Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 8
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 8: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 8. "Alhamdulillah Sir! Yanzu kam komai ya kammala kenan, sai jiran umarnin fara…
4,451 words
"Alhamdulillah Sir! Yanzu kam komai ya kammala kenan, sai jiran umarnin fara campaign". "Haka ne Imran, amma ni duk ma jikina yayi sanyi. Badan al'amarin Haysam ba banga abinda zai kai ni shiga siyasa ba. Dan siyasar ƙasar nan sirrikan cikinta basu da daɗin tonawa. ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara kare mana imaninmu". "Amin ya rabbi Sir. Amma abubuwan dama ko ba'ace komai ba duk mai hankali yasan akwai ɗunbin kwamacala a ciki kam. ALLAH dai ya kare mana ku, ya azurtamu da shugabanni na gari." "Iyakarta kenan kam. Mu dai ku cigaba da mana addu'a, ku dinga saka yara na mana." "In sha ALLAHU Sir za'a ƙara dagewa, dama anayi a koda yaushe. Sir nace yanzu bazaka sake sama mana damar ganawa da Haysam ba. Wlhy ina cikin matsanancin matsin zuciya na kewarsa matuƙa. Shekara biyar ba kwana biyar ba". Sosai tausayin Imran ya sake cika zuciyar Janar, dan har idanun Imran ɗin sun cika da ruwan hawaye. Cikin kwantar da murya ya ce, "Kayi haƙuri Imran, na san kai da zuri'ar Haysam da iyalinsa dole ne ku kasance cikin bege da kewarsa. Kuma hatta muma muna cikin wannan yanayin. Amma ina sha ALLAHU aski ne yazo gaban goshi, kasan kuma masu iya magana sunce daman yafi zafi. Dole ne mu cigaba da daurema zukatanmu, dan wannan gaɓar da muke da babban shiri a kansa tafi kowace gaɓa nauyi da haɗari, idan mutanen nan suka fahimci muna da wani shiri wlhy zasu iya kashe Haysam ta guba da hanyoyi masu sauƙi dan a yanzu sun fimu kusanci da shi. Mu cigaba da masa addu'a kamar yanda muka saba, tunda muna samu labari mai daɗi akan kasancewar sa cikin koshin lafiya daga yaron nan Captain Ibrahim, na yarda da yaron bazai kawo mana zancen daba haka yake ba, muma shaida ne tunda ya kawo mana wasiƙa da muka tabbatar daga Haysam take. In sha ALLAH ko ban samu mulkin nan ba a wannan karon zan ƙara ƙaimi Imran". "Maganarka haka take Sir, kayi haƙuri nima kewa ce da damuwa harta sani faɗar hakan. ALLAH ya saka maka da alkairi ya bada ladan zuminci." "Karka damu Imran, wlhy har cikin zuciyata nake jinku kai da Haysam da Haydar, dan naji matuƙar daɗin aiki da ku fiye da yanda kuke tunani. Shiyyasa nake jinku tamkar ƙannena da muka fito uwa ɗaya uba ɗaya. Zan iya bada rayuwata akan ganin Haysam ya fita, dan ya yimin abubuwa da bazasu ƙirgu ba. Sau biyu Haysam na tarar harsashi a wajen bani garkuwa, kuma duka biyun a jikinsa suka ƙare har yay jiyya. Taya zan manta da irin wannan ƙanin a duniyata in dai ina numfashi." Hawaye Imran ya share yana ɗan murmurshi, ya ce, "Ka cancanci fiye da haka a wajenmu Sir. ALLAH dai ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, ya kuma cika burin alkairi". Sun cigaba da hira da duk ta shafi batun Dada da siyasa. Kafin Imran yay masa sallama ya fito. Da yake cikin ɓadda kama yake maimakon gida sai ya ɗauki hanyar kasuwa, dan jiya Mimi ke sanar masa haihuwar ta, yanzu haka ma ya bari Aunty Hafsat zata je can barka. Wani shago ya fara shiga, sai da ya tabbatar babu mai bin bayansa daga gidan Janar sannan ya fito ya nufi babban shagon su Ma'aruff da yafi kowane shago girma da cikar kaya a kasuwar. Dan kuwa ƙaton waje ne da zaka iya samu abubuwa da yawa da duk ya shafi kwalliyar jiki. Ɓangare-ɓangare ne, akwai atamfofi, abayas, lesuka, shadda, materials, kayan yara tun daga kan jarirai har zuwa samari. English wears na mata dana maza, mayafai. Kai duk wani abinda ya shafi sutura ta maza da mata, yara da manya akwai ta. Sai bangaren kayan kwalliya, akwatina, cosmetics komai har zinari suna sayarwa. Kai shagon nan dai sai Alhmdllh, dan ko yara masu aiki sunfi ashirin a ciki. Suko manyan gwasake na office abinsu. Ga camaras tako ina da suke kallon shiga da fitar kowa daga ofisoshin nasu... A tare ma ya taddasu a office ɗin Ja'afar, dan sakatariyansu batama yi yunƙurin fara zuwa neman masa izinin shiga ba sanin wanene shi a wajensu. Sai ma gaisheshi data shiga yi cike da girmamawa. Ya amsa mata a taƙaice yana wucewarsa yay knocking direct, sannan yay sallama ya shiga. Cike da farin cikin ganinsa da girmamawa suke masa barka da zuwa. Ma'aruff ya ajiye kofin tea ɗin hannunsa da yake sha yana miƙewa ya gyara masa kujera, dan basuyi breakfast a gida ba saboda sun makara aka haɗa musu suka taho da shi. "Cin abinci a office sai kace tuzurai?". Imran ya faɗa cike da tsokana. Dariya sukayi a tare. Ja'afar ya ce, "Yaya makara mukayi wlhy, kasan kuma twiny da wutar ciki ya azalzalan dole muka taho da shi. A haɗo shayi ko coffee ko kunu?". "Haba sai kace wani ku, sai da Auntynku ta cika min ciki na fito nikam. Bani ruwa mara sanyi kawai it's okay". Ja'afar na dariya ya kawo masa ruwan, da kansa ya zuba masa a kofi sannan ya zauna suna gaishe shi a tare. Da kulawa ya amsa musu, da faɗin, "Gobe su Mammah zasu dawo ko?". "In sha ALLAHU Yaya, wlhy duk kewarta ta ishemu gidan ba daɗi. Autocinta ma duk sunyi sanyi ko ƙiriniyar basa yi da ƙyau kwana biyu". "Ai ni kaina kewar tata nake. Jiya da safe dana leƙa gidan duk sai yay min wani iri. Dan itama Ammah ta maƙale a ƙauye taƙi ta dawo Abbah nata ƙorafi". Cikin dariya har suna haɗa baki wajen faɗin, "Ai jiya da muka je da daddare yanata faɗa, wai yau tunda safe zai aika driver a ɗakkota, shi ya gaji su Mabruka nata bashi kwamacalar abinci, tuwon ma jiƙaƙƙe suke masa". Yanzu kam dariya suke harda Imran. Dan rikicin Abba sai Hajjo ke iya masa. Itama idan ya rikice mata wani lokacin sai ta haɗa shi da Mammah da yake ɗauka tamkar babbar ƴarsa ake samun lafiya. Sun cigaba da hirarsu har suka gangaro kan batun Bilal da shima dai watan gobe zai dawo gida in sha ALLAHU. Sai magana auren Biebah data dage ita bazatai aure ba sai Dada ya fito, in ba haka ba ita da aure har abada. Imran da yasan ga shirin da suke yace su barta kawai in sha ALLAHU komai zai warware. Bai bari shagon ba sai bayan sallar azhar. Ya haɗo shopping na kayan babys da turamen atamfa har akwati biyu aka kai masa mota. Gida ya wuce kai tsaye, zaije ya ɗan samu ya huta bayan la'asar sai ya leƙa gidan Mimi yaga baby dan dama siyayyar duka tata ce......✍️
[12/10/2025, 11:28 PM] Zeenaran 😘: 18
.........Sai da sabon driver ya tabbatar su Nimrah sun gama shigewa sannan ya koma cikin mota. Wayarsa ya ciro daga aljihu ƙarama tecno, ya kashe ta ya cire murfin da batteryn ta. A mamakina rigarsa ya ɗan ɗaga ya zaro leda mara girma sosai, koda ya kwance ta tsumma ne fari ya fara bayyana da aka nannaɗe wani abu a ciki. Ya shiga warware tsumman sai ga ƙaramar bindiga ta bayyana, ƙaramar takardar dake tare da bindigar a nannaɗe itama ya ɗauka ya warware layukan waya da yawa suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka ya saka a wayar ya maida batteryn ya kunnata. Kira yayi tare da kaita kunensa yana gyara zama. Ba'a wani jima ba aka ɗaga daga can. Kasancewar speaker ɗin wayar a buɗe take sosai yasa ake iya jin abinda nacan ke faɗa. Gaisuwa suka fara kafin nacan ya cigaba da faɗin. "Ai harna fara tunanin sakawa a bi bayanka Mole, naji har kwanaki uku babu wani bayani daga gareka. Ina fatan dai lafiya? Ka samu karɓuwar da muke so a gidan?". Iska mai ƙarfi ya furzar cikin damuwa da ɗacin da yake ji a cikin maƙoshinsa ya furta, "Oga na samu ƙarɓuwa kam, sai dai akwai matsala gaskiya." "Matsala kuma? Yarinyar bata tare da su ne?". "Tana nan a gidan. Ta girma sosai ta zama budurwa. Sai dai babu wata alamar dake nuna tasan tana da wasu iyaye bayan su. Da alama abinda Goje ya taɓa sanar mana na an mantar da ita iyayenta gaskiya ne." "Amma uwar nan tata muguwa ce gaskiya. Tabbas da ace tana raye har yanzu ba ƙaramin barazana zata zame mana ba ita da ubanta." "Ai ko yanzu ta zame mana, dan ban san ta inda zan fahimtar da Uwa wanene ni ba har tai mana abinda muke buƙatar daga ƙarshe ta dawo hannuna". "Karka damu dole mu tafi mataki na biyu ne kawai gaskiya. Amma ka bari zan yi magana da oga muji wace shawara ko shiri yake da shi akan hakan. Tunda dama ya kamata mu sanar da shi da kanka zakai aikin yanzu, dan kar a samu irin matsalar da Buba yaso bamu. Yanzu a gidan kake kwana?". "A'a haba kaima kasan bazan kwana a nan ba. Dan wannan Imran ɗin da kuka raina shima shegen kansa ne. Tunda ya ganni alamun tsarguwa suka bayyana akan fuskarsa. Dole sai nayi taka tsantsan da shi. Dan ni kasan bana raina abokin gaba". "Kamar ni kake, dama su Oga ne ke ɗaukar Imran mai sauƙi, sun kasa fahimtar irinsu sunfi illa fiye da shi wanda suka ɓoye ɗin da bai iya shanye abu. Amma ka barsu za'aje gaɓar da zasu gane shima ba abinda zasuyi wasa da shi bane. Kai kuma ka ƙara yin taka tsantsan". "Ba damuwa sai na jika". Daga haka sukai sallama ya sake kashe wayar ya cire layin ya maida shi inda yake tare da bindigar nan. Sannan ya tada motar yabar wajen.....
(Hummm wa kuke tunani wai?)
}}}}}}}}}{{{{{{{{{ ★PRISON★
Bai san fuskar ba, bai taɓa ganinta ba. Dan haka ya zubama vistor ɗin nashi jirkitattun idanunsa masu bulale abokan gaba koda bai tanka ba har na tsayin minti ɗaya. Tabbas ALLAH ya bama Dada basira mai ƙarfi, nutsuwa, dattako da sirrin iya aiki matsayin jami'in tsaro. Zakai matuƙan shan mamaki idan akace maka a wannan kalon na minti ɗaya kacal ya fahimci fuskar bogi ce a tare da mutumin, hakan na nufin yayi amfani da facemask wajen ɓoye ainahin fuskarsa. Wani murmushin da sam bai niyyasa bane ya suɓuce masa, murmushi daya saka vistor ɗin nashi murmusawa shima, duk da bai fahimci ma'anar murmurshin Dadan ɗin ba shi. Shiru ya sake biyo baya a cikin ɗakin batare da yunƙurin tankawar kowannensu ba na tsawon lokaci. Tamkar Dada na ƙirga lokutan zamansa a wajen ne, minti biyar na cika daga agogon ɗakin da suke ya miƙe tsam batare da yace komai ba ya juya zai bar wajen. "Bai kamata ka ƙosa haka da wuri ba, domin mu mutuwa ne, ana rayuwa da mu ne dole, tun daga ranar haihuwa". Cak Dada ya tsaya a takunsa na uku, sai dai bai juyo ba bai kuma ce komai ba har tsahon minti guda cir. Kafin a hankali cike da ƙasaitarsa mai tafiya da nutsuwar masu izza ya juyo gaba ɗayansa. Idanun nan nasa masu kaifi da zafi ya zuba masa, kafin a bazata yay wani sakaran murmurshi mai cike da ma'anoni masu ƙarfi da ya nema tarwatsa zuciyar vistor ɗin a cikin ƙarjinsa. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kansa. Sai kuma ya buɗe lips kaɗan, gira a sama ya amsa masa da. "Ni kuwa kaga anan sai banga siffofin kamala irin na mutuwa mai cika umarnin UBANGIJINA ba. Siffofin akuyoyin dake gudun tsiran neman mafaka a yayin da ruwan sama ya sauka kawai na gani a gabana". Sosai fusata ta nuna a fuskarsa vistor ɗin, duk yanda yaso danne fusatarsa hakan na neman gagara. Idanunsa sun yi ja sosai har hannunsa na rawa sai da ya dunƙuleshi a cikin juna ya matse yatsun. Dada dake kallon hannun nasa ya kauda idanunsa yana murmurshi. Ai ko sai hakan ya sake hasalashi, a kausashe ya daki tebirin yana furta, "Mune akuyoyin kenan?". "Amsa mai ƙyau". Dada ya bashi amsa kai tsaye yana sake takowa ya dawo wajen. Duk da hannunsa akwai handcuffs cike da salon manya ya juya kujerar ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya suna kallon juna ido cikin ido. Dai-dai lokacin masu tsaronsa suka shigo saboda bugun teburi da baƙo yayi. "Sir! are you all right?". Kansa kawai ya jinjina musu batare da ya kallesu ba balle yin magana. "Okay". Suka faɗa suna salute ɗinsa da ɗan kallon baƙon da ya gama kaiwa wuya suka fice. Sai kuma ga wasu sun sake shigowa niƙi-niƙi da kwalaye. Su kam gaisheshi sukai kawai tare da sanar masa oga ne ya aikosu da kayan zasuyi aiki a ɗakinsa. Kamar zai ce wani abu sai kuma yay shiru da basu dama da hannu suka wuce ɗakin nasa. Ya ɗan bi kwalayen da kallo. Har sai da baƙon nasa yay wata dariyar iskanci da izgili. A wulaƙance ya ce, "Karka ji ka damu fa, mun ƙara maka matsayi ne, dan bai ƙyautu ace lokacin da mutanenka ke ihu da kururuwa kai kunnenka baya ji ba, idanunka basa gani ba. Shiyyasa muka kawo maka gift ɗin da zai baka damar ji da gani kusa da kai gab..." Tsahon sakanni bashi da niyyar tankawa daga kalamansa, sai hakan ya bama vistor damar taɓe baki da sake faɗin, "Kana jin tsoron rasa rayuwa ne? Ko faɗa ka bada amsa ne kake jima fargaba?". Da wani irin salon luuu Zak-Dada ya ɗago idanunsa yana kallonsa cike da izza da nutsuwarsa da ALLAH ya mallaka masa a kowane hali. Sai kuma ya ɗan matso kaɗan ya dafe duka hannayensa dake sanye da handcuffs a saman table ɗin, idanunsa ya sake ajiyewa kai tsaye cikin nasa tamkar zai soke ruhinsa da su. Da golden voice ɗin nan tasa mai razanasu ya furta, "Jarumin gaske sulƙen yaƙi da linzamin dokinsa ne kawai GUZIRINSA. Duk lokacin da kaji abokin faɗa ya zagaye kansa da MAKAMI ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi na faɗa maka tsoro ne ya saka shi". "Tsoro!?". Baƙo ya faɗa cike da son aro jarumta da ƙarfafa kai na dole. Sai kuma ya murmusa yana ɗan buga yatsunsa akan tebur. "Kana da yawan cika baki a magana. Amma ka sani mu ba da suna muke aiki ba. Idan suna ya bayyana, haske zai shigo. Idan haske ya shigo, tsarin ya lalace. Mu mune mazaunan ƙasa a ɓoye. Mu ne masu murɗa jijiyoyin gwamnati. Mu ne masu rubuta dokar da gwamnati ke karantawa." Ya sake matsawa kusa kusa sosai. "Yau shekaru takwas kenan muna kallonka daga nesa. Kana tunanin wannan gadarar taka ce ta baka wannan filin? Ko har yanzu gurɓataccen tunaninka na cigaba da baka wancan ƙarfin ikon da kake gadara da shi a baya har yanzu yana da tasiri? Ka manta cewa ƙasar nan tun kafin ka yi tunanin kare ta, mun riga da mun shafe shekaru muna sarrafa zuciyar manyan da kake kira shugabannin cikinta. Kalli kanka mana, har yau baka ɗauki darasi daga ikonmu bane?. Mu muka bar ka a nan. Mu muka hana a kashe ka. Mu muka hana a sake buɗe shafin ka. Ba wai saboda kana da muhimmanci a garemu bane. A'a…" Ya yi kakkarfan numfashi yana wani murmushi, ya cigaba da faɗin, "…saboda muna son ka zauna ka kalli yadda ƙasar da ka ɓata shekarun ƙuruciyarka a kareta ta koma filin WASAN ƘWALLON ƙafarmu. Da jinin abokanka, zuri'arka, ƴan ƙasar taka zata zame mana mai danshin da zamu ji daɗin gudu a kanta. Kaɗan da zamu rage a cikinsu ka kalli yadda suke bauta mana. Ka kalli yadda za mu rusa duk tsarin da ka kare rayuwar taka a karewa. Ka bar gudanar da tunanin cewa kai ka san makircin ƙasa. Kai ɗan wasa ne a wani katafaren wasan da muka fara shekaru masu yawa da suka wuce tun kan haihuwarka, kaga hakan yayi kama dana masu TSORO?". Ya ƙare dogon sharhin nashi yana gyara zama da jifan Dada da kallon raini yana wani dariyar iskanci da izgili. Sai dai maimakon yaga Dadan ya firgita ko nuna tsorata da matsanancin tashin hankali kamar yanda sukai tsammani sai yaga saɓanin hakan a bayyane. Domin kuwa da wata nutsuwa da baƙon bai taɓa gani ba, ya ɗaga kansa ya kalle shi da idanun da suka saba ganin bala'i ba tare da girgiza ba.........✍️
A gaya masa gaskiya ko a barshi da Dadan kai?. To bari dai mu gaya masa ko kaɗan ne 😂💃.
😝Kai kam baƙo duk wanda ya baka shawarar zuwa wajen nan ba sonka yake ba, yo ubanwa ke zuwa gaban zaki yay wasa ya kwashe kayan wasan salin alin ya koma gidansu yay barcin hutu.🥱. Amma dai bari muji amsar da MAZAN FAMA zasu baka🤣.
Barkanmu da dawowa, ya weekend?😎 [12/10/2025, 11:28 PM] Zeenaran 😘: 19
.........Ana fitowa sallar azhar driver ya kawo musu abinci da ɗaukar su Aheel. Babu yanda Ruky bataiba suje su amso Nimrah taƙi, dan ita kam haka kawai ganin mutumin nan tayar mata da hankali yake ta rasa dalilin haka. Tana zaune a inda Ruky ta barta ta dawo ta sameta. Tana ma buɗe abincin ta sake ɓata fuska ganin minene a ciki. Dariya Ruky tayi, dan tasan Nimrah bata damu da doya ba sam. Harararta tayi kuwa, ƙarshe ta miƙe wai ita ta ƙoshi bazata ci ba. Sanin butsutsunta yasa Ruky bata takura mata ba, anan ma ta barta ita ta koma aji. Sai da taci iya abinda zata iya ta rufe sauran ta koma ajin itama. Sun cigaba da ɗaukar darasi, Nimrah nata mutsu-mutsun yunwa, gaba ɗaya sai Ruky ta damu, har cikin ranta taji haushin su Kulu da suka aiko musu da doya bayan sun san Nimrah bata ci. Jakarta ta ɗakko ta ciri kuɗi tare da miƙewa taje gaban sayyadinsu cikin ladabi ta sanar masa zata fitsari. Bai hanata ba dan hakan normal ne. Tana fita maimakon restroom sai ta wuce shop ɗin makaranta. ALLAH ya taimaketa ta samu sauran meatpie bai ƙare ba ta amso mata biyu ta dawo tunda suna da ruwansu. Sai da ta zauna sannan ta saka mata a hijjab. Kallonta Nimrah tayi, sai kuma ta tattaɓa abinda ta ajiye mata akan cinya. Wani irin ƙaunar Ruky ce ta sake cika mata zuciya. Idanunta cike da ƙwalla ta ce, "Thanks you Sweetheart". A hankali. Murmushi kawai Ruky tai mata. Cikin hijjab ta shige tana ci, duk da kuwa hakan doka ne ba'a ciye-ciye a aji. Amma da yake Sayyadi Kamal nada wani ƙudiri a ransa game da Nimrah ɗin duk da ya fahimci abu take ci baiyi magana ba. Haka ta kammala tasha ruwa sannan ta fito itama ta maida hankalin ta a karatun. Ya kammala ya fita wani malamin ya shigo, haka dai har lokacin tashi yayi. Yau dai sambarka ƴan caskalen Mammah basuyi faɗa da kowa ba. Abinda take ji aduk sanda suka haɗu da driver yasa tai juriyar ƙin kallonsa a yanzu har suka isa gida. Ita ta fara fita ta shige ciki. Baƙar yunwar da take ji ya sata wucewa kai tsaye kitchen tace su Kulu su dafa mata noodles da ƙwai soyayye ɗaya. Kafin ta shige ɗakin su. Ruky na kwance a gado tana maida numfashin gajiya, dan haka ita bata zauna ba sai ta wuce bathroom kawai yin wanka. Kafin ta fito kuwa an kawo mata indomie ɗinta har Ruky na ƙoƙarin ɗanɗanawa. Doke mata hannu Nimrah tai tana ƙwacewa, Ruky ta lunƙuma wadda ta ɗiba a baki tana dariya da faɗin, "Shike nan ke in kina jin yunwa sai baƙar rowa". Cike da jin haushi ta bata amsa da, "Ai sai na musu rashin mutunci yau a gidan nan, sun san bana cin doya sukayi, maimakon su dafa min wani abun". Ta ƙare maganar da ƙwafa idanunta na cika da ƙwalla. Dan harga ALLAH taji haushi, sai dai bata san miya hasala zuciyarta ba kuma har kamar haka. Itama Ruky ta fahimci a hasale Nimrahn take dan haka batace komai ba ta wuce bayi tana murmushi...
Shaf-shaf suka kammala shirin zuwa gidan Aunty Mimi. Sunyi ƙyau cikin abaya iri ɗaya kalar brown da adon duwatsu masu haske. Daga Ruky har Nimrah akwai son kwalliyar tsiya. Ga iyayi kuma da ƴammatanci kamar ba ƙwailoli ba😝🏃🏼♀️. Koda yake sunce su ba ƙwaila bane ba😂, dan duk abinda cikakkiyar budurwa ke taƙamar da shi suna da. Fes suka fito abinsu, kai tsaye ɗakin Biebah suka shiga, itama dai ta shirya cikin nata gayun, sannin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387 suka biyo ya sata ɗauke kwalbar tana ƴar hararsu. "Kai waɗan nan yara baƙwa mantuwa". Dariya suka kwashe da ita a tare, Ruky ta ce, "Humm Small Mom ya zamu manta da wannan daddaɗan turaren, ai kafin a kawo mana namu muma sai su Ammy sun ɗiba mana komu sato". "Ai dama kun saba ɓeraye". Dariya suka sanya a tare nan ma. Ta daddagwala musu kowa ya shafa suna faman lumshe idanu. Dan ƙamshin turarrukan ba ƙaramin ratsa zukatan mai shaƙa suke ba. (Nima shaida ce masu karatu. Wlhy maza ku garzaya neman turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Kaf turarrukanta babu na yarwa, nayi amfani da su na gani, koma nace ina kan yin amfani da su a yanzu haka. Tana kawo turarrukanta ne masu inganci da tsaftatacen ƙamshi. Akwai Turare wuta da khumra kaloli har uku: black khumra, white khumra, brown khumra. Akwai oil perfume da kullacham ma, akwai Genine da Turare kabasa kaloli uku shima: white, black, and brown kai harma abinda ban lissafo ba. Dan tana saida kayan gyaran jiki suma na amare dama mata ƴan ƙwalisa uwargidaye masu san gyaran fata batare da kin ɓata skin ɗinki da mayukan bleaching ba. Karku ji komai ta gida ce tana nan zaune a garin Kaduna kuma tana aika kaya aduk inda kake harda kasashen ƙetare ma. Duk mai so kawai ya nemeta ta nan. Tana bada har sari ma fa masoya. +234 704 229 3387😌💃🏼🥰👍🏼). "Kai kuko wane kalar ƙamshi kukeyi haka? ya subahanallah". Mu'azz ne mai maganar yana faman buɗe hanci. Dariya Ruky da Biebah sukayi, Nimrah kam da duk take jinta cikin rashin daɗin zuciya murmurshi kawai tayi. Ganin haka yasa Mu'azz kallonta, cike da kulawa ya ce, "Yaya dai Ninah? Ko baki da lafiya ne? Naga tunda muka baro makaranta baki da walwala". Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai. Bata basu damar magana ba ta ce, "Ku muje ALLAH na ƙagara naje naga Baby". Tana gama faɗa ta fice a falon gaba ɗaya. Duk da kallo suka bita suma fuskokinsu na nuna damuwar. Koda suka iskota a waje babu wanda yace komai, kasancewar Mu'azz ne zai jasu sai ta sauke ajiyar zuciya. Ita ta shiga gaba Ruky da Biebah na baya. Su Afrah dama suna can, dan daga makaranta can driver ya kaisu kai tsaye. Koda maigadi ya buɗe musu gate bata ganshi ba, dan haka ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Suna ɗaukar titi kowa ya fara mata tambaya, saita wayance tace kewar Mammah ce. Duk sun gamsu, dan sun san Nimrah da Mammah sai ALLAH. Nimrah akwai ƙulagucin iyaye, dan haka tai bala'in sakin jiki da Mammah duk da har yanzu bata manta da Ummanta ba, sai dai bata iya tuna fuskarta sosai saboda ƙarancin shekaru na wancan lokacin. Tunda ta fara hankali da wayo cikin hikima Mammah ta koyar da ita yima mahaifanta addu'a kwanciyar kabari cikin aminci. Kulawa da take samu yasa bata jin maraici, ba kuma ta taɓa zaman yin kukan rashinsu ba sakamakon babu wani abu na labarinsu data sani ko take ji a yanzu balle ya tuna mata abubuwa a kansu. Garama Ummanta wasu ƴan abubuwan kan mata flash ɗin baya game da ita a cikin zuciya musamman idan Mammah ko su Aunty Ummi da zasu iya zama sa'annin Umman ita da Ammie (Aunty Hafsat mahaifiyar su Ruky kenan Matar Imran) takanji kamar Ummanta. Suna isowa tun Mu'azz bai gama kashe motar ba ta fita da gudu tai cikin gidan. Dariya kawai sukai mata. Aunty Biebah na addu'ar ALLAH ya cika musu burinsu na fitowar Dada sarari wataran Nimrah ta haifa musu Baby gudan jinin sa. Ita kanta bata san yanda zata misalta irin farin cikin da wannan ranar zatazo musu da shi ba balle Mammah....
"Oh ya ALLAHU ka shirya min Ninah jama'a ke da wa?". Zama Nimrah tai kusa da Aunty Mommy dake rungume da Baby tana saka masa kaya an mata wanka tana murmushi, sai da ta shafa kan babyn sannan cikin shagwaɓa ta bama Aunty Momyn amsa. "Mum ba kowa fa, kawai ina gudu na fara ganin Baby ne. Jiya fa dan mugunta Ruky ina barci taƙi tada ni suka taho". Aunty Mimi data kasa haƙuri ta ce, "Ai Dada zai sha fama a wajen nan dai kam. ALLAH yasa sanda zai dawo kinyi hankali Ninah". "Mamy shi Dada ina ruwansa da hankalina koda ya dawo? Kuma ALLAH inada hankali". Kasa haƙuri sukai kowa sai da ya dara. Ita kam ko'a jikinta tunda ta samu ta amshi Babyn gaisuwa ma sama-sama tai musu ta koma gefe. A haka su Biebah suka shigo niƙi-niƙi da kaya suna sanar da zuwan Daddy Imran. Dai-dai lokacin kuma Aunty Hafsat ta fito daga bedroom ɗin Aunty Mimi da alama salla tayi. Ai ko zaram Nimrah ta miƙe ta nufeta tana faɗin, "Ammie na dan ALLAH Babyn nan kalleta da ƙyau dawa take kama?". Dariya Aunty Hafsat tayi ta ce, "Da ke. Sai dai ALLAH yasa kada tayo ƙiriniyar taku ke da hassanar ki". Aunty Lailah dake fitowa a kitchen ita da Aunty Shariffa sai ƙanwar mijin Aunty Mimi ta ce, "A'a gara dai ta biyo komai da komai zaifi armashi Aunty". Nan ma dariyar aka shiga yi, a haka Imran ya shigo ya samesu. Sai da ya zauna kowa ya gaisheshi cike da girmamawa sannan ya dubi Nimrah data ƙanƙame Baby bata da niyyar bayarwa. "Daughter baza'a bani Babyn bane?". Murmushi tayi har haƙoranta na bayyana, sai kuma ta miƙe ta je gabansa tana faɗin.........✍️
[12/10/2025, 11:29 PM] Zeenaran 😘: 20
......."Daddy ai kaine za'a baka. Amma minti biyar zatayi ka sake bani. ALLAH ji nake kamar kada na ajiyeta fa. Daddy dan ALLAH na dawo nan da zama har ayi suna?". "To Nimrah in kin dawo makarantar fa?". "ALLAH Daddy in ta dawo nima sai na dawo". Ruky ta faɗa itama. Cikin girgiza kai yace, "Ai bama zan bari ku dawo ɗin ba. Daga yau ba zaku sake zuwa ba sai ranar suna." Zasu fara magiya ya ce, "Okay nace Mammah tai zamanta kada ta dawo goben kenan?". Ai tuni suka saki batun dawowa gidan suka fara murna jin Mammah zata dawo. Abin zai birgeka har su Auntys ɗin farin ciki suke yi. Shi dai Imran yay ma Baby addu'a sosai ya ɗan zauna suka taɓa hira sannan ya miƙe zai tafi. Dole Aunty Hafsat ta miƙe suka wuce tare. Su kuwa sai anyi sallar magriba sannan koma isha'i....
>>>><<<<★★>>>><<<< ★DUBAI★