Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 18
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 18: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 18. *DANISH* ne a tsaye hannun shi ruƙe…
3,246 words
*DANISH* ne a tsaye hannun shi ruƙe da rigar shi, tun daga ƙasa har sama take kallon shi, kamar wani bugagge sai faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, shafaffan cikin shi tamkar wanda bai ta6a cin abinci ba, ranta a matuƙar 6ace ta miƙe saboda tsabar fusata bata ɗauki rigarta ta sanya ba, ta rufe shi da faɗa" kai wani irin jaki ne ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko? Tunda ta soma balbale shi da masifa bai yi yunƙirin tanka mata ba, kuma bai motsa ba ya dai yi kasaƙe yana kallonta, sai da takai ƙarshen maganar tana haƙi cikin sanyin murya yace"Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir......."kafin ya kai ƙarshen maganar, ta sunkucin bokitin ruwan da ta tarba, gaba ɗaya ta sheƙa mashi ruwan a jikin shi, sharkaf ta jiƙa shi, Runtse idanuwan shi ya ɗanyi saboda ruwan daya shiga ciki, long eye lashes ɗinshi sun jiƙe sharkaf, hannu ya sanya tare da share ruwan dake akan fuskarshi, kafin ya buɗe idanuwan shi, ta yi saurin ɗaukar rigarta da ke a saman igiyar ta zurata a jikinta, Tana huci ta ci gaba da kallon shi tana fadin"Zaka fita ko saina ƙara watsa maka wani ruwan? Ƙaton banza kawai matsalar ace mutun baida addini kenan, ko dabba tafi shi kan gado," A lokacin ya ƙarasa buɗe idanuwan shi, jinjina kan shi ya yi still bai tanka mata ba, ya juya ya fita daga cikin toilet ɗin, Lamarin ya ɗaure mata kai, har ta soma tunanin kodai yana da ta6in hankali ne? In ba haka ba taya zai faɗo mata bagatatan Cikin toilet batare da ya tambayi ko akwai mutun aciki ba, idan ma ya yi tunanin babu kowa ne why bazai yi knocking ba? Guntun tsoki taja, aranta tace"Amma dai wannan anyi sullu6iyo, Shashasha sauna, next time idan ya kuskura ya ƙara faɗo mun irin haka, saina koya ma shi hankali," takai ƙarshen maganar tare da nufar ƙopar toilet ɗin da nufin ta rufe, hannunta ta ɗaura saman handle ɗin ƙopar, shiru ta ɗanyi jin alamun bai tafi ba, zurfi tunani ta shiga lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin ta manta bata yi locking ɗinta ba, kodai ya yi tunanin babu mutun ne shiyasa ya faɗo ciki? Don ta lura Haka suke yi idan suka ga ƙopa ba a datse ba, shi ne babu mutun a ciki, idan kuma suka ganta a datse to shi ne ke da akwai mutun, kenan itace ta yi ba dai dai ba? Da ace ta rufe ƙopar danish bazai iya shigowa ciki ba,
Ta6e baki ta yi, ta tura ƙopar ta rufe, ta koma ciki domin yin wanka, Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin wankan, ta mayar da kayan jikinta, ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, tana buɗe ƙopar ta same shi a tsaye ya jingina bayan shi jikin bangon toilet ɗin, da alama jira yake ta fito ya shiga,
Wuce shi tayi zuwa cikin ɗakin, A tsaitsaye ta same su, banda mutun biyu Batool da Aziza, "angel" hannah ce ta kira sunanta, ƙarasawa ta yi kusa da ita ta tsaya, Fuskarta ɗauke da murmushi tace"kin fito kenan, nima wankan nake so inyi ina jira su batool su fito sai in shiga," "Idan ku kayi wanka babu wani abu da ku ke shafa ma jikin ku"? Angel ce ta yi mata tambayar, girgiza mata kai ta yi tare da cewa babu, mu ma haka muke zama duk in mu ka yi wanka, "Comb fa? Ina so in taje gashin kaina", "Guda ɗaya ne muke da shi, kuma yana a wurin danish, da shi muke amfani in kina so sai in aro maki," da sauri tace"a'a na fasa" aranta kuma tace komai danish danish sai na koya mashi hankali, sullu6uyo kawai,
Tafiya ta yi zuwa gefen gadonta, ta zauna tana bin kowannan su da kallo,
Motsi buɗe ƙopa su ka jiyo daga can kusurwar da benan ya ke,
Nan fa su Hannah suka fara murna sunsan abinci ne za'a kawo masu,
Takun tafiyarsu tamkar na dawakai, saukowa su kayi daga saman matattakalar benan, Giants ne Hannayen su ɗauke da farantai, shiga ciki su ka yi a dai dai saitin carpet ɗin nan suka ɗaura sauke tray ɗin,
Kafin su ka ja baya tare da goya hannayen su saman ƙirjin su,
Fuska a ɗaure angel ke kallonsu, ko gunki bazai nuna masu iya tsayuwa ba, abun na ci mata tuwo a kwarya, wai su waɗannan mutanan su wanene? Basa ji basa magana, kullum kuma cikin shiga iri ɗaya kuma sun 6oye ainihin suffar su, Jin jina kai ta ɗan yi aranta tace"A sannu zan gano ko su wanene ku,"
"Angel ki taso mu ci" Hibba ce ta kirata ganin ta yi zugudum saman gadon,
Saukowa ta yi tare da tunkarar inda suke zaune itama ta zauna gaban farantan, ta lanƙwashe ƙafafunta, mutun uku suka rage basu ƙaraso ba,
Javed yace"wai ina danish ya ke ne? da su batool, wani yaje ya yi masu magana su zo mu ci," yunƙurawa haris ya yi da niyar yaje ya kirasu sai gasu sun fito daga cikin ƙopar shiga toilet ɗin a tare, komawa ya yi ya zauna, gefen angel batool da aziza su ka zauna, danish kuma ya zauna gefen javed, yana fuskantar angel tun da suka haɗa ido, ta wurga mashi harara tare da murguɗa ma shi small mouth ɗinta,
Bin ta ido kawai ya yi, don baima san menene ta ke yi ba, haushin shi take ji ta ƙara jin tsanar shi saboda sharrin da yayi mata, da ya ce ƙirjinta kamar bangon ɗakin su, tsohuwa ma tafi ta abun kirki, kalaman nan sun baƙanta mata rai, kuma taci alwashin sai ya ɗanɗani kuɗar shi,
Batool ce ta ya ye jan ƙyallen da aka rufe saman trays ɗin, Hamburger suka samu tare da chicken legs na ƙosassun kaji anyi masu jar suya har wani maiƙo suke yi, kowa zai samu burger ɗaya da kuma Chicken leg ɗaya, a tray na biyu Tea pot ne sai jerin wooden Cups, faranti na ƙarshe basket ne mai ɗauke da kayan marmari, a gefe ɗaya kuma bottle waters ne' fuskar kowannan su awashe, baƙaramin daɗi suka ji ba, duk da sau ɗaya ake a basu abinci arana, Amma suna Ci su ƙoshi wani lokacin ne ba'a basu abun da zai ƙosar dasu, amma yau kam ba laifi, kowannan su Tunanin wanda zai rage yaci da anjima yake yi, Batool ce ta zuzzuba masu kakkauran tea a kowani Cup, ta miƙa masu ɗaya bayan ɗaya, kusan atare suka kai baki suna sha, Idonta idon danish Sun hana juna sakat, gani take kamar wani abun yake ayyanawa aranshi tun da ya ganta babu riga a jikinta, nan take ta murtuƙe fuska, a ƙule tace"Stop looking at me" "Ae bani ke kallon ki ba, ke kike kallona," amsar daya bata kenan, daga haka ya ɗauke idonshi daga kanta, ya kai hannu ya ɗauki burger ɗinshi yana ci, Yunƙurawa tayi tare da miƙewa, kowa yabi ta ido, batool tace"Har kin ƙoshi"? Fuskarta a hautsine tace"Zan ajiye ne da anjima inci" takai ƙarshen maganar tare da kai hannu ta ɗauki Chiken leg ɗinta, ta ɗibi fruits, ta kuma ɗaukar bottle water ɗaya,' duk fa don saboda danish tabar wurin, Saman gadonta ta koma ta zauna, kuma still bata daina kallon shi ba, lamarin ya ɗaure ma shi kai, shi dai baisan zunubin daya aikata mata ba, sam ta tsani ganin shi, abunda bata sani ba danish mugun shakkarta yake ji, shifa har yanzu kallon monster yake yi mata, bai yarda cewa itama mutun ce kamar su, saukowa ta yi daga saman gadon ta nufi gadon batool, ta zuƙunna bakin gadon ta zura hannu a ƙarƙashi ta janyo kwandon da batool ke ajiye ragowar abincin ta, a ciki itama ta ajiye Fruits ɗinta, apple uku sai ayaba guda biyu, ta raba cinyar kazar biyu ta tura rabi aciki, rabin kuma anan zuƙunne ta cinye ta, tana kammala ci ta buɗe murfin robar ruwan tasha rabi, bayan ta gama ta rufe kwandon, ta tura shi Ciki, kafin ta miƙe hannunta ruƙe da bottle water ɗinta, ta koma saman gadonta, daga ƙasa ta ajiye bottle ɗin,
a lokacin suma sun kammala cin nasu abincin, wasu sun rage cinyar kazarsu, wasu kayan marmari suka rage, kowa dai ya ɗauki robar ruwanshi don ya ajiye zuwa anjima,
Tattara kayan abincin giants su kayi, A jere suka fuce daga cikin ɗakin, prisoners kowa Ya koma saman gadon shi, Anci an ƙoshi saura bacci, aikin su kenan Abun ba ƙaramin ɗaure wa angel kai yake yi ba, wai su kwata-kwata basa gajiya da rayuwar kulle? Daga ɗaki sai toilet, daga anci abinci kuma sai hawa gado ayi bacci, anya kuwa suna da lafiyar kwakwalwa?
Ganin da gaske bacci za suyi yasa tayi saurin cewa""Wai ku baku tunanin fita daga cikin kurkukun nan? Ko baku da ra'ayin yin rayuwar ƴan ci ne, Cikin mutane?
"Ta ya zamu sanyawa ranmu fita daga cikinsa, bayan tsohuwa ta faɗa mana cewa mutanan dake awajen kurkukun nan baza su ta6a ƙaunar mu ba, wahala zamu sha tunda bamu da kowa a ƙarshe ma akashe mu da ranmu," yasmin ce ta bata amsa,
Rubina tace" bamu da kowa tsohuwa itace gatan mu, taya zamu yi tunanin barin kurkuku bayan babu ƙofar fita daga cikin shi? idan mun fita wurin wa zamu je"?
Guntun tsoki angel taja"daga anyi magana sai kuce tsohuwa, bansan me ta jiƙa ta baku kuka sha ba, wanda har ya gusar maku da tunanin ku, Amma ni inada tabbacin ba hakanan aka ƙyale ku ba, saboda babu mutumin da zai juri a kulle shi, tamkar yadda ake kulle dabba,"
Harara danish ya jefa mata, dama haushin ta yake ji, bai dai ce komai ba haris ne yace"yanzu kina so mu yadda dake mubar 6angaren tsohuwa? Wai ke da me kike taƙama ne? idan bakisan wacece tsohuwa ba, bari in ƙara tunasar dake, itace ta raine mu ta kuma gatanta mu, bamu da tamkarta a duniyar nan,'
Cike da takaici angel tace"dukkan ku baku da tunani, bakusan ciwon kan ku ba, Ni bansan taya zan fahimtar daku ba, gidan kurkukun nan ba alkhairi bane, gatan da kuke faɗin tsohuwa ta baku, ba gata bane gata shine abar mutun ya yi rayuwar ƴanci, amma ku an killace ku, an hana ku ganin hasken rana, acikin kurkukun ma an yi maku iyaka da shiga ko'ina, a rana sau ɗaya kuke samun abinci, an haɗa maza da mata ɗaki ɗaya suna kwana shin wannan gata ne? Kullin mu ne yawo cikin uniform kala ɗaya, wai ku baku gajiya da rayuwa a kulle ne? Kuyi tunani mana babu alkhairi atattare da kurkukun nan"
Murmushi Batool ta ɗan saki, kafin tace"angel, dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa indai akan tsohuwa za ki yi magana babu wanda zai ta6a fahimtar ki, its better ki yi shiru da bakin ki, yadda kika ganmu kibar mu kawai mu haka ƙaddarar tamu rayuwar take a cikin kurkuku"
Shiru angel ta ɗanyi, sai lokacin ta ƙara tabbatarwa kanta cewa An gama dasu tabbas ba hakanan tsohuwa ta ƙyale su ba, batasan wata irin huɗu ba ta yi masu ba, da har suka gaza fahimtar dai dai, taso ace sun yarda da maganarta ta hakan ne zasu haɗa hannu wurin nema ma kansu mafita, sai dai kash sunƙi bata haɗin kai,
"Ina son fita daga cikin kurkukun nan, amma bansan meyasa ba, bana jin zan iya rayuwa awajensa, a duk lokacin da nayi tunanin fita daga cikinsa sai inji ƙunci da raɗadi suna taso mun acikin zuciyata" javed ne ya yi maganar,
"Nikaina ina sha'awar wata rana in ganni awajen kurkukun nan, but i don't know why bana jin zan iya fita daga cikinsa koda na samu damar yin hakan"
Kasa kunne angel ta yi tana sauraron su kowa yana tofa albarkacin bakinsa, banda Danish, da ya lumshe idanuwan shi tamkar mai yin bacci,
"Tsohuwa ba gaskiya take faɗa maku ba, nasan zaiyi wuya ku fahimce ni, amma kuyi tunani mana, Kowani ɗan adam Da Allah ya halitta A duniyar nan, ba daga sama ya faɗo ba, shin kun ta6a tunanin Ina iyayen ku su ke? Meyasa kuka kasance marayu? Idan iyayen ku sun rasu ina danginku su ke? Idan na baku labarin rayuwata ina da tabbacin zaku fara kwaɗayin yin rayuwa a wajen kurkukun nan, kuma zakuyi tunanin Ina iyayen ku da dangin ku su ke......." muryar Deeja ce ta katse mata xancen nata da cewa,
"Kince kowani ɗan adam da Allah ya halitta? Waye ɗan adam ɗin kuma wanene Allahn da kike magana akai"
Mamaki ƙarara akan fuskar angel ta ɗago tana kallon deeja dake zaune can saman gadonta, fuskarta babu alamun wasa ta yi tambayar,
Speechless sam ta kashe mata baki, tsabar mamakin tambayar da Deeja ta yi mata, har wani shock taji, sai lokacin ma ta tuna dasu wa take magana, ta jima tana mamakin wannan ikon Allahn, Gaskiya yaran nan an cuci rayuwar su, basu san komai ba game da wanda ya halicce su, wato su kawai rayuwa suke yi kara zube,
"Kinyi shiru baki ce komai ba"? Deeja ce ta yi maganar, jin tayi shiru bata ce komai ba, buɗe baki angel ta yi da niyar ta bata amsar tambayarta, ba zato ba tsammani taji an daki kokwan kanta, wani irin duhu cikin idanuwanta, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta dake yi mata raɗaɗi muryarta na kerma ta shiga ambaton"LA'ILA HA'ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!!" gaba ɗaya suka tsareta da ido ganin ta runtse idanuwanta, Jikinta na kerma, da sauri batool da su hanna suka sauko daga saman gadajensu suke nufi gadon angel, Suna tambayarta lafiya meya faru, bata basu amsa ba, jiki ba ƙwari ta sulale saman mattress ɗinta ta kwanta, Kallon juna su ka yi cike da tsantsar mamaki, Hanna tace"Anya kuwa lafiya? Kodai bata jin daɗin jikin ta ne" miƙa hannu batool ta yi saman wuyan angel ta shafa shi, Sanyi taji sosai " kallon su tayi"lafiyarta qalou, bacci ta ke yi," Sautin dariyar Haris suka ji, a tare suka juya suna kallon shi, hannun shi rungume da pillow, "Dama karta farka, kowa ya huta" Hararar shi batool ta yi, tare da kawar dakanta, Cigaba da magana Haris ya yi"Saboda ita duk kun ta shi hankalin ku, yarinyar nan fa ba son mu take yi ba, saboda bata son tsohuwa....." kafin yakai ƙarshen maganar shi, Danish yace"haris, pls stop talking about her,' shiru haris ya yi saboda Danish ya nuna baya son yana maganarta, A gefen gadon angel su batool suka zazzauna suna jiran ta farka, hankalansu sam bai kwanta da irin baccin da angel ta yi ba, shiyasa suka gaza komawa saman beds ɗinsu, Lamarin ya ɗaure masu kai, tsawon awanni tana bacci, Tun suna sanya ran zata farka har suka fara fidda rai, "Kodai inje in faɗa ma Tsohuwa ne? Acewar Hibba, Batool tace"Mu ɗan ƙara jira mu gani, wata'ƙil kafin dare ta farka,' Azeeza duk tafi shiga yanayi saboda ita tausayi gareta ga tsoro, muryata a sanyaye tace"Ni bana so wani abu ya samu angel, saboda ina sonta,'
Haris dake sauraron su, kamar ya miƙe yaje ya rufe su da bugu haka yake ji, don shi ya tsani ya ji suna damuwa da ita,
Saukowa javed yai daga saman gadon shi, hannyen shi Cikin Aljihun wandonshi ya nufi gadon angel, inda suke a zazzaune, a tsaye ya tsaya yana kallon su"ku kwantar da hankalin ku, zata farka ne, zaman ku anan yana ƙara takura mata" "To kai meye ruwanka da ita'? Haris ne yai maganar, Kallon shi javed yai tare da cewa"Cos she's my sis, i must worry about her, " yakai ƙarshen maganar shi, tare da janye idon shi daga kan haris Ya mayar da shi kan su batool da har yanzu basu matsa daga saman gadonta ba, Dogon tsoki Haris Yaja rai aɗan 6ace yace"daga zuwanta har ta fara canza maku tunanin ku," Mubeen yace"Ka fa iya bakin ka, halan ka manta bugun da muka sha a hannunta ɗazu da safe, kodan kaga tana bacci ne"? Cike da zolaya yakai ƙarshen maganar yana dariya, Janyo pillow haris Yayi tare wurga ma mubeen saman fuskar shi, Cafke pillown mubeen ya yi a hannun shi still da dariya akan fuskar shi yace"Yarinyar fa akwai ƙarfi, Na lura gaba ɗaya tsoranta ku ke ji, duk masu nuna basu sonta sunfi kowa jin shakkarta,' wannan maganar da mubeen ya yi ce tasa Danish satar kallon shi ta wutsiyar idonshi, yadda mubeen ya yi maganar kamar ya karanci abunda ke a cikin zuciyoyonsu, shifa a halin yanzu bai ƙi angel taƙi farkawa ba, saboda ko motsi ta yi sai yaji gaban shi ya faɗi, Ya tsani mutun mai tsiwa ita kuma taci ka kwakwazo, ɗazu a cikin toilet ɗinnan da ta rufe shi da faɗa har zazza6i ya ji a jikin shi, dauriya kawai ya yi wurin mayar mata da martani, don baiso ta gane yana jin shakkarta, "Zan koya mata hankali ne, ai ba ƙyale ta nayi ba," haris ne yayi maganar fuska a ɗaure, Javed yace"Zaka koya mata hankali ko zata koya maka hankali? Nakasa fahimta,' shiru haris yae bai tanka ma shi ba, "Yarinyar nan fa duk cikin mu babu tsaranta, saboda ƙarama ce, amma sai shegen wayau ga ƙarfi, Ni har tsoro take bani in tana magana, ƙwayar idonta ma tsoro take bani, Ita sam bata jin shakkar kowa" Deeja ce ta yi maganar,
Naufal yace"Ni kuma ba ƙaramin burgeni take yi ba, yanayin rayuwarta ya banbanta da namu, tana da ƙwarin gwiwa sosai, babu tsoro acikin lamuranta,"
Naufal nakai ƙarshen maganar shi, Batool tace"Ni ina ji araina zuwanta cikin rayuwar mu, tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, idan har zamu zauna da ita cikin lalama zata koya mana abubuwa da dama waɗanda bamu sani ba, saboda ita ta yi rayuwa A wajen kurkukun nan, muna buƙatar neman ƙarin haske dangane da rayuwar mutanan dake a wajensa" Jinjina kai eve ta yi tare da cewa"Kalamanta na ɗazu sun tsaya mun araina, har na fara tunanin Ina iyayen mu su ke waɗanda suka haife mu? Ina dangin mu? Nafara doubting akan wani abu, Amma kafin nan, inaso angel ta farka ta bamu labarin rayuwarta, Inaso inji, kuma inaso ta faɗa mana wanene Ya halicci kowa, kuma wanene ɗan adam da ta take magana akai,"
Maganganun da su ke yi ba ƙaramin ƙona ma haris rai su ke yi ba, ganin Yarinyar ta fara cin galaba akansu, taya wata can baƙuwa zata shigo cikinsu, ta soma kokarin canza masu tunanin su' A harzuƙe ya daka masu tsawa, har saida Danish ya firgita, don baisan Tsawa ko kaɗan, Jikin shi har kerma yake yi, idon shi akan Haris dake ta faman huci, Nuna su ya yi da yatsan hannun shi "kada wanda ya kuskura ya ƙara magana makamanciyar wannan acikin ku, ban ta6a sanin baku da hankali ba, sai yau, taya zaku fara ɗaukar maganganun ƙaryar da take faɗa maku? Yarinyar na fa bata da cikakken hankali, batasan me take yi ba......" muryar shi a disashe yakai ƙarshen maganar idon shi akan danish daya daddafe kanshi da hannayenshi biyu, jikinshi nata kerma
Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan Danish, Sun san lalurar shi ta rashin son hayaniya, idan abun ya motsa kusan burkice masu yake yi,