sakawa a can Bauchin ƙyauta, da shi suke ci suke sha. Sannan kuma suka ɗauki nauyin karatun yaransu a makaranta mai ƙyau. Gwaggo Nanah kam ta fita zakka a cikin ƴaƴan Inna, tana iya ƙoƙarinta dama tun ma suna cikin wahalar rayuwa kamar yanda Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya keyi. Sai dai tsoron ƴan uwanta su Yaya Babba ke hanata zuwa inda su Mammah suke. Wannan karon kuwa itama sun mata halin nasu, dan mijinta ya gudu ba'a san inda yake ba shekara biyu kenan duk sun ƙi taimaka mata, ga wahala tana ciki ita da yara. Babu mai taimaka mata sai Uncle Jamilu da su Gwaggo Khadijah ɗin. Shiyyasa ta yanke shawarar zuwa sunan nan danta sanar ma Mammah halin da take ciki ko zata samu wani taimako. Kuɗin mota ma Uncle Jamilu ne ya biya mata. Ba ƙaramin daɗi Mammah taji da ganinsu ba. Musamman Gwaggo Nanah da matar Uncle Jamilu Badiyya da suketa ɗari-ɗari suna jinjina hukuncin UBANGIJI da ganin gidan da Mammah ke ciki a yau da zuri'arta. Lallai duniya budurwar wawa, wanda yace shine kuwa ba shi ɗin bane ba. Tuni Mammah ta saka su Kulu masu aiki suka gyaro musu ɗakunan baƙi, dan sunyi isowar wuri lokacin sha ɗaya na safe, sunce tafiyar asuba sukayi dan mota suka ɗakko kai tsaye. Mammah dake ta farin ciki ta ce, "Ku fara yin wanka da ruwa mai zafi sai kuzo ku karya. Bara kiga nasa a kakkaɓo min yaran nan duk suna gado jiya sun raba dare ne suna shargallen su". Gwaggo Khadijah tai ƴar dariya da faɗin, "Aike da gayyar nan taki Maman Ma'aruff sai ALLAH. Kinga barsu suyi barcinsu, muda ba yau zamu koma ba. Anjima ma wata hidimar ce ta bikin suna a kansu". "Kamar ko kin san harda fati suka shirya wai. Biebah ce kawai ta iya bin su Lailah gidan maijegon, yanzu babu jimawa suka fice suma dan jiya sai goma suka dawo". Yanzu kam Gwaggo Alawiyya ce ta ce, "Kai waɗan nan yara ALLAH dai ya saka musu da alkairi. Wlhy samun surukai irinsu sai an tona Addah." "Ai su Shariffa sun wuce surukai ƴaƴane Alawiyya. Babu abinda zan cigaba da musu sai addu'a da fatan suma ALLAH ya basu masu yi musu". Gwaggo Nanah dake jinjina kai ta ce, "Wlhy ki musu ki ƙara muma muyi musu, ga gidan Yaya Babba can su Haire su da surukai ba arziƙi. Jiya matar Haƙilu kamar zatai dambe da Haire akan ɗanta, ke bakiji wannan tujara ba abin kaico". Murmurshi Mammah tayi, saboda a saki zancen ta ce, "ALLAH ya ƙyauta to, ai zamanin ne ya zama abin tsoro sai addu'a kawai. Kunga kuyi wankan kuzo ku karya hirar tafi armashi". Godiya suka yi ta juya ta fita. Dukan su suna jin ƙaunarta a ransu, Badiyya kam kunyarta take ji sosai shiyyasa tunda suka gaisa tai shiru kanta a ƙasa. Sarai Mammah ta fahimceta, dan haka ta ƙuduri aniyar cire mata abinda ke ranta gaba ɗaya, dan ita babban fatanta ta haɗe kan zuri'ar Abdul-rasheed ba rabuwar kansu ba....

★ Sai sha biyu su Nimrah suka tashi da ƙyar, shima sai da Mammah tazo da kanta ta tashesu. Dan suna yin sallar asuba suka koma gado. Aiko sai shagwaɓa suke mata wai ta barsu sai ƙarfe ɗaya sannan. "Shike nan kun fasa zuwa gidan sunan kenan? Ai da nasan haka ne sai na tadaku kun wuce Tahafiz. Ga ƴan Bauchi can tun sha ɗaya suka iso ku kuna nan kuna barci". Tuni duk suka watsakke, cike da farin cikin jin zuwan ƴan Bauchi. Zasu nufi ƙofa a guje Mammah ta dakatar da su. "Kai kuji min ƙazaman banza. Haka zakuje musu da kayan barci? Ba brush kamar wasu ƙazamai. Maza ku koma ku gyara jikinku, wata taje ɗakin Biebah yanda zakuyi sauri". Cike da farin ciki sukace to. Mammah ta fito tana murmurshi. Koda ta dawo falon wajen su Gwaggo Alawiyya ta samu su Ma'aruff sun iso gidan. Dan tun ɗazun ta sanar musu sukace zasu zo yanzu. Sai ko gasu da ledoji niƙi-niƙi na kayan ciye-ciye. Fuskokinsu washe da murmushin ganin gwagwgwannin nasu. Badiyya na sinƙe-sinƙen kai ganin yanda suma basu nuna mata komai ba kamar Mammah sai ta ware aka fara gaisuwa da tambayar yara. Yaya Ja'afar ya ce, "Haba Gwaggo, kwa taho ku kaɗai duk babu yara? Bayan kun san ba ganin juna ake ba tsahon lokaci sai irin haka ta faru". "Makaranta tasa haka Ja'afar, amma in sha ALLAHU idan anyi hutu sai su zo. Tunda kudai kun tattaramu kun watsar, yaushe rabonku da Bauchi balle Maiduguri?". "Dama idan sunje Bauchin ba ganinsu muke ba Adda Khadijah, iyakarsu gidan Yaya Jamilu da Adda Alawiyya. Dan nidai sau biyu suka taɓa zuwa min lokacin rasuwar Inno surukata, da ciwon Ahmadi". "Munyi laifi Gwaggo Nanah, amma kiyi haƙuri zamu gyara in sha ALLAHU. Wani lokacin abubuwan ne ke yawa. Mafi yawan lokuta kuma zuwa Bauchin kasuwa ke kaimu. Ki tambayi Aunty Badiyya sau da yawa shima Uncle Jamilu a kasuwa muke samunsa ba gida muke zuwa ba. Itama Gwaggo Alawiyya takan jima bata gammu ba. Maiduguri ne dai kam ma zamuce muna shiga dan ziyara kai tsaye". "To na gamsu, amma dan ALLAH a gyara, mun san mu masu kuskurene a gareku, amma kuyi mana afuwa kunji, Yaya Abdul-rasheed mutum ne mai son zumunci da Adda A'isha da Adda Yakura, na tabbatar kuma akwai wanan jinin alkairin nasu a tare daku, kar ku biyema aikin son zuciyar wasunmu ku watsar damu gaba ɗaya. Suma lokaci zai yi da zasu yi nadamar abinda suka shuka. Dan har ma wasu sun fara, Yaya Babba a tsakanin nan babu abinda yake sai tafka asarori kala-kala, ga yara cike da gida, mata har huɗu. Yaya Haruna ne ma za'ace da ɗan sauran damshi-damshi. Shi ko Yaya Garzali ma yaje ya tare saudia aikatau ƙiri-ƙiri ko takan matan baya bi sai ya gadama." Sosai zancen ya girgiza su. Sai dai basu ce komai ba face ALLAH ya ƙyauta. A haka Ammar ya shigo shima da Mu'azz. Nan fa falon ya sake lacamewa da farin ciki. Sai kuma gasu Nimrah na fitowa cikin kwalliya tsaff suna baza ƙamshin turaren da suka satarma Aunty Biebah na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Cike da farin ciki suka rungume Gwaggo Alawiyya da Gwaggo Khadijah dan su suka sani sukam. Abin birgewa bazaka taɓa cewa ba jininsu bane su. Sun gaida su Gwaggo Nanah suma. Suka amsa musu da kulawa duk da basu san alaƙarsu da gidan ba. Garama Fiddo ƴar Aunty Mommy data kwana a gidan itama, tunda sun jajje Bauchin ita. Gwaggo Khadijah ta ce, "Oh ni Dije Maman Ma'aruff ƴan matan nawa duk sun miƙe. Kaga yara kamar wasa sun ƙosa. A wannan sai aure". Caraf Mu'azz ya ce, "Tab ɗin wazai kwasa Granny? Wannan gayyar ciwon kan da basu iya komai ba sai dambe da neman masifa da ƴaƴan mutane". Baki duk suka tura gaba. Gwaggo Khadijah ta ce, "Kunga ƙyaleshi ƴan uku Ko nace ƴan huɗu dan banbu Bintu ne. Ai ana yin auren duk zaku daina ko. Kuma dai ai kowa da ƙuruciyarsa, shima idan za'a faɗi abinda yayi ai sai kowa ya gudu". Dariya suka shiga yima Mu'azz suna masa gwalo, shiko yana hararsu da musu alamar zai kama su. Su Yaya Ma'aruff dai na murmurshi ne, Yaya Ammar kam dining ya nufa yana faɗin shifa yunwa yake ji, mi aka dafa ne?. Miƙewa su Nimrah sukai suma suna faɗin yunwar suke ji. Daga haka suka koma kan dinning ɗin harda su Mu'azz aka bar su Yaya Ja'afar suna hira da su Gwaggo Khadijah.....

<<%>><<%>><<%>>

Da yamma shagalin suna aka sha sosai a gidan Aunty Mimi, duk da kuwa haihuwa ce ta huɗu tayi. Babu ƙarya su Nimrah sun cashe da rawa iya iyawarsu. Kasancewar hall aka kama iyakar kuma mata ne kawai a wajen dan ko su Mu'azz basu shiga ba sai abin ya ƙayatar. Ƙarfe shida aka tashi saboda sallar magriba. Nan fa motoci suka fara ɗibar mutane zuwa gidajensu. Su Nimrah dai yau a gidan Aunty Mimi zasu kwana. Dan haka sukabi ƙanin mijinta da yazo kwasar yaranta dana family ɗin mijinta. Duk da dai da farko ca sukai su bazasu shiga cikin yaran ba, sai da Aunty Shariffa ta fara musu faɗa da tabbatar musu zako ta kaɗa kansu zuwa gida sannan suka nutsu saboda suna son zuwa can ɗin su ƙarasa weekend ɗin su. Ga Bintu kuma ta ƙaru sun zama su huɗu yanzu. Haneef dake matuƙar son Ruƙayya na sharewa yana faman murmushi yace su jira shi ya kai yaran ya dawo to. Feedo ce ta amsa masa da "To Uncle". Su Ruky kam aka wani ɗauke kai gefe. Murmurshin shaƙiyanci Nimrah tayi, tare da ɗagama Bintu gira ɗaya cike da gulma. Aiko suka kwashe da dariya. Ruky da tasan da ita suke ta balla musu harara da jan tsaki zata bar wajen Nimrah ta riƙota........✍️ [12/10/2025, 11:35 PM] Zeenaran 😘: 27

........."Sorry Trouble Buddy na. ALLAH ke ɗin ce kin cika wulaƙanci, Uncle Haneef fa ya haɗu ALLAH. Amma kiyita wani shan ƙamshi. Dan ALLAH ko kaɗan ki dinga kulashi mana, ALLAH idan ya ganki zakiga duk bakinsa yaƙi rufuwa". "Ai shiyyasa bazan kulashin ba. Ni fa bana son susun namiji haba. Mutum babu wani jan aji. Kuma ni an faɗa masa za'a min aure ne yanzu mtsoww!!". Bintu dake dariya ta ce, "Baby ai kece zaki saita shi yanda kike so. Amma kina wani yayyarfashi, jifa da salla yanda ya mana siyayya". "Mayya dama ke ai kwaɗayi ne zai kashe ki ke da Ninah". "Ya kashe mu dai, tunda tare muke". Cewar Nimrah tana hararta. Ramawa tai itama, sai dai dai-dai nan Haneef ke dawowa dan haka hirar tasu ta tsaya. Fitowa yay da kansa ya buɗema Ruky gaba, zata zille ta shiga baya inda su Nimrah ke shirin shiga suka turata suna ƙumshe dariya. Juyawa Haneef yay ya kallesu da musu jinjina yana murmurshi. Daga haka ya rufe mata ƙofar ya zagaya dan suma har sun rufe. Yana fara tafiya a titi ya ɗan kalla Ruky, cike da son birgeta ya ce, "Muje shan Ice-cream ne Baby?". Kai ta girgiza masa alamar a'a. Sai ya ɗan marairaice fuska, tare da maida lallonsa kan su Nimrah dake baya ta mirror. "Yaran Uncle muje mu sha ice-cream ne?". Cike da iyayi Feedo ta ce, "Yes Uncle". Nimrah zatai magana Bintu ta rufe mata baki, dan sun san bakinta ɗaya da Ruky. Ganin zata fisge itama Feedo ta ɗaura nata hannun akan na Bintu suka haɗu suka danne Nimrah. Sai da ta sakar musu wasu shegun mintsini masu zafi suka saketa kowanne na sosa wajen. Badan Nimrah da Ruky sun so ba akaje wajen shan wannan ice-cream dai. Haka ya jasu har ciki kowacce ta zaɓi flavor ɗin da take so. Ya ƙara musu da snaks. Duk yanda suka so ya maida su gida ƙi yay, haka ya janye ra'ayinsu suka zauna a wajen. Sai dai rashin sabo ya sasu kasa sakin jiki su dukansu. Dan abu ne da su dukansu ba tarbiyyarsu bace. Shi ko yanata tsiyaya musu zance da ɗaukarsu hoto da wayarsa iPhone. Ganin fa an fara sallar isha'i hankalin Nimrah ya tashi. Dan in har ka gansu a waje irin wannan lokacin tabbas da wani a cikin Uncles nasu ne ko Ya Mu'azz ko Aunty Biebah ko kuma sun raka su Aunty Lailah anguwa ko Ammie. Amma basu kaɗai ba balle wannan da saurayi ma wai. "Nimrah ya naga kin miƙe?". Haneef ya faɗa yana kallonta. "Uncle Haneef kayi haƙuri ka maidamu gida. Wlhy idan Mammah taji zatai mana faɗa, balle Daddy ko su Uncle's". "Haba-haba ai in sun san nine babu wani faɗa da zasuyi". Miƙewa itama Ruky tayi, hakan yasa suma su Feedo duk suka miƙe. Kafin ma Nimrah ta bashi amsa Feedo ta ce, "Wlhy Uncle koni Abbana ya sani ubana zai ci. Muje ɗin kawai ma ƙarasa a gida". Babu yanda ya iya dole ya miƙe, ya tayasu tattare kayan suka fito. Kamar ɗazu yanzu ma dole Ruky gaba ta shiga. Cikin ƙankanin lokaci ya iso gidan Aunty Mimi da su. Yay horn maigadi ya buɗe masa gate ya shige. Suna fitowa a motar maigadi ya iso inda suke. Kai tsaye gaban Nimrah ya isa yana miƙa mata ledar hannunsa da faɗin, "Hajiya gashi wani yace a baki. Yata jiran dawowar ku amma yaji shiru yanzu babu jimawa yabar wajen nan." Ba ita ba hatta su Ruƙayya da mamaki suke kallonsa. Cikin kasa daurewa Nimrah tace, "Kuma ni Nimrah yace a bamawa?". "Tabbas ke yace, yace sunansa Kamal malaminku na islamiyya". Ruky ce ta amshi ledar tana faɗin, "Wato shima Sayyadi Kamal ɗin nan ɗan naci ne fa na lura". Daga haka tabar wajen fuuu. Tsaff su Nimrah sun fahimci fushin Haneef tai amfani da shi akan Kamal. Dan haka suka wayance da masa godiya suka shige cikin gida. Sun sami sauran dangin mijin Aunty Mimi da basu kai ga wucewa ba. Suka gaishe su suka wuce ɗakin da suke sauka in har sunzo gidan. Dama can suka kai kayansu da daddare. Ƙaton gado ne da zai iya isarsu koda su shida ne a ɗakin, sai wadrobe da mirror, sai ƙofar bayi. Kayan hannunsu duk suka ajiye suna zubewa a gadon kowa na faɗin wash, dai-dai nan Ruky data rigasu shigowa ta fito daga bayin alamar har tayi alwala. Suma duk miƙewa sukai, dan rashin yin sallar akan lokaci na tsaye a ran kowannensu. Bintu ce kawai ke period dan haka taja ledar snaks ɗinsu ta fara ci tana faɗin, "Bari muga mi Sayyadin ya aiko mana da shi shi kuma". Tsaki Nimrah tayi a karo na farko tana shigewa bayi abinta. Fiddo ta sanya dariya dan Ruky ma harta kabbara salla. Dariyar su Bintu data cika ɗakin ya saka Nimrah fitowa da sauri, itama Ruky dai-dai tana idar da sallar ta juyo tana kallonsu. Litattafai ne a ledar saƙon Sayyidi Kamal suka nuna musu. Feedo ta ce, "Wannan fa shine auren ustaz ɗin, kaga wata lukutar jaraba wai saƙon littafai. Ninah kina cikin yanayi gaskiya". Nan ma dariya suka sanya harda Ruky yanzu kam. Dan haka Nimrah ta watsa musu harara ta kabbar sallarta itama. Koda ta idar sun gama mata shaƙiyancin nasu, dan haka bata sake tada zancen ba ta haye gadon ta kwanta wai kanta ke ciwo. Da ƙyar suka lallaɓata ta zauna suka ƙarasa shan Ice-cream ɗinsu da snaks ɗin bayan Feedo ta idar da salla itama. Dan haka koda Aunty Mimi tai kiransu suzo su ɗeba abinci sukace mata sun ƙoshi. Bata takurasu ba dan taga abinda suka shigo da shi, ta kuma san aikin Haneef ne......

<<<<<<(⁠✷⁠‿⁠✷⁠)>>>>> ★CAMPAIGN★

Kwanaki 100 na campaign suna gab da cika, dan kuwa ana satin ƙarshe na kammala taron kowane kamfen. Dan haka amsa kuwwar cikar kwanakin tamburan siyasa na gab da cika, tako ina ƙasa ta kara hargitsewa dan kowa burinsa satin ƙarshen nan ya tumfayesa da zuciyar yan kasar. Baka iya jin komai sai sautinkan waƙoƙin da aka rairana ƴan siyasa. Yayinda hankalin matasa kacokan ya koma can. Wasu ma sun ajiye harkokinsu da sana'o'in su ne kacokam. Kamar dai yanda aka saba alƙawuran nasu guda huɗu ne ga al'ummar ƙasa a lokacin da suke kan munbarin campaign. Zamu gyara muku harkar karatun, zamu inganta wutar lantarki, zamu wadata ku da ruwa, zamu gyara asibitoci. Cikin rashin lissafi da auna abubuwa a yanda ya dace, da taro da kwabon da ake raba mana mu talakawan ƙasa da ɗan sabulai da zannuwan ɗaurawa mai hoton ƴan siyasar a jiki sai kaji mun sallama muna bada kai bori ya hau. Babu ruwanmu da tantance wane shugaban ya dace damu? Mi muke so a ƙasar da kawunanmu bayan waɗan can lissafin huɗu da ko a karatu sukazo ya kamata ace mun haddace su tsaff zuwa yanzu daga daɗin bakinsu mu nemo cigabansu. Amma ina babu batun tantancewa, a wasu wajajan ma siyasar ta haɗa rigima ne tsakanin ƴan uwan juna saboda ni ina son wannan wane ɗan uwana yana son wancan ba jam'iyyar mu ɗaya ba. Wasu har gaba zakaga ta ƙullu mai girma a tsakaninsu. Yayinda su ƴan siyasar da sukeyi domin su suna can tare suke shan shayi, tare suke ƙulla mai fishshesu musamman akan abinda zasu ribantu da shi game da kuɗaɗen da suka kashe wajen jawo ra'ayinku idan sun haye. Wanda ma bai haye ba akwai hanyoyin da za'a bi dan maida masa wahalarsa ta bayan fage kune a ruwa...

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull