Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 4
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 4: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 4. .......Adeel ibn Ubaidullah Qureshy. Cikakken balarabe ne ɗan asali gaba da…
4,342 words
.......Adeel ibn Ubaidullah Qureshy. Cikakken balarabe ne ɗan asali gaba da baya. Jinin sarauta dan kuwa daula babba suke da ita a yankin larabawa. Sannan zuri'arsu zuri'a ce mai ɗunbin dukiya da kaso huɗu na arziƙin Dubai yana da alaƙa da shi. Adeel irin gagararrun yaran nan ne da giyar mulki data kuɗi ke ɗawainiya da su. Dan kuwa iya shegen da yake zubawa a cikin Dubai ba'a magana. Harkar business ce ta haɗashi da Hajiya Hasiba, a dalilin First Lady da suke aminta. Sunyi wani zaman meeting Hajiya Hasiba ta kasance kujerarta kusa data Adeel a meeting room ɗin, irin ta ajiye wayarta a table sai aka irin kirata ɗin nan, bata ɗaga ba kasancewar suna a halin meeting har kiran ya tsinke, dai-dai screen ɗin wayar na komawa yanda yake ƙyaƙyƙyawan hoton Nabeeha dake a fuskar wayar Hajiya Hasiba ya bayyana. Sai ko karaf a idon sa. Cak ya tsaya da bayanin da yake ya zubama wayar ido, abokan meeting ɗin nasa sukaji shiru duk sai suka ɗago suna kallonsa, cike da basarwa ya ɗauke idanunsa ya cigaba da jawabinsa, amma bini-bini idonsa nakan screen ɗin wayar Hajiya Hasiba har aka tashi. Hajiya Hasiba ta lura da kallon da Adeel kema wayarta, amma sai bata kawo komai a ranta ba har suka wuce. Mizai faru da daddare kawai sai ga Firt lady ta kirata wai Adeel nason magana da ita, idan ba damuwa kuma so yake su haɗu. Mamaki ya kama Hajiya Hasiba, ta tambayi ko lafiya? First Lady ta bata amsa da cewar wai akan wani hoto ne da ya gani a fuskar wayarta sanda suke meeting. Sosai Hajiya Hasiba ta zaro idanu tana dafe baki, kafin ta ce, "Kai ranki ya daɗe ɗiyarki ce fa Nabeeha, kin san dai tana da aure kin kuma san waye mijinta da fitinarsa". Cikin nuna rashin damuwa First Lady tai murmurshi da faɗin, "Yo ALLAH na tuba sai me Hajiya Hasiba, aure nawa ne a wannan zamanin da shi gara babu. Ke dai kawai ai sha'ani. Mijinta kuwa girman kansa na banza ba ko sisi, kin san waye kuwa Adeel? Hummm na baki dama daga nan zuwa minti talatin ki bincika sai ki yanke hukunci. Ni dai na isar da saƙo yace zai turo mota a ɗaukeki a kaiki inda yake ". Daga haka ta yanke wayarta. Shiru Hajiya Hasiba tai na tsawon lokaci, dan babu abinda ke zuwa mata a zuciya da brain sai fuskar Zak-Shadow. Amma dai ta daure ta fara binciken waye Adeel kamar yanda First Lady ta bata shawara. Tun a ambaton farko kanta ya nema bugawa, jin nasabar gidansu kawai, jin ɗan waye daga zuri'ar daya fito. Data bincika arziƙin zuri'ar tashi kawai bama shi wadda ya mallaka ba bata san ta rikito a kujera ba tsabar rawar jiki. Har lokacin da za'a ɗauketa yayi bata iya ta dawo a hayyacinta ba saboda matsanancin mamaki. Ai babu ɓata lokaci ta shirya a gurguje tabi ɗan aiken. Ai ko kanta da zuciyarta sun nema fashewa saboda inda aka kaita matsayin wajen hutawarsa. Wani mahaukacin azababben garden ne da in ka kirashi da suna aljannar duniya bakai ƙarya ba. Ga masu hidima zagaye da wajen da wasu mugayen masu tsaro ya subahanallah. Ita dai haka aka kaita har inda yake jiki na ɓari. Kallo ɗaya yay mata ya maida kansa ga laptop ɗin gabansa, a haka cike da isa ya nuna mata wajen zama. Sai ta dinga jin kamar ba Adeel ɗin juya bane da sukai zaman meeting, koda yake ko'a jiyan dama yanda yake magana da isa da ƙasaita kasan akwai girma da izza. Amma a yau ɗin ba'a magana. Ya share fin mintuna goma sannan ya gyara zamansa, babu wani tauna harshe ko girmamawa kai tsaye yana kallonta ya furta, "Yarinyar dana gani kan wayarki nake buƙata, ina fatan ba hotonki bane dan naga kuna kama sosai, tsufa kawai zaki nuna mata". Kan Hajiya Hasiba a ƙasa tana murmurshi ta ce, "A'a bani bace. First born ɗina ce, sunanta Nabeeha". "Nice..." Ya faɗa cike da iskanci yana ajiye kofin hannunsa. Sai da ya ƙara busar iska ya cigaba da faɗin, "Za'a iya kawo min ita a yau? Zan bada ko nawa ake buƙata, daga biliyan 1 zuwa sama". Daburcewa Hajiya Hasiba tayi, cikin rawar murya ta ce, "Bazai yiwu ba matar aure ce, shekararta goma da mijinta haihuwa ce kawai basu taɓa yi ba." Kai tsaye ya furta, "Bani da matsala da aurenta, kawai tamin". (Ga ƙoshi ga kwanan yunwa) Hajiya Hasiba ta ayyana a zuciyarta, a fili kam sai ta daure ta masa bayani yanda zai fahimta, amma sai cewa yay taje dai ta gwada, ya bata wata ɗaya ma danta samu isasshen lokacin kawo masa ita. Daga haka ya sallameta da maƙudan kuɗaɗen da suka rikita lissafin ta, dan kuwa a yawon neman kuɗinta na shekara da shekaru bata jin ta taɓa mallakar ko kwata ɗin su. Hajiya Hasiba ta gama haukacewa, shiyyasa ta komo gida a rikice wancan lokaci. Ko bari ta huta bata yi ba ta hau haɗa kaya sai ƙasarta ta haihuwa. Tsaff ta zayyanema first Lady komai, ita ko ta bata dukkan shawarar da take ganin ta dace wato girgiɗe auren Nabeeha. Ta gamsu da wannan shawara kuwa, dan itama dai abinda take saƙawa a nata ran kenan tunda dama ba son zaman wancan auren ƙaddarar da Nabeehan keyi ba take. Dan haka ta nufo gidan Nabeeha a washe gari, sai kuma cikin sa'a ta tadda badaƙalar kawo Nimrah da ake ciki tsakanin Zak-Shadow da ita. Wannan yasata jin farin ciki dayin amfani da wannan damar amma Nabeeha taƙi, daga ƙarshe dai taci nasarar tsigeta a gidan suka wuce Dubai ɗin. Tunda Adeel ya ƙyalla ido yaga Nabeeha a zahiri ya sake susucewa, kai tsaye ya danƙarama Hajiya Hasiba gida daya amsa suna gida matsayin tukuy ci, sai dai me Nabeeha ko kallonsa batayi, karo na farko da yay ƙundunbalar tunkararta na kai tsaye ta sanar masa ita matar aure ce, kuma tana son mijinta. Daga haka ta tashi ta barshi. Bai damu ba, dan ransa ya kwaɗaitu matuƙa da ita, sai kawai ya tabbatar ma Hajiya Hasiba in har Nabeeha zata kashe aurenta shi ya shirya zai aureta. To da wannan fa aketa fama da fafatawa tsahon shekaru amma Nabeeha taƙi yarda, ta dage akan tana son mijinta. Duk yanda Adeel ke kashe musu mahaukatan kuɗi taƙi. Dan har su Ismat yanzu suna a Dubai ɗin, har kuma su Hajiya Hasiba ta nunama Adeel yace shi dai Nabeehar yake so. Ita da ƙanwarta mamansu Amima sunyi-sunyi amma ina abu yaci tura. Koda akace mijin Nabeeha na prison kum ba'a bari kowa ya ganshi har ita Adeel ya tabbata mata in har ta yarda suna haɗuwa zata saka ya bata sakinta shi kuma zai je har ƙasarsu ya shiga ya fita a barta ta gana da mijin nata, amma fa da sharaɗin takardar sakinta zata anso. Duk yanda Nabeeha ke kwaɗayin son ganin mijinta taƙi aminta da wannan zance, acewarta in ma zai ƙare rayuwarsa a can ne ita kuma zata mutu da aurensa, dan daya fito ma ya rayu da Nimrah matsayin mata ita gara yana prison ɗin su duka su rasa, tunda ta tabbatar taurin kansa da kuma magana ɗaya bazai saki yarinyar ba kamar yanda ya tabbatar mata. Wani lokacin kuma idan kishin ya ciyota sai taji kamar ta biyema su Momynta, amma dai tuna irin son da take ma Haysam kan saurin tsawatar mata. Dan duk kuɗin Adeel da mulkinsa, da kawunsa na jar fata, jar fatarma balarabe jinin sarauta idan ya tsaya gaban Haysam ɗinta sai ya raina kansa. Bawai dan Haysam ya fishi ƙyawun fuska bane, sam ko kusa ko alama, Adeel yafi Haysam ƙyawun fuska ita shaida ce, amma kwariji, cikar kamala, nagarta da tsantsar mazantaka tana a wajen Haysam ɗinta. Dan Haysam namijin gaske ne da ko cikin mazan jajayen fatan samun mai irin cikar kamalarsa sai an tona. ALLAH ya bashi darajar kwarjini da matuƙar kiyaye dokokin UBANGIJI da take da tabbacin sune linzamin gwarzan takarsa da kwarjini irin na ma'abota bautarsa da riƙe gaskiya. Idan tai sake ta barshi, zata ƙare rayuwarta bata samu mai maye mata gurbinsa ba dan kowane bawa da irin baiwasa ai.....
<<<<<<•>>>>>>
Isowar su Yaya Ma'aruff yayi dai-dai da isowar ƴan sandan da Hajiya ta kirawo. Zuwa yanzu malamai biyu sun ƙaru a office ɗin principal ɗin. Ɗaya class master ɗin su ne ɗaya Discipline master ɗin makarantar, sai dai kuma bashi da ikon duka a tsarin dokar makarantar, idan ɗalibi yay laifi mai girman da har aka zauna da shi iyakarsa bashi suspension ne kawai. Su Yaya Ammar na shigowa Nimrah da Ruƙayya suka zabura kansu. Sai dai hararar da suka shiga antaya musu ya sakasu nutsuwa kowacce ta tura baki gaba. Bayan kowa ya zauna su kan dai har lokacin suna tsaye an hanasu zaman. Hajiya zata fara babbotai principal ya dakatar da ita... "Hajiya kiyi haƙuri ga yayyensu nan sunzo, in sha ALLAHU kuma zamu ɗau mataki muma". "Bana buƙatar wani ɗaukar mataki anan, kawai ga ƴan sanda nan sun zo su tafi dasu, idan munje kotu sayi bayani tunda su basu da tarbiya". "Hajiya baza'ayi haka ba, kiyi haƙuri dai a tattauna a samu masalaha". Zata ƙara magana principal ya shiga roƙonta, dole tai shiru tana zuba musu harara. A karo na farko Principal yay ma su Yaya Ma'aruff bayani, a kusan tare shi da Ammar suka kalla Nimrah da Ruƙayya, Yaya Ammar ya ce, "Kune ke da aljanu?". Cikin tura baki Nimrah ta ce, "Eh Uncle Ammar, kawai basa tashi a gida ne sai makaranta. Kuma basa cutar da kowa fa har mu, sai irin marasa tarbiyyar nan kamar ta. Kuma ma fa sunƙi bari mu faɗa musu mi yarinyar ta aikata..." "Kaji ko principal, yarinyata ce ma bata da tarbiyyar...." "Hajiya kiyi haƙuri dan ALLAH". Principal ya sake faɗa yana maida kallonsa ga ƴar tata. "Muhibba miya haɗaki da su?".........✍️ 9
.........."Sir kawai fa dan na taka ita Ruƙayya ɗin ne ban kula ba, kafin na bata haƙuri sai ta hankaɗe ni ta ƙwace wayata ta jefar a ƙasa ta fashe, ni kuma na zuba mata ruwa a jiki ƴan class suka yi dariya. Itafa Nimrah ɗin ma bata ajin ta fita, kawai tana shigowa ba tambayar ba'asi ta hau dukana itama Ruƙayyan na tayata, ni kuma naji wahala na cijesu kawai suka gwara kaina da bango wai aljanunsu ya tashi..." "Da dai kin fito kin faɗi gaskiya yarinya da yafi miki". Cewar Ruƙayya tana hararta. Uwarta zatai magana principal yay saurin tarar numfashinta. Idanunsa akan su Ruƙayyan ya ce, "Ke haka akai?". "Sir ta ɓoye asalin zancen". "To miya faru?". "Yarinyar nan ƴar iska ce Sir, a bayan desk ɗinmu suke ita da ƴar iskar ƙawarta, kullum sai suna damunmu da kallon Film ɗin iskanci a waya, mun musu magana akan idan suna kallon rashin tarbiyyarsu a waya suna saka Bluetooth amma sun ƙi dainawa. Kawai yau suna kunnawa na juya na ƙwace wayar na fasa banza, shine tazo zata min hauka ni da Ninah muka sauke mata nata ƙaramin hau ɗin". Rawa jikin yarinyar ya fara, ta fara rantsuwa ita sharri su Ruky sukai mata. Uwarta ma bala'i ta fara wai za'a ma ƴarta sharri bazata yarda ba. Kodai principal ya bari ƴan sanda su tafi dasu Nimrah ɗin ko kuwa tai ƙarar makarantar gaba ɗaya. Cikin takaici Ammar ya ce, "Hajjaju ya kike Abu kamar baƙya ganewa ne, shin anan akwai wai mai tsoron zuwa police station ɗin ne anan akace miki. Yaran nan sun faɗi abinda ya faru har sukai rikici da ƴarki, maimakon ma ki damu da abinda take aikatawa kina neman juye wa mutane shirme. To muma bazamu yarda ba, dan bazata ɓata mana tarbiyyar yara ba, banda ma rashin kula har yara na kallon banza da wofi a waya iyaye basu sani ba, kuma miye na zuwa da waya makaranta? Gasu nan ko waya basu da ita yaran nan kuma basu taɓa damuwa ba duk da sun kai ƴammatan daya dace ace an barsu da ita, idan anyi maganar ku daina bama yara waya ko ku dinga kula dasu idan kun basu musamman masu tashen sabuwar balaga irin su kuga kamar an raina ƙoƙarinku ne. Ba haka bane, a irin wannan gaɓar waɗan nan abubuwa suke kwaɗaituwa a zukatansu, dan haka muma bazamu yarda ba, yaranmu masu tarbiyya ne, bakuma za'a ɓata mana su anan ba, kuma yanda sukai mata sun min dai-dai...." Hayaniya sosai ta kaure a office ɗin tsakanin Hajiya da Ammar, sai da ƙyar aka fitar da Ammar itama Hajiyar principal yace taje zasuyi bincike akai. Dan haka an bama yaran suspension na sati ɗaya su duka ukun har sai an tabbatar da gaskiyar mai laifi. Suko ƴan sandan data kira suka sallamesu. Suma ƴan sandan sanin makarantar ta jiga-jigai ce basu ja da nisa ba suka wuce. Yaya Ma'aruff dake hararar su Nimrah ya ce, "Sai ku wuce muje masu kunnen ƙashi. Hankalinku ya kwanta ai ko. Banda ma fitina ku kuma haifeta da zaku hukuntata? Ba kusan hanyar kai report bane, jibeku da kawuna kamar kullun magani". Babu wanda a cikinsu bai cika baki da iska ba. A haka suka fito suka shiga mota shima Yaya Ammar na zuba musu tashi hararar.....
★ Koda suka iso gida ko kallon inda suke su Yaya Ma'aruff basuyi ba suka shige ciki abinsu. Kallon juna Nimrah da Ruƙayya sukayi, cikin marairaicewa Ruky ta ce, "Wlhy yau akwai matsala Trouble Queen...." "Babba ma kuwa". Aka faɗa daga bayansu, a tare duk suka juya, Mu'azz ne daya zama matashin saurayi ɗan shekara goma sha takwas, dan kuwa ya kammala Secondary ɗinsa ma yana shirin shiga jami'a. Yanzu kam Nimrah ce tace, "Ya Mu'azz kaji tsoron ALLAH". "Oh, to da tsoron ku nake ji. Ba kunce ku baƙwa jin magana ba. To Daddy ma na nan zuwa dan Uncle J ya kirashi shima". Wani mugun ƙwalalo idanu waje sukayi a tare, shi ko ya kwashe da dariya yana barin wajen. Da sauri sukabi bayansa, amma yaƙi tsayawa har suka shigo falon. Cak kuwa suka tsaya, ganin kowa yana nan har su Aunty Lailah. Yaya Ja'afar ne ya fara zuba musu harara da faɗin, "Sannunku ƴan wrestling ko ƴan boxing ma zance ban sani ba nikam". "Yaya J ai sunce aljanu ne da su". Cewar Ammar yana harararsu shima da danne dariya. "Aljanu kuma?". "Wlhy haka sukace musu twiny". Yaya Ma'aruff ya bashi amsa yanzu shima dai dariyar yake dannewa da ƙyar. Dariya aunty Lailah da Aunty Shariffa suka gimtse suma, duk dauriyar Mammah sai da ta murmusa. Cikin son ingiza wutar Mu'azz yace, "Wai bazaku ƙaraso ciki ba ko aljanun ne suka sake tashi?". A tare suka balla masa harara, yay musu gwalo. Cikin kai ƙara Nimrah ta ce, "Mammah kin ganshi yana mana gwalo ko". Karon farko Mammah ta kallesu, sai kuma taima Mu'azz daƙuwa da faɗin, "Ai kaima duk kanwar ja ce, yau ɗaya da sukayi babu kai, hasalima kai ne malaminsu ai duk abinda suke yi. Kunga ku rabu da shi ku ƙaraso. Babu wanda zan bari ko dingurinku yayi a gidan nan." Jin haka yasa suka sake zabgama Mu'azz harara suna ƙoƙarin ƙarasawa ciki. Kamar abin baki sai ga sallamar Daddy Imran. Daburcewa Ruky da Nimrah sukayi, sai dai kafin suyi wani yunƙuri Imran ɗin ya shigo ciki. Kallo ɗaya yay musu kuma ya fahimci rashin gaskiyar su. Amma duk da haka sai da ya ce, "Ku kuma lafiya?" sai kuma ya kalli agogo ya ce, "Miya dawo daku gida bayan ba'a tashi ba?". Caraf Mu'azz ya bashi amsa da "Daddy ƴar mutane suka naɗawa na jaki aka korosu harda suspension na 1week". "What! Ya rabbi". Hararar Mu'azz Mammah tayi, zatai magana Imran ya ce, "Shi miye laifinsa, ga waɗanda zaki harara nan Mammah, ki haɗa musu da duka ma. Wai sai yaushe zamu huta da halin Ruƙayya da Nimrah a gidan nan ne?. Ku kuma kun zauna kuna kallonsu, mai makon tun a school ɗin ku naɗa musu bugun kawo gishiri suji a jikinsu kamar yanda sukama ƴar mutane". "A'a wannan muguwar shawara ce Imran. Ya zakace su dakar min yara. Naji sunyi kuskure, amma kowa dai da irin ƙuruciyarsa, sai ku musu addu'a. Nan da lokaci kaɗan duk zasu bari, sannan wannan faɗan akan gaskiyarsu ne". "Mammah idan jikinsu ya gaya musu ko. Shike nan nasan maganinsu, Boarding school zasu koma bari su kammala tarm ɗin nan." Kuka Nimrah da Ruƙayya suka ɓarke da shi, dan a duniya sun tsani Boarding school. Tuni sun zube a ƙasa sunyi gurfane suna roƙon Daddy Imran da tuni ya zauna. Karo na farko Aunty Shariffa da Aunty Lailah suka gaida Imran ɗin da fara bashi haƙuri suma akan a bar batun Boarding ɗin nan dan ALLAH. "Ina ku barsu ai gara suje muma mu huta. Kuma wannan zaman suspension ɗin zaku gane kuran ku da shi. Masu aikin gidan nan duk su shirya suje gida su huta. Kune zaku koma gyaran gida, har sashen Auntys ɗin ku, kuma kune zakuna abincin gidan duka da wanke-wanke safe, rana, dare". "Wlhy Daddy indai baza'a je Boarding school ɗin ba mun yarda zamuyi ko Sisy?" Nimrah tai maganar tana kallon Ruƙayya, da sauri Ruky ta ɗaga mata kai da faɗin, "Eh wlhy Daddy mun amince. Uncles dan ALLAH kusa baki, Mammah mun tuba, Aunty please ku bashi haƙuri". Ganin yanda su Yaya Ja'afar duk suka kalleshi suma fuskarsu na sauyawa alamar zasu fara roƙon nashi ya hararesu, kafin ya juya yana nunama su Nimrah hanyar upstairs yace, "Ku tashi ku bama mutane waje". Ai da gudu-gudu suka miƙe sukai sama. Ko gama hayewa basuyi ba Ja'afar yace, "Yaya Please hukuncin yayi tsauri da yaw....." Bai ƙarasa ba Imran ya hararesa. "Eh ai dama duk kune ke shagwaɓasu. To bazan bar gidan nan ba ma sai masu aikin sun tafi, duk wanda ya tayasu kuma shima sai na bashi nashi horon". Tsit sukai kowa yana tura baki gaba. Dan kuwa umarnin Imran dai-dai yake dana Dada a wajensu. A yanzu ma da babu Dada shine ya maye musu gurbin komai nasa a gidan. Daga ƙarshe dai ɗaya bayan ɗaya suka fara zare jikinsu a falon, su a dole an taɓa musu kafi auta. Cikin gatse Imran ya ce, "In kunji haushi ku ɗaukesu ku bar ƙasar inga tason ƴaƴa". Dariya Mammah tayi, sai da suka gama fita itama ta bama Imran ɗin haƙuri da faɗin, "Aikin ya musu yawa ayi haƙuri, koda girkin gidanan aka barsu na safe kawai ya ishesu hukunci". "Mammah ALLAH yaran nan basa ji da yawa, ki yi haƙuri kona kwana huɗu suyi ƙila su dawo hankalinsu. Ɗazun nan fa Asma'u ke sanar da ni jiya an basu suspension a islamiyya har sai da Ja'afar ma yaje, yara suna abu kamar wasu maza". "To ya za'ai kowa da irin ƙuruciyarsa sai haƙuri. Watarana sai kunga kamar ba'ayi ba in sha ALLAH". "ALLAH yasa muna da rabon kaiwa wannan lokacin. Dama nazo ne akan batun ganin likitan ki, komai ya kammala sai ku fara shiri ke da Ammar ɗin ko". "To ALLAH yay muku albarka. Yanda kuke ƙyautata mana kuma ALLAH ya baku tsahon rayuwar da ƴaƴanku zasu ƙyautata muku su jiyar daku daɗi nan". "Amin Mammah, ALLAH ya ƙara muku lafiya da tsohon rayuwa kuma. Sai batun Haysam, a cigaba da tayamu addu'a in sha ALLAHU muna ganin nasara a wannan karon. Dan yanzu haka ma daga wajen Janar nake, kin san yau sunyi primary election na party ɗinsu Alhamdullah kuma shine yaci matsayin candidate". Wani irin yalwataccen farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Mammah, ta haɗiye hawayen da suka cika mata ido tare da faɗin, "Alhamdullahi ya rabbi, UBANGIJI Ya tabbatar mana da alkairinsa. Yasa iyakar jarabawarce tazo". "Amin Mammah, in sha ALLAHU iyakance tazo. Dan in har Janar ya haye kujerar nan ina mai tabbatar da ko sati bazaiyi a gidan gwamnati ba Haysam zai fito." "Idan shi alkairi ne ga ƙasa gaba ɗaya, ALLAH ya bashi nasara, bazan so saboda nasarar fitowar nawa jinin wasu su ƙuntata ba, dan haka zamu cigaba da addu'ar zaɓin alkairi in sha ALLAHU". "Haka ne Mammah, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairin". Sun ɗan ƙara tattauna abinda ya dace kafin yay mata sallama ya wuce..........✍️
10
........Su Nimrah dake laɓe da tunanin za'a sake maganar makarantarsu jin shiru su Mammah ma sun ɗauki wani zancen daban suka bar wajen. Suna shiga ɗaki Nimrah ta ce, "Trouble Buddy! Kin san mi zamuyi?". "A'a sai kin faɗa". "ALLAH in dai Daddy ya dage sai ya kaimu Boarding ɗin nan randa aka kaimu samun wata Senior ɗin zamuyi mu lakaɗa mata dukan da a washe gari za'a kirashi ace an koremu gaba ɗaya. Idan mun dawo gida mu dage masa kan bamu san munyi ba aljanu ne damu da gaske." Sai da Ruky tai dariya sosai sannan ta ce, "Sai da ke Hot Pepper! Amma fa ni kin san wani lokacin ina da ɗan tsoro, kada muje wajen ƙaryar aljanu a samo wani ustazu ya daki banza da sunan Rukya, ko'a ƙara na kwanaki yace zai aurama su maigadi mu." "Ai ke banza ce. To bari kiji ALLAH bazasu bari a dake mu ba. Balle ma in har za'a Boarding ɗin nan dole muyi sanadin da za'a haɗa harda Fiddo da Bintu". "Muguwa naga mu kaɗai mukai laifin? ALLAH ki dinga jin tsoron ALLAH Ninah". Itama dariya tayi yanzun kam, ta wani juya idanunta manya cike da iyayi, "Yo da tsoronki nake ji Ruky. Bazaki gane ba idan muka haɗu mu duka sai Boarding ɗin ma tafi daɗi idan ta zama ƙaddarar mu. Mu haɗu mu dinga darje bakin ƴan iska da duk suka nuna mana yatsa." Tafawa sukai suna dariya....
Nace ALLAH dai ya shirya waɗan nan yara🏃🏼♀️. Daddy Imran ka rufa mana asiri ka barsu a Day school ɗinsu, kada wataran suja maka ka sake komawa inda Dada yake.🏃🏼♀️🏃🏼♀️😂.
____________★
Aiki gida dai ya tabbata akan ƴan caskalen gidan Mammah, dan kuwa a bazata washe gari tunda safe sai ga Imran a gidan, suna tsaka da barcinsu ya saka Aunty Biebah taso masa su. Da farko sai faman layi suke suna ma Biebah kukan shagwaɓar ta barsu su barci suke ji, amma suna cin karo da Daddy suka watsakke, a tare suka zube suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu tare da faɗin, "Oh barci ma kuke yi har zuwa yanzu? Batun breakfast, shirya ƙannenku zuwa school duk wa zai yi?". "Daddy kayi haƙuri, ALLAH bamu san barci ya sake ɗaukar mu ba". "Na baku mintuna goma ku wuce ku shiryo su Abees". Kafin ma ya gama rufe baki sun fice a sashen. Kai tsaye sashen su Yaya Ja'afar suka nufa kamar zasuyi kuka, dan suyi sauri sai suka rabu. Nimrah ta shiga sashen Yaya Ma'aruff ita kuma Ruky na Yaya Ja'afar. Shigowar Nimrah dai-dai da fitowar Aunty Lailah daga ɗakin su Aheel, fuskata da murmushi ta ce, "A'a Ninah miya faru ba'ai shirin makaranta ba?". Kamar Nimrah zata saki kuka ta ce, "Ammie kin manta muna suspension? Zan shirya su Aheel kije ki kwanta kawai". "Oh na manta, amma Ninah aikin zai muku yawa, ga haɗa breakfast ɗin gida gaba ɗaya, ga gyaran sashen ku. Kije kawai bari na shirya su kinji". "Ammie Dady fa na nan". Cikin ɗan waro idanu Aunty Lailah ta ce, "Gidan Yayan yazo da sassafen nan?". Kai ta jinjina mata. Dai-dai da fitowar Yaya Ma'aruff ya ce, "Wayo yazo da sassafe?". "Wai ya Imran". Murmurshi kawai Yaya Ma'aruff yayi yana girgiza kansa da faɗin, "ALLAH yanzu gaba ɗaya Yaya Imran ya canja zuwa Dada, da dai babu ruwan shi da faɗa amma yanzu ya gaje halin twiny sa. Ninah zo nan". Sum-sum Nimrah ta iso inda yake, zama tai a ƙasan lallausan carpet ɗin tace, "Uncle good morning". "Morning sarakin ƙiriniya, ke dai ke da Ruky ku saka mutane surutu shine jin daɗin ku ko. ALLAH idan baku canja ba duk randa Dada ya dawo gidan nan sai kun gane Yaya Imran bai iya komai ba". Caraf Nimrah ta ce, "Uncle kenan Dada shi mugu ne?". Dariya yanda tai ɗin yaso saka Ma'aruff, amma sai ya danne ya murmusa kawai. "Dada ba mugu bane, amma baya son rashin ji, ku tambayi Ammar zai baku labari dan shi ma da rashin ji ya fara Dada ya saita shi da horon sojoji. To kuma idan baku nutsu ba duk randa ya dawo jiki magayi". "In sha ALLAHU zamu ma bari, amma dan ALLAH Uncle wai shi Dadan yana wace ƙasa ne? Yaushe kuma zai dawo? ALLAH ina son na ganshi, kaga sai a hoto muka taɓa ganinsa shima sau ɗaya ne Mammah tasa aka tattare hotunan aka ɓoye". Sai da Yaya Ma'aruff ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan yay ma Nimrah murmurshi kaɗan. Bayan su masu hankali har yanzu daga Mu'azz har su Nimrah basu san Dada na prison bane, kawai ance musu yana wata ƙasa ne yin wani aiki mai muhimmanci. Dan ko Biebah ba komai ta sani ba sai kaɗan-kaɗan daga cikin lamarin shima dan ya watsu a media ne lokacin... "Ninah in sha ALLAHU Dada zai dawo, ina ji a jikina nan kusa ma kuwa zai dawo gare mu. Ku dai ku cigaba da addu'a kawai. Dan zuwansa garemu zai iya zama tamkar haɓo ne kinji". "ALLAH yasa Uncle, kuma in sha ALLAHU kullum zamu dinga zama mu da su Abees muna addu'ar". To ALLAH yay muku albarka. Ina Sisin taki?". "Mun raba aiki ne tana can zata shirya su Abees". "To kinga tunda ga Ammien ku na shirya su Aheel anan tashi muje, ni zan janye Yaya Imran ɗin sai kuyi sauri ku haɗa breakfast kawai". Sosai farin ciki ya kama Nimrah, koda suka fito suka leƙa sashen Yaya Ja'afar sai suka sami Rukyn ma ba aikin take ba, tana gyarama Afrah gashi ne dan har an musu shirin makarantar ma. Sai kawai ta kamota suka fito zuwa sashen Mammah, ta ƙofar baya ta kitchen Yaya Ma'aruff yace su shiga, shi kuma ya zagaya riƙe da hannun Afrah dake zuba masa surutu, dan itama dai akwai baki ta gado su Nimrah ɗin.....