Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 10
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 10: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 10. Koda su Oga Jush suka gama sauraren Dagger sai ya saki wani murmushin da…
4,492 words
Koda su Oga Jush suka gama sauraren Dagger sai ya saki wani murmushin da akan jima ba'a gani akan fuskarsa ba. Kafin kowa yay magana shiya fara faɗin, "Yarinyar takai shekara nawa yanzu?". "15years ne Sir, harda kusan watanni biyar". "Zamu iya ganin hoton ta?". "Har ma videos akwai Sir, dan tunda aka sanar mana tana raye tare da shi Molen a kuma gidan su Zak-Shadow shekara huɗu kenan na saka ana bibiyar al'amarinta batare da ko shi kansa Mole ya sani ba." "Shiyyasa kake birgeni, dan kasan aikin ka sosai". Oga Jush ya faɗa yana ma Dagger murmurshi. Suma sauran dai sun nuna alamun jin daɗin abinda Dagger ɗin yazo da shi. Dan su biyar ne kacal a meeting ɗin iya su manya. Oga Jush, Black Spider, Mr Specter, Viper sai shi Dagger ɗin dake matsayin yaro. Babu wani ɓata lokaci Viper ya amsa wayar Dagger akai connecting da ƙaton television ɗin dake meeting room ɗin. A take hotunan kyakkyawa Nimrah suka fara bayyana a mabanbanta wajaje. Makarantar Islamiyya da boko, wasu wajajen ma a super market ne sunje shopping, wasu taron Birthday party ne na ƙawayensu kona cikin family. Babu dai wanda suke a titi kasancewar babu inda ake bari suna zuwa da kansu a abin hawa na kasuwa. Kusan a waje uku akwai Ruƙayya a ciki, ɗaya da Mu'azz da Biebah. Sai da suka kammala kallo har ƙarshe da videos ɗin ma kafin Mr Specter yay tambayar sauran wanda suka gani tare da ita. Kai tsaye Dagger ya fara musu bayani yana dawo da duk inda take ba ita kaɗai ba baya. "Wannan ɗiyar abokin nan nashi ce Imran, koda yaushe suna a tare, da alama itama yarinyar ta koma gidan su Zak-Shadow ɗin da zama ne. Duk wani rashin ji tare suke yinsa sunanta Ruƙayya. Wannan kuma namijin sunansa Mu'azz, ɗan ƙanwar Zak-Shadow ɗin ne, ubansa kuma yayan Imran ne wanda in baku manta ba farkon aikinmu muka nema bayanan Zak-Shadow a wajensa yaƙi bayarwa aka saka Zinga ya kashe shi. Sai babbar autar su Zak-Shadow ɗin ce wadda ubanta da ban a cikinsu." "Lallai yara sun ƙosa". Cewar Black Spider yana dariyar ƙeta. Suma sauran dariyar suka ɗanyi. Kafin Mr Specter ya sake faɗin, "Miye labari akan yarinyar?". "Bata jin magana ƙwarai da gaske oga. Dan a duka makarantun da tayi babu inda sunanta bai zama fitacce ba ita da wannan ɗiyar Imran ɗin. Fitinannun yara ne na bugawa a jarida. Bata san wani abu tsoro ba, balle kurari. Ga kauɗi da jarumta". "Wannan kam kayanmu ce. Za kuma a amfana da ita kwarai da gaske. Kamar yanda uban nata ke burin ta dawo hannunsa zamuyi amfani da hakan zakuma mu dawo masa da ita. Ko muce zata dawo garemu." "Sir ai ba dawowar ce matsala ba, shima fa uban kansa ta manta waye shi. Mutanen gidan kawai takema kallon ahalinta." "Zamu goge mata duk wannan tunanin. Dole tasan ainahin ubanta a yanzu. Ta hanyar sanin makashin uwarta da zuri'arta". Duk kallonsa suke alamar basu fahimta ba. Dan haka kai tsaye ya ce, "Zamuyi amfani da edited video ɗin nan. A nuna mata shi, shi ne kawai zai sata fara bincike da neman hanyar sanin ainahin maruƙan nata, da sanadin zuwanta gidan. Mu kuma sai muyi amfani da damar binciken nata mu jawota jikinmu muna bata dukkan information ɗin da take nema da buƙata. A ƙarshe mu sakata yi mana aikin da muke buƙata akan family ɗinsa, sai dai zamu ƙarfafata ne akan itace zata ɗauki fansa". Cike da gamsuwar bayanin ogan nasu suka shiga tafi farin ciki na bayyana akan fuskar su. Shi kansa Dagger bakinsa yaƙi rufuwa dan daɗi, a ƙasan ransa kam ayyana wa yake masoyiyarsa ta kusa zama tashi dai kenan. Dan tun sanda aka fara kawo masa hoton Nimrah da videos yarinyar taima zuciyarsa shigar sauri. Ya kuma yi ma kasan alƙawarin mallakarta matsayin mata. Yanda ya gama zama tuzurun nan shekara da shekaru babu aure sai a kan ƴaƴan titi yake sauke lalurarsa ya samu wannan ƴar shilar ai ya gama nasara. Dan tabbas zai sheƙe ayarsa gwargwadon iko... Ƙarƙarewar zancen ta katse masa tunani, dan Oga ya bashi damar zuwa su samar da wanda zai musu aiki ta bayan fage daba a cikin gidan yake rayuwa ba. Sai Mole ya kula da komai. A karo na farko ma Oga Jush ya bada damar Dagger ya kawo masa Mole gabansa da yana son ya gana da shi. Duk da Dagger yaji wani iri a ransa baiƙi amsa umarnin ogan ba. Amma zuciyarsa sai faman kai-kawo take akan miyasa oga Jush ɗin ke son ganin Mole a karo na farko? Shifa koma mi za'ayi ayi amma kada ace za'a shiga al'amarinsa da Nimrah, dan bazai iya ɗauka ba. A zahiri dai baice komai ba. Ya amshi maƙudan kuɗaɗen da basa gajiya da bashi yay musu sallama ya tafi ransa fal wasi-wasi.........✍️
[12/10/2025, 11:31 PM] Zeenaran 😘: 23
.........A wannan rana ƙarfe sha biyu na rana jirgin su Mammah ya sauka, tare take da Ammar ɗinta sai ƙaninta Tasi'u da Ammar ke kira Uncle. A tsakkiya suka sakata har inda motoci suke. Aiko cikin sa'a sukai arba da tagwaye biyu Yaya Ma'aruff da Ja'afar da suka zo ɗaukarsu da kansu. Sai dai me suna yunƙurowa a tare suka koma suka ƙame kamar gunkinaye idanunsu akan Uncle Tasi'un. Dan duk da suma suna yara sosai ya aikata abinda ya aikata hakan bai sa sun mance wannan fuskar tasa ba. Dan bayan mahaifin Biebah shine mutum na biyu daya bar musu tabo a zuciya na zahiri. Abinda dangin mahaifinsu suka aikata duk a labari suka sanshi, a labarin ma ba komai ba daga bakin Mammah ko Dadansu. Gwaggo Alawiyya ce ta gaya musu komai. Ganin yanda sukai ɗin ya saka Mammah cikin dakewa furta, "Oh bakwa farin ciki da ni na koma kenan ko?". Jikinsu ne yay sanyi, cikin dauriya da danne zukata suka nufota, batare da ko kallon Uncle ɗin nasu sun sake yi ba suka rungumeta ita da Ammar suka manta da shi. Ammar daya tsargu da abinda ya farun da ƙyar ya iya dannewa yana murmurshi. Haka suka kama Mammah a tsakkiya har mota. Sai da ta shiga suma suka shiga Ammar ya shiga, ganin Uncle Tasi'un bai shigo ba Mammah tace su masa magana ya shigo. Kallonta sukai kamar zasu fasa kuka. Amma kallon da itama tai musu na gargaɗi ya sasu risinar da kawuna Ja'afar ya fita yay masa magana. Sum-sum kamar munafuki ya shiga kusa da ita suka sakata a tsakiya shi da Ammar......
Sun iso gida da yake shiru kasancewar basawan cikinsu duk ana makaranta. Masu aiki ne kawai sai Aunty Shariffa da Aunty Lailah da yay basu je gidan haihuwa ba saboda dawowar Mammah. Hasalima da kansu suka shiga kicin yi mata abincin da suka san tafi so da ƙauna. Masu aiki da suma ke farin ciki da dawowarta na tayasu da ƙananun ayyuka. Daga Aunty Shariffa har Aunty Lailah kowace fama take da ƙaramin ciki, dan cikin ikon ALLAH kamar yanda sukai haihuwar su Abees a tare da tasu Afrah da Ayyan haka wannan cikin ma basu da nisa a samu. Sai dai Aunty Lailah ce ta fara samu kafin Shariffa. Dan haka nata yafi fitowa sosai har ana iya gani. Mu'azz ya fita akan batun karatunsa dan Imam ne yazo har gida suka fita a mashin ɗinsa. Wannan ya ƙara haifar ma da gidan shiru. Motar su Mammah na gama tsayawa Lailah da Shariffa suka fito cike da ɗoki da farin ciki dan Mammah uwa ce a garesu ba uwar miji ba. Itama fuskata ƙawace da murmushi ta fito da taimakon Ammar. A tare ta kamosu jikinta ta rungume tana mai jin farin cikin ganinsu da sanya musu albarka. Yayinda suma suka zame suka zube cike da girmamawa suna mata barka da dawowa. Ta amsa musu da kulawa tana kamasu ta miƙar. Cike da tsokana Ammar ya ce, "Wato kunga Mamanku ni in ma na ɓata a can babu ruwanku ko Auntys?". Yanda yay maganar yana cika baki da iska har su Ma'aruff dake faman haɗe fuska saboda Uncle Tasi'u Sai da suka dara. Suma cike da tsokana sukace, "Mu mun isa muso kawun yara ya ɓata. Ai sai suyi mana bore suma Yaya Ammar". "Ato naga ba'a wani ji dani ne sai Mammah kawai". "To ayi haƙuri, kasan rashin ta ya maida mu kamar marayu a gidan cike muke da ƙaguwar son ganinta. Kaima bari kaga ƴaƴanka su dawo duk kanka zasuyi". "Ai shiyyasa ma ban damun ba. Dan da kaina zanje na ɗakkosu a schools". Duk hirar da suke zugawa Uncle Tasi'u na kallonsu ne kawai cikin damuwar kallon banzar da su Ja'afar ke masa a kaikaice. Su ko su Lailah basu lura da shi ba sai daga baya. Kamaninsa da Mammah dake a bayyane ya sakasu kasa jurewa suka bishi da kallon sakanni. Sai kuma suka duƙar da kawuna cikin ƙaulani da rashin tabbaci suka shiga masa barka da zuwa. A karo na farko yaɗan sauke ajiyar zuciya. Dan koba komai girmamawar tasu ta ɗan sakashi jin sanyi a ransa. Ya amsa musu da kulawa shima. Mammah ta katse su da faɗin, "Kumuje ciki kun san fa ni bana jurar tsaiwa". Da to suka amsa mata suna sakata a tsakkiya, dai-dai nan kuma maigadi da sabon driver suka iso wajen cike da girmamawa suka duƙa har ƙasa suna gaida Mammah. Tabbas Mammah zata iya haihuwarsu idan muka musalta da yanayin auren da na ƙarancin shekaru musamman ma itama da akai mata tana ƴar 14. Dan driver dai zai iya zama sa'an Dada, maigadi ko bai wuce sa'an su Yaya Ja'afar ba, idan ma Dada zai girme ma sabon driver ɗin kaɗan ne, sai dai yanayin jin daɗi ba ɗaya ba, duk da a yanzu basu san yaya Dadan yake ba amma ya fishi ƙyawun jiki da ƙuruciyar zahiri. Dan shi wannan ma har furfura ta cika masa gemu duk da dai kansa akwai hula tashi da ƙwaƙwa baƙa data ɓoye gashin kan nasa, sai na iya fuskar zaka shaida zuwa gemu dan yana da saje... "A'a bawan ALLAH tashi-tashi kaji, mun sameku lafiya ko Almu. Ka yi baƙo ne?". Maigadi ya bata amsa da mata bayanin ba baƙonshi bane su Yaya Ma'aruff ne suka kawo shi. Kafin tace wani abu sabon driver wanda shima a karo na biyu fuskarsa da murmurshi ya amsa mata, kafin ya miƙe yana sake mata barka da dawowa da sannu da jiki. Sannan ya juya yana gaida Uncle Tasi'u da Ammar. Ma'aruff ne ya juyo yana kallon Mammah ya ce, "Sabon driver ne daya maye gurbin Baba Ari. Sunansa Buba kwana uku da tafiyarku ya fara aiki". Fuskar Mammah da fara'a sosai ta ce, "Masha ALLAH. Sannu da zuwa Malam Buba. ALLAH yasa zamanmu tare ya zama alkairin da zamu shiga aljanna gaba ɗaya. Ina dai fatan babu wani damuwa a zamanka tare da mu ɗin?". "Amin Hajiya. Amin Amin. Babu wata damuwa sai godiya tsakanina da ku. Dan kuwa kwanakin da nai kawai na shaida alkairin mutanen wannan gida." "To Alhamdullahi ALLAH yasa mu dace. Bari naje na huta munsha zaman jirgi zuwa anjima ka shigo mu ƙara gaisawa?". "To to shike nan Hajiya, ALLAH ya huta gajiya nagode sosai." Fuskar Mammah da murmushi ta amsa da amin Kafin su Shariffa su kamata har zuwa ciki. Shi dai Uncle Tasi'u na biye da su sum-sum kamar munafuki, sai dai harga ALLAH yayi matuƙar girgiza da ganin irin wannan katafaren gida mai kama da wani ƙaramin estate wai duk mallakin Adda A'isha ne da zuri'arta. Addarsa fa dake wujiga-wijiga akan marayun ƴaƴanta dana gayyar soɗi na kishiya data kama ta riƙe ita mai son miji. Addar nan tasa dai daya damfara gida ya gudu ya batta da sanin bata ga tsuntsu bata ga tarko a lokacin, amma a yanzu sai gasu a wannan ƙosashen gidan a babban birnin tarayyar ƙasa da dukkan alamu suka nuna nasu ne, kai shifa tun a motar dasu Ja'afar ɗin suka ɗakkosu dama zuciyarsa ke bugawa, yanzu kuma da suka shigo gidan ma sai yaga motocin da sukafi wadda suke ciki, sannan ba ɗaya ba a ƙalla motoci sun kai bakwai a gidan harda wadda suka dawo ta takwas. Bai ji zuciyarsa na tsitstsinkewa ba sai da suka shiga cikin katafaren sashen Mammah ita ɗaya, dan dama sashenta dana Dada sunfi kowanne girma a gidan. Kafin kace mi kuma ƴan aiki har uku sun zagayeta suma da tasu gaisuwar girma. Ga waɗan nan tsala-tsalan matan daya fahimci matan su Ja'afar ne sai rawar jiki suke akanta kamar wata uwarsu mahaifiya...
.....★DUBAI★.....
"Inaga a wannan gaɓar zan saka a kashe mijin nata, dan hakan ne kawai zai saka ta yarda ta saduda ta mallaka min kanta". A wani irin firgice Hajiya Hasiba ta ɗago tana kallon Adeel mai maganar. Mamawo kuwa abincin da suke ci ne ya nema ƙwareta. Sai da ta ɗauki ruwa tasha da sauri. Shi ko ko'a jikinsa, dan tamkar ma bai ga halin da suke ciki ba ya cigaba da maganarsa. "A karo na farko ina son sanin wanene shi mijin nata? Miya taka a ƙasar taku? Ɗan wace zuri'a ce? Miye ƙarfin ikon sa?". Su duka biyun rasa mai bashi amsa akayi, dan dama daga su sai shi ne a dining room ɗin. Su Ismat sunbi Nabeeha sun fice a gidan tun da sukaji zancen zuwansa. Ɗan dukan table ɗin yayi ta yanda suka dawo hayyacinsu firgigit. Da ƴar tsawa da raini da wulaƙanci ya ce, "Ko kuma kuna bin bayan wulaƙanta ni da take ne....?" "A'a wlhy bama bin bayanta. Da muna da iko da zuciyarta ma da tuni kun jima da zama ma'aurata maybe ma kun haihu. Mijinta ba kowa bane, ba ɗan kowa ba, baya da komai, baya taƙama da komai. Kawai soja ne a ƙasar mu, kamar yanda muka sanar maka tun farko kuma yana prison yanzu haka, shekaru ashirin da biyar kuma aka yanke masa a can". "What! Shine kuma take tunanin zaman jiransa?". "Shirmenta ne kawai Prince, amma tun kan ya shiga prison ma ita ta bar masa gidan sakamakon auren yarinya ƴar shekara 7 da yayi saboda ya ɗakota a wajen yaƙi. Daga ƙarshe ma mukaji ashe shine ya kashe mata iyaye dan ya aureta, da alama wani laƙanin asirin aka bashi dan dama yanda yake juya sojojin da wani gadararsa har manyan suna tsoronsa kai ka san ba haka kawai bane, dole akwai aikin asiri a ciki". "Woow naji daɗin wannan labarin ƙwari da gaske. Yanzu ita yarinyar tana ina ne?". "Tana a gidansu tare da ahalinsa. Sai dai a yanzu takai kusan 15years da wasu watanni". Komai bai sake cewa ba ya miƙe kawai, da kallo suka bishi yana tafiya cike da ƙasaita da gadara, sai da yaje gab da fita a dinning room ɗin sannan ya juyo yana kallonsu. "Zamuje ƙasarku tare da ɗaya a cikinku". Daga haka ya fice abinsa batare da jiran amsarsu ba.........✍️
[12/10/2025, 11:31 PM] Zeenaran 😘: 24
..........Shiru sukai kowa ya gagara iya cewa komai. Sai zuwa can Mamawo ta ja numfashi mai ƙarfi ta furzar. Sai kuma ta ajiye spoon ɗin hannunta ta rabga tagumi da hannu biyu. "Anya Aunty mutumin nan bada wata manufa yake son Nabeeha ba?. Wlhy nikam al'amarin nan fa ya fara bani tsoro gaskiya. Duk matan ƙasar nan ko a cikin nan Dubai irin sa, da masu shigowa baƙi kullum, dana ƙasashen da yake yawo ace ya rasa matar aure sai Nabeeha da aka jima da sanar masa tana da miji. Abin mamaki duk cin kashin da take masa bai taɓa nuna koda damuwa a fuska ba balle zuciyarsa. Kai wannan batu yana buƙatar dubawa fa. Kalla gidan nan daya mallaka miki halak mallak, ga motar hawa, mu dukanmu yasa akai mana katin zama ƴan ƙasa. Yanda suke da ƴanci a ƙasar nan haka fa muma muke da ƴancin shiga duk inda muke so a lokacin da muke so.."
"Ni kaina a wannan gaɓar na fara tsorata Mamawo. Balle ma maganar kashe Haysam da yayi, bawai bana son ya kashe san ba. Nasan wannan kuma abu ne mai sauƙi a wajensa aikata hakan. Babbar damuwar wataran Nabeeha tasan yanda komai ya faru wlhy bazata rufa mana asiri ba. Dan tsaff zata ce damu aka haɗa kai akayi. Shi yana da kuɗi da mulkin da zai cire kansa, muko mune a ruwa.." "Tabbas zancenki na kan hanya Aunty, sai dai ai zamu iya roƙonsa karya sanar mata, sannan zuwan da zai yi ma duk yanda zamuyi kawai muyi kada ta sani. Dan na tabbatar ya samu Nabeeha duk abinda muke so a duniyar nan zamu sameshi a wajensa, ni dai kawai babbar damuwa ta mu fara sanin wai minene ma manufarsa akan son nata". "To ta yaya zamu sani kuwa Mamawo? Tunda ba zuciyar tasa zamu tsaga mu duba ba". "Ai bata wannan ake gane sirrin zuciya ba Aunty, shiryawa zakiyi wuff muje India wajen mai mun aiki, koma minene shirinsa sai ya sanar mana shi". Shiru Hajiya Hasiba ta kasa magana. Bawai bata bin bokaye bane, sai dai mafi yawa irin wannan leƙe-leƙen bata yinsu a karan kanta first lady ce ke aikenta, kuma tunda suka sauka a mulki ta ɗan rage yi sai na kan kasuwanci da takan je mata, wani lokacin kuma suje tare..... "Aunty kinyi shiru?". "Ba shiru nayi ba Mamawo, ina auna yanda tafiyar tamu zata kasance ne, balle kinji shi yace zai tafi da wata a cikinmu. Kinga bamu da tabbacin yaushe ne ko?". "Haba aunty mu sai kace ba mata ba. Zaki iya bagarar da shi akan tafiyar gaggawa ta taso miki wani business ɗinki haka. Kinga sai muyi mu gama da wuri mu dawo. Dan haka ya kamata ma ace cikin watan nan mu tafi". "To bari muga zanyi tunani". Daga haka ta miƙe tabar haɗaɗɗen dinning room ɗin da aka cika kayan abincin alatu duk saboda Adeel. Sai gashi ko cikakken lauma uku baiyi ba ya tashi ya barsu da kayansu.....
<%><<<%>>><%>
Mintuna talatin da isowar Mammah da Ammar su Aunty Ummi suka shigo gidan ita da Aunty Mommy. Cikin matuƙar farin ciki suka rungume Mammah dan yanayin ta kaɗai ya tabbatar musu da lafiya ta ƙara samuwa Alhamdullah. Suma dai hankalinsu bai kai ga Uncle Tasi'un ba sai da suka gama gaishe-gaishen su. Turus sukayi suna kallonsa. Ba kallon sani ko tuna waye shi ba. Kallon mamakin kamaninsa da Mammansu kawai. Dan suma sanda wancan abin ya faru basu da wayon tuna komai gara ma Ma'aruff da Ja'afar ɗin. To balle ma Mimi ƴar ƙarshe ita da Ammar da lokacin basu wuce shekaru shuda ba. Biebah kuwa na jaririyar wata baifi biyu ba. Maida kallonsu sukai ga Mammah, kafin ma suce wani abu ta basu amsa da, "Kawunku ne". "Kawunmu Mammah? Na ina to? Mudai a sananinmu ƙannenki duk sun rasu, gashi kuma yana kama da ke". Sai da ta ɗan girgiza kanta da murmurshi kawai sannan ta ce, "A'a Bashir ne dama ALLAH yay ma rasuwa, Tasi'u kam ƙaddara ce ta nisanta mu". A take murmushin fuskokinsu ya ƙarasa ɓacewa. Dan duk da bata taɓa basu labarin abinda Uncle Tasi'un ya aikata mata ba duniya ta jima da sanar musu. Koma suce cikin danginta. A taƙaice sukace, "ALLAH sarki". Tare da gaisheshi sama-sama suka bar wajen. Cikin sake raunanuwar zuciya Uncle Tasi'u ya bisu da kallo. Mammah da duk take jin babu daɗi da yanayin tarbar da ɗan uwan nata ke samu wajen ƴaƴanta cikin sanyin murya ta ce, "Sai kayi haƙuri da abinda zaka gani a wajensu. ALLAH ne shaida ban taɓa sanar musu koda kuskuren dangin mahaifinsu ba balle naka a gareni, sai dai yau da gobe ta wuce wasa duniya da dangin sun gama sanar musu batare dana sani ba. Amma ka bani lokaci ƙanƙani, in sha ALLAHU zan zauna da su ni da Yaya Nasiru zasu fahimta". Murmurshin ƙarfin hali yayi cikin girgiza kai. "Ba komai Adda, kuma ki sani ni banga laifinsu ba sam. Kawai ina jin tsoron isowar yaran nan da kullum zancen su danginsu danginsu kuma su fuskanci abinda bashi nake fata ba daga dangin. Nine nai laifi basu ba, dan haka dan ALLAH ko sunzo suyi haƙuru su su amshesu koda ni bazasu ashe ni ba". "Kaima zasu amshe kan in sha ALLAHU. Kadai bani lokacin. Bismilah muci abinci sai ka samu kaje ka watsa ruwa lokacin Azhar na gabatowa. Yanzu kuma gidan zai sake rikicewa dan masu shi na gab da dawowa daga makaranta". Murmurshi kawai yayi. Ya gyara zama ya fara cin abincin da aka shirya musu a tsakkiyar falon....
★★★
"Tab ɗi, wai yaya mi hakan ke nufi? Miya kawo wannan mutumin rayuwarmu a wannan gaɓar? A ina ma su Mammah suka samo shi wai shin?". Ya ƙare maganar tana kallon Ammar. Ammar cikin sake ɓata fuska ya ce, "Aunty acan muka haɗu da shi cikin asibiti fa. Ni kaina nayi mamaki da Mammah ta bashi damar wai ya biyomu, nazata kawai zata barshi ya koma inda ya fito ne". Hawaye Aunty Momy ta share, muryarta na rawa ta ce, "Sun manta damu a lokacin da muke buƙatar tainakonsu da ƙarfinsu. A yanzu zasu fara dawowa rayuwarmu kenan a lokacin da ƙarfinsu ya ƙare mu mukai ƙarfin. Ni tsorona ma kada ya sake zuwa yaye dukiyar tamu ne ya gudu". "Shi ɗin banza". Cewar Ja'afar a hasale. Ya cigaba da faɗin, "Ai ko a wancan karon dan Dada baya nan ne ya samu nasara, kuma yana da hakki a wancan amma a wannan fa. Ko a yanzu da babu Dada akwai halifofinsa a kusa. Idan da rabon yazo yayi ta ransa ne bismilah". Cikin furzar da iska Ma'aruff ya ce, "Wlhy ni nama rasa tacewa sam. Amma al'amarin ɗan adam bai taɓa bani ƙarshen mamaki ba irin yau. Wai dama Uncle Tasi'u har yana da ƙarfin zuciyar iya sake tunkarar Mammah?". "Ai baida kunya Yaya Ma'aruff gashi kuwa yayi ka gani. Wlhy ina matuƙar jin kewar Dada. Ya ALLAH ka saka mana ka tarwatsa farin cikin duk wani azzalumi dake da hannu a kama mana shi. Wlhy wani cin kashin ma da yana nan da bazasu kwatanta mana shi ba. Dan na tabbatar duk tsawon shekarun can saboda shakkarsa yasa ko ƴan Bauchi kasa sake tunkarar inda muke. An kama shi dan kar su zo mu nema taimakon sun suka sake ja baya damu. Yanzu kuwa tunda sunga ALLAH ya rufa mana asiri zasu fara kawo kansu..." "Ai ko zasu fuskanci wulaƙanci da tozarci a garemu. Dan mu mun jima da sallama dangi a duniyar mu. Mune dangin kammu mahaifiyarmu da Dada sun ishemu uwa uba a duniya. Azzalumai kawai masu matacciyar zuciyar watsar da marayu". Ammar ne ke maganar yana kuka. Rungumeshi Ja'afar yayi yana shafa bayansa. Haka ma Aunty Momy hawaye take ta sharcewa ita da aunty Ummi. Kasancewar a sashen Yaya Ja'afar suke zaune sai suka ƙi komawa sashen Mammah har sai da yara suka dawo school. Basa son su fahimci komai dan haka suka dawo sashen Mammah ɗin. Inda suka sameta zagaye da yaran cike da farin ciki kowa ji yake kamar ya koma cikinta. Ita ko bakinta ya kasa rufuwa. Abinci ma ita ta dinga basu abaki tun daga kan Nimrah, Ruƙayya, Abees, Aheel, Afrah da Ayyan ƙarami. A haka shima Mu'azz da Imam suka shigo gidan suka samesu. Suma daɗi ya kamasu da ganin Mammah ta dawo. Ai tuni suma sunyi zaman dirshan suna amsar abincin. Wannan farin cikin ya saka su Aunty Ummi mantawa da damuwarsu. Dan Mammah na kammala bama yaran abinci suka dawo wajen Uncle Ammar shima kowa na tambayar tsarabarsa. Musamman Nimrah da Ruky da suka bada sakwanni na musamman......
<•><•><•><•><•>
Kusan lokaci ɗaya Uncle Nasiru da Daddy Imran suka shigo gidan. Dan dukansu daga wajen aiki suke. Sabon Driver dake zaune tare da maigadi ya bisu da kallo su duka. Dan yau kwanakinsa shida a gidan bai taɓa ganin Uncle Nasirun na, sai Imran sau 1 shima. To Daddy Imran ɗin kuma yayi ƴar tafiya bayan wucewar Mammah da yazo sau ɗayan daya gansa, kwanansa huɗu ya dawo. A randa ya dawo yazo gidan lokacin shi kuma yaje ɗakko yara daga Islamiyya. Motarsa na fita shi kuma ya dawo da su. Tun ranar kuma bai sake zuwan ba sai yau. Uncle Nasiru kuwa dama tunda Mammah tai tafiya bai leƙo gidan ba saboda ayyuka sun masa yawa, ya kuma san yaran duk ba zama suke ba sai matan su Ja'afar kawai. Suna tsaka da gaisawa Maigadi ya gama rufe gate ya nufesu, dole shima driver ya bishi suka iso inda suke. Rissinawa sukai suna gaishesu duk da kusan sa'an Imran yake shi sabon driver, koma ya iya girmarsa kaɗan duk da shi Imran akwai jin daɗin rayuwa da kulawa da lafiyar jiki irin ta soja a tattare da shi. Uncle Nasiru yana tsokanar su. Shi ko Imran sai ya ɗan zuba ma sabon driver idanu. Har sai da Uncle Nasiru ya ce, "Imrana yaya dai? Ko ka san shi ne?". Cikin ɗan murmushi Imran ya girgiza kai da faɗin, "A'a Uncle. Kawai na tafi wani tunanin ne daban". Bai jira amsawar Uncle Nasiru ba ya juya ga drivern ya amsa masa gaisuwarsa. Daga haka suka bar wajen driver na binsu da ido. A zuciyarsa kam dake bugawa ayyanawa yake (lallai akwai matsala. Shegen nan ko bai gane ni ba ya tsargu da ni. Lallai dole na canja takuna kenan. Dan banzo nan dan na tafi batare da na kammala abinda ya kawoni ba) a zahiri kam miƙewa yay ya koma gate ya zauna a kujera. Sai kuma ya zaro wayarsa ƙaramar nokia ya shiga danne-danne kafin ya kai kunnensa.........✍️ [12/10/2025, 11:34 PM] Zeenaran 😘: 25
..........★A falo kam daga Imran har Uncle Nasiru sunji matuƙar daɗin ganin yanda jikin Mammah ya ƙara ƙyau. Da alama ta samu maganin da yafi wanda take samu anan gida. Dan wannan ne karon farko da suka fita Egypt ɗin dama. Kasancewar su Nimrah duk sun wuce islamiyya da ƙyar gidan shiru, dan ca sukai bazasu ba yau suna murnar dawowar Mammah. Sai da Yaya Ma'aruff ya fatattakesu sannan kowa ya wuce baki a sama. Sai Biebah kawai itama bata jima da dawowa daga school ba. Mu'azz yabi Imam gida. Mammah ta kalla Biebah dake laƙai-laƙai ɗin cin abinci saboda bata jin daɗi yau da ciwon kai ta dawo makaranta ganin Mammah ɗin ne ma ya ɗan watsakkar da ita. Sai dai ganin baƙon dake gidan ya tsaya mata a zuciya kamar sauran ƴan uwanta. Dan yanzu haka ma Aunty Momy da Aunty Ummi da Ammar na ɗakinta suna sake tattaunawa. "Biebah tashi kira Uncle ɗin ku". Idanu Biebah ta ɗago tana kallon Mammah, sai kuma ta amsa da to cikin sanyi tana tashi. "Kina lafiya kuwa Biebah?". Cewar Imran. Idanunta na cika da ƙwalla ta ce, "Yaya kaina ke ciwo". "Ayya Auta stress ne sannu. Jeki dawo kizo kisha magani kije ki ɗan kwanta kafin akkunayen gidan su dawo su hanaki". Kai ta jinjina masa. Shima Uncle Nasiru yay mata sannu. Nan ma amsawa tai ta wuce aikar Mammah...