Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 14

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 14

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 14: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 14. ★A yau daren farko na sabon shugaban ƙasa Janar Yusuf Shu'aibu Tafida cikin…

4,369 words

★A yau daren farko na sabon shugaban ƙasa Janar Yusuf Shu'aibu Tafida cikin gidan gwamnati. Tsaye yake cikin ƙayataccen falon daya kasance na ƙarshe sai bedroom ɗin barcinsa, tunda ya shigo gida bisa rakkiya bai buƙaci ganin ko ɗaya daga iyalansa ba, sakamakon son fara zartar da babban birinsa. Komai kashe yake a falon in ka cire ac kawai shima ba'a wani sakashi da ƙarfi ba, an sauƙaƙa hasken fitilu gaba ɗaya dan falon na cikin ɗan duhu-duhu, zaune yake shi kaɗai kamar yanda yafi buƙata, tunaninsa gaba ɗaya ya tsaya ne akan mutum guda ɗaya, mutumin da yake ma kallo mafi muhimmanci na farko da zai shimfiɗa wannan mulkin mai cike da cakwakiya da ƙalubale kashi-kashi da shi, dan tun a yau ɗaya da fara shigarsa office ya fahimci hakan. Saboda haka bazaiyi ƙasa a gwiwa ba ko sakaci, yana buƙatar Haysam Abdul-rasheed Shehu a cikin wannan tafiyar tasa tamkar yanda ƴan ƙasa ke buƙatarsa koda basu san muhimmancin sa a garesu ba. Ƴar ƙarar buguwar agogon dake bango falon ya katse tunaninsa, numfashi ya sauke a hankali, dan ƙarar ta bugane tamkar da bugawar umarnin zuciyarsa dake ambaton (lokaci ya cika, ka fitar da takardar zartarwa kawai, rikicin da kake kallo da ƙalubalen bai fi nauyin burin nan naka ɗaya ba, cikashi tun a wannan daren masalaha ce ta zuciya da kwanciyar hankali ka, fitar Zak-Shadow daga dunkulallen makircin da aka garkame shi cikin kurkuku tsawon shekaru takwas itace zai tabbatar ma masu shirin mamayeka kai ba kurar wasansu bane, aiki kazo yi ga ƙasa da al'ummar ƙasa ba aikin aljihunansu ba). Cike da gamsuwar shawarar zuciyarsa ya sauke numfashi, cikin nutsuwa ya ɗauki wani file da takarda a cikinsa mai tambarin ofishin shugaban ƙasa (Presidential Seal). Wannan shi ne takardar ikon afuwa da zai miƙa wa Ministan Tsaro, wanda zai tafi kai tsaye zuwa hannun Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa. Duk da yasan aikin bamai sauƙi bane a garesu; dan akwai al'amuran cikin gida da ya sani zasu taso, munafukan dake da hannu akan lamarin Haysam, waɗanda ba a san ainihinsu ba har yanzu, amma yasan zasu bayyana ne da wuri akan wannan fitar ta Haysam, dan dole suna da tasiri a cikin gwamnati harda tasa kamar yanda Haysam ɗin ya faɗa. Shi kansa daya samu wannan mulkin cikin sauƙi duk da yasan komai hukuncine daga UBANGIJIN, amma sanin wacece wannan ƙasar tasu akwai tambayoyi a ransa: Su wanene ainihi? Kuma me yasa Zak-Shadow ya zama barazanar da suka ƙuduri aniyar kawar da ita? Miyasa kowa Haysam dai Haysam dai?. (Fitar tasa ce zata baka hasken samun wannan amsar) Zuciyarsa ta ayyana masa. Murmurshi ya saki mai ƙayatarwa cike da gamsuwa ya ɗauki wayarsa dake gefe. Kai tsaye number Imran yay kira.....

★A yau gaba ɗaya Imran ya kasa barin office har zuwa wannan lokacin, zaman jiran kiran mutum ɗaya tak yake, kuma bazai ƙosa da wannan jiran ba daga nan har wayewar gari in sha ALLAHU. A dai-dai wannan lokacin da Shugaban kasa ke neman layinsa yana tsaye jikin windown ofishin sa yana kallon titin da ke cike da motocin jami'an tsaro. Rabonsa da cikakken barci tun dare shekaran jiya, gaba ɗaya barci ya gushe masa a cikin idanu tun bayan samun saƙon shugaban ƙasa ta text message bayan kammala rantsuwa. Dan haka ya ƙare wannan yinin gaba ɗaya da ƙagautar jira, jiran kiran Janar da a yanzu ya shigo wayar tasa a bazata. Jikinsa har tsuma yake wajen kai hannu ya ɗaga. "Assalamu alaikum Your Excellency…" ya faɗa cikin ladabi da kuma farin ciki da bai iya ɓoyewa ba. Janar daya fahimci ƙagautar Imran a bayyane ya saki murmurshi, batare da jan rai ba ya furta "Imran, lokaci yayi. Takardar afuwa ta kammala." Ya ɗan yi shiru, irin shiru mai nauyin tasiri, kafin ya cigaba da faɗin, "Ina so ka shirya tawaga mai tsabta. Ba na son hayaniya, ba na son labari ya fito. Ka tabbatar da babu wanda idonsa ke buɗe a kanku". Da wata irin sauke ajiyar zuciya mai masifar nauyi Imran ya lumshe ido cikin jin daɗin kalmar da ya dade yana jira kamar mafarki. Muryarsa na rawa ya furta, "Za'a yi sir. Da izinin ALLAH Zak-Shadow zai fito gobe ƙarfe tara na safe." "Good. Kai nake son ka jagoranta Imran. Na san kai kaɗai zaka iya tsallake duk wata inuwa daga ƙalubalensu. Zaku wuce inda na tanada dan duba lafiyarsa da saituwar al'amarinsa. Ka tsare shi da ranki. Har sai ya koma randa zai dawo ƙasa ya zama barazana, dan Zak-Shadow nake son a gani ba firsinan shekara takwas ba". Daddy Imran ya murmusa, murmushin jarumi wanda ya dace da mai ɗauke da nauyi mai girma na tsakanin soja da dangi. Sai da ya ƙame tare da salute sannan ya furta, "Na rantse da ALLAH za'a yi fiye da umarninka Sir. Ba zan bari koda iska tai barazanar kaɗa nauyin daya rage masa ba kafin ka gan shi duniya ta ganshi zuri'armu su ganshi." "I'm proud of you, Soldier". "Thank you, Sir. I'm proud of you too"...

Daga haka suka katse kiran, amma zuciyar Imran kamar zatayi tsallen kwaɗon sojoji dan farin ciki. Sai da yay sujidar shukur sannan ya miƙe bakinsa ya kasa rufuwa dan murmushi, ji yake kamar UBANGIJI ya sauke masa wani babban nauyi daya toshe bugun zuciyarsa a tsawon shekaru. Wayar ya ɗauka ya tura sako ga ɗaya daga manyan abokan amana da zai jagoranci motar sirri zuwa prison wato Haydar Galadima (Faro)........✍️

[12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 33

..........Fuskar former First Lady ɗauke da murmushin ƙasaita take kallon Hajiya Hasiba, sai kuma ta girgiza kai da faɗin, "Hummm.. Adeel! Adeel. Yanzu kina nufin tare da shi kuka zo ƙasar nan?". "Sosai kuwa ranki ya daɗe. Dan yanzu haka ma yana masauki. Kuma abinda na sanar miki ya ambata ne ya kawo shi, wato kashe Haysam. Sai dai bamu san ta wace hanya zaibi ya tabbatar ba". "Yana da daman bin kowace hanya, dan yana da ƙarfin ikon dukiya da sunan zuri'ar gidansu. Sai dai abinda ke ban mamaki wace manufa yake da ita akan Nabeeha har haka? Dan nasan Adeel matuƙar sani, nasan al'amarinsa akan mata. Tabbas idan yana a giyar kwaɗayin tarayya da mace komai yana iya aikatawa, da zarar ya cika burinsa kuma shike nan." "Amma yana iƙirarin auren Nabeeha zai yi ai. Shiyyasa ma ya iya juriyar shekaru kusan tara kenan a kanta." Murmurshi mai haɗe da ƴar dariya First Lady tayi. "Bazan ce miki ƙarya yake kai tsaye ba Hajiya Hasiba, sai dai zan iya miki yaƙinin ba haka bane ainahin abinda ke ransa. Duk wannan iskancin da kike ganin Adeel nayi yana matuƙar tsoro da bin dokokin ahalinsa. Ba Nabeeha ba, ko ƴar shugaban ƙasar wannan ƙasar tamu zuri'arsa bazasu bari ya aura ba. Maybe da a yankin turawa ne su barshi yay hakan, dan sunfi ɗaukarsu da kima da daraja fiye da al'ummar yankin Afirika da suke amsa sunan baƙaƙen fata. Mu a wajensu bayi ne kawai, bayin da zasu musu bauta a gidaje da masana'antu, sannan bayin da zasu gusar da kishirwarsu cike da wulaƙantarwa da izgili. Ƙalilan ne a cikinsu masu mana kallon mutane, bari na miki ƙaramin misali mana, Kinga dai ance musulmi ɗan uwan musulmi ne, amma ko a saudia idan kinje ibada baki taɓa lura da yanda in kika haɗa sahun salla da mai jan kunne ke ƙoƙarin hana gangar jikinsa raɓar taki ba?". "Tabbas nasha ganin hakan ranki ya daɗe". "Good. Idan har basu so baƙin fata a sahun bautama UBANGIJIN daya tabbatar musu su da mu babu banbanci ba sai wanda yaji tsoronsa ta yaya zasu zo mu a haɗaka ta mu'amula mai girma irin wannan? Dan haka zan sake tabbatar miki ƙarya Adeel yake yana da manufa akan bibiyar Nabeeha, akwai burin da yake son cimmawa kuma bana jin na sha'awa ne". "Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kai biri yayi kama da mutum gaskiya. Bazan ɓoye miki ba kullum cikin yima kaina irin tambayar nan nake. Sai dai ganin yanda take masa rashin kunya da nuna halin ko'in kula balle nuna jin haushi kan shafe min tantama ta. Yanzu ranki ya daɗe minene mafita? Kin san mutumin nan nada ƙarfi, kota wace hanya zaibi dan cimma manufarsa a kammu". "Tabbas zai bi, dan shafe babin rayuwar ɗan adam ƙaramin aiki ne daga tarin ƙananun ayyukansa. Sannan kunyi gangancin sanar masa mijin Nabeeha na rufe ne, duk da nasan idan yaso sanin hakan zai yi koda bata hanyar ku ba. Yanzu kije gida ki bani lokaci zanyi tunani, abinda na yanke zan kiraki mu haɗu ko nazo gidan na sameki, shima kuma zan je har masaukin nashi duk da banda isasshen lokaci, saboda gobe zamuje gidan gwamnati domin ganawa da sabuwar First Lady. Kin san ɗan takarar CSP candidate ɗin Excellancy ne. Dama nayi niyyar nemoki a satin nan kizo ƙasar saboda rantsuwa da akai, sai kuma gaki ALLAH ya kawo ki ma duk da an riga an gama dai". "Ranki ya daɗe duk abinda kuke so zamuyi, ni dai a taimaka na fara maganin wannan matsalar dan samun nutsuwa". "Karki damu Hasiba. Idan ta kama Excellancy ya shiga wannan maganar zai shiga. Zan saka ya nema Adeel da kansa koya gayyato shi nan gidan idan ALLAH ya ɗaura mu akansa dan abune mai wahala yazo ɗin. Amma zamu gwada sa'ar mu". "Nagode sosai ranki ya daɗe. ALLAH ya bar zuminci. Ya tabbatar da nasarar ku daga nan har ƙarshen rayuwa". "To amin Hasiba".

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ★★..10/9/2021..★★ 🔥8:55 AM🔥

Duk da kasancewar hantsi ya ɗaga kurkukun ya yi shiru yau fiye da kowanne rana. Tun 8 aka kammala basu abincin safe kamar yanda komai yake a tsari aka saka kowa komawa ciki saboda baƙin sirri da zasu shigo. Sai irin su Dada da ba'a bari su fito sai da ƙwaƙwƙwaran dalili dan haka kai musu akeyi su har ɗakunansu. A bakin ƙofar gate 8:55am motocin sojoji ne masu duhun glass guda biyu suka tsaya kamar taurari a cikin duhun dare. A motar farko kawai aka sauke gilashi ƙasa tare da miƙama securitys ɗin ƙofar takarda. Suna duba abinda ke ciki suka ƙame jikinsu tare da salute ɗin motocin. Kafin da hanzari a wangale musu ƙofar suka shige a jere. Basu tsaya ko'ina ba sai a ƙofar sashen da Dada yake. Inda shugaban prison ɗin da kansa ke tsaye tare da jami'an soji na gidan guda uku alamar jiransu suke dama. Sai da sojojin ɗayar motar suka gama fitowa da hanzari suka zagaye wajen kafin a buɗe ta ƙarshen. Col. Imran Abbas ne a ciki, cikin farin kaya na musamman bana soja ba, sai Brig. Haydar Usman Galadima (Faro). Cikin nutsuwar girma irin na masu kamewa suka fito a hankali, a take sojojin da suke tare da su harda na cikin prison dake tare da shugaban su suka ƙame tare da sara musu. Suna ajiye hannu shugaban prison ya ƙaraso shima gabansu, ƙame jiki yay shima tare da salute nasu irin na girmamawa, suma sai suka ƙame ɗin sukai salute ɗinsa na girmamawa. Hakan na nufin kowa ya girmama girman kowanne, dan su duka ukun kowanne nada matsayin girmama ɗan uwansa a dokance. A karo na biyu sukai musabaha, kowanne fuska da murmushin mutunta juna. Kafin Colonel Imran Abbas ya miƙa takardar Presidential Pardon ga shugaban prison. Sai da ya ƙame a karo na biyu yay salute ɗin Imran sannan ya amsa takardar. Shima sai Imran ɗin ya sake salute nashi a karo na biyu idanuwansa sun yi kaifi tamkar yana hango duk wani inuwa da zata takura masa a cikin idanun shugaban prison, sai dai babu dama, babu dalilin bijirewa. A karo na farko, kai tsaye Brig. Haydar Usman Galadima ya furta, "Muna so a fito mana da Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu yanzu." Duk da shugaban prison yasan abinda ya kawosu kenan sai da numfashinsa ya tsaya cak na wucin gadi, jikinsa yay wani yamm kamar an jefasa da dusar kankara. Amma bashi da zaɓin daya wuce bin umarni na zahiri da gaskiya. Gudun kada yaransa dake zagaye da shi, da yake da tabbacin akwai idanun ɓoyayyun mutanen da suka kawosa wannan gidan suka ɗora a wannan kujerar yasa ya ɗanyi jarumtar son cizawa. Murya a takure ya furta, "Sir… zuwa yanzu babu wani…" Cikin zafi Imran daya gama fahimtarsa ya katsesa da faɗin, "Shi kawai muke buƙata a gabanmu. Wannan umarnin shugaban ƙasa ne. Ko akwai wani daga cikinku da zai ce bai san ma'anar wannan tambarin ba?". "I'm sorry, Sir!". Shugaban prison ya faɗa yana ƙara ƙamewa. Kafin ya juya yayma yaransa umarni da idanu. Duk da mamaki na neman kashe da yawansu saboda fahimtar abinda ke shirin faruwa basu da zaɓin daya wuce bin umarnin suma. Dole da sauri suka shige domin zartar da abinda aka saka su.....

★A dai-dai lokacin da suke ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin, Dada na zaune ne ya idar da sallar walha yana karatun Alqur'ani. Motsin buɗe ƙofar da shigowarsu bai saka ya dakata ba balle kallonsu. Dan haka suma suka tsaya tsamm alamar jira. Sai da ya kwashe mintina biyar cir da shigowar tasu sannan ya rufe Alkur'anin yana mai ɗagowa ya kallesu. A tare suka nuna girmamawar soja, kafin suyi gaisuwa da sanar masa umarnin da aka basu. Maimakon amsawa idanu ya lumshe a hankali, sai kuma ya kife zuwa sujuda. Minti biyu cir kafin ya ɗago. Ya ɗauki Alkur'anin sa ya maida inda yake. Sai kuma a dai-dai nan jami'ai biyu dake tare da su Imran suka shigo. Suma sunyi gaisuwar sannan suka fara tattara kayansa na buƙata masu muhimmanci. Komai baice ba, sai bin ɗakin da yay da kallo, kallo irin na bankwana da tuna abinda ya shuɗe, kafin ya juya a hankali ya nufi ƙofa jami'an farko suka take masa baya.....

A hankali ƙofar corridor ɗin ta buɗe. Sai kowa ya sake nutsuwa da zubama ƙofar ido musamman Imran, Faro, shugaban prison. Yaran sojojin uku da suka rage a wajen kawunansu a ƙasa na girmamawa. Sakan goma tsakani jarumin jarumai ya bayyana, bayyanar data saka gaba ɗaya sojojin wajen harda su Imran ƙamewa a tare suka sara masa. Sai da ya lumshe idanunsa ya buɗe a kansu, sannan shima ya dunƙule hannaye duka yana ɗan miƙasu gaba alamar amsar girmamawar su. A karo na biyu, shugaban prison, Imran, Faro suka sake ƙamewa da sarawa irin ta girma da girma. A yanzu kam shima sai ya ƙame ya sara musu su ukun murmushin mai nauyi ya bayyana a fuskarsa. Kai tsaye ya saka idanunsa cikin na Faro da shima ke murmushi, ido ɗaya Faro ya kashe masa da sake yin wani salute na abokantaka da amintaka. Dada ya girgiza kansa yana murmusawa da yima Faro alamar (bazaka taɓa canjawa ba) da idanunsa. Sai kuma ya janyesu a slowly ya maida kan Imran da ya tsaya cak kawai yana kallon sa shima. Idanusu ne suka haɗu cikin juna, shekaru takwas na ɓacin rai, rashin adalci, fushi da raɗaɗi duk suka bayyana cikin wannan idanuwa huɗun tamka a film ɗin da aka dannama pause. Zak-Shadow ya sakarma Imran murmushi cikin nauyin zuciyar da ya saba ɓoyewa. "…Imran Abbas?". Dada ya faɗa a karo na farko da wani irin salo na jini yaga jini. Imran ya saki murmurshi tare da matsawa kusa da shi gab, sai kawai ya rungumeshi. "Shagwaɓaɓɓena". Dada ya faɗa cikin kunnen Imran jin saukar hawayensa akan kafaɗarsa. Share hawayen yayi sannan ya ɗago yana murmurshi. "Alƙawarin ALLAH ya cika. Rubutacciyar ƙaddara daga littafi na gaskiya ta taƙaita. UBANGIJI ya tabbatar mana zai jarabcemu, sai dai da jarabawar nan zai ɗaga darajojinmu a sama idan mun kasance masu haƙurin cinyeta. Ƙasarka ta jira dawowarka. Zuri'a bata manta da kai ba. Rundunar soji na kwatance da sunanka. Bararka da zuwa mai son a gina gaskiya a zartar da ita koda zata ƙona kai da kai. ALLAH ya cigaba da amintar da wannan RUHIN bisa kyakkyawan gini na gaskiya. A yau zan buɗe muryar data disashe saboda kukan kewa na faɗama duniya cewar Haysam Abdul-rasheed Shehu is back again". Murmurshi Dada ya saki mai nauyi, zuciyarsa ta rikice da son fitar da abinda ke zagaye da ita na kewa tsahon shekaru, ba dan prison ba, ba don wahala ba, sai dan kalaman Imran dasuka ratsata har cikin jini da jijiya dama ƙashi. Amma da yake mazan maza ne sai suka rikiɗe da ƙarfafa kai bayyananne. Da nayin kamewa da nutsuwa ya furta, "Imran! You are my destiny. I am proud of you........✍️ [12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 34

.........."Almu na maka kiran gaggawa ne saboda ƙarin abokin aiki da zaka samu". Cikin tashin hankali maigadi ya ɗago yana kallon mutumin dake zaune cikin lallausar kujerar ƙayataccen falon. Sai kuma ya sake maida kan nasa ƙasa da sauri. Zuciyarsa na bugawa da yin rawa a cikin ƙirjinsa ya furta, "Ranka ya daɗe nawa aikin baya tafiya dai-dai ne?". Sai da mutumin yaja fin sakan uku kafin ya amsa cike da isa. "Aikin ka na tafiya dai-dai Almu, anzo gaɓar da shima wannan ɗin dole sai ya shiga gidan ne". "Shike nan ranka ya daɗe, yanda kace haka za'ai. Ni dai ALLAH ina sake roƙon arziƙi kada a cutar min da ƴar uwa. Kaima ka sani mu marayu ne, bamu da kowa a wannan duniyar sai kammu mu biyun nan rak." "Bijirema umarni na ne kawai zai iya sakawa ta cutu. Idan ka kiyaye ta kiyaye lokaci kaɗan ya rage muku ku samu freedom." "Zamuyi duk abinda kake buƙata in sha ALLAHU ranka ya daɗe. Amma dan ALLAH zan iya ganinta?". Wani banzan kallo daya saka maigadi sake nutsuwa mutumin ya watsa masa. Sai kuma yaja tsaki yana ɗaukar wayarsa dake gefe yay danne-danne. Kunnensa ya kai, sai dai a taƙaice ya furta, "Zaka iya fitowa". Daga haka ya ajiye wayar. Shiru falon ya ɗauka, sai ƙarar tv dake fita ƙasa-ƙasa dana ac. Cikin abinda bai gaza mintuna biyar ba wani ya fito. A ƙalla dai bazai wuce shekara talatin da shida ba. Shima cike da tashi izzar yay ma Almu kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Sai da ya zauna a kujera sannan wancan mutumin dake kallonsa fuska da murmurshin da tun da Almu ya shigo bai gani a fuskarsa ba. Almu ya nuna yana gyara zama. "Wannan shine mutumin da nake gaya makan. Yana aikin gadi a gidan kusan shekara huɗu ke nan, bayan mun tsige wancan ganin bazai iya mana komai ba." "Shi wannan yana yin abinda ake so kenan?". Saurayin yay magana a karo na farko. "Tabbas yana yi, dan tunda ya fara aiki babu wani kuskure da zance mara daɗi. Sunansa Almu." "Okay". Ya faɗa a taƙaice. Mutumin bai nuna ya damu ba ya cigaba da faɗin, "Zaka shirya ne ku wuce tare? Ko zaka bishi daga baya?". "Kawai mu wuce taren, ai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe. Sai dai ya kamata nasan wane aiki zan iya samu a gidan?". Yanzu kam mutumin baice komai ba, illa juyawa da yay shima ya kalla Almu. Da sauri Almu yace, "Ranka ya daɗe sai dai in munje can ɗin, amma a yanzu gaskiya a gidan nan babu wani aiki. Dama a wata biyu daya wuce ne driver ɗinsu ya samu hatsari to da an samu sai ya maye gurbinsa. Amma yanzu ma inada tunani guda, akwai mai sharar tsakar gidan kullum da bama filawoyi ruwa. Yakan zo da safe yayi ya dawo da yamma. Sunyi-sunyi ya dinga zama nan koma kwana yaƙi, acewarsa yana wasu ayyukan ne idan ya kammala da nan. To ko shi zamu tunɓuke ta hanyar maƙarƙashiya sai shi ya maye shi?". "Eh wannan ma kazo da zance mai ƙyau. Amma miyasa ban san da labarin driver ba? Bayan kuma na sanar maka ko sabuwar kaza akai a wannan gidan nasan da ita. Ko cokali ya faɗi nasan da sautin ƙarar faɗuwarsa...." "Ka gafarceni ranka ya daɗe, na nemeka amma ban samu ba, idan baka manta ba jiya daka turo min saƙon kana son ganina na tura maka amsa da dama inada wata magana. To dama maganar kenan". Maimakon amsa zancen sai cayay, "Kaje waje ka jira shi zai fito". Idanun Almu cike da ƙwalla ya jinjina kai. Yayi kamar zai miƙe sai kuma ya sake komawa ya duƙa. "Ranka ya daɗe dan ALLAH ko zan iya ganin ƴar uwata ɗin?". "No!". Ya bashi amsa a ɗan tsawace. Da sauri maigadi ya miƙe jikinsa na rawa ya fice a falon. Idanunsa kuwa tuni sun cika da ruwan hawaye. Zuciyarsa kam raɗaɗi take masa. Tabbas badan da ƴar uwarsa da mutanen nan suke amfani wajen juyashi yanda suke so ba sun san basu isa ba. Shine fa Almu, Almu na babba ƙarfe bashi ratsa jininka. Guduma mai fasa kan tantiri.... Ƙwafa yayi yana mai cije laɓɓansa, daga haka ya samu waje a bakin baranda ya zauna......

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

A gidan Mammah rashin barcin wuri saboda murnar dawowar Uncle Bilal yasa yau kusan kowa sai da ya makara. Gasu Nimrah zasu je makaranta tunda an koma hutu. Ganin yanda lokaci yaja suka so lanjarewa akan bazasu je ba, gashi yau monday fa. Amma Uncle Ammar ya buɗe musu wuta dole suka shirya suna faman ɗaga baki. Uncle Bilal dake biye musu kuwa suna fitowa ya fara lallashinsu, ƙarshe yace shine ma zai kaisu school ɗin da kansa. A take bakunansu suka washe da farin ciki, dan suna matuƙar ƙaunar Uncle Bilal. Breakfast ɗinsu aka shirya musu a lunch box Mammah tace suci a mota. Sun fito Mu'azz na tsokanarsu wai sun zama su Abees ƴan Nursery, Uncle Bilal ne yace karsu kulashi, dan haka harara kawai suka zuba masa suka shige mota. Tunda suka ɗauki hanyar school suna karyawa suna ma Uncle Bilal hira, duk da kuwa jiya babu kalar labarin da bai sha ba da ƙyar suka barshi ya kwanta. Su Aheel ya fara saukewa a tasu school ɗin, su Rukyn suka taimaka masa ya raka su har ajinsu yay magana da class masters ɗinsu. Dan Aheel da Abees ajinsu ɗaya. Afrah da Ayyan ma haka. Basu ɓata lokaci ba suka fito suka koma mota. Suma har aji Uncle Bilal ya raka su, sunyi sa'a Teacher Khalil ne a ciki. Ya gaisa da Uncle Bilal cikin mutunci kasancewar sun san juna. Sannan ya bada hakuri akan makarar ƴaƴan Mammah. Fuskar Teacher Khalil da murmurshi ya ce, "Ba komai Uncle ai yau da gobe sai ALLAH. Sai nazo gida cin tsarabar turai." Ƙaramar dariya Bilal yayi da faɗin, "Sai kazo ina nan ina jiran ka." daga haka yayma su Nimrah bye ya wuce. Ƴan ajin kam da yawansu sun ƙyasa, yo sunga handsome masha ALLAH. Cike da neman magana Nimrah taja tsaki da taɓe baki tana magana cikin ƙunƙuni. "Mudai kar a cinye mana uba, naga mayu sunyi yawa a ajin nan haba irin wannan kallo haka kamar sabbin kwartaye". Dariya Ruky ta sanya, sai kuma tai saurin toshe baki saboda tunawa akwai Teacher Khalil a ciki. Kuma sarai yaji mi Nimrah ɗin ta faɗa da dariyar Rukyn. Dan kai tsaye ya juyo daga rubutun da yake akan allo. Sai dai baiyi magana ba, suma duk sun wayance sun ɗauka books kamar basu suka aikata ba. Yayinda mafi yawan ƴan ajin suka shaƙa da baƙar maganar Nimrah, sai dai sun san ba damar maida murtani Zakanya da Damisa su daki banza. Hibba dai tunda taci duka a wajensu take neman shishshige musu ayi ƙawance. Amma wulaƙanci irin na Ruky da Nimrah sai yarfata suke.....

★★★

"Wai Mammah ko duk farin cikin dawowar Bilal ne. Tunda na shigo gidan nan na fahimci farin cikin ki a bayyane yake". Murmurshi Mammah ta sake yi tana kallon Aunty Ummi mai maganar, ganin suma su Shariffa da su Mimi sun zuba mata ido sai ta sake sakin murmurshin da faɗin, "Inaga dawowar Bilal ɗin ce, dan yau kam wani farin ciki mai girma da ni kaina na gagara misaltashi ne zagaye da zuciyata. Dan haka na saka su Kulu suyi abinci mai yawa a fitar sadaka." Addu'a suka shiga jero mata da fatan ALLAH ya ƙara mata farin ciki da nisan kwana masu albarka. Ta amsa musu da amin tana shafa kan Mimi data kama hannunta ta sumbata. Dai-dai nan Bilal daya dawo daga kai su Nimrah school ya shigo falon. Ture Aunty Mommy abokiyar karawar tasa yay daga kusa da Mammah ya zauna yana faɗin, "Mi ake tattaunawa auntys." Aunty Mommy dake harararsa ta ce, "Anƙi a faɗa ɗin. Kawai dan neman faɗa kazo ka wani ture ni, da kama samu nazo ganinka tuzuru kawai". Cikin dariya Bilal dake amsar Babyn Aunty Mimi a hannun Aunty Lailah ya ce, "Humm kwantar da hankalinki yarinyar nan, kwanan nan kalmar nan ta tuzuru zaki bar faɗarta ne." Cike da zumuɗi Aunty Mimi ta taso ta dawo kusa da shi. "Dan ALLAH da gaske Yaya Bilalu? Dan ALLAH guntsa min wacece?". "Uwar gulma kenan". Cewar Bilal. Dariya gaba ɗaya suka sanya. Aunty Shariffa ta ce, "Wlhy dama nasan sai ka faɗa haka. Dan ALLAH a bamu musha Yaya Bilal. Dama gidan shiru kwana biyu babu shagali dan ma mun ɗan rage da sunan Baby Nawal ne". "Aunty Shariffa karki damu, lokaci ne zaku sani, amma shagalin biki sai Dada na nan in sha ALLAHU". A take falon yay tsitt, Dan shima yayi maganar ne muryarsa na ɗan rawa. Mammah ce tai gyaran murya, dan tasan yanzu zasu fara mata koke-koke. Cikin canja hirar ta ce, "Mudai yanzu tashi ka ɗakko mana tsarabar mu nan duk ita mukai zaman jira". Cikin dariya Bilal ya ce, "Kai Mammah harda ke? To kowa yay haƙuri baza'a buɗe tsarabar nan ba sai yarana sun dawo school gaskiya. Dan sune zasu buɗe ta". "Yau muna ganin jalala, har sai su kafi auta sun dawo za'a bamu tsarabar?". Yanda Aunty Lailah tai maganar yasa kowa fashewa da dariya........✍️

[12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 35

.......... ★PRISON★

9:30am dai-dai motocin sojojin biyu suka fice daga cikin prison ɗin cikin tsaro mai cikakken sirri, yayin da hukuncin UBANGIJI da ƙarfin ikonsa suka tabbata a daidai wannan lokacin wani razani ya gitta a zukatan wasu mutane daga ɓangaren Ƙungiyar duhu, a ƙasan rayukansu suka dinga jin cewa abu mafi hatsari ya faru. Sai dai daga ina? Daga wane yanki? Akan mi? A dalilin mi? Duk UBANGIJI ya toshe wannan amsoshin daga garesu, koda ata hanyar yaransu dake cikin prison ɗin babu wani labari da suka samu saboda gargaɗin shugaban ƙasa......

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull