Kenza eBookz

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 76

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 76

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 76: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 76. Ataƙaice, Cikin ƴan kwanakin nan da…

3,331 words

Ataƙaice, Cikin ƴan kwanakin nan da aka dawo masu da batul, Sun samu farin ciki mara misaltuwa, Tamkar an ya ye masu damuwar dake damun so, koda yaushe suna atare da ita, dama batul akwai iya kalami mai ratsa zukata, haka zata zauna tana kwantar masu da hankalinsu, da deeja tare da Angel, waɗannan mutun ukun sun zama tamkar iyaye agare su, yanzu batul ta fara murmurewa, tsawon sati biyu da aka dawo da ita Jikinta yafara dawowa normal, babu ramar nan, hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, har tambayar Angel tayi bayan bata nan an ƙara ɗaukar wani cikin su Hibba, ta sanar da ita cewa ba a ƙara zuwa ɗaukarsu ba, saboda babu wanda ya ƙara yin jinin a cikinsu, Allah ya yaye masu, sun samu salama, har cikin ranta taji daɗin jin hakan, Angel taso ta tambayi batul game da labarin da Gabriel ya bata na yarinyar daya gani tana gudu saman hawa na uku, saboda a suffar da aka dawo da batul yayi dai dai da yarda ya zayyana mata ita, hada guntuwar rigar daya gani a jikinta, Tabar abun a cikin zuciyarta ne, tun da ta nuna bata son maganar.

Har ila yau shiru ba'a dawo dasu Haris ba, Sun zuba ma sarautar Allah ido, addu'a kawai suke binsu da ita, A 6angaren Angel bata ƙara tada zancen dura tagar nan ba, saboda alƙawarin da Danish yace ta ɗaukar mashi akan bazata haurata ba, duk da a lokacin bata amsa mashi ba, sai dai taji ba za ta iya karya mashi alƙawarin ba..........

💔PRISONERS💔

Kwakkwance suke saman gadajensu, suna ta sharar bacci, har safiya ta yi amma basu farka ba, Jiya sun aikatu sosai, sai da suka wanke uniform ɗinsu duka da tsafaffin da sababbin kamar yarda suke yi in zasu wanke su sai su ɗaura bargunansu a jikin su,

Bayan sun kammala wankin su ka shanyasu zuwa lokacin da suka bushe suka mayar da tsoffin a jikinsu, sababbin suka ninninke su acikin akwatinansu, basu huta ba saida suka wanke bargunansu, suka shanyasu saman igiya, bayan sun kammala suka wanke toilets dinsu duka uku, suka bama furennin nan ruwa, Daga bisani, suka dawo cikin ɗakinsu, shima suka gyara shi tsaf tsaf komai Ya koma normal, a lokacin dare yayi suka kwanta don su huta, in the midnight Angel ta tada kowannansu don su yi addu'a kamar yarda suka saba, ga bacci a idonsu da gajiya amma ahaka suka zaune tare da ɗaga hannayensu sama suna kai kukansu wurin Allah, bayan sun kammala ne wani baccin ya ƙara yin awon gaba dasu, Shiyasa har gari ya waye basu tashi ba, saboda basu samu isasshen bacci ba jiya.

Azeeza da Jamimah suna a kwance saman gaɗo ɗaya, sarah tana a kwance ƙasa saman shimfiɗarta, yayin da batul ta ke a kwance saman gadon Danish ita da Angel, ƙudundune cikin bargo, atakure su ke gadon ya yi masu kaɗan ahaka suka kwana, su parveen duk suna asaman nasu gadajensu.

Wata irin zufa ce ta soma wanke fuskarta, ta dinga tsastsafo mata daga jikinta, Yatsun hannayenta da ƙafafuwanta suka soma kakarwa, Mafi yawancin lokaci idan hakan ya faru to mafarki ne ta ke yi acikin baccin ta,

_Ta tsinci kanta acikin wani gini mai girman gaske, mai ɗauke da tagogi babu ƙopa ko ɗaya a jikin shi, tsananin tsoro da firgici ya kamata, ta dinga kuka tana ambaton sunan Allah akan ya kawo mata ɗauki, wasu halittu ne ke fitowa ta jikin bango ɗauke da suffar namun daji, munanan gaske, gaba ɗaya ita suke tunkarowa, gashi babu hanyar da zata gudu daga cikin ginin, fashewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai tana girgiza kanta tamkar zai 6alle, Halittun na dab da ƙarasowa gabanta, Sai ga wata halitta ta faɗo ta saman ginin ɗauke da manyan fuka fuki sai shawagi take yi tana kewaye tsakiyar Ginin, kafin ta karyo kwana ta sanya hannayenta biyu ta ɗauke Angel tayi sama da ita ta fuce daga Cikin Ginin_

A dai dai nan mafarkin nata ya katse, A firgice ta farka daga baccin tana faman zare idanuwanta, hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa, zufa duk ta wanke fuskarta, muryarta na rawa ta soma ambaton

"A'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem" sau uku tana ambatonta.

Bayan ta kammala taji sauki acikin ranta, ta juya ta kalli batul dake ta sharar baccinta, ajiyar zuciya ta sauke tare da zuro ƙafafuwanta ƙasa ta sauko daga saman gadon, zuciyarta acunkushe da tunanin mafarkin da ta yi yau, ta rasa gane me ma'anar mafarkin ke nufi kodai shaidan ne ya haddasa mata yin shi, sai dai tana ji acikin ranta kamar akwai wani abu da ake son nuna mata acikin mafarkin, Taya zata iya fahimtar hakan? Wani ginine ta gani acikin mafarkinta? Babu ƙofa a jikin shi sai dai tagogi, ga wasu halittu na ƙoƙarin kawo mata hari, abun da ya ɗaure mata kai, wannan halittar data 6ullo ta saman ginin dake a datse babu ƙopa, taya akai ta shigo ita? Harta taimake ta kuma ta fitar da ita daga cikin ginin da babu ƙopa a jikin shi?

Ganin tana ƙoƙarin burkita lissafin ƙwaƙwalwarta ne yasa ta dakata da yin tunanin, da sauri ta juya ta nufi toilet don ta yi fitsari, shiga ciki tai tare da jan jam lock ta datse ƙopar, Juyawar da zatayi keda wuya taji gabanta ya faɗi ras! Ba tare da sanin dililin hakan ba, Acikin zuciyarta ta soma ambaton Innalallahi wa'inna ilaihirraji"un"

kusan sau shida har saida taji zuciyarta ta ɗan lafa tukunna ta ƙarasa shiga ciki, Tayi abunda ya kawota, bayan ta kammala kafin ta fita ta ɗan juya ta kalli furennin dake acikin tukunyar, wannan dogon furen daya kere tsayin sauran launin punch pink, ganyayyakin Jikin shi sunyi baƙiƙƙirin dasu, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta koma ta ɗebo ruwa a bucket takai shi bakin tukunyar ta zuƙunna tana goge bakin jikin shi da hannayenta gani take kamar goga mashi baƙin akayi, sai dai koda ta goge babu abunda ya canza har ruwa ta zuba mashi ta wanke shi yaƙi canza launi, miƙewa tayi taje ta ɗauko detergent tsabar hauka hada Soso ta zuƙunna gaban tukunyar ta dinga goge ganyayyakin jikin furen don su koma launinsu na asali, sai dai kash sunƙi komawa, kamar tana ƙara masu baƙi, a ƙarshe data gaji ta maida soson da omon, ta fito daga Cikin toilet ɗin Jikin ta ba ƙwari, hakanan ta dinga jin kamar faɗuwar gabanta yana da nasaba da canzawar launin ganyan furen nan, duk da batasan ran wanene akan shi ba.

A bakin ƙopar toilet ɗin ta jingina bayanta, Idanuwanta acike tab da ƙwalla, daga Cikin ɗakinsu ta soma jin motsin buɗe ƙopa, da farko ta yi tunanin giants ne masu kawo masu abinci, shiyasa taƙi motsawa

kwatsam! Ta soma jin shessheƙar kukan mutun acan cikin ɗakinsu, Da gudun gaske ta faɗo ɗakin a sukwane ta kai idanuwanta kan benan inda take jiyo sautin, Bakowa idanuwanta ke nuna mata ba face Majnoon fuskarshi ta yi jawur da ita, jan tabo ta ko'ina a jikin shi, jini ya kwanta sosai, daga shi sai jan wandonshi a jikin shi babu riga, ya rame sosai, kamar ba mutun ba, hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tana ƙoƙarin motsa la66anta donta kira sunanshi karaf idanuwanta suka sauka akan fararen ƙafafuwan mutumin dake a gefen shi, a matuƙar ruɗe Angel ta shiga bin ƙafafuwan da kallo daga gani macace, koma wacece taji jiki na fitar hayyaci ta jigata sosai, duba da irin yarda jikinta keta kerma babu alamun lafiya atattare da ita, Hannunta ɗaya ruƙe da pant na mata launin Pink colour..........."

💋PRISONERS💋

Muryarta a ruɗe ta ambaci sunan ta,

"UNAIZA"! a yayin da ta ke ƙare mata kallo na ban al'ajabi, kamar fatalwa ta rame ta bushe ta ƙanjame, Irin rigar da aka dawo da batool itace a jikinta launin ja guntuwa wadda da kadan ta zarce mazaunanta ta yi wani irin haske, babban abunda ya tayar ma Angel hankali yakushin akaifar da ta gani akan fuskarta, wuyanta da fuskarta duk sun faffashe ta ko'ina red marks ne, hatta la66anta a fashe su ke sun kumbura, idanuwanta sun ƙanƙance daga gani ba ƙaramin kuka tasha ba, kamar ma bata a cikin hayyacinta, tsananin tashin hankali ne akan fuskar Angel, zuciyarta ba ƙaramin tashi tai ba, ta rasa akan wa zata tsayar da idanuwanta, tsakanin majnun da ya ke yin shessheƙar kuka da kuma Unaiza da ke A tsaye jikinta na kerma, gabanta na faɗuwa ta soma tafiya tana tunkarar su, koda majnoon yai arba da fuskar Angel nan ta ke ya kware baki yana kuka yana ambaton sunanta, da gudun gaske Angel ta nufe shi tunkan ta ƙarasa gaban shi a wani slow ta zube saman gwiwowinta dab da shi ta sanya hannayenta biyu da ke yin kerma ta rungumo shi zuwa jikinta, tsabar tausayin shi da ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske tamkar ranta zai fita, sautin kukanta ne ya karaɗe cikin ɗakin nasu, Wanda silar hakan ya farkar da masu Bacci, A firgice kowan nan su yai wurgi da bargon shi a lokaci ɗaya su ka mimmiƙe zaune saman gadajen su suna faman mutsustsuke idanuwan su da hannayen su, ba zato ba tsammani idanuwan suka sauka akan Angel da ta rungume majnoon a ƙirjin ta, babu wanda Ya lura da Unaizah a cikin su,

Da ƙarfi Deeja ta furta sunan shi"CHINONSO!" ai ko da gudu Suka diddiro daga saman gadajen su Jamimah hada tuntu6e garin yin sauri jin an ambaci sunan abokin wasan ta, Azeeza ta watso da gudu, Gaba ɗayan su ne suka hallara a bakin benen Suna kallon shi, Hankalin su yai mugun tashi Zuciyoyinsu sun karaya, ganin irin tabbunan da ke a saman fatar shi, masu saurin kuka tuni sun fara irin su azeeza, tuni ta zube saman gwiwowinta tana yin kuka.

Hawaye ne kwance a cikin idanuwan su, Batool dake a tsakiyar su tana bin bayan majnoon da ido, tuni ta gane cewa su ne sabbin prisoners ɗin da Angel ta bata labari akan su, waɗanda giants su ka tafi da su.

Muryar deeja a rauna ce ta furta "Inna lillahi wa inna ilayhir raji'un! Mutanan nan basu da Imani, mugaye ne azzalumai, Ku jibi yadda suka canza mishi halittar shi! Bawan Allah dame zai ji! Da ta6in hankalin dake damun shi ko kuwa da lalurar da yake fama da ita? Ga shi ƙarami dashi baisan komai ba, amma a haka su ka yi amfani dashi, Allah kaɗai yasan irin cutarwar da su ka yi mashi, nashiga uku ni yau! Mu kuma haka rayuwar mu zata ƙare a wulaƙance......." wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta wanda ya hanata ƙarasa maganar, Jamimah sai kuka take yi tana faɗin "Wayyo Allah Majnoon ɗina, Waya yayi maka haka? Jikin ka duk jini! Waye ya cutar min da kai"! Tsananin tausayin shi duk ya kamasu, Jikin batool ba ƙaramin sanyi yayi ba, ta duƙar da idanuwanta ƙasa hawaye ne kwance a cikin su, har yanzu babu wanda ya lura da Unaiza acikin su, Angel kaɗaice tasan da zamanta a wurin.

"Wacece wannan?" Ras gaban su Ya faɗi jin muryar batul tana tambaya, kusan atare suka ɗago da idanuwan su suka sauka kan fuskar Unaiza, Muryar su da alamun mamaki suka ambaci sunanta "yar Gidan daddy!" A tsorace suke kallonta, tun daga ƙasa har zuwa sama, girgiza kai Deeja tai muryar ta aruɗe ta furta "I can't believe it! Unaizah ke ce kika koma haka? Ko dai idanuwana ne su ke nuna min ba dai dai ba? Meya same ki har haka? Ina abubuwan ki su ke"?

Maganar da Deeja ta yi ce ta jawo hankalin su zuwa ga kallon ƙirjin Unaiza, Tsabar firgici ne yasa wasu daga cikinsu suka daddafe saitin zuciyoyinsu da tafin hannayen su, hatta Angel da ke a zuƙunne rungume da majnoon sai da ta zabura ta miƙe tana kallon ƙirjin Unaiza dake a shafe kamar Allon bango, babu nono babu alamar shi a wurin, yanayin kallon da su ke bin ta dashi ya nuna tsantsar mamaki da al'ajabi, ruɗani da firgici.

Batul ce ta yi ƙarfin halin cewa bai kamata mu tsaya muna kallonta ba, tana a cikin mawuyacin hali, mu taimaka mata ta shiga ciki" miƙa hannu batul ta yi da niyar ta ruƙo hannun Unaiza, a firgice ta shiga girgiza mata kai, babu wanda yai tsammanin zata iya yin magana duba da irin raunatar da jikinta ya yi.

"Don't let anyone touch me, just leave me alone, I don't want to see any of you, I hate you, saboda kun 6oye min gaskiya, a lokacin dana tambaye ku ina ne nan ba ku faɗa min ba......" A wahalce ta ke yin maganar cikin karyayyar murya,

"Tuntuni naso na faɗa maki gaskiya amma Danish shine ya hanani saboda gudun halin da zaki shiga idan kika ji, Unaiza kada ki ga laifin mu, because we're not the reason you came to this prison! Your father is an evil tyrant who sacrificed you to meet his needs, Unaiza mahaifin ki ya cuce ki baya son ki fiye da yadda baki tunani......" zafafan hawaye ne suka wanke fuskar Angel, Yawu ta haɗiya mai ɗacin gaske, ga dukkan alamu zuciyarta ta gama karaya.

"I can't believe what my heart is telling me, that my father lied to me and brought me here to humiliate my life, ko a mafarki ban ta6a tsammanin hakan ba, saboda yana sona fiye da yadda ya ke son kan shi....." cikin shessheƙar kuka ta yi maganar tana nuna ƙirjin ta da index finger ɗinta, girgiza kanta ta yi hawaye na cigaba da bin fuskarta, ta ɗaura da cewa

"Duk da ba a ƙasa ɗaya muke rayuwa dashi ba, yana bani kulawa, kowace rana sai ya kira ni video call don yaji lafiyata, yasha faɗa min cewa bashi da tamkata a duniyar nan, nifa har ce min yai akaina zai iya 6atawa da kowa har mahaifiyar shi saboda ƙaunar da ya ke yi min, tun da na taso rayuwata ba a ta6a yi min tsawa ba, balle har ta kai ga ata6a lafiyar jikina, nayi rayuwar gatanci, Masu aikin dake kula da ci na da sha na sun fi mutun shidda, abunda nake so shi ake girka min, sannan a baki suke bani abinci, ina da likitocin da ke duba lafiyar jikina wanda mahaifina ne ya ɗauki nauyin yin hakan, Angel ko tari nayi sai an kira Dr ya duba ni, komai na ke so sai daddyna ya yi min shi, I don't ave any financial problems, before nabar gida ina da dala miliyan 2 a cikin account ɗina, wanda shine ya zuba min su don in yi sharholiyata, idan zanyi birthday sai na za6i ƙasar da nake so inje a shirya min party, suturar sanyawata duka babu na ƙasa da dubu ɗari, duk wani abu da kika sani mai tsada na mallake shi, a rayuwata bansan babu ba, bansan menene rashi ba............" dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana jan majina, tun da ta soma magana hawaye basu daina gangarowa saman fuskar Angel ba, idanuwanta sun canza launi sosai, tausayin unaiza ya ta6a zuciyarta, da zuciyoyin su Deeja da ke sauraronta, Azeeza tuni ta ɗauki majnoon ta ɗaura shi saman laps ɗinta ta ƙanƙameshi tana ta lallashin shi ita da jamimah kamar zasu ɗauke mashi ciwon da ke a jikin shi.

"Dan Allah ki daina magana, kina ƙara ma kan ki ciwo, ni tausayi kike bani," idanuwan batul cike tab da ƙwalla ta yi maganar, murmushin takaici Unaiza ta saki tana kallonta,

"Idan banyi magana ba zuciyata zata fashe ne, bakisan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata bane, nagaza yarda da abunda zuciyata ke raya min na cewa mahaifi na ne ya yaudare ni, Shine ya kawo ni nan don a Wulaƙanta rayuwata, Mahaifina fa! Wanda yayi silar zuwana duniya!......." girgiza kai ta ɗan yi fuskarta jawur, tasa harshe ta lashe ƙwallar da ta gangaro ta saman la66anta, duk suna kallonta gwanin ban tausayi.

"Nasan bana jin magana, sannan bani haƙuri indai akan biyan buƙatar kaina ce, amma ban ta6a ganin masifa da bala'i ido da ido ba sai dana tsinci kaina a hannun waɗanda suka fi ni iya shaiɗanci, sun ƙarar min da komai, sun kashe min rayuwata, babu abunda yai saura a jikina, yadda su ka yi treating ɗina ko dabba sai haka, An ci zarafi na an wulaƙanta ni an ƙasƙantar dani kamar karya........." A gigice Angel ta daka mata tsawa wadda ita kanta bata san ta furta ta ba, Ta yi hakan ne saboda gudun kada Unaiza ta furta abunda aka yi mata agaban su Hannah, saboda ta fahimci cewa tana acikin hayyacinta tasan komai da aka yi mata, tunanin ta bai gushe ba, idan kuwa harta buɗe baki ta faɗi ainihin me aka yi mata, zasu fuskanci tashin hankali.

Sosai Ta fashe da kuka Saboda tsawar da Angel ta yi mata, jikin su duk yai sanyi, ta sagar masu da gwiwa, Angel ta yi danasanin tsawar da ta daka mata, ganin yadda take ta yin kuka, ga jikinta da ke ta yin kerma yasa Angel ta miƙa mata hannu, cikin sanyin murya tace

"Am sorry bada son raina na yi maki tsawa ba, ki yi haƙuri ki daina kuka, ki zo mu shiga ciki, na yi maki alƙawarin zan taimaka maki akan duk wani abu da ya dace," hawaye jaga jaga akan fuskar Unaiza da ke kallon Angel, cikin sanyin murya tace "idan kin yi min alƙawarin zaki taimake ni inaso dani da ke mu ke6e, akwai maganar da nake son yi da ke," Jinjina kai Angel tayi alamar gamsuwa da maganar ta, sai da ta fara kallon su Deeja waɗanda ke a tsaye cirko cirko, hawaye sharkaf akan fuskokin su,

"Zan shiga da ita sashen toilet, dan Allah ku kula da majnoon, yana buƙatar ku atare dashi" amsa mata su ka yi da toh, zuciyoyin su duk ba daɗi, ran su yana basu cewar kamar wani mummunan abu zai faru" Deeja ce ta ɗauki majnoon ta nufi cikin ɗakin su, suma sauran suka bi bayanta, ya rage saura Angel da Unaiza.

"Bazan iya tafiya ba, idan zaki iya ki goya ni a bayanki muje" juya wa Angel tayi tare da zuƙunnawa tace mata ta hau, baiwar Allah da ƙyar ta iya hayewa saman bayanta ta ƙanƙameta, Su hanna sai satar kallon su suke yi, Miƙewa Angel tayi ɗauke da ita a bayanta ta nufi sashen toilet da ita, koda suka shiga ciki tace mata ta buɗe toilet tafi so suyi nisa da kowa, bayan Angel ta buɗe toilet ɗin ta shiga ciki da ita, A jikin bango ta sauke unaiza da ke ta faman yin nishi, ta sanya jamlock ta rufe ƙopar kafin ta dawo ta zauna suna fuskantar Juna,

"Pls ki daina zubar da hawayen ki unaiza, kina ƙara karya min zuciyata," runtse idanuwanta tayi sosai, hawaye ne masu ɗumi su ke tsattsafowa daga cikin su, ba tare da ta buɗe idanuwanta ba tace "Angel inaso ki fahimtar dani komai agame da gidan nan, saboda inaso insan dalilin daya sa kika ce mahaifina ne mugu wanda yai silar sadaukar dani, ki bani hujjojin da zasu sa in gamsu da maganarki........." hannu Angel ta ɗaura saman fuskarta tana share mata hawayenta ayayin da ta soma magana cikin tausasa harshe

"Farkon zuwana gidan kurkukun ƙaddarar nan, Sato ni aka yi cikin Mota, a lokacin na gudo daga hannun fulanin daji......" Labari Angel ta fara bata dangane da rayuwarta, tun daga kan haihuwarta da mahaifiyarta tayi ta barta acikin kwamin wanka har zuwa rayuwarta a hannun fulanin Daji, da gudowarta daga wurinsu, da sace ta da aka yi, har izuwa ga rayuwarta cikin gidan kurkukun ƙaddara, tunkan ta ƙarasa bata labarin taga unaiza ta fashe da wani irin kuka na fitar hayyaci, Da sauri Angel ta daddafe kafaɗunta da hannayenta biyu tana lallashinta haɗi da tambayarta me yasa ta kuka?

Daƙyar Unaiza ta sassauta da yin kukun nata, muryarta a raunane take faɗin"Daddyna ya cuce ni! Ya karya min zuciyata! Ya gama da rayuwata......"

Readers Also Read