Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 36
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 36: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 36. Bayan ta kammala yin addu'ar, Da…
3,355 words
Bayan ta kammala yin addu'ar, Da ƙwarin gwiwarta ta kai hannu ta rarumi bokitin ƙarfen, Sai da taja da baya ta watsa dagudu ta buga tsalle ta daki glass ɗin Da iya ƙarfinta na karshe, Amma wani abun takaici ko tsagewa Baiyi ba, kamar dai kullum haka taci gaba da bugun glass ɗin da bokitin amma Yaƙi nuna alamar ana bugunsa, saboda tsabar zufar dake tsastsafo mata ajikinta Tamkar wadda aka tsamo daga Cikin teku, Idanuwanta sun rune saboda wahala, Hannunta sai zogi yake yi mata, ga wani irin fitsari daya Matseta, da sauri ta jefar da bokitin gefe ɗaya ya gangara ƙasa, Tasanya hannu ta kwale wandon jikinta, Zuƙunnawa tayi a bakin magudaji tana fitsari, sai da ta kammala taje gaban fanfo tayi tsaki, tana kokarin miƙewa kwatam ta hango mutumin jingine da bango, Ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, Tun kafin ma ta ƙarasa juyawa ta gane kowanene, Sakamakon doguwar sumar kanshi data hango,
Muryarshi ce ta ratsa kunnuwanta,
"Can I give u a hand"? ras taji gabanta ya faɗi, azuciyarta tace"Danishi! Nashiga uku, kada ace ya ga abunda nake ƙoƙarin Yi, wayyo Allah na" rai a6ace ta ƙarasa juyowa tana fuskantar 6angaren da yake atsaye ya jingina bayan shi jikin bango, Rai a6ace ta nuna shi da yatsa"Wannan wani irin shashanci ne danish? Why zaka dinga faɗo mini Cikin toilet? yanzu da ace na tu6e kaya ina wanka ko ina wani uzirin Shikenan ka gane mini tsiraci na, Wlh bazan ƙyale ka ba" A fusace ta nufi bokitin data jefar ƙasa tasa hannu ta ɗaukeshi Ta daddage ta wurga mashi bokitin, Da sauri danish ya sanya hannayen shi biyu ya cafke bokitin a hannunshi, ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu akan fuskantar,
"Raunata ni kike so Ki yi? A ƙule tace"kashe ka zanyi " Cikin sanyin murya yace"Am really sorry, na kar6i laifina, kada ranki ya 6aci, daga yau bazan sake ba faɗo maki cikin toilet ba," yakai ƙarshen maganar a yayin da ya ajiye bokitin ƙasa, ya ɗago idonshi Yana kallon Tagar da angel ke ƙoƙarin fasawa,
Zaro idanuwanta ta yi ganin yana kallon glass window ɗin da alama yaga abunda take Yi, muryarta na kerma tace"Nasan kaga abunda nake kokarin yi, So nake in fasa gilashin tagar nan, Saboda Ina da matsalar kwakwalwa, Tun lokacin da ina agidan daddyna kafin zuwana kurkukun nan, Na fasa gilassai bila adadin saboda Ni idan nayi tozali da gilas tsoro Yake bani, kuma hakan yana jaza mini matsala, Likita ma yace Idan ina yawan zama inda ke akwai glass zan Iya mutuwa" angel sarkin wayau, idanuwanta cike tab da kwalla takai karshen maganar, hada marairaice mishi fuska don Yaji tausayinta, ya kuma yarda da maganarta,
Danish bai kawo komai aranshi ba, har cikin zuciyarshi ya yarda da kalamanta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta, Idanuwan su acikin na juna, Cikin sigar lallashi yace"Am sorry angel, don't cry pls, da kin faɗa mini tuntuni da na jima da sauke miki gilashin," ta6e baki tayi tare da cewa"Ae bazaka Iya ba, ko Ni nasha gwada cirewa amma na kasa, kullum saina sha wahalar," ta fadi hakanne don tasan Cewa danish bazai Iya ba, ita kanta da take da ƙarfi ta jaraba ta kasa balle shi da yake sai a hankali ba ƙoshin lafiya ba,
"xan jaraba in gani idan zan iya," yakai karshen maganar yana tattara hannun rigarshi, da sauri angel ta ɗauko mashi bokitin ta miƙa mashi, bakinta ƙumshe da dariya So take yasha wahala kamar yarda ta sha, Shima Yaji ajikinshi,
Girgiza mata kai yayi"bana buƙatar yin amfani da bucket, I will use my hands" dariyar rainin wayau angel tayi mashi"wlh bazaka Iya ba, Da hannu fa ka ce, haba dai, kai dai ka kar6i Bokitin inga iya ƙarfin ka," Bai saurareta ba, Ya tunkari Glass window din, Da yake Allah yayi shi da tsawo, Yafi angel tsayi ba sai yasha Wahalar yin tsalle ba kamar yarda take yi, Agaban tagar ya tsaya yana kallonta,
Angel ta ruƙe qugu, Tana jiran ganin Ikon Allah, Fuskarta ɗauke da dariyar mugunta,
hannayen shi biyu ya sanya yana shafa Jikin glass ɗin da ya yi uwar ƙura, ƙasan glass ɗin Ya ruƙo da yatsunshi, Ƙura ido angel tayi ganin glass ɗin kamar ya fara motsi, Gabanta ne ya faɗi ganin Danish ya daddage Ya 6a66ako glass ɗin tun daga tushen shi can cikin ginin dutsen da aka zura shi, Haka ya zaƙulo shi gaba ɗaya ya curo faskeken glass ɗin, Tashin hankalin da ba'a sama shi date,
Kanta Ya gama ɗaurewa, Ta zazzaro idanuwanta waje, kwayar idon kamar zata faɗo ƙasa saboda tsabar mamaki, Gaba daya tabi ta ruɗe ta rikice, Tarasa bakin magana sai bin shi da ido take yi kamar wadda aka dasa ma Aya,
A ƙasa Ya jingine glass ɗin Jikin bango, Ya ɗago yana kakka6e tafin Hannayenshi da ƙura ta buɗe su, A wani slow Ya juya bayan shi Yana kallon angel dake atsaye Ko motsi bata Yi, Ta ƙame kamar abun bautar ƙasar india wato kirishna,
Cikin sanyin mirya ya ambaci sunanta"Angel"? Shiru bata amsa mashi ba, domin kuwa sam bata acikin hayyacinta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya dafa kafaɗunta,
"Meke faru ne? Maimakon inga farin Ciki akan fuskarki, Ko baki ji daɗi bane? Na sauke maki glass ɗin, daga yanzu kin daina shan wahalar bugun shi da bokiti" shi kaɗai yake ta maganarshi, kwata kwata bata a hayyacinta, hura mata iska Yayi asaman fuskarta da bakinshi, Amma ƴar tahalikar nan ko ƙyata idonta bata yi ba, Janyota yayi zuwa jikinshi Ya kwantar da kanta saman chest ɗinshi, Ya sanya hannunshi abayanta yana shafa sumar kanta, kafin ya matso da lips ɗinshi saitin kunnanta yayi mata raɗa"angel, faɗa mini meya faru? Ko kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet ɗin gaba ɗaya, yadda bazaki sake ganin shi ba? Jin taƙi yi mishi magana, ya raba jikin shi daga nata, Ya nufi gaban fanfo Ya kunna ruwa ya ɗebo a tafin hannunshi, Ya dawo inda take atsaye kamar gunki, Ya watsa mata ruwan saman fuskarta, Nan take Taja dogon numfashi, har wani zabura tayi ganin shi agabanta, a ruɗe ta wurga idanuwanta kan tagar, Tayi tsammanin ko mafarki take Yi, amma sai taga akasin Hakan dagaske dai Danish Ya cire Glass ɗin tagar da take ta shan wahalar son fasa shi, Tsawon kwanaki, Lamarin Yayi matuƙar ɗaure mata kai, yadda har ya iya 6a66ako shi tun daga tushen shi ya zaro shi, Wanda Tayi imanin Babu wani mahaluƙin da zai Iyayin wannan aikin hakanan siddan ragadan batare da Akwai wani shiri atare da shi ba, Tsohon ginine fa kuma na dutse, A yanayin fuskarta baka iya gane halin da take Ciki, Ta yi farin Ciki da cire glass din da Danish Yayi ko kuwa batayi ba? Tabbas tayi fari ciki mara misaltuwa sai dai mamaki Ya hana ta nuna wannan farin Ciki, Ayanzu ta ƙara zargin cewa danish Ba shi kaɗai bane, Kuma ba wani ke sarrafa shi ba, tunda da ace wani ke sarrafa shi da baza a bari Ya cire glass ɗin nan ba, ganin irin kallon da take Yi mashi ne yasa shi ruƙo hannunta acikin nashi yace"Angel baki bani amsa ba, kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet din"? kamar wata sakarya haka take binshi da ido, sai da ya sake maimaita maganar tukunna ta iya bashi amsa da cewa"Inaso ka maida shi yadda ka ciro shi, Kaga duk lokacin dana shigo cikin toilet ɗin sai in zaro shi in kawar dashi wani wurin yadda bazai iya yin affecting ɗina ba" amsa mata yayi da toh, Ya juyawa ya nufi inda ya ajiye glass ɗin Ya ruƙo shi ya shiga kiciniyar mayar dashi, Bayan Ya kammala Ya juyo yana kallonta a lokacin Ta juya baya tare da ranƙwafawa Ta ruƙo hannun fitilar da tazo da ita, ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi, Daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tasakar mishi, muryarta na rawa tace
"Nagode sosai danish, you're so kind, ka damu dani kuma kana bani kulawa, miƙa mashi hannunta tayi"Zo mu koma ɗaki mu kwanta, Dare yayi sosai," ƙarasawa danish yayi inda take atsaye ya zura hannunshi acikin nata, ta ruƙe sosai tana faɗin"pls keep it under wraps, saboda bana so kowa Yasan cewa Mun cire glass ɗin nan kaga tsohuwa za ta yi mana faɗa idan taji awurin wani, koba haka ba" ɗaga mata kai yayi alamar eh, tare da cewa"I will zip my lips, daga ni sai ke," Cike da jin daɗi tace"Mu biyu kaɗai muka sani, Idan naji maganar awurin wani To kaine, duk da nasan bazaka faɗa ma kowa ba," Ba ƙaramin daɗi danish yaji ba ganin yadda take ta fara'a saboda Ya cire mata gilashin dake Sanya mata jin tsoro, yayin da ita kuma angel ɗin Shine abun tsoro awurinta, don kuwa ga dukkan alamu Akwai wani abun al'ajabi attare dashi,
Kusan atare suka duro da ƙafafuwansu Cikin ɗakin nasu, Adai dai Lokacin kunnuwansu suka soma Jiyo musu motsin buɗe ƙopar ɗakinsu, Mamaki ƙarara akan fuskarsu suka kai idanuwansu saitin benan dake a ɗakin, daga saman matattakalar benan suka Fara kallon ƙafafuwan Mutun Uku dake saukowa, masu sanye da jajayen Uniform, daga bayansu Kuma Giants ne Hannayensu a ruƙe Da Kayan abinci......shin su wanene?
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Tun daga ƙasa har sama su Angel ke binsu da kallo, Yayin da giants suka Wuce Cikin ɗakin zuwa Inda Dining carpet ɗinsu Yake, Bayan sun ajiye masu dinner ɗinsu, Batare da 6ata lokaci ba, Suka fuce daga Cikin ɗakin,
Atare Suka kalli juna ita da danish fuskokin su da alamaun mamaki, ga dukkan alamu basu gane su wanene ba, duk sunyi tsammanin Ko sabbin ɗauka ne aka kawo musu acikin kurkukun,
"Danish su wanene ko ka gane su"? Girgixa mata kai Yayi alamar a'a, Jan hannunshi Tayi"muje mu gani," Tayi gaba Yabi Bayanta, Suna ƙarasowa bakin benan Inda suke atsaye, Ta haska fuskokinsu da fitilar Hannunta, Ras taji gabanta ya faɗi, da ƙarfi ta ambaci sunayensu"PARVEEN! RUBINA! DEEJA" sai da ta kira sunayen su Tukunna danish Ya gane cewa sune, Sunyi matuƙar girgiza da yanayin da suka Yi tozali da ƴan uwan nasu, Sam sun kasa Yi masu magana, Fatar Jikinsu Tayi haske sosai, Fuskarsu tayi jawur abunka ga farar fata, Idanuwansu duk sun kumbra suntum ga dukkan alamu ba ƙaramin kuka su kayi ba, Kayan jikinsu sun yi uban squeezing Kamar waɗanda aka kwato daga Bakin kura, Sumar Kansu Kuwa Ta hargitse ta fita hayyacinta, kai kace sabbin mahaukata ne, Kwata kwata babu natsuwa atare dasu, Yatsun hannayensu dana ƙafafuwansu sae kerma suke Yi, kamar waɗanda sanyi yayi ma mugun kamu, Tsabar ruɗu Ya hana Angel da danish su furta wani abu, Duk irin Zumuɗin da suke Yi nasan adawo musu Da ƴan uwansu Jikinsu Yayi laƙwas, domin kuwa ba haka suka tsammaci ganinsu ba, wani tashin hankalin ma La66ansu dake a bushe sun faffashe, hada busasshen jini ajikinsu,
Muryar angel cikin damuwa ta ambaci "Innalallahi wa'inna ilaihirraji"un! Parveen! Deeja! Rubina! Meya faru daku? Meyasa kuka canza har haka? Dan Allah kuyi mini magana, Me akayi maku? Duk kun canza kun rame kun fita hayyacin ku," Idanuwanta acike tab da kwalla ta yi maganar, hawaye ne masu ɗumi suka soma gangarowa akan fuskokinsu, Lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kuka mai tsuma Zuciya, hankalinsu danish Yayi matuƙar tashi, Koke koken Da suke Yi ne Ya yi silar farkawar su Batool, har cikin kunnuwansu sautin kukansu parveen ke kai musu, Aikuwa Jiki na rawa suka Yaye bargunan da suka lullu6a dashi, Da gudun gaske Suka nufi wurin su ɗaya bayan ɗaya suka ƙaraso bakin stairs ɗin banda mutun ɗaya, Azeeza dake fama da lalurar makarantar dare, Ta farka daga bacci amma bazata Iya kawo kanta inda suke ba,
Koda su Batool Suka ɗaura idanuwansu akan fuskokinsu Parveen, wani irin farin Ciki ne Ya bayyana akan fuskokinsu, Sam basu Lura da yanayin da suke Ciki ba, Saboda tsabar murna Batool ta cakumo deeja da niyar ta rungumeta aikuwa Ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara, wadda tayi matuƙar girgizasu, da sauri Danish ya sanya hannayenshi Saman Ears ɗinshi Ya toshe su gudun kada lalurar shi ta motsa, aruɗe suka haɗa baki suna tambayar lafiya meya faru dasu? Meyasa su ke Kuka? maimakon suga farin Ciki akan fuskokinsu,
Muryar batool a sanyaye tace"deeja meyasa kika saki ƙara saboda ina ƙoƙarin Rungumarki ajikina? Ba ku yi farin Ciki da dawowa Cikin Mu bane"? shiru babu wanda ya amsa mata acikinsu sai kuka suke Yi, Yasmin tace"Na lura gaba ɗaya ma basa acikin hayyacinsu zaiyi wuya ace sun gane mu" javed yace"pls Stop shedding ur tears kuna ƙara tayar mana da hankali, meyasa duk kuka canza? Tsohuwa ta faɗa mana cewa kuna acikin ƙoshin lafiya, Har ma tace mana kuna kewarmu, amma sai gashi Yadda muka ganku a yanzu ba haka mukayi tsammani ba, why pls"? Zuciyarshi a hautsine ya ƙarasa maganar,
"Angel Ki yi mana bayani? Yaushe aka dawo dasu? Meyasa kuma basa Iya magana" Cikin shessheƙar kuka Batool Ta jefa mata tambayar, Itama angel ɗin kukan take Yi, daƙyar ta iya tsagaitawa ta bata amsa da cewa"Kamar yarda kuka gansu haka muma muka gansu, Giants ne suka shigo tare dasu, Hada abincin ma suka kawo mana gashi can sun ajiye farantan saman dining carpet, Dukkan mu mun shiga ruɗanin halin da muka riskesu, Ko magana ma sunƙi yi mana"
Matsawa haris yayi tare da kai hannu Ya ruƙo yatsun hannun Rubina, afirgice ta zame hannunta daga nashi, ta runtse idanuwanta tana faɗin"Zafi nake ji ku daina ta6ani bana so, Ku ƙyale ni ku rabu dani, bana son ganinku" lallashinta hannah tayi"Shikenan tunda bakya so ba zamu ƙara ta6aki ba, Kiyi shiru kinji" Tayi maganar tana leƙen fuskarta,
Angel tace"Ni dama nasan za'a rina, Mutanan nan raina mana wayau suke yi, Tsohuwa tayi mana ƙaryar cewa An kaisu treatment room inda za'a duba lafiyarsu, tsawon 2 weeks kenan, Ga shi yau an dawo dasu babu alamun sauƙi ajikin su, ga dukkan alamu ma wani sabon Ciwon aka jaza musu " rai amatuƙar 6ace angel tayi maganar tana huci, Mubeen yace"pls Mubi komai a hankali, ko dan saboda su Deeja, Ni inaga yakamata aje a sanarma tsohuwa tazo ta duba halin da suke aciki...."tun kafin mubeen yakai karshen maganar shi angel ta wurga mashi uwar harara, kamar zata rufe shi da bugu tace"Amma baka da hankali wlh, wai har yaushe ne zaku fahimci cewa matar nan Muguwace ba sonki take Yi ba, Kuma babbar maƙaryaciya ce! Tayi mana ƙaryar cewa A cikin satin da aka ɗauki su parveen za'a dawo dasu, Sai gashi yau tsawon 2 weeks kenan, Sannan bayan haka ta sanar damu cewa Su parveen sun samu lafiya harma suna tambayarmu, To yau gashi dai an dawo dasu Ba kamar yarda aka ɗauke su ba, kwata kwata babu cikakkiyar lafiya atare da su, ku baku lura da canzawar da su kayi bane? Muryarta a harzuƙe tayi maganar, Jijiyoyin wuyanta duk sun bayyana jikin fatarta saboda tsabar masifa, Kowa yayi shiru yana sauraronta, Cigaba da magana tayi"Kun maida kanku kamar gumaka, Ana cutarku baku ganewa, Yanzu ku kalli fuskokinsu deeja da la66ansu, wlh ko makaho ya shafa jikinsu sai yaji ajikinshi cewa basu da ƙoshin lafiya, Balle ku da kuke Mutane, Su parveen ba Maganin ciwonsu akayi musu ba, Ƙara musu wani ciwon akayi bisa wanda suke dashi"
Wannan bayanin Da angel ta kora musu Yasa sun fara Kokwanton Kalaman tsohuwa, Sun kuma fara yarda da ita, Muryar hibba asanyaye tace"angel ae mu bamu san komai ba, Rayuwa kawai muke Yi acikin duhu, ba lallai mu iya fahimtarki ba," Haris Yace"Tun da kike atare damu ban ta6a Yarda dake ba, Saboda ina zargin ke ɗin Kamar babu gaskiya acikin lamurranki, Yau ce rana ta farko Da kika fara sanya mini kokwanton wani abu acikin raina, Sai dai bazan ta6a Yarda dake ba har sai kin bani kwakkwaran Hujja da zata tabbatar mani cewa Cutar da rayuwarmu ake Yi,' haris na kai karshen maganar shi, Batool tace"Muna goyan bayan haris, Idan har dagaske Ana Cutarmu a gidan kurkukun nan, To kiyi ƙoƙari ki bayyanar mana da kwakkwarar hujjar da zamu aminta dake, Ɗaya bayan ɗaya Angel ke binsu da kallo, wai wace irin hujja ce suke so Ta kawo musu? Bayan ga abu nan zahiri sun gani, acikin zuciyarta tayi tambayar, Tunawa da irin rayuwar da suka taso suna yi yasa ta Yi musu uziri, dole suna da ƙarancin fahimta, kansu Yana acikin duhun Jahilci, idan har bata lalubo hujjar da zasu Gasgata maganarta ba, to kuwa bazasu ta6a yarda da kalamanta ba, taya za'ae ta samo hujja bayan tsohuwa ta gargaɗe ta akan kada ta kuskura Tace zata Zurfafa bincike akan Gidan kurkukun, har ga Allah tana matuƙar fargabar Abunda zai biyo baya idan har tace zata Kawo musu hujja,
Sautin kukan Azeeza ne Ya jawo hankulansu, kusan atare suka Waiwaya baya suna kallonta, Har ta sauko daga saman gadonta, Sai faman laluban hanya take Yi tana faɗin" Wai bakowa ne akusa, Ni baza'a nuna mini su parveenar mu ba, dagaske an dawo mana dasu? Ina ta magana tun ɗazu babu mai ji na,"
Kallon Naufal Haris yayi tare da cewa"Kaje ka ruƙo ta kada ta faɗi" Naufal ya amsa mashi da toh, Da hanzari Ya tunkari parveen, Yana ƙarasawa gabanta, Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Ya janyota zuwa inda suke abakin benan, "to ina su parveenar suke Ae ban ganinsu" Tsoki Haris Ya ɗan ja"kefa matsalarki kenan abu kaɗan sai kuka, Kamar kinfi kowa baki, Ki barmu muji da abunda Ya ishe mu," a ƙule yayi maganar, cikin sanyin murya danish yace"haris ka bi ta a hankali, banaso kana yi mata magana irin haka" jinjina kai haris yayi tare da cewa na daina, kawai bana son yawan kukanta ne,"
"Ni dai ku nuna mini Su, kuma kuka bazan daina ba, Yanzu na fara sai dai ka buge ni" rai a6ace azeeza tayi maganar, mutumin dake fama da kanshi, kwata kwata bata iya ganin fuskokinsu, Biji biji take gani,
Matsar da ita naufal Yayi zuwa gabansu deeja da suka ƙame Sai shessheƙar kuka suke yi, ko gajiya basa yi,
"Gasu nan Agabanki Kiyi musu magana" naufal ne yae maganar, Hannayenta ta ɗaura asaman kirjin deeja tana shafata, Harta samu ta ruƙo hannunta ta ɗago shi zuwa saitin hancinta ta shinshina shi, duk suna kallonta, farin Ciki ne ya bayyana akan fuskarta, rungumeta tayi tana faɗin"Deeja Ashe kune dagaske, Nayi farin Ciki da aka dawo mana da ku, yanzu shikenan kunji sauƙi baza'a ƙara raba mu daku ba, Ni dai na roƙe ku kada ku ƙara Yin rashin lafiya, Kodan saboda kada araba mu daku, Saboda bamu jin daɗin rashin ganinku acikinmu" ita kaɗai take ta sambatunta, Javed ya kira sunanta"Azeeza Kiyi hakuri ki ƙyaleta, Basu son ana ta6a su, Har yanzu da sauran Jikin nasu" Cikin shessheƙar kuka tace"meyasa toh basu son ana ta6a su? Basuyi farin Ciki da dawowa Cikin mu bane? Duk irin kewarsu da muka Yi," babu alamun zata fahimce su, angel ce tace"Javed ka barta, tun da naga yanzu Deeja bata Yi ƙara ba kamar yarda tayi ɗazu da batool ta ruƙota," Eve tace"Nima na lura da hakan"
"Nidai kuyi mini magana, Wai sai kace baku Ji na, ko fushi kuke Yi damu ne"? matsawa tayi gaban Rubina Ta ruƙo hannayenta takaisu saitin hancinta ta shinshinasu, kafin ta faɗa jikinta ta rungumeta tana faɗin rubina, Kema bazaki Yi mini magana ba? Duk kun shareni," jin shiru bata amsa mata ba, yasa ta janye jikinta daga na rubuna, da alama Jikinta yayi sanyi, Ruƙo hannun Parveen Tayi, batare data shinshina shi ba tace"parveen, Ke ma ba za kiyi mini magana ba? Meyasa bakwa farin ciki da dawowarku Cikinmu ne? Duk irin kewarku damu kayi, Munji raɗaɗin rashinku acikinmu, Tun ranar da Giants suka zo suka tafi daku, Kusan kullum ne sai Mun ajiye maku abinci, amma abanza yake lalacewa, mun yi maraicinku sosai" takai kai karshen maganar tare da ɗaura kanta saman kirjin parveen, hada ƙoƙarin zagayo da hannayenta zuwa bayan parveen ta ƙanƙameta,
"Yanzu ya zamuyi da su? nifa nagaji da tsayuwa ƙafafuwana har sun fara Yi mini zogi, Yakamata Mu koma Cikin ɗaki Mu xauna, yasmin ce tayi maganar,