Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 29
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 29: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 29. Dariya taso kufcewa Ummu, amma dai ta daure ta gimtse, sai itama ta ce, "A…
3,540 words
Dariya taso kufcewa Ummu, amma dai ta daure ta gimtse, sai itama ta ce, "A ina kenan?". "Oh kema baki san da mutum ba ma ashe?". Uncle Nasiru ya faɗa da iya gaskiyarsa. Zaram Hajiya Hasiba da ke jin kamar zuciyarta zata kama da wuta ta ce, "Aikin banza aikin wofi, to sai me daga hakan? Shi daya ajiye ki bai isa bama balle ke sha-sha-sha kawai. Kai kuma Nasiru nazo maka gargaɗine akan saƙon daka aika Ismat ta isar min, ta isar da shi dalla-dalla, sai dai ka sani idan kace zakai wannan wasan da ni zaka faɗi ne ƙasa wanwar wlhy. Ai na faɗa maka ka manta ka taɓa haihuwar wasu yara a baya ko? Idan ba haka ba kuwa zakai kuka da idanunka. Idan ba jaraba da masifa ba yara sunce uwarsu suke so amma sai bibiyar su kake yi. Ka aurar da biyu an sakani na ƙyaleka shine itama Ismat kake yaudararta kai mata yanda kai musu. Ita kuma Nabeeha ka maidata gidan waɗan can faƙirin faƙara'u ɗin da basu ajiye ba basu ba wani ajiya ba jinin talauci da gallafiri. To wlhy ahir ɗinka, aniyar moɗa tabi randa. Dan Nabeeha tabar Haysam har abada kenan, yaje ya zauna da tsintacciyar magen daya kawo. In ce dai shike nan ai ko?. Kuma......" Cikin katseta Uncle Nasiru ya girgiza kai kawai yana kallon matarsa da faɗin, "Juwairiyya kinga nikam nayi nan. Ga kiran Baffa nan na shigowa. Ai min dambu fa kar a manta, yaji gyaɗa sosai da man kyaɗa da zogale. Sannan ayi abincin dare da Haysam dan yace zai shigo, ban sani ba ko shi kaɗai ko da su Ja'afar ne". "Ba damuwa duk za'ayi Abban Jiddah, ALLAH ya tsare ya kiyaye hanya. A gaida Hajjo da Baffan". "Zasu ji, a gaida yara idan sun dawo, Imam ya ɗauka motar nan ya kaita service yau kar yace min ya manta". "In sha ALLAHU". Ummu ta faɗa tana masa murmushi. Da alama tun fara maganar tasu Hajiya Hasiba tai kamar wadda tai sumar tsaye, ganin sun manna mata hauka. Har Uncle Nasiru ya fice bata farfaɗo ba, sai da ya maida ƙofa ya rufe. Ai wata ashariya data mulmulo Ummu bata san dariya ma ta kufce mata ba, ta dai samu ta shige cikin bedroom abinta ta sake mannawa Hajiya Hasiba hauka. Ai ko ta haukace ɗin, dan zage-nage ta dinga jerawa kamar wata ƴar tasha, lamarin sam babu aji a ciki dai zattakaici. Nan kuma da za'a taɓata sai tace ita mace ce mai aji manyan mata, ke ko ta kusa da matar tsohon shugaban ƙasa ai ba'a magana. Surukar Adeel ɗan Larabawa jinin masarauta, ga kuɗi.........✍️
Gaskiya ya kamata mu fara girmama Hajiya Hasiba, ita kuma Ummu ta fita sabgar ƙawar Zainabu ehe.😜🤭🥱...
[12/27/2025, 2:02 AM] Zeenaran 😘: 71
.........Nimrah kam maimakon komawa falo ɗakin su ta shige, ta dannama ƙofar key tana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin Ruky bata ciki. Kai tsaye wadrobe ɗinsu ta nufa, can wani lungun wadrobe ɗin data san hankalin Ruky zai daɗe bai je ba ta zaro abinda Dagger ya bata watanni biyu da suka shuɗe. Ƙasa ta zauna share-share ta zazzage. Hotuna suka faɗo. Hoton farko data fara cin karo da shi shine hotonta, kuma abin mamaki exactly irin wanda ta gani a ɗakin Dada yanzu. Sai dai na nan ma biyu ne, ɗaya tana a cikin kwalla, ɗaya tana a hannun Dadan jikinta duk jini. Hoto na biyu Ummanta durƙushe tana kuka a gaban Dada, akwai sojoji kusan biyar tare da shi. Ɗayan sojan shima taga hoton shi a ɗakin Dadan, an rubuta Captain Musa, sai wanda ke gefen haggunsa yana miƙa masa bindiga shi kuma Ojo taga ansa a nashi hoton acan ɗakin Dadan dai. Sauran hotunan ta cigaba da bi ɗaya bayan ɗaya, mabanbanta fuskoki, yara da manya, harda Iya kakarta. Wasu kuma sai ta jima tana kallonsu ma dan ta manta suna, amma kuma duk a hankali take ta faman tuna su wanene. Dan duk da akwai ƙuruciya a tare da ita bazata manta ƴan gidansu ba, musamman Iya da Kawu Tanimun ta, da abokan wasan ƙasa su Lawwali. Ai bama tasan ta fashe da kuka ba, dan abubuwa ne ɗai-ɗai ke dawo mata a rayuwarta da Kawu Tanimu a ƙauyen su. Ta jima a wannan yanayi na kuka kafin ta share hawayenta, zuciyarta na tabbatar mata yanzu ba lokacin kuka bane, lokacin nutsuwa da bincika gaskiya ne, lokacin daya kamata tasan ainahin wacece ita ne? Lokacin gane waye Dada waye Daddy Imran ne? Lokacin sanin kalmar nan da tafi kowace kalma mata girma ne, wato kalmar data fita a bakin Daddy Imran. (Aure) Ta kasa fahimta sam, auren waye? Sai da taji kamar Daddy Imran yace ita da Dada. (kai ina bataji daidai ba ne) Wani sashi na zuciyarta ya faɗa. Sai taji ta gamsu da hakan. Miƙewa tai ta tattare komai ta maida inda yake. Duk da fargabar dake manne da zuciyarta. Amma ta fara tunanin yadda zata sarrafa sirrin da ta tsinta yau a zuciyarta, ta fara fahimtar cewa mahaifiyarta ta kasance cikin wani babban labari, kuma akwai haɗari da zai shafi rayuwarta. Akwai ɓoyayyen al'amari daga zuriarta da tushenta da ake ɓoye mata kuma ya kamata ta sanshi. Sai ta ɗan yi murmushi mai ciwo, tana tunanin yadda Mammah zata ji idan ta san ta tsinci wannan. "Yanzu ya kamata in fara tunani… amma yadda zan yi, ba komai ba ne." ta faɗa a zahiri hankalinta na sake komawa akan hotuna da videos ɗin baya masu gogayya da juna. Tabbas duk abin da ta gani, yana haifar mata da tunanin cewa lokaci ya yi da zata fara fahimtar gaskiya da kuma ɗaukar mataki. Sannan dole tai amfani da wayonta akan Dada, ta cusa kanta jikinsa cikin hikima ko hakan zai sa taga fiye da abinda ta gani a yau, sannan tasan ainahin waye shi, ainahi fuskar da yake ɓoyewa da ƴan uwansa basu sani ba. Daga yanzu WASAN YA FARA...... Da wannan ta shiga bayi ta wanke fuskarta tayo alwalar la'asar da ake kira. Koda ta fito gaban mirror taje ta canja kwalliya sannan ta shimfiɗa abin salla. Dai-dai nan Ruky tai knocking ƙofar, buɗe mata tayi. Ruky na shigowa ta rungumeta cike da farin ciki tana faɗin, "Albishirin ki Ninah?". Cikin dauriya Nimrah dake murmurshi ta ce, "Goro". "Ammy haihuwa zatai". Idanu sosai Nimrah ta waro waje da faɗin, "Haba dai?". "Wlhy, gata can ma zasu tafi asibiti. Tun ɗazun na ƙagara ki gama gyara ɗakin Dada ki sakko ai. Mammah ma bata sani ba sai yanzu. Ni da Small Mom da Mamy kawai muka sani dan muna sashen tun ɗazun." Duk da damuwar da Nimrah ke ciki hakan bai hanata nuna farin cikinta ba. Salla sukai suka fito. Zuwa lokacin mazan gidan ma sun san halin da ake ciki. Dan har an wuce da Shariffa asibiti. Da wannan damar Nimrah tai amfani wajen zare jiki ta nufi gate, cikin sa'a ta samu Sanda kawai zaune maigadi ma salla yake, da alama sallar la'asar ce baiyi ba duk da ba'a jima da kammalawa ba. ALLAH ya sota, tana amsar wayar ta zagaya baya Dada da Imran da suka dawo salla na shigowa gidan, wuff Sanda ya shige bayinsu yana danne ƙirjin sha da ƙyar, dan yau kam ALLAH ne ya yabawa aya zaƙinta da sai anyi kaciɓus tsakaninsa da Dadan, duk da ba Dada kawai ba shi fa har Imran wasan ɓuya yake da shi daman. Shi kuma baima san Imran bai taɓa wani maida hankali a kansa ba. Number ɗin nan ta saka na wancan karon dan ta kasa mantawa da su. Sai dai har wayar ta tsinke ba'a ɗaga ba. Addu'a ta fara yi a ranta tana sake kira. Yanzu ma sai da ta kusa tsinkewa a ka ɗaga. Jin waccan muryar dai da bazata layance mata ba ta sata sauke ajiyar zuciya. Duk da Dagger a ƙage yake da wannan kira na Nimrah tsahon wattani biyu hakan bai hanashi yi mata na ƴan duniya ba. Dan maimakon amsa gaisuwar ta bayan ta sanar masa ita ce sai cayay, "Lafiya kika kirani?". Duk da taji haushi sai ta danne, maimakon masa rashin kuwa sai ta furta, "Kayi haƙuri, sai yanzu lokacin dazan iya kiran naka yayi. Ina son mu haɗu da gaggawa dan ALLAH". "Bani da wannan lokacin, dama na gaya miki zan iya ɓace miki ai. Yanzu ma sa'a kika ci na ɗaga wayar ki. Kuma yanzu zan kashe." "Dan ALLAH kada ka kashe. Sannan karka manta kai ka ɗora ni a wannan hanyar daban san da ita ba, bai kamata kai walagigi dani a lokacin da nake son sanin sirrin ta ba da taimakon ka. Ni mai rauni ce a yanzu, sannan makauniya dake buƙatar koda sandar jagora ce. Na maka alƙawarin bazan sake wasa da damar da zaka bani ba". "Shike nan naji, zanyi haka ne kuma kawai dan Ummanki data bani amanar faɗa miki gaskiya a duk lokacin da kika kai minzalin girman ki. Sannan ta bani wasu sirrika na baki. Ban baki da farko bane, sabo da ina son auna hankalinki da yardarki gareni. Yanzu sai ki faɗi ina zamu haɗu". "Na gode sosai. Sai dai kamar yanda na faɗa maka a baya ba'a barina fita ni kaɗai, sannan a yanzu gidanmu zagaye yake da jami'an tsaro saboda dawowar mutumin dake cikin video ɗin nan. Idan suka ganka zasu zarge ka ko kazo cutar da shi ne, dan saboda shi aka ajiye su......" Wani mugun girgiza zuciyar Dagger tayi, kaɗan ya rage yawun bakinsa ya biyo masa ta hanci tsabar yanda kalmar Nimrah ta dake sa. Da rawar lips ya maimaita, "D...awo wa...?". Ɗan jimmm Nimrah tayi, sai kuma tace, "Eh mana, ba shugaban ƙasa ya masa afuwa ba? An fiddo shi ko ka manta ne?". "Haka ne! Haka ne! Na manta ne sam, kin san abubuwan yawa suke". Duk da yanda yayi ɗin ya ɗan sake taɓa zuciyar Nimrah da bata mamaki sai ta share kawai. Ta ce, "Ka bani nan da mintuna goma, akwai mamanmu zata haihu suna asibiti, idan an yarda muzo zan kiraka da wannan layin, dan zan riƙe wayar a wajena sai mu haɗu a cikin asibitin". "Shike nan ba damuwa, sai na jiki". Ya faɗa daga can wasu jerarrun zufa na yanko masa ta ƙofofin gashin jikinsa gaba ɗaya. Ita ko da bata san yanayi ba wayar ta yanke tana barin wajen. Koda ta fito maimakon zuwa gate ta bama Sanda wayarsa sai ta wuce ciki kawai....
+++++++++++++
"Tabbas gaskiya mutumin nan ya faɗa Oga, Zak-Shadow na cikin ƙasar nan, a cikin gidansu. Kuma a ƙalla sati guda kenan yake cikawa. Kaga kenan kwanaki huɗu kacal tsakani da sanar da afuwar shugaban kasa. Wato mutumin nan lallai ya masifar raina hankalinmu. Dan a majiya mai ƙarfi na samu tabbacin Zak-Shadow yafi wata biyu da barin prison, a ƙalla satin da ya fara shiga office ya fitar da shi." Gaba ɗaya Oga Jush yama gagara iya cewa komai saboda yanda zancen yay masa dukan tasar ruwa a kai. Shin Yusuf Tafida ne ya raina musu hankali? Ko yaran da suka zagaye ko'ina a ma'aikatun ƙasar ne suka maidasu wawaye jahilai?. To lallai lokaci yayi da sabon wasa zai tashi, badai sai sun bari ayi mulkin lafiya ba. Daga shi Tafidan har Zak-Shadow ɗin zasu ɗanɗana kuɗarsu ne. Batare daya tofa komai ba akan batun ya bama Iron Fang umarnin sanar da meeting, ko ina kake kuma dole ka dawo ayi wannan zaman dakai, ba'a buƙatar kowa ya kiran waya ko video call. A zo kawai.. Iron Fang yasan oga ya ɗau zafi, sai kuma abinda ALLAH yayi, dan dole itama ƙasa ta ɗauki zafi a wannan gaɓar, zafin daya tabbatar muninsa sai yafi na baya girgiza kowa. Bai musa ko ja da nisa ba ya rubuta text message ya turama kowane member na ƙungiya. Shima ya kaɗa kansa ya tafi tashi sabgar sa........✍️
[12/27/2025, 2:21 AM] Zeenaran 😘: 72
.........Gaba ɗaya gidan Mammah ya hargitse da farin cikin saukar Shariffa lafiya. Bakin Uncle J kam har kunne. Suka rungume juna shida Twinyn sa. Bilal da Ammar ma suka haɗasu suka rungume. Dole suyi farin ciki zuri'arsu nata ƙara yawa da faɗi. A take sukai kiran Mammah suka sanar mata, dan tana gida bata bisu asibiti ba, sai ma su Nimrah ne dake ta damunta suje-suje?. Da farko ta hana su ne, dan bata son su tafi su barta ita kaɗai a gidan, dan Dada da Imran sun fita. Su Kulu kuma yau juma'a sun tafi gida su gaisa da mutane kamar yanda sukeyi duk bayan sati biyu. Su Dayyan kam sai a hankali, dan zatace ma tun bayan dawowa massalaci ta sake ganinsu ba. Garama Hanoon uwar son kallo da tana maƙale da tv kafin ta tashi itama ta shige. Hankalin Nimrah a rabe yake, ga farin cikin samun ƙaruwa da sukai ga lamarin son haɗuwa da Dagger. Ta tabbatar idan su Ammyn suka dawo gida ba lallai ta samu wata dama ba kuma balle suna hutun tahfiz ma gobe babu, dan cikin satin sama za'ai bikin saukar ƴan ajin sauka su su maye gurbinsu. Duk da suma dai saura ƙiris ne fa. Kawai dan makarantar nada ƙa'idar bin komai daki daki ne. Ganin yanda suka dage Mammah tace su duba idan driver na nan, idan baya nan sai dai su haƙura kam, tunda yanzu suma zasu dawo kasancewar an haihu lafiya asibiti bazasu riƙesu ba. Nimrah tafi kowa zumuɗi, kasancewar tata fitar da manufa biyu ne. Koda Ruky taje ta duba sai gata ta dawo baki a sama. Wai Malam Buba ya fita. Kaɗan ya hana Nimrah ta saki kuka, ta dai daure dan kar Mammah ta fahimci halin da take ciki. Suna cikin hakan ma sai ga ƴan asibitin sun dawo da kyakkyawan Jariri mai kama da Uncle Ja'afar Masha ALLAH. Sam ba haka Nimrah taso ba, dan ba ƙaramin ƙwallafa rai tayi da son haɗuwa da mutumin nan tai ba a yau. Sai dai ta san wannan damar kuma ta suɓuce mata. Dole ta saki jiki aka cigaba da murnar jariri, dan tabi ta katantane ta hana kowa ɗauka saboda Nimrah akwai son yara matuƙa. Kusan ma ganin jinjirin ne ya kwashe kaso mafi yawa na damuwar tata ta ɓuya daga fuskar ta, duk da sai da Mammah ta tambayeta ganin idonta ya canja tace abu ne ya faɗa mata.....
================
Hajiya Hasiba ta baro gidan Uncle Nasiru rai mace kiran Fomer First Lady ya sake harziƙa mata zuciya. Dan ko gaisuwa bata bari sunyi ba cikin bada umarni tace tazo tana nemanta duk inda take. Daga haka kuma ta yanke kiran batare data bari tayi magana ba. Tsabar takaici kamar zuciyarta zatai bindiga haka taji, kuma dole taje kasancewar da bazar First Lady ɗin take rawa. Akalar motar ta canja tana jan tagwayen tsaki. Mintuna kaɗan ya kawota gidan saboda gudu tai sosai. Securitys ɗin gidan sun riga sun san wacece ita a wajen masu gidan, tunma suna gidan gwamnati bata da shamaki. Dan haka kai tsaye suka buɗe mata gate ta shige. Tun a compound ta fara gamo da abin takaici, wasu matan ƴan siyasa dake zaman jiran son ganawa da First Lady ɗin sukai mata caaa. Sama-sama ta amsa su da cewar su jirata shiga tukunna, daga haka ta shige. Yanda bata tsaya falo na farko ba balle na biyu zai baka tabbacin lallai ita ɗin ƴar gida ce. Dan kaitsaye upstairs ta haura abinta. Ga masu aiki nata miƙa mata gaisuwa cike da girmamawa. A falon saman ta samu First Lady harda tsohon shugaban ƙasa, sai Zahir dake kwance a kujera zuru-zuru alamar baida isashen lafiya. Idonta akan Zahir ɗin ta gaida shugaban ƙasa da take kira Daddy, sannan ta gaida First Lady. Cikin ƙasa haƙuri ta furta, "Zahir lafiya kuwa?". Kai tsaye First Lady ta amsa mata da, "Inafa lafiya Hasiba, wasu shegun yara ne a makaranta suka nema illatashi. Shiyyasa ma Excellency yace na kiraki, dan binciken mu ya nuna yaran nada alaƙa dake". "Alaƙa dani kuma ranki ya daɗe? Nida yarana sun kammala har University su duka balle secondary. Sannan banda yaro namiji da har zai iya faɗa da Zahir". "Ba alaƙar jini ake nufi ba. Sannan ba maza bane yaran mata ne". "Mata fa! Suka masa wannan abun?. Amma ina fatan ba'a barsu ba ko Daddy?". Daga First Lady har Fomer President cikin takaici sukai ƙwafa a tare. First Lady ta ce, "Yanzu ne dai zamu ɗau mataki, dan mun saka ƴan sanda sun kama su amma sun sake su wai basu cika shekara 18 ba. Sai dai sukai maganar kotu." "Ai gwara aje kotun, kaji ƴan iskan yara kamar wasu ƴan daba. To wai ƴaƴan ma uban waye a ƙasar nan?". "Wannan shine dalilin da yasa muka kira ki. Dan muna son musan ƴaƴan waye ɗin. Dan a bincike na naga abokin mijin Nabeeha ne yaje ya cire yaran daga station, ya kuma kai lawyer. Sannan sunje da wani gadararren mutum daya ɓoye fuskarsa shine ma yace aje kotun Saboda yaran sun faɗi wata magana. Yanzu haka sun shigar da makarantar ƙara gaba ɗaya. Shi kansa alƙalin Excellency ya kirashi kan ya kora ƙarar yace case ɗin yafi ƙarfinsa". "Abokin Haysam! Imran kenan? Indai kuma haka ne zata kasance ƴaƴansa ne shi Imran ɗin. To amma waye suka je taren?". "Wannan shine amsar da muke nema muma. Yaran kuma ɗaya tabbas ƴarsa ce, dan da sunan sa take amfani, suna ma kama. Ɗaya kuma Muhammad". "Miye sunanta?". "Naja'atu Muhammad". "Mom anfi kiranta da Nimrah, a register kawai ake kiranta da Naja'atu ". Zahir yay magana da ƙyar a karo na farko. "Nimrah, eh lallai wannan yarinya sheɗaniyar yarinya ce. To ai itace nake gaya miki shi Haysam ɗin ya tsinto a ƙauye shekarun baya wai an kashe iyayenta. Nabeeha tace bata yarda ƴarsa bace shine ya aureta. Mafari kenna na samu Nabeeha ta baro gidan". Salati First Lady ta fara, shiko tsohon shugaban ƙasa da bai fahimci zancen ba ya nema ƙarin bayani. Nan fa sukai masa. A kuma lokacin ne tunanin Hajiya Hasiba ya dawo baya. Ta ce, "To kodai zancen Ismat gaskiya ne. Kusan sati guda kenan muna Chaina ni dake ba Amima ta kirani ba take min bayanin....." "Tabbas anyi haka". Cewar First Lady. Hajiya Hasiba ta ce, "To shine fa ni kuma na kullesu a ɗaki har yanzu na hana su fita, yanzu haka ma daga yima Uban nasu gargaɗi nake dan na zata shine ya shiryo makircin dan itama Nabeeha ya janye hankalinta. To lallai bana raba ɗayan biyu Haysam ne. Dan babu mai wannan ɗabi'ar gadarar irin tasa. To amma yaya haka? Duka yaushe shugaban ƙasa yace ya masa afuwa? Kodai makirci ne abun dama ba'a prison ɗin yake ba?". Gaba ɗaya tsohon shugaban ƙasa ya ma kasa magana, sai first lady ce ta furta, "A lallai biri yayi kama da mutum. Kuma yanzu na yarda gargaɗi mai razani akama alƙalin nan. To ai inaga Hajiya Hasiba kawai ki bar Nabeeha ta koma gidan, ta haka ne zamu san gaskiya. Dan tabbas bazamu bar wannan abin ya tafi a banza ba, dole ne yaran nan sai sun ɗanɗan kuɗarsu. Bazasu illata min yaro a banza ba, dan yanzu haka likitoci sunce sai an fiddashi waje, in ba haka ba nan gaba ya samu matsala a privete part ɗin". "Kai jama'a wann shaggun yara. Banƙi ta taki ba ranki ya daɗe, kanku komai kuma zan iya yi. Amma baƙya tsoron sharrin Adeel. Jiya jiyan nan nake ganin saƙonshi wai na shirya zai sake sauka a ƙasar nan, kuma wannan karon komai yake so ayi a gama". "Karki wani damu, ki barmu dashi. Yanzu kawai kije ama Nabeeha gyara kona kwana uku ne ta koma a cikin satin nan. Zan tura miki kuɗi, zan kuma kira ƴar Kamaru ta sameku gida". "An gama raki ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma".....
×==×===×==×===×==×
Sai dare Dada ya dawo gidan, lokacin kusan tara. An kawo masa jinjiri domin ya gani. Nimrah dake maƙale da shi ce kuma ta kawo. Dan har faɗa sukai da Ruky babu jimawa da taƙi bata shi shine tai zuciya taje tai kwanciyarta. Itako ko alamar barci bata ji, ga yunwa na cinta taƙi cin abinci, Mammah da Ammie dake gidan sunyi faɗa har sun gaji. Tunda ta shigo falon ya zuba mata ido. Dan yanda ta rungume jaririn famm abinta sai tai masa ƙyau. Kai tsaye ta nufo inda yake tunda shi akace ta kawo mawa. Cikin tsokana Ammar yace, "To ALLAH yasa dai shi Dada a bashi kona minti biyar ne, dan mu minti bibbiyu aka bamu". Dariya Mammah tayi, "Ai ku kun samu minti biyun ma, Mu'azz sai a hannunta ya gani. Ruƙayya kam yanzu ba jimawa ta shige tayi fushi". Dariya Bilal da su Ma'aruff suka sanya, Mu'azz ya dalla mata harara da faɗin, "Ai wlhy sai na rama". "Sai dai kuwa ka rame". Cewar Nimrah tana murguɗa baki. Kasancewar Dada a falon kuma ya sa ta tsaya iya hakan. Takawa tai ta ƙarasa inda Dadan yake, dan shima Mu'azz ya mata shiru saboda Dadan na nan. Maimakon ta bashi sai ta durƙusa a gabansa tana faɗin, "Dada gashi ka gani a haka. Idan aka tattaɓashi da yawa zai yi ciwon jiki"...........✍️
🤣🤣ASHE Dadan ma bazai tsiraba Ninah😂🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️.
[12/27/2025, 2:35 AM] Zeenaran 😘: 73