Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 17
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 17: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 17. Yanzu dai ta zubawa sarautar Allah…
3,242 words
Yanzu dai ta zubawa sarautar Allah ido, ta daina haukan guduwa daga cikinsa tun da ta ga babu hanya, amma fa bawai hakan yana nufin ta haƙura ba, tana nan akan bakanta! ta lura cewa idan har zata cigaba da borin haukan da take yi masu tofa bazata ta6a samun nasara ba, wannan dalilin ne yasa ta nema ma kanta maslaha, tayin rayuwa cikin salama don ta samu damar yin bincike ta gano ainihin sarƙaƙiyar dake acikin Kurkukun ƙaddara, don tun daga kan ma'anar Sunan kurkukun fassara ce me zaman kanta, Kuma kullum tana cikin yin azhkar na safe dana mare ce, wanda daddynta ya koya mata, har tsakar dare bata runtsawa xama take yi tsakiyar gadonta, ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu'o'i akan Allah ya kawo mata mafita acikin rayuwarta,
*Boss Bature✍️💋*
*After some weeks*
Zaune take a tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, idanuwanta suna arufe fuskar nan ta yi jawur idanuwan sun kumbura, ga busassun hawaye duk akan fuskarta, Kasancewar safiya ce ba su jima da farkawa daga bacci ba, Sautin dariya taji ƙasa ƙasa taji muryoyinsu suna yin gulmarta "Wari take yi, tun da tazo bata yi wanka ba daga gani dai ƙazama ce," can ta ji muryar wani ya kuma cewa"idan muka ƙyale ta mu zamu cutu, jiya fa daƙyar nayi bacci saboda warin jikinta gaba ɗaya ya cika ɗakin nan," tuntsure wa su ka yi da dariyar shaƙiyanci, "Ku ta shi muje muyi mata magana, ta je ta yi wanka, in ba haka ba mu zamu yi mata da kan mu," haris ne ya bada wannan shawarar, Angel dai ta natsu tana sauraronsu, dama mugun haushin su take ji, tana jiyo sautin tafiyar su a bakin gadonta suka tsaya kusan su shida, Gyaran murya ɗaya daga cikin su yai mata"ke tashi ki je ki yi wanka" a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗan kalle su, wanda ya yi magana shi ne Haris, a halitta baƙi ne yana da jiki, "Ba zamu zuba maki ido kina cutar damu ba, jiya nan daƙyar mu ka yi bacci saboda warin jikin ki, don haka ki tashi kije ki yi wanka ko mu yi maki da kanmu" cike da ƙwarin gwiwa javed ya yi maganar, dogo ne launin fatarsa chocolate, Jin ta yi banxa ta ƙyale su yasa Mubeen jinjina kai ya kalli naufal dake a gefen shi yace "je ka cika mana bokiti da ruwa," ya yi maganar yana naɗe hannun rigar shi, Danish da ke a kishingiɗe saman gadon shi bai tanka masu ba, yasan suna yi duk don su ƙuntata mata ne saboda tsanarshi da ta yi, ƴan matan dake a tare da su Deeja da yasmeen, sun ruqe qugu suna sakin murmushin mugunta, Da alama dai hada ƙuruciya ke damun su, don dukan su gaba ɗayan su baza su wuce shekara shabiyar ba, mazan cikinsu ne ke akwai ƴan shekara sha bakwai, kamar danish dasu haris, "Bakya ji ana maki magana"? muryarta na kerma tace" duk wanda ya yi gigin ta6a ni, zanyi mashi illah, babu ruwanku da rayuwata," tamkar xata fashe da kuka ta yi maganar, "Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, zamu gani mu dake wazai ma wani illah," haris ne ya yi maganar, tare da naɗe hannun rigarshi yace dasu Naufal su ɗauko mashi ita, akaita toilet su yi mata wankan tsarki, Jin haka yasa ta durowa daga saman gadon, Duk da jikinta ba ƙwari daure wa kawai take yi, hannu haris yakai zai ruƙo kwalar rigarta, aikuwa ta daddage ta ɗaga kafarta tare da kai mashi naushi tsakiyar cikin shi, azabar zafi yasa ya yi saurin dafe cikin shi, rai a6ace javed ya kai mata bugu aikuwa ta damƙi ƙafar shi ta hagu ta dinga janta har saida ta yarfar dashi ƙasa, faɗa ne ya kaure a tsakaninsu, bugu tadinga kai masu da naushi, dama ta ƙware wurin iya cixo da yaku shi, duk sai da ta raunata su, sai faman nishi suke yi, da taga ta gama da mazan ta koma kan matan,
Haɗe kawunan su tayi, ta ruƙo gashin kansu, tadinga ja tamkar xata tsunka su, kuka hada majina suka dinga yi,
koken koken da suke yi ne ya farkar da su Batool da sauran ƴan uwan nasu dake bacci, ganin yadda Angel take Mazgarsu yasa suka sauko daga saman gadon suka nufeta suna ƙoƙarin rabata da su, daƙyar suka samu nasarar janye Angel gefe ɗaya, sai huci take yi kamar kuranya, Su deeja da yasmin suna zuƙunne ƙasa, dafe da kawunansu sai kuka suke yi,
Duk wannan abun dake faruwa tsohuwa tana a tsaye baƙin ƙopar ɗakinta, hannunta ruƙe da sanda, ta yi tsaye tana kallon sabuwar ƴar wasan damben da suka samu,
Danish kuwa dake kishingiɗe saman gadon shi, hankalin shi kwance dama yasan za'a rina, shiyasa bai shiga cikinsu ba, koda suke xancan zasu je suyi mata magana akan wanka, don ya lura ƙarfi ne da ita, gashi duk cikinsu itace ƙarama amma tafi su ƙarfi,
Gyaran murya tsohuwa ta yi, da sauri angel ta ɗago tana haki, suka haɗa ido da ita,
"Aikin ki ya yi kyau, tsanar da ki ka yi masu har takai ga bugunsu so ki ke ki kashe su?" Rai amatuƙar 6ace tace" bugun su yanzu na fara idan har ba su daina shiga gona ta ba, kuma wlh idan har baku fitar dani daga cikin kurkukun nan ba, zan addabi rayuwar kowa ne, nace banaso ku ƙyale ni inyi rayuwata na tsani gidan nan, Natsani kowa dake acikinsa, kince nan gidan marayu ne kuma za'a gatanta mu but why kuka killace mu sai ka ce dabbobi? haka ne gatancin Abinci sau ɗaya a rana? Kun hana mun yin ibada, uwa uba kun haɗa mu rayuwa da maza a ɗaki ɗaya? Me hakan yake nufi iye"? Idanuwanta azazzare ta yi maganar, tamkar ta sanya hannu ta shaƙo wuyan tsohuwar hake take ji,
Maimakon tsohuwar ta bata amsoshin tambayoyinta sai ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya, Runtse ido angel ta yi cikin jin zafin dariyar tsohuwar, cije lips ɗinta ta ɗanyi kafin ta buɗe eyes ɗin nata,
"Wlh ban yadda dake ba, saboda gaba ɗaya babu gaskiya acikin kurkukun nan, idan kun 6oye mana manufarku ta killace mu anan baku isa ku 6oyewa Allah ba, yana ganinku kuma asannu Allah zai warware mana komai, ni nasani zuwana gidan kurkukun nan jarabawa ce ta ubangiji........."daƙyar takai ƙarshen maganar saboda hawayen da suka cika mata idanuwanta,
"Dabbar dake yawo a daji, tafi mu gata tafi mu ƴan ci, idan su basu damu ba, zai iyayiyuwa don sun taso rayuwarsu acikin kurkukun ne, kuma sunsan basu da kowa, amma nifa ina da dangina masu sona, hakanan anje an sato ni an kawo ni cikin wannan munafukin ƙaddararran kurkukun mara kan gado," "Angel" muryar batool ce ta ambaci sunanta, a harzuƙe angel ta juya baya tana kallon batool tace, "Nasan bai wuci ki ce xaki bani hakuri ba, akan inja bakina inyi shiru, Batool bazan Iya ba, narasa gane meyasa bakwa fahimtata ne, iya cutuwa an cutar da rayuwata, tun ina jinjirata mahaifiyata ta gudu tabarni a wulaƙance cikin kwamin wanka, nata so cikin so da ƙauna na mahaifina, An raba ni da shi, An kashe mun shi duk da har yanzu ban gasgata hakan ba, sannan na faɗa hannun fulanin daji, na rayu acikin daji tare dasu a matsayin tsintacciya, wai ni Angel ƴar gidan daddynta, na shiga mawuyacin hali na rashin mahaifina atare dani, na saba dashi mun shaƙu sosai, komai shi yake yi mun wanka, ya gyara mun gashin kaina mu kwana rungume da juna, dama haka rayuwa take? Lokaci ɗaya narasa gatancin nan, na dawo ina kwana a saman tabar ma cikin bukka, bani da abinci daya wuce gasassar masara da fura, yanzu kuma gashi na tsinci kaina acikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, ya a ke so inyi da raina? Wlh da rayuwa acikin kurkukun nan kwara na ƙare rayuwata a hannun fulani daji, koba komai zan sha iskar duniya, in yawata inda nakeso, inyi rayuwar ƴan ci, Amma nan fa? Ta karfi ta tsiya aka kawo ni cikin shi banma san ta ina aka shigo dani cikin gidan kurkukun nan ba, don kuwa sai da aka fara gusar mini da hankalina tukunna, in banda munafurci taya xa'ace gidan marayu ne? Meyasa da za'a kawo ni cikinsa ba'a barni cikin hayyaci na ba? Meyasa za'a hana mu shige da fice, An tauye mana haƙkin mu na rayuwa an hana mu sakat wai da sunan za'a gatanta mu......................'
(SHIN ME KU KE TUNANI AGAME DA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? MU HAƊU A NEXT PAGE IN ALLAH YAKAI MU DA RAI DA LAFIYA, HAR YANZU FREE PAGES NE WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA YI MUN MAGANA 08103884440, WASAN FA YANZU AKA SOMA BUGA SHI, DOMIN KUWA BAMU NUTSA CIKIN LABARIN BA, YANZU AKA FARA)*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
Daga alƙalamin Boss Bature✍️
Cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, hawaye ta ko'ina akan fuskarta, tabbas jikin kowannan su ya yi sanyi, banda mutun biyu, danish dake kwance saman gadon shi sai Haris dake zaune ƙasa ya dafe cikin shi, Saukowa batool ta yi tare nufar inda angel take tsaye agaban tsohuwa, ta dafa shoulder ɗinta"I feel ur pain angel, abun da ciwo labarin ki akwai ta6a zuciya, dole kiji ɗaci aran ki, kuma dole ki ƙuntata acikin kurkukun nan, abunda yasa kika ga mu ba mu damu ba saboda bamu da wanda zai yi kukan rashin mu! Mu matattu ne a idon jama'a kamar yadda tsohuwa ta faɗa mana, a gidan nan aka raine mu agidan nan muka taso, tunda mu ke bamu ta6a yin tozali da hasken daya fito daga wajen kurkukun nan ba, ina yawan tambayar kaina koya wajen kurkukun nan zai kasance? Ya mutanan dake rayuwa a wajen sa su ke? Bani da amsar tambayata amma ina fata wata rana nima wata rana in fita daga cikin sa, sai dai nasan abune mai wuya......" cikin sanyin murya takai ƙarshen maganarta, "Zan iya zuƙunnawa saman gwiwowina in roƙe ki akan ku fitar dani daga cikin kurkukun nan, inaso na rayu cikin ƴan uwana" angel ce ta yi maganar muryarta a rauna ce,
Jinjina kai tsohuwa ta yi a yayin da take binsu da kallo da waɗannan kwarkwararrun idanuwan nata, tsawon mintuna kafin tace"koda ace kin zuƙunna saman gwiwowin ki don ki roƙe ni akan in fitar dake daga cikin prison ɗin nan, hakan bazaiyi aiki ba idan ku ka yi haƙuri a sannu zaku fahimci manufar wannan kurkukun na tara ku acikinsa, Amma a yanzu shawarar da zan baku shi ne, ku so junan ku tun da baku da kowa ku xama naku ku kaɗai, ku kasance masu faranta ma juna" daga haka bata ƙare cewa komai ba, ta dogara sandarta tare da juyawa tana ɗangyala ƙafa ta nufi cikin ɗakinta, tana shiga taja ƙopa ta datse,
Zubewa angel ta yi saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsancin kuka mai cin rai tamkar ranta zai fita,
Rankwafawa batool ta yi tare da ruƙo hannayen angel cikin nata, ta miƙar da ita tsaye, ta rungumeta ajikinta tana lallashin ta, sun ɗauki tsawon mintuna, kafin ta raba jikinsu,
Kallon sauran ƴan uwan nasu ta yi, kowa yana a tsaye banda Danish dake kwance
Ɗaya bayan ɗaya ta shiga kiran sunayen su"Hannah, Hibba, deeja parveen, Eve, yasmin, rubina, Aziza" kowa ya kasa kunne yana sauraron abunda zata ce masu, juyawa tayi kan mazan dake acikinsu ta ambaci sunayen su one by one"Danish, javed Haris, mubeen, naufal" sai faman huci haris yake yi saboda haushin bugun da angel ta yi masu, Calmly ta soma magana cikin sanyin murya"kamar yadda tsohuwa tace mu so junan mu, Let's consider ourselves as blood relatives, inaso mu yi ma juna alƙawarin duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, Sa'annan bana jin daɗin yadda ku ke ware angel acikin mu, i thought we are all the same, bamu da banbanci jinsi ɗaya ne mu da ita duk abu ɗaya ne, idan ba mu so juna ba, wa zamu so? Nasan kuna jin haushin angel ne saboda abubuwan da take yi wanda bakomai ya jawo hakan ba face ƙuntata rayuwarta da a ka yi, taya mutumin da ya saba rayuwar shi a sake rana ɗaya a tsamo shi daga cikin danginshi a kawo cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA! taya bazai ƙuntata ba"? dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana bin fuskokin su da kallo, "Batool ni dai inason Angel, kuma bazan ta6a faɗa da ita ba, zan ɗauke ta tamkar yadda na ɗauki kowannan ku," bakowa bace ta yi maganar fa ce AZIZA, yarinya ce me ƙarami jiki fara ce sosai duk cikin su babu me gajartar ta, ɗaƙyar angel ta iya buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗaura su akan fuskar aziza da ta yi maganar, ba ƙaramin son yarinyar ta ji ba, saboda ita kullum a cikin fara take baka ta6a ganin fuskarta a ɗaure, "batool, nima xan ɗauke ta tamkar yar uwata," kallon wadda ta kuma yi magana angel ta yi, hibba ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi, Lumshe ido angel ta ɗanyi tare da buɗe su tana ci gaba da kallon su, "Nima na goyi bayan Batool, angel tamkar ƴar uwa take acikin mu" acewar Parveen Murmushi batool ta ɗan saki, har cikin zuciyarta ba ƙaramin daɗi taji ba, Miƙa hannunta na dama tayi saman iska tare da kallonsu tace"ina so muyi wa juna alƙwarin kasancewa atare, zamu so juna kuma zamu taimaki juna, sannan babu faɗa atsakaninmu kuma babu nuna wariya, duk wanda ya amince ya ɗaure tafin hannun shi a saman nawa," Angel ce ta fara ɗaura tafin hannunta saman na batool, matsawa aziza ta yi itama ta ɗaura nata hannun, Hibba ta ɗaura nata parveen ma ta ɗaura nata, kallon sauran Batool ta yi ganin sun ƙi matsowa su ɗaura nasu hannuwan, "Duk wanda bazai so zaman lafiya a cikin mu ba, babu ruwan mu da shi domin kuwa baya atare da mu" Jin wannan maganar da batool ta yi yasa Eve ta matsa ta ɗaura nata hannun, rubina ma ta sanya nata, mutun biyu suka rage Cikin mata basu sanya hannayensu ba, deeja da yasmin Sai kuma mazan su, don shi danish har yanzu bai motsa daga saman gadon shi ba,
Zuba masu ido batool ta yi tana bin sauran da su ka rage da kallo, Masu girman kan Cikin su,
"Idan har baku ɗaura hannayen ku ba, kada ku yi tsammanin idan wani abu ya faru da ɗaya daga cikin ku, xamu share mashi hawayen shi,"
Gyaɗa kai Javed ya yi tare da kallon su haris, kafin ya wuce su zuwa inda su batool su ke A tsaye shima ya ɗaura hannun shi fuskar shi ɗauke da murmushi ya ce"Nima ina goyon bayan ki batool, kuma ina ba angel haƙuri akan irin wariyar da muka nuna mata" yakai ƙarshen maganar idanuwan shi akan fuskar angel, itama kallon nashi ta ke yi, har cikin ranta taji daɗin waɗanda suka nuna suna sonta, Matsowa kusa Yasmin ta yi, "idan muka yarda da junanmu, muka so junanmu tabbas xamu cimma nasara, nima ina goyon bayan batool," takai ƙarshen maganarta tare da ɗaura hannunta saman nasu, Kallon deeja su ka yi dake a tsaye ta toge saboda haushin angel take ji, Matsawa mubeen ya yi da sauri haris ya ruƙo hannun shi"badai zuwa zaka yi ba"? Jinjina mashi kai ya yi"zuwa zanyi, saboda inason mu samu maslaha a tsakaninmu," ya janye hannun shi daga ruƙo da ya yi mashi, ya wuce wurin su shima ya ɗaura hannun shi, murmushi batool ta saki tana kallon shi, Kallon haris naufal ya yi tare da cewa" am sorry bro but am not supporting, also am advising u, ka aje makaman yaƙin ka kazo mu rungumi junanmu," yana kai ƙarshen maganar shi yaje wurin su, sai da ya fara kallon angel ya sakar mata murmushi kafin ya sanya nashi hannun, kallon kallon aka koma yi a tsakanin Deeja da haris da kuma mr arrogant dake kwance saman gadon shi, ganin suna kallon shi yasa shi rufe eyes ɗinshi tamkar mai yin bacci, tasan indai ba sanya hannun shi yayi ba, haris bazai ta6a supporting ɗinsu ba, gyaɗa kai ta yi tare da kallon deeja tace"ke baza ki goyi bayan mu ba? Bana so ki yi abunda zaki yi danasani, duk wanda bai sanya hannun shi ba, to baya a tare mu" Kallon harris tayi ganin yana maƙe mata wuya alamar karta shiga cikin ku, ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kan fuskar batool, ganin ba ta da mafita yasa ta shiga cikin su, itama ta sanya nata hannun Murmushi batool ta saki, kafin ta ce su maimaita duk abunda tace, suka amsa mata da toh, alƙawari ne suka ɗaukarwa juna, Banda mutun biyu Haris da Danish, bayan sun kammala yi ma juna alƙawari gaba ɗaga suka shiga rungume junansu, a yau suna jin kansu tamkar ciki ɗaya suka fito, Bayan kowannan su ya samu natsuwa, Batool da angel su ka kalli juna, lokaci ɗaya suka sakar ma juna murmushi, "Idan zaki shiga toilet, muje tare nima ina so zanyi wanka,"
Gaba ta yi angel tabi bayan ta, har zuwa ƙopar shiga toilet ɗinsu hannu batool ta sanya tare da tura ƙopar suka shiga daga ciki, ƙofofi ne kusan guda uku kowanne a rufe ya ke, ɗaya daga ciki angel ta shiga, itama batool ta buɗe ɗayan toilet ɗin ta shige ciki,
Sai yau ta samu damar ƙarewa toilet ɗin kallo na ƙurulla, ko'ina a tsaftace ya ke, sai dai babu wadatattu kayan amfani, akwai dai toilet seat, sai shower ta tsaye wani ajiyayye bucket, kwandon wanka me ɗauke da soap and sponge, a kwai cabinet dake ɗauke da sabulai da hada ledar detergent da kuma Shampoo ɗaya, saman ceilling ta wurga idonta, wasu munafukan tagogi ne kusan uku, masu murfin ƙarfe an garƙame su da kwaɗo jikin su har ya yi tsatsa, mayar da idanuwanta ta yi akan tagar jigin bango guda ɗaya jikinta wani tsohon glass ne duk yayi ƙura, tunani ta shiga yi idan har zata iya samun makamin da zata iya fasa glass ɗin jikin glass ɗin da shi tabbas zata iya kutsawa ta cikin tagar ta dira ta baya, daga nan zata samu damar shiga cikin kurkukun taga me ke wakana, jinjina kai ta yi tare da cewa"I will try", sauke idanuwanta ta yi akan tukunyar fular dake ajiye daga ƙasa jikin bango tana da girma, fulawar cikinta duk ta yagalgale saboda rashin kulawa, ta6e bakinta ta yi kafin ta mayar da idonta kan igiyar da ke a ciki da a lama ta sagala kaya ce, tafiya ta soma yi tana bin kowace kusurwa ta makewayin da kallo, bakin magudajin da ruwa ke bi ta tsaya wasu ƙananun hudoji ne da basu fi shida ba, tanan ruwa yake bi ya wuce, akwai wasu fanfuna guda biyu da su ke a kashe,
Sai da ta kammala bin ko'ina da kallo tukunna ta sanya hannayenta ta kamo ƙasan rigarta, ta cireta tare da rataya ta saman igiyar,
"Ko madubi babu da mutun zai kalli fuskarsa, ta ya zan gane ina ƙara kyau ko muni nake yi"? tayi maganar acikin zuciyarta,
Bokitin nan ta janyo tare da tara shi gaban fanfon ta kunna, ruwa ya soma bulbulowa daga cikinsa, tafi sha'awar ta yi da bokin akan ta kunna shower,
Zuƙunnawa ta yi tana jiran ruwan ya cika, kamar daga sama taji an banko ƙopar toilet ɗin da ta ke ciki, A gigice ta ɗago tare da wurga idonta kan door ɗin don taga wanene ya shigo,