Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 13

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 13

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 13: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 13. .........Isowarsu ɓangaren da Dada yake ya tabbatar min da lallai ba wannan…

4,412 words

.........Isowarsu ɓangaren da Dada yake ya tabbatar min da lallai ba wannan jami'an bane ainahin vistors ɗin, dan a ƙofar wajen suka samu wanda akaima rakkiyar. Bayan sun ƙame tare da salute ɗinsa ɗaya ya matsa yana sanar da ogan nasu cikin magana ƙasa-ƙasa. Kansa kawai ya jinjina batare da yin magana ba, kuma ba'a ganin fuskarsa dan ya saka norse mask ga eyeglass, sannan kansa da hula p-cap data sake ɓoye ainahinsa. Yana sanye cikin ƙananun kaya daga sama har ƙasa baƙaƙe. Har cikin ainahin ɗakin ganawar securitys ɗin sukai masa rakkiya, dan shi kaɗai ya shiga banda jami'an sa. Koda suka nuna masa kujerar zama bai zauna ba, yana daga tsaye kawai a cikin dakin yana jiran shigowar wanda zuciyarsa ke bugawa saboda tsoron abin da zai gani, tsawon shekaru biyar har da wattani huɗu a kai bai ga Zak-Shadow koda daga nesa ba. Mintina kaɗan da suka kasance masu nauyi na cika wanda yake begen gani da ƙagauta ya iso. Cak numfashinsa yaso tsayawa sakamakon bayyanar mazan fama, sosai ya rame fiye da wancan ganin da yay masa na shekarun baya. Duk da lokaci-lokaci ana masa aski hakan bai hana gashin saje taruwa a farar fuskarsa ba da kansa. Fata kam tayi haske da kwanciya saboda zaman waje guda. Sai dai baza'ace akwai laushi na jin daɗi ba. Yanda yake kallonsa haka shima Dada ke kallon nasa, dan duk da ya rufe fuska a kallo ɗaya ya gane wanene, dan ko cikin rububi manta wannan halittar ta gabansa sai dai ɗimuwa a lokacin magagin mutuwa amma ba a cikin hayyaci ba. A karo na farko baƙon ya ɗan murmusa da ƙoƙarin danne abinda ke yunƙuro masa. Sai kuma ya kai hannu a hankali ya zare glasses ɗin idanunsa. A tare idanuwa nasu suka haɗu a cikin na juna. Imran ya kasa motsi. Haka shima Dadan bai motsa ba, dan kai tsaye zuciyarsa yake kallo a zahiri. Fin sakan talatin suna a haka kafin Dada ya saki wani ɗan murmushi da lumshe idanu ya buɗesu a lokaci guda, a hankali ya cigaba da takowa har inda Imran yake. Har yanzu nutsatstsiyar fuskar nan tasa da murmushin nan nashi na ƙasaita, ya motsa lips kamar mai son raɗa ya furta, "Ranka ya daɗe, soja… har yanzu baka daina kuka da ido ba?". Kauda kai Daddy Imran yayi yana haɗiye hawayen da basu ƙaraso cikin idanunsa ba, amma da yake Zak-Shadow ɗin nasa Zak-Shadow ne shi har ya karantosu daga ƙirjinsa. Wata ƴar ƙaramar dariya Dada ya saki da kaiwa zaune, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya hannayensa da yau babu handcuffs harɗe a ƙirjinsa ya sake faɗin, "Sit mana my Boss". Yanzu kam shima murmushi Daddy Imran yayi, sai kuma ya gyara kujera ya zauna irin zaman Dadan suna kallon juna tamkar wani saurayi da budurwa. "Na yi missing naka sosai, Zak..." kalma mafi nauyi da girma dake riƙe da zuciyar Imran ta fito daga bakinsa. Sai kuma hawaye suka cika masa idanu. "Idan ka cigaba da wannan kukan, how many missions za ka gama?. Kalleni da ƙyau ina raye, kuma ina cikin ƙoshin lafiya mi kake buƙata bayan hakan daga UBANGIJI? Ko sai na tashi mun gwada ƙarfi ne?". Dariya sosai Daddy Imran keyi cikin hawaye, dan ya fahimci yau raha Zak.. ɗinsa ke ji. Kai tsaye ya ce, "Kai dai ba zaka canza ba." "Zama da kai ne Imran, kwana biyu sai nake jin matsanancin kewar ka. Ashe kana gab da ni ne shiyyasa." "Duk randa muka zama a nesa da juna lallai ƙasa ta bizne idanun wani a cikinmu ne ko mu duka. Sai dai ni nafi fatan fara tafiya na barka dan nasan bazan iya ɗauka ba idan kai ne ka barni". Idanu sosai Dada ya zuba masa. Dan haka shiru ya biyo baya, irin shirun nan mai cike da abubuwan da bazasu faɗu ba. Tsohon lokaci kafin Daddy Imran ya katse yanayin nasu ta hanyar miƙa masa briefcase daya shigo da ita. "New President Yusuf Tafida… ya buƙaci nazarin shari'arka tun daga farko har ƙarshe. Sai dai ba yau za mu faɗi komai ba. Amma daga yau ɗin game ya fara dawowa." Cak numfashin Dada ya tsaya ba ƴan sakanni, ya kuma zuba ma Imran ido tamkar zai haɗiyo shi da su, "Sabon shugaban ƙasa, zai iya zama yana da alaƙar huɗɗa da waɗanda suka karyar da ni fa Imran, sai dai maybe shima bai sani ba." "Miyasa kai wannan tunanin? Dama ce fa tazo mana daga UBANGIJI. Kafa san wanene Janar". "Tabbas nasan Janar, sani na nagarta da mazantaka. Ba kuma bana farin ciki da damar bane, ina ganin kamar yazo da gaggawa ne, gaggawar da zasu iya kaishi ƙasa da ita a kaina, dan yazo musu da bazatar abinda ba shi suke hasashe ba a kansa. Dole ya zama mai zaɓi biyu a lokacin da ya bayyana musu ainahin fuskarsa a kaina. Saboda a tsarinsu babu wani shugaban ƙasa da zai kasance baya abota da su. Koda sun ɓoye masa waccan fuskar tasu a yanzu inada tabbacin zasu bayyana masa ita ya sansu ya san aikinsu. Matsalar kuma idan har yana son gaskiya, to sai ya tabbatar min da hakan da aikin shi. Ba da kalamai ba. Dan kar ya kasance na amince na fita ya zama yana cikinsu bazan ƙyalesa ba koda shine Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi". Daddy Imran ya fahimci hangen Dada, dan haka ya sauke numfashi mai nauyi yana jinjina kansa da faɗin, "Haysam na yarda da ku kai da Janar da Faro. In sha ALLAHU Janar bazai bamu kunya ba, yanda muka fara da shi zamu ƙare a tare koda sai bayan babu ran mu ne NASARA zata bayyana. Na tabbatar shima kamar mu ya ke, idan gaskiya tana gona, zai haƙo ƙasa ya nemota da kansa." Dada yayi murmushin mai zafi fiye da bala'in da yake hangowa da ƙurar da zata tashi. "Shike nan Imran! ka gaya masa, idan yana neman gaskiya, kada ya zo da haske. Duk wanda yake neman ƙasar nan, sai dai ya biyo duhun dare. Ni zan fara jiranku daga yau. Ku dinga tuna kuma zan dawo da gudunmawata. Game on.... again." yay furucin ƙarshe da wani salo yana kashema Imran ido ɗaya da yin alamar harba bindiga da yatsu biyu. Dariya Imran ya kece da ita, irin dariyar da shi kansa yasan ya jima baiyi ta ba. Kai koda kwatance baya kawota a zuciyarsa balle ma fuskarsa. Shima Dadan kallonsa yake yana wani shegen murmushi mai bayyana haƙwara, kai daka gansu kasan ƙara'in farin ciki ne na tsahon shekaru ke fidda kansa tun daga ƙasan zuciya har zuwa fuskokinsu. Sai dai Imran yasan minene ma'anar murmushi irin wannan a fuskar Zak-Shadow ɗinsa. Ya tabbatar zafin daya jure cikin wannan duhu na tsawon shekaru takwas da wata huɗu, sakamakon wannan murmushin idan ya fito ƙasa za ta sake girgiza......

<%><%><%><%>

"Malam Almu maganar ciwo ai ta wuce wasa, kuma ta kori komai a rayuwa. Dan haka babu batun neman alfarma zuwa gida daga garemu. Ka shirya kawai abinka ga kuɗin mota. Wannan kuma sai kai amfani da shi wajen kaita asibiti, ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne. Zaka wuce yau ne ko sai zuwa gobe? Dan muma zamuje airport ne ɗaukar Bilal yau zai dawo". "Kai kai Masha ALLAH. Yau Alhaji Bilal zai dawo ashe? To bari na jira ya dawo tukkuna ai kamar zai fi". Kai tsaye Mammah dake saurarensu ta ce "A'a Malama Almu ban goya bayan haka ba, kaje dai tunda zaka dawo ai. Itama Innarka na buƙatar ka, kuma tana buƙatar a kaita asibiti. Ina ga ma idan kaga jikin babu daɗi sosai kawai ka ɗakkota zuwa goben ku taho nan a kaita asibiti zai fi". Godiya maigadi yake jerama Mammah dasu Yaya Ja'afar har hawaye na cika masa idanu. Yana tausayi da mamakin alkairan bayin ALLAHn nan, shiyyasa a lokuta da dama idan ya tuna dalilinsa na zaman gidan nan tare da su sai yaji zuciyarsa na karaya akan ƙudirinsa. Haka ya miƙe yana shartar hawayen da shi kaɗai yasan dalilinsu ya fita...

A gurguje maigadi ya shirya tare da damƙa gate a hannun sabon driver kamar yanda su Ja'afar suka ce masa. Ya wuce ya tafi yana ayyana wa a ransa ai bazai wuce jibi ba, idan har zuwa kwana uku bai dawo ba to bazai wuce safiyar kwana na huɗu ba in sha ALLAHU. Dan babu wani ciwo da Innarsa keyi kamar yanda ya faɗa, ogansa ne ya bashi umarnin zuwa ya sameshi da gaggawa a yau. Saboda shi Innarsa ma ta jima da rasuwa, a hannun kishiyar uwa ya tashi, azabar data bashi da wahala ta maida shi yanda yake a yau, sai dai a gidan Mammah sanin mutum cikakke sukai masa mai nagarta sakamakon ɓoye ainahin wanene shi da yayi a garesu....

Tofa, wata sabuwa maigadi🤔🤐🏃🏼‍♀️.

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ ★DUBAI★

Duk yanda su Hajiya Hasiba suka so tafiya India bincike akan Adeel bai yiwu ba. Dan kuwa randa ta samesa da dabarun zuwa India business a ranar yace mata ya kammala shirin tafiyarsu. Ta jira har su dawo sai taje. Kota sanar masa business ɗin da kamfanin da zasuyi koma miye a kawo mata shi. Jin haka yasa ta saurin cewa ba damuwa suje ɗin kawai su dawo tayi nata uzirin daga bayan. Shirin nashi bai bata tsoro ba sai da ya tabbatar mata harda su Nabeeha za'a. Ta tambayesa ba'asi yace hankalinsa zaifi kwanciya idan tana acan tare da shi. Dan karma ya barta anan wani abu ya faru. Duk da kuwa yana da ƙarfin ikon sakawa a bibiyar masa ita duk inda ta shiga a cikin ƙasar. Amma baya buƙatar hakan, dan bayan abokinsa ɗaya jal babu wanda yasan yana bibiya ko son auren Nabeeha. Abinka da sai yanda akai da kai, dole suka hau shirin tahowa. Sai dai ran Nabeeha da Ismat fal farin ciki. Hakama Mamawo, dan koba komai itama akwai nata shirin data barma tata zuciyar game da Adeel ɗin, tana ganin kuma zuwansu ƙasar tasu ce zai iya cika cikin sauƙi saɓanin anan da wasu dalilai zasu iya hanata. Amima da Raihana ko basu so wannan tafiya ba. Dan harga ALLAH su daɗin zaman Dubai suke ji, har basa son tuna zuwa ƙasar haihuwarsu. Shiyyasa ma suke matuƙar jin haushin Nabeeha da taƙi bada haɗin kai bori ya hau. Dan wlhy da a cikinsu Adeel ya nuna yana son wata hohoho da wani labarin ake ba wannan ba ma..........✍️

[12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 31

........Sun iso cikin dare. Kasancewar a babban birnin suka sauka yay bucking hamshaƙin hotel na gani na faɗa da yafi kowane hotel tsari da ƙayatarwa. Su kuwa gidan Hajiya Hasiba suka sauka. Dan tun a can ya nuna musu baya son asan tafiyarsu ɗaya da shi har ya kammala aikin nasa su koma. Ba laifi gidan babba ne sai dai ba ƙato ba. Six bedrooms ne. Sai faluka guda uku. Akwai na baƙi da bedroom ɗaya, sai falon ƙasa shima da bedrooms 2, sai upstairs da falo da 3 bedrooms shi kuma. Akwai kitchen a ƙasa. Sai can gate akwai ɗakin maigadi. Shi kaɗaine kuma a gidan da matarsa da yaransu biyu. Kasancewar idan suna nan itace ke musu aiki. Dan haka tun suna can ta sanarma maigadin zuwansu. Haka matar ta yini yau tana ƙalƙale gidan, da yamma mai musu abinci tazo tai musu, sai da ta shirya komai a dinning sannan ta wuce dan dama ba'a nan take kwana ba. Tun kan Hajiya Hasiba ta shiga siyasa tana da kuɗi, dan kuwa tako wace hanya nemansu akeyi. Alaƙarta da manyan ƙasar musamman first lady ya sake armasa dukiyarta da sanin manyan mutane da ake harkokin da basai ance komai ba (🥱🤭🤫), ko wannan gidan ƙyautarsa aka bata sukutum kamar juye alalar gwangwani a plate 🥱🤣. A yanzu kuma ga Adeel ya ida jiƙeta. Duk da ba wata gajiya ce a tare da su ba kowa sai wayyo-wayyo yake yi. Duk suka zube a falon ƙasa suna sauke numfashi, maigadi da matarsa nata kai-kawon shiga musu da kaya da jera musu sannu. Da ƙyar suka iya tashi bayan wani lokaci suka haye sama su duka. Dan duk can suke da ɗakunan barci har Mamawo ɗin ma daba wani zama take sosai a ƙasar ba. Wanka suka fara gabatarwa sannan suka nema abinci. Suna kammala ci kowa ya nema makwanci. Basu tashi farkawa ba a washe garin ma sai ƙarfe kusan sha biyu. Haka sukai wanka suka sakko ƙasa neman abinci. Sunko samu Joy ta kammala komai har na rana, aiko suka far masa da ci sai da kowa yay ƙat. Wajen ƙarfe uku Nabeeha tace tana son zuwa gidanta ɗakko wani abu. Aiko daga Mamawo har Momyn tasu suka hayayyaƙo mata da masifa. Da farko shiru tai musu, sai daga baya ta saka musu kuka. Jikinsu ne kuma yay sanyi, dan haka Momyn tata tace ta shirya amma su Ismat ne zasu rakata su dawo tare, amma yau yamma tayi ta bari sai gobe. Bata musa ba tace ta yarda.......

<<%>><<%>><<%>>

Kamar kullum yau ma a dai-dai lokacin da aka saba tashinsu islamiyya aka tashe su. Kasancewar Yaya Mu'azz ne ya kawosu sun tabbatar bazai zauna zaman jiransu ba kamar driver har zuwa yanzu. Sai dai zai dawo ya ɗauke su. Su duka zukatansu cike suke da zumuɗin komawa gida saboda Uncle Bilal, dan ba ƙaramar kewarsa sukai a watannin nan da baya nan ba. Sune farko fitowa a aji, ajin nasu kuwa daga shi sai na ƴan sauka, duk da suma dai gab suke da kaiwa sittin ɗin in sha ALLAHU. Hayaniyar dake tashi a ajin ƴan saukar ne ya daki kunnuwan su Nimrah da suka fara fitowa, kallon juna sukai ita da Ruky, sai kuma suka nufi ajin da sauri dan ganewa idanunsu abinda ke faruwa. Gaba ɗaya ajin ya hargitse da ɗaliban ƴammata da samarin cikinsa, dan kuwa sun girmi su Nimrah su zasu iya kaiwa sha bakwai ne. Yanda suka dunƙule waje guda suna jefe-jefen takalmansu yasa Nimrah data kutso kai cikinsu kallon abinda suke jifar. Abin takaici abin mamaki ba komai bane sai mage. Wata baƙar mage ce da jariran ƴaƴanta biyu, ɗaya fari tas ɗaya baƙi da kwalliyar golden a jikinsa. Mai kwalliyar golden ɗin na kwance kansa da jini alamar wani ne ya jefesa, farin kuwa ya maƙale jikin uwar da itama har an jimata ciwo sai wani irin nishin kuka take. Ai bama tasan ta zabura inda magen take ba jikinta na rawa. Ihu ƴan ajin suka fara mata da kiran karta je ba mage bace aljana ce ko wata mayyar ta rikiɗa tunda ance mayu na zama mage, amma kota kansu batabi ba ta ƙarasa. Hannu ta saka ta ɗauki magen ta rungume, tare da ɗaukar farar itama dake jaririya abin sha'awa, tana kai hannu zata taɓa golden ɗin dake kwance a ƙasa kawai cikin ƴan ajin wani ya wulwulo dutsina har biyu. Ai ko ɗayan ya sauka akan magen babba ɗaya akan Nimrah. A tare suka saki ihu ita da Nimrah ɗin kan magen ya fashe, Nimrah tai luuu ta zube a ƙasa magunan biyu rungume a jikinta. Sake rikicewa ajin yay da hayaniya, sai dai kowa ya kasa ƙarasawa inda suke sai Ruky da ALLAH ya bama dama kutsowa cikinsu da ƙyar ta ƙaraso da gudu tana kiran sunan Nimrah dake kwance a ƙasa jini ya wanke fuskarta da hannunta da jiki babu alamar rai a tare da ita. Ga maguna har biyu a jikinta ƙaramar na kuka babbar kanta a fashe alamar jininta ne ya ɓata uniform da jikin Nimrah ɗin. Ihu ta fashe da shi tana jijjiga Nimrah da kiran sunanta, sai kuma ta juya tana kuka da kallon ƴan ajin. "Wlhy wlhy idan ƴar uwata ta mutu kuma duk sai na kashe ku. Ƴan iska kawai azzalumai". Ta sake juyawa tana jijjiga Nimrah. "Ninah! Ninah! Dan ALLAH ki tashi, ki tashi Ninah". Ina babu alamar rai a tare da ita. Dai-dai nan malamai biyu suka shigo ajin, dan wata ɗaliba taje ta sanar musu kasancewar offices ɗinsu na daga can gefe yasa basu san abinda ke faruwa ba. Suma hankalinsu ya tashi da ganin abinda ke faruwa. Nan danan sukai kan Nimrah da Ruƙayya ke jijigawa tana kuka. Kai tsaye suka fahimci suma tayi, Sayyadi Kamal ya juya yana faɗin a bashi ruwa... Ana zuba mata ruwa ta farfaɗo, sai dai jinjin dake zuba a goshinta yasa idanunta sai faman juyawa suke. Magunan akai ƙoƙarin amsa a hannunta ana bama ɗalibai mata umarnin kamata a fita waje dan kaita asibiti. Amma taƙi saki. Sai da Ruky ta ce, "Ninah ki sake su dan ALLAH a kaiki asibiti, magen ma ta mutu". Kai ta girgiza mata alamar bazata saki ba. Sai hawaye kuma suka fara bin fuskarta a karo na farko. Sayyadi Kamal daya fahimci bazata bayar ta sauƙi ba cikin lallashi ya ce, "Yi haƙuri Naja'atu ki bada magen, kanki na zubda jini kar kema ki rasa ranki. Na miki alƙawarin ajiye miki ɗayar tunda ita tana da rai kinji". Da ƙyar ta iya buɗe idanunta ta kalleshi, ya jinjina mata kansa alamar tabbatarwa. Sai lokacin aka samu ta saki magunan. Sayyadi Kamal ya amshi ƙaramar data rage a raye, sannan aka kama ta aka fita da ita. Dai-dai lokacin kuma Imam da Mu'azz da suka zo ɗaukarsu suka iso. Hankalinsu ya tashi da ganin halin da Nimrah ɗin ke ciki, su Aheel dake tare da su kuwa kuka suka fara ganin Ruky na kuka itama. Koda suka tambayi ba'asi Sayyidi Kamal yace yanzu ba lokacin kace nace bane kawai asibiti ya dace a kaita dan raunin nada girma da alama...

★+++++++★

Sai da Mu'azz yay ma Nimrah jan ido ta nutsu aka duba raunin. Kasancewar ta cikin gashi ne dole aka ɗan cire gashin wajen akai mata ɗinki dan taji ciwo sosai. Mataimakin shugaban makarantar da Sayyadi Kamal da suka bisu ne ya biya kuɗin komai duk da Mu'azz yaso hanawa. Aka bata magunguna sannan suka fito. Sosai malaman nasu suka sake basu haƙuri, sukace zasu bisu gida kuma dan ƙara bada haƙuri. Mu'azz ne yace suje kawai basai sun bisu ba tunda ALLAH ya taƙaita abin ba wani babba bane da girma. Biyosu asibitin ma ya wadatar ai. Godiya suka sake yi, Imam ya buɗe musu mota suka shiga. A karo na farko Nimrah dake jikin Ruky ta dubi Sayyadi Kamal. "Ya Sayyadi mage na fa?". Murmurshi yayi yana mai kallonta cike da wani irin yanayi da yake ƙoƙarin dannewa da tsiya-tsiya, "Kiyi haƙuri in sha ALLAHU zuwa gobe zan kawo miki ita har gida". "Ni dai muje yanzu na amsa". Kafin ma Sayyadin ya bata amsa Mu'azz ya ɗan harareta. "Ba inda zamu je daga nan sai gida. Ga Mammah nan sai jera main kira take dan kar mu tada musu hankali munce holdup ne. Tunda yace zai kawo da safe ba shike nan ba. Dalla ku shiga mota". Baki sosai Nimrah ta tunzura gaba, sai dai bata sake cewa komai ba Ruky ta taimaka mata ta shiga mota, suma su Aheel suka shiga. Daga haka sukai sallama da su Sayyadi da sake musu godiya suma suka shiga....

★"Yaya dan ALLAH ku siya mana ice-cream". Juyowa Imam yay yana hararar Ruky da tai maganar. Kafin yace wani abu cikin sake lanjarewa Nimrah ta ce, "Dan ALLAH Yaya. ALLAH su Afry ma naso ko?". Ta juya tana kallon su Aheel. Magiya suma suka fara. Sai lokacin Mu'azz daya ɗan juyo ya hararesu ya sake maida kansa ga titi sannan yay magana. "Ku yaran nan kun cika nemarwa mutane hanyar kashe kuɗi. Ga asarar salla a jam'i da kuka jawo mana. Wai kun manta yau Uncle Bilal zai dawo ne" Su dai basu kula faɗansa ba suka cigaba da maguyarsu duk da ransu cike yake da farin cikin batun dawowar Uncle Bilal da zaiyi a daren nan. Sai da yay ƙwafa sannan ya rage gudun motar. Canja hanya yay zuwa inda yasan ana saya musu ice-cream ɗin da suke so. Basu wani jima ba suka iso. Har zasu fito ya hararesu yana faɗin, "Ina zaku bimu da uniform a jiki ace satoku mukayi, ke kuma ga rauni a kai". "Abinda ba'a ganin ciwon na rufe da hijjab. Dan ALLAH ka barmu muje". Nimrah ce mai maganar cikin tura baki. Mu'azz zai ƙara magana Imam ya ce, "Barsu dan ALLAH Bro. Muje, muna sake tauye lokacin salla ne kawai a wannan surutun". Ba yanda Mu'azz ya iya yayi gaba suka bishi, Ruky harda masa gwalo. Su Imam na gaba riƙe da hannayen su Abees, su kuma suna biye da su, suna gab da shigewa Ruky ta riƙe hannun Nimrah ta tsayar da ita, batare da tayi magana ba takai hannu tana gyara mata hijjab ɗinta ganin bandage ɗin kanta ya fito. Hakan yasa suka rigasu shigewa. Dai-dai suma suna ƙoƙarin shigewa suna gulmar su Mu'azz ɗin ƙasa-ƙasa suka kusa cin karo da mutanen dake ƙoƙarin fitowa. Da sauri Ruky tai baya tana jan hannun Nimrah, sai dai cikin rashin sa'a ta tafi zata faɗi, a cikin waɗan can ɗin ɗaya yakai hannu zai riƙota. Cike da tsiwa ta ce, "Malam miye haka, karka taɓani". Duk da da hausa tayi, bai ji mita faɗa ɗin ba saboda ba yarensa bane yanda sautin muryarta mai cike da tsiwa ta daki kunnensa sai ya tsaya cak, tare da ɗago manyan idanunsa ya kalleta. Sai akai sa'a kuwa dai-dai itama ta balla masa harara...........✍️ [12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 32

.........Ba ƙaramin motsawa zuciyar Adeel tayi ba, batare da ya shirya ba ya saki murmurshi mai faɗi yana ƙare mata kallo. Sake balla masa harara Nimrah tayi tana bin Ruky dake jan hannunta sukai ciki. Yako lumshe idanu ya sake buɗewa a kansu. Zai iya rantsuwa tunda yake bai taɓa ganin baƙar fatar data gama tafiya da duniyarsa lokaci guda irin yarinyar nan ba. Gata dai ba wata ƙatuwar budurwa ba, hasalima a ƙasarsu bata wuce babyn raino ba, amma tayi masifar tafiya da dukkan zuciyarsa. Abin mamaki kuma ba irin son da yake jin yanama matan baya bane na sha'awa, wannan wani baƙon al'amari ne mai girman gaske a gareshi da ban mamaki... "Oga ya dai?". Wanda suke tare ya faɗa yana taɓa shi. Juyowa yay ya kallesa, sai kuma ya ɗan sake murmusawa da faɗin, "Mi ta faɗa ɗazun?". Murmurshi wacan ɗin yayi, duk da bai san wanene Adeel ba a matsayi na rayuwa balle ma ƙasar da ya fito. Dan kuwa daga hotel ɗin daya sauka ne ya buƙaci ɗan rakiya zaga gari shine aka bashi ma'aikacinsu ɗaya da mota, har sun wuce wajen nan ya ɗauki hankalinsa yace su shigo dan ya ga harda kilishi ake saidawa. Cikin harshen turanci ya sanar masa abinda Nimrah ta faɗa. Kawai sai ya sanya dariya. A ransa yana raya (Wato ita tana jinta wata mace ce karna taɓa ta). A zahiri kam waje ya ƙarasa fita, sai dai ya tsaya a jikin motar su ne ya zubama hanyar shiga da fitar idanunsa.... Babu jimawa kuwa su Nimrah suka fito su Mu'azz biye da su. A gaban idanunsu duk suka shiga mota, sai da yaga Imam daya amsa tuƙin yanzu ya tada mota sannan shima ya shiga tasu yana faɗama abokin tafiyar tasa su bisu. Bai kuwa musa ba tunda aikin kuɗi yake. Haka ya dinga binsu a baya ta yanda bazasu gane ba har gida. Daga can ɗan nesa kaɗan suka dakata, har motar ta shige aka maida gate ɗin aka rufe. Kai tsaye Adeel ya ce, "Ya sunan Street ɗin? Sannan kasan gidan waye?". Kai ma'aikacin hotel ɗin ya girgiza masa da faɗin, "Ban san gidan waye ba gaskiya. Amma sunan nan ɗin KOBI STREET." Sunan Kobi Street ɗin ya maimaita da karyayyen harshensa, kafin yace, "Okay zaka iya sake kawoni gobe?". "In sha ALLAHU Sir!". Fuskarsa da murmushi yace, "Muje inda zan samu layin ƙasar nan da waya". "Okay Sir". Daga haka suka bar wajen.

________

A cikin gida kuwa tunda su Nimrah suka fito a mota sabon driver malam Buba dake tsare da gate a yau ya zuba mata ido. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa, sai da ya iso inda suke yana tambayar lafiya kuwa yaga bandeji a goshin Nimrah ɗin. Imam ne ya bashi amsa a taƙaice da cewar "Ciwo taji a islamiyya". Itako da tunda tai masa kallo ɗaya tsigar jikin nata ta fara tashi ta kauda kanta. A taƙaice ta gaisheshi kamar kowa sukai gaba ita da Ruky. Haka ya bisu da kallo yana jin kamar ya bisu ciki. Sai dai ya danne zuciyarsa da ƙar, amma can ƙasan rai ayyanawa yake (Lokaci yayi da zai fitoma Nimrah ɗin a mutum tasan shi ɗin waye). A ciki ma hankalin Mammah da su Aunty Shariffa ba ƙaramin tashi yayi ba. Dan su Yaya Ja'afar sun tafi Airport ɗaukar Yaya Bilal dake gab da sauka, tuni sun cire mata hijjab suna duba wajen. Sai ita ke magana cikin shagwaɓa da son kwantar musu da hankali tana faɗin, "Babu fa zafi. Tunda aka min allura ya daina ciwo". Faɗa Aunty Biebah ta fara akan cewa bazasu yarda ba, gobe sai taje islamiyyar da kanta dole yaron nan a hukunta shi. Sai da Mammah tai maganar "Baza'a kai ga nan ba. Tunda ance kuskure ne to a barshi a hakan ALLAH ya kiyaye gaba." Badan sun so ba suka haƙuran. Amma Mu'azz dama ya ayyana a ransa sai yaci uban yaron tunda shima islamiyyar yay sauka, yanzu kuma weekend kawai suke zuwa Tahafiz shi da Aunty Biebahn. Ɗaki suka wuce yin salla. Mammah tace Biebah ta bisu tasa towel a ruwan zafi ta gasa mata goshin da fuskarta. Da to ta amsa tana bin bayan nasu...

<<<<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>>> ★RANTSUWA★

A yau sati uku da fadar da tabbatar da Janar matsayin shugaban ƙasa ta cika, a yau kuma ake shirye-shiryen rantsar da shi da shiga gidan gwamnati da aka kammala gyarawa tsaf. Tuni a cikin sati ukun nan ya kammala komai akan fiddo Dada, office kawai yake fatan shiga ya zartar da hukunci. Yanda kuma suke komai a sirrance daga shi sai Imran, da Haydar yasa zai mamayi mutane da yawa akan wannan kyakkyawan ƙudiri nasa. Kamar yanda aka tsara an gabatar da rantsuwa tako wane fanni a ƙasar, sabbin shugabanni da wanda suka sake komawa tenure ta biyu duk sun shiga gidan gwamnati a wannan rana ta litinin tare da sabbin ofisoshin su. Sai dai mu cigaba da musu fatan alkairi da nasarar yin adalci ba satar kuɗaɗenmu ba😝🏃🏼‍♀️. (Mai son soyayya da ɗan shugaban ƙasa tamun magana mu sasanta ta biya cin hanci na haɗasu🥱💃. In baki da ko sisi karma kizo😏🙄🤭🏃🏼‍♀️.)

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull