Kenza eBookz

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 35

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 35

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 35: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 35. Duk sun damu da rashin ƴan uwansu,…

3,277 words

Duk sun damu da rashin ƴan uwansu, hakan yasa suka kasa samun natsuwa especially angel, Zarya ta soma Yi acikin aɗakin, idan takai ƙarshen bango saita dawo ta sake zagayowa, Har saida ƙafafuwanta suka soma Yi mata raɗadi tukunna ta dakata da yin zirga zirgar, Ta nufi gadonta da niyar ta huta, gefen gadon ta zauna Zugudum, Zuciyarta acike fal da tunanin duniya, wuraren marece su ka Jiyo alamun motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Bayin Allah da gudu suka duro daga saman gadajensu, Jikinsu na 6ari suka ƙarasa ƙopar ɗakin nata suna jira ta fito,

Sandar hannunta ce ta fara leƙowa, Kafin ta zuro kai ta fito waje, Jikinta sanye da jan doguwar rigar nan ta gado,

Kusan atare suka haɗa baki Wurin gaishe da ita, Ta amsa masu fuskarta asake, Sai faman mamular baki take Yi kamar me cin goro, fuskarnan a jagwale saboda tsabar tsufa ta koma kamar aljana, hurhura ta ko'ina,

"Tsohuwa Ya jikinsu Deeja? Tun jiya muke ta tsammanin jiran dawowarsu amma shiru ba'a dawo mana dasu ba, Munyi kewarsu sosai, Bacci ma daƙyar muka Yi shi, Ko abinci bama Jin daɗin Cin shi saboda rashin ƴan uwanmu" yasmin ce tayi maganar cikin nuna damuwarta,

Mubeen Yace"tun daga Lokacin da aka ɗaukesu har zuwa Yau, kullum Cikin zullumi muke," Angel dai ta tsareta da ido kamar yarda itama tsohuwar idonta ke akan angel, Kowa da abunda yake saƙawa aranshi,

"Kinyi shiru baki bamu amsa ba? Yaushe za'a dawo mana da ƴan uwanmu? Idan mensturation ne Yanzu ya isa ace jikinsu Yayi sauƙi," Fuska aɗaure angel ta yi mata maganar,

Jinjina kai tsohuwa Tayi, Sai da ta mula tasha Iska Tukunna tace"Ƴan uwanku suna acikin koshin Lafiya, Bazan Iya sanar daku lokacin da za'a dawo dasu ba, Saboda bani da masaniya, amma nasan bazasu wuce Cikin week ɗin nan ba," A ƙagare Azeeza tace"Dagaske Su parveen Sun Ji sauƙi? Kuma Suna tambayar mu? Suma sunyi kewarmu"? Murmushi tsohuwa ta sakar mata tare da cewa"Eh mana, sun damu daku sosai, Kuma suna tambayarku, da zarar Sun ƙarasa Jin sauƙi za'a dawo maku da su" wani irin murmushin farin Ciki ne Ya bayyana akan fuskokinsu, In ka cire mutun Huɗu Batool Angel da javed sam babu walwala akan fuskokinsu, Baka iya tantance awani yanayi suke ciki, da alama suna kokwanton kalaman Tsohuwa, sun dai yi shiru ne kawai,

"Just for today, Ki kaimu inda suke domin muyi musu Ya jiki, Tunda Kince Suma sun Yi kewar mu, hakan zai rage musu damuwa" angel ce tayi maganar

Girgiza kai tsohuwa Tayi tare da cewa"Ba'a bada iznin ɗaya daga Cikin ku, Yaje inda suke ba, Idan Ku ka yi hakuri zasu dawo ne" batare da angel ta yi mata musu ba tace"Shikenan zamu zuba ido mu gani idan za'a dawo mana dasu"

Kallon su Batool angel tayi tare da cewa"Ku koma kuje ku zauna, inaso zanyi magana da tsohuwa" Jin wannan maganar yasa tsohuwa tayi saurin kallon angel fuskarta da alamun mamaki,

Juyawa su batool suka Yi atare suka tafi izuwa saman gadajensu, duk wannan abun dake faruwa danish Yana a kwance saman shimfiɗarshi, ko sarki bazai nuna mashi Jin daɗin gado ba, Ya cancanci da akirashi da MAJI DAƊIN GADO,

"Ƴar nan ina sauraron ki, wata Irin magana ce ki ke son Yi dani kuma? Yau ke da kanki"? tsohuwace tayi maganar, fuskarta akwa6e,

cikin sanyin murya angel tace"Inaso mu shiga daga Cikin ɗakin ki, Muyi magana" zaro ido waje tsohuwa tayi jin abunda angel tace, Can kuma saita yamutsa fuska tace"Ba dole sai mun shiga daga Ciki ba, Kome Ki ke son tattaunawa dani, Kiyi mini magana anan ya wadatar"

"Meyasa baki son in shiga ɗakin ki"? Ko akwai wani abu da bakya son in gani ne? Da tuhuma angel tayi mata maganar, girgiza kai tsohuwa ta yi tare da cewa"Babu abunda nake 6oyewa kawai dai bana bada iznin A shiga ɗakina, idan magana zakiyi dani to mu yi ta anan, babu wanda zai ji mu,"

Ta6e baki angel ta ɗanyi still idanuwanta akan tsohuwa tace"yau tsawon shekarata Biyu agidan kurkukun ƙaddara, Ban ta6a ganin wani ya shiga Cikin ɗakin ki ba, Bansan me kike 6oye mana ba, Amatsayinki na uwa agare su, meyasa baki bari muna leƙawa cikin ɗakin ki? Kuma bakya zama acikin mu domin Yin fira, Ko hakan ya sa6awa dokar prison ne"?

Bazawarin murmushi tsohuwa tasaki kafin ta Juya Tana dogara sanda tace da angel"Ki shigo daga Ciki," tsananin mamaki ne Ya kama angel, Jin ta amince mata akan ta shiga Cikin ɗakin nata,

Sai da angel ta fara juyawa ta kalli su batool, ganin hankalinsu gaba ɗaya baya akansu Yasa ta bi bayan tsohuwa, Kafin ta shiga ɗakin tsohuwa Sai da takaranta addu'o'in neman tsari, sannan ta zura ƙafarta Cikin ɗakin, bakinta ɗauke da sallama,

A tsakiyar ɗakin Angel Ta tsaya tana bin Ɗakin tsohuwa da kallo, Abun mamaki abun al'ajabi, Bakomai bane aciki face Shufke sufken fulawowi,Ta ko'ina tamkar ɗan garde, Sai wasu tsoffin Kujeru guda Biyu suna fuskantar Juna, tsakiyarsu table ne mai ɗauke da Tea pot, da ƙananun Kofina guda Biyu, bayansu babu wani abu na furniture, Gado ko katifa,

Bayan ta kammala Kallon Cikin ɗakin na tsohuwa, Ta wurga idanuwanta kan tsohuwa dake yunƙurin zama saman ɗaya daga Cikin kujerun guda biyu dake fuskantar juna,

Muryarta angel ce ta katse mata hanzarinta da cewa"ina kayan ɗakin suke? Naga babu gado ko katifa? A ina kike kwana"?

Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa tasaki, Mai matuƙar sautin gaske, Angel tuni tasha jinin jikinta, Muryar tsohuwa ashaƙe tace"Ƴar nan Badai Iya tambaya ba, Dama ganin kwakwaf kika zo Yi mini acikin ɗakin nawa? Keda kika ce Magana zamuyi ae kamata Yayi ki zo ki zauna ga kujera har ma da shayinmu na tsoffi in zuba maki musha don muji daɗin tattaunawa" Takai ƙarshen maganar tana nunawa angel kujerar da hannunta,

Jikinta tamkar na wadda aka zarewa Laka haka Taci gaba da tafiya Ta nufi kujerun Ta shiga Ciki ta zauna, tana Bin tsohuwa da kallon Ban yarda dake ba,

Ƙarasa xama saman kujerar tsohuwa Tayi, a yayin da suke fuskantar Juna ita da angel, Ido cikin ido suke Kallon juna,

"Ina sauraronki wata magana ce kikeson tattaunawa dani"? Ta yi tambayar a ƙagare da son ji,

Angel da ƙarfin hali tace"Tambayoyi ne nake son Yi maki, Ina fata zaki amsa mani" Wani irin kallo tsohuwa ta jefa mata, da mitsi mitsin idanuwanta,

Cigaba da magana angel tayi"Badan Hali na ba, Alfarmace nake nema awurinki, duk da nasan zaiyi wuya ki amsa mini tambayoyina, bansani ba ko yin hakan ya sa6awa dokar Prison"

Gajeren murmushi tsohuwa ta saki, kafin tace"A dokar gidan kurkukun ƙaddara, Ba'a ba mu damar Yin magana da prisoner ba dangane da abunda ya shafi Kurkukun, Yin hakan babban laifina wanda hukuncinsa mutuwa ne.........." aruɗe angel ta ɗan zaro ido tana kallonta, Tsohuwa tace"Kinga kuwa babu ta yadda za'ai In iya amsa maki tambayoyinki kodan saboda in tsira da raina"

Angel tace"Amma ae babu mai ganin mu, Daga Ni sai ke ne acikin ɗakin nan, Babu wanda zai san anyi" Cikin sigar wayau angel ta yi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba tsohuwa ba, ganin ƙaramar yarinya na neman raina mata hankali, su da suka ga jiya suka yau

"Mu sha Tea mana, " tayi maganar tare da kai hannu ta ɗauki tea pot, tana tsirara musu ruwan tea Acikin Cups,

"Ko kin zuba bazan Sha ba," acewar angel, kallonta tsohuwa tayi"saboda me"? "Ban yarda da duk wani abu da zai fito daga gare ki ba," "Amma meyasa ƴar nan"?

"Saboda Ina kokwanto Akan shayin da da zaki bani, Shekaran Jiya da kika ba su batool apples Sunyi bacci Na tsawon yini guda batare da sun farka ba, Har safiya tayi, ina da tabbacin cewa silar apples ɗin da kika basu ne, Shiyasa nake tsoron in sha tea ɗin nan, wata'ƙil kinsa Poison aciki,"

Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Da ace naso kashe ki da tuni na aiwatar da hakan, kada ki manta kina acikin ɗakina ke kaɗai, Koda sandar hannu zan Iya cutar dake, ƴan uwanki kuma dana bawa Apples Taimakonsu Nayi saboda bani da ikon da zansa Giants su dawo masu da abinci, Shiyasa na baku Apples ɗinmu na gidan kurkukun ƙaddara, Domin kuyi bacci Har gobe Ta yi saurin zagayowa ko kun samu Ku ci abinci" dariya angel ta ɗanyi Tare da cewa"Hakan Yayi kyau, yanzu dai tun da bakyaso In tambayeki agame da kurkukun ƙaddara, Inaso Nayi maki tambaya biyu bata Cikin kurkukun bace...."tsohuwa tace "ina sauraronki"

"Gidan Kurkukun ƙaddara A Cikin Nigeria Yake? Sa'an nan kince Mutum baya ta6a kasance Acikin kurkukun nan dole sai in na Jininsa ne Ya sadaukar da shi, Abunda da nake so In sani, Na jinin naka daya sadaukar dakai Kamar wa kenan"?

"Kin manta abunda na faɗa maki kenan? kiyi mini ko wace irin tambaya amma kada Ki tambayeni game da gidan kurkukun nan....." tunkan takai karshen maganar angel ta katse ta da cewa"Amma ae ba'a Cikin kurkukun Nayi maki tambayar ba, Kawai ni inaso insan a wace nahiya Yake, Sannan Na jininka da zai Iya sadaukar dakai Kamar wa kenan"?

Tsohuwa bata amsa mata tambayarta ba, sai da ta fara miƙa hannu ta ɗauki kofin da ta zuba shayi acikin shi, takai bakinta tana kur6arshi kusan sau uku, Angel dai ta zuba mata ido, bayan ta Ajiye kofin saman table ɗin, Tana faman mulmula baki tace"Shayin da daɗi, Ki jaraba sha mana" girgiza kai angel tayi"Na ƙoshi, ni dai kawai ki amsa mini tambayata" dariya tsohuwa tayi"Ban ta6a ganin yarinya mai wayau da kaifin basira ba irin naki, Gaskiya Iyayenki Sun Iya haihuwa gaki Kyakkyawa Kamar ke kika ƙera Kyanki,.." ɗaure fuska angel tayi ganin tsohuwa Na ƙoƙarin Kaucewa Tambayarta, ta hanyar canza wani zancen,

Rai a6ace tace"ba wannan na tambayeki ba, Ki bani amsar tambayarta,"

Jinjina kai tsohuwa Ta yi idonta acikin na angel tace"idan na baki amsar tambayarki, Ni kuma me xaki bani? Kinsan ance gwammanti bata aikin banza" kallon rainin wayau angel tayi mata"Amma ae kinsan bani da abunda zan Iya biyanki da shi ko?, Ni dai kawai ki amsa mini tambayata"

Tea pot tsohuwa Ta ɗauka ta ƙara tsirara ruwan tea ɗin acikin cup ɗin gabanta, kafin ta ajiye pot ɗin ta ɗauki kofin takai baki tana sha" Sai da ta kur6e shi duka ta sauke kofin saman table, Tukunna tace"Tambaya ta farko, Gidan kurkukun ƙaddara Ni kaina bansan awace Nahiya yake ba, Abunda na sani shi ne ba'a Cikin kowace ƙasa Yake ba, mashin ko mota bazasu Iya kawo ki cikin kurkukun nan ba"

aruɗe angel ke kallonta, sai da takai karshen maganarta angel tace"Amma Ni lokacin da za'a kawo ni acikin mota aka ɗauko Ni, idan har zan Iya tunawa" dariya tsohuwa Ta saki,

"iya saninki kenan, A mota aka Cafko ki, Amma Bayan nan bazaki Iya tuna Ta Cikin ina aka ƙaraso dake nan ba," shiru angel ta yi Zuciyarta cike da was wasin maganar tsohuwa, Gani take kamar ƙarya take Yi mata,

Muryar tsohuwa ce ta katse mata Zancen nata da cewa"Tambaya ta biyu, Na jinin ka da zai Iya sadaukar dakai, Mafi rinjayen sadaukarwa Iyayene waɗanda suka Yi silar zuwan ka duniya sune suke sacrificing ɗin ɗansu, Uwa Ko Uba, Bayansu Kuma sai Cikin Blood relatives ɗinka, Domin kuwa Bare bazai ta6a Iya sadaukar dakai ba"

A matuƙar kiɗime angel ke kallon tsohuwa, Muryarta har rawa take yi wurin furta"Iyayen mutun? uwa ko Uba? Anya kuwa zan Iya yarda da maganarki? Duk irin ƙaunar dake a tsakanin Iyaye da ɗansu Zasu Iya sadaukar dashi zuwa ga wannan ƙuntatacciyar rayuwar? To Meyasa zasu Yi hakan?

Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Kina mamaki ne?, dama nasan zaiyi wuya ki yarda da magana ta, Yanzu dai Ina sauraronki, Idan akwai tambayar da kike da ita, Ki faɗa mini kafin in tafi"

Angel dai ta jinjina maganar tsohuwa abun Ya tsaya mata arai, ya cunkushe kwakwalwarta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Tambaya Ta ƙarshe da nake so Inyi maki, Mu prisoners dake rayuwa a gidan Kurkukun ƙaddara, Jinsi ɗaya ne? Dukanmu ƴan nigeria ne? Naga da yawan mu kamar fararen fata ne,

Tsohuwa tace"meyasa Ki kece haka"?

Angel tace"saboda Sam babu kamanceceniyar Jinsin baƙar fata atare da mafi rinjayenmu, Misali Kamar danish da Parveen da Javed Sun fi kama da ƴan ƴankin Asia, Azeeza Kuma kamanninta sak da European, Ita kuma batool tafi kama da Jinsin Larabawa, idan muka koma 6angaren Hanna da Hibba, sun fi kama da buzaye Ƴan ƙasar niger....." ɗaya bayan ɗaya saida angel ta korawa tsohuwa Bayani adangane da Jinsin da kowannan su take hasashen yana kama da shi, takai ƙarshen maganar, a ƙagare da son jin amsar da tsohuwa zata bata,

"Lokacin da kina atare da Iyayenki, Mutane da wani jinsi suke kwatantaki"? Tsohuwace ta jefa mata tambayar yayin da take sakin murmushi,

Yatsina fuska angel ta yi tare da cewa"Sun fi tsammanin Ni balarabiyace wasu kuma baturiya, amma asalin mahaifiyata half cast ce, auntyna ce ta faɗa mini cewa kakata mace balarabiyar ƙasar egypt ce"

Tsohuwa tace"Kinyi kyan kai, Wannan tambayar da kikayi mini, Kina da amsarta ahannunki, ina fata zaki tashi ki tafi Cikin ƴan uwanki tunda na amsa miki tambayoyinki," maƙe kafaɗa Angel tayi alamar bazata tafi ba

"Korata kike Yi daga ɗakin ki? Tsohuwa tace"a'a kawai dai Akwai inda nake son xuwa ne" Mamaki akan fuskar angel tace"ta ina xaki bi ki fita daga Cikin ɗakin nan naki bayan naga babu ƙopa, Koda yake ba abun mamaki bane, ae naga kafin ma in shigo Ciki, Kincanzawa ɗakin suffarshi duk don kada In yi maki leƙen asiri" tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya, Itama angel ɗin dariyar tayi, sai da suka kammala shan dariyarsu kamar wasu ta6a66u, bayan sun tsagaita da yin dariyar angel tace

"Na jima inaso in tambayeki, Ya akai kika san Tarihin rayuwata? Kinsan komai dangane dani, Bayan haka kuma inaso insan asalin sunanki, Daga kin amsa mini waɗan nan tambayoyin xan Tashi intafi Cikin ƴan uwana"

Tsohuwa bata amsa tambayar ba, har sai da ta ɗauki tea pot ta ƙara zuba ruwan shayi a kofi ta kur6a sau biyu, Sannan ta ajiye kofin ta soma magana atsanake,

"Amsar tambaya ta farko, Duk yaron da aka sadaukar agidan kurkukun ƙaddara, Muna bibiyar rayuwarshi ne tun Yana acikin Cikin mahaifiyarshi, Har zuwa lokacin da zata haife shi, zamuyita bibiyar rayuwarshi da zarar yakai shekarun da muƙe buƙatarsa To babu makawa xamu ɗauke shi ne...."

"hakan na nufin tun ina jaririya kuna atare dani? Kenan kune kuke sanyani duk wani mugunta da nake Yiwa daddyna"? Da ruɗu akan fuskarta tayi tambayar, tsohuwa tace"A'a, bamu bane, baƙin aljanine dake atare da mahaifiyarki, Yana matuƙar sonta, Kuma yana da zafin kishi, shine maƙasudin rashin jituwar Iyayenki, Ya tsani Mahaifinki tajudden yaso ya tarwatsa shi, Amma hakan ya faskara saboda Daddnyki mutunne maison yin ibada, bai wasa da azkhar, kuma yana yawan yin sadaka, sannan babbar kariyar dake atare dashi, Yana Yin nafilfilin tsakar dare, A lokacin da benazir ta haifeki, Baƙin Aljani Ya fita daga jikinta ya koma a jikin ki, domin ɗaukar fansa akan mahaifinki, yayi amfani dake wurin ƙuntata mishi, Amma A yanzu Baƙin Aljanin baya atare dake,

Angel fa ta shiga ruɗu, duk da tana kokwanton maganar tsohuwa, Bakasafai Take yarda da zantuttukan ta ba saboda sanin Cewa Ita ɗin Babbar maƙaryaciya ce,

"Kin tambayi sunana, Zaki iya kirana Da TAMIRA Shine Asalin sunana," Tsohuwa Na kai ƙarshen maganarta, Ta yunƙura ta miƙe daga saman Kujerarar, Da sandar hannunta ta nuna ma angel hanyar fita daga ɗakin, batare da musu ba, Angel ta miƙe ta nufi hanyar fita daga Cikin ɗakin Har takai bakin ƙopat fita, Muryar tsohuwa ta dakatar da ita,

"Shawarar Da nake so Na baki, Kada ki kuskura kice zaki Sanya naci akan sai kin gano ainihin ma'anar Kurkukun ƙaddara, domin kuwa daga ranar da kikasan ma'anarshi, Bazaki sake runtsawa ba, Kuma ba zaki sake Jin daɗin abinci ba, duk wani kingin jin daɗi da ya yi saura acikin rayuwarki, Zaki rasa shi ne! Wani irin mummunan faɗuwar gaba angel taji, Har saida ta dafe kinjinta saboda bugun da zuciyarta tayi mai sautin gaske,

Tsohuwa taci gaba da cewa"Ƴan uwanki suna farin Cikin kasancewarki acikinsu, Saboda Kin kawo musu canji acikin rayuwarsu, Ina fata zaki mayar da hankali wurin faranta musu rai, Amma fa kinsan da sanin duk ranar da kika Binciko ma'anar The destined prison, daga ranar daga ke har su, Zaku fuskanci matsanancin tashin hankali, Kuma daga wannan Lokacin bazaku ƙara Yin tozali da TSOHUWA TAMIRA ba, Zaku yi ta yin gwagwarmayar rayuwa ne atsakaninku, na gargaɗe ki ne saboda Ina sane da duk wani ƙudurinki nasan bin kwakkwafin Gidan kurkukun ƙaddara, Shiyasa na sanar dake irin matsalar da zaki jefa kanki da kuma ƴan uwanki" angel na ƙoƙarin Waiwayowa baya ta kalli tsohuwa taji an ingizata waje, Ƙopar ɗakin ta rufe,

Kamar an jehota ta faɗo ƙasa, Cikin ɗakinsu, har kanta saida Ya bugu,

Tun daga wannan Ranar Angel tashiga ruɗani, Kalaman tsohuwa sunyi matuƙar ɗaure mata kai, Tarasa Ina zata tsoma ranta taji daɗi, Kowa Saida Ya lura da canzawar da tayi, Sam tadaina shiga cikinsu, Gani take kamar Dukansu mutuwa zasuyi shiyasa take janye jikinta gudun kada sabon Yayi yawa ta yadda zata rasa kanta idan ta rasa wani acikinsu, Su batool duk sunyi tsammanin rashinsu Parveen Ne yasa ta canza ta shiga damuwa, Kullum cikin Lallashinta suke yi, Akan tayi haƙuri su koma kamar yadda suka ada, Daƙyar suka samu angel ta koma Yi musu wasa da dariya, Harma tana koya musu wasu wasanni donsu farantawa junansu,

Akwana a tashi Yau tsawon Sati Biyu kenan, Ba'a dawo musu da ƴan uwansu ba Har sun fidda rai da sake ganinsu, tun suna tambayar tsohuwa har sun gaji sun daina, kowa ya zubawa sarautar Allah Ido👀

Yau Tun da Suka tashi daga bacci suke ta jiran a kawo musu abincinsu suci amma shiru giants basu zo ba, Tun safe Har marece, Jikinsu duk Ya yi laushi, azeeza tuni ta fara Yi musu kukan yunwa, Lokacin da dare Ya ratsa hasken ɗakin Yayi duhu, Nan fa suka ƙara shiga tashin hankali ganin zasu kwana basu Ci abinci ba, la66ansu duk sun bushe, Ruwa kaɗai suke tasha tun safe, Cikinsu harya ɗaure, wasu daga Cikinsu hada amanshi su ka yi,

a ƙarshe suka haƙura Da abincin, Kowa Ya hau saman gadonshi ya kwanta, Cikin sa'a bacci ya ɗauke su, Ganin sun nutsa acikin baccin su yasa angel ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6e fuskarta da shi, Saukowa ta yi daga saman gadonta, Sumar kanta duk ta cukurkuɗe kamar ƴar mahaukaciya saboda rashin gyara, Cikin duhu take tafiya tana laluban hanya, Fitila taje ta ɗauko ta kunnata, Tana haske Saitin gadajensu Hannah, ganin babu mai motsi acikinsu Yasa tayi sauri Cikin sanɗa ta nufi sashen toilet ɗinsu, har yanzu bata haƙura da Ƙudirinta ba, Nason fasa gilashin nan, Alwashi ne ta ɗaukarwa kanta Koda zata rasa ranta saita Ga uban me ake aikatawa acikin gidan kurkukun, Duk da tana Jin fargaba akan irin gargaɗin da tsohuwa tayi mata, don a lokacin harta fara tunanin ajiye makaman yaƙinta, amma daga baya sai ta dinga jin tamkar ana tunzurata akan taje taci gaba da jaraba fasa gilashin zata Ci nasara, Zuciya da saƙe saƙe, gani take kamar idan ta fasa gilashin ta dira ta cikin tagar, zata samu damar zuwa wurinsu deeja ne, Harma ta dawo dasu Cikin ɗakin, Da yake sune damuwarta,

Tana shiga Cikin toilet ɗin, Taja ƙopa ta garƙameta da jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, ta ɗaga hannayenta Sama tana roƙon Allah Ya bata Ikon Fasa Glass ɗin a karo na karshe don daga yau ta sanyawa ranta cewa idan har bata fasa shi ba, ta gama zuwa tana shan wahala, zata haƙura ne,

Readers Also Read