Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 16

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 16

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 16: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 16. Da ƙyar abokin ma'aikacin hotel ɗin nan ya yarda ya biyoshi kiran Adeel,…

4,182 words

Da ƙyar abokin ma'aikacin hotel ɗin nan ya yarda ya biyoshi kiran Adeel, sai da yazo yaga kuma mai kiran nashi duk ya rikice. Dan duk da bai san waye Adeel ɗin ba a zahiri abubuwan dake zagaye da shi ya tabbatar masa wani shegen duniya ne. Cike da gadara kuwa Adeel ya ajiye masa rafofin kuɗi masu kauri yana sanar masa buƙatarsa akan gidan da yake zaune yake son ya bashi wajen zama a ciki. Sannan ya masa bayani akan gidan su Nimrah. Gaye yaga kuɗi duk ya gigice, yo dala wasa ce. Jiki na rawa ya tabbatar masa da ya amince yazo su zauna. Batun gidan su Nimrah kuwa yace shi ba komai ya sani game da su ba gaskiya, amma yana gaisawa jefi-jefi da wani yaron gidan da safe idan ya fito zaije jugging shima zai je. Fuska a ɗan yamutse Adeel ya ce, "Ba damuwa wannan alaƙar ɗin ta wadatar. Zamu iya wucewa gidan naka yanzu, dan bana son ɓata lokaci. Miye sunan ka?". Da ɗan rawar baki yana kallon abokinsa ma'aikacin hotel ɗin ya ce, "Yohana!". "Okay yayi, zamu iya tafiya". Duk da zuciyarsa na rawa haka ya amince, dan shi da abokin nasa ma suka ɗauki ƙaramin traveling bag ɗin Adeel ɗin daya kasance ƙaramin troly ne zuwa harabar hotel ɗin. Sai dai yabar wasu ɗan abubuwan sa a ɗakin hotel ɗin dan haka da card ɗin buɗe ƙofar ma ya wuce. Kusan ƙarfe takwas suka iso anguwar, ko'ina da haske fes ga anguwar shiru babu hayaniya sai securitys kawai dake kai kawo. Ta gaban gidan su Nimrah suka wuce. Sai Adeel yaji kamar ya sauka anan ya shiga ya ganta. Sai dai babu dama. Tsakanin gidan Yohan da gidan su Nimrah bai wuce gidan huɗu ba. Kuma su suna ɗayan hannun ne ta yanda daga gidajen su Yohan ɗin ma kana iya ganin gate ɗin su Nimrah tsaf musamman idan kana upstairs ne. Can ma gate aka buɗe musu suka shiga, da yake wani ɗan ƙaramin estate ne yake, mai ɗauke da apartment da basu wuce goma ba gaba ɗaya.........✍️ [12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 38

.........."Tofa, gyaran gidan nan aka sake yi haka Aunty Nabeeha?". Ɗago kai Nabeeha da hankalinta ke kan wayarta tai ta kalla gidan a karo na farko. Ba ƙaramin ƙyau gidan yayi ba kam dan tun daga waje zaka shaida hakan, flowers ɗin da suka ƙawata katangar gidan ta wajen kawai abin kallo ne, ƙamshinsu ya cika wajen sosai kuma. Balle baƙin gate ɗin. Ajiyar zuciya Nabeeha ta saki a hankali batare da tace komai ba. Ismat da Raihana kuwa suka cigaba da santin su har Malam Buba ya leƙo sakamakon horn da Ismat ɗin tayi dan itace ke jan motar. Malam Buba bai sansu ba, dan haka ya fito sosai yana tambayar "Su waye ku?". Sai da duk sukai masa kallon sama da ƙasa, a yamutse Amima uwar rashin kunya ta ce, "Matar gidan ce da ƙanen ta". "Kiyi haƙuri Hajiya kumin bayani yanda zan gane, ni baƙone anan, dan dole zan fara sanar da masu gidan kafin na barku ku shiga". Sai a lokacin Nabeeha da taja tsaki ta kallesa a wulaƙance. "Kai sha-sha-sha ka buɗe mana gate mu wuce. Shi gidan ya zama na shugaban ƙasa ne yanzu da ba'a shigarsa sai da doka komi?". "Ba haka bane Hajiya, ina kan aiki na ne". A fusace Amima ta buɗe ƙofa ya fito, hakan kuma yay dai-dai da isowar taxi wajen. Ba kowa bane a ciki sai ainahin maigadi da baƙonsa. Malam Buba ya maida hankalinsa kansa yana ɗan murmurshi da faɗin, "Alhamdulillahi Malam Almu sannu da zuwa?". "Yauwa Malam Buba, mun sameku lafiya? Ya na ganka a waje haka kai da su way...." Ya haɗiye sauran maganar saboda ganin Amima. "A'a Hajiya ashe kune, sannunku da zuwa. Malam Buba buɗe musu ƙofa ai ƴan gida ne". Amsa masa Malam Buba yay yana juyawa, Amima kuwa taja tsaki tana komawa cikin motar dan ta fito ne da shirin wanke fuskar mutumin nan da mari. Sai da motar tasu ta shige Malam Almu ya kalli abokin tafiyarsa da ya ce, "Su kuma su wanene su?". Cikin ɗan sauke ajiyar numfashi Malam Almu ya amsa masa da, "Matar Baban yayansu ɗin nan da nake gaya maka sunce yana ƙasar waje ce, sauran ƙanenta ne. Ba zama take a gidan ba sai lokaci-lokaci take zuwa tana iskance-iskancenta. Nama fi shekara uku banga ta sake zuwa ba sai yau". Kai kawai ya jinjina masa batare da yace komai ba, daga haka suka shige ciki suma. Malam Buba nata jera musu sannu, ya kawo musu ruwa sannan ya zauna suka gaisa yana tambayar mai jiki. Malam Almu ya ce, "Da sauƙi sosai, ɗan uwana dake Niger yazo ya tafi da ita can a nema mata magani, shiyyasa ƙanina ma ya biyo ni nan dan kar a barshi shi kaɗai. Sunansa Sanda". "Kai masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Malam Sanda sannu da zuwa kaji". Yay maganar yana bama Sanda hannu suyi musabaha. Hannun shima Sanda ya bashi suka gaisa.. Dai-dai nan Rayhana ta ƙaraso wajen cike da tsawa da gadara ta ce, "Kai wani yaje can sashen ya amso mana key ɗin ɓangaren mu". Su duka kallonta sukayi, Malam Buba zai yi magana Malam Almu ya katsesa da faɗin, "Hajiya ai ɓangaren nan babu komai a cikinsa tunda aka kammala aikin gidan nan. Ina ga zaifi ƙyautuwa ku shiga wajen hajiyar da kanku dan tana nan. Ko ta fita ne Malam Buba?". Yanda yay maganar ƙarshe yana kallon Malam Buba da sigar tambaya ya sashi amsa masa da, "A'a tana nan bata fita ko ina ba. Dan yau ma gidan cike yake da baƙi kamar jikokin gidan ne duk suka zo. Sai dai naga matan su Ja'afar sun fita su kam". "To kinji Hajiya, ku shiga kawai zai fi". Harara Rayhana ta zuba musu su duka, batare da tace komai ba ta juya ta koma inda su Nabeeha ke tsaye a ƙofar sashen nata suna jiranta. Abinda ta sanar musu ya saka Nabeeha jan tsaki. Cike da takaici ta ce, "Nifa ban son iyayi, to ina suka kaima mutane kayansu?". "Muje dai wajen Mammah ɗin sai muji kamar zaifi". Ismat ta faɗa tana binsu da kallo....

★Gaba ɗaya falon ya cika da hayaniyar su Aheel dake wasan guje-guje, sunma falon kaca-kaca da tarkacensu. Amma hakan bai hana Mammah dake zaune yin hirarsu ita da Ummu (Hajiya Zuwairah matar Uncle Nasiru) hirarsu ba. Sun juyama ƙofa baya, hakan yasa har su Nabeeha suka shigo falon basu sani ba. Babu tabbacin sunyi sallama ko a'a, sai wani kallon yaran suke a yamutse kamar sunga wasu abin ƙyama. Yaran da suma shigowarsu bai hanasu wasan su ba duk da wasu sun gansu wasu basu lura da su ba, Abees dake bin Ishaq da bindiga da aka zuba ruwa ciki yana fesa masa suka iso inda suke. Ishaq ya shige tsakkiyarsu yana ɓoyema Abees suna dariya, shiko Abees ya cigaba da fesa ruwa har a jikinsu. Cikin wani irin takaici Rayhana ta kwaɗe Abees da marin daya saka yaron sakin gigitacciyar ƙarar data saka su Mammah juyowa da sauri. Dai-dai Nabeeha ta finciko Ishaq dake bayanta ta hankaɗashi kan Abees itama. Wannan al'amari na mari da hankaɗewa yayi dai-dai ne da fitowar Nimrah daga lungun ɗakinsu ɗauke da magenta zata haɗo mata madara. Magen ta dire saman stairscase tayo wajen ranta a ɓace. Miƙewa Mammah da Ummu duk sukai suna kallonsu, haka sauran yaran tuni sunyi tsit kamar anyi ruwa an ɗauke. Sai khairat ce mai ɗan wayo ta ƙaraso inda su Abees suke da sauri. Isowar Khairat dai-dai da ƙarasowar Nimrah da babu ma wanda ya lura da ita a kaf falon sai yanzu. Kafin Mammah data buɗe baki zatai mata magana tayi kawai sukaji saukar mari mai ƙara a fuskar Rayhana, ba kuma kowa yayi mata shi ba sai Nimrah. Kafin ma Rayhana ta dawo cikin hayyacinta ta watsama su Amima da suka wani yunƙuro kanta a fusace manyan idanunta. Babu tsoro babu shakka duk da sun fita girman jiki da tsayi, dan ma itama ɗin dai doguwar ce, amma kasancewar sun girmeta nesa ba kusa ba sun fita tsayin. Amma tsabar bushewar idanu ko'a jikinta. Sai ma cike da gargaɗi da kaushin murya ta ce, "Oh zaku rama mata ne?". Cikin matsanancin baƙin ciki Amima ta ce, "Ai ba rama mata mari kawai ba duka zaki ci". "To bari kema na baki rabonki sai ku rama mata ɗin". A bazata ta sake sauke wani marin a fuskar Amima. Rayhana ta yunƙuro zata cakumeta tasa ƙafa ta taɗeta sai gata a ƙasa wanwar. Ai ko yaran suka saka ihun dariya suna tafi da tsalle da faɗin, "Aunty Ninah! Aunty Ninah!". Inda suke yanzu kam Mammah ta iso, dan Nabeeha ma ta yunƙuro kan Nimrah zata cakumota, sai dai Nimrah ta riƙe hannun nata tana mata kallo mai cike da rashin kunya da tsiwa. Yayinda Amima ta cakumi rigar Nimrah ɗin ta baya, Ismat da hankalinta ya tashi dan ita bata fatan ayi wani abu mara ƙyau ita dake fatan samun fada ta shiga janye Amima tana faɗin, "Wai miye haka dan ALLAH." "Nimrah! Sake ta". Mammah data iso wajen ta faɗa idonta akan Nimrah. Tashin hankali, duk fa wannan abu dake faruwa su Nabeeha basu gane Nimrah ba, haka ma Nimrah bata gane su ba, dan sanin datai musu na ƙuruciya ne, zuwan da sukeyi jefi-jefi kuwa basu taɓa haɗuwa ba tana makaranta, idan ma sun kwana kasancewar randa suka shigo kawai suke zuwa gaida Mammah harsu wuce bata ganinsu. Suma kuma rabonsu da ita tun tana ƙaramar, tsabar yanda suka tsaneta basu taɓa sha'awar idan sun zo gidan su ganta ba musamman Nabeeha. Sai gashi a yau yarinyar da suka sani mitsila ta zama budurwa, ga hasashen ƙyawu da sukama yarinyar a baya ya tabbata. Dan kuwa Nimrah akwai dogon hanci da ɗan bakinta dai-dai ita, ga manyan idanu farare tas da suka ƙawata baƙar doguwar fuskarta mai cike da tsiwa da rashin tsoro. A tsaye yarinya ce doguwa, duk da ƙirjinta ba wani cike yake taf na wuce misali ba komai dai ya bayyana na yammatanci, dan doguwar rigar jikinta ta fitar da komai, tun daga tudunsu har zuwa shafaffen cikinta da kugunta mai faɗi kaɗan dake tabbatar da nan gaba shekaru suka ƙaru zai sake buɗewa sosai, dan ko a yanzu ka kalleta kasan akwaisu har sunfi na Amima da Ismat ɗin ma dake kusan 27years a duniya. Baƙar fatarta kuwa sai wani sheƙi take da ɗaukar idanun mai kallonta, da gani kasan zatai laushi da sulɓi dan babu ɗigon ƙurji balle tabonsa a fuskata. Kanta ba ɗankwali, hakan ya bayyana gashinta mai yawa duk da kitsone a kanta shiku yama ɗan tsufa. Maganar da Mammah tai ya sakata sakin Hannun Nabeeha datai sumar tsaye, dan ambaton sunan Nimrah da Mammah tayi sai da taji kamar an kwaɗa mata guduma a saman kai ne, ta wani kafe yarinyar da ido ko ƙyaftawa batayi. Hatta su Ismat sunyi wani irin kasare suna kallon Nimrah, dan harta doke hannun Amima data riƙe mata riga ta baya da alama itama tayi sumar tsaye ne. Dan da gaske fa ƴar yarinyar da bata kai ko sha shida ba ta fisu jikin mata, sai dai su nuna mata shekaru kawai da farar fata. To zama a iya jera masu farin nasu gaban maza ɗari su tsallakesu su zaɓi Nimrah ɗin dake baƙa, dan mazan sun gama zige mata da kalmar fara ko mayyace duk sunbi sun kwaile jikinsu yanzu sun dawo baƙaƙen suke kwashewa sukai gidan aure. (Yo ko mijinki kika biyema da kankare can, tada can, ALLAH sai kin gama wahala da kashe kuɗin da ɗorama kanki ciwuka ƙarshe ya auro wadda bata kaiki komai ba ya sota ya tiritata🤣. Kai mata ku dawo habkalinku, babu biyayya ga abokin halitta akan saɓon UBANGIJI. Wanda ya halicceki ya fiki sanin abinda ya dace dake. Kici abinci mai ƙyau da nagarta kiga yanda zakiyi ƙyau, ba shafe-shafe man gyaran fata da ƙarin haske, ko saka gashi da farce, kankare gira shan supplement na ƙarin baya da gaba, ƙarin girar ido kankare haƙori ke saka mace ƙyau ba. Kiyi ibada, kici abinci mai ƙyau, ki kwantar da hankalinki kiga ƙyau hajjaju, wlhy kyau na asali UBANGIJI kawai ke bada shi ba shirme da sabon ALLAH ba. A duk sanda kika damu da yin ƙyau dan burge mutanen duniya sune zasu taru su zageki da tsine miki kafin zuwa gaban UBANGIJI da kika saɓamawa kika nuna bai iya ba sai ke ƴar iya😏🙄).........✍️

[12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 39

........Mammah data fahimci halin da suka shiga da yanda suke kallon Nimrah ɗin sai ta ɗan murmusa, batare da ta sake magana akan abinda ya farun ba ta kama hannun Nimrah tana barin wajen da faɗin, "Bismillah ku ƙaraso ku zauna". Sai da suka kalla juna, kafin su bi bayanta jiki a saɓule. Karasowar su falon dai-dai Nimrah da Mammah ke miƙama ruwa alamar tasha na faɗin, "Mammah su waye su?". "Sha ruwa". Mammah ta faɗa batare data bata amsa ba. Sai da ta tura baki gaba sannan ta amshi ruwan tasha. Ismat dake fatan al'amarin ya tsaya iya haka ta zamo a kujera tana gaishe da Mammah da Ummu da taƙi cewa komai sai mamakin ma ganinsu Ismat ɗin daya cika zuciyarta. Saboda tuna kusan wata ɗaya kenan da kiran Jiddah da sukai akan an hanasu baro Dubai. Da mamaki Nabeeha da su Amima ke kallon Ismat, itako ta fuske dan tasan abinda tai shine dai-dai. Mi Nabeeha ɗin ta gani oho mata, itama sai ta daure ta gaida Mammah kaɗai banda Ummu. Mammah ta amsa mata da kulawa tamkar komai bai faru ba, harda tambayarsu mahaifiyarsu. Nabeeha ta ce, "Tana lafiya. Mammah dama zamu amshi key ne". Ɗan murmushi Mammah tayi da kallon Nabeeha da ƙyau. Ta ƙara ƙyau sosai da ƙiba alamar tana cikin kwanciyar hankali da ƙoshin lafiya. Cike da dattako ta bata amsa da, "Aiko akwai matsala Nabeeha, dan sashen nan naku babu komai a ciki. Tunda za'ai gyara aka fidda komai, abubuwanku masu muhimmanci ne kawai aka bari suna cikin nan sashen ma, amma funichars duk an bada su kuma ba'akai ga zuba wasu ba ganin ba kowa ke zama ba kar aita asara". "Amma Mammah da an gaya min kafin a kwashe ɗin, musamman kayan bedroom ɗina dana kitchen dan duk ina buƙatarsu. Gashi na ajiye abubuwa masu muhimmanci da sirrina ne da ya dace ace ni da kaina na ɗaga su a wajen ba wani ba". Zuwa yanzu Nimrah ta fahimci wacece a gabata, wato matar Dada data taɓa yankata a cinya, har yanzu tabon na nan kuma. Yanda takema Mammah magana cike da rashin taunawa da girmamawa, yasa zuciyar Nimrah sake zuwa wuya. Hakama Biebah da duk suka fito zuwa yanzu ranta a ɓace ta ƙaraso wajen. Sai dai da ido Mammah tai musu gargaɗi su duka akan kada suce komai. Dan kusan lokaci guda Nimrah da Biebah ɗin suka yunƙuro zasu bata amsa. Babu yanda zasuyi, dan Mammah tafi ƙarfin basu umarni su tsallake. A karo na farko Ummu tai magana tana kallon su Nabeeha ɗin. "Amma wannan maganar taki babu tarbiyya a ciki, dan ko Adda A'isha bata haifa miki Haysam ba matsayin ƙanwar mahaifinku take Nabeeha. Kayan da kike magana basu suka taɓa miki ba ai Jiddah ce tai komai da ƴan uwanki su Halimatu". Rai ɓace Nabeeha ke kallon Ummu, sai dai kafin ta fara maganar da take tattarowa a zuciyarta Ja'afar da suke shigowa shi da Yaya Ma'aruff, Bilal da Ammar ya katseta. "Ummu daina ɓata lokacinki wajen yi mata bayani. Ke Nabeeha kike ko wa? Tashi ki tattara waɗanan tarkacen ku wuce anan." Wani mugun kallo Nabeeha ta zuba masa. Ya ɗage gira sama cike da rashin mutunci. Tasan waye Ja'afar dan karonsu babu daɗi. Shi da Ma'aruff shegen zuciya ne da su mai zafi fiye data Dada, kawai dai su suna da barkwanci ne da hira ba kamar shi da baida yawan magana ba. Sannan shi akan jima ba'aga fushinsa ba saboda ya iya shanyewa... "Malama kina kallona ko akwai magana ne? Nace ku tashi ku bar mana gida.." "Ni kuma twiny na ƙara mata da gargaɗi na ƙarshe. Kada na sake ganinki a wannan gidan namu, dan baki da sauran hurumin zamansa sai in har Dada ne ya dawo yace ki dawo da kansa. Yanda kika saka ƙafa kika fita da kanki, ki cigaba da zama acan bama buƙatarki a cikinmu. Idan kuma taurin kai yasa kika cigaba da zuwa kina nunama mahaifiyarmu rashin tarbiyyarki, wlhy Ninah da Ruky kaɗai zamu barki da su sai sun saitaki a layi". Ma'aruff ya ƙare maganar yana nuna mata Nimrah da Ruƙayyan. Aiko ƴar wulaƙancin suka wani tuntsure da dariya Nimrah na faɗin, "Yess Uncle, wlhy ni kaɗai na ishesu su duka ma koba Buddy na. Idan mutum shi ɗan daba ne mai yankan mutane da wuƙa, ni Zakanyar Mammah ce mai kai manyan namun dawa ƙasa harma da ƙananu. Darje baki nake cikin ƙasa, na cikashi da ƙasar taf ta yanda zai iya yima manya magana". Ihu Ruky da Bintu da Fiddo suka saka cike da ƙarin haushi suna faɗin, "Naja bomb! Naja bomb! Sai dake Zakanya, Trouble Queen". "Mai bombing ɗin ƙananun tantirai ba". Nimrah ta basu amsa cike da salon iyayi tana wani juya manyan idanunta. Yanzu kam dariya harda su Yaya Ja'afar ɗin, Mammah ta kai mata rankwashi. Tashi tai da gudu tana dariya taje bayan Aunty Biebah ta maƙale. Ummu dake murmushi itama ta ce, "ALLAH ya shirya ku yaran nan. Nimrah dai kin zama Gang leader? Ga mabiya nan irinki kin tara yayunku kuma na ɗaure muku ƙugu. Bari Abban Jiddah yazo aure zance ai muku". "Aure Ummu?". Suka faɗa a tare suna waro idanu. Asma'u dake dariya tace, "Wlhy Ummu da kin taimake mu, dan yaran nan jinsu suke kamar muma sun girmemu ma". Amshewa Halimatu tai da, "Ashe angunan zasu sha shirme da rashin kunya". Cike da shagwaɓa suka kalla su Uncle Ma'aruff a tare sukace, "Uncles kun gansu ko? Ai dama sun saka mana ido". "Ku barsu sune za'aima aure ba kuba". Cewar Bilal yana kallon Asma'u ƙasa-ƙasa. Cike da farin ciki suka dawo inda yake suna ma su Asma'u gwalo. Su Nabeeha sun fahimci fa an ma manta da su a falon gaba ɗaya, yayinda Ismat ta shagala a kallon Ja'afar idanunta cike da ƙwalla. Shi ko ko kallon inda take ma baiyi ba. Bare ma da taga su Aheel sunzo inda suke sai taji wani kishi ya cika mata ƙirji, tana jin inama itace ta haifi su Aheel ɗin.....

_____________★

Tunda Adeel ya dawo gidan Yohan baida aiki sai zaman balcony dake facing gate ɗin su Nimrah. Ga alaƙa ta ƙullu tsakaninsa da Ammar a dalilin fita morning jugging. Dan a washe gari saka Yohan yay suka jira har Ammar ya fito a gida, kasancewar sun saba gaisawa normal Ammar ya bama Yohan hannu suka gaisa, sannan ya bama Adeel shima. Daga haka suka fara abinda ya fito da su, suna gudu kaɗan-kaɗan Yohan ke gabatar da Adeel ga Ammar matsayin abokinsa. Hannu biyu Ammar ya amshesa, haka sukaje suka dawo tare, su suka shiga gida shima ya wuce. Tun daga ranar kuma sai hakan ta cigaba da faruwa, kamar wasa bayan kwana biyu suka haɗu a massalacin anguwar nan ma, tun Ammar baya wani sakin jiki da Adeel bayan gaisuwa harya fara suna ɗan yin hira kaɗan-kaɗan.

Yau ma kamar yanda ya saba yana a balcony ɗin tsaye, gaba ɗaya kuma hankalinsa akan gate ɗin gidan yake. Kunensa da headphone mai shegen ƙyau, sai dai babu tabbacin waƙa yake ji ko wani abun daban. Ganin an buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ya sa ya ƙara nutsuwa da maida hankalinsa da ƙyau, cikin wata irin bazatar mamaki Nabeeha dake fitowa ta bayyana cikin idanunsa. Da sauri ya cire headphone ɗin daga kunnensa dan tsabar mamaki, ya ciro wayarsa ya shiga camara. Zooming ɗinta yay ta ciki dan gani yake kamar idanunsa ne ke faɗa masa hauka. Itace ɗin kuwa idanunsa ba ƙarya sukai masa ba, dan dai-dai nan Ismat ta fito itama tana waige-waige alamar nemanta take. Ganinta a gefe ta dafe kai da hannu ya sata ƙarasawa inda take da sauri, sai dai baya jin mi take ce mata har aka wangale gate ɗin duka mota ta fito. Dai-dai inda su Nabeeha suke Rayhana tai parking, buɗe motar da fitowar da sukai ita da Amima suma suka nufi su Nabeehan ya sake cire masa tantama. Sai ma ya rasa abin cewa shi kam. Yana anan tsaye tamkar wani gunki Yohan daya fito ya kai dubansa inda yake kallo, bai san su waye matan ba, dan haka ya juyo ya kallesa tare da faɗin, "Sir ka sansu ne?". Shiru kamar Adeel bazai tanka ba sai kuma ya ce, "Ba saninsu bane mai muhimmanci, sanin alaƙarsu da wannan gidan. Zaka iya bincika min". "Mizai hana nayi hakan". "Yanzu yanzu fa. Ko zaka kira abokinka ne Ammar?". "Kodai kayi haƙuri zuwa anjima, kuma ba Ammar ya kamata a tambaya ba dan kar ya zargi wani abun tunda mun samu ya fara sakin jiki damu." Ji Adeel yay kamar yace bai yarda ba, amma sai ya daure dan baya son Yohan yaga zalamarsa a fili da yawa, har ya kawo masa raini dan har yanzu bai san shi ɗin waye ba. Kuma baya son ya sani har ya gama abinda ya kawo shi ya bar ƙasar nan. Duk da yau da safe yaga saƙon Ummu ɗinsa ta Email akan tana son ganinsa da gaggawa, ya tabbatar koma miye take nemansa a kansa ba na wasa bane. Kuma dole ya amsa wannan kiran dan baya tsallake maganar iyayensa..... Bai sake magana ba sai ma barin wajen da yayi ya koma kan kujerar da take a balcony ɗin ya zauna zuciyarsa fal abubuwa. Dan gaba ɗaya yarinyar can ta rikita masa lissafi ko zancen abinda ya kawo shi ƙasar nan bai sake waiwaye ba. Kai su kansu su Hajiya Hasiba ɗin tunda suka iso bai bi takansu ba, sai ma da yaga Nabeeha yanzu ya tuna da al'amarinsu...........✍️ [12/25/2025, 8:54 AM] Ummul Adnan: 40

.........Gaba ɗaya ran Hajiya Hasiba a dagule yake. Koda su Nabeeha suka koma gida da nasu ɓacin ran sun sameta tana faman kai-kawo a falo. Aunty Mamawo zaune itama ta rabga tagumi. Ismat ce kawai tai ƙarfin halin tambayar su ko lafiya? Amima da Rayhana kam da ƙorafin abinda ya faru suka fara. Nabeeha dai ranta a ɓace yake, dan haka bata tankama kowa ba ta wuce upstairs abinta. Dan a wannan gaɓar ta gama yarda dole ta nemawa kanta mafita. Mafitar kuma ɗaya ce jal shine komawa gidan su Haysam. Dan a can ne kawai zata samu damar maganin wannan shegiyar mayyar yarinyar da ganinta ya gama birkita mata dukkan lissafinta, sannan ta samu mafakar gujema Adeel da bata san manufarsa ta biyosu ƙasar nan ba. Tsakanin Aunty Mamawo da Hajiya Hasiba babu wanda ya kula tambayar Ismat, sai ma umarnin su wuce ciki da Mamawo ta basu. Hakan ya sake tabbatar musu babu lafiya. Wucewar sukai, dan sun san halinta da masifarta bata musu ta wasa. Shiyyasa ma suka fi son Hajiya Hasiba dan tafita sauƙin kai. Koda suka hauro saman ma kowa inda yafi masa ya nufa, dan kowa da abinda ke ransa da zuciyarsa. Ismat dai a wannan gaɓar ta gama yanke shawarar komawa gidan mahaifinsu. Dan tayi alƙawarin bazata sake komawa Dubai zama ba sai inda ziyara itama tare da mijinta Yaya Ja'afar in sha ALLAHU. Dan a wannan karon yaƙi zatai ɗan gaske babu gudu babu ja da baya. Ta share ƙananun hawayen da suka cika mata ido, wani irin wutar sonsa na sake ruruwa mata a zuciya, saboda ganinsa ba ƙaramin tayar mata hankali yayi ba. Ya ƙara ƙyau da cikar jiki da buɗewa irin ta magidantan dake samun dukkan gata a wajen iyalansu. Tunda yay auren nan bata yarda taga matarsa ba saboda bata buƙatar hakan, amma a yau tana jin kwaɗayin ganin Shariffa ɗin duk da ta santa dama can. Akwatin kayan da tazo dasu daga Dubai ta buɗe, kasancewar ƙaton gaske ne dama kuma ta haɗo komai nata mai muhimmanci daga can sai ta sake tattare na nan gidan ma ta loda a ciki, ganin ya cika da yawa ta sake ɗaukar wani ƙarami ta zuba sauran abinda ya rage ta rufesu. Bakin gado takai zaune ta ɗauki wayarta ta fara kiran Aunty Jiddah. Gidanta take son fara zuwa, dan tai mata rakkiya gidan Abban. Da mamaki Aunty Jiddah data ɗaga wayar ta ce, "Yaushe ke kuma a gari haka?". "Aunty mun jima da zuwa. Kina gida ne dan ALLAH?". "A'a ina gidan Aunty Fateema, zata aurar da ƴarta Aminatu muna shirye-shirye dan za'a fara gobe idan ALLAH ya kaimu." "ALLAH ya sanya alkairi, yaushe zaki koma?". "Amin ya rabbi. Lafiya kuwa?". "Aunty zan zo ne, ni dai yaushe zaki koma?". "Ki tafi kawai ai yara na nan, Shafa'atu ƙanwarsa ma na gidan tazo weekend". "Okay tom. Ki gaida Aunty Fateeman, in sha ALLAHU dani za'ai kamun gobe". Daga haka ta yanke wayar tabar Jiddah da mamakinta....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull