Kenza eBookz

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 58

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 58

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 58: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 58. Naufal na kai ƙarshen maganar tashi,…

3,359 words

Naufal na kai ƙarshen maganar tashi, Yasmin tace"Nima nayi tunanin hakan, idan ku ka lura da rubutun dake akan cake ɗin, Kamar Ana yi ma wasu barka da zuwa ne," eve tace"in dai haka ne kuwa nayi mamaki, daga gani waɗanda za'a kawo mana ƴan gata ne, don ko time da aka kawo Angel ba'a shirya mata cake ba" Mubeen ne ya bata amsa da cewa"ae ita angel ita kaɗai aka kawo daga waje, su kuma waɗannan ina hasashen dukansu ba acikin prison suke ba, Sannan kuma ki duba da kyau Ajikin Cake ɗin an rubuta Prisoner's Day, that mean an shirya shi ne domin mu kan mu muyi enjoying ɗin ranar mu ta prisoners," Da mamaki akan fuskar Hanna tace"Abun da ɗaure kai, Har wani prisoner's day gare Mu," ta6e baki Haris yae, yama rasa ta cewa, kwata kwata baiyi farin ciki da ganin cake ɗin ba, acewarshi maimakon adawo musu da ƴar uwarsu batool, An dage sai faranta musu akeyi, gani yake kamar ana ƙoƙarin ɗauke musu hankali ne daga tunaninta,' a fili Yaja guntun tsoki, fuskarshi amurtuke babu walwala, Deeja ta lura da yanayin fuskarshi, tunaninsu yazo ɗaya, itama abunda take hasashe kenan acikin zuciyarta, sai dai basu fito sun faɗa ma sauran ƴan uwan nasu ba, kodan gudun kada su tarwatsa musu farin Cikin da suke ci. Ganin yadda suke ta zagaye cake ɗin, Cikin Jin daɗi,

"Muje mu yi wanka, mu canza kaya, kafin Mu zo mu yanka Cake" Rubina ce tai maganar, da gudu suka nufi sashen toilets, suna ƴar rige rigen shiga, Mutun uku ne suka fara shiga, sauran suka tsaya suna jiran su fito suma su shiga, Waɗanda suka rage Acikin ɗakin Danish dake zaune gefen gadonshi, Sai angel da haris and deeja da kuma naufal dake tsaye gaban ƙaton Cake ɗin, daga bisani ne Angel ta koma gefen Danish ta zauna, tare da kallon fuskarshi tace"Ka tashi lafiya"? Ya mutsa fuska yae muryarshi adisashe yace"A'a, baccin bai ishe ni ba, azeeza ne ta farkar dani,"

"Ka kwanta mana, ka yi bacci, amma idan kana jin yunwa ka bari mu fara cin abinci, in yaso daga bisani sai ka koma baccin" girgixa mata kai yae tare da cewa"na haƙura da komawa baccin, tun da kin farka ƙwara nima na kasance a farke" Yaƙarasa magnar yana faman lumshe idanuwashi akan fuskarta, "Ko zamuje muyi wanka ne"? amsa mashi tae da toh," Ya ruƙo hannunta acikin nashi, suka nufi toilet, a lokacin su Parveen sun kammala nasu wankan sun fito daga sashen toilet ɗin, Sai da suka je bakin ƙopar toilet ɗin Taga yaki sakin hannunta, tace"Ka shiga mana" ni sai na shiga ɗayan toilet ɗin" da buɗar bakinshi sai cewa"why bazamu shiga atare ba? Ni inaso na taimaka maki ne wurin yin wankan" fuskarshi a yamutse yai maganar, ita ko ta saki baki tana kallon shi, Mamaki Ya hanata magana,' har saida yaja hannunta da niyar su shiga ciki, da sauri ta fusge tana faɗin"Kai fa ba cikakken hankali ne da kai ba, na faɗa maka babu kyau ka daina cewa mu shiga toilet ɗaya, hakan bazai ta6a yiwuwa ba, Kana namiji ina mace kuma ka ce zaka yi mini wanka" ta ƙarasa maganar tana jifar shi da harara, ta lura haryan zu Danish baida linzami, shi dai burin shi yayi mata wanka, sai kace wata ƴar tsana,

"Angel ba wani abu bane fa, kafin zuwanki prison ɗin nan, munayin wanka dasu Batool, so wannan ba wani matsala bane....."daƙyar ya ƙarasa maganar saboda kallon da take watsa mishi,

"Ba ka ji me ka ce ba? Kafin zuwana kurkuku, That's mean lokacin kuna a jahiliya period! bayan nazo Kuma saina zo maku da tsarkakakken addini, da ya hana mace da namiji su ke6e awuri ɗaya, sannan babu kyau kallon tsiraici, baida amfani ma mutun ya dinga kallon tsirai cin shi balle ya kalli na wani kuma, fatan Ka fahimce ni" ta yi maganar tare da yi mashi gwalo, tana dariya ta fada toilet taja ƙopa ta datse, bayan ta shiga ciki, ta sanya hannu ta dafe ƙirjinta, tana faman sauke ajiyar zuciya, lamarin Danish yafi ƙarfinta, Dole sai tana taka mishi burki, idan ba haka ba, wata rana zaifi ƙarfinta ne ya ɗauketa yakai ta toilet da sunan zai mata wanka,

Saboda ta ɗauke su tamkar Ciki ɗaya suka fito, shiyasa ma take bari suna ruƙe juna, don Lokacin da take tare da daddynta, babu namijin daya isa Ya ruƙe mata hannu tun tana ƴar ƙaramarta, bayan shi sai Uncle abdallah sai kuma Uzair, saboda ta tsani Namiji ya ta6a jikin ta, akwai ranar da wani malaminsu na makarantar boko yayi gigin Shafa la66anta, ya gansu pink sun burgeshi, aikuwa ta daddage ta gartsa mashi cizo, ɗan tahalikin nan jinya har gadon asibiti, saboda cizonta tamkar dafi gare shi, zai yi wuya ta ciji mutun batare da zazza6i ya rufar mashi ba, kamar dai yadda ta yi ma danish a kwanakin baya kafin su fara shiri daya tona mata asirin ta ɗauki wuƙa, ta yakushe shi tare da gartsa mashi cizo, zazza6i ya rufe shi har giant suka tafi dashi,"

tana Jiyo alamun buɗe ƙopor ɗayan toilet ɗin dake a jikin wanda take Ciki, murmushi tasaki saboda ta gane shine Ya shiga, aranta tace"ɗan rainin wayau, saboda kawai ka ganmin budurcina shine zaka sa naci akan sai ka yi mini wanka," ta ƙarasa maganar tana faman Cizon la66a,

Kafin wani lokaci gaba ɗayansu su kayi wanka, Kowa Ya cire tsaffin uniform ɗinshi suka maida sababbin ajikinsu, Wani irin kyaune ya bayyana akan fuskokin kowannan su, Farin Ciki ta ko'ina, Sun kewaye Cake ɗin suna ƙare mashi kallon kafin suyi tunanin Yanka shi, Angel tace su jira ta fara yi musu addu'a, Suka amsa mata da to, Kowa Ya natsu A yayin da take karanto musu addu'o'in ta tofa ma Cake ɗin, Haris yace"kin fake da addu'a kina watsa mana yawu akan cake ɗin mu" Da zolaya yayi maganar yana hararanta, gaba ɗaya suka sanya dariya, fararen haƙoransu kamar gonar auduga,

"Waye xai yanka mana cake ɗin? maji daɗin gado ko kuwa Maji daɗin abinci"? naufal ne yai maganar, parveen uwar zumuɗi tace"Ni xan yanka" Azeeza tace wlh baza abaki ba, indai aka baki sai an bani nima na yanka" harara parveen ta watsa mata tana faɗi"Dallah jibarki can ƙasa, In banda rigima taya za'ae ki iya yanka cake ɗin nan"? Saboda tsabar baƙin cikin kalaman Parveen yasa azeeza ta zuƙunne kasa tana raira musu kuka," rai a6ace angel ta kalli parveen"bansan meyasa kike son kushe halittar mutun ba, Bakisan babu kyau ba, yanzu ita da kike ma gorin halitta, shin ita ta halicci kanta? Ke kanki fa Girma kikayi kika ganki ahaka, Ko ke kika tsara ma kanki halitta ne" ɗaure fuska parveen tayi tuni idanuwanta sun ciko da kwalla, angel tace"ni ban faɗi hakan don na 6ata maki rai ba, kawai inaso kisan cewa ba abu bane mai kyau kushe halittar mutun, cos bashi yai kanshi ba, haka Allah ke son ganin shi, ke kanki, nafi ki tsayi, Ni kuma Danish Yafi ni, so kinga ni kowa Da irin nashi halittar" ganin zasu 6ata masu farin Cikin su yasa haris, Yin saurin dakatar da Angel ta hanyar yi musu magana"its okey, pls maganar ta wuce, indai akan yankar cake ne na yanke shawarar Danish Shine xai fara Yankawa, saboda shiyafi dace wa Daya yanka shi, Idan ma kuka kwantar da hankalin ku kowa ma xai yanka, ba kuga girman Cake ɗin ba? Ai mutun ɗaya bazai iya yanka shi ba, dole sai an haɗa hannu,"

Duƙawa Danish yai tare dakai hannu ya ruƙo Azeexa ya ɗago da ita, gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanshi ganin ya ɗaurata Saman wuyanshi kamar wata ƙaramar yarinya, nan fa ta fara washe baki ta koma tana yi ma parveen gwalo saboda anyi mata makawuya tsayinta ya zarce na kowa,

"Ku bata knife ɗin, Ita nake so tafara Yankawa" Acewar Danish, da sauri Haris ya ɗauki wuƙar Ya miƙa ma Azeeza dake asaman wuyan Danish, Tasa hannu ta kar6a tana dariya, Ita kanta parveen batasan lokacin data kwashe da dariya ba, ganin yadda Azeeza take alfahari da tsawon da ba nata ba, sai da suka fara ƙirga one two three Kafin Azeeza ta ɗaura wuƙar zata yanka Cake ɗin, sai dai bata kai ga yankawa ba, Suka Ji motsin buɗe ƙopa, a firgice suka kai idanuwansu kan benan,

A matuƙar ruɗe suke kallon ƙafar matashiyar budurwar data fara leƙo wa, wasu matsiyatan Highheels ne a ƙafar masu shegen tsini, Kai daga ganin fatar ƙafar ta rainon madara ce fara tas, saboda tsabar ruɗi azeeza batasan time da ta saki wuƙar yanka cake ɗin dake a hannunta ba, Tabarakallahu ahsanul khalikin, wata irin tafiya yadda kasan bata son taka ƙasa, Daƙyar take taka staircases ɗin, takalmanta har wani sauti suke badawa ƙwas ƙwas! Daga gani ba ita kaɗai bace, akwai sauran dake abayanta, kowannan su sanye Cikin Uniform ɗinshi...........❤

Haƙiƙa Ta yi matuƙar tafiya da hankalinsu, Kyakkyawar matashiyar budurwa, jawur da ita, Uniform ɗin Jikinta Style ɗin yasha banban da nasu, Ita nata gajeran skirt Launin Ja Ko laps ɗinta bai rufe ba, fararen tsala tsalan cinyoyinta sun bayyana a suffarsu kamar ba'indiya, daga sama Coat ce launin Ja, daga Ciki ƴar vest ce, Hannunta na Hagu na ruƙe da igiyar ƙatuwar backpack ɗin data rataya saman shoulder ɗinta.

yarinyar bata da ƙiba ko misƙala zarratin, sai dai wani abu dake da matuƙar jan hankali ajikinta, shi ne ƙirjinta, duk rashin ƙibarta ƙirjinta a cike suke fam, Boobs ɗinta tamkar zasu fasa rigar jikinta, tana da doguwar fuska, dara daran idanuwanta farare ƙal launin ocean blue, Jar sumar kanta anyi mata kitso guda biyu, bata da yawan gashi sai dai akwai tsayi, wutsiyoyin kitson sun sauko ta side by side na shoulders ɗinta, hancinta hada nose ring golden colour, earrings ɗinta na zallar gold ne, gefen wuyanta zanan tattoo ne na bindin ɗawisu, Launika daban daban, A bunka ga farar fata zanan yayi bala'en yi mata kyau, daga gani yarinyar ƴar gidan wani shege ce, mai ji da Naira, sai dai daga ganin fuskarta, ba ƙaramar wayayya bace, zai yi wuya tayi kunya a ido.

Hankulansu Haris gaba ɗaya yana akanta, Har sai da taƙarasa saukowa daga saman benan, ta ɗan dakata da yin tafiyar tana faman wurwuga manyan idanuwanta akan fuskokinsu, Sauran Sabbin Prisoners ɗin dake a bayanta, Daga Cikinsu akwai wani matashin saurayi dogo twins ne shida ƴar uwarshi, wuyansu na sanye da sarƙar cross wanda ke nuni da addininsu, kyawawan gaske, Launin fatarsu kala ce mai tsada wadda ake kira da Chocolote, yadda kasan ɗan wrestling haka ƙirar Jikinshi take, ga wata irin haɗaɗɗiyar sumar kai, Curly har ta gaban goshin kanshi, Uniform dinsu jajayene, Bayansu Akwai wani Ƙaramin yawo da bazai wuci shekara sha biyu ba, Albino ne (Zabiya) Hatta sumar kanshi Fara ce fat kamar hurhura, daga gani baida cikakken hankali don tunda suka faɗo ɗakin ya ke ta tsalle Yana dariya, Bayan su akwai wata Doguwar budurwa yadda kasan fatalwa, Bata da ƙiba ko kaɗan, sai tsawo tubarkalla kamar qugunta zai karye, duk tsayin Danish To ga wadda ta taka shi, gwanin ban tsoro tana tafiya kamar macijiya, launin wankan tarwaɗa ce ta ɗaure guntuwar sumar kanta da ribbom,

Tashin sense, tsabar ruɗu Ya hana su angel cewa komai sai kallon kallo suke yi a tsakaninsu da sabbin prisoners da aka kawo musu, Aranta tace wannan karan Hada Jinsin Aljanu aka bankaɗo mana, Mun shiga ukun mu, Ashe Zaune bata ƙare ba,

Daga Cikin sabbin prisoners ɗin akwai wata ƴar ƙaramar yarinya da bazata wuci 10 years ba, Komai na jikinta sak irin na azeeza, banbancin shine ita azeeza tana da shekaru, girman jiki ke babu, Ita kuma wannan yarinya ce da gaske, Gata kyakkyawa itama, ga wani ƙato mai manyan kumatu, da mazannai, Namiji ne baƙi wulik, yana tafiya tsokokin Jikin shi na motsawa, hatta ƙirjinshi acike yake kamar na mace, tashin hankali akwai gwarama fa,

a hankali Danish Ya sanya hannayen shi biyu ya sauke azeeza daga saman wuyan shi, Ya ajiye ta ƙasa, Yanayin fuskar kowannan su Ya canza, Lokacin da Sabbin prisoners ɗin suka kammala shigowa ciki Su Goma sha takwas ne, Sanye Cikin Uniform jajaye kalar nasu Parveen, A jere suka tsaya cikin ɗakin kamar masu jiran abasu Umarni, Kallon kallo su ke ta yi a tsakanin su dasu Deeja, Kowa Yasha Jinin Jikin shi, A hankali suka soma Jin takun tafiyar mutun daga can saman stair ɗin, Da sauri Su angel suka kai idanuwansu kan Mai shigowa bakowa bace face*TSOHUWA ZAFREEN*cikin shigarta ta jajayen Kaya Ta rufe ko'ina na Jikinta, Idanuwanta kaɗai ne awaje, Yayin da hannayenta ke a ruke da sandar ta, daga bayanta Giants ne kusan su Uku, Gabza gabza, Masu ƙirar Samudawa, suna ƙarasa saukowa Cikin ɗakin, Da sauri Danish Yace masu Parveen su gaishe ta, Atare suka ɗan russina Cikin girmamawa suke gaishe ta, Wani abun mamaki Mutun ɗaya ce bata russina mata ba, Saboda ƙarfin hali irin na angel hada goya hannayenta saman ƙirjinta, Fuskarta babu annuri, don ta gane cewa itace tsohuwa zafreen, Ba ta yi tsammanin zata ankara da ita ba, Sai ji tayi tace"Ke baki Iya gaisuwa bane"? Cikin ƙarfin hali angel tace"Na iya, Ina kwana,"

Al'ajabi ne ya kama Zafreen, Hankalin Danish kuwa idan yai dubu toh ya tashi, da ido yake yi ma angel magana akan ta duƙa ta gaishe da ita, amma ƴar tahalikar nan sai tayi kamar bata gan shi ba, hada ƙoƙarin ɗaure fuska idonta na kallon ƙasa,

Da kakkausar Murya Tsohuwa zafreen tace"Ki gaishe ni kamar yarda sauran ƴan uwanki suka yi mini" Cikin jin fargaba da ƙarfin hali angel tace"wuya na ke ciwo, bazan Iya russina kai na ba, amma ki gafarce ni"

Tsabar mamaki yasa Idon kowa ya koma kan Angel, Hatta Giants dake a bayan Zafreen Acike suke da al'ajabin maganar Angel, Idan ka kalli fuskarta zaka ga ta ɗaure ta tamau, kuma babu alamun wuyan nata na ciwo, ita kanta amma a firgice take, saboda wani irin mugun tsora da take ji, kuma da gangan taƙi russina mata, Saboda ba ta yi Niyya ba ne, don bata ga dalilin da zaisa ta ƙasƙantar da kanta wurin gaishe da tsohuwa Zafreen ba.

Jinjina kai tsohuwa zafreen tayi babu alamun ta fusata, Sai ma ta miƙa mata hannu don su gaisa, a ruɗe angel ta kalli tafin hannun zafreen dake a sanye cikin jar safa, Wani irin fagaba taji

"am happy to see your face, my granddaughter, Ƙwarin gwiwarki ya burge ni, tun da nake a duniyar nan ban ta6a ganin mahalukin da baya jin shakkar Yi min magana irin ki ba, ga ki ƙarama Kamar insa ƙafa in take" Jin wannan magana yasa angel taji hankalinta ya ɗan kwanta, har ta samun damar ɗaura hannunta acikin na tsohuwa tsaffin, Sosai ta ruƙe hannun angel acikin nata, Kafin daga bisani ta sakar mata hannunta,

Cikin ƙasaita Ta Juya baya ta kalli Giants da ta zo dasu, Da hannu ta yi masu magana ba tare da ta furta musu a baki ba, Yatsu Biyar ta watsa musu sau biyu, Gaba ɗaya su angel suka shiga ruɗani sunyi tsammanin wani mugun abun zata yi musu sakamakon Abunda Angel tayi mata, Amma sai suka Giant Sun Kalli Sabbin prisoners da suka zo dasu, Da hannu Suka nuna mutun biyar na farko da suka fara shigowa, su ka yi musu alamar su tsaya a ɗakin, Sauran Goman Cikin su Da hannu su kayi musu alamar su wuce su tafi, A matuƙar ruɗe Su angel suke kallon su Cike da mamakin Ina za'a kai Mutun Goma da Giants suka ware? kenan an fasa ajiye su a ɗakin su? can kuma ta tuna da maganar da Batool ta ta6a faɗa mata na cewa Akwai wasu 6angarorin da prisoners suke rayuwa a gidan kurkukun basu ka ɗai bane, wata'ƙil can za'a kai su.

A jere mutun Goman nan suka nufi saman Benan zasu koma, Christian ɗin nan Namiji Ya fasa wata irin ƙara da taja hankalinsu, da gudu yabi bayan waɗanda aka tafi dasu, Sai dai bai kai ga ƙarasawa ba, Giants suka Damƙo hannun shi, sosai idanuwanshi suke fitar da hawaye Yayin da yake miƙa hannu yana nuna ƴar uwarshi mace, Yana faɗin"My twin sister pls kada ku raba ni da ita, bazan iya rayuwa babu ita ba, " Fashewa da kuka ƴar uwar tashi ta yi kamar ranta zai fita, da gudu ta dawo ta faɗa jikinshi ta ƙanƙameta, Kamar zai maida ta Cikinsa, wani irin tausayin su ne ya kama su angel, azeeza tuni ta fara yi musu kuka saboda sun yi matuƙar ta6a mata zuciyarta, bayin Allah Kamanninsu sak iri ɗaya, Daga gani suna matuƙar ƙaunar junan su, saboda rashin Imani na Giants suka sa ƙarfi wurin raba su da juna, Su ka tasa ƙeyar macen gaba suka haura saman benan, Sai kuka take tana faɗin"My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka," shima yana kuka yana kiran sunanta, Ahaka har aka fuce da ita" Bayan fitar su ɗakin yai tsit Ya rage Saura Su Angel da tsohuwa Zafreen sai mutun biyar da aka Bar musu cikin sabbin prisoners, Haƙika Tagwayen sunyi matuƙar ta6a Zuciyoyin su, Namijin sai share kwalla yake yi, idanuwanshi sun yi jawur dasu, ga wata irin zufa dake tsastsafo mishi, Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi, An raba shi da twin sister ɗinshi, Giant sun yi yankan ƙauna.

Gyaran murya tsohuwa zafreen ta yi musu kowa Ya shiga natsuwarshi, Cikin harshen turanci ta soma Yi musu magana

"Ina fata tsohuwa Tamira ta yi maku bayanin komai a dangane dani, ba sai na maimaita ba," Har suna haɗa baki wurin ce mata eh,

Jinjina kai tayi Yayin da take kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kafin ta tsaida Tsoffin idanuwanta kan fuskar angel,

"Sai dai ga dukkan alamu akwai waɗanda basu san wacece ni ba, Amma asannu zasu fahimta"

Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kalli Sabbin prisoners da aka Bar musu tace"Ya rage naku, Ku zauna lafiya ko akasin hakan, Bata shafe ni ba, zan dinga zuwa akai akai ina duba ku, A koda yaushe ku kasance Cikin shiri"

A hankali ta soma ja da baya Still idonta akan Angel, Kafin ta ɗauke su tare da juyawa ta nufi stairs ta haye, Giants su ka take musu baya, Suna jiyo datse ƙopar ɗakin, Nan fa kowannan su Ya shiga sauke ajiyar zuciya, don ba ƙaramin shakkarta suke ji ba,

Sai lokacin su Haris suka samu damar yin magana

"Wannan wani irin rashin imani ne? Don me za'a raba shi da ƴar uwarshi? Bayan akwai sauran gadajen da kowannan su zai samu wurin kwana, Ni bansan me ke damun waɗannan mutanan ba, tsabar zalunci ne kawai" Haris ne yae magana yana mai jan tsoki, Azeeza tace ni wlh tausayi suka bani bayin Allah, hakanan an raba su"

Angel ta shiga ruɗani, Ita damuwarta ina za'a kai sauran toh? Ga kuma gadajen su A ajiye, Allah dai yasa ba wani mugun abun za'ayi musu ba, bakowa tafi jima tausayi ba face christian ɗin nan, Ya yi tsaye hawaye ta ko'ina akan fuskarsa.

Danish ne yai ƙoƙarin zuwa wurin shi Ya janyo shi tare da rungume shi yana lallashinsa, Cikin shessheƙar kuka yake faɗa mishi cewa ƴar uwarshi, tun da suka taso atare suke rayuwa komai atare suke yi, basu ta6a rabuwa ba, Amma yau An raba shi da ita," daƙyar Danish ya samu Ya lallashe shi, Har ya daina kukan, Tukunna Ya raba jikin su,

Tun da suka shigo ɗakin Yaron nan da aka bar musu zabiya, Sai tsalle Yake Yi yana dariya, babu wanda ya lura dashi saboda Halin da suka shiga, Ya haye saman gadajensu Yana ta ɗaukar fululluka yana watsar dasu ƙasa Hada bargunansu.

"Hey, y'all! my name is Unaiza, and i'm excited to get to know u all."

Da sauri suka kalli bakin mai magana, wata irin zazzaƙar murya mai cike da kwarkwasa da duniyanci, Bakowa bace face Ƴar madarar nan, da alama taji sunyi tsit basu tarbesu ba, Shiyasa tayi fara yi musu magana, ae daga ganinta wayayyiya ce, Murmushin yaƙe kowannansu ya sakar mata, Batare da sunce komai ba, ta kuma cewa

Readers Also Read