Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 9

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 9

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 9: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 9. Cikin zafin rai take magana kuma da harshen turanci. Shi ko yayi sabale yana…

3,838 words

<%>°<%>°<%> PRISON

Wani zuba masa kaifafan idanunsa yay a hankali, tare da sakin wani murmushi mai zafi da izza, mai tabbatar da cikakken izgili da raini fiye da nashi. Dan a ƙarshe da wani salo irin na maida mutum banza sakarai Dada ya taɓe baki. Sannan cikin son tunzurawa ya ɗan karkatar da kansa, fuskar sa ta cika da izza mai nutsuwa. Like yana magana da wani shasha can ya furta, "Tofa! kaga fa kana ƙoƙarin bani mamaki." Ya yi murmushi mai ɗan kaifi, ba na farin ciki ba, na jarumin da ya saba da iya riƙe nauyin abu a zuciya da ƙwaƙwalwa batare daya bari abokin gaba ya fahimci lagonsa ba. Cikin halin ko in kula ya cigaba da da ɗin, "Ka zo nan kana min barazana da dorinar ƙarya, ka ce ku ne ƙasa, ku ne haske, ku ne gwamnati. Amma duk da wannan ƙarfin ikon naku kuma kuka zaɓi ɓoye fuska kamar masu tsoron haske a gaban ZAKIN dake ɓoye cikin keji?. Gaskiya ban yarda da wannan ƙarfin ikon naku mai kama dana ƴan wasan kwaikwayo ba, ya kamata ku koma ku canja shiri." Ya ɗan sake matsawa gaban tebirin sosai yana sassauta murya kamar mai son yin raɗa idanunsa na sake shiga cikin na baƙon, sai dai muryar tasa ta cika da nauyin, da ƙarfi irin na masu izzar ƙarfin zuciya da jarumtar ƙwarai dake jinsu ko a ɗaure su ba masu risinawa wawaye bane. "Ɗan aike!. Ka manta da abu ɗaya." Shiru ya mamaye ɗakin. Baƙon ya tsaya tamkar an dasa shi a wajen yana kallon Zak-Shadow da jin ƙaguwar son barin wajen dan wani irin firgitashi al'amarinsa keyi, dauriya kawai yake da dannewa saboda sanin akwai camara a jikinsa dake ɗaukar komai. Kai tsaye kuma duk abinda suke tattaunawa ƴan ƙungiya ma na kallonsu........✍️ [12/10/2025, 11:29 PM] Zeenaran 😘: 21

........Tunaninsa ya katse sakamakon cigaban kalaman Zak-Shadow masu zafi da sanya zuciya raɗaɗi. "Idan kaje ka sanar da iyayen gidanka saƙo daga ni Haysam Abdul-rasheed Shehu. Ku na mallakar gwamnati, amma ba kwa mallakar ƘASA. Ku na mallakar masu muƙami, amma ba kwa mallakar mutanen da suke amsa sunan KASAR. Ka sanar musu. Idan suna tunanin zasu sarrafa ni kamar karnukan su… to su sake tunani tun kafin lokaci ya ƙure musu. Ka faɗa musu. Wannan ba ƙarshen wasan ba bane, farkon rugujewar su ne, domin kuwa yanzu ne za'a FARA WASA na GASKIYA. Ka faɗa musu. Wanda yake da cikakken iko ba ya zuwa ya gaya wa wanda yake tsoro barazana. Domin wannan zuwan naku tabbatar min yay da kun MATSORATA ne, kuma ni abin tsoronku ne. Na ji ƙamshin wannan tsoron naku tun shigowarka nan. Ka faɗa musu. Idan kun kasance da ikon da kuke ikirari… ku kasheni kawai zai fi muku sauƙi da samun cikar burin ku cikin salama" ya ɗan yi dariyar da ta sake tsokano zuciyar bako. Batare da bashi damar cewa komai ba ya cigaba da faɗin, "Ka faɗa musu. In har kukai sakacin ƙin kasheni da ɗaukar zantukana cika baki, to ku shirya… ku shirya wasan da muka fara ba lissafin saƙar zaren ginin gidan GIZO-GIZO ba. Ka faɗa musu. Shi wannan filin da suke cika bakin samarwa domin ƙwallon ƙafa, da jinin da zasu jiƙa ƙasar domin ta tausasa. Ni ne zan samar da filin WASAN, sannan na jiƙa ƙasar da jinin jikinku. A maimakon buga wasan ƙwallo na ɗaura muku sarƙar mata a ƙafafuwa ku zagaye filin da takun RAWAR ƘOROSO. Ka faɗa musu. Ni nake tsara gangar da masu kiɗanta, kuma tabbas in sha ALLAHU sune zasu taka wannan rawar fa. Ka tafi ka faɗa musu. Na gane kun TSORATA. Sannan wannan SAƘON daka kawo zai zama kuskurenku na farko. Na biyun zai biyo bayan fitowata daga nan. Ka faɗa musu. Idan har iyayensu sun haifesu da alfaharin igiyar aure, kamar yanda ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi A'isha da Abdul-rasheed suka haifeni da wannan alfaharin ku rubuta kalamaina ku ajiye da yaƙini a saman dutse. Sannan ku shirya." Ya turo kujerar ya tashi a hankali yana sakin murmurshin ƙasaita tamkar sarki ya miƙe daga gadon mulkinsa. Ya zubama agogon hannunsa idanu na sakanni tare da sake sakin murmushi mai ma'anoni da yawa sannan ya fara takun dake nuna alamar barin wajen. Da sauri shima baƙon ya kalla agogon nashi mai ɗauke da camara saboda kallon da Zak-Shadow yay ma agogon ya tabbatar ɗayan biyu ne, ko dai ya fahimci camara ɗin ce ko ya tsargu.... Dada da yay takun da bai gaza biyar ba ya tsaya cak, tare da juyowa a hankali, idanunsa suka sauka a kan mutumin. Fuska ta bogi, amma mugunta ta gaskiya.... Murmushi ya sake saki da ɗan taɓe baki. Cikin salon isar da saƙon ƙarshe a inda yake da tabbacin masu aiken na kallonsa yanda ya dace domin idanunsa kam a kan agogon mutumin ya furta, "Ni bana kare gwamnati. Bana kare hukumar soji. Bana kare kujerun ƴan mulkin mallaka. Amma ku sani. Na kare ƙasa. Na kare mutanen ƙasa. Na kare gaskiya duk da ƙarfin ikon UBANGIJI mai IZZA da cikar mulki na gaskiya. Wannan kuma… Shine abinda kuke tsoro. Zan ƙara tabbar muku, idan har kuka bar Haysam Abdul-rasheed Shehu a raye, zai cigaba da tabbatar muku wannan tsoron a cikin ZUKATA. Bance zan iya komai ba, amma bazan taɓa raina kaina a gaban ALADU irin ku ba". Ya ɗan yi shiru yana murmurshi mai ciwo, dan kowace kalma yana fitar da ita ne daga zuciyarsa kamar takobi mai kaifin gayawa jini ya wuce. Baƙo da zuciyarsa ke dukan uku-uku cike da ƙarfin hali ya ɗan taɓe baki, numfashinsa dake fita da rawa ya fisgo da ƙyar dan neman ƙwace masa yake. A karo na farko ya ji wani abu ya motsa masa a ƙirji, ba tsoro bane kawai, ba kuma bakin ciki bane kawai. Bayyanan nen rauni ne dake tuna masa, shima fa ɗan ƙasa ne tamkar Zak-Shadow, yana da dangi a ciki ba iyalai kawai ba, yana da ƙarfin ikon kiranta tushe ba son tara dukiya da ƙarfin ikon son mulki kawai ba.... Dada daya gama fahimtar raunin nasa dake son bayyana ya juya zai fita abinsa yana murmurshi, sai kuma ya sake tsayawa tare da juyowa a lokaci guda. Da tabbatar wa ya ce, "Ya kamata na sake jaddada muku domin fita hakki. Kar ku barni a nan domin in gani daga shirin shirin ku. Idan kukai wannan sakacin zan zauna in rubuta yadda zan rushe ku daga cikin ɗakin nan da wawancin ku ke sakaku kallonsa keji". Ya kammala da murya mai sanyi, amma mai ɗauke da tabbataccen iƙirari. "Kuna da duhu. Ni kuma ina da hasken da yake huda duhun nan naku. Saƙo na ƙarshe, duk wanda ya sake zuwa inda nake da saƙon ku, zan bashi amsar da zai maido muku. Sai dai GAWARSA ce zata dawo da amsar da gangar jikinsa ba BABU RUHI...." Ya saki murmushi tare da salute da yatsa ɗaya kacal sannan ya juya abinsa cikin takun nan nasa da wanda basu fahimcesa ba ke kallon na izgili da izza. Ƙofar ya buɗe ya fita ba tare da ko waiwaye ba yabar baƙo da rawar zuciya da jiƙewar gumi, ga shi ya gagara koda motsi a wajen tamkar wanda gangar jikinsa ta mutu ta barshi da fitar numfashi kawai........

<%><%><%><%>

Cike da nutsuwa take haɗa masa abincin karin a gabansa, duk da kuwa tana daga tsaye ne shi a zaune kan ɗaya daga kujerun daning ɗin. Ya zuba mata idanunsa na girma fuskarsa da murmurshi. Sai da ta kammala zata matsa ya riƙo hannunta. Kallonsa tayi itama a karo na farko, sai dai fuskarta ita sam babu walwala alamar akwai abinda ke damunta ko ranta a ɓace yake. "Juwairiyya mike damunki ne wai?". Yanda yay maganar cikin taushin murya yana sake tsatstsareta da idanu ya sata sunkiyar da kanta. Sai dai batace komai ba. Numfashi ya ja ya fesar tare da sake matsa hannunta cikin nashi, ya buɗe baki zai magana kenan takun fitowar wani daga cikin yaran ya sashi yin shiru yana sakar mata hannun. Itama matsawa tai kaɗan dan mai fitowar har ya bayyana. Ba kowa bane face Abdul-rasheed da suke kira Imam saboda sunan aboki, amini kuma mahaifi gasu Dada da yaci. Imam shine babban ɗanta a gidan, sa'anni suke shi da Mu'azz koma muce ya girmesa da kusan 2years. Yarone nutsatstse yana tsananin kama da Uncle Nasiru, akwai mai bi masa Halimatus'sa'adiyya. Sai Bintu sa'ar su Nimrah, itama dai ƙawarsu ce dan ƙiriniyarsu ɗaya da ita, idan suka haɗu sam basa jin bari musamman idan an samu hutun makaranta sukan haɗu anan ko gidan Mammah ko gidan Daddy Imran. Adam da Sadiq sune ƙananu a gidan, dan Hajiya Zuwairah ta haifesu ne ma kusa-da-kusa sakamakon gwanne data samu, ta haifi Adam da wata uku ta sake samun cikin Sadiq, hakan yasa tsiransu nasu ba yawa.

"Abba ina kwana? Ummu Ina kwana?". Imam ya faɗa yana mai kaiwa duƙe. Hannu Uncle Nasiru ya miƙa masa alamar suyi musabaha yana murmurshi, yayinda Hajiya Zuwairah ta amsa masa da kulawa. Fuskar Imam da murmurshi ya bama Abban hannu kamar yanda yake masa kullum. Dai-dai lokacin Sadiyya da Bintu ke fitowa suma dan ɗakinsu ɗaya. Abba ya ce, "Abdul-Rasheed kaifa abokina ne ba suruki ba". Murmurshi Imam yayi kamar yanda ya saba a duk sanda Abban nasu ya faɗi haka. Hakama Hajiya Zuwairah na tayashi. Imam na kaiwa zaune a kujera shima su Bintu suka ƙaraso dining ɗin, cikin girmamawa suka gaida Abban sannan Ummu da Yaya Imam. Duk sun amsa musu da kulawa, Ummu ta kalli Sadiyya tana faɗin, "Halimatu taso min su Adam suzo suyi kari, dan yanzu haka ma basu tashi ba balle batun tafiya Tahafiz, ni narasa miyasa kukafi ɗaukar tafiya boko da muhimmanci a rayuwarku fiye da islamiyya". Sadiyya data zama budurwa sosai tai ƴar dariya da faɗin, "Ummu itama islamiyya muna so ALLAH, baga Yaya Imam nan ba har jami'a fannin Islamic ya zaɓa". "To ai shi dama yana son karatun addini ba irinku ba. Dan magajin mai sunan nashi ne da Haysam." Hajiya Zuwairah ta bata amsa. Murmurshi Uncle Nasiru yayi, zuciyarsa na tuno masa amininsa kuma ɗan uwa Abdul-rasheed, tare da jin raunin zuciya na gagara taka kowacce irin rawa akan al'amarin babban ɗa na ƙwarai irin Haysam. Wannan raunin nada matuƙar tasiri a zuciyarsa, dan a shekarun nan da Dada ke a rufe kusan shine ya sake assasa ciwon Uncle Nasiru ɗin matuƙa fiye da shekarun baya... Bintu ce ta katse tunaninsa da faɗin, "Abba dan ALLAH ya maganar maidani makarantar su Nimrah ɗin? ALLAH ina son na koma can zanfi yin ƙoƙari da himma, dan ALLAH kuma har islamiyyarsu nake so". "Zaki ƙara ƙoƙari da himma ko zaki ƙara shiririta da rashin ji. Kune zaku haɗu a waje guda kowa bai shiga tamanin ba. A yanzu ma ita da Ruƙayya ya aka ƙare dasu balle kin ƙaru. Abba kada ka wani maidata can idan bazata zauna a inda take ba ta barshi. Dan suna haɗuwa su ukun nan kowa yaga boni". Tamkar Bintu zatai kuka ta ce, "Kai Yaya Imam, maimakon ka tayani sai ka zuga Abban kuma. ALLAH bazamuyi ba. Ai ko su basa wasa da karatu kaima ka sani fa. Ummu dan ALLAH ki saka baki". Sai hawaye sharr. Dariya suka sanya mata. Uncle Nasiru ya shafa kanta da faɗin, "Haba Mamana harda kuka. Nima fa ba naƙi bane, ina duba ta Imam ne kawai. Dan nasan kuka haɗu a school ɗaya ke da Nimrah da Ruƙayya sai dai ta ALLAH kawai, wai Gwari ta sai maye. Yanzu ma yaya aka ƙare da su su biyun, kwanaki fa a lokaci guda aka basu suspension boko da islamiyya. Ɗiyar ɗan majalisa guda suka fasama kai tsabar rashin tsoro da ƙiriniya, to idan kuka haɗi ai nasan wataran ƴar shugaban ƙasa zaku bazar a ƙasa ko minista". Dariya Imam da Ummu keyi, Sadiyya dake isowa wajen su Sadiq biye da ita ta ce,........✍️

[12/10/2025, 11:31 PM] Zeenaran 😘: 22

........."Wlhy Abba zasu aika kada ka amince da daɗin bakinta. Idan ba haka ba nima sai dai a maida ni makarantar su Asma'u ai ƙawaye basu ƙawaye ba". Caraf Adam yace, "Muma haka Abba". Dariya kowa ya sanya. Abba ya shafa kan Adam da Sadiq. "Kenan dai na gane a gidan nan kowa yana jealous da Mamana kawai". "A da alama kam". Cewar Ummu tana murmushi. Itako Bintu tayi kicin-kicin da fuska alamar jin haushi. Sai da Ummu ta lallasheta sannan ta yarda ta zuba abinci. Daga haka suka nutsu suka fara karyawa babu mai magana. Sai da suka kammala kowa ya miƙe dan zuwa yay shirin Tahafiz har Imam. A lokacin ne Uncle Nasiru ya sake kallon Hajiya Zuwairah dake gyara gurin duk da su Bintu duk sun kwashe kwanikan sun kai kitchen. "Zamu iya magana yanzu?". Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta tura baki kama ƴar yarinya. Dariya yayi yana haɗe hannayensa da faɗin, "To ni dai duk ma laifin da nayi ayi haƙuri ai min afuwa. Amma dan ALLAH a sanar min damuwa kada zuciyata ta sake kumbura." Kanta ta sunkuyar kawai batare da tayi murmushi data saba yi ba a duk sanda yay irin wannan maganar, sai kuma ta ɗan sauke numfashi cike da nutsuwa ta ce, "Abban Jiddah akan maganar jiya da kaƙi sauraren Jiddah akai ne. Bayan kuma ni da kai duk munji abinda Ismat ta faɗa fa. Yanzu dan ALLAH sai ka bari ɓacin rai ya rinjayeka barin yaran nan a cikin tarkon musiba? Kana jin fa abinda ke faruwa; a tunaninka watarana mahaifiyarsu bazata ci galaba akansu ba musamman ma Nabeeha dake ɗauke da igiyoyin aure a kanta! Nasan Nabeeha mai laifi ce a gareka, dan babu izninka babu na mijinta ta koma wata ƙasa da zama bayan ana cikin damuwa da halin da mijinta ke ciki, amma abinda zamu kalla ko tana da laifi wani kaso ne a ciki Hajiya Hasiba nada wani, saboda tana da tasiri ƙwarai da gaske akan al'amarin yarannan idan ka cire Jiddah da ALLAH yay saurin fargarwa..." Cikin ɗacin murya da sauyawar idanun da ɓacewar murmushin kan fuskarsa ya ce, "Ya kike so nayi Juwairiyya? Shin basu ne suka zaɓi irin rayuwar ba shiyyasa suke ciki? Ai su duka ba yara bane har Ismat ɗin da ake ganin batai aure ba, amma suke biyewa gafalar uwarsu da son duniya ta rufema idanu ko". "Hakane, amma abinda zamu duba har yanzu su yara ne akanmu. Sannan mata ne. Mufa mata a kowace sigar rayuwa a karkacen nan muke tamkar haƙarƙari. Shekaru basa saka mu canja ko ilimi. Sai wanda UBANGIJI yaso ya gane kawai daga cikinmu. Mu godema ALLAH da yarannan basu tasirantu da huɗubarta ba ma har suka fahimta illar al'amarin. Dan wlhy UBANGIJI ne kawai ke riƙe da igiyoyin auren Nabeeha saboda Haysam mutumin kirki ne, in sha ALLAHU ALLAH bazai haɗa masa zafi biyu a lokaci guda ba. Dan ALLAH kayi wani abu kodan Haysam, saboda koba komai da saka hannunka ya auri Nabeeha, sannan yana sonta". "Hummm Juwairiyya...." "Dan ALLAH karka ce A'a Abban Jiddah". Tai maganar cikin katse masa hanzari. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kawai. Tare da faɗin, "Shike nan zan duba. Amma ki sani Adeel yaro ne mai dauɗar duniya a hannu, sannan ya fito daga babbar zuri'ar da yake da ƙarfin aji ako ina a duniya musamman ma ƙasashenmu na Afirika. Barowarsu ƙasar nan zai zama babban al'amari. Amma zan gwada wata hanya idan za'a dace." "ALLAH yasa a dace, dan duk ƙarfinsa bai kai na UBANGIJI ba ai. Darajar auren dake kan Nabeeha ALLAH zai hanashi dukkan nasara. Itama ALLAH ya shiryar da ita ta gane halakar da take neman jefa yarannan da kanta." "HUmmm". Kawai Uncle Nasiru yace, itama sai ta saki zancen ta ɗakko na batun zuwa sake duba Aunty Mimi mai haihuwa duk da kuwa randa ta haihu taje. Amma a matsayinta na kamar uwa koda Mammah na nan dama ita ya kamata ta yi abinda uwa zatayin, saboda ita da Mammah suna jin kansu kamar ya da ƙanwa uwa ɗaya uba ɗaya. Kamar yanda Uncle Nasiru ke ɗaukar Mammah ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗayan. Bai hanata ba, shima ya miƙe yana faɗin zai shirya dan yau yana da ganawa da sanata Yusuf Shu'aibu Tafida tsohon janar. Addu'a tai masa dan tasan dai ganawarsa da Janar ɗin baya wuce akan batun fitar Haysam da suke ta fafutuka da kai-kawo tsahon shekaru.....

===============

Chapter notes and social links

Cikin zafin rai take magana kuma da harshen turanci. Shi ko yayi sabale yana kallonta dan komai tayi birgeshi take. Shi kaɗai yasan irin wutar masifar sha'awarta da yake ji tsahon shekaru. Ya kuma kasa binta ta ƙarfi batare da yasan dalili ba. Bayan kuma hakan abu ne mai sauƙi a garesa duk da kuwa yasan tana da aure. Yasan inda wata ce ba ita ba yanda yake narkama uwarta kuɗi duk da hakan ba komai bane a garesa da tuni ya mata fata-fata ta yanda ko rayuwarta sai ya ce ga yanda zatayi sannan zata gudanar da ita. Yanzu haka yana ƙasar Garmany ne harka business ɗinsa Hajiya Hasiba ta tura masa saƙon kudirin Nabeeha, yana gani hankalinsa ya tashi, a take ya kira duk wani Companyn sauka da tashin jirage yasa aka rufe damar Nabeeha na barin ƙasar. Amma duk da haka hankalinsa yaƙi kwanciya a daren ya baro ya dawo dubai ɗin. Kai tsaye gidan nasu yayo, cikin sa'a kuma ya sami Nabeeha a falo zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka. Zama yay kusa da ita da kai hannu zai taɓata ta zabura, shine take zazzaga masa ruwan masifa data sakashi zuba mata ido kawai yana kallonta... Su Ismat dake laɓe farin ciki ya kamata, dan itama wlhy ta tsani guy ɗin nan, dan bata da wani burin daya wuce Nabeeha ta koma ɗakin aurenta. Ta haka ne kawai itama zata samu cikar nata burin na mallakar Ja'afar. Cike da munafunci Amima ta dannama Hajiya Hasiba kira da mahaifiyarsu data shigo gari tun cikin satin daya gabata. Aiko cikin mintinan ƙalilan suka iso dan duk suna kusa da gida ne dama. Wata tsawa Hajiya Hasiba ta dakama Nabeeha. Cikin zafin rai ta ɗaga hannu zata mareta caraf Adeel ya riƙe hannun. Cike da gadara ya ce, "Karma ki fara dan ina ganin mutuncinki na haihuwarta da kikayi, amma da a maimakon riƙe hannun nan naki sai dai ki jisa a ƙasa yana lilo". Maimakon jin zafin abinda yay mata murmushi Hajiya Hasiba tayi daga ita har ƙanwarta Mamawo. Cike da girmamawa suka shiga faɗin, "ALLAH ya huci zuciyar babba ɗan manya jinin alkairi. Nayi kuskure ayi haƙuri raina ne ya ɓaci. Taya zata zauna tana gaya maka irin wannan shirmen.." "Karki damu ta isa ne ai, girmanta ne. Ni zan koma kawai, amma zan dawo anjima anan zanyi dinner". "An gama ranka ya daɗe". Hajiya Hasiba ta faɗa cike da girmamawa. Yayinda Mamawo ke wani shegen murmushi tana binsa da wani kallo zuciyarta cike da abubuwa. Amma a zahiri baka isa karantar abinda ke ranta ba dan cikakkiyar ƴar bariki ce data iya takunta. Yana ficewa suka koma yima Nabeeha faɗa da nuna mata karfa ta dawo tana dana sani da wannan damar da ALLAH ya bata. Wai miye akai akayi wani Haysam can da bata da tabbacin yana ma raye ko an jima da kashe shi ne. Kuka ta saka musu cike da bori da rashin kunya tabar wajen. Dole sukai shiru bayan duk sun ja tsaki. Bayanta itama Ismat tabi zuciyarta na zafi. Koda ta shiga ɗakin taga Nabeeha ta kwanta tana kuka zaman lallashinta tayi, ganin taƙi yin shiru ta ɗauka wayarta a karo na farko ta danna kiran Jiddah, abinda sai ta jima batayi ba saboda duk haushinta suke ji akan gaskiya da take gaya musu. Batai zaton zata ɗaga mata ba ma, amma sai gashi ta ɗaga cikin tsaftatacciyar sallama. Da ɗan rawar murya Ismat ta amsa mata, sai kuma ta fara gaisheta. Ɗan jimmm Jiddah tayi kafin ta amsa tana kallon Abban su dan taje barka gidan Aunty Mimi ne shine ta biyo gidan gaishe su. Kukan da Ismat ɗin ta fashe da shi ne ya saka Jiddah faɗin, "Ismat lafiya kuwa? Ko wani ne ya rasu?". "Aunty babu wanda ya rasu, kawai abubuwa ne suka mana yawa. Mom ta takura dole sai Aunty Nabeeha ta kashe aurenta ta auri wannan mayen mutumin. Jiya mukai shirin gudowa kawai ta sace passport ɗinmu ta ɓoye. Yau kuma sai gashi yazo. Aunty ki taimakemu ki sanar da Abba yazo ya tafi damu. Wlhy gida muke son dawowa, aunty Nabeeha na son komawa gidan mijinta". Jiddah dake jin jikinta ma na rawa ta ɗan saci kallon Abbansu. Ai ko yayi kicin-kicin da fuska yama maida hankalinsa a television inda ake hira da ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyar SGP, wato tsohon janar ɗin soja kuma ɗan majalisan tarayya mai ci Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. Yawu masu kauri ta haɗe, cikin damuwa ta maida kallonta ga Hajiya Zuwaira da suke kira Ummu a gidan. Idan ka cire Nabeeha da Ismat da har yanzu basa ko gaisheta. Kai Ummu ɗin ta girgiza mata alamar ta kwantar da hankalinta, dan taji komai itama kasancewar hansfree ta saka wayar. Cikin dauriya Jiddah ta ce, "Wannan shi nake nuna muku tun farko amma kuka kasa ganewa Ismat daga ke har Aunty Nabeeha. Yanzu dan ALLAH yaushe rabonku da kiran wani a cikinmu har Abban, aƙalla shekara uku kenan fa. Ni kuma kun saka ni a black list kona nemeku bata shiga harta WhatsApp. Ni yanzu a wannan gaɓar mizan iya yi, wane tabbaci ne dani akan baku biye ma Momy ɗin ba akan ƙudirinta....." "Wlhy aunty bamu taɓa aikata wani abu saɓanin abinda kike tunani ba mu kammu balle Aunty Nabeeha". Duk da Jiddah bata da tabbaci sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, duk da tasan wacece mahaifiyarsu akan son duniya babu abinda bazata aikata ba. Itafa ko uwarmi zasuyi suyi ba ruwanta tunma suna ƙananunsu indai kuɗi zai shigo fine. Hawayen da suka cika mata ido ta haɗiye, ta ce. "Shike nan Ismat ki bani zuwa gobe, yanzu haka ma bana gida naje barkar Aunty Mimi ne data haihu. Amma zan yi magana da Abban". "To aunty dan ALLAH ki taimaka mana, ke kaɗai ce hope ɗinmu a yanzu wlhy". "Karki damu in sha ALLAH duk yanda muke zan taɓoki, ni dai fatana ku cigaba da riƙe mutuncinku kada ku biyema Mom". "In sha ALLAHU Aunty ki mana addu'a". "Ita nake muku kullum". Daga haka ta sauke wayar. Tun kafin ma tai magana Uncle Nasiru ya dakatar da ita da faɗin, "Tashi ki wuce gida dare yayi? ALLAH ya bamu alheri". Yanzu kam sosai idonta ya tara hawayen, ta waiwaya tana kallon Ummu. Kai ta jinjina mata alamar taje, tabar komai a hannunta kawai. Sai kawai ta miƙe tai musu sallama ta fita. Dama ita ta tuƙo kanta. Aiko tana shiga motar ta kife kanta a sitiyari kawai ya fashe da kuka. Ta jima tana kuka har sai da maigadi yazo yana mata knocking glass sannan ta haƙura ta share hawayenta taima motar key......

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull