Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 15

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 15

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 15: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 15. ★A ɓangaren su CSP Alpha shugaban prison bayan fitar motocin su Imran biyu…

4,429 words

★A ɓangaren su CSP Alpha shugaban prison bayan fitar motocin su Imran biyu sai wajen ya sake nutsuwa takar an ɗora dutse a zukatansu, ga iskar da suke shaƙa ji suke kamar ta rikice da wani irin nauyin da babu mai iya fassara shi. CSP Alpha bai iya ya motsa daga tsayen da yake ba har bayan an kulle ƙofar gate ɗin. Jikinsa ya ƙara sanyi, numfashinsa na fita a cure, zuciyarsa ta kumbura cikin ƙirjinsa. Jin tamkar hajijiya na neman zubar da shi babu shiri ya jingina da bango kaɗan, hannunsa na riƙe da takardar Presidential Pardon da yake jinta da uban nauyin da yafi na takarda a hannunsa, ta koma mata tamkar nauyin dutse ne. Dai-dai nan wani sojan da ke tare da shi ya matsa kaɗan yana son yin magana, amma CSP Alpha ya kaɗa masa ido cikin gargaɗin tsoro da rashin tabbas.... "Ka tafi! Ku tafi ku duka…!" Muryarsa ta fita da ɗan kauri cike da bada umarni irin na manya. Kai tsaye sojojin suka bar wajen, sai dai zukatansu nata tsalle-tsalle, tsallen da suka tabbatar da in ya wuce zuciya yace zai zo kan harshe zasuyi nadama ne ta har abadan. Dan haka kowa ya ajiye abinda yaji ya kuma gani anan dan wata shirun tafi alkairi. Musamman ma daya kasance an musu gargaɗi na haƙiƙa dan tamkar an zaɓesu ne akan al'amarin... Sai a lokacin shima CSP Alpha ya tuna da maganar da shugaban ƙasa janar Yusuf ya yi masa kwanaki biyu da suka gabata a cikin waya… "Ka kiyaye sirri fiye da kiyaye rayuwarka. Idan ka yi kuskure, ba zan iya kare ka daga hukumar tsaro ko daga mutanen dake a waje suna jiran Zak-Shadow ba. Kuma wlhy duk wanda ya san wannan al'amari kafin lokacin da ya dace, to kai kanka ka yi masa jagora zuwa lahirarsa". Wannan kalamai ne da har cikin jinin CSP Alpha suke da tasiri mai saka razani da ƙaulanin zuciya har yanzu. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, goshinsa ya cika da zufa. Hannu ya kai ya sharce gumin, kafin ya furta da ƙasa-ƙasa kamar mai roƙon iska. "Ya ALLAH an sakani a tsakiya?. Wane irin mutum ne wannan Zak-Shadow ɗin da shugaban ƙasa ya zo kan al'amarinsa haka da gaggawa?". Bashi da amsa, babu kuma mai bashi ita a yanzu. Dan haka bai yiwa kansa dogon tambaya ba ya haƙura. Tsoron da yake ji game da maƙudan mutanen da ke bayan fage ya fi ƙarfin neman amsoshin tambayoyin nan dake danƙare a zuciyarsa.......

<<<%>>><★><<<%>>>

Tunda suka baro cikin prison ɗin shiru ya ratsa motar, sai sautin AC da numfashin su dake fita iyakar motsin ƙirazansu. Baradan jaruman haziƙan sojojin uku Imran, Faro, Zak-Shadow. Ba wanda ya ce komai. Kowa da abin da yake tattaunawa da zuciyarsa. Sai rufaffen gilashin motar da ke nuna hasken rana daya fara zafi, launin duhun sa ya bayyana fuskokinsu dake da sanyin annuri. Daddy Imran yana kallon Dada akai-akai tamkar idan ya ɗauke idanun nasa zai ɓace masa ne, ko yana son tabbatarwa wannan ba mafarki ba ne. Faro dai sai murmushi yake yi irin wanda yake nuni da cewa (Na gaya maku wataran ƙaddara da ƙarfin ikon wanda ya fiku iko zai dawo da shi a duniyar ku). Amma shi Dada ya rufe idanunsa cikin nutsuwa, yana fitar da numfashi a hankali da shaƙar mai tsabta fiye da duk wanda ya shaƙa a cikin shekaru takwas. Yawan jin idanu a kansa dan in har ana kallonsa sai yaji a jikinsa, balle wannan kallon yana jin ƙarfin idanun mai su a cikin ƙirjinsa. Ya kuma tabbatar da Imran ne ke da wannan tasirin. A hankali ya buɗe idanuwan nasa, sai ko suka sauka kai tsaye akan Imran ɗin da yay hasashe. Hararasa ya ɗanyi, tare da ɗage masa gira ɗaya, da murya ƙasa-ƙasa amma cikin zurfi ya furta, "Kallon fa?". Ƙaramar dariya Imran yayi da faɗin, "Ina tsoron karka sake ɓace min ne". Kauda fuska Dada yay kaɗan da sakin ƙaramin murmushi, batare daya tanka batun Imran ɗin ba ya sake jeho masa sabuwar tambaya. "Motar nan ina take son kai mu?" Daddy Imran ya ɗan taɓe baki da matsawa kaɗan ya jingina da kujera. Shima cikin salon raɗa ya ce, "Wurin da ba wanda zai same ka. Wurin da babu ƙungiya, babu siyasa, babu duhu. Wurin da zaka samu iska ta ƴanci bayan shekara takwas daka rasa". Dada ya girgiza kai a hankali tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda. "Na gode muku Imran, Faro, na gode sosai." Kafin Imran yace wani abu Faro ya katse su cikin siririyar dariya mai armashi da jin daɗi. "Zaki wlhy idan ka sake irin wannan sakon godiyar, zan fara tunanin da gaske zaka canja halinka." Dada ya kalle shi yana murmushin ƙasaita sai kuma ya maida kansa ya kwantar a jikin kujera ya lumshe idanunsa har lokacin da murmushi a kan fuskarsa. Sai a lokacin ya furta, "Ga shi kai baka da ranar canzawar da wannan sa idon naka". Dariya Imran da Faro suka sanya, cikin irin dariyar da ta bayyana ƙyallin ruwan hawaye daga idanun Imran da ya kasa ɓoyewa.... Dada dake murmushi zuciyarsa ta tafi sabon tunani. (Shugaban ƙasa da kansa ya yanke wannan hukuncin da gaggawa? Mi yasa? Mi ya faru da ƙasata cikin wannan lokacin? Mi ake shirin bani? Mi ake buƙata daga gare ni?). Kafin ya samo amsoshin waɗan nan tambayoyi masu nauyi Imran ya katse shi da faɗin, "Muna da tsaro mai ƙarfi, babu wanda zai kusance ka har sai ka shirya. Koda likitoci sun gama duba ka zaka cigaba da zama a ɓoye. Babu wani abu da zai kusanto ka. Sai mun kammala gyara rashin adalcin da aka yi mana, dan ƙasa tana buƙatar komawar ka a Zak-Shadow ɗin data sani ne. Mammah zatafi farin ciki idan ta ganka a Haysam ɗinta itama. Balle kuma ƴaƴan Dada". Dada ya ɗan furzar da numfashi da buɗe idanunsa dake a rufe, zuciyarsa cike da wani nauyin da bai gama wargajewa ba. Tabbas a yanzu ba wanda ya fi buƙatar son fara gani kamar Mammah da ƙannensa, amma zai daure ya jure dan yasan duk yawan kwanakin da suke so yayi anan bazasu kai yawan wanda yayi a baya ba. Shima zai fi son Mammah ta gansa cikin ƙyaƙyƙyawan kamanni ba wannan kamannin da yake a yanzu ba da zasu iya raunana zuciyarta har ta gagara mantawa da su. Numfashi ya sauke a hankali, a yanayinsa na Zak-Shadow da suka sani ya furta, "Imran kun tabbatar babu wanda ya san dawowa ta?". "Ai ko motar nan ta bari wasu suka ji Zak-Shadow ya dawo, ta riga ta mutu." Imran ya ƙare maganar yana dariya mai taushi. Faro ma hannu ya ɗaga yana dariya da faɗin, "Duniya zata san dawowar ka ne lokacin da ka yanke hukunci, ba lokacin da kowa yake jin yanada ƴancin faɗar abinda ya gani ba koda Imran da Faro da shugaban ƙasa ne." "ALLAH ya shiryeku, yau kuma kun zama ƴan comedy". Cewar Dada yana ɗaukar takardar dake gefensa. Yanzun ma dariya suka sanya, dan har ƙarƙashin zukatansu suke jin wannan nishaɗin mara misali. Shi kansa Dada yana jin fiye da nasu, kawai dai ya fisu kamewa ne, sannan halayyar su dama can ba ɗaya bace, su sunada faran-faran da magana, sabanin shi da ko wasa bai iya ba, dama dai da Imran ne wani lokacin idan ya matsa masa, sai shima Faro ɗin idan ya gallabesa wasu lokutan yakan maida musu murtani.....

⭐ 10:43am dai-dai Motocin biyu suka isa secret medical base wuri na musamman mai tsafta, nutsuwa, da ƙa'ida. A yanda gurin yake a killace zaka ɗauka Shugaban ƙasa yasa an tsara shi ne tamkar dan ɓoye Dada ɗin ne anan. Dan tuni har likitoci suna jiran su, likitoci kam na musamman ne aka tanada dan duba lafiyarsa, saboda duk ƙarfin halin da Dada ke nunawa su sun san abu na farko da yake buƙata shine duba lafiyar tasa. Sun masa tarba ta girmamawa suma, dan duk da halin da yake ciki kwarjinin yawan ibada da UBANGIJI ya bashi yana nan a tare da shi sai ma ƙaruwa da yayi da sake ɗaga darajarsa ga duk mai kallonsa. Shi ɗin DODO ne a kowane irin yanayi, dan haka a nutse yake bin komai da aka shirya da nazari irin na masu nutsuwa: Kayan aiki, ma'aikata, da tsaro mai ƙarfi. Sai da Idanunsa suka gama tantance kowanne daga cikinsu, kamar yadda yake nazarin duk wanda zai shiga cikin binciken sa. Imran dake lure da shi ya saki murmurshi ya juya kansa zuwa ga Faro. "Faro, ka tabbata babu wanda zai san dawowar sa." Faro daya fahimci saƙon da Imran ke son isarwa ya ɗaga hannu tare da kashe masa ido ɗaya ya ce, "Babu wanda zai sani, har sai lokacin da Zak-Shadow ya yanke hukunci." "Kayi ƙyan kai Faro. Lokaci zai bayyana komai da kansa. Duk wanda ya ga fitowarsa ba a shirye ba kuwa zai zama...." Imran yay alamar mutuwa. Su suke maganar, amma Dada nazartar likiticin daya tabbatar su su Imran kema wannan zaurancen yake. Ganin yanda suka duƙar da kawuna yasa shi fahimtar suna fahimtar komai suma. Baiyi magana ba yay gaba kai kace yasan wajen ne. Da sauri likiticin suka zabura dan masa jagora, Imran da Faro suka sake kallon juna da murmurshi, sai suma sukabi bayansu..........✍️ [12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 36

........Ciwon kai sosai ya gallabi Nimrah a makaranta saboda raunin kanta da bai gama warkewa ba. Babu shiri wajen sha biyu aka maidata gida bayan an kaita clinic ɗin cikin makaranta sun dubata. Ba ƙaramin tashi hankalin su Mammah da su Aunty Ummi dake gidan yayi ba. Dan duk ciwon da zakaga ya kwantar da Nimrah haka ba ƙaramin jinsa take ba. Ga jikinta zafi zau da zazzaɓi. Mammah ɗakinta ta Kaita ta kwantar bayan kowa ya gama jera mata sannu da addu'a. Da kanta ta zame mata uniform ɗin jikinta ta barta da vest da shot kawai, ita ta goge mata jiki da ruwan sanyi tasa aunty Mimi ta ɗakko mata riga mara nauyi a ɗakinsu. Aunty Shariffa ta kawo mata kunun madara, da ƙyar aka lallaɓata tasha tana hawaye dan ji take kamar kan zai rabe mata biyu, kaɗan tasha kunun tasha magani Mammah ta kwantar da ita tana tofa mata addu'a har barci ya ɗauketa......

<<<<<★★★★>>>>>

"Sir na bincika kamar yanda kace. Gidan nan gidan wani soja ne, akwai mahaifiyarsa a ciki da ƙanensa, amma shi yana ɗaure shekaru takwas kenan. Ita kuma yarinyar ban sani ba ko ƙanwarsa ce ko ƴa gaskiya. Dan ban samu wani cikakken bayani a kanta ba, a dai gidan take, kuma ƴar gidan ce". Gaba ɗaya ma'aikacin hotel ɗin yayima Adeel bayanin ne da harshen turanci, dan da shi suke magana kasancewar shi baya jin yarensa shima baya ji, amma dukansu sunyi tarayya akan yaren turanci. Ajiyar zuciya Adeel dake saurarensa ya shiga saukewa. Dan tun marecan jiya da yaga Nimrah bai sake jin cikkiyar nutsuwa ba a zuciyarsa. Yau ɗin nan yana da zama da tsohon shugaban ƙasa, amma bai iya yaje ba saboda ba waccan damuwar bace yanzu gabansa ta yarinyar da ko sunanta bai sani ba ce. Hatta su Nabeeha bai sake bi takansu ba. Ko wanda yasa yana bibiyarsu da yazo da safen nan masa bayani kamar yanda ya bashi umarni cayay yaje kawai yana buƙatar hutu. Da turancin ya ce, "Miye sunanta?". "Nimrah!". Sai da ya wani lumshe manyan fararen idanunsa ya buɗe sannan ya saki murmurshi. Dan kuwa sunan ya dace da ita. Dan a cikin sakannin da suka haɗu ya tabbatar da ita ɗin zakayyarce, zuciyarsa ta shiga wassafo masa ɗan mitsitsin bakinta na tsiwa mai ɗauke da kyawawan lips pink da baƙi. Yanda ta zazzaro masa dara-daran idanunta farare tas masu suffar ƙwai da masa gargaɗin kada ya taɓata da yaren da bai gane komai ba. Ya saki ƴar dariya da sake hango idanunta da suka watsa masa harara. Galala ma'aikacin hotel ɗin yay hana kallonsa, dan lallai ya yarda wannan guy ɗin ya faɗa da yawa. Koda yake baiga laifinsa ba. Dan yaran fa sun haɗu, su duka biyun wanke hannu ka taɓa ne. Daga gani kasan ƴan hutu ne kuma ƴan gata ƴaƴan manyan ƙasa. Duk da basu wani gama cika manyan ƴammata ba ko a haka za'aje da su, damma a cikin hijjab suke ba komai nasu ake gani ba face fuskoki..... "Ka samo number wayan ta?". Adeel ya katse masa tunani. Kansa ya girgiza da faɗin, "A'a Sir, bayan waɗan nan bayanan babu abinda na samu gaskiya. Dan gidan nan ba ƙaramin gida bane da samun information ɗinsu zai mun sauƙi. Wannan ma sa'a akaci na ga wanda na sani a street ɗin, shima kuma bai wani jima da kama haya ba." "Good kaje ka zomin da shi". Kai ya jinjina masa a ransa yana mamakin irin wannan haukacewa haka daga ganin yarinya? To amma ina ruwansa, aikin kuɗi yake yi, ya tabbatar kuma idan Adeel ya samu abinda yake so shima zai ja kaya. Dan Vvip ɗin da ya kama kawai ya isa ya sanar dakai mugu-mugun mai kuɗi ne shi. Balle manyan agogo da designers kayansa zuwa takalmi, kai wayar hannunsa kanta kai kasan lallai akwai manda. Dan zai iya rantsuwar bai taɓa ganin irinta ba balle kamfanin da ake yinta. (😜Ƙaryar marubutan ta motsa anan. Ya kuka iya🤣 ku karanta kawai🥱. Amma in gaskiya za'abi ai akwai masu kuɗin nan dai ko🥱😎). Hannu Adeel ya ɗaga masa, ya ɗan risina na girmamawa sannan ya fice.....

>>>>>>>%<<<<<<<

Yau ta kasance juma'a ce, sakamakon ciwon da Nimrah ta kwanta na kwana biyu bataje Makarantar boko ba, dan tun ranar Monday da suka dawo da ita gida da kansu bata sake zuwa ba. Sai su Ruky da su Abees kawai. Mu'azz da Biebah ma duk suna gida. Dama Biebah ce mai fitar. Kasancewar ciwon kai data kwana da shi cikin dare tana ta wayyo-wayyo Mammah ta maidota ɗakinta. A gado ɗaya suka kwana tana mata addu'a har barci ya ɗauketa gab da asuba. Lokacin salla Mammah bata tasheta ba, sai da gari yay haske dan ta rage nauyin idon da ciwon kan. Aiko da ƙyar ta nutsu tai sallar saboda barci, ta sake komawa gado ta kwanta. Dan haka Mammah tace bazataje school ba yau ɗin ma. Barci tasha sosai dan sai kusan 12 ta farka. Alhamdullahi babu ciwon kan gaba ɗaya, barcin ma ya wadace ta sai rashin ƙarfin jiki. Sai da ta gyaro gadon Mammah fes sannan ta koma ɗakinsu tai wanka. Doguwar riga mara nauyi ƙirar Dubai mai ƙaramin hannu ta saka, ta yafa ƙaramin mayafi ta fito. Samun Mammah da Daddy Imran a falon ya sakata jin daɗi sosai. Ta gaishesu cike da girmamawa. Duk suka amsa mata da kulawa Daddy Imran na tambayarta yaya kan nata? Dan Mammah ta masa bayani. Sai da ta ɗan ɓata fuska ta amsa da, "Daddy da sauƙi, amma sai na rama duk randa na koma Islamiyya, kusan sati fa kenan banda lafiya". Idanu Imran ya ɗan waro waje, sai kuma cike da lallashi ya ce, "A'a karma naji an fara wannan aiki, abinda ya faru ai ƙaddara ce da tsautsayi. Tunda ba wata rigima ta haɗa ku ba. A dinga haƙuri ALLAH yana tare da masu haƙuri". "Amma Daddy ai zalunci yasa suka kashe magunan. Ni dama ba nawa zan rama ba magen da yaranta zan ramawa". "Karki damu UBANGIJI zai rama musu Daughter. Ke kuma ALLAH zai baki ladan kariyar da kika basu." Kanta ya jinjina masa. Mammah dake saurarensu tana murmushi ta ce, "Tashi ki nema abinci kici. Sai kisha maganinki". Amsawa tai tana miƙewa zuwa kitchen, inda take jiyo hirar Aunty Biebah da su Kulu masu aiki.....

★A dai-dai wannan lokacin kuwa acan gate Sayyadi Kamal ke shigowa gidan bayan yayi knocking gate ɗin maigadi ko muce malam Buba sabon driver dake zaune a gate ɗin ya buɗe masa. Da farko tambaya ya jefa masa batare da ya barsa ya shigo ba. "Lafiya kuwa? Wanene kai?". Kai tsaye Sayyadi ya amsa da "Sunana Kamal. Malamin islamiyyar su Naja'atu Muhammad ne. Na kawo mata saƙo ne". Shiru Malam Buba yay yana kallonsa kafin ya maida idonsa kan kwalin dake hannunsa mage na leƙowa ta shagar da akayi don shan iska. Ba komai ke masa kai-kawo ba sai sunan Nimrah dana Muhammad da aka laƙaba a gaba maimakon sunan mahaifinta. Hakan na nufin an canja mata sunan mahaifi ko ita ta canja da kanta?. Shi dai Muhammad ba sunansa bane, ba kuma sunan uban da ya haifesa bane. Idan ma zai iya kallon sunan a matsayin dangantaka sai dai yace na surukinsa ne mahaifin Hassatu idan bai manta ba. A kuma doka ta addini ai haramun ne yin amfani da wani suna ga ƴaƴa matsayin mahaifi idan bana mahaifin ba ko.... "Baba ko akwai matsala ne?". Sayyadi Kamal ya katse masa tunanin daya fara zurfi a ciki. Ajiyar zuciya ya sauke ta dawowa a hayyaci, sai kuma ya matsa baya yana ɗan murmurshi da faɗin, "A'a yaro shigo daga ciki". Abinda Kamal ke buƙata kenan, dan haka babu jayayya yabi bayan nasa suka shiga. Farar kujerar dake ajiye guda biyu ya nuna masa guda. Kusan a tare suka kai zaune Kamal na rungume da kwalin nan dai kamar ya ɗakko ɗa. Sai da suka sake gaisawa malam Buba ya jeho masa tambaya yana ɗan murmushi. "Mage a kwali baka tsoron ta kufce?". Murmurshi Kamal yayi da faɗin, "Baba shiyyasa ai na ɗaure da igiya, dan kufcewar magen nan ba ƙaramar matsala bace a wajena. Na tabbatar Naja'atu bazata sake kallona ba". Dariya Malam Buba yay a karo na farko, cike da zolaya irin ta manya ya ce, "To kodai ba malamin bane kawai akwai wata a ƙasa. Kaga gara mu sani dan kaga ɗalibar taka ƴar gida na ce, sai na saka hannu wajen maka campaign nima". Kamal na ƴar dariya da shafa kai ya ce, "To kusan haka baba, amma ai da sauran lokaci tunda nasan baza'a mata aure yanzu ba nima kuma haka". "Kai! A wannan shekarun naka?". "Baba tsahon ƙafa ne kawai, amma ba wasu shekaru bane dan ashirin da biyar ne kacal". "To ai sune dai-dai auren ɗana. Mutum ya more yanda yake so ba auren bariki ba sai an gama tsofewa a ɗakin soro. Mu kaga iyayenmu sun mana gata a sha tara ma suka mana auren". "Baba sha tara fa?". "Sosai. Ba gashi mun mora auren yanda ya kamata ba. Itama kuma ai in a ƙauye ne yanzu ta isa haihuwa ma ta biyu ko ya yaye na farko tana da cikin na biyu. Shekara sha biyar fa tana cikin ta sha shida koba haka ba?".. "Tabbas haka ne Baba". "To ka gani, ai karka wani damu kanka, ka fara yaɗa manufa kawai muma zamu tayaka". "To baba ALLAH ya tabbatar mana da alkairi". "Yawwa haka nake so naji ka faɗa". Cewar Malam Buba yana miƙewa. Ya cigaba da faɗin, "Kaga jirani bara na kirata, dan naga kwana biyu ma bata zuwa makaranta sunce bata da lafiya. Kwana kusan biyar kenan taji ciwo a islamiyyar su ne..." Cike da jimami Kalam ya amsa masa da, "Haka ne Baba, wlhy a islamiyya ne fa....." Ya kwashe labari tsaff ya sanar masa. Malam Buba dake saurarensa cike da nazari yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa. Dan kuwa tabbas yau ya samu hanya mai sauƙi da yake nema da fata. Tabbas Kamal shine zai kasance makamin amfaninsa akan cimma burinsa kan Nimrah. Labarin nan kuwa yay masa matuƙar daɗi da ɗaukar hankalinsa. Tuni ya nufi cikin gida kiran Nimrah.........✍️

[12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 37

.........Imran ya miƙe kenan zai wuce Malam Buba yay sallama. Amsa masa suka yi shi da Mammah, kafin Mammah ta bashi izinin shigowa. Koda wasa bai kalla sashen da Imran yake ba, dan haka kawai yake jin tsarguwa idan Imran ɗin na kallonsa. Daga bakin ƙofar ya rissina ya gaishesu, sannan ya isar da saƙon Nimrah tayi baƙo. Cike da mamaki a tare Mammah da Imran suka furta, "Baƙo kuma?". Har yanda sukai ɗin ya bama Malam Buba mamaki. Amma sai ya shanye mamakin nasa yay ƙarin bayani da, "Yace malamin su ne na islamiyya, mage ce ya kawo mata, yace kuma itace da kanta ta buƙaci haka." Mammah tasan labarin mage, dan har Nimrah a kwanakin tana mitar batun kawota da malaminsu baiyi ba. Kusan yanzu ma take jiyosu daga kitchen Nimrah na batun da tasan number sayyadinsu data kira a wayar Biebah ta tuna masa batun magenta. Sunan Nimrah ɗin ta kira, ta amsa tana fitowa daga kitchen ɗin hannunta da kofin tea, ganin sabon driver ɗin su da ko sunansa bata riƙe ba har yanzu ya sata ɗan tsayawa turus, sai kuma ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ƙaraso wajen Mammah. Hannu Mammah tasa ta amshi kofin shayin hannun nata tana faɗin, "Saka hijjab kije ga malamin ku yazo kawo miki magen taki". Washewa fuskar Nimrah tayi da murmushi, cike da farin ciki ta ce, "To Mammah. Ta ɗauki hijjab a inda suke ajiyewa ta saka. Malam Buba na gaba tana biye, haka kawai ta samu kanta da zubawa bayansa ido duk da zuciyarta dake bugawa. Imran na daga ciki sallama yay ma Mammah ya fito dan kiran Faro nata shigo masa a waya, yasan kuma zai iya yiwuwa Dada ne, shi kuma baya son ɗagawa a gaban Mammah dan ko a fuska bai nuna mata fitowar Dadan ba. Dai-dai Nimrah na kaiwa gate, cikin ɗan risinawa ta gaida Sayyadi Kamal daya zuba mata ido. Ita kam kanta a ƙasa batama san yana yi ba. Idanu sosai Imran ya zubama Kamal ɗin daga inda yake tsaye cike da nazari, yayinda shi kuma hankalin Malam Buba yake kan Imran a kaikaice shima yana nazarin kallon da yake ma Kamal ɗin. Nimrah kam bata ɓata lokaci ba ta miƙa hannu amsar kwalin magen. Kamal na murmushi da kallonta ya miƙa mata tare da miƙewa, kaɗan ya matsota yana magana ƙasa-ƙasa. Nimrah ta yamutsa fuska da ɗan jan jikinta baya, yayinda fara'ar fuskarta ke raguwa alamar maganar daya gaya mata ce batai mata ba. Dan kamar wadda take a ƙage ma yana sakar mata kwalin ta baro wajen tana masa sallama da tafiya duk a lokaci guda. A haka ta ƙaraso inda Imran yake tsaye yana kallon Kamal dai dake binta da kallo.. "Daddy kaga mage na". Nimrah ta faɗa dai-dai tana isowa gabansa, murmushi ya saki yana ciro hannunsa daga aljihu ya amshi kwalin cike da kulawa. Da kansa ya kwance ɗaurin zaren da akaima kwalin yasa hannu ya ciro kyakkyawar magen fara tas ƴar ƙarama. "Masha ALLAH Babyn daughter ta iso gida lafiya. ALLAH ya rayata ta haifa mana yara da yawa duk a raba mana". "Amin Daddy". Nimrah ta faɗa cike da farin ciki. Maida mata ita yay a kwalin. "To ya sunanta?". "Uhmm Daddy sai Ruky ta dawo zamu saka mata suna". "Oh na manta, Ussaina bata yanke hukunci sai Hassanarta na nan. Bari na wuce idan an saka sunan maji a waya". Nimrah na dariya ta ce, "Daddy ALLAH ya tsare hanya. Ka gaida Ammie da su Aunty Ma'u gobe zamuzo daga nan muje gaida Grandpa tunda Grandma taƙi dawowa daga ƙauye. Sai mu wuce mu gaida Ummu da Grandpa suma ko". "Tunani mai ƙyau Daughter, ALLAH ya kaimu. Amma ki kwantar da hankalinki ma su Asma'u suna hanyar zuwa nan gaida Mammah suma." Wani irin farin ciki ya sake kamata. Tai ciki tana murna da faɗin zataje tai ƙwaɓa fulawa nayin ɗanwake da kalallaɓa". Fuskarsa da murmurshi ya bita da kallo harta shige. Kasa riƙe abinda yake ayyanawa a zuciyarsa yayi sai da ya ambata, "My Zaki ɗiyata ta zama macen nan da kake tunanin za'a jima bata kai ba, Abu na farko kenan da zai fara baka mamaki idan ka taka ƙafarka a gidan nan". Sai kuma ya sake sakin murmushi yana girgiza kai saboda hasaso cakwakiyar dake gaba. Har yanzu Nimrah bata san akwai aure a kanta ba, shiyyasa suke kaffa-kaffa da al'amarinta ko nan da can ba'a barinsu zuwa su kaɗai sai da driver ko Mu'azz.. dai-dai yana isowa wajen motarsa, kallon da yaron nan da akace malaminsu ne ya faɗo masa a rai. Juyawa yay ya kalli gate ɗin, sai yaga sabon drivern nan daya sakama alamar tambaya ne kawai a wajen yaron baya nan alamar ya wuce. Lallai dolene yay saurin tsaida wannan alaƙar, dan ya lura akwai wani abu mai girma a idanun yaron game da Nimrah. Mota ya buɗe ya shiga, bayan an buɗe masa gate ya fice yana mai kallon agogon motar dan yana son daga massalaci ya ziyarci Janar ne su tattauna batun ƙarasowar Zak-Shadow gida tunda likitoci sunce bawani damuwa, sai dai sakamakon gwaji ɗaya da ake jira kawai yau ya fito suji......

>>>>>>%<<<<<<

Bayan sakkowa massalacin juma'a gidan Mammah ya kacame da hayaniya. Tuni su Ruky sun dawo gida, ga yaran gidan Uncle Nasiru da matarsa Hajiya Zuwairah da kowa ke kira (Ummu). Yaya Imam, Aunty Halimatu, sai ƙawa aminiyar su Ruky Bintu, da autoci Sadiq da Adam. Hakama daga gidan Daddy Imran akwai Babban Yaya Haysam da suke kira Khalifa, sai Asma'u dake bimasa suna kiranta Aunty Ma'u, Ruƙayya ke bima Asma'u, sai Auta Marwan suna kiransa (Lolo). Yaran Aunty Ummi huɗu suma sun iso, Firdausi itace ke bima Mu'azz, itama sa'anni suke da su Nimrah, sauran uku duk maza ne. Abdul-rasheed suna kiransa Dady, sai Harun, da auta Saddam. Sai na Aunty Mimi itama uku. Ita kam duk maza ne da ita jinjirarta ce kawai nace a yanzu, Fu'ad, Salman, Ishaq. Sai na Aunty Momy huɗu itama. Maza biyu mata biyu. Kasancewar mazan sune manya matan sai suka kasance ƙanen su Nimrah. Itama tana da Na'eem, dan sunan surukinta yaci suke kiransa Na'eem, sai Sauban. Matan Nusaiba, da Khairat. Tunda aka kammala kaya-kayar cin abinci kowa yaja sa'anninsa suka dasa hirarsu. Halimatu da Asma'u suna tare da Aunty Biebah duk da dai ta girmesu, sai dai da yake suma sun gama cika ƴammata sunfi su o'e ƙwailoli iyayen kankanba da rashin ji nustuwa😂. Sai Imam, Mu'azz, Khalifa suma suna ɗakin Mu'azz abinsu matasan samari kenan ƴan shiga jami'ar bana. Suma sauran na ƙasan kowa yaja tashi da irar sai ƙananun sosai su Afrah dake manne da Mammah da Ummu. Ƙawayen juna masu ji da tashen farkon balaga ma dai suna can sun kulle kansu a ɗaki ana cafta. Nimrah, Ruky, Bintu, Feedo. Kai da kaji yanda suke hirar kasan basa ɗaukar kansu fa ƙwailoli sai manyan ƴammata. Dan Feedo ke basu labarin saurayi da tai cousin ɗinsu daya dawo daga karatu Saudiyya shine fa aka baje kolinsu cike da iyayi ana cafkewa......

++++++++++++++

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull