Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 2
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 2: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 2. Washe gari tunda sassafe ya baro gidansa saboda tsabar zumuɗi, maimakon…
4,366 words
Washe gari tunda sassafe ya baro gidansa saboda tsabar zumuɗi, maimakon office kuwa kai tsaye Special Military Corrections Facility North Central Command Base ya wuce. Haka ya samu waje can nesa da prison ɗin ya tsaya zaman kusan awanni uku har lokacin da aka bashi ya cika sannan ya kunna motar ya karasa. A hankali motar sa ta tsaya a gaban babban ƙofar ƙaton gate ɗin. Tsaron wajen ya banbanta da duk wani waje da Imran ya taɓa gani, dan shi ba'a nan aka ajiye shi ba a nashi zaman. Birgedun sojoji biyu a wajen ƙofar, camaras a jikin bango, wasu guards suna sintiri cikin takun da ke nuna horo mai tsauri a wajen. "Major Imran Abbas?" ɗaya daga cikin guards ɗin ya tambaya. "Eh, ni ne". Muryarsa ta yi nauyi kamar anyi masa sarƙa a wuya saboda yanda yake jin kansa da zuciyarsa dake bugawa da sauri-sauri. "Follow me, sir." Kansa kawai ya jinjina, a ƙasan zuciyarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya bi guards ɗin zuwa wani dogon corridor da yake a tsaftace alamar ana kula da wajen sosai fiye da kima. Daga can suka kai shi wani ɗaki da shima yake zagaye da camaras kamar tsiya. "Ka ajiye wallet, takardu, da belt. Za a bincika ka kafin a shiga." Babu wani nuna damuwa Imran ya cire belt ɗinsa dan wannan yasan dokar soja ce. Bai taɓa tunanin zai zo wannan wuri saboda Haysam ba. Bai taɓa hango cewa watarana ƙaddara zata kwaso su zuwa wannan ramin mai tudu da kwazazzabo ba. Bayan an kammala bincike sa yanda ya dace suka fita a ɗakin, wani ƙaramin ɗakin ganawa suka kai shi, wanda ke da tebur biyu da gilashi tsakanin su. Amma shi an canja musu saboda matsayinsa daga shi har Zak-Shadow ɗin, dan haka aka basu ɗaki na musamman ba tare da gilashi tsakanin su ba. Wani irin duka zuciyar Imran take tamkar ƙarfen agogo dake bada sakanni na motsawa ne da ita. Minti biyar.. Minti goma.. shiru. Sai zuciyar Imran ta ƙara ƙarfin bugawa kamar bugun gangar yaƙi, dan adadin mintinan da aka saka zai iya fitowa sun cika..
Dai dai nan kuwa aka buɗe ƙofa a hankali. Sojoji biyu suka shigo da Lt. Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi. Sai dai ba irin Zak-Shadow ɗin da duniya ta sani bane a baya. Wannan Zak-Shadow ɗin ya canja da canje-canje masu yawan gaske, musamman a suffa ta soja zuwa wani abu daban, gashinsa ya yi tsawo sosai sama da yadda yake da, fuskarsa ta ajiye saje saɓanin da da babu ko ɗigon gashi a fuskarsa saboda kasancewarsa soja, fuskar sa ta ɗan rame amma kwarijin da cikar kamalar da gizago zaratan MAZAJEN na nan shimfiɗe a kanta. Ga tambarin sallarsa ya sake fita baƙi sosai akan goshinsa saboda hasken zaman waje ɗaya da fatarsa ta sake yi, ainahin haskensa na da kafin wahalar soja ta dusar da shi ya sake bayyana. Idanun nan kam sun wani sake juyewa kamar na kumurcin maciji. Hannunsa na sanye da ƙananan cuffs saboda dokar prison. Shi dama can bamai ƙiba bane, amma jikinsa a buɗe yake da ginannen ƙarfi irin na masu kulawa da tattali, dan haka ko a yanzu bazakace ya rame na tashin hankali ba, dan daga ganinsa kasan bai daina motsa jikin ba, zaka tabbatar da haka saboda takunsa dai nasa ne na soja mai ji da kansa, ko a cikin jeji, ko a cikin duhu. Ko a cikin bainar jama'a wannan takun ƙasaitar da jarumta baya canjawa. Ya ɗan tsaya kafin ya zauna. Sai kuma ya kalli guards ɗin da juyayyun idanunsa ya kaɗa kai kaɗan. Su sun san nan ɗin ba wajen wargi bane, dan ko KURA TA RAME TAFI ƘARFIN WAWASON ƘANANUN NAMUN JEJI. Ga shi dai a tsare, amma takashi ko manyan KAYA sun gagara, shiyyasa a tsaren yake amma girmamawa babu abinda ya canja. Ai ko mahaukaci yasan kallon ZAKI sai daga nesa, a nesan ma daga bayan keji, dan ko hannu ya samu zai iya yin wawaso. Yafi ƙarfin kallon banza ma balle ace za'a dake shi. Fitar kuwa sukai da sauri suka barsu su kaɗai. Shiru ya cika ɗakin. Shiru mai nauyin da ko ƙarar bindiga da harbi bai zama lallai ta iya yankesa ba. Su duka biyun sun zubama juna ido ne kawai kamar masu kallo a cinema. Imran ya ji hawaye sun cika masa ƙwayar ido. Amma ya danne. Zuciyarsa na ƙaraji. Dole ya kauda nasa idanun da kansa gefe yana ƙoƙarin haɗiye hawayen. Zak-Shadow ya ɗan girgiza kansa, tare da zama, a hankali ya jingina bayan sa da kujerar. Juyayyun idanunsa suka sauka a fuskar Imran daya sake juyowa kamar yana lissafa duk wani abu da bai faɗa masa ba shekaru uku da suka shuɗe. Ganin Imran bashi da niyyar yin magana shi ya motsa nashi lips ɗin da sukai jazur cikin dakakkiyar golden voice ɗinsa dake cike da izza da amo ya furta, "Major Imran Abbas." Kalmomi uku ne kacal. Amma Imran ya jisu har cikin tsakiyar zuciyarsa da brain. Da ƙyar ya iya dauriyar amsa wa da. "Sir…" Muryarsa ta kasa fita gaba ɗaya saboda sabbin hawayen dake cika masa idanu.........✍️
4
........Dada dake kallonsa kallo mai cike da ƙauna daga UBANGIJI ya ɗan ɗaga hannunsa yana masa Alamar ka tsaya ka nutsu. Sai kuma ya sake motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta "You're a soldier Imran… but seeing you like this is giving me a headache. What's happening to you?why are you acting like a woman?". Shima ya ɗan kawar da kansa gefe saboda idanunsa na son suyi wani abu saboda hawayen da suka sakko a fuskar Imran sharrrr. Kuka ko ɓacin rai ne shi kansa bai ma san wannene yake ji da ganin hawayen Imran ɗin ba. Cikin dakewarsa, idanunsa na kallon gefe ya sake furta, "Bazan tambayeka yaya kowa yake ba? Dan hakan shine mafi girman abinda zai sosa min ZUCIYA. Na ganka, shi ne abinda yafi komai muhimmanci Imran." Da ƙyar Imran ya tsaida hawayensa. Fuskarsa da murmurshin ƙarfin hali ya ɗan matsa gaba, hannayensa duk biyu ya ɗaura kan teburin. "Munyi ƙoƙari.. Munyi komai… amma suka zaɓi yimana wannan zaluncin Haysam…" Dada ya katse shi da murya mai sanyi amma mai ƙarfi da nutsuwa, "Ba zalunci bane. Siyasa ce. Dama kuma ita siyasa ai ba ta rabuwa da jini." Kai Imran ya girgiza. Cikin son ƙarfafa kai ya ce, "Na fahimta, kenan sun kulle ka saboda sun tsorata. Sun tsorata da kai. Sun tsorata da gaskiya. Sun tsorata da abin da ka sani". "Na sani." Dada ya furta a hankali yana ɗan murmurshi. Shiru ya sake mamaye ɗakin kowa da abinda yake tunani, fin sakan goma ya maida kallonsa kan Imran kai tsaye, kallon da ya tattara shekara uku masu zurfi: jarunta, kewa, hikima, da raɗaɗin da ya gama zagaye zuciyar mutum daga mutum ta zama tamkar dutse. Imran ya katse shirun da faɗin, "Kurakuraina suka kawo ka nan Haysam, zan sadaukar da rayuwata domin ganin ka fita kuma" ya share hawayen da suka sake silalo masa, batare daya bari yayi magana ba ya cigaba da faɗin, "Bayan rufe mu sun sauke COAS shima, sai dai bai daina gwagwarmaya ba, dan yanzu haka da tsayawarsa nazo nan." Idanu Dada ya lumshe a hankali, batare da kula zancen Imran na farko ba ya furta, "ALLAH ya saka masa da alkairi, dama nasan ba zasu barshi ba shi da duk masu goya mana baya. Imran… ka dawo min nan idan ka samu lokaci. Muna da magana mai tsawo. Kuma kada ka sake jin damuwa. Kai kaɗai ne wanda ban taɓa zargi ba." Idanun Imran suka sake zubo hawaye saboda wannan kalmomi na ƙarshe. Cikin jinjina kai ya ce, "Zak… har abada damuwa bazata barni ba in har kana a wannan wajen. Dan haka bazan taɓa barin ka a nan ba har abada". Dada ya yi murmushi. Ba mai annuri ko farin ciki ba. Murmushi ne kawai irin na jarumta da taurin zuciya. Shi yasan fitarsa a wannan wajen sai wani ikon ALLAH, amma ba abune mai sauƙi ba. "Karka damu Imran. Ina a nan ne. Amma ba zan tsaya nan ɗin ba kamar yanda ƙaramin tunaninsu ke basu". Sai ya jingina da kujera yana ɗan lumshe ido. "Kamar yanda na gaya maka kai ƙoƙari ka dawo. Idan ba haka ba ka fara zargina da guduwa, dan babu gudu babu ja da baya sai na ƙarasa wannan aikin". Tabbas Imran ya tabbatar da alwashinsa cikin idanunsa da suka sake rikicewa, ya kuma san wanene Zak-Shadow ɗinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya ƙudurta. Zama ya gyara cikin sassauta murya dan baya son akai ga matakin da Haysam ke harin saboda komai zai sake jagulewa ne. "Dan ALLAH kar akai ga haka MAZAN FAMA. Ina sha ALLAHU zan dawo. Zan dawo duk rintsi, zan......" Motsin buɗe ƙofar da ake yi ya katse Imran. Sojojin ɗazun ne suka dawo, hakan ya sasu fahimtar lokaci ya cika. Dan haka kafin ma suyi magana Dada ya miƙe abinsa, sai kuma ya ɗan zubama Imran ido na sakan ɗaya, kafin cikin dakakkiyar muryarsa ya furta, "Imran…" Imran ya ɗago kai yana kallonsa fuskarsa cike da damuwa da kewa.. Ƙaramin murmushi yay masa, tare da furta, "Ka tsare min kanka. Daga yanzu ka saka a ranka sabuwar ƙaddara ta fara motsi." Daga haka ya juya abinsa yay gaba, ya bar Imran cikin shiru mai nauyin da bin bayansu da kallo, idanunsa cike da hawaye, dan a wannan ƙadamin yama manta da kansa a matsayin soja.......
<<>><<>><<>><<>>
Da ƙyar Imran ya iya jarumtar hana kansa sanarma su Mammah ganawa da Dada da yayi. Dan ya tabbatar zai saka musu sabuwar damuwa ne bayan sanyaya zukatansu da UBANGIJI yayi badan sun manta da damuwarsu ba tsahon shekara uku da wasu watanni. Amma kamar yanda Dada ya roƙesa kada yay masa zancen kowa saboda zai zama fami a zuciyarsa yasan suma a garesu haka ne. Sai kawai ya zaɓi yin shiru ko Aunty Hafsat matarsa bai gayama komai ba. Hatta Janar dake jiran jin ta bakinsa ya gagara ganawa da shi. Dan a wani irin cinkushe zuciyarsa take a gaba ɗaya satin. Cikin kwanaki uku kacal bayan ganawar ta su rayuwar Major Imran Abbas ta canza. Ba ci, ba barci, sai tunanin kalamomin Zak-Shadow da yadda suka tsaya masa a wuya kamar an daure zuciyarsa da igiya. Duk inda ya zauna shi ne kawai a gabansa. Hatta aikinsa ya samu rauni a kwanakin nan. Ranar alhamis karfe biyu na rana yake cikin ofishinsa shi kaɗai, ya na kallon rubutun bayanin da ya yi wa janar mai ritaya jiya. Dan ya yanke shawarar tunkararsa kawai a yau su tattauna yanda ya kamata. Kamar abin almara dai-dai lokacin wayarsa ta fara tsuwwa, sunan da yaga yana yawo a screen ɗin ya sashi kasa ɗagawa har sai da ta tsinke, sake kira na biyu ne ya maidoshi a hayyacinsa, ya sauke numfashi mai nauyi kafin ya ɗauki wayar yakai kunnensa. Cike da girmamawa yay sallama, tare da miƙa gaisuwa. Daga can General Yusuf ya amsa, cikin damuwa ya cigaba da faɗin, "Imran kana lafiya kuwa? Kwanaki uku kenan ina saka ran ganinka amma shiru?". "Kayi haƙuri Sir kawai ina cikin ruɗani ne. Amma dama yau na shirya samunka a gida bayan na tashi aiki". Cikin sauke ajiyar zuciya Janar ya ce, "Nasan hakan zata faru, amma yaya zamuyi sai haƙuri Imran. In sha ALLAH watarana sai labari, duk wuya da juyin juya halin da za'ai Haysam bazai wulaƙanta ba da iznin UBANGIJI. Kazo dan nima na matsu mu tattauna". "In sha ALLAHU Sir zan zo". Daga haka sukai sallama Imran ya ajiye wayar.
★Kamar yanda Imran yay alƙawari yana barin office gidan tsohon General Yusuf Shu'aibu Tafida ya nufa dake tsaftatacciyar anguwa. Sai dai sai da ya kira Aunty Hafsat ya sanar mata yau bazai shigo gida da wuri ba. Hayaniyar da yaji yake tambayarta "lafiya nake jin hayaniya haka?". Ta ce, "Lafiya lau mutanenka ne. Kaima kasan idan Nimrah da Ruƙayya na nan bakin kowa baya shiru. Daga Islamiyya suka zarto nan wai sai ka dawo ka maidasu gida". Murmushi yayi da girgiza kansa, zuciyarsa na ayyana masa 'ai dama sai hali yazo ɗaya ake abota' dan rashin jin da Nimrah da Ruƙayya ke zubawa abin har ba'a magana. Tuni sun koma masu gida biyu, basu gidan Mammah basu nan gidansa. A fili kam sai ya ce, "In dai banan zasu kwana ba ki kira Ammar ya ɗaukesu, dan nikam ba yanzu zan shigo ba. Kin san kuma Mammah bata ƙaunar suyi dare a waje". Cikin girmamawa tace, "Bari na kira shi to dan sunce komawa zasuyi. ALLAH ya dawo dakai lafiya". Da Amin ya amsa mata yana yanke wayar. Dai-dai kuma isowarsa babban gate ɗin gidan General Yusuf. Yay horn maigadi ya buɗe masa bayan ya leƙo yaga waye. Kasancewar ba yau ya fara zuwa ba, kuma maigidan ya sanar da zuwan nashi yasa aka buɗe masa gate ɗin kai tsaye. Yana gama parking ɗaya a cikin sojojin dake gidan yay masa rakkiya har babban falon General Yusuf kai tsaye, dan ba'a ajiye shi a falon baƙi ba ma. Tunda ya shigo Genaral ke murmushi, Imran ya kai zaune cikin kujera shima tashi fuskar da ƙaramin murmushi. Gaisuwa yay masa irin ta oga kuma uba. Dan Genaral ya girmesu sosai a ƙalla yakai shekara 69 a duniya. Suko yanzu ne ma suka haura arba'in ɗin da wani abu. General ya amsa masa da kulawa, dan har cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar Haysam da Imran saboda kwazon su da sanin aiki da gaskiya.. "Bismilah ga ruwa nan, ka kuma tashi muje muci abinci". Imran ya ɗan sake murmusawa yana shafa kai, cike da girmamawa ya ce, "Sir zan sha ruwan dai, abinci kuwa amin afuwa kada madam tayi fushi nabar nata". Ƙaramar dariya Genaral yayi duk da kuwa shima ba mutum ne mai yawan fara'a ba. Cike da dattako ya ce, "Gaskiya bazan so ɗiyata kam tai fushi ba. Amma duk da haka sai kaci, dan na saka an shirya maka ne na musamman". Babu yanda Imran ya iya dole ya haƙura suka hau teburin cin abincin da aka cika da kayan daɗi. Sai da suka fara cin abincin cikin nutsuwa falon shiru janar ya katse shirun da faɗin, "Ina fatan babu wata damuwa tare da Haysam? Yana cikin ƙoshin kafiya?". Sai da Imran ya haɗiye abincin bakinsa sannan ya jinjina kansa, sai dai fuskarsa ta janza zuwa damuwa. "Alhamdullih Sir. Babu wata bayananniyar damuwa ta zahiri. Dama kuma mun san bayan killacewa babu abinda zai yarda ya ɗauka ga wani na ƙasƙanci in dai Haysam ne. Dan har yanzu JININ MAZA na'a kan FARCE". Sosai Janar yay murmurshi mai faɗi. Ya ɗauki ruwa yana tsiyayawa a kofin gilashi. "Wato Imran da ƙasar nan tasan asarar da tayi na killace Haysam na kwana ɗaya kawai data jima da yima kanta da kanta ALLAH ya isa. Balle ma ace na tsawon shekaru uku da wasu watanni. Irinsu Haysam a ƙasa tamkar hasken diamond ne a tsakiyar sahara. Amma ban san miyasa ba, maimakon aga haskensu anfi kallon wahalar ɗakkosu da gujewa zafin saharar ne da yawanta.." "Sir bazasu fahimta ba, irinku ƙalilanne ke fahimta saboda zukata masu ƙyau da ALLAH ya baku. Amma wlhy a tsayin rayuwata ban taɓa cin karo da mutum mai tsananin kishin ƙasa da son cigabanta ba irin Haysam. Mutum ne shi mara tsoro, mai tsayawa akan gaskiyarsa koda kuwa ace zata ƙona shi. Sannan yana so da sauri, shiyyasa yake komai da sauri. Amma na rasa miya tare musu?"........✍️ 5
........."Bai tare musu komai ba, gaskiyarsa da rashin tsoro yasa suka kasance su a tsoracen. Sannan an tasirantar da siyasa ne a cikin al'amarin a yanzu." "Shima abinda ya gaya min kenan, da nace masa zaluncine yasa suka rufemu. Yace ba zalunci bane siyasa ce kawai". "Ƙwarai da gaske maganarsa gaskiya ce, wasan ya canja daga yanda ya fara ya koma siyasa saboda an janyo hankalin wasu masu zuciyar kwaɗayi a cikinsu da kuɗi, sannan duk masu son ayi gaskiya an daƙilesu. Kaga dai sunyi duk yanda zasuyi sun hana wasu a cikin adalan shugabanin komawa tenure ɗinsu ta biyu, sun ƙalama ministoci da yawa sharrin da sai da suka bar ƙasar. Yanzu sun ɗora wanda suke so akai gashi har sun shiga shekara ta uku akan mulki, sun samu damar yin yanda suke so. Duk da lafawar hare-haren nan dakaga an samu akwai manufar da suke son cimmawa ne kawai, sannan sun sami abinda suke so wato cigaba da haƙar ma'adanai." "ALLAH zai mana maganinsu Sir". "In sha ALLAHU Imran, sai dai muma dolene mu tashi tsaye sannan ne zamu samu taimakon UBANGIJI. Dan tabbas in dai ba wani motsi mai girma mukai ba akwai babbar matsala da zata iya faruwa anan gaba. Ciki kuwa harda halaka Haysam dana samu tabbacin suna shirin yi." Cikin matsanancin tashin hankali Imran ke kallon General. Shima sai ya jinjina masa kan nasa. "In sha ALLAHU bazasu samu dama ba. Shiyasa ma na yanke wani hukunci. Wanda ta hanyarsa ne kawai naga mafita a fitowar Haysam daga prison". Imran ya ture plate ɗin abincinsa gefe, cikin bugun zuciya da rawar murya ya ce, "Sir wane irin hukunci ne wannan? Wlhy komai wahalarsa da haɗarinsa zan kasance tare dakai muyi domin kuɓutar da Haysam, dan raina fansa akan Haysam Abdul-rasheed Shehu". Cikin jinjina kai da sauke ajiyar zuciya General ya ce, "In sha ALLAHU wannan abotar taku sai kunci moriyarta mai tsaho a duniya sannan ku kasance a aljanna tare. Imran a yanzu kaf hanyoyin fitar da Haysam na bisu amma duk an rufe su ta hanyar makirci da ƙarfin ikon masu mulki. Dan haka nai nazari nima da gane hanya ɗaya muma ta rage mana. Wato irin hanyar da sukabi suka rufe kaf ƙofofin muma dole ne mubi tanan mu buɗe ƙofifin. Dan tabbas Haysam shine ƙashin bayan karya waɗan nan mutanen da shirye-shiryen su. Badan wasu bazasu iya bane, badan babu kamar Haysam bane, badan babu masu irin gaskiyarsa da jarumtarsa bane. Akwaisu da yawa cikin matasan sojojinmu dama sa'anninku ɗin, kai harma wanda suka fishi duk za'a samu. Kawai Haysam shine ya fara musu illa, yay musu sani na haƙiƙa, sannan yake firgitasu da basu tsoro tunda har suka tattara duk karfinsu wajen son ganin sun danne shi. Dan haka ina son shi daya fara wannan aikin ya ƙarasa shi dan su san ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...... Sannan da gaske shi ɗin KIƊA A RUWA NE MAI TADA HANKALIN SU. Dan haka Imran zan shiga SIYASA.." "SIYASA! Sir?!". "Ƙwarai kuwa Imran SIYASA. Dan yanzu haka na fara shiga jikinsu, har wasu a cikinsu sun ɗorani a shawarar fitowa ɗan majalisan tarayya. Na kuma yarda na amince musu, sannan zan musu duk yanda suke so dan babbar kujerar mai gaba ɗaya nake hari nan da shekaru huɗu masu zagayowa bayan an gama tenure mai zuwa bayan wannan". "Turƙashi". Cewar Imran yana zuba tagumi da hannu biyu. Murmurshi Genaral yayi mai faɗi, cike da dattako ya ce, "Yaƙin namu ne mu duka. Wannan shine hikimata ta cewa kada ka ajiye aikinka. Dan a yanzu haka kaima suna shirye-shiryen ƙara maka girma. Acewarsu zasu fara jan ra'ayinka dan zafafa zuciyar Haysam da ɗarsa masa cewar baka tare da shi. Su kuma samu sirrikansa...." "ALLAH ya kiyaye, bana buƙatar ƙarin girmansu...." Ƙaramar dariya Genaral yayi, cikin katse Imran ya ce, "Kwantar min da hankalinka mazan fama. A yanzu da bamu da zaɓin daya wuce maida kammu sakarkaru. Ta haka ne kawai zamu kamo bakin zaren, mu kuma tantance su waye ainahin munafukan. Su waye masu gaskiyar? Sannan mu cimma burin mu kuma. Amma na baka dama kaje kai tunani mai zurfi. Sannan zan sake shiga da fita dan ka sake ganawa da Haysam a karo na biyu, ka nema shawara a wajensa kuma. Imran idan wani zai iya gane zuciyar Haysam daga cikin duhun prison, kai ne. Ka koma. This time, ka saurare shi da idon zuciya, ka kuma gaya masa shirin mu da manufar mu. Na tabbatar zai bamu goyon baya shima."
Wannan maganar ta General Yusuf ita ta kulle ma Imran baki tun jiya. Haka kuma ya cigaba da yawo da ita tsakanin safiya zuwa marece na kowane rana. Har ALLAH yasa a karo na biyu ya sake samun damar ziyartar Zak-Shadow a karo na biyu bisa tsayawar Janar ɗin......
<<•>><<•>>•<<>> A PRISON GATE...
Ranar ta yi zafi sosai kasancewar ya tareta ne a lokacin zafin nata. Domin kuwa ƙarfe ɗaya ne a lokacin. Dan daga massalaci ma ya wuce special Military Corrections Facility.... ɗin. Wani nauyi ya lulluɓe zuciyar Imran tun daga lokacin da ya taka ƙasa ya ƙarasa gaɓar ƙofar babban prison ɗin. A karo na biyu cikin satittika biyu yana zuwa wurin da rabin zuciyarsa ke tsare. Ya shigar da sunansa kamar zuwan farko, aka tabbatar da izinin shigarsa bisa doka. Daga haka aka rakashi zuwa ɗakin ganawar kamar na wancan lokacin. Wurin nan buɗaɗɗe da babu shamakin gilashi a tsakaninsu kamar saura, kujera biyu, teburi a tsakiya. Cikin mintuna kaɗan aka kawo Dada. Hannayensa daure da handcuffs, fuskarsa ɗin nan a ɗaure kamar yanda kowa ya santa, sai dai a yanzu babu zafafawa kuma ba murmushi. Amma idanunsa sun kasa ɓoye gajiyar shekaru uku da wahalar ƙuncin rashin aikin daya zamewa jiki da zuciya sabo. Imran ya zuba masa ido batare da yace komai ba. Shi ma Dada bai yi magana ba har sai yada ya zauna. Sai wani ɗan shiru mai zurfi ya cika ɗakin. A hankali Dada ya zubama Imran ɗin juyayyun idanunsa, kamar yanda shima Imran ɗin ke kallonsa. "Ni karka cinye ni". Dada ya faɗa yana hararar Imran. Murmurshi Imran yayi a karo na farko. Shima sai ya furta, "Da zaka haɗiyun ma ai da na huta. Kaga sai mu fice abinmu batare da kowa yaji ya gani ba mu koma gida kaga yanda Mammah ta ƙara ƙyawu. Nimrah da Ruƙayya dasu Asma'u da Khalifanka suka girma. Ma'aruff da Ja'afar suka zama magidanta harda ƙyawawan yara masu kama da kai da duk suka ci sunanka da sunana. Ammar da Bilal suka sake girma. Mu'azz ma ya fara zama ɗan saurayi. Ummi da Momy da Mimi sun sake haihuwa, Biebah ta sake zama budurwa ƴar jami'a. Nabeeha na cikin kewa da son ganinka." Wani sassanyan murmushi Dada yayi yana mai girgiza kansa da sake tsatstsare Imran ɗin da idanunsa. "Shike nan ka faɗa kaji daɗi, ALLAH ya albarkaci rayuwarsu gaba ɗaya. Ya sanya farin ciki da kwanciyar hankali a ciki. Ina fatan Mammah bata da wata damuwa?". Shima cikin murmurshi Imran ya ce, "Alhamdullahi Mammah na cikin ƙoshin lafiya. Duk da dai an shiga ruɗani a farkon ƙaddarar, amma zuwa yanzu zuciya ta amsa da hannu biyu kuma ALLAH ya saka nustuwa da farin ciki. Sai dai addu'a ba'a gajiya ba. Dan kwanan nan ma suka dawo daga Umrah su dukansu dan har Nimrah da Ruƙayya ba'a bari ba. Kasan yanzu sune autocin Mammah, suna zuba shagwaɓar su yanda suke so da rashin ji. Dan a wata biyu kawai da tawa dawowar an gayyaceni makarantarsu karo na huɗu kenan akan rashin jin su. Mammah kuma da anyi magana ta tare ko ina ta hana ai musu faɗa. Koda yake suma su Ja'afar ɗin babu mai son musu faɗan, sai Hafsa ce ma ke ɗan lallasasu idan sunje gidan shiyaysa basa son zuwa can su kwana". A mamakin Imran murmushi mai faɗi Dada yayi a yanzu fiye dana farko har haƙoransa na bayyana. Ya ɗan taɓe baki da faɗin, "Ai nasan za'a rina. Dan tun a ranar farko na fahimci kam hali yazo ɗaya. Shike nan dai Mammah ta cika min burina na ƙwace Ruƙayya." Imran ya ɗan murmusa shima da faɗin, "Ta cika maka kam ita da Nimrah, dan Nimrah ta taka rawar gani wajen janye hankalinta da ƙyau". "ALLAH ya raya su". Ya faɗa a taƙaice. Imran ya lumshe ido, muryarsa a raunane ya ce, "Amin ya rabbi. Gani na dawo Zak.... Ina bukatar ka bani dama dan fahimtar abin da bakace ba a ranar farko." Dada ya ja dogon numfashi. Ya jingina da kujera kamar mai yaki da wani abu a zuciya. "Babu abin da zan iya faɗa da baki ba tare da ya cutar dani ko ya cutar da ku ba". Imran ya jinjina kai. "Na fahimta, amma ka sani nazo jin duk abinda zaka iya rubutawa… Sannan a wannan gaɓar faɗar tafi amfani, dan nima ina tafe da muhimmiyar magana. Idan ba yau ba, yaushe?" "Haka ne". Cewar Dada yana zaro wasu murɗaɗɗun takardu daga ƙarƙashin rigarsa ta prison. Kai tsaye ya miƙa takardar ga Imran kamar yana mika zuciyarsa. "Ka sakata a jikinka dan nasan bazasu bari ka fita da ita ba. Na rubuta wannan cikin shekaru uku. Babu kuma wanda ya kamata ya gani sai kai." Hannu Imran ya miƙa masa shima, bai karɓa nan take ba saboda nauyin da kalmar "Sai kai" ta yi masa. Idanun Dada suna cike da gajiya amma akwai hasken wanda ya tsaya tsayin daka, wanda bai fasa ba, baya jin kuma zai fasa ɗin koda na daƙiƙa guda ne, duk da cin zarafi, yaƙi, da shekaru uku na shiru sukazo masa da shi. Ba wanda suka killacesa anan yake kallo ba ƘASAR da masu tasowa a GOBEN ƘASAR kawai yake hange da kallo. Shiyyasa ya yarda zai sadaukar wajen ginawa tare da duk mai zuciya irin tasa, domin ƴaƴa da jikoki su amfana a bayan rayuwarsu. Imran ya karɓi takardar cikin sauke ajiyar numfashi. Kallonta yake cike da nauyi saboda sirrikan dake cikinta. Yana buɗewa ya ga layuka marasa yawa amma masu nauyi: Sunaye. Abubuwan da suka faru. Kurakurai. Shakku. Hujjoji. Da kalma guda ta ƙarshe. Sai kawai ya nannaɗeta kamar yanda ya bashi ya ɗaga rigarsa ya sakata a cikin ɗammararsa ta soja. Imran ya haɗiye wani abu mai zafi da ya tsaya masa a makoshi. Cikin ɗacin murya ya ce, "Zak… me kake so mu fara? Ina kake so mu fara kalla ko tunkara?". Dada ya ɗaga kai ya kalle shi kai tsaye. Wannan kallo Imran bai taba mantawa da shi ba tun lokacin da suka yi fice-ficen yaki tare. Muryar jarumta ta shiga kunensa da izza da tabbacin MAZAN SUNA NAN A MAZANSU NA FAMA. GWARAZA KUMA BARADAI Masu tsayayyar zuciya da tsayayyar KALAMA..........✍️ 6