Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 17

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 17

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 17: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 17. ★ Anan falo kam bayan wucewarsu Aunty Mamawo ta furzar da iska mai zafi…

4,473 words

★ Anan falo kam bayan wucewarsu Aunty Mamawo ta furzar da iska mai zafi tana kallon Hajiya Hasiba. Ta ce, "Aunty tunani ko damuwa bazata kaimu ko ina ba. Kawai muje wajen wani mutimina, shima yana ƙoƙari ya iya aiki, da rafanai yake aiki na tabbata zai mana nasa ƙoƙari kafin muje India ɗin. Dan dole gaskiya muyi wani motsi a wannan gaɓar, dan ina ji a jikina shirun Adeel bazai zama alkairi ba". "Kina ganin zamu samu mafita kuma?". "Tabbas Aunty, dan na yarda da aikin Malam Ƙolo sosai". "To shike nan muje ai kawai mi zamu jira. Dan mutumin nan na tabbatar shima yana can ya bazama hanyar samun damar ganin Haysam, dan gaskiyarki kam shirunsa bazai zama alkairi ba." "Wlhy ni wannan bai dameni ba Aunty, idan ma ya saka an kashe shi matsalarsu ce. Miye amfanin wani Haysam a rayuwar Nabeeha, banda soyayyar wahala da take masa ma. Garama ya kashesa ta samu wanda ya fisa koda ace zata bar Adeel ne, idan ma babu wata illar da ita First lady ɗin ta ambata ba shike nan ba. Dan ni ban yarda ma da matar ba kin san dai mutane da baƙar hassadar tsiya a wannan zamanin. Kowa yafi son ace shi shine kai kana ƙasanshi kana masa bauta bare ma manyan ƙasar nan". "Nima irin wannan tunanin naki na zomin a rai. Musamman dana fahimci ba tayi wani serious bane kan batun sai ma zancen ƙulla auren da suke sonyi tsakanin ƴar su da ɗan shugaban kasa. Duk da yaron ya nuna ba sonta yake ba sun nace." "Kinji ba! Ai halin ɗan Adam sai shi wlhy." Da wannan zantukan suka fice a gidan batare da sunma yaran nasu sallama ba. Sai fitar motarsu sukaji a gidan. Da wannan damar Ismat tai amfani ta fito itama tabar gidan da kaya niƙi-niƙi. Sai dai maigadi ta saka ya tare mata taxi a waje bata ɗauki motar kowa ba. Dan dama dai Mamansu da Aunty Mamawo da Nabeeha keda mota kawai a gida. Su basu da ita......

================

Anan gidan Mammah bayan tafiyar su Nabeeha Malam Almu ya kawo ƙaninsa ciki dan su gaishe da Mammah su mata barka da dawowa. Da fara'a kuwa ta tarbe su. Tare da amsa musu gaisuwa da kulawa tana tambayar Malam Almu mai jiki. Kamar yanda yay ma malam Buba bayani itama haka yay mata duk su Yaya Ma'aruff na jinsa. Ya kuma nuna ƙaninsa Sanda ya musu bayani a kansa da aiki da ya fito nema idan ya samu. Sai dai bai nuna anan gidan ba kamar yanda suka shirya. Cikin sa'a kuwa Mammah ta ce, "To ai bai kamata yay nesa da kai ba ko Malam Almu. Sai a bincika anan idan da wani aikin sai ya dinga yi, kaga sai kuyi zamanku ka samu abokin hirar dare tunda shi driver ba kwana yake ba yana tafiya gida da yamma". "Nagode Hajiya Mama, ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Sanda kayi godiya mana". Godiyar Sanda ya fara shima kamar yanda yaga malam Almu nayi, suka juya suna sake godiya gasu Yaya Ma'aruff suma. Sai da Mammah tace ya isa sannan sukai shiru. Daga haka ta ɗan yima Sanda tambayoyi yana bata amsa. Kai ta dinga jininawa cike da nazarin al'amarinsa, kafin ta sallamesu su koma bakin aikinsu...

Suna fita Yaya Ammar ya ce, "Mammah wai baƙya jin tsoron ɗauke-ɗauken nan kada wataran mu ɗauki abinda zai dame mu. Yanzu fa akan al'amarin Dada kowa zai iya shigowa jikinmu dan ya cutar damu. Shiyyasa kikaga ma Yaya Imran kullum yana kaffa-kaffa". "Hummm Ammar kenan, banda abinka bawa na iya gujema ƙaddararsa daman? Duk abinda kaga ya faru hukuncine na UBANGIJI. Jarabawa ba tawaya bace. Ba kuma faɗuwa bace ga bayi, sau tari kankarewar zunubi ce ko tsanin nasara daga wata ɗaukaka da UBANGIJI zai kai bawa kanta. Kar ku damu da makircin masu makirci, idan duk wanda ke zagaye da kai mugune mai fuska biyu, in har ka tsaida gaskiya, kai ka zauna da shi da kyakkyawar zuciya bisa umarnin ALLAH, wlhy ko shine ibilis akan sheɗanci da mugunta sai dai yayi ya barka. Dan shi bai isa canja komai daga ƙaddararka ba koda murmushi fuskarka ne, sai dai yayta wahalar banza da ɓata lokacinsa akan ka amma ko badaɗe ko ba jima saika cimma wannan nasarar. Ƙilama UBANGIJI yay masa tsahon ran da zai koma neman taimakon ka. Kudai kuyi addu'a kawai, idan ma da manufa mutum yazo mana, ALLAH zai hanashi nasarar cutar damu. Shima da yake can ALLAH zai kuɓutar da shi idan lokaci yayi, dan bana yanke ƙauna da rahamar UBANGIJI akan Muhammad zai fito ya dawo garemu. Ban taɓa jin na sare akan wannan fatan ba, duk da ina jin tsoron kar su cutar mana da shi. Amma ALLAH na tare ta shi, addu'a ta da taku na tare da shi. In sha ALLAHU indai gaskiyarsa ce ta kaisa wancan wajen komai tsahon lokaci zata ƙwatoshi daga hannun azzaluman makirai..." "In sha ALLAHU Mammah". Suka faɗa a raunane, Biebah da Ammar kuwa sai da suka share hawaye. Su Ja'afar dai idanun sun canja launi amma babu hawayen. Su Nimrah dake laɓe suna sauraren su suma dai duk jikinsu yayi sanyi. Cikin Zuciya Nimrah ke jin tana son sanin inda Dadan yake? Miya faru da shi? Mi ake ɓoye musu game da shi?. A zahiri kam batace komai ba ta nufi komawa ɗakinsu, sauran duk suka bita dan dama tun shigowar maigadi Mammah tace su koma ɗaki abinsu. Shine suka laɓe, da farko dariyar shigar ƙanin Maigadi suka maƙe sukeyi, dan yayi wani shigar gayun ƙauye irin masu iyayin nan ne abin dariya......

•••••••••••••••••••••••••••••• ★ONE WEEK LATER★ ★10:15 AM★

SECRET MEDICAL BASE

"Colonel Imran… mun kammala dukkan gwaje-gwajen da muka yi masa." Dr. Idris Ali, ya faɗa yana ɗan gyara gilashinsa. Imran bai ce komai ba. Ɗaga masa kai yay alamar ya ci gaba. Doctor ya jinjina kansa, kafin ya buɗe baki ya cigaba da faɗin, "Mu godema ALLAH jikinsa ya nuna ƙarfin juriya mai ban mamaki. Idan ba haka ba, da gubar da aka saka masa ta riga ta yi mummunan tasiri a lafiyarsa zuwa yanzu." Cikin wani irin bugawar kai Faro ya ɗan matsa gaba, murya ƙasa-ƙasa da alamar tashin hankali a ciki ya furta, "Guba kuma Doctor?". Dr. Idris ya ɗan numfasa, kamar yana neman kalmar da zai musu bayani da ita da bazata ɗaga musu hankali ba fiye da kima. "Eh. Poisoning ne… dan abinda sakamakon bincikenmu ya nuna mana kwanaki uku kenan shiyyasa ma muka sake masa sabon gwaje-gwaje akan hakan, kusan wannan dalilin ne ya hanamu faɗa muku komai a ranar wednesday data gabata mukace ku saurare mu. Sai dai ku kwantar da hankalinku poising ɗin bai jima da fara shigarsa ba, da dai ya jima a inda yake ne zai cigaba da shiga kamar yanda koma su waye suka tsara, sanan zai dinga tasiri a jikin nasa ne a hankali har sai ya gama yima jikinsa illa ne zai bayyana. Dan haka ko a yanzu babu wani damuwa mai girma. Sai dai idan aka bar shi haka a jikinsa, akwai haɗari sosai anan gaba". Imran da gaba ɗaya yake jin jinin jikinsa na tsiyayewa tamkar an ɓula ledar ruwa da tsinin allura ya rumtse idanu yana matse hannunsa.........✍️

[12/25/2025, 8:55 AM] Ummul Adnan: 41

........Da ƙyar Daddy Imran ya iya fisgo kalma ɗaya wajen furta, "Wace irin guba ce?". "Slow-acting toxin. An tsara ta ne don ta lalata jiki a hankali ba kashewa nan take ba. Hakan na nuna wanda ya aikata ya so yaga yana rayuwa cikin rauni ne." Shiru ɗakin yay dan kowa da kalar da raɗaɗin da zuciyarsa ke masa akan jin wannan baƙon al'amari mai rikita lissafi. Suna cikin farin cikin babu wani damuwa a tare da Dada a kwaje-kwajen farko, ashe tashin hankalin na gaba. Da ƙyar Faro ya yanke shirun nasu. "Doctor yanzu minene mafita? Tana da makari ne?". Doctor ya ɗan gyaɗa kansa. "Tabbas za'a iya samun makarinta, abin da ya rage mana shi ne inda zamu same sa, musamman a ƙasar nan tamu kuma da bana jin zamu samu ɗin kai tsaye, idan ma mun samu hankalinmu bazai kwanta ba ga duk wanda zai bamun. Dan duk wanda ya samar da gubar dama dole shine mai makarinta. A yanzu kuma mu kowa ba abin yarda bane a wajenmu. Musamman tunda bamu san wanda ya aikata masa haka ba. Sai dai mubi wata hanyar sirri da cikakken tsaron da zamu fitar da ita gaba ɗaya." Imran ya ɗago kansa ya zuba masa idanunsa da suka juye jazur. Kai tsaye ya furta, "Waje ke nan?" "Tabbad Sir! Asibiti na musamman a waje ya kamata mu kaishi. Zaman wata ɗaya zuwa biyu. Idan aka yi hakan da wuri zamu tsare rayuwarsa da cikakkiyar lafiya." Komai Imran bai sake cewa ba, sai ma ya tashi tsaye a hankali, sai dai nauyin abin da yake ji ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa da kuzarin jikinsa. Ɗan juyowa yay ya kalla Doctor ɗin, cike da gargaɗi ya furta, "Babu wanda zai san wannan bayan mu ukun nan." Dr. Idris ya gyaɗa kai da girmamawa. "Mun riga mun ɗauki rantsuwar sirri ai Sir." Imran ya juyo ga Faro, idanuwansu suka haɗu a waje guda. "Zan sanar da shugaban ƙasa yanzu." Faro ya ɗan murmusa da gyaɗa kansa, sai dai murmushin da ke ɓoye fushi. "Ka sanar da shi. Amma ka faɗa masa gaskiya ɗaya: Zak-Shadow bai fito daga prison don ya mutu a asibiti ba." Imran ya gyaɗa kansa yana ɗaukar wayarsa, harya fara tafiya ya tsaya a ƙofar ɗakin, a taƙaice ya furta "Ba zai mutu ba in sha ALLAHU." daga haka ya fice ya bar Faro da Doctor Idris na cigaba da tattaunawa.

Dada da basu san duk ya gama jin abinda basa son yajin ba ya bar jikin ƙofar yana murmurshi. Drip da ake faman saka masa a kwanakin nan dama doctor ɗin ya saka masa bayan sallar isha'i, shine ya saka shi barci har su Imran ɗin suka shigo gidan bai sani ba. Yanzu ma ya farka ne sai yaga ruwan ya ƙare ya cire da kansa, ruwa da yake buƙata na sha daya duba babu a ɗakin ya saka shi ƙoƙarin fitowa duba Dr Idris ɗin, dan koda yaushe Doctor na tare da shi a gidan. Barin wajen yay ya koma ya zauna a bakin gado. A zuciyarsa yana faman maimaita kalmar poising ɗin, sai dai fuskarsa da murmurshi, dan ya jima da fahimtar hakan a tare da shi, musamman a watannin nan da suka gabata. Har ma yana tunanin yaushe hakan ta faru? Tun yana a prison ɗin, dolene a ɗayan biyu gubar ta shigesa. Mafi ƙarfi a zuciyarsa shine television da aka kawo ɗakinsa watannin da suka wuce, ko kuma ta hanyar securitys ɗinsa......

%★%★%★%★%

A ɓangaren su Hajiya Hasiba kam abinda suka jiyo ga bokan Mamawo ya matukar rikitasu, amma sai Hajiya Hasiba tace ita dai su sake zuwa wajen wani mana. Ko suje India ɗin kona kwana biyu ne. Mamawo ta yarda da shawarar, amma tace su fara fuskantar Adeel. Itama Hajiya Hasiba bata musa batun ba, sai dai sun nema ganin Adeel ɗin shi kuma ya toshe hakan. Dan yama ɓoyema ganinsu gaba ɗaya dan haka dole sukai hakuri dan zuciyarsu na kitsa musu ko wani abu yake shiryawa. Ga First lady ta takurama Hajiya Hasiba akan harkokin bikin ƴarta, dole ta haƙura da batun India ɗin ta maida hankali a kanta. Har takai ma bata fahimci Ismat bata gida ba sai bayan kwana biyu. Sai dai tana taɓota tace tana gidan Aunty Jiddah zatai kwana biyu sai ta saki batun ta. Dan bata kawo a ranta wani abu Ismat ɗin ke shiryawa na komawa gidan babansu ba. Ita ko Nabeeha tunda suka baro gidan Mammah a waccan ranar al'amarin Nimrah ta ɗauka ta saka a zuciyarta dan girman yarinyar ya tayar mata da hankali matuƙa. Tun tana ɗaukarsa ƙaramin abu har yake neman zame mata ciwo a kwanakin gaba ɗaya bata jin daɗin ranta dama jikinta duka. Babu abinda take saƙawa sai yanda zatai da Nimrah. Wannan ya ɗauke hankalinta itama bata shiga sabgar kowa da komai na gidan. Su kuma su Amima holewarsu suke hankali kwance da yawon tsiya ita da Rayhana kullum. Dan uwarsu ta tsaya musu.....

<<%>><<%>><<%>>

"Waye shi wannan?". "Wani yaro ne malamin islamiyyar su. Gaba ɗaya alamominsa sun nuna sonta yake yi. Dan haka da shi ya dace muyi amfani wajen yi mana wannan aikin. Saboda gidan tako ina zagaye yake da ƙyamarorin zamanin nan. Sannan kamar yanda na sanar maka ranar da gaske sun mantar da ita asalinta, su kaɗai take ma kallon iyaye a yanzu." "Da gaske mutanen nan shu'umai ne fa Mole, wannan halayyar a jininsu take ba Zak-Shadow ɗin bane kawai shege". "Zan tabbatar musu mun fisu shu'umci, ba laifinsu bane kuma. Laifin Hafsatu ne data ɗaukar min yarinya ta bashi. Kuma ta godema ALLAH data mutu, dan da ace tana raye har yanzu, sai na ɗanɗana mata fiye da abinda take tsammani na azaba a tafin hannunta duk da son da nake mata".. "Mole manta kawai, wauta ce irin ta mata da zigar ubanta. Ba gashi sun kuma ɗanɗana daga hukuncinmu ba yanzu sai labarinsu. Yanzu shi wannan yaron mai gemu kamar jelar tsatso ya za'ai yazo hannun mu? Dan su Oga sun ce muyi faka-faka babu ɓata lokaci muna buƙar yarinyar mu Nimrah tai mana aikin nan da gaggawa ta dawo hannumu." "Karka damu wannan duk mai sauƙi ne. Dan tana nan da halin nan nata dana santa da shi har yanzu. Na tabbatar idan taga videon nan kodan son da takema uwarta zata dawo hankalinta. Ballema idanunta ya sake buɗewa yanzu tayi karatu. Kamar yanda kace babu ɓata lokaci kawai saƙon nan na farko ya dace ya fara riskarta, dan yaran ya sanar min watannin baya ya aika mata ƙyautar litattafai, kaga sai muyi amfani da wannan damar nake ga ko." "Hakan yayi, zan saka a cikin satin nan a sace min yaron. Amma fa kaima sai ka sake kula gaskiya. Dan Imran ɗin nan na tabbatar shegen kansa ne zuwa yanzu. Duk da dai a zahiri baya wani abu da zai tada mana hankali, ina jin tsoron shiru-shirun sa". "Ni ko kaga bana wani tunani mai girma a kansa, saboda uban ƴan taurin kan can shi ne ƙarfinsa, rashin sa a kusa da shi kuma duk ya sake rage masa kuzari." "Kai ma kayi magana ta gaskiya. Amma duk da haka kada mu sakankance. Bari naje dan asuba ta gabato. Sai na jika". Sunyi sallama Dagger ya bar gidan, dan gida ne dama na haya mai mutane da yawa Mole yazo ya kama ɗaki. A yanda yake kuma baka isa kace yana da wata suffa ta mutanen banza ba. Tsabar iya taku ma jama'ar gidan da sunan Malam suke kiransa......

<<<<<✷⁠‿⁠✷>>>>>

A gidan Mammah kam yau su Nimrah gidan Daddy Imran suka tafi zasu kwana. Harda Feddo da Bintu kuma suka shirya weekend ɗin nasu. Uncle Bilal ne ya kaisu da kansa, dan dama su ƴan gatansa ne. Tunda suka iso suka cika gidan da hayaniyarsu da karaɗi, aka fara faɗan ƙa'ida tsakanin Ruky, Nimrah da auta da suke kira Lolo. Dan shine sakon Ruky, dan haka yake ganin itama Nimrah sakon tashi ce. Wani lokacin kuma suke jansa tsiyar, dan ko yau suna shigowa ɗakinsa suka wuce suka kwaso masa chocolates na makaranta suka hau ci. Shi ko yana dawowa daga Islamiyya aka fara, sai da Ammie ta shiga tsakani. Sun gama da Lolo suka koma kan Aunty Ma'u. Wai sai ta faɗa musu miye tsakaninta da Uncle Billa. Cike da baƙar magana tace su shaƙeta ta sanar musu to. Da yake shaƙiyay ne suka sakata a gaba wai ai sun sani, Fiddo harda cewa ai taga wani bangle a ɗakin Uncle Billa an saka sunan Aunty Asma'u ɗin. Duk abinda suke Ammie na jinsu, itama kuma hirar tasu ta fara kai hankalinta akan al'amarin Asma'u ɗin da Bilal, dan kwan biyun nan ta fahimci ko yaushe Asma'u na maƙale da waya, idan ta tambayeta sai tace wai assignment take yi. Ashe ita ta maida assignment ɗin. Kai yaran yanzu sai a barsu dai kawai. Tai murmushi mai yalwa, dan har cikin ranta wannan haɗin ya mata. Wlhy idan duk ƴaƴan data haifa zasu kasance matane ace yaran gidan Mammah suka auresu zatafi kowa farin ciki, dan jinin Mammah jinin alkairi ne. Abotar Imran da Haysam babban rahama ce kuma alkairi ga zuri'arsu guda biyu. Addu'ar fatan alkaici tayi ta cigaba da sabgarta.........✍️ [12/25/2025, 8:55 AM] Ummul Adnan: 42

........Bayan la'asar su Nimrah suna a garden suna basket ball su duka huɗu sai Yaya Khalifa, Yaya Mu'azz da Yaya Imam da suka zo gidan babu jimawa, sai Auta Lolo. An raba team ɗin biyu, amma Nimrah da Ruky sunƙi yarda a rabasu, dan haka sai ƙwange sukema su Mu'azz da rinto. A yanzu ma ana tsaka da gardama Nimrah da Ruky sun dage kuma akan rinto ne Khalifa ya hararesu da faɗin, "Kufa matsalar ku rinton jaraba, shiyyasa sam bana son haɗa sabga da Ninah da Ruky munafukan yara ne ALLAH". "Ashe ka gane Broth, wlhy haka suke". Cewar Mu'azz shima yana hararsu. Baki Ruky da Nimrah suka taɓe, Nimrah zatai magana sallamar maigadi ta dakatar da su. Imam ne ya amsa masa duk suka juyawa suna kallonsa. Kai tsaye inda Nimrah take ya isa, ya miƙa mata ƙaramar ledar hannunsa yana faɗin, "Saƙo ne wani ya kawo wai a baki. Yace malamin ku ne na islamiyya Kamal". Tsit wajen yay ana kallan kallo, sai Bintu ce da tai dariya da faɗin, "Humm guy ɗin nan fa ya dage wlhy". Kafin wani ya bata amsa Lolo ya amshi ledar, maigadi ya juya abinda yabar wajen. Dai-dai Lolo na fiddo littatafan cikin ledar. Yanzu kam dariya Feedo, Ruky, Bintu suka kwashe da shi. Yayinda Nimrah taja tsaki. Aunty Asma'u kuma ta tambayesu waye ya kawo?. Labari su Feedo suka bata, har su Mu'azz duk na saurarensu, sai dai abin mamaki duk fuskokinsu sun canja, dan cikin faɗa Khalifa ya ce, "Zamu ci uwar guy ɗin nan kuwa, ƙannenmu da aka tura makaranta ne abin bibiyarsu da soyayya? Dan ubansa aure akace za'ai musu?". Cikin ɓacin rai Imam ya ce, "Dolene muje har makaranta muja masa gargaɗi kam, wannan ai rashin hankali ne". Mu'azz kam daya kume bai iya ya tanka ba, dan fuuu yabar garden ɗin ma. Khalifa da Imam suka take masa baya. Daga haka wasan ya watse. Ammie dake falo sai ganinsu tai suna shigowa ɗai-ɗai. Bata ce da su komai ba dan tana waya da Daddy Imran ne....

Washe gari daga Nimrah har ƙawayenta babu wanda ya sake bin batun litattafan Sayyadi Kamal kamar wancan karo da suka ma barsu a gidan Aunty Mimi. Dan tunda suka tashi ma suka taya masu aiki gyaran gidan da haɗa breakfast. Bayan sun karya kuma sukai shiri wucewa gidan Baffa dan Hajiyar Daddy Imran ta dawo daga ƙauye jiya da yamma. Tunda Aunty Asma'u ta sanar musu sukace yau can zasu yini. Duk da Ammie na son su zauna babu yanda ta iya. Dole ta haɗa lafiyyayen farfesu da kunun aya da kunun gyaɗa tace su kaima Baffah da Hajiyar (Iyayen Imran kenan). Nimrah ce ƙarshen fitowa a ɗakin. Ta kammala rolling veil ɗin abayarta kalar maroon da adon milk da taji stone tana maida kayan kwalliyarsu a make-up kit ɗinsu idanunta suka sauka akan books ɗin Sayyidi Kamal dake zube a side drawer inda tun jiya Bintu ta zube su. Samun kanta tai da ƙarasawa inda suke ta ɗaukesu su duka uku yau dai tana kallo. Zuuu taɗan buɗesu a tare, sai ga wata ƴar ƙaramar takarda ta faɗo a ɗaya daga cikinsu. Takardar tabi da kallo, ganin rubutun jikinta ta kai duƙe ta ɗauka. _Ba litattafan bane muhimmanci a gareki yau kamar saƙon farko, ainahin saƙon yana a littafi mai jan bango shafi na hamsin da uku da shafi na tamanin, ki tabbatar ke kaɗai kikaga abinda ke ciki batare da kowa ba har aminiyarki, saboda muhimmancin abinda ke ciki da zai amfaneki ke kaɗai. Idan kuma kika bari wani ya gani bayan ke to tabbas zai mutu._ Takardar ta ɗan jujjuya cike da mamaki zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri saboda kalaman ƙarshe, dai-dai nan akai knocking ƙofar ana kiran sunanta. Dan haka ta maida takardar kawai cikin littafin farko tana amsawa da haɗiye abinda ke shirin hargitsa mata brain, sai kuma ta buɗe handbag ɗinta ta saka duka books ɗin a ciki dan basu da wani girma sosai. Haka ta fito zuciyarta na kai-kawo akan abinda ta karanta. Amma da yake tana da wayo sai ta danne ta yanda kowa bazai fahimta ba. Yau kam Yaya Khalifa ne ya kwashe su zuwa can gidan Baffan. Cike da farin ciki suka zagaye nutsatstsiyar tsohuwar mai cike da kwarjinin ibada da lafiyar data haɗu da jin daɗin rayuwa. Hajjo tsohuwa mai ran ƙarfe kenan, mahaifiya gasu Imran da a yanzu ta zama uwa harga su Mammah, sannan kaka gasu Nimrah. Dan dattakonta yasa itama bata san raba ɗaya biyu ba, ta zama ginshiƙin dunƙule familyn nan uku da basu da alaƙar jini a yanzu sunfi ma waɗanda keda alaƙar jinin gina ƙyaƙyƙyawan zuminci... "Oh ni Bilkisu, yaran nan ina zakuje da girman jiki? Ba'a kauda uwarku Biebah ba balle yayunku amma neman dannesu kuke da girman jikin ku, anya bazance a haɗeku rana ɗaya da Habibah da su Asma'u ba". A tare suka gwalalo mata idanu, cike da shagwaɓa har suna haɗa baki wajen faɗin a'a gaskiya su auren su sai sannan da shekara goma. "Shekara goma? Kuji min shaƙiyan yara, sannan kuma in sha ALLAHU ai sai dai lissafin auren ƴaƴanku. Ni yanzu kunga tunda gaku ku duka huɗun yau ba lalaci da surutu zaku yimin ba. Tashi zakuyi kumin kwalemar ɗaki a fitar da komai a canja min jere na, dama su Asma'u zance suzo suyi, amma tunda gaku shike nan sun huta". A tare suka amsa mata da to. Sai kuma Nimrah da duk bata da kuzari ta ce, "Granny ina Baffa wai?". "Naja'atu sun fita shi da baban ku Ammar, dan kamar ma suna can gidan kakanku Nasiru. Amma nasan anjima kaɗan zasu dawo". Kai Nimrah ta jinjina, har sun miƙe Hajjo dake binta da kallo ta kira sunanta, juyowa tai, sai kuma ta tako inda Hajjon take. Sai da ta kama hannunta ta zaunar kusa da ita sannan taima su Fiddo da suka tsaya suna kallonsu alamar suje su. Basuyi musu ba suka wuce hanyar bedroom ɗinta. Ita kuma ta maida hankalinta ga Nimrah. "Naja'atu mike damun ki? Ko baki da lafiya ne?". Sai da gaban Nimrah ya faɗi, dan bata taɓa zaton wani zai gane halin da take ciki ba. Amma sai tai ma Hajjo murmushi da girgiza kanta. "Ba komai Granny, mi kika gani?". Hajjo dake kallonta cike da nazari ta ce, "Ban yarda ba Naja'atu, nafa san halin kowa a cikinku, ko yaya kuka canja kuma ina ganewa." Har Nimrah ta buɗe baki zatai mata bayanin abinda ta gani a takardar nan sai kuma ta tuna kalaman ƙarshe na cewar duk wanda ta bari ya sani zai mutu, da sauri ta canja zancen tana kwantar da kanta jikin Hajjo ɗin. "Granny da gaske ba komai. Kawai dai yau na tashi ne duk zuciyata wani iri ba daɗi, kuma gabana nata faɗuwa". Ajiyar zuciya Hajjo ta saki a hankali, sai kuma ta shafa kan Nimrah ɗin cike da lallashi da so da ƙauna ta ce, "Ki yawaita ambaton Hasbunalahu wani'imal wakil da talatin ANNABI kinji. In sha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Barsu ma suyi aikin muyi hirar mu". "Granny zan taya su ina son nima nayi. Amma kin zo mana da farar mu?". "Buhu guda ma kuwa, tana nan a store dama in baku zo yau ba zan bayar a kai muku, damma na manta ne da A'isha tazo ɗazun ita da Bilalu ban basu ba". Farin ciki sosai ya bayyana a fuskar Nimrah, sai kawai ta nufi ɗakin Hajjo tana ƙwalama su Ruky kira. Da kallo Hajjo ta bita tana murmushi, dan har cikin ranta take ƙauna da tausayin Nimrah.......

<•><•><•><•><•><•><•>

★ SECRET MEDICAL BASE ★

Yanda Imran yake a ruɗe ko damuwa da kallon lokaci baiyi ba ya dannama shugaban ƙasa kira. Cikin sa'a kuwa ba a jima ba aka amsa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin yay sallama. Daga can shugaban ƙasa da alamu ya nuna barci yake ya amsa, duk da dai a cikin murya mai nutsuwa ne. "Imran." "Ranka ya daɗe ka gafarce ni na tashe ka a barci bazan iya haƙuri bane shiyyasa ko lokaci ban damu da dubawa ba na kira ka." "Karka damu Imran nima barcin ya ɗauke ni ne kawai batare da na shirya masa ba. Nima ina son kiran naka a daren nan ai. Amma minene ya tada maka hankali haka?". Shiru kaɗan ya biyo baya Imran ya gagara magana saboda abinda ya toshe masa maƙoshi. Shima sai Shugaban ƙasa bai iya yace komai ba yana dai saurarensa cikin shiru, irin shiru na masu fahimtar juna ba tare da doguwar magana ba. Tsohon minti guda Janar ya katse shi da faɗin, "Ka samu abin da ka je nema ne Imran?" Imran ya sauke numfashi karo na farko a hankali. Muryarsa da ɗaci ya furta, "Eh, ranka ya daɗe. Amma abin ya fi yadda muke zato nauyi." "Faɗa min kawai". "Akwai guba a jikinsa. Ba ta gaggawa ba, amma an tsara ta ne don ta lalata shi a hankali. Likitoci sun tabbatar da cewa a nan ba za a iya magance ta gaba ɗaya ba, koda akwai makarinta zai iya kasancewa a hannun wanda sukai aikin yake ko suna da alaƙa da wanda suka yin, dan dole mai makarin shike da gubar. Fitar mu nemata zai basu ƙofar sanin sirrinmu". Shiru ne ya sake biyo bayan bayanin Imran ɗin. Dan Janar ya kasa koda motsin kirki tsabar yanda zancen ya buge shi shima. Imran ya san wannan shirun na Janar shiru ne na mutum da ke ƙoƙarin riƙe fushinsa shima, dan dole Janar zai ji kamar yanda suka ji a lokacin da Doctor ke sanar musu. "A wajen akwai maganin? ta hanyar da muke buƙata?". Janar ya faɗa cikin wata irin murya mai bayyana ɗaci da zafi. Amsa Imran ya bashi, "Akwai, ranka ya daɗe. Amma zai iya ɗaukar wata ɗaya zuwa biyu inji Doctor." Muryar Janar ta sauya kaɗan zuwa matsayin shugaban ƙasa, cikin nauyin umarni ya furta. "Amincewar UBANGIJI kawai muke nema. Amma babu wanda zai ji wannan har Haysam." "Mun riga mun kulle komai Sir." "Zan zo yanzu. Ina son na gansa." Imran bai yi mamaki ba, dan haka kai tsaye ya ce. "Muna maraba da zuwanka ranka ya daɗe." "Uhhm". Janar ya faɗa yana yanke kiran.........✍️

[12/25/2025, 8:55 AM] Ummul Adnan: 43

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull