Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 6

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 6

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 6: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 6. ..........Da gudu Nimrah tabi bayanta saboda wani fillon da Mu'azz ya ɗauka…

3,544 words

..........Da gudu Nimrah tabi bayanta saboda wani fillon da Mu'azz ya ɗauka alamar zai ƙara jifarta da shi. Nan ma Biebah ta girgiza kai kawai tana cigaba da aikinta. Ita kuma ta nufi babbar kular abincin gidan ta ɗauka plate mai ƙyau ta zuba abinci. Dan su babu wani banbancin kwanon cin abincin masu gida da masu aiki. Suna daraja su, suna basu girmansu na ƴan adam. Gorar ruwa da lemo ta ɗauka duk ta haɗa akan tray, har zata ɗauka Biebah tace, "Dama kin haɗa dana maigadi shima dan bana jin Hinde takai masa". "Small Mom wlhy zai mun nauyi, wannan ma fa da ƙyar zan kai". "Nauyi fa? Ninah anya bada tsallen tsalli watsanga ba ranar haihuwar ki? Ke dai son jiki kamar wata kasa." "Small Mom ni bama zanyi auren ba ai balle na haihun, babu inda zanje nabar Mammah ta da su Uncle's ɗina. Kema bana son kiyi aure, kawai muyita zamanmu a haka yafi daɗi". Ta ƙare maganar tana kashewa Biebah ido ɗaya. "Mara kunya kawai, ni wuce ki ban waje". Biebah ta faɗa tana dariya. Acan ƙasan ranta kuwa babu abinda ke faɗo mata sai fuskar Dada a ranar da aka ɗaura aurensa da Ninah ɗin, auren da Mammah ta hana kowa sake tada batunsa a gidan tace idan lokacin a sani yayi ayi. Murmurshi ta sake saki dabin bayan Nimrah data fita itama tana murmushin cikin tafiyarta ta yanga kamar yanda kowa ke faɗa. Dan Nimrah da Ruky irin ƴammatan nan ne masu shegen iyayi da gwalangwaso tun basu tafasa ba suke neman ƙonewa. Shekara biyu da suka wuce sannan suna 12years js 1 ta kamasu suna shirin makaranta sun ɗura suwa a leda sun saka cikin bra ɗinta da suka sata bata sani ba suka saka, suna ganinta suka ɓoye, ta tsaresu akan sai sun nuna mata kota rubuta ta ajiye duk randa Dada ya dawo ta nuna masa. Duk da basuyi hankalin sanin Dada ba labarinsa da yanda idan sukai laifi ake tsoratar da su da sunansa yasa suna jin shakka da girman mai wannan suna fiye da kowa a gidan. A wasu lokutan Ruky tafi Nimrah tsoro, sai ta sanya kuka tana nuna mata hannun bra ɗin. Ta shiga salati da tafa hannaye, cikin mamaki ta ce, ("Yanzu ku ubanwa ya saka ku saka bra?"). A lokacin bakin Nimrah a sama ta ce, ("Small Mom wasu shaggun yara ne su Zerah a ajinmu suyita tura ƙirji sama wai su masu abu, sai suyita mana iyayi da labarin period, idan munyi magana suna mana dariya wai mu yara ne ƙwailaye, shiyyasa muma mukace zamu nuna musu munfi ƙarfin ƙwailaye wlhy") dariya sosai zancen ya bata a lokacin, sai ma ta kasa musu faɗan ta shiga tuntsurawa. Ta kuma kasa hanasu tama fita. Ba kuma su fasa sakawar ba har sai da suka fara ƙirgar dangin na gaske, abubuwan suka fito. Shiyyasa idan ta tuno ita kaɗai sai taita dariya. Dan ko a yanzu tana fahimtar wataran ciko suke yi a cikin bra ɗinsu dan ƙirjin ya cika fiye da nasu duk da kuwa su duka ALLAH ya basu ba laifi. Sai dai da yake ba'a gama cika ƴammatan ba suna nan dai-dai da ɗan jikin su.....

<<<★>>><<<<★>>>><<<★>>> ★SOUTH AFRICA ★

"Amma baka ganin zuwanka gidan zai iya zama haɗari? Musamman daya kasance akoda yaushe Imran ɗin nan yana zaryar shiga da fita a cikinsu. Kai komai ma na zartarwar gidan shine tamkar a madadin abokin nashi a yanzu. Akwai zuminci mai girma da faɗi a tsakaninsu da bashi da shamaki da su fa". "Na sani ɗan uwa, amma bani da wani zaɓi sai nayin hakan. Shiyyasa nace maka zan ɓadda kama ai, kai dai kawai ka sama min irin facemask ɗin nan mai ɓadda kamanni da muke gani a films, dan gaskiya ba zan sake iya sati a wannan ƙasar ba. Dole na koma a gaɓar da za'a sake sabon wasa da yafi na baya zafi da armashi. Lokacin ɗaukar fansa yayi. Lokacin da Zak-Shadow zai tabbatar da KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA kenan." Ƴar dariya abokin nasa yayi da faɗin, "Ka san miyasa kake birgeni kuwa Dude?". "Sai ka faɗa". "Kai jarumi ne, tsayayyen mutum mai ra'ayin kansa da bai da tsoro. Na tabbatar zaka iya fiye da abinda ka faɗa. Ina bayanka kaje a dama da kai cikin wannan babbar ƙurar dan ɗaukar FANSA. Ni kuma na maka alƙawarin baka kowane irin taimako kake buƙata, kawai da kaji ƙyaras ka danna min kira". "An gama abokina, shiyyasa nake sonka". Tafawa sukai suna dariya cike da farin ciki. Kafin abokin ya ce, "To yanzu a matsayin me zaka je musu?". "Ina kan tunani ban yanke ba. Amma a labari mai inganci na samu cewar driver ɗinsu yayi accident 4weeks ago, inaga zanje matsayin me neman aikin tuƙin". "Alright hakan yayi, amma dai kabi a hankali dan kasan shima Imran ɗin nan shegen kansa ne, tamkar Hussain ɗin Zak-Shadow yake". "Karka damu oh, nima fa yanzu hatsabibin kaina ne, zan iya da kowane kalar zafin kansa. Tunda ma ba shine Hassan ɗin ba ai da sauƙi". "A Hassanu kam na can a garƙame". Dariya sukayi a taƙaice, saboda yanda abokin nasa yay maganar yana wani yarfa hannu da tallabe haɓa kamar ɗan daudu....

~~~~~~~~~~~~~~

★Nimrah kam data fito da trayn abinci kai tsaye bakin gate ta nufa, sai da tunda ta fito daga kitchen taji wani mummunan faɗuwar gaba ta sameta. Ajiyar zuciya mai ƙarfi taja tare da furzar da numfashi ta maida ƙofar ta rufe. Dama ta baya tabi saboda Mu'azz abokin faɗanta da kullum ne sai sunyi da shi ita da Ruky sama da sau goma. Yanzu zasu cashe anjima kaɗan ka gansu suna hira kamar abin arziƙi, da wahala kuma akai ƙarshen hirar ba'ai sabuwar rigima ba. Shine suke kallo kamar sakon su, shima kuma hakan yake kallonsu shiyyasa suka koma kamar kajinaye. Mu'azz tsokana, Nimrah da Ruky tsiwa. Kamar mara laka a jiki ta ƙaraso bakin gate ɗin, inda tunkan ta ƙaraso maigadi ya miƙe da sauri yana faɗin, "Autar Mammah da kanki? Ai da kin kirani na amsa ko?". Batace masa komai ba face ɗan murmushi, sai da ya amshi tray ɗin sannan ta furta, "Na baƙo ne, bara naje na kawo maka naka kaima, ko su Kulu sun kawo maka ne." "To to ƴar albarka sannu nagode. Basu kai ga kawowa ba kam inaga aiki ne yay musu yawa". Nan ma bata tanka ba ta juya ta koma, zuciyarta na ƙara ƙarfin rawa kamar zata faso ƙirjinta. Kai har cikin ƙafafunta take jin wani kalar sanyi na ratsata da kasalar jiki. Haka dai ta daure ta sake ɗebo wani abincin ta sake kawo musu. Dai dai baƙon mutumin na fitowa daga bayin maigadi da buta a hannu. Ido su ka haɗa, ƙirjinta yay wani mummunan motsawa, har ta kusa cin tintuɓe zata faɗi ALLAH ya taimaketa maigadi ya tare abincin data watsar da shi a wajen kam. Sannu maigadi ke mata yana kallon ƙafarta, haka shima baƙon a karo na farko ya ce, "Yi a hankali, badai kiji ciwo ba ko?". Idanunta a kansa ta jinjina kanta, sai kuma cikin rawar murya ta ce, "Ina yini". "Lafiya Lau, mun sameku lafiya? Ya tsofaffin?". A taƙaice ta ce, "Alhamdullah". Sai dai muryarsa sai wani irin kai kawo da mata maimaici take a cikin kunneta da zuciya da ƙwaƙwalwa. Sai kuma ta bar wajen da sauri. Tayi ɗan nisa ta waiwayo ta sake kallonsa illahirin jinin jikinta na gudu kamar mai shirin tsiyaye wa ta ƙofifin gashi, karaf kuwa suka haɗa ido alamar shima kallon nata yake. Sai kawai ta ƙara sauri. Koda taje bakin ƙofar ma ta sake juyowa nan ma suka haɗa ido. Wufff ta shige ciki har Biebah na tambayarta lafiya. "Ba komai Mom". Ta samu kanta da bama Biebah amsa a taƙaice tana share zufar data jiƙe mata goshi. Dole ta kama hijjab ɗin jikinta ta cire ta ajiye ko zata samu iska ta ɗan ratsata. Dan jikin window ma ta koma tana ta sauke ajiyar zuciya tsahon mintuna kafin ta koma gaban fright ta ɗauka ruwa mai sanyi sosai ta sha har roba ɗaya. Daga haka ta ƙaraso kusa da Biebah ta ɗauki wainar fulawa ɗaya tasa a plate dan dama ita suke soyawa ko hakan zai sa ta samu sassaucin yanayin da take ciki kafin wani ya farga.

A can gate kuwa murmushi maigadi yayi da faɗin, "Ɗan uwa bismilah ga abinci ko. Karka damu in dai Auta ce zakaga fiye da haka a wajenta. Ba komai ke ɗawainiya da ita ba sai gata da ƙuruciya. Dan kuwa kowa ji yake da su ita da hassanarta kamar tsoka ɗaya a miya a gidan nan". Mutumin da tunaninsa ya katse saboda maganar maigafi ya ɗan murmusa yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da kaiwa zaune. Sai kuma ya kalla maigadi yace, "Ƴan biyu ne kenan?". Kai tsaye maigadi ya ce, "Eh tana da hassana kwarai da gaske. Sai dai sam basa kama da juna sai a hallaya, Hassanar ma fara ce, ita kuma ka ganta baƙa. Fitinannun yara ne na bugawa a fasta. Sai dai akwai tarbiyya da girmama na gaba dasu. Dan ni dai tsakanina da su wlhy sai sambarka. Hakama sauran ma'aikatan gidan nan babu wanda zakaji yace musu ALLAH wadarai. Rashin jin su da sa'anninsu ne a makaranta. Wannan kam kullum cikin kawo ƙararsu ake gidan nan. Abin mamakin kuma su yayyen nasu babu mai dukansu akan hakan balle ƙwaƙwƙwaran tsawa. Dan ita wannan ɗin ma tsabar rashin ji ZAKANYA ake ce mata, ita kuma Hassanar DAMISA". Sai kuma yay ƴar dariya da tura masa abincin gaban sa. "Uhm kaga ci abinci nabi na cika ka da surutu. Tunda dai kana nan ai a hankali zaka gane komai in sha ALLAHU. ALLAH dai ya bamu haƙurin zama da juna. Amma zakaji daɗin zama da waɗan nan mutanen saboda mutanene na kirki masu karamci da ƙyaƙyƙyawar zuciya. Damma naji sunce babban gidan baya ƙasar, akoda yaushe zaka same su cikin begensa, narasa mi yake zaman yi a wata ƙasa shekaru masu zurfi haka". A karo na farko mutumin da alamu ya nuna bashi da yawan magana ya ce, "Ƙila aiki yake ko? Kasan masu kuɗin nan da son ƙasashen ƙetare kamar talaka da son gidan alfarma ne". Dariya maigadi ya tuntsure da ita yana cika baki da abinci. Shima mutum sai ya murmusa kawai yana cin abinci nasa. Sai dai gaba ɗaya zuciyarsa tayi nauyi sosai, kaɗan-kaɗan kuma sai ya kalla hanyar da Nimrah ta shiga yana jan ajiyar zuciya.........✍️

Tofa waye a South Africa? Waye kuma a gidan su Nimrah?. Mutane na yanzu fa za'a fara wasan😎💃.

14

.........Shekaru sun ja, ƙungiya ta ƙara bunƙasa da cikar samuwar sabbin members. A hasashe na hankali zuwa yanzu zamu iya cewa duk abinda ƙungiyar duhu ke buƙata na dukiya da mamaye babba da jaka na ƙasar sun same shi. Tama kai hatta nauyin masu faɗa ajin da hukunci da zartarwa yanzu a hannunsu yake sakamakon kafa mutanensu a dukkan madafun iko. Sun ɓatar da mutane da yawa da suka ƙi basu haɗin kai a cikin masu mulki da jami'an tsaro harma da sarakunan gargajiya. Kai hatta malamai basu ɗagama ƙafa ba da ma'aikatan gwamnati. Idan ka yarda ka bisu kuwa shike nan ka tsira da rayuwarka da dukiya anan duniya sai kuma jiran sakamakon shugaba mai hukunci akan hukuncin wawaye na irinsu. Abinda zai baka mamaki daga sakaye Zak-Shadow da suka ruruta wutar tabbatarsa zuwa yanzu babu wani harin ta'addanci daya sake wanzuwa a ƙasar, hakan kuma wani shiri ne nasu na musamman da manufar cimma buri a ƙasar dama wajen ƙasar. Zamu iya cewa sun samu, dan wani ɓangaren samuwar zaman lafiyar yasa hatta suma talakawan sun fara mantawa da wani batun Zak-Shadow balle gwagwarmayar sa a kansu. Yara masu tasowa ma kuwa basu san labarinsa ba sam balle jarumtarsa. Kowa ya shagaltu da neman dukiya da son jin daɗi. Hatta ƴan gudun hijira da suka baro ƙauyukan Bankaura da sauran su zuwa yanzu wasu a ciki sun koma. Sai dai su bazasu ce sun manta komai ba, dan da yawansu an bar musu tabo a zuciya da gangar jiki da har abada bazasu manta ɗin ba. A kowanne family zaka samu an rasa wasu a ciki ta hanyar mutuwa a wancan lokacin ko ɓata na rashin tabbacin ina su wane suke. Wasu ma babu kowa a gidajen nasu da dama sun rushe wanda suka dawo ma sai da suka dinga sake sabon gini sannan garuruwan suka farfaɗo. Wasu ko zaman birni da cikin ƙauyukan da suka koma ya riga yayi tasiri a jikinsu sun haƙura bazasu iya komawa ƙauyukan nasu ba. Haƙar ma'adanai kam zuwa yanzu sai abinda ma yay gaba. Dan tuni sauran ƴan ƙauyukan sun zama suke wahalar haƙo musu, wasu sukan mutu a cikin rami ƙasa ta rufesu wasu wahala ta yau da kullum kan kwantar da su ciwo har su rasu suma. Amma hakan baya hana matasa masu tasowa amsarsu da cigaban wahalar dan ta zama itace mafi sauƙi da girman hanyar cin abincinsu a yanzu. Yau da kullum takai ba mutanen yankin kawai ba har wasu matasan na zuwa da ga wasu yankunan suma yin aikin haƙar matsayin balaguro. Dan haka da yawan matan garin suka maida hankali kan sana'o'in abinci da kayan ciye-ciye yaransu ƴammata da masu tasowa na ɗaukar talla zuwa wajen. Ta haka ne kuma yara da yawa ke rasa budurcinsu sakamakon yaudarar da mazan ke musu da kuɗaɗen da suke samu na wahalar ayyukansu. Wasu iyayen basu sani ba, wasu ko son duniya da yaudarar kai ta rufe ganinsu sunyi tamkar basu fahimci halin da yaran nasu suke ciki ba. Sai tsautsayi yasa ciki ya bayyana jikin yarinya kaji iyaye na kuka da kururuwa mara amfani dan aikin gama dai ya riga ya gama. Daga haka wasu kan zauna har su haifi cikin idan cikin yaran garin ne a tilasta su aure su, idan ɗan balaguro ne kuwa ya gudu ya barsu da ƴaƴan shegu. Tsangwama da habaici irin na mutanen ƙauye kan saka yarinya ta gagara jurewa ta gudu ta bar gida ta shiga yawon duniya a cigaba da buga harka acewarsu aljanna ta mai rabo ce (Hummm). Tun iyaye na damuwa da sauran jama'ar gari akan irin waɗan nan sabbin abubuwan har zuwa yanzu ya zame musu jiki koda ta fasu ma babu mai nuna damuwa sai kalmar ALLAH ya ƙyauta daga haka kowa yaja bakinsa yay shiru. Dan kuwa a cikinsu suma ɗin kaɗan ne da basu da irin wannan kashin a ɗuwawu tunda al'amarin ya zagaye kusan kowacce zuri'a ta ƙauyukan yankin a yanzu....

An buga tambarin siyasa, lokacin sabon campaign na sake matsowa. Hakan ya saka members na ƙungiyar duhu dake cikin ƙasa da wajenta fara hallarowa babbar mahaɗa domin fara tsare-tsare da sabbin shiri kamar yanda suka ambata a watanin baya da sukai zaman ƙarshe. Idan oga Jush yay kira babu makawa sai an amsa saboda tsabar bin dokarsa da tsoron hatsabibancinsa kasancewarsa ɗan ƙetare mai ƙarfin faɗa aji da ƙarfa-ƙarfar madafun iko da aka san ire-iren su dayi a yankunan mu na masu ƙaramin ƙarfi da rashin gata da tun iyayenmu da kakanni suke bautar da mu. Kamar yanda suka saba haɗuwar cikin dare a wannan karon ma bata canja zani ba. Sun cika sabon meeting room ɗinsu taf da baka jin komai sai ƙarar ac's dake a kowanne bango, ɗakin mai cike da ƙarancin haske kamar yanda suka saba. A gaban kowa akwai mabanbanta abubuwan kaiwa baka. Wasu giya ce, wasu lemo, wasu abin motsa baki na nau'in abinci saboda ƙaracin cikakkiyar lafiya basa iya shan giyar ko lemon da akai dan more rayuwa. Wasu ma sigari suke busawa abinsu wasu ko ruwa ne kawai da suke ganin ya fi musu komai na kwanciyar hankalin jiki sai dai zukatan babu ƙyau da nagarta a cikinsu. Bayan oga Jush ya gama shan ƙamshinsa da bushe-bushen ƙatuwar sigarinsa ya fuskancesu cike da gadara da nuna isa irin ta shugabanci. "Da farko ina ma kowa barka da zuwa wannan kira da bin doka da oda. Anyi kira kun amsa, wannan kuma shine ke tabbatar mana da kowa matsayin abokan tafiya. Ƙungiyar duhu na alfahari da ku ƙwarai da gaske". Tafi ɗakin ya saki raf-raf-raf. Sai da sukai na fin sakan biyar suka tsagaita shi kuma ya cigaba da magana. "Shekaru takwas kenan da sakaye rasa kunya ɓeran tanka mai karambani akan isar da bashi da ita cikin ɗakin duhu. Hakan ya samu tsagaita dukkan ayyukan mu sai na nema da tara dukiya kawai. Ina da tabbacin kuma zuwa yanzu bamu da muka fara tafiyar ba hatta da sabbin members na ƙungiya sunci sunyi nak da abinda suka samu da har jikokin jikokinsu bazasu taɓa talauci ba". "Yes boss!!". Suka faɗa cike da tabbatarwa kowa bakinsa a washe. Shima murmurshin yayi yana sake gyara zama da kunna sabuwar sigarinsa ya kai baki. Sannan ya cigaba da faɗin, "To lallai idan har munci mun ƙoshi, kuma mun gamsu da ƙoshinmu inaga lokacin fara sabon wasa yayi. Lokacin tunawa taƙadarin nan Zak-Shadow yake ko mi alƙawarinmu na fasa zuciyarsa yayi. Lokacin da zai san duk DUHU sunansa DUHU koda na rufe idanu ne yayi. Sannan duhun dare abin tsoro ne koda da hasken farin wata a cikinsa. Zamu cika dukkan alƙawarin mu a kansa da kan mutanen da yake tunanin yana da jarumtar zamewa garkuwa. Sai mun kumbura zuciyarsa, sannan mu huhhudata mu tsiyayar da jinin cikinta ya koma ƙarƙashin na'urar likitoci tsakanin rayuwa da mutuwa. Dan haka zamu fara sabon mission, batch a, season one episode one". Raf-raf-raf wani mahaukacin tafi da yafi na farko ya gauraye hall ɗin. Bai hanasu ba sai da sukai iya son ransu fuskokinsu cike da farin ciki sannan suka tsagaita. Yanzu kam gefensa ya kalla, inda mataimakin shugaban ƙungiya ke zaune wato Mr Specter. Wani murmushin ƙasaita da isa yayi, dan tunda aka bashi wannan shugabancin girman kansa ya sake ƙaruwa. Sai da ya maida fuskarsa ya tsuke kafin ya fara magana cike da izza da isa. "Tabbas maganganun oga duk haka suke. Kuma muna matuƙar farin cikin kasancewarsa jagoran wannan tafiya a garemu. Muna fatan rayuwa mai tsaho a garesa da cikakkiyar lafiya. Ya cigaba da janmu daga nan har ƙarshen duniya". (Hummm, tunda ta ubanku ce duniyar ba🥱) Nan ma tafin suka shiga rabgawa kamar yaran nursery da basa gajiya da tafi da waƙoƙi🙄😏. Mr Specter ya cigaba da faɗin, "Kamar yanda ya faɗa zamu tafi batch a season 1 episode 1 a sabon mission ɗin mu. Dan haka a wannan karon zamu kasa shugabancin ƙasar uku ne. Mu ɗauki kaso ɗaya, sauran kashi biyu a bawa sabbin fuska ta yanda aiki zai tafi dai-dai. Hikimar haka zai sa talakawa dinga mararinmu da ganin mune muka dace da shugabantar su waɗan nan sun kawo musu azabobin rayuwa. Hakan kuma zai bamu damar baza ayyukan mu yanda muke so muke buƙata. Sai dai fa mun sani dama waɗan can kaso biyun dama suma a ƙarƙashin ikonmu suke ta ƙarƙashin ƙasa batare da sun fahimta ba, dan dukansu dai yaran da kuka raina ne da hannunku akan siyasa zaku bamu. Hakanne zai bamu damar mamaye su tamkar hadari a tsakiyar hasken rana. Dan haka kowa yaje ya kawo sunan wanda yake buƙata da shugabancin da za'a bashi". Sosai yanzu kuwa ɗakin ya hargiƙe da farin ciki. Duk da kuwa zukatan wasu sun sosu matuƙa gaya. Musamman ma waɗanda zukatansu suka kwaɗaitu da son a basu kujerar shugaban ƙasa da wasu manyan kujeru. Sai dai jawabin na yanzu ya tabbatar musu da suɓucewar wannan ƙudiri da burin nasu.......

∆∆∆∆∆∆★∆∆∆∆∆∆ ★PRISON★

Ɗaki ne ƙarami dan gaba ɗaya faɗinsa da tsayi bai wuce girman ƙaramin kitchen na mai ƙaramin ƙarfi ba. Babu wani kayan alatu a cikinsa balle ƙyale-ƙyale dan hatta fentinsa ma duk ya dushe wani gurin ma ya ɓare. Babu window sai wasu ƙananu guda kusan goma dake can sama gab da silin da bazasu wuce faɗin ƙofofin bulo na gini ba, tanan hasken rana ya haske ɗakin har ake iya tantance abubuwan dake ciki. Akwai katifa ƙarama irin ta makaranta a saman gadon ƙarfe shima dai irin na ƴan makarantar ne, gadon da bedsheet, da filo sai bargo suma dai madaidaita. Sai ɗan table dake jikin gadon ƙarami da ƴan tarkace a kansa na jaridu da jug na ruwa sai ƙaramar kula da flaks ƙarami irin na silver ɗin nan. Sai ƙaramar kula itama ta silver ɗin dai. Ta ƙasan table ɗin akwai kwali mai ɗan girma dake rufe bamu san mike ciki ba, sai samansa da Alkur'ani ajiye, da wasu littatafan addu'oi harma dana ilimi da hadith. Daga can ta gaban gadon randa ce ta ƙasa mai ɗan girma tanata raɓa alamar akwai ruwa a cikinta, a rufe take da plate na roba da kofin ruwa ƙarami da ake kira moɗa. Sai ƙarfen gadon ta can ƙarshe an rataye sallaya. A ƙasan ɗakin tils ne daya tsufa sosai irin na da ɗin nan da sai a gidan masu kuɗi kake ganinsa, amma duk da haka fes yake kamar kaci abinci a kansa. Akwai ƙofa guda ɗaya a ɗakin dake tabbatar da toilet ne sai dai a rufe take. Ba ƙamshi a ɗakin ba kuma wari, kamar yanda babu wadataccen haske babu kuma duhu. Ba sanyin ac ko fanka, babu kuma zafi mai cutarwa.........✍️

15

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull