Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 28
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 28: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 28. .........Cikin ɗan jin takaici ta furta, "Wayyo ji salon ƙara min aiki" Ta…
4,378 words
.........Cikin ɗan jin takaici ta furta, "Wayyo ji salon ƙara min aiki" Ta furta a hankali, tana ƙoƙarin fara tattaresu. A bazata taci karo da hoton Umman ta da shima ya faɗo daga cikin file ɗin. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, ta ƙurama hoton ido zuciyarta na hanƙoro, "Miya kawo hoton Ummana wajensa?" ta sake faɗa a fili tana fara ɗaukar sauran hotunan da suka kife tana birkitosu. Hotunan farko guda uku sojoji ne bata san su waye ba, sai dai a baya an rubuta sunan (Captain Musa, Ojo.... Da sauransu) sai a hoto na huɗu Kakanta ne cikin jini ga handcuffs a hannu kamar dai a video ɗin can data gani, banbancin kawai anan hoto ne. Koda tazo hoton bayansa jitai kanta na neman tarwatsewa, nan ma hoton Ummanta ne a cikin jini Daddy Imran tallafe da kanta shi kuma Dadan na tsaye da bindiga a hannu gefe ga wani mutum kwance da bindiga shima sai dai da jini jikinsa alamar an kashe shi ne. Hawaye masu zafi ne ke kwaranya a idanunta, ta ajiye hotunan ta fara buɗe file ɗin, bayan hotunan da bayanai masu yawa. Sunan ƙauyensu, sunan mamanta, sunanta harda hotonta tana yarinya, ɗayan hoton kuma tana ɗauke a hannunsa jikinta kaca-kaca da jini kamar tana barci ne ma oho. Gaba ɗaya tai masifar birkicewa, musamman da taga har ma wasu hotuna da bayanai game da wani wai shi Dagger da abubuwan da suka shafi sunan wata ƙungiyar duhu. Bayanan sun mata tsauri da yawa, ba komai take iya ganewa ba, amma duk da haka bata ajiye ba ta cigaba da dubawa...... A bazata aka buɗe ƙofar ɗakin data sakata razana. Yanda ta zabura da sakin file ɗin, komai na ciki ya ƙarasa tarwatsewa a gadon. Ya saka Dada da bai san da ita a ɗakin ba tsayawa cak. Dan dawowarsu kenan daga massalaci shi ko zama a falon baiyi ba ya hauro sama. Koda yaga Ruky ita kaɗai a jikin Mammah sai da ya tambayi zuciyarsa ko ina twin ɗin tata, ashe tana nan ɗakinsa tana abinda bai san mizai kira shi ba. Nimrah da gaba ɗaya ta gama birkicewa da ganinsa a bazata ga abinda ta gani takardun ta fara tattarewa da hotunan tana turawa cikin file ɗin kawai, ga hawaye sun kasa tsaya mata sai dai tana ta ƙoƙarin sharesu dan kar ya gani. Dada daya zuba mata ido takowa ya fara yi cikin ɗakin sosai batare da yayi magana ba har lokacin, wanda suka zubo ƙasa ya ɗauke, ya matsa da nufin ɗauke laptop ɗinsa da take neman hayewa ta firgita. Wani irin wantsalowa tai a gadon tare da wurgar da file ɗin a saman gadon ta nufi ƙofa. Sai dai yanda ta birkice ƙofar toilet ta nufa saɓanin ta fita. Nan ɗin ma dai da kallo kawai ya bita, shi yama rasa wane tunani zai yi akan yanayin nata. Ganinsa ne? Ko kuwa abinda ke cikin file ɗin ne?... Tunaninsa ne ya katse sakamakon sake fitowa da tai a bayin alamar ta fahimci ba hanyar da take nema bace. Ta nufi ƙofar a yanzu. Sai dai anan ma ta gagara buɗewa tanata kici-kici da key kamar sabuwar marainiya. Kansa ya girgiza kaɗan, tare da ajiye hotunan hannunsa da takardu daya kwashe a ƙasa ya shiga takawa wajen ƙofar, tsayuwarsa a bayanta ya ƙara harmutsata, kici-kicin ta ya ƙaru, har tana neman buga kai da bango. Dan ta tafi gaba ɗayanta da nufin kifewa a jikin bangon ko zata samu sassaucin halin da take ciki. A hankali ya lumshe idanun da suke neman juyewa ya sake buɗesu a kanta, kafin ya kai hannunsa jikin bangon dai-dai saitin inda ya tabbatar goshinta zai sauka, dan ya tabbatar yanda ta tafi gaba ɗayanta in har goshinta ya bugu bangon nan sai ya fashe. Nimrah ma ta gama sadaƙarwa harta runtse idanunta da ƙarfi, sai taji saɓanin saukar goshinta a bango ya sauka kan tattausan abu. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ce ta kufce mata, ta sake runtse idanun da ƙarfi. Yayinda can wani gefe na zuciyarta ke faɗa mata (Nimrah relax, wai mi kike yi haka? Bai kamata ki haukata kanki ba harya fahimta, ki tuna da zantukan mutumin daya baki videos ɗin nan mana). Tasirin maganganun zuciyarta ya sakata fara sauke ajiyar zuciyar nutsuwa, ta shiga maimaita kalmar: "لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله" "La ilaha illal-lah". A hankali nutsuwa ta fara riskarta, numfashinta ya daidaita, ta haɗiye hawayenta tare da kai hannu ta share wanda suka jiƙa mata fuska. Jinta a takure tamkar an mata rumfa ya sata jan jikinta baya a hankali tana ɗagowa, abinda ya bama goshinta kariya ta fara kalla, zuciyarta ta harba da ƙarfi ganin hannun Dada, gashi kamar ta jingina da abu ta bayanta kuma, ai bama ta san sanda ta juyo da sauri ba, sai da kanta ya bugi ƙirjinsa kuwa saboda a yanda yake tsaye. Ta waro idanu sosai tana mannewa da bango, tare da duƙar da kanta tana ambaton ALLAH a zuciyarta. Duk abinda take Dada bai motsa ba daga yanda yake tsayen tamkar ya mata runfa ma, ga hannunsa har yanzu yana a bangon bai cire ba. Sai dai ya zuba mata idanunsa masu kaifi. Kusan mintuna biyu suna a haka, Nimrah ji take kamar ta saki fitsari, dan yanda yake ɗin, gasu gab da juna, fuska a haɗe sai kace yana filin yaƙi. Rasa abin yi ya sata buɗe baki a karo na farko ta furta, "Dan ALLAH Dada kayi haƙuri". Bashi da alamar zai tanka mata har shuɗewar wasu sakanni, kafin a bazata ya jefa mata tambayar data sakata ɗagowa ta kallesa da manyan idanunta da sukai ja saboda kukan da tayi da halin da take ciki, duk da tana ƙoƙarin shanyewa. "Kinyi laifi ne?". Maimakon samun salama da kalmomin nasa guda uku ita wlhy sake hargitsata sukai. Sai kawai ta hau jinjina kai, kamar kuma wadda ta fahimci mi tayi, sai ta girgiza alamar a'a. "Uhhm! Mi kike yi anan?". "Mammah!... Mammah ce tace nazo nayi maka gyara". Tai maganar idanunta na sake cikowa da hawaye, dan a yanda suke tsayen ta takura, da ace wani ne ba shiba da tuni ta hankaɗe shi ta wuce, kota kirashi da ɗan iska, ƙilama ta ƙara da zagin tsamar nama. Amma ina, shi wargi ma waje yake samu. Sannan ko kura tasan gidan mai babbar sanda.... "An saki aiki, amma kina min bincike?". Ba ƙaramin dukan ranta furucin nasa yayi ba yanzu ma. Sai kawai ta fashe masa da kuka da faɗin, "ALLAH Dada ni banyi maka binciken komai ba. A gadon fa na gansu zan ɗauke suka faɗi, shine nake kwashe wa". "Hy Kiddo! Nayi ƙarya kenan?". Nan ma kai ta shiga girgiza masa tana tura baki. Ga hawaye share-share da ke neman sakashi murmurshi yana dannewa da ƙyar. Handkachiff ya fiddo ya miƙa mata, ɗagowa tai ta kallesa da yanayin kamar mai mamaki. "Na maida abuna ne?". Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Sai ta samu kanta da tura baki, caraf kuma ta riƙo handkachiff ɗin da yake ƙoƙarin maidawa aljihu. Ƙin sakar mata yayi, cikin sake ƙasa da murya ya furta, "Ai na fasa, dama aro ne". Cikin shagwaɓa tana sake sakar masa hawayen da take maƙalewa ta ce, "Dan ALLAH". Lips ɗin data tura ga hawaye na shatata ya zubama idanunsa da sukai matuƙar shigewa ciki, ga launinsu ya canja matuƙa. A bazata taji saukar yatsansa a tsinin hancinta ya ɗan ɗalle shi. Daburcewa ta nema yi, shi ko ya sake tsuke fuska yana wara mata idanunsa da faɗin, "Ni kike ma wannan shagwaɓan?". Itama sai ta waro masa nata idanun da faɗin, "Da... dahh!". "Uhumm Kid.... doo". Ya amsa mata da yanayin da tayi kiran sunansa. Ai da gudu kawai ta saki masa handkachiff ɗinsa ta juya baya ƙirjinta na wani irin motsi, dan gaba ɗaya ya juye mata kamar ba Dadan ba. Sai ta dinga jin ma anya ba mafarki take ba. Shi ma bai sake ce mata komai ba ya janye jikinsa a wajen. Sai ko data saki wata wawiyar ajiyar zuciyar data saka ɗan mitsilin murmushi kufce masa. ALLAH ya so shi ma ya riga ya juya ne bata gani ba, duk da koda kallonsa take ba lallai ma ta fahimci yayin ba. Sai da ya zauna akan sofa yana ciro wayarsa a aljihu, kallonta ya ɗanyi, tana a inda ya bartan tana faman cuɗa yatsu cikin juna, ya fara karantar wannan dabi'a tata ta cuɗa yatsu da har in tanayi akwai abinda ke damunta ko bata jin kanta free a inda take. "Zo ki ƙarasa aikin ki". Ya faɗa yana cire hular kansa da kwantar da bayansa da kan jikin kujerar ya lumshe idanunsa kawai. Simi-simi Nimrah ta tako bayan ta saci kallonsa, a yanayin da take ciki da ace ba shi bane ALLAH bazata iya ƙarasa aikin nan ba, dan kaɗaici tafi buƙata a yanzu. Tunanin take son yi, so take tai nazari akan abubuwa masu yawa. Tana ganin a yau kuma dole ta yi ƙoƙarin kiran mutumin nan, amma sai ta duba saƙon ƙarshen nan daya bata a randa sukai haɗuwar farko kuma ta ƙarshe da shi kafin taga idan ya dace suyi wayar. Tambayoyi take son yi masa, wanda da ace zata iya Dadan zata yima su, sai dai yi masan tamkar ganganci ne. To taya zata bama kura ajiyar nama, daga shi har Daddy Imran a yanzu zuciyarta rawa take a kansu. Idan ba rami miya kawo rami to?...........✍️ [12/24/2025, 2:58 PM] Zeenaran 😘: 69
.......Duk tana aikin tattare takardun data watsar da kanta ne tana wannan tunanin, yayinda take jin idanu a kanta, idan ta saci kallonsa kuma sai taga idonsa a rufe suke shi kam. Haka ta daure da ƙyar ta kammala har gyaran gadon. Ta kalli tsintsiyin shara ta kalla inda yake, a mamakinta sai taga ya maida ƙafafunsa saman table. To kenan yana kallonta, tunda har ya fahimci yanayin ta. Nan ma sai taji ta sake daburcewa, ta dai danne da ƙyar ta fara sharar dan gara tayi-tayi tabar ɗakin nan kafin zuciyarta ta fita waje. Sauri-sauri ta kammala ta hau mopping, turaren wutar data shigo da shi na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ta zuba a bonner ta kunna socket. Cikin sanɗa ta nufi ƙofar zata fita a tunaninta ko yanzu barcin gaskiya yake yi, duk da tana ji a jikinta ana kallonta, amma ita shari'a ko'a gaban alƙali ai sai da hujja, a yanda yake ido a rufe ita kam bata da hujjar cewa shine kenan. "Zonan". Cak ta tsaya tana mai runtse idanunta da ƙarfi. A zuciyarta ta furta (Na shiga uku na). Yanda bai sake maimaitawa ba, ya sata juyowa dole....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
"Wai halan zaka je wani wajene? Naga kanata sauri Abban Jiddah". "Juwairiyya da neman magana kike, kina duba lokaci kuwa? Nafa gaya miki zan raka Baffa ɗaurin aure, kuma da'an sakko massalaci ne dai-dai. Kalla agogo yanzu ƙarfe nawa? Gashi ko wanka banyi ba. Kuma da ƴar tafiya ba'anan cikin gari bane?". "Yi haƙuri na shafa'a ne gaba ɗaya, tunda dana tasheka ai tun ɗazun. Dan ko yara da zasu wuce makaranta sai da sukai cigiyarka." "Karsu damu idan na dawo ma gaisa. Ita wannan bata dawo gidan ba har yanzu?". "Wlhy kuwa, ni hankalina yama fara tashi". "Miye abin wani tashin hankali tunda kin san ina ta tafi. Dama kece ai kika dage, amma ni nasan yaran nan bazasu taɓa canjawa ba, uwarsu ta riga da ta ɗorasu akan wani layi da yayi tasiri a tare da su". "Kayi musu addu'a, kuma yau zan bincika dai duk da na kira wayarta yafi sau nawa bata shiga. Zan kira Jiddah taje gidan maman nasu ta bincika." Baki kawai Uncle Nasiru ya taɓe yana miƙewa abinsa. Itama sai bata sake masa magana ba tabi bayansa dan haɗa masa ruwan wanka. Ta kammala ta sake fitowa tattare kwanikan da yaci ɗumamen tuwon a dinning ta tadda baƙuwar bazata. Ba kowa bace face Hajiya Hasiba. Tayi wani zaman ƙasaita ɗan ƙwali agaban goshi. Duk da Ummu taji bugawar zuciya da wannan ziyara ta bazata sai ta hau ambaton ALLAH kafin ta ƙaraso falon. ALLAH ma yaso ta cikin kwalliyarta take fes Masha ALLAH. Ga ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Na tashi, dan shine tun daga kabasa har cikin gidan dama su khumra data saka. Ba Ummu ba itama kanta Hajiya Hasiba sai da gabanta ya faɗi, dan Ummu ta fita yarinta, ga nutsuwar zaman gidan aure bashi dai-dai da mata irinsu gantalallu da ba'a nan ba'a can kullum. Shi kansa ƙamshin nan ba ƙaramin rikita mata lissafi yay ba. Ta dai daure ta haɗiye tana wani yamutse-yamutse. Murmurshi Ummu ta saki da faɗin, "Oh manyan baƙi ne damu haka a gidan? Barka da zuwa". Wani kallon banza Hajiya Hasiba tai mata ta watsar, sai kawai Ummu tai murmurshi da komawa sabgar gabanta, dan irin mutanen nan ne ita marasa ɗaukar wulaƙanci, zata baka girma fa dan girma, dan wani lokacin ma sai ka ɗauka kamar bata san ciwon kanta ba, amma data fahimci daga wane jinsin hali ka fito tofa zata nuna maka ta fika iya kalar hali naka. Aiko bata sake bi takan Hajiya Hasiba ba ba harta kammala sabgarta. Koda ta kintaci lokacin fitowar mijinta wanka yayi sai ta koma ɗakinsa. Bata faɗa masa yayi baƙuwa ba ta hau taimaka masa ya shirya suna hirarsu cike da nishaɗi. Zuwa can sai gasu sun fito suna dariyarsu Hajiya Hasiba ta gama cika, ai ko sai dariyar tasu ta sake kunnata matuƙa. Shi Uncle Nasirun ma bai lura da ita ba sai da taja tsaki sannan ya waiwaya inda take. Nan ma ido ya ɗan zuba mata kamar wani makaho. Kafin ya juya yana kallon Ummu da faɗin, "Wai wacece haka zaune kuma Juwairiyya?".
★✨★✨★✨★✨★
Sum-sum Nimrah ta koma kamar munafuka ta ƙaraso inda yake, cikin ƴar bada tazara a tsakaninsu ta kai zaune saman tattausan milk carpet dake gaban sofa ɗin da yake zaunen. Sai dai bata yarda ta kallesan ba dai. Shima bai gyara zamansa ba, a yanda yaken kuma a haka ya cigaba da kallonta, har ita da kanta taji kallon ya mata yawa ta ɗago a hankali ta saci kallonsa. A mamakinta yana a yanda yake idanun a rufe kamar yanda ta gani, bata san ta ƙasa-ƙasa yake kallon ba musamman saboda kansa kwance yake a jikin kujerar. Samun kanta tai da shagala a kallonsa. Kallo irin wanda bata taɓa kwatanta masa ba. To inama taga fuskar yin hakan. Dada yana da ƙyau, irin ƙyawun da aka san baƙaƙen fata ƴan ƙasar nan tamu kuma yankin mu da shi. Sosai ta fahimci kamaninsa da Ammar da Aunty Ummi, kawai dai yafi su Ammar hasken fata ne sosai, duk da suma dai sauran yana kama dasu amma yafi yi da Ammar ɗin da Mamy ɗin gaskiya. Gashi dai duk ance ya girma kowa a gidan, amma jikinsa mai ƙyau ne, dan irin ƴan gayun matasan dattijan nan ne masu matuƙar kula da jiki da son gyara.... Ta matuƙar shagala a kallonsa har bata san ya motsa ya gyara zamansa ba ma. Sai da yay gyaran murya tai firgigit ta dawo hayyacinta, sai kuma ta kama sosa wuya na borin kunya. Basarwa yay kamar bai fahimci halin da take ciki ba, sai ma tambaya daya jeho mata. "Ta ya kuka san yaron yama wata fyaɗe?". Ɗiff ta ɗanyi na sakanni, kafin ta saki numfashi da ɗagowa tana kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta sake maida kanta tana ɗan tura baki. Sai kuma ta ce, "Dada!". "Uhumm". Ya amsa mata yana danna waya. "Ni da Ruky mun san abubuwa da yawa a makarantar nan kawai bama faɗa ne." Biye mata yay ya ce, "Uhmm-umm manyan yara ne ku kenan? Ta ya kuke sani?". Ajiyar zuciya ta sauke duk da ɓoyayyar damuwarta a kansa na nan a ranta bata gushe ba, to amma ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi ne. Dan haka ta fara jera masa zance. "Wanda ke son ƙawance da mu ne ke faɗa mana. Wani kuma mun sani ne dan muna gani. Suma fa malaman inaga dan suna jin tsoron students ƴaƴan masu ƙuɗi ne, kada a daina biyan kuɗin school fees ɗin su halan. Amma makarantar nan freedom yayi yawa, shiyyasa kaga mun zama jan wuya, dan mun gane ƙarfin, shike ƙwatarka kawai. Duk wanda ya mana sai mun masa. Shi shegen yaron nan ya jima yana abubuwa, dan dasu aka buɗe makarantar wai, gashi da ƴammata da yawa, haka zaita haɗasu faɗa wai shi namiji, ko ina mazan suke?...." Yanzu kam kaɗan ya rage dariya ta kufcema Dada ya dai daure, jifa wai ƴar yarinyar nan har ta wani san maza da wanda ba maza ba. Kai jama'a ƴar amana ta girma... Ita ko da bata san tunanin da yake ba ta cigaba da baza masa zance hankali kwance, har ma da abinda bai tambaya ba, shi ko yana recording. Tun yana basarwa har ya zuba mata idanunsa da sukai wani kalar laushi da ƙyalli-ƙyalli kamar ruwan kogi mai irin light blue ɗin nan na motsi. Kamar an kaɗa mata ƙararrawa ta farga da yanda ya zuba mata ido, sai ta tura baki cikin suɓutar baki da manta a gaban wanda take ta ce, "Dada banda kallo". Samun kansa yay da faɗin, "Mi yasa?". "Babu ƙyau ne ana ganin munin mutum". A zuciya ya furta, (childish) a fili kam sai ya samu kansa da furta, "Ke mummuna ce?". Hannu takai ta shafa fuskarta, sai kuma ta taɓe baki da girgiza kai alamar a'a. Sannan ta ce, "Hummm ai mutane suna cewa farare sunfi baƙaƙe ƙyau. Wasu fa har zagi suke da kalmar baƙar banza, ko irin dai hakan, wasu kuma da shafe-shafe ne, idan zaka bayyana tasu halittar sai ka gudu dan muni. Amma idan muna ganin ƴan comments na media a wayar Small Mom zakaga masu aibanta halittar mutane kamar ALLAH abokin wasan su ne. Ai naga shine dai yayi halittarsa, kuma mutum ko cinnaka babansa ma bazai iya yi ba balle shi. Amma jahilci da daƙiƙanci na damunsu. Idan kuma kace musu jahilai sai suce suba jahilai bane. Shifa jahilcin mai karatu yafi na jahili muni. Dan ILIMI DABAN, KARATU DABAN." A wani kalar slowly ya lumshe idanunsa dake neman fallasa sirrin zuciya. Ya haɗiye wani busashshen yawu daya saka maƙoshinsa yin sama ya dawo da sauri. A ƙasan zuciyarsa kam ayyanawa yake (Idan na biye abar nan ba gajiya zatai da zance ba) a zahiri kam buɗe idanun yayi a kanta, tsabar rashin man kai yasa ɗiyar ga bata gane komai da yanayinsa ba, koda yake banga laifinta ba, dan fuskar dai a tsume take kamar yanda suke ganinta kullum, sannan a zaunen ma a kamenwar sa yake cike da ƙasaita, launin idanun ne kawai suka sauya kamar abinda ke cikinsu zai amayo kansa. Haka ma muryarsa ta shaƙe tamkar mai mura. Dan ko kalmar ƙarshe daya furta da ƙyar ya iya fisgota. "Kiddo tashi kije." Dama a takure take, kawai dai surutun ne baki ya riga ya saba. Ko'a wane hali sai an furta. Yanda ta nufi ƙofa da sassarfa ya tabbatar masa dama hanyar fitar take nema. Sai kawai ya runtse idanunsa yana ambaton ALLAH dan shine kawai mafita.....
Itama data fito yanda ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tana kallon ƙofar ɗakin ya saka Imran dake haurowa hannunsa da kaya tsayawa kallonta. Kusan mintuna biyu kafin ta juyo da nufin barin wajen suka haɗa idanu. Da sauri ta haɗiye yanayin nata tace, "Daddy sannu da zuwa". Shima haɗiye nasa mamakin yayi ya amsa mata da, "Yauwa Daughter dama kina nan?". Sai da ta ɗan tura baki gaba da shagwaɓa ta ce, "Mammah ce tace nazo nayi shara". Murmurshi yayi da faɗin, "To ALLAH ya bada lada. Dadan naku fa?". "Yana ciki"........✍️
[12/27/2025, 1:45 AM] Zeenaran 😘: 70
........Shigowar Imran baisa ya buɗe ido ba, dan tunda Nimrah ta fita yana a yanda yake bai motsa ba. Sai dai ya zubama ƙofar data maida ta rufe idanu, shiyyasa a kan idonsa Imran ya shigo. Ganin haka yasa Imran nufin tsokanarsa. "Ikon ALLAH ashe kana ciki! Shiyyasa naga yarinyata ta fita a birkice. Alhajin ALLAH mi kai mata ne?". A mamakinsa yau kam murtani ya samu, dan cike da gatse Dada daya buɗe idanun sa da suka canja launi yana harararsa ya ce, "Abinda zuciyarka take tunani". Dariya Imran ya fashe da ita yana kaiwa zaune da faɗin, "Naga tabbacin a idanunka kam haƙun. Haba Suger Daddy ai ka bari na baka ita tukunna". "Kai dai ALLAH ya kimtsa wannan gurɓataccen tunanin naka". Dada ya faɗa yana sauke ƙafafunsa ƙasa da miƙewa ya shige bathroom. Shi dai Imran dariyarsa yake da cigaba da tsokanarsa. A haka bayan wasu mintina kusa goma sha ya dawo ya zauna inda ya tashi batare daya tanka masa ba....
★A ƙasa Nimrah na sakkowa Mammah tace mata ta ɗauki abincin Dadan ta kai masa gashi nan an haɗa. Da lafiya-lafiya ne sai ta shagwaɓe fuska. Amma yanzu sai kawai ta jinjina ma Mammah ɗin kai bayan ta gaida Uncles ɗin nasu da surutunsu ya cika falon. Babu Ruky babu Small Mom da Mamy ma. Hakan yasa ta ɗauka abincin salin alin ta juya ta koma saman, har Mu'azz na gulmarta da faɗin, "Oh yau su Ninah anyi hankali". Dariya su Ammar sukayi, Bilal ya ce, "Daina yabon ɗan kuturu, dan dai aikin Dada ne kawai, amma Ninah da son jikin tsiya. Ruky ta fita son aiki". "Itama in bata jin tsiyarta ba". Cewar Ammar. Nan ma dariyar sukayi. Dayyan da Afeef dai basu tanka ba. Dan har yanzu cike suke da Nimrah da Ruky a rai...
______
Nimrah data dawo sama kuwa ta ɗan tsaya kamar mai nazari kafin ta ƙarasa gaban ƙofar, nan ma sai da ɗan yi shiru na sakanni sannan ta kai hannu zatai knocking. Amma sai ta tsaya cak sakamakon furucin Daddy Imran. "Kana nufin taga komai dake file ɗin Zak...?" Sai da wasu sakanni suka shuɗe kafin ta jiyo Dadan ya bashi amsa da, "Ta gani, dan baje-baje na taddata da su a gadon nan, nasan kuma a haɗe na barsu cikin file ɗin daka kawo su. Naga tana kuka, sai dai ban fahimci dalilin yinsa ba, saboda bana jin akwai abinda zata fahimta". "Hakane, babu dalilin ta na fahimta, sai dai ina tsoron karta gane hoton Mamanta da Babanta dana tsohon nan da nata ma. Dan kasan a shekarun baya ta taɓa ma Mammah tambayar data saka ta sanar mata Mamanta ta rasu da babanta, na tabbatar wayonta bazai sa ta manta da hakan ba kuma, kuma bazata manta da fuskar mamanta ba. Ya rabbi, ALLAH yasa bata fahimci komai ba ɗin dai. Dan bana son a yanzu Nimrah tasan abinda ya faru a baya har sai mun kammala project ɗin nan, shiyyasa ma ko batun aurenka dake kanta muka ɓoye mata". Ƙirjin Nimrah yay wani bala'in bugawa, har bata san ta furta kalmar, "Aure?!". a lips ɗinta ba. Yayinda kalaman Daddy Imran ke mata wani kalar amsa kuwwa a cikin kunne da ƙwaƙwalwa. (Basa son ta san komai har sai sun kammala project ɗin nan? Ke nan ta tabbatar Dada nada alaƙa da mutuwar Ummanta ko mi? Idan ba haka ba miyasa zasu so karta sani to? Wane project ne haka? Sannan waye ma keda aure? Wa kuma ake aure?). Babbar bala'i, wannan wace irin rana ce a gareta? Mike shirin faruwa?. Wlhy ta gagara gane komai fa.... "Imran ina son zan sai gida a anguwa mai ƙyau, dan aikin nan bazai yiwu anan ba. Yaran nan basa ji, na tabbatar kuma zasu cigaba da shigowa ɗakin nan musamman ita, idan na adana wani abun wani zan iya mantawa na bari ta cigaba da gani". Furucin Dada ya katse mata tunani. Amsar da Imran ke bashi yasa ta ƙara kanga kunne. "Nima nayi tunanin hakan gaskiya, ya kamata ace kana da wani privete place kodan ma yanayi tsaro, kaima hakan zai baka damar yin aikin batare da damuwar komai ba. Sai dai yanzu sayen gida zai iya jan hankalin masu biye da lamarinmu". "To ya kake so ayi?". "Gashi ka duba cikin waɗan nan gidajen namu ko akwai wanda yay maka". Imran yay maganar yana miƙa masa wayarsa. Maimakon Dada ya amsa wayar sai ya zuba masa idanu. Cikin ɗan waro idanu Imran ya ce, "Wai kallon fa?". Kauda kai Dada yayi, sai kuma ya amshi wayar da faɗin, "Kana nufin har yanzu kana wannan business ɗin?". Cikin ƴar dariya Imran ya ce, "Zak.. nawa, to mi za'a fasa. So nake ma ka ƙara nutsuwa na maka bayani akan yanda abubuwa suka ƙara bunƙasa, dan cikin watannan zamu fara fitar da ayyukan gine-gine kai tsaye daga kamfanin SAMRAN in sha ALLAHU." Dada ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yana kallon hotunan gidaje tunaninsa na komawa baya, lokacin da Imran ya matsa su haɗa kuɗi su fara sayen filaye suna sayarwa, a lokacin gidan nan ɗaki biyu ne zagaye da langa-langa, ga albashinsu bai taka kara ta karya ba, ga biyan kuɗin makarantar su Ma'aruff, ga halin baƙin ciki da Mammah ke ciki akan abinda ƙaninta Tasi'u ya aikata mata da mahaifin Biebah. Yay gajeran murmurshi daya saka Imran ma murmusawa. Dai-dai nan Nimrah tai knocking ƙofar jin basu cigaba da zancen ba. Ga ƙafafunta sun fara nauyin gagara ɗaukarta, sai ta yanke shawarar kawai basu abincin ta fita ko zata samu filin yin tunanin abinda ke faruwa da rayuwarta itama. Dan tana ji a ranta addu'ar data dage da yi ce yau UBANGIJI ya fara warware mata gaskiya... Buɗe ƙofar da Imran yayi ya sata dawowa hayyacinta, tai murmurshin yaƙe da faɗin, "Daddy abinci ne in ji Mammah". Murmurshin ya mata shima da bata hanya alamar ta shigo. Kallo ɗaya taima Dada daya canja rigar shaddarsa zuwa baƙar t-shirt data kama jikinsa sosai ta kauda kai, duk da wandon shaddar na nan shi bai cire ba. Shi ko ko sau ɗaya baima kalla inda take ba, hankalinsa nakan waya gaba ɗaya. Ita dai tana ajiyewa ta fito abinta...
>>>>>>>%<<<<<<<