Kenza eBookz

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 57

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 57

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 57: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 57. jin wannan maganar ta Angel, yasa shi…

3,303 words

jin wannan maganar ta Angel, yasa shi yin saurin xagayo da hannun shi ta bayanta zuwa saman kafaɗarta ta hagu, Ya ɗan kwantar da kanshi saman right shoulder ɗinta, Har ga Allah bai son kallon Mirror, Ba yadda zai yi ne don sun matsa mi shi, kuma a yanzu yana son farin cikin su shiyasa ya amince musu,

Kanga madubin ta yi saitin Fuskarshi tare da cewa"Ka buɗe idanuwanka a hankali," bin umarnin ta yae wurin buɗe eyes ɗinshi slowly ya ware su akan Round mirror ɗin, har wani lumshe su yake yi, Murmushi angel ta saki ganin yana kallonta ta cikin madubin tace"Bani xaka kalla ba, Fuskarka zaka kalla" ta6e mata lips dinshi yae irin an takura shi ɗin nan,

Su haris sai dariya suke tiƙa, sun samu Abun kallo, hada ƙoƙarin zuƙunnawa bakin gadonsu, saboda sun gaji da tsayuwa, duk yadda ta so Danish Ya kalli fuskarshi acikin mirror yaƙiya sai dai ya kalli fuskarta, Javed yace"its okey, Hakan ma ya wadatas, Yanzu A ajiye madubin gefe, Ga chicken leg ɗinsa nan ki bashi ya ci, idan ya kammala da kazar sai ki ba shi fruit ɗin shi" Amsa mashi tae da toh tana murmushi ta miƙa ma parveen madubin ta sanya hannu biyu ta kar6e shi, ta juya ta nufi box ta ajiye shi, ta dawo ta zuƙunna gefen su hanna, Duk fa wannan budurin da suke Yi basu san cewa Dare Yayi ba, don tuni Hasken Fitilun ceilling ɗinsu Ya ɗauke, Na floor lamps ne Ya Haskaka Room ɗin nasu, ba tare da sun ankara ba, Wasu irin fitilune Da zarar duhu yayi da kansu suke kunna kansu, Kamar dai na saman ceiling ɗinsu, banbancin shi ne, da zarar dare yae suke ɗauke wa su kuma na ƙasan sai in duhu yayi suke kunna kansu, Kuma haskensu baida banbanci, da alama babu mai jin bacci acikinsu, sakamakon baccin da suka sha ɗazu da marece, hada ƙarin hakan yasa suka gaza gane cewa Dare ya yi.

Azeeza ce ta miƙa ma Angel Kwandon Tasa hannu biyu ta kar6a ta ɗaura shi saman Laps ɗinta, kafin ta zura hannun ta na dama ta ruƙo cinyar kazar ta ɗago da ita, saitin bakin shi ta kanga mashi ita, Sai gashi Ya xaƙe dai ci ya ke yi su mubeen suna ta yi mishi clapping, sai da ya Cinye rabi Ya janye bakin shi, ta tambaye shi ko ya ƙoshi ne? yace mata eh, zata iya cin sauran, parveen kamar zatai kuka tace mufa,' Dariya angel tae tare da miƙa ma azeeza Naman kazar maimakon parveen tace"Saboda rashin tsoron Allah Parveen Nafa ga wurin da kika yaga, hada sahun haƙoran ki, a jikin cinyar kazar, ko an gaya maki ban lura ba ne," Yatsina fuska parveen tayi, Hada murguɗa baki, Azeexa kuwa ta kar6a cinyar kazar daga hannun Angel, ta ɗan gutsira ta miƙa ma hanna itama ta yaga, ɗaya bayan ɗaya saida kowa Ya Ci naman, A ƙarshe suka miƙa ma parveen Ƙashi, su ka ce Ta gwaigwaye shi, Hada ƴar ƙwallarta saboda tsabar baƙin ciki, kuma hakan baisa taƙi kar6ar ƙashin ba,.

Apples ta curo kusan Uku da suka rage mashi, Yace mata shi ɗaya ya ishe shi, sauran ta basu su ci, tace mashi hada sauran fruit din? Don akwai ayaba guda uku, Yace mata Ta ajiye mashi ayaba ɗaya ta basu sauran su ci, Sai daɗi suke Ji, Ta miƙa ma haris Apples biyu da ayaba Biyu Yasa hannu ya kar6a, Shi ya rarraba musu, tare da miƙa ma kowannan su, suka kar6a suna ci.

Abaki angel taci gaba da bashi apple ɗin yana Ci, sai da ya ci rabi, yasa hannu ya kar6a, Ya koma yana bata abaki tana ci, Ayabar ma shi ya 6are 6awon Ya zura mata a baki, taci kusan rabi kafin ya ƙarasa cinye sauran, bayan sun kammala suka sha ruwan su dake acikin bottle,

Haris ne ya kawar da kwandon Ya maida shi a ma ajiyarsa, Parveen kuma ta kwashe 6awon Ayabar da su ka 6are ta nufi toilet ta zubda su cikin trash can, Daga bisani ne suka gane cewa dare ya nutsa, Angel tace su jira tayi musu addu'a kafin su kwanta, Suka amsa mata da toh, Saukowa tae daga saman gadonta, tabar Danish zaune yana kallonsu, Cikin harshen larabci ta shiga karanto musu addu'o'in tana tottofa masu, suna amsa mata da ameen, bayan ta kammala, Hannah ce ta basu shawarar su Cire sabbin Uniform ɗinsu, Su sanya tsoffin gudun kada su yi squeezing,

In yaso gobe da safe sai su maida sabbin, Angel tace kin kawo shawara mai kyau, daga yanzu old uniforms ɗinmu sun zama sleeping dress ɗinmu, Kowa Ya ji daɗin wannan shawarar, without wasting time suka sauya Kayan jikinsu, Kowa Ya ninke nashi ya tura a cikin akwati, Suka ɗauko Tsaffin suka sanya ajikinsu, daga bisani Kowannan su Ya nufi gadon shi ya kwanta Suka ja bargunansu, in a short time bacci yae awon gaba dasu, ɗakin yae tsit ba ka jin hayaniyar komai, Mutun biyu ya rage angel da Danish, babu alamun zasu runtsa, Ae yau suna cikin farin Ciki,

Ya yi tsammanin zata dawo ta kwanta saman gadonta, sai kuma yaga ta nufi ƙopar shiga sashen toilet dinsu, har sai da ta shige, kafin ya sauko daga saman gadon yabi bayan ta, A bakin ƙopar toilet din ya la6e yana kallonta,

A yayin da take zuƙunne gaban tukunyar flowers din nan, kamar mai ta6in hankali, haka ta zauna tana ba furen Batul labarin abunda Ya faru Yau, hada ƴar ƙwallarta tace"Naso ace kina atare damu, a ka yi wannan shagalin, nasan zaki yi farin ciki sosai, saboda burin ki ne, kiga mun haɗa kan mu, Ina matuƙar ƙaunarki ƴar uwata rabin raina..." kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon hawayen da suka wanke mata fuskarta.

Sam ba ta ji takun tafiyar shi ba, sai dai ta ji shi, a gefenta Ya zuƙunna, ɗagowa ta yi da rinannun idanuwanta suka haɗa ido da juna, a hankali ya cire hannun shi ya ɗaura shi saman sumar kanta, Ya ɗan kwanto da kanta saman shoulder dinshi, cikin sanyin murya ya soma lallashinta, Har ya samu ta ɗan lafa, Da kanshi ya share mata hawayen dake akan fuskarta, a tsanake suke kallon furen batool Ya miƙe tsaye babu lanƙwasa, Red leaves ɗin shi sun bubbuɗe sun cixa launinsu, Haka furen daddynta Yana a tsaye launin shi kore Ya cixa, sai dai wani abun mamaki furen Ya xuƙunna, kamar mutun " aɗan ruɗe tace mashi"me hakan ke nufi? Furen dad ɗina Ya zuƙunna," hannu Danish ya kai tare da shafa ganyen furen yace"Bani da amsar tambayarki, amma A ilmin da nake dashi kan furenni, Daddyn ki, Yana yin wani abu adai dai irin wannan lokacin" bakomai ya faɗo mata arai ba, face Sallah, saboda sanin cewa a lokacin baya daddynta yana yawan Yin nafilfilin dare, duk da bata da tabbacin cewa idan Yana araye, ko kuma Lokacin ƙasar Nigeria da kuma Na kurkukun ƙaddara Ɗaya ne, zai Iyayiyuwa asamu banbanci tunda kurkukun tana hasashen ba acikin ƙasar Nigeria Ya ke ba,"

jin ta yi shiru yasa shi kallonta in a cool voice yace"what are u thinking"? Da sauri tace mashi ba komai, yace mata"muje mu kwanta, idan ma kina so zan goya ki abaya na" murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, har time ɗin ba ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar shi ba.

wani irin daɗi take ji, ita fa jin Danish take yi kamar wani sashe na sassan Jikinta, da ke taimaka mata wurin yin numfashi, idan ta haɗa jiki da shi, ba komai take tunawa ba, face Daddynta, Yadda take tumurmusarshi, idan suka kwanta a gado ɗaya, wani lokacin da gangan take ɗaura mashi ƙafafuwanta saman ƙirjin shi, duk don saboda ta takura mishi, a lokacin data addabi rayuwarshi, Allah sarki tajuddeen Namijin Duniya!

Numfasawa ta yi kafin ta Canza akalar tunanin nata zuwa ga Aunty Aneelerh, Bakomai ya fado mata arai ba, face ranar da ta faɗo musu ɗaki babu sallama, Sun fito daga Cikin toilet Kowannan su ɗaure da white towel a ƙugun shi, hankalinsu ya tashi ganin Angel, Uwar gulma da son tsegumi ga tambaya kamar ƴar jarida, A lokacin ita da uzair duk suka sha Jinin jikinsu aka rasa me magana acikinsu, Ita ko ta ruƙe qugu tana binsu da kallon tuhuma. ta ce su fada mata me suke yi acikin toilet su biyu, har suna haɗa baki wurin ce mata, babu abunda suke yi, dama sunga yayi datti ne shine suka shiga suna mopping ɗinshi, wani irin kallo ta jefa musu tace"To meyasa suka fito da ɗan towels a ƙugunsu? Ina kayan su suke"? Saboda tsabar ruɗi uzair yace"ita ce take wanka, ta kira ni don in cuɗa mata bayanta, saboda hannun ta bai kaiwa" Dariya angel tasaki tana fadin"wai ita zasuyi ma wayau, sun ganta ƴar ƙarama, hmm basu san tasan komai ba, tun da sunƙi faɗa mata, zata je ta faɗa ma daddyn ta ne abunda suke aikatawa acikin toilet, tana kai ƙarshen maganar, ta watsa da gudu zata fuce, aikuwa aguje suka bi bayanta, har suna bangaje juna Abakin ƙopar fita bedroom dinsu, ta dinga yi musu yawo da hankali, tana zagaye falon suna bin bayanta, daƙyar suka samu Allah ya taimake su, suka damƙota, Suna faman sauke ajiyar zuciya, a saman sofa suka zaunar da ita, sai tiƙar dariya take yi tana kallonsu, su fa duk a tunaninsu tasan komai game da ma'aurata, tunda sun san halinta, kamar aljana haka take ga shegen wayau, sai da suka tambayeta me zata faɗa ma daddynta, tace musu abunda suka faɗa mata suna yi acikin toilet, ba ƙaramin kwanciya hankalinsu yae ba, ganin bata fahimci komai ba, yasa aneeerh ta miƙe taje ta buɗe frigde ta dauko mata fura acikin roba, ta miƙa mata, Duk don saboda su mantar da ita komai, Aiko tun da tasha furar nan taji daɗi yakai mata karo, tace musu, ae ta fasa faɗa ma daddynta su kwantar da hankalinsu, Ita yanzu ma gida zata tafi ta kunna kallo"

sai bayan da tabar gidan suka dinga yima juna dariya,

murmushi ne ya bayyana akan fuskar angel hada ƴar dariyarta, sam ta manta cewa Danish Yana a tare da ita,

"Why are u laughing? Ko kin tuna wani abu ne"? Muryar Danish ce ta ratsa kunnuwanta, a shagale ta kalle shi tare da cewa"Aunty aneelerh, matar daddy uzair, su na tuna, ina matuƙar ƙaunarta, saboda tana so na, kamar ita ta haife ni, ba kamar mahaifiyata ba, da ta gudu tabar ni, na tsane ta fiye da mutuwa ta," Fuskarta a ɗaure ta ambaci hakan,

Saboda ya faran ta mata rai yace"Idan kina so, zamu Iya duba furen auntynki Aneelerh," da sauri ta ɗago da kanta daga saman kafaɗarshi tace"Are u serious"? Jinjina mata kai yae alamar Eh, Cike da zumuɗi tace mishi Toh, ya duba mata" ta ambaci hakan tare da runtse idanuwanta, tun kafin ma yace ta rufe su, Sai da ya gama kalle kyakkyawar fuskarta, kafin ya miƙe Ya nufi fanfo, Ya kunna shi ruwa ya soma kararowa, Ya tarba tafin hannuwanshi biyu ya ɗebo ruwa ya gumtse shi abakin shi, Da sauri Ya juya ya Koma bakin Tukunyar fulawar, Har lokacin Angel bata buɗe idanuwanta ba, shi kawai take jira Ya bata umarnin ta buɗe su.

"Za ki iya buɗe wa yanzu," A hankali take mutsu mutsun buɗe eyes ɗinta, biji biji ta fara Hango tsiron wani kyakkyawan Fure dogo, Launin Ɗorawa, Yellow kenan a turance, mamaki ne ya kamata Ganin wani ɗan ƙaramin fure A jere da dogon furen Shi kuma Launin shi fari fat, Ganyansa masu kyan gaske, ' waro ido waje ta yi yayin da take kallonsu, Tsabar ruɗu ya hana tace komai, Idan ta kalli furen da saita kalli fuskar Danish, Ya tsareta da idonshi ba tare da ƙyaftawa ba, muryarta na rawa tace"Am..ma.ya akai naga furenni Guda biyu? Ɗaya dogo ɗaya kuma ƙarami? What does that mean? Tae tambayar Cikin ƙagara da son jin amsar shi,

"I don't know what that means, nima ban yi expecting ɗin furennin zasu futo su biyu ba, bansan ma'anar hakan ba" Tamkar zata fashe mashi da kuka tace"pls Danish, Think about it, am so eager naji ma'anar wannan ƙaramin furen mai kyan gaske,"

ashagwa6e ta ƙarasa maganar, sai kallonta yake don ba ƙaramin kyau take yi mishi ba, ɗauke idanuwanshi yai daga kan fuskarta, Ya kalli ceilling na tsawon mintuna, Da alama nazari yake yi, can dai ya dawo da dubanshi gare ta, yace"faɗa min ko kina da ƙaramin ƙani ne"? Tur6une fuska tae"A'a, Bani da ƙani, auntyna ma bata ta6a haihuwa ba," murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, kafin yace"duk da bani da tabbaci, but apparently the little flower means a little boy, so there might be a little boy in your aunty's house, a hasashe na kenan, Cos duk wani fure da kika na fitar to mutunne mai rai"

Yadda kasan malamin duba haka ya zaƙe yana kora mata bayani, babu alamun wasa akan fuskarshi, tun kafin ya kai ƙarshen maganar, ya lura da irin kallon hararar da ta ke jefa mashi, bata ta6a yarda cewa ƙarya yake yi mata ba, sai yau, ta ya zai ce ƙaramin mutunne furen can, Bayan Ita a iya saninta, Har ta bar Gida babu wata ƙaramar halitta, dama i tace Yarinyar, kuma yanzu ta girma" taso ta ƙaryata shi amma sai takasa, saboda ta fara jin bacci a idonta.

"Muje mu kwanta" tayi maganar tare da ruƙo hannun shi, Yace mata ta hau bayan shi Ya goya ta, ba tare da tayi mishi gaddama ba, Ya juya mata back din, Ta daddage Ta haye, ya yunƙura ya miƙe ɗauke da ita suka nufi cikin ɗakin su, ba ka jin hayaniyar komai saita sautin minsharin su parveen, A saman gadonta Ya kwantar Da ita, Yaja mata bargo ya lullu6eta, kamar wata ƴar baby, har ya juya zai nufi gadon shi, Ta ruƙo hannun shi, tare da cewa"Why ba zaka kwana asaman sabon gado ba? Akwai ɗaya daya rage ka kwanta mana" girgiza mata kai yae alamar a'a yace"Nafi son, tsohon gadona, saboda wannan ba mallaki na bane, duk ranar da masu shi suka zo, bazan Ji daɗi ba, saboda na saba dashi" kalaman Danish sunyi matuƙar burgeta, Tana murmushi tace"Ka faɗi gaskiya, don haka nima bazan kwana asabon ba, Muje mu kwana a saman tsaffin gadajen mu" ba ƙaramin daɗi yaji ba, dama yana ta tunanin tafiya ya kwanta shi ka ɗai, tun da sun shirya da ita, yafi son su kwanta suna fuskantar juna,' saukowa tayi daga saman gadon, hannunsu ruƙe Cikin na juna, suka nufi gadajensu, Sai da ta fara bari ya hau saman bed din shi ya kwanta, Ta yi mashi addu'a ta tottofa mishi saman jikinshi, har yana cewa"wai duk tabi ta tofa mishi yawu ajiki," ta bashi amsa da cewa addu'a ce tae mishi, bai dai ce mata komai ba," bayan ta gama Ta koma saman nata gadon ta kwanta suna fuskantar juna, wani irin kallo suke jefa ma juna, tsawon lokaci kafin Bacci 6arawo yai awon gaba dasu............

Good Morning🌅

A washe garin ranar babu wanda ya farka acikinsu, bacci ya yi daɗi, sun saki baki da hanci anata minshari, a hankali motsin buɗe ƙopa Ya soma karaɗe Cikin ɗakin nasu, kafin wani lokaci, Sai Ga Giant Su Uku Masu Kawo musu abinci, Hannayensu ruƙe da wooden trays, Daga bayansu Wani Giant din ne Guda ɗaya Hannun shi biyu ruƙe da table mai ɗauke da tanƙameman Cake, Haɗaɗden gaske, daga gani zai yi daɗi a baki, launin uniform ɗinsu red and black, saman try din da aka ɗaura Cake ɗin Akwai Ƙaramar wuƙa ta yanka cake, tare da spoon, abun dai sai wanda ya gani, a Jikin Cake ɗin an yi mishi rubutu da ya bayyana sunan kurkukun ƙaddara Cikin harshen turanci aka yi shi kamar haka

_Welcome to the Destined Prison and happy prisoner's day_

Ya yi matuƙar yin kyau, kusan hawa bakwai ne ajikin cake ɗin, A tsakiyar ɗakin Giant mai ɗauke da table ɗin Ya sauke shi, Sauran dake ruƙe da wooden trays suka sauke farantan saman dining Carpet ɗinsu, basu tsaya jiran su farka ba, a tare suka juya tare da fuce wa daga cikin ɗakin, "

ƙarar rufe ƙopar ne Ya farkar da Azeeza daga bacci, abun ka ga ruɗaɗɗa. A firgice ta ware Idanuwanta, Hannunta dafe da saitin zuciyarta, dake ta faman harbawa, Tayi tsammanin ko zuwa za'ae a ɗauki wani daga Cikin su, jikinta na kerma ta ɗan yunƙura ta miƙe zaune don taga su wanene, A tsorace take kallon Cikin ɗakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan Ƙaton cake ɗin, mai matuƙar ɗaukar ido, Mamaki ne Ya kamata, Ta zaro ido tamkar ƙwayar zasu ƙundumo ƙasa, Jiki na 6ari ta sauko daga saman gadon ta nufi Cake din, Saboda tsabar girman shi, da kuma tsayin table din dake dauke shi, sun kere mata, bata iya ganin ƙarshen cake ɗin idan tana a kusa dashi, Kamar wata baƙauyar Daji haka ta dinga zagaye Cake din har saida kanta Ya fara juyawa tukunna ta ɗan dakata, Hannunta ruƙe da qugunta, Sai faman Jinjina kai take yi, alamar mamaki, ta wutsiyar idonta, ta hango kamar kayan abincinsu, Da sauri Ta juya ta 6angare da Daning Carpet ɗinsu yake, waro ido tayi, badan tana mamakin Abincin da aka kawo musu ba, face Sabbin farantan da aka canza musu masu tsayi.

Wani irin ihun farin Ciki ta saki, kai tsaye sautin ihun ya daki dodon kunnan masu bacci, Saboda tsabar firgitar da su ka Yi, kusan atare suka Yaye bargunan da suka lullu6a dasu, Kowannan su Ya miƙe xaune, wasu suna hamma wasu suna Yin miƙa, hada masu miyan bacci abaki irin su parveen da mubeen, At same time suka kai idanuwansu kan Azeeza Kafin suyi yunƙurin Yi mata magana tai saurin Nuna masu ƙaton Cake ɗin da hannunta,"

Zallar mamaki da al'ajabi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Nan take baccin da bai ƙarasa sakin su ba, ya washe, ɗaya bayan ɗaya suka dinga saukowa daga saman gadajensu suna tunkarar ƙaton Cake ɗin, a wani irin kasalance, Danish ne kaɗai bai sauko daga saman bed dinshi ba, Yana zaune daga bakin gadon idonshi akan cake ɗin, Ga dukkan alamu baccin bai ishe shi ba, katse mashi shi akayi, sai faman lumshe eyes ɗinshi yake yi,

A jere Suka kewaye Cake ɗin, Kowa Ya baza na mazurinsa, Ko ƙyaftawa ba su yi, parveen ce tai ƙoƙarin kai hannu don ta ta6a shi da sauri Javed Ya ka6e mata hannu tare da cewa"Uwar Hankali, Daga ganin cake kinsan Wanda Ya ajiye shi ne?

Azeeza ce ta bashi amsa da cewa"Ina tunanin Giants Ne suka kawo shi, tare da breakfast ɗinmu," ta ƙarasa maganar tare da Juyawa tana nuna mashi Dining Carpet ɗinsu, atare Su naufal suka kai idanuwansu kan abunda take ƙoƙarin nuna musu, mamakine Ya ƙara kama su ganin an canza musu farantan abincin su, don suna sane da Irin trays din da ake kawo musu abinci cikinsu, To yau an canza musu wasu sabbin farantai, masu tsayi,

Angel dai ta rasa bakin magana, tarasa gane wannan sabon salon na Kurkukun ƙaddara, abubuwa suna ta canzawa, Anya wannan farin Cikin bana ƙarshe bane acikin xamansu Prison? Na farko an canza musu kayan amfani na toilets da sabbin uniforms duk da tsohuwa tace musu itace ta buƙaci abasu akayan don ta faranta mu su,

Tsawon kwanaki tunda aka tafi da batool ba'a ƙara ɗaukar wani acikinsu ba, duk da bata ga wani ya ƙara yin menstruation ba, wata'ƙil shiyasa ba'a zo an ƙara ɗaukar wani ba,

ta yi zurfi Acikin tunaninta, muryar Naufal ce ta dawo da ita Cikin hayyacinta

"Nifa ina tunanin Sabbin prisoners za'a kawo mana Yau, yakamata muyi wani abu akai, Mu gyara musu gadajensu, sannan muje muyi wanka mu sanya sabbin uniform ɗin mu kada suxo su ganmu kaca kaca suce xasu raina mana wayau,"

Readers Also Read