Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 5
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 5: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 5. Tun a haɗa breakfast Nimrah da Ruƙayya suka san ALLAH ɗaya ne. Masu aiki kuwa…
4,005 words
Tun a haɗa breakfast Nimrah da Ruƙayya suka san ALLAH ɗaya ne. Masu aiki kuwa na ƙoƙari kwarai-ƙwarai da gaske. Suna wayyo-wayyo Uncles ɗin nasu da Auntys na dariya suka jera a babban family dining table ɗin makeken falon Mammah. Dan dama haka suke cin abincinsu a tare tun daga na safe har na rana ga wanda suke a gida. Na dare kuwa dama kowa yana nan. Kowa na ƙoƙarin kammalawa ya wuce aiki suko suna haƙilon gyaran kitchen, ga Mu'azz ya saka rayuwarsu gaba. Daya motsa sai ya ƙwala musu kira. "Ninah bani kaza, Ruky baku ajiye abu kaza ba". Suko takaici ya ƙulesu sai su ɗakko a hasale su dangwarar masa. Dariya kamar ta kashe su Aunty Shariffa. Aunty Biebah ce ma suka bata tausayi bayan tafiyar Daddy Imran tace su gyara falo kawai bari ta tayasu gyara bedrooms tunda dai can ai babu camara balle Yaya Imran ɗin ya gani. Dan koda zai wuce sai da ya sake jaddada musu idan ma basuyi ba zai gani ta cctv Camaras dake zagaye da gidan tako ina. Wannan ya sake sasu tsorata suka dage. Duk da taya sun da Aunty Biebah tayi basu kammala komai ba sai 12 da wani abu, a wahale sukai wanka sukazo falo inda su Aunty Shariffa ke hira dan su basa zuwa aiki, shiyyasa koda yaushe suna sashen Mammah suna ɗebe mata kewa. Balle yanzu hirar na armashi Mu'azz yana gida zaune kafin ya wuce University. Yau kuma anyi sa'a Aunty Biebah ma dake gab da kammala master nata bazataje school ba. A ƙasan lallausan carpet ɗin falon suka zube kowa na maida numfashi. Mu'azz ya kwashe da dariya cike da mugunta. "Oh ALLAH yau ga mata sunyi aikin gida. Ku a haka za'ai muku aure kuje kunayi, dan ALLAH ji Ninah kamar an tsamo mage a ruwan zafi, gara-gara ma Ruky". Kamar Nimrah zatai kuka ta ce, "Mammah kin jisa ko, wai nice mage a ruwan zafi". "Shi kuma muzuru ko?". Cewar Biebah na jifansa da filo. Cafewa yay yana dariya da faɗin, "Kai small Mom muzuru kuma. Dan ALLAH kar ki saka yaran nan su raina ni mana. In ba haka ba ALLAH zan zuga Daddy a kaisu boarding school ɗin nan mu huta. Su Ayyan sun ishe mu". "Idan su basu tafi Boarding school ba ai kai ka tafi, tunda baka san inda za'a cillaka karatun ba". Kallon Aunty Shariffa mai maganar yayi da faɗin, "Kai Mamy banda fata, kin san bakin iyaye da saurin kama ɗa, in sha ALLAHU nikam ina nan cikin garin nan babu inda za'a kaini". Mammah dake fitowa a ɗaki ta ce, "Ni dama za'a kaika wani ƙasan da yarana sun huta da damun su da kakeyi babban banza". "ALLAH Mammah na tafi kema sai kinyi kewata. Suma haka kuma, dan sun san ina rufa musu asiri a gidan nan. Amma tunda kun shigar musu yara duk zaku gane kuran ku. Daga yanzu ko tarin banza kukayi zan fara rubutawa ne, kuma Dada zan ajiyewa yanda zaku fi caskaluwa dan na Daddy mai armashi ne yanzu". A tare suka kwashi fillo suka shiga jefa masa. Gashi sun kasa tashi saboda ƙafafinsu sunyi dayin wahalar aiki. Aiko mi za'ai in ba dariya ba. Da ƙyar Mammah ta raba faɗan nan ta hanyar janyesu ta shafa musu man zafi a ƙafafu. Ga shi lokacin yin girkin rana yayi. Haka suka shiga kitchen ɗin suna sharɓar hawaye, ga camaras da suke ji kamar su fincike su su yardar su samu a tayasu. Amma ba dama, dan duk bayan wani ɗan lokaci sai Daddy Imran ya kira waya ya tabbatar musu duk yana kallonsu dan yayi connecting da wayarsa, suma kuma sun san haka ɗin ne tun ma ba yanzu ba..........✍️
Gaskiya kuzo muje balling Trouble Buddy da Trouble Queen kafin Daddy Imran ya kaisu gadon asibiti🤣🤣.
11
.........Kwanaki kusan biyar su Nimrah na cin ƙaniyarsu da aiki, sun jikatu matuƙa sunyi laushi, kuka da roƙo babu kalar da basuyi ba, hakama kawunansu sun bama Daddy Imran haƙuri amma yace idan suka bar aikin nan Boarding fa babu fashi. Da ga ƙarshe dai suka zagaye suka kira Aunty Ummie a waya suna mata kuka suka sanar mata. Dama kwana biyu bata leƙo gidan ba saboda aiki. Aunty Mommy kuwa basa ƙasar ita da mijinta sai a satin nan zasu dawo. Ita ko Aunty Mimi ciki gareta tsoho haihuwa ko yau ko gobe shiyyasa Mammah ta hanata zuwa gidan. Alhamdullahi zuwan Aunty Ummi da suke kira da Big Mah-mah ne ya cecesu a hannun Daddy Imran. Dan bayan an sako massalacin juma'a yazo gidan gaida Mammah ta tareshi da daɗin baki da ban haƙuri har ya haƙura masu aiki su dawo gobe. Amma duk da haka da sharaɗin daga yanzu kullum dasu za'a dinga shiga kitchen yin girki. Da wannan ALLAH ya ƙwacesu. Masu aiki suka dawo, su kuma suka samu sauƙi. A cikin satin ma suka koma zuwa islamiyya dan suspension ɗin ta ya ƙare, sai kuma karatun da akayi basa nan ya sakasu a gaba. Sati ya zagayo suka koma boko ma, amma duk da haka sai da akai zama da Hajiya ta kafa sharaɗin babu su ba yarinyar ta, dole kuma a raba musu wajen zama sannan case ɗin ya mutu. Dan an dai gane ƴarta na kalle-kallen banza a waya da gaske kamar yanda su Nimrah ɗin suka faɗa......
>>>>><<<<<<
Yau ta kasance juma'a, dan haka an tashesu da wuri. Sai dai shiru babu drivern su babu alamarsa. Sun san maybe ya fara zuwa ɗaukar su Abees kafin yazo nan, duk da kuwa a kulum su yake fara zuwa ya ɗauka kafin su ƙarasa makarantar su Abees ɗin saboda suna rigansu tashi. Tun suna kallon agogo har suka sare, ga mafi yawan ɗalibai duk sun wuce anzo an ɗaukesu. Makarantar su nada doka kuma ma tilas zuwa ake ɗaukar kowane ɗalibi bawai buɗe musu gate ake su fito ba kawai. Sun gaji ga Ruky na ciwon mara, dan ita in zatai period ba ƙaramin jikata take ba. Ganin ta fara kuka hankalin Nimrah ya tashi. Ofishin Principal ta nufa amma ta tasar baya nan wai sun shiga meeting da malamai. Da gudu ta dawo wajen Ruky, ta sameta durƙushe azaba ta isheta, bata son suje clinic ɗin cikin makaranta dan an riga an tashi. Idannunta na cika da ƙwalla itama ta kamata ta miƙar. "Tashi muje wajen security ko zai taimaka ya barmu mu fita kawai, amma shima Baba Driver bai ƙyauta mana ba". Da ƙyar da ƙyar Ruky ta iya miƙewa suka isa gate ɗin, cikin sa'a suna isowa sai ga motar Yaya Ammar na isowa. Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke, dai-dai Mu'azz na fitowa daga motar, ya ƙaraso inda suke da sassarfa yana faɗin, "Lafiya kuwa? Miya sami Ruƙayyan?". "Yaya ciwon mara, muyi sauri mu tafi kasan idan ya fara tsanani sai suma. Amma Yaya driver fa?". Sai da ya buɗe musu suka shiga yake bata amsa yana reverse. "Baba driver accident yayi, yanzu haka ma yana asibiti". "Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, badai da su Aheel ba?". "A'a bada su ba, shi kaɗai ne yaje ɗakko motar Ummie (Aunty Lailah suke cema Ummie, Shariffa Ammie) daga wajen wanki". "Ya rabbi, ya jikin nasa?". "Gaskiya yaji jiki sosai, dan har yanzu ma ba'a bari an gashi ba. Motar kuwa tama tashi aiki, dan babbar mota ce ta haye shi". Gaba ɗaya jikin Nimrah ya ƙara sanyi, ita kanta Ruky dake fama da kanta hankalinta ya sake tashi, a haka suka iso gida ciwon marar ya ƙara tsanani, dole ma sai Mu'azz ɗaukarta yayi. Gaba ɗaya hankalin ƴan gidan a tashe yake da hanlin da baba driver ke a ciki, dan mazan gidan duk suna can. Ganin hanlin da Ruky ke ciki kuma duk sai suka maida hankali a kanta. Babu bata lokaci aka kira family doctor ɗin su, da yake ya san matsalarta yana zuwa allurai yay mata....
Basu sami ganin Baba Driver ba sai ranar Lahadi da yamma. Gaba ɗaya gidan suka shirya suka je suka duba shi. Yaji jiki kam kwari da gaske, amma Alhamdullah yana samun dukkan kulawar data dace. Ga matarsa an ɗakko tana jiyyarsa. Komai na asibitin Kuma su Yaya Ja'afar ne suka biya. Sosai matar ke godiya akan yanda suka bama al'amarin mijinta muhimmanci, inda wasu ne ko'a jikinsu, ƙilama suce sai an biyasu motar miliyoyin kuɗin data tashi aiki. Amma su bata motar suke ba ta lafiyarsa sukeyi. Shima Baba Driver kallonsu kawai yake yana hawaye, dan baya iya magana har yanzu. Su duka sun ɗauka yana kuka ne kawai akan halin da yake ciki. Dan haka Mammah tai masa nasihar haƙuri da tawakkali akan ƙaddara. Kusan awar su ɗaya suka koma gida suna sake jimanta al'amarin. Satin baba driver biyu ya fara samun sauƙi, zuwa yanzu kuma Mu'azz ke jigilar kai su Nimrah makaranta da ɗakkosu kullum. A haka kwanakin tafiyar Mammah da Yaya Ammar suka cika zuwa Egypt ganin likita. A tare suka mata rakiya airport cike da kewa, dan Ruky da Nimrah harda kukan su. Ƙarshe Uncles ɗin nasu suka koma lallashinsu da tabbatar musu ai sati biyu kawai zatai ta dawo. Haka suka dawo gida. Tafiyar Mammah da Yaya Ammar da kwanaki biyar al'amarin karatun Mu'azz ya taso, dole su Yaya Ma'aruff suka fara batun neman driver, dan su basu da isasshen lokaci, wani lokacin ma da ƙyar suke ƙulla sati uku a ƙasar. Ammar yana fama da aikinsa, ga Bilal ma baya ƙasar, ko yana nan aikinsa shima ya ishesa, bazasu so kuma matansu kullum na gantalin kai yara makaranta da ɗakkosu ba, balle Biebah da bata da magana yanzu sai ta project ɗinta. Sunata tunanin ina zasu samu sabon driver mai amana kamar Baba amma sun rasa makama. Shawarar kota hanyar Baban za'abi Yaya Ma'aruff ya bayar, dan haka suka amince da hakan. Bayan sun taso kasuwa suka nufi gidansa dake can wani ƙaramin ƙauye, sai dai atanan yankin babban birnin yake. Sun sameshi jikinsa Alhamdullah, sai dai ƙafa data samu nakasa sosai har yanzu anata fama. Sun sake jajanta masa da ajiye masa alkairin da basa gajiyawa wajen yi masa sannan suka sanar masa abinda ya kawosu. Cewar suna son ya sama musu wani drivern mai amana kamar shi dan sun yarda da shi. Da farko shiru yayi idanunsa na cika da ƙwalla. Sai da Ja'afar ya ce, "Baba wannan ai ba abin kuka bane. Mun yarda da kai ne da amanar ka shiyyasa muka sake biyowa ta kanka, kuma in ma ALLAH ya baka lafiya muna maraba da dawowarka cikinmu". Hawaye Baba ya share, "Na sani ku mutanen arziƙi ne masu tarin alkairi, har abada kuma bazan manta da tarayyata da ku ba. Amma mizai hana ku cigaba da kai yaran makaranta da kanku?". "Baba bazai yiwu ba, kasan yanda uziriri sukai mana yawa dai, idan muka ce mune zamu kaisu za'aita samun matsala. Ga boko ga islamiyya, ga cefanen gida kai Mammah anguwa da iyalanmu". Baba yay shiru zuciyarsa na kai-kawo, dan yasan bazasu fahimci mi yake nufi ba daman kai tsaye, shi kuma tsoro bazai barshi fitowa ya buɗe musu komai ba kai tsaye, sai kawai yace to su bashi lokaci zai kira a waya. Cikin gamsuwa sukai musu sallama suka tafi. Cikin damuwa matarsa ta ce, "Wai miyasa kake ta musu kwana-kwana malam? Mutanen nan mutanen kirki ne, banyi zaton zasu zo da damuwa kanada damar musu maganinta ka kasa ba". "Ba kasawa nai ba Tabawa, kawai ina duba al'amarin ne dai kawai, kin san yanda rayuwa ta lalace yanzu ba kowa ke raɓarka da ƙyaƙyƙyawar zuciya ba. Ko ni ɗin ma alkairin su da hukuncin UBANGIJI ne ya sauya ni daga dalilin raɓarsu". Cikin rashin fahimta ta ce, "Kamar ya? Ban gane ba malam!". Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba ya barta da wasi-wasi. Awa ɗaya ba'ayi da tafiyar su Yaya Ma'aruff ba Baba Driver yayi baƙo. Kasancewar matarsa tasan mutum ya saba zuwa wajensa bata kawo komai a ranta ba ta shiga ciki gida ayyukanta ta basu waje. Dan yana jiyyar a ɗakin soro ne... "Rabe! Kana ganin taurin kanka zai cigaba da baka nasara ko? Halin da kake ciki bai zame maka aya ba kenan?". Murmurshi Baba Driver yayi mai ciwo, idanunsa cike da ƙwalla ya ce, "Ba darasi ne ban ɗauka ba Ari, ina tausayin bayin ALLAHn nan ne. Wlhy mutanen nan munanen kirki ne su da mahaifiyarsu. Sannan ya kamata mu yarda ba laifinsu bane akan abinda ya faru baya, shima kansa wanda ake son azabtar da su ta dalilinsa mufa sani rayukanmu ya jajirce wajen karewa, ALLAH ne ya ƙaddara za'a tarwatsa mu a ƙauyukanmu har mu watse irin haka. Hasalima mutanen nan dake munana shi a garemu sune silar faruwar komai akan waɗan can abubuw......" "Rabe! Kana nufin wuyanka yayi kaurin bijirema su Oga Dagger ko? Amma kasan minene hukuncin yin hakan a gareka ko? Karka manta kana cikin ƴantattun da aka bama damar zuwa su rayu a cikin mutane har suyi aure su hayyafa cikin ƴanci. Baku san wahala da azabar da mu dake cikin jeji kullum a ɓoye muke sha ba. Mutanen nan da kake ƙoƙarin karewa ance maka kaje kai musu wani abu ne? Information ɗin abinda ke gudana a rayuwarsu kawai akace ka dinga kawowa. Musamman ita wannan yarinyar Nimrah, amma taurin kai yasa ka zauna kana kawowa mutane ƙauli da ba'adi, gashi nan har sai da ka jama kanka zaman guri ɗaya, da da ƙarar kwana ma yanzu wani labarin ake ba naka ba. Ni dai yanzu ga saƙo, Oga Mole da Oga Dagger sunce gobe zasu turo sabon driver ka turashi ga mutanen nan ya maye gurbin ka, zaɓi ya rage naka kayi koka kuskure kai ne zakai kuka, dan a yanzu ba kai za'a hara ba ƴaƴanka ne ko matarka"... Yana gama faɗa ya miƙa batare da ya saurari magiya da roƙon Baba Driver ba.....
★>><<<<★>>>><<★ ★DUBAI★
Ganin yanda Nabeeha ke faman haɗa kaya ya bama Ismat data kawo mata breakfast har ɗaki tsoro. Duk yanda taso daurewa saita kasa. Cikin damuwa ta ajiye tray ɗin da take ɗauke da shi ta nufeta. Hannunta ta riƙe cikin rauni da damuwa ta ce, "Aunty wai mi kike yi haka ne? Ina zaki kike haɗa kaya?". Hannun nata ta fisge, kukan da take faman riƙewa tun daren jiya saboda taurin zuciya a karo na farko ta fashe da shi..........✍️
12
........."Ismat zan koma ƙasata, wlhy na gaji da wannan rayuwar, bazan iya ɗaukar huɗubar Momy ba, gara na koma gidan mijina nai zaman jiran dawowarsa ko nan da shekara hamsin ne ma ba ashirin da biyar ba". Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ismat ta sauke, dan koba komai itama an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi dama. Ta kama hannun Nabeeha suka koma bakin makeken gadon ɗakin da yaji shinfiɗu na alfarma, dan duk da haɗuwar gidan da komai na cikinsa ɗakinta na musamman ne. Gyara irin na ƴar gata Adeel yasa akai mata. Hannayenta duka a cikin na Ismat ta ce, "Aunty wlhy koni ina bayanki ki koma gidanki, dan ita Momy idannunta sun rufe da son kuɗi bata duba abinda muke so koya dace damu. Ita kawai tafi kallon abinda zata samu. Gamu dai a cikin ƙaton gida a kuma ƙasa irin ta Dubai da kowa ke buƙatar yazo, amma wlhy Aunty Jiddah ta fimu kwanciyar hankali, tana rayuwar auren ta ga yaranta abin sha'awa, shiyyasa wlhy nima na fara ji a raina zanyi na nata na koma gidan Abba na bashi haƙuri na samu miji nayi aure. Dan in har muka cigaba da rayuwa da Momy anan wataran sai mun lalace, dan waɗan nan shaggun mutanen babu abinda suka iya sai son mata kamar su babu matan a cikin nasu ƙabilar". "Ismat wlhy ni duk bama wannan ba, babban abinda ke bani mamaki da Momy itafa kawai na kashe aurena saboda wannan mutum yace mata aurena yake son yi, haba miyasa ba zatai tunanin daya dace ba, dukiya irin ta mutumin nan, da nasaba ta gidan mulki, mulkin ma mai ƙarfin gaske ne zai zauna wani auren baƙar fata ƴar Africa saboda rainin hankali da ɗaukar mutane jakai. Kiga yanda suke wulaƙanta matan African fa kamar wasu dabbobi dan ko bayi na baya sun fi matan da ake kawo musu suna iskanci da su a yanzu mutunci da daraja. Wlhy Ismat ina son mijina, duk da ina jin takaicin auren shegiyar yarinyar nan har yanzu a zuciyata...." "Na sani Aunty, ki share wani batun yarinya kawai muyi tafiyar mu, dan uwarta mune zamu miki maganinta, da ƙafarta zata bar gidan batare da kowa ma ya sani ba ta koma ƙauyen su, idan tace ita ƴar hau ce mu ƴan hau-hau ne to". Ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske Nabeeha ta saki, tana mai jin nutsuwa da gamsuwa da zancen autar tasu. A gefe zuciyarta na jin matsanancin kewar mijinta da buƙatar son kasancewa da shi da akoda yaushe take yaƙi da kanta a kai, sauƙi-sauƙin ma da take samu kullum cikin mafarkinsa da yanda yake tafiyar da ita a shimfiɗa take, shiyyasa take samun sassauci da jinsa kamar a kusa da ita har yanzu.....
Da baya-baya Hajiya Hasiba tabar bakin ƙofar ranta a matuƙar ɓace da tattaunawar yaran nata. Ƙayataccen ɗakinta ta shiga, ta zauna a bakin makeken nata gadon hannunta dafe da kanta. Jitake kan nata na wani mugun sara mata, sai dai abinda ke mata kai-kawo na takaicin yaran nata na son danne ciwon. Lallai lokaci yayi da zata nunama su Nabeeha ita ba sankaran uwa bace sha-sha-sha kamar yanda suke tunani. Taya zata bari ma Nasiru yaci nasara a kanta, bayan ya rabata da Jiddah ya rabata da Nabeeha da Ismat da suka rage mata kuma. Ta jima da fahimtar soyayyar da Ismat kema Ja'afar, sai dai bata damu ba ganin yanda shi Ja'afar ɗin yaƙi kulawa, amma yanzu ta fahimci Ismat na zuga Nabeeha ne su koma gidan ubansu saboda son da take ma Ja'afar, kenan da sunje sun kwantar ma da ubansu kai itama sai ya aura mata shi, shekenan ita kuma A'isha ta haifama ƴaƴa ko? To kuwa zasuci ubansu. Da wannan tunanin tai ƙwafa, tare da miƙewa zuwa gaban wadrobe ɗinta, ta ɗibo duk passport ɗinsu dake wurinta, cire na Nabeeha da Ismat tayi ta canja musu waje, daga haka ta hau shirin fita. Dan tana buƙatar ganawa da Adeel yanzu nan basai gobe ba.....
§§§§§§§§§§§§§§§§ ★EGYPT ★
"Mammah muje ki huta yau kam kin gaji fiye da kullum. Ga su Yaya Ma'aruff nata kira nasan burunsu kawai suji yanda results ɗin suke ne. Aunty Ummi ma naga ta kira video call ta WhatsApp". Murmushi Mammah tayi, cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ammar yarana duk sunyi kewata ne, nima ina tsananin jin kewarsu. Dan haka ni kam ba sai sati biyun nan ya cika ba zuwa jibi tunda sunce babu wata damuwa suna bamu maganin nan kawai mu koma gida". "Duk yanda kike so haka za'ai Mammah". Yay maganar yana ɗan rungumota ta gefe, dama kuma suna tafiyar ne hannunta riƙe a nashi. A yanda ya ɗan rungumetan yana dariya itama yana murmurshi da kai masa rankwashi a kai yasa basa kallon gabansu balle mai tahowa. Karaf kuwa sukaci karo da wani abun da ya saka Mammah faɗin, "Subahanallahi". Shima sai Ammar ɗin ya sake ta yana waiwayawa da ambaton, "Ya salam". A dai-dai lokacin shima wanda sukai karon ya ambaci, "Subahanallahi" ɗin yana kaiwa duƙe da son riƙo takardun hannunsa da suka tarwatse a ƙasa. Cikin sauri Ammar ya bishi shima yana ƙoƙarin taimaka masa da sake faɗin, "I'm sorry sir". Fuskar mutum da murmurshi ya ce, "Karka damu ɗana, nima harda nawa laifin hankalina nakan takardun ne shiyysa ban lura da tahowarku ba. Mama kiyi haƙuri kem......" Ya kasa ƙarasawa saboda dai-dai ya ɗago ne zai kalla inda Mammah ɗin take sukai ido biyu. Dan itama ta miƙo masa takardar data ɗakko ne datai gefe zatai magana a lokacin, sai ta dakata cak tana kallonsa. Ko shekara dubu tayi bazata manta wannan fuskar ba a duniyarta, balle shekarun da basu wuce talatin ba. Jin sunyi shiru Ammar daya gama tattarowa shima ya juyo yana kallon su, Mammah ya fara kallo datai tsaye ƙyam baki buɗe tana kallon mutum, da sauri ya maida kallonsa kansa shima. Ai da sauri ya wani ja baya yana waro idanu waje da faɗin, "Ya rabbi! Mammah waye shi?". Mammah da gaba ɗaya kanta yay wani dimmm ta gagara cewa komai, sai hannunta dake ƴar rawa har sai da Ammar ya matso ya riƙota jikinsa, sai dai har lokacin idanun nasa akan mutumin da alamu ya nuna shima dai yayi sumar tsugunne ne......
>>✿<<>>✿<<>>✿<<
"Assalamu alaikum". Aka kwaɗa sallama daga bakin ƙofar falon bayan anyi knocking har sau biyu. Ƙaramin tsaki Mu'azz dake zaune shi kaɗai a falon yana cin abinci yaja, ya tsani tashi yana cin abinci, dan yana tashin shike nan abincin ya fita a kansa kuma. Hanyar kitchen ya kalla inda yake jiyo surutun Nimrah da dariyar Biebah. Sai kawai ya ɗaga murya ya ce, "Ninah!". Daga can ta ce, "Kai Yaya Mu'azz miye kuma dan ALLAH? Bana kawo maka harda ruwa ba". "To uwar son jiki, dalla fito kiga waye ana knocking ne". Baki a sama ta fito, tana sanye cikin shirt da riga na lass milk da furanni coffee. Tayi ƙyau sosai daka ganta kaga ƴammatan zamani masu shegen iyayi da rawar kai. Harta nufi ƙofa ya ce, "Haka zaki fita ba hijjab?". Baki ta ƙara turawa gaba, ta dawo ta ɗauka hijjab da sukan ajiye a falon saboda irin haka, dan Mammah ta saba musu sakawa musamman idan akai baƙon ido ko suka saka ƙananun kaya, wani lokacin ma sai taga kamar anfi takura mata da sakawa fiye da Ruky da Aunty Biebah. Sai da ta saka ta zura hannayensa sannan ta nufi ƙofar da aka sake bugawar, sallamar maigadi ta amsa tana buɗe ƙofar. Ya ɗan ja baya yana gaisheta. "Baba ni dai ka daina rissina min dan ALLAH. Ina wuni?". Murmurshi maigadin yayi da faɗin, "Ai girmanki ne Hajiya. Dama baƙone yazo yace kuma sabon driver ne Malam Buba tsohon Driver ya aikosa". Ɗan jimm tayi sai kuma ta ce, "Okay to bari na sanarma Yaya Mu'azz, dan su Uncle's duk basa nan. Ammie da Ummie ma sun tafi gidan Mom (Aunty Mimi suke kira Mom) data haihu ɗazun". Fuska ɗauke da murmushi ya ce, "ALLAH sarki ALLAH ya raya, ya albarkaci abinda aka samu". "Amin ya rabbi". Ta faɗa tana rufe ƙofar ta juya ciki. "Yaya wai sabon driver ne, kuma Baba Driver ya turoshi". Ɗagowa Mu'azz yay yana kallonta, sai kuma ya maida kansa ga television yana faɗin, "Oh to sannunsa da zuwa. ALLAH ya iyakance min jigilarku kullum kuna damuna da surutun ku da fitina. Ki haɗa abinci ki kai masa dan abinci nake ci sai na kammala na fita mu gaisa". Sai da ta cika baki da iska cikin ƙunƙuni ta nufi kitchen tana faɗin, "Ni wlhy yau ƙafafuna duk ciwo suke, dan anga Mammah bata nan sai wahala ake bani, yau tunda muka dawo school ban huta ba komai ni...." Fiiiffgg! Filon kukera da Mu'azz ya jiho ya sameta a baya. Tako dage ta ƙwalla ƙarar data saka Biebah fitowa daga kitchen da gudu tana tambayar lafiya da riƙo Nimrah ɗin. Kai Mu'azz ya girgiza cike da takaici yana nuna fillon daya jefeta da shi. "Small Mom fillo fa kawai na jefa mata dan tana min ƙunƙuni shine take wannan ihun. Wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH. Wai uwar wa ma ya hanaki bin su Ammie ne kamar yanda Ruƙayya tayi?". "ALLAH sai na gayaka da Uncle, kuma ai dai naji zafi. Tunda na dawo kaketa sani aiki, na maka gyaran ɗaki, kace na maka ɗan wake, duk baka gani ba sai da ka ci zalina". "Oh gori kike min saboda kin min gyaran ɗaki da ɗan wake? Lallai ma Ninah ni ko". Kai Biebah ta girgiza da jan ƙaramin tsaki ta koma ciki tana faɗin, "Kudai bazaku taɓa canjawa ba ALLAH ya shirye ku. Ba sai ku cinye kanku ba jarababbu. Wlhy na ƙagara Mammah ta dawo gidan dan kun isheni"..........✍️
13