Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 3
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 3: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 3. .........."Ku fara da gaskiyar Ojo. Akwai wani abu da bai dace ba. Kuma akwai…
3,436 words
.........."Ku fara da gaskiyar Ojo. Akwai wani abu da bai dace ba. Kuma akwai hannaye da yawa da suka fi mu ƙarfi har a cikin gida. Sai dai fuska biyun su tasa sun zame mana masu lulluɓin biri". Shiru ya cika ɗakin. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Imran. Cikin kasa haƙuri ya furta, "Idan kuwa har akwai masu fuska biyu zan kasance mai tsoro da shakkar mu'amulantar kowa?". "Wannan shine gaskiyar magana, amma a ciki akwai ɗaya tamkar da dubu. General Yusuf Shu'aibu Tafida. Col. Haydar Galadima (Faro), Brigadier General Abraham Yohana, yaranmu Dabo, Yusuf. Amma saura duk ka ajiye kowa. Akwai saƙo a ɗakina na ajiye maka, idan ka haɗa da wannan zai baka abinda nake buƙatar ka fahimta. Dan na tabbatar daga yau bazasu sake barinka ka ganni ba." Da ƙyar Imran ya iya furta, "Janar ya shiga SIYASA..." Cak numfashin Zak-Shadow ya tsaya, hakama bugun zuciyarsa kafin su dawo a tare. "SIYASA?!". Ya furta yana tsatstsare Imran da idanu. Kai tsaye Imran ya jinjina masa kai. Sai kawai Dada yayi murmurshi tare da wani ɗan lumshe idanu sannan ya sake buɗesu luuu akan Imran. "Na amince kayi aiki da shi Imran...." Cikin tsatstsareshi da idanun shima Imran ya ce, "Zak… kana nufin kaci karo da mutanen da kowa yaji tsoron ɗaga su?". Wani ƙaramin murmushi mai zafi, mai ɗaci ya bayyana a gefen labban Dada. "Ni ba wanda nake tsoro, Imran. Amma gaskiya… ita ce abin da suka hana ni gani tsawon shekaru uku. Ni kaina kuma na yarda da hasashen General, ta irin hanyar da suke kai, kawai zamu bi mu gano su, mu kuma yaƙe su" ya ɗanyi shiru na sakan biyu. Sai kuma ya cigaba da faɗin, "Yau na baka wannan rubutun. Ka tafi da shi. Kada ka bari kowa ya gani a yanzu har Janar. Dan kai kaɗai nake son kayi waɗan nan binciken" Idanu kawai Imran ya kafeshi da su ya ma kasa magana. Wato idan Zak.. ɗinsa na wani abu a wasu lokutan yakan ga tamkar mai aljanu ko mai gani har hanji da yara kan faɗa. Kai har ɗan duba ma zai iya kiransa, amma yasan duk ba haka bane, tsabar kaifin basira ne kawai da iya sanin kan duniya da mutanen cikinta da ALLAH ya bashi. Shi ko Dada ganin kallon da Imran ɗin ke masa, sai kawai ya jingina da kujera a hankali ya lumshe idanunsa. A haka ya ce, "Ban san miya baka mamaki ba ka tsaya kana kallona bayan lokacin ka ƙayyadadde ne. Idan rana ta yi zaka gane me yasa naga mutuwa ta fi wannan shari'ar sauƙi." Imran ya kasa magana yanzun ma, a haka har lokaci ya ƙare, masu tsaronsa suka buga ƙofa. Miƙewa kawai Dada yayi zai bar gurin, sai kuma ya tsaya ya kalle shi for the last time yasan kafin a sake ganin juna sai bayan shekaru. Dada ya lumshe ido tare da furta masa a hankali kamar sirrin da baya buƙatar iska ta ɗauka zuwa gaba a tsakanin su. "Ka zama hasken da nake bukata a waje. Ka cigaba da zama UBA kuma nagartaccen MIJI a cikin GIDA". Daga haka yay gaba batare da ko waiwayen Imran ba. Shi ko Imran ya kasa motsi sai kai-kawo furucin ƙarshe na Zak-Shadow ɗin ke masa amsa kuwwa a cikin kai, dan magana ce a dunƙule ya bashi kuma mai ƙarfi.....
(((★)))(((★)))(((★))) ★ 2021..... ★
Duk wanda yasan gidan a shekarun baya takwas da suka shuɗe yanzu idan ya zo ba lallai ya gane ba. Domin kuwa gidan nan da Mammah da yaranta tara mai sassa biyu kacal a yanzu ya zama mai sassa da yawa sakamakon iyalanta da suka ƙara yawa. Kamar yanda Dada ya barma Imran wasiyyar dawo da ginin su Ma'aruff a cikin gida a wacan lokacin hakan ta tabbata, duk da kuwa shima Imran ɗin dole ya bar ragamar a hannun Uncle Nasiru sakamakon prison ɗin daya shiga na shekara uku. Duk da suna cikin ɗacin yanayi Uncle Nasiru yayi abinda ya dace harda kuɗin aljihunsa. Anyi bikin Ma'aruff da Ja'afar da amarensu Shariffa da Lailah, sai dai bikin baiyi armashi ba sakamon jarabawar da wannan ahali suke ciki a wancan lokaci na rasa jigon gidan da suke ma kallon Uba bawai yaya kawai ba. Amare sun tare a gidan Mammah kowace da ɓangarenta, kuma Alhamdullah dukansu masu tarbiyya ne da suka fito daga gidan tarbiyya. Dan kuwa akwai abubuwa da yawan gaske da suka bambanta su da surukar gidan ta farko Nabeeha. Mammah mace ce mai sauƙin kai da sanin haƙƙin ɗan adam, tana da zafi idan kace zaka kawo mata wargi, dan in har kaji muryarta a sama lallai an kaita maƙura ne. Duk wanda yazo jikinta ya zama ɗa na halak da zata haɗe da nata ƴaƴan ya riƙe babu bambanci a ciki, wannan yasa biyayya da nutsuwar Aunty Shariffa da Aunty Lailah ya basu fiye da abinda suke zato da farin ciki a gidan aurensu. Dan kuwa suna matuƙar kiyaye al'amarin Mammah a matsayinta na uwa, hakama ƙannen su Ma'aruff sun maida su ƴan uwansu na jini ba dangin miji ba, sai hakan ya bada masalaha da shaƙuwa mai ƙayatarwa da birgewa a wannan gidan, idan ka cire rashin Dada dake zagaye da zukatansu dan suna jin hakan a ransu a kowacce rana tamkar sabo. Babu ranar banza da zata zo ya wuce ba'ai hirar Dada ba, za kuma ka samu hatta su Ma'aruff dake magidanta kuma manya yanzu a gidan sai sunyi kuka suma. Mammah ce kawai jaruma mai danne komai a gabansu sai dai idan tana ita kaɗai ta share hawaye. Shekarar su Lailah ɗaya a gidan duk suka haihu, kuma Alhamdullah haihuwar tasu babu wani nisa tsakani. Dukan su yara maza suka samu, kuma yaran sunan Dada da Imran aka saka musu wato Haysam da Imran. Sai dai ana musu alkunya da Abees da Aheel. A shekarar da Imran ya fito bayan ya gana da Dada sau biyu sannan suna cika shekara uku-uku da aure suka sake haihuwa, sai dai wannan karon Shariffa mace ta samu, ita kuma Lailah Namiji. Bayan haihuwar tasu ne kuma Imran ya sake tada saban aikin gyaran gidan na su Mammah. Dan kuwa gaba ɗaya aka rushe sashen Mammah dana su Zak-Shadow tunda Nabeeha ba zama take ba sai jefi-jefi take zuwa gidan, shima ɗaukar wani abu ne ke kawota, wani lokacin ma sai tazo ta fita su Mammah basu sani ba. A wannan karon ne akama gidan gyara fiye dana baya, dan komai da fasalinsa an canja, hatta Ammar da Bilal an musu nasu ɓangaren. Sai ya zama anyi sashe huɗu ta can baya, an fitar da gate ta wancan Street ɗin, ta cikin gida akwai katanga tsakanin ɓangaren su Ja'afar ɗin dana su Mammah da Dada da suma suke su biyu. Tsarin ya bada kamar gida biyu. Dada da Mammah a sashe ɗaya, su Ma'aruff su huɗu a sashe ɗaya sai dai kowa da part ɗinsa, akwai katanga tsakaninsu amma akwai ƙofar da zaka iya shigowa sashen su Mammah basai ka zagaya ta wajen gate ba. Wannan gyara shine ya sake sauya gidan Mammah daga mai sashe biyu na talaka mai ƙaramin ƙarfi zuwa na masu rufin asiri da wadatar zuci a yanzu, ga irinmu ma talakawa kai tsaye zamu kirashi ana masu kuɗi.....
))))(((()))))((((
A ɓangaren Imran yanzu haka dai shekarunsa biyar kenan da ganawa da Dada dake cika shekaru 8 a prison, kamar yanda Dada ɗin yay hasashe ya faɗa kuwa ba'a sake bashi damar ganinsa ba. Babu irin shiga da fitar da baiyi ba amma sun hana masa damar sake ganinsa. Dan haka Janar ya zauna ya lallashesa akan yayi haƙuri komai yana da lokacin sa. Badan hankalin Imran ya samu kwanciya ba ya haƙura. Sai dai ya maida hankali akan binciken dukkan abubuwan da Dada ɗin ya bashi. Sannan yaje ya ɗauki saƙon daya ce ya ajiye masa. Inda saƙon ya fahimtar da shi abinda Dada ya shirya. Dole ya ajiye batun damuwarsa da kewarsa a gefe ya maida hankali akan aiki yanda ya kamata....
Burin Janar ya cika na shigewa cikin siyasa tsundum da sha'anin ƴan siyasa. Cikin nasara ya lashe kujerar da aka tsaida shi a takarar ɗan majalisan tarayya. A yanzu haka yayi ɗan majalisa shekara huɗu kenan. A kuma yanzu haka ana shirin sake buga tambarin sabon zaɓe, babban shirinsa kuma shine fitowa takarar shugaban ƙasa. A gefe kuwa Imran ya sake samun girma zuwa Colonel saboda kwantar da kai da yayi shima bisa shawarwarin General ɗin dana Dada.....
✷✷>><<✷✷>><<✷✷ ★SCHOOL★
"Yau sai naga waye ubanku a cikin ƙasar nan, ƴan iskan yara kawai kamar wasu ƴan daba ku kama min yarinya da duka, koni dana haifeta da ubanta bamu taɓa dukanta haka ba. To wlhy idan kuna taɓa wasu ku zauna lafiya yanzu kun taɓoma kanku kuwa, dan har prison sai na saka ubanku yayi bama ku ba......." "Ranki ya daɗe dan ALLAH kiyi haƙuri, mahaifinsu bashi da laifin komai sune sukai miki ba daidai ba. Wlhy mu kammu yaran nan sun kai mana wuya a makarantar nan, kawai dai babu yanda muka iya ne....." "Oh babu ma yanda kuka iya? Wato tsoronsu ma kuke ji saboda uban su ne shugaban ƙasa, yara na irin wannan ta'addacin amma kuke iya barinsu a cikin makarantar ku harda faɗin babu yanda kuka iya....." Kasa cewa komai principal yayi, sai ma haƙuri daya cigaba da bama hamshaƙiyar matar da kallo ɗaya zakai mata kasan matar babban mutum ce a ƙasar. Dai-dai nan akai knocking ƙofar ofishin, principal ya bada izinin shigowa. Wani matashin saurayi ne da alamu suka nuna shima ma'aikaci ne a makarantar, yay sallama ya shigo sannan ɗalibai biyu dake bayansa riƙe da wata matsakaiciyar budurwa da bata wuce 15years ba suma suka shigo. Zaram matar ta miƙe tai kansu, jikinta har rawa yake ta kamo hannun yarinyar da suka riƙo kanta naɗe da ƙaton bandeji, fuskata kuwa da ganin yanda tai suɓu-suɓu kasan tasha maruka da kuka ta kuma ci bugu, dan idanun jazur suke suma luhu-luhu. Jikinta yarinyar ta faɗa, yayinda ita kuma ta ɗauki dogon salati ta dire tana mai ɗago yarinyar a jikinta.........✍️
Wannan aiki nasan sai Zakanya da vice ɗinta Damisa🤣.
7
.......Cikin matuƙar bala'i da ihu matar ta ce, "Babbar bala'i kai, wlhy bazan yarda ba, dolene ma yaran nan suje police station dan sai nayi shari'a da su....." Da sauri matashin malamin nan ya katseta da faɗin, "A'a ranki ya daɗe kada ai haka. Mudai bari a zauna dasu aji miya haɗasu, duk da nasan Naja'atu da Ruƙayya fitinannun yara ne amma basa faɗa sai da dalili..." "Oh yanzu na fahimta, to kodai kaine ka sakasu su aikata ma saboda kana nemansu? Dan ba abin mamaki bane idan muka dubi yanda malamai suka koma fasiƙanci da ɗalibansu a makarantu". "Innalillahi wa'ina ilaihiraji'un, Hajiya wane irin magana ce wannan? Dan na faɗi abinda yake gaskiya kuma sai ki aibantani da yaran da suke tamkar ƴaƴanki. Amma dai....." "Teacher Khalil ya isa haka. Ka fahimta kawai ranta ne ya ɓaci. Yanzu dai ka kira gidan su yaran sannan azo min da su nan yanzu nan". Sosai ran wanda aka kira da Teacher Khalil yake a ɓace da zancen matar, sai dai bai sake cewa komai ba ransa na ƙuna ya shiga neman layin wanda yasan Yaya ne gasu Ruƙayya, amma fin kira goma bai shiga ba. Ganin ba samu zaiba principal yace ya sake kiran wata number mana, canja kiran yay zuwa ɗayar number da yake da ita, cikin sa'a kuwa ta shiga. Koda aka ɗaga cikin nutsuwarsa yay bayanin daya dace, a ƙarshe ya sanar da ana buƙatar ganin wani nasu babba daga haka ya ajiye wayar ya fita a office ɗin....
Mintina kaɗan Teacher Khalil ya dawo, sai da ya shigo sosai matasan ƴammata biyu suka bayyana. Ta gaba fara ce tas kuma ƙyaƙyawa, siririya daga ganin fuskata kasan zatai rashin ji. Wadda ke biye da ita ma da zasu iya zama kai ɗaya black beauty ce masha ALLAH, itama dai daga ganin fuskar nan kasan zatai tsiwa. Su duka sanye suke da uniform skirt peach color da farar riga long sleeve shirt, sunyi zanzaro da skirt ɗin, sai ɗan ƙaramin baby hijjaf fari shima da iyakarsa matashin ƙirjinsu da ake kiran kamar su da suna ƙwailoli. Daga ƙasa safa ce doguwa data zo har gwiwar ƙafa saboda skirt ɗin nasu kaɗan ya zartar gwiwar sai takalman sandal baƙaƙe na ƴan makarnta. Ga shi dai uniform ne ana saka shi badan ado ba, amma yayi musu matuƙar ƙyau da zaunawa a madaidaicin jikinsu ɗas kamar ka lashesu. Ga wani ƙamshin turare mai sanyin daɗi na fita a jikin nasu da gogaggun uniform ɗin su da suka sha karin guga kamar batun safe suka sakasu ba. A makarantar ba'a dukan ɗalibai sam, dan makaranta ce ta kuɗi kuma ta ƴaƴan manyan ƙasa. Duk wanda aka gani a school ɗin lallai ubansa yaci ya ƙoshi ne. Shiyyasa daga ƴaƴan masu mulki saina jami'an gwamnati dana manyan ƴan kasuwa. Dan makarantar ma ta baƙin haure ce ƴan ƙasar waje ba ƴan ƙasa ba. Rabi da kwatar malaman cikinta duk masu jajayen kunne ne, sauran tsiraru irinsu Teacher Khalil ne kawai ƴan ƙasa baƙaƙen fata, sai kuma shi kansa principal ɗin shima dai ɗan ƙasa ne. Da farko idanu principal ya zuba ƙyawawan ƴammatan biyu, yayinda matar nan ke zuba musu uwar harara kamar idannunta zasu zubo. Hakama ƴarta dake lafe a jikinta tun shigowar yammatan dake sa'ointa ta sake mannema uwarta tana harararsu. Suko sun wani tamke fuskoki suna cika suna batsewa. Haɗa ido baƙar tayi da yarinyar, tako watsa mata uwar harara da nunata da yatsu biyu alamar saita tsokale idon... Wani irin takaici ya sake mamaye zuciyar uwar, dan ta kasa gane ita zata tsokalewa ido ko ƴar tata tunda itama hararar take. Baki ta buɗe zatai magana principal ya katseta sakamakon ambaton sunan yaran da yayi. "Ruƙayya Imran Abbas". A cinkushe farar tace, "Yes Sir!". Ya sake maida idonsa ga baƙar ya ce, "Naja'atu Muhammad". Itama cikin tura baki tace, "Yes Sir". "Ku miyasa bakwa jin magana ne, yara kamar ibilis ne malamin ku kullum cikin kawo ƙararku ake. Yanzu ku duba yanda kuka fasa mata kai, inda abin yazo da ƙaddara fa...?" "Sir sai kun haɗa da addu'a fa a lamarin nan, dan lokuta da dama aljanun mu ne ke wannan aika-aikar bamu bane ba ko my Trouble Buddy?". Ta ƙare maganar da juyawa tana kallon Ruƙayya. Caraf Ruƙayya ta amsata da "Hakane wlhy My Trouble Queen, Sir wani lokacin bayin kammu bane ba. Amma zamu faɗa a gida su ƙara dagewa da addu'a da neman magani ko zamu nutsu. Wani lokacin kuma yaran ne tarbiyyarsu bata cika ba shine muke ɗan daidaita musu sahu." Kallon kallo aka koma tsakanin Principal da Hajiya mai ƴa, yayinda Teacher Khalil daya san halin kayansa ya kauda kai yana murmurshi kawai. Yarinyar kuwa kuka ta fashe da shi, "Wlhy Momy ƙarya suke, babu wani aljanu da suke da shi. Haka suke yi sai sun gama rashin mutuncinsu sai suce aljanun su ne suka tashi." "Barsu Baby zan nuna musu su ƙananun ƴan iska ne, badai sun ce su basa ji ba." tai maganar tana ɗaukar wayar ta. Ƙoƙarin dakatar da ita principal keyi amma taƙi saurarensa. Abinda zai baka mamaki ko'a kwalar rigar Ruky da Nimrah. Tsabar sun shahara ma chocolate Nimrah ta ciro a aljihun gaban rigarta ta shiga barewa, koda ta gutsira sai ta miƙawa Ruky ma ta gutsira hankalinsu kwance suke ci kuma. Takaici kamar ya shaƙe principal, bai iya sake magana ba kawai ya zuba musu ido.....
★★★
Da steps uku-uku yake tsallako stairscase ɗin ƙayatacen falon dake fidda ƙamshi mai ɗan karen daɗi. Waya ce manne a kunnensa, sai da yazo gab da direwa ya cire wayar yana cusata a aljihun jallabiyar jikinsa. Ko kaɗan bai dubi sashen kujerun falon ba balle ya san akwai mutane ma. Fuuu ya wuce kai tsaye ga ƙofar fita abinsa... "Wai saurin mi kake haka kamar zaka tashi sama ko ganin mutane bakayi?". Juyowa Ammar yayi dai-dai yana gab da fita a ƙofar falon gaba ɗaya, cikin ɗan dafe kai da furzar da iska ya dawo cikin da baya dan shi sam baima lura da su ba saboda tsabar hankalinsa baya a jikinsa. "Sorry Yaya wlhy ni ban ganku ba ma. Daga makarantar su Ninah aka kirani wai ita da Ruƙayya sun fasama wata yarinya kai da duka har iyayenta sunje school ɗin da ƴan sanda, shine principal ɗin ya kirani saboda yanata neman layin Yaya Bilal bai shiga ba, shine nace masa baya ƙasar ne, da akace su bada number wani suka bada tawa". "Ya rabbi, anya wataran waɗan nan autocin na Mammah bazasu saka a tattare kaf jama'ar gidan nan zuwa station ba. Ni kam ba jiya Ja'afar yaje wata shari'ar tasu Tahafiz ɗinsu ba?". "Jiya ne wlhy Yaya Ma'aruff, dan bama a gama case ɗin ba yau sai Yaya J ɗin ya sake komawa suka ce." Kiran daya sake shigowa wayar Ammar ce ta hana Yaya Ma'aruff magana, shima bai ɗaga ba, sai kallon Yaya Ma'aruff ɗin da yayi. "Yaya bari naje sune suke sake kira fa. Da alama abin fa serious ne". "Nima ai banga ta zama ba muje kawai dama zanje wani wajene na biyo gidan amsar takardu wajen Mammah. Amma yau inaga sai na zane Ninah da Ruky a gidan nan, yara sai baƙin fitina saboda sunga Mammah na hana a duke su." Ƴar dariya Yaya Ammar yayi a karo na farko, dai-dai yana kama handle ɗin ƙofar ɗakin ya ce, "Ashe Mammah zatai ma kowa baki yabi titi a gidan nan, taɓa mata kafi autoci ai yaƙi ne mai zaman kansa. Yaya kaima nasan ka faɗa ne kawai ba iya dukansu zakai ba". "Ai ko yau zan baka mamaki". Yaya Ma'aruff ya bashi amsa dai-dai suna kaiwa ga mota....
✯✯>><<✯✯>><<✯✯ ★DUBAI★
"Yanzu ke dai Nabeeha ina nuna miki abinda zai fisheki amma kullum kina runtse ido ko? Shekara fin takwas idan na taroki nan sai ki zille nan kamar nice zanji daɗin rayuwar bake ba". Sake tsuke fuska Nabeeha dake kwance a gado tana sarrafa laptop ta sake yi. Shiru kamar bazata tanka ma Momyn nata ba sai kuma ta ɗago tana kallonta. Rai ɓace ta ce, "Momy wai mi kike so nayi ne? Aure kan aure ko bin mazan waje da aure na?. Kinfi kowa sanin fa Haysam ba saki na yayi ba, da auren kenan zan kula mutumin da ranki ke so dan kawai yana da kuɗi yana kuma baki?". Zaune Momy takai kusa da ita, cikin kwantar da murya ta ce, "Ni ba haka nake nufi ba Nabeeha, taya zan so ƴar cikina tabi maza ne. Kawai dai ina son ki farka daga wannan nannauyan barcin naki. Yaron nan shekara ɗai-ɗai har ashirin da biyar aka yanke masa a gidan yari, a hakan ma baki da tabbacin zai fito. Ki duba yanzu shekarunsa takwas kenan, Imran da yake ubansa mai kuɗi ne shekara uku ya fito, shi ko ubanwa ya sani ko ya sanshi, manyan nasa ma duk ya bisu ya zage da rashin mutuncinsa da girman kai. Kina ganin da ƙuruciyarki da ƙyawunki zan bari ki ƙare rayuwarki a jiransa ne. Ganinsa ma ya gagareki kwata-kwata. Amma ki duba mutumin nan yanda yake mutuwar son ki, hotonki kawai ya gani a waya ya haukace tsahon shekaru kuma bai taɓa fushi ba. Ƙyaƙyƙyawan Balarabe jinin mulki ga kuɗi tamkar sune ƙasar takawar sa, ƙyawawan mata nawa ƴan uwansa larabawa ya watsar yace kece zaɓinsa. An kawo masa ƴaƴan sarakuna kala-kala a dauloli daban-daban na larabawa amma ko kallonsu bayayi. Ya nace sai ke, ke ɗin nan da kika taɓa aure tsahon shekaru a gidan miji, ƴar Africa, Africa ɗin ma a ƙasa irin tamu, a ƙasar tamu ma a yankin mu da tsiya ta mamaye. Haba Nabeeha kima kanki faɗa wlhy. Idan jirgi kikace kina so na kanki mutumin nan sai ya baki shi, kalla gidan nan da muke ciki fa ƙyauta ya ɗauka ya bani shi batare da yaji ko ɗar ba. Shi wancan matsiyacin da ya rufe idonki in ce ko mota bai taɓa siya miki ba, hasali ma gidan da kuke ciki da kuɗin ubanki aka gina shi. Saboda ya nuna miki shi tattacen ɗan iska ne gagararre ya auri ƴar cikinki. Idan zaki dawo hankalinki ki dawo tun kan lokaci ya ƙure miki. Idan ba hakaba zakiyi dana sani a lokacin da kika rasa Adeel shi kuma aka tabbatar miki ya mutu a gidan yarin shasha kawai".. Ta miƙe fuuu zata bar ɗakin cike da takaici da baƙin ciki. Dan gaba ɗaya ta fahimci baƙin cikin cigaba ƴar tata take mata.........✍️ 8