Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 86
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 86: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 86. Bamu ji maganar shi ba, Muka ƙi…
3,349 words
Bamu ji maganar shi ba, Muka ƙi tafiya saboda mun sanyawa ranmu cewa dole sai dashi zamu gudu, Muna tsaka da ƙoƙarin dawo dashi hayyacin shi don ya tashi mu tafi, Giants ɗin dake kawo mana abinci suka ritsa damu, Nan take kuma mahaifinmu Ya cika, Mu kuma suka tasa ƙeyar mu zuwa can cikin kurkukun, nasan dole an neme mu an kuma yi Addu'oi sosae saidae bawa baya wuce ƙadddarar sa, tun daga wannan lokacin Suka maida Mahaifiyata ma'aikaciyar su ni kuma suka bani horon zama Giant, horo mafi wuya a duniyar nan, Miƙa wuyan da mu ka yi gare su muka zama masu biyayya shiyasa suka yarda damu sosai musamman mahaifiyata tsohuwa tamira, Tabbas mun aikata babban kuskure na bin umarnin matsafa saboda son ɗaukar fansa duk da da farko da suka yi mana tayin aikin ko su kashe mu kin yarda mukai sai daga baya ita Mahaifiyar tawa ta amince saboda a tsarin su ba su yi ma mutun sihiri don ya amince zai yi masu aiki sun fi so da kan ka Amince kana a hayyacin ka, sai daga baya ne ake baka sihirin a koya ma abubuwa, lokacin ba irin ƙoƙarin da ban yi ba wurin nusar da ita kan illar hakan don kuwa sai mun yi ridda amman ta kafe dama kuma tubabba ce, ina ji ina gani mahaifiyata tabar addinin musulunci ta shiga Cikin matsafa sosai saboda taci galaba akan su, a lokacin ta roƙe su kan kar su wulaƙanta gawar Mahaifina su maida ta gida a samu ai masa sutura suka amince don dama ba zatai masu Amfani ba sai ma taja masu matsala, Amma ni an sha daga dani kan in amince naki, k'arshe dai soyayyar uwa ta kwashe ni da kuma nuna man da tayi in muka kawo k'arshen su hakan kaman jahadi ne mukai daga baya sai mu tuba mu rok'i Allah ya yafe mana, da haka na amince saidae ni har yanzu musulmi ne don zuciyata tak'i yarda in bar musulunci sai dai kuma bana sallah gaskiya, Saboda a gidan kurkukun ƙaddara ba'ayin sallah shine abu mafi muni da suka tsana shiyasa a duk lokacin da mutun yai niyyar yin sallah suke burkita mashi lissafin ƙwaƙwalwar shi, Ba don mun so muka kasance Ma'aikatan gidan kurkukun nan ba, kafin mutuwar mahaifina yayi mana addu'a mai ƙarfi akan Allah Kada ya basu nasara akan mu, Ya roƙi Allah da ya bamu ikon Tarwatsa matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddarar nan, Inaji araina cewa Addu'ar mahafina ce take bibiyar Rayuwata shiyasa har yau har gobe hankalina bai ta6a gushewa ba, ina sane da komai, duk wani zalunci da ake aikatawa bana ɗaya daga Cikin masu yi, ban ta6a kisa ba tun bayan da aka horar dani nazama Giant, silar hakan yasa har yau basu bani matsayi mai girma ba amman suna d'aga man sosae sakamakon mahaifiyata da tay mubaya'a gaba daya, Ina matuƙar tausayin rayuwar Danish! ni na fara rayuwa a gidan kurkukun nan na mallaki hankali na, shi kuma tun yana jinjirin shi bana tunanin ko cibi an yanke mashi a haka aka kawo shi nannaɗe cikin Towel, Matsafa sun girgiza da ganin irin kyan da Allah yayi mashi, wlh banji daɗin yadda suke sarrafa rayuwar shi ba, Yaron yana da kaifin basira fiye da tunanin ki, Allah yayi mashi baiwar da zaiyi wuya asamu mai irinta, Yana da saurin haddace abu, he's a gifted sannan Yana da ƙarfi tunkafin su sanya mashi sihiri ajikin shi Danish Yaro ne mai ƙarfin gaske, ko ni nasha jaraba yin dambe dashi a gidan kurkukun nan tun yana da shekara sha biyar yake bamu wahala, Da biyu suke haɗa mu Faɗa dashi, don su jaraba ƙarfin shi, Abun da zai baki mamaki mu tsafi ne ajikin mu, shi kuma babu sihiri a haka yake cin uban mu......" Sosai Angel ta fashe da matsanancin kuka tausayin danish ya kamata, ashe tun yana jariri aka sadaukar dashi agidan kurkukun ƙaddara, maganar da Salsabeel ya gaya mata ta ƙara Sanya mata ƙaunar Danish acikin zuciyar ta, son shi ya ƙara ninkuwa, Ji take kamar tayi fiffike taje inda zata ganshi don ta rungume shi a jikin ta.
"Sauran tambayoyin da kikayi mini bazan iya amsa maki ba saboda babu isasshen lokaci, zasu iya riskar mu, Abu ɗaya da nake so kiyi mini alƙawari shine kiyi ƙoƙarin ganin kinbi duk wasu sharuɗɗa da zan faɗa maki don ku tsira daga Cikin kurkukun nan, Mun ɗaura buri akan ki Unaiserh, saboda ta hanyarki ne kaɗai zaki iya tona asirin matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddara! Muna so duniya tasan da zaman su, A san me ake aikatawa a gidan kurkukun, yin hakan da zakiyi shi zai janyo hankalin mutanan duniya daga nan za'a samu waɗanda zasu Iya kawo masu farmaki, Inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka, Ga dukkan alamu sun gaji da ganin Zaluncin da ake aikatawa agidan kurkukun ƙaddara
Tun tana yin kuka har muryarta ta disashe da ƙyar ta samu ta tsagaita tana kallon shi tace "NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi'iznillahi,
Ajiyar zuciya ya shiga saukewa kafin ya daidaita natsuwar shi yaci gaba da cewa "Silar sabunta ginin da aka yi ƙofar ta 6ace mana, amma muna hasashen tana a cikin ɗaya daga cikin waɗannan makewayin naku guda uku, akwai wata tukunyar fulawa da ke ajiye Cikin toilet ɗinku Mahafiyata ce ta ajiyeta saboda bayan an sabunta ginin shafen dake a ƙasan wurin bai zauna da kyau ba, kuma bakomai ya jawo hakan ba face silar zaman da mahaifina yayi awurin na tsawon kwana biyu yana ibada, to duk wani abu da ke da sihiri idan ya ta6a wurin bazai zauna ba sai ya nuna alama, gudun kada ta manta da ƙofar yasa ta ajiye wannan tukunyar fulawar, Idan kuna so shafen dake akan ƙopar Ya 6a66ako batare da kun sha wahala ba, Ku yi amfani da ruwan zafin da ake kawo maku a matsayin ruwan shan ku, da zarar kun yayyafa shi asaman wurin zai tsastsage daga nan ƙofar zata bayyana, amma fa sai kun yi takatsantsan, kada farin cikin ganin ƙopar yasa ku fasa ihu wanda zai janyo hankalin su........."
Wani irin Farin ciki ne ya lullu6e Angel, Bakinta yaƙi rufuwa
"Kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku zaku tsira, ba abune mai sauƙi ba, dole ku fuskanci tarin ƙalubale wurin ku6uta, musamman Makullin nan ɗaya da baya a cikin ku wato Danish dole ku dawo da shi saboda shi kaɗai ne zai Iya Cire murfin ƙarfen da ke a jikin ƙofar cikin sauƙi ba tare da kun sha wahala ba.
Cikin shessheƙar kuka tace"Taya zamu iya gano Danish har mu iya dawo dashi Cikin hayyacin shi"? bai amsa mata tambayar ta ba, ganin ya miƙe tsaye yasa itama ta miƙe tana kallon shi,
"Akwai ruwan zam zam da mahaifina yake yawo dashi cikin aljihun rigar shi, ya mallake shine a wurin wani hamshaƙin malamin addini wanda ake kira da Shaykh al-ikhlass ɗan ƙasar Madina, shi ya yi mashi kyautar jarkar ruwan zam zam ɗin duk mutumin da ya kur6i ruwan abakin shi ya haɗiya to zaiyi wuya Sihiri yayi tasiri a jikin shi, sannan waraka ne ga kowace irin lalura da izinin ubangiji, Dubarar da mahaifina yayi sai ya dinga ɗibar ruwan xam xam din yana ɗura shi cikin ƙananun robobi, duk in zai fita a cikin aljihun shi yake ɗauka ya tura, saboda tsaro baisan ko Allah zai haɗa shi da mai buƙatar taimakon wata lalura dake damun shi, shiyasa Yake yawo da robobin ruwan cikin aljihun shi, to aranar da matsafa suka farmake mu tsakar dare suka kawo mu kurkukun nan akwai kingin roba ɗaya da ta rage a cikin aljihun jallabiyar shi, Kafin ya rasu ya damƙa ma mahaifiyata ita mun 6oyeta wurin da babu wanda ya sani daga ita sai ni, Robar ruwan zam zam ɗin tana a cikin ɗakinta inda ku ke rayuwa, da zarar kun dafa jikin bangon ƙofar zata buɗe da kanta, Sai ku shiga ku ɗauko ta.
Ke za ki nemo Danish a gidan kurkukun nan saboda ke kaɗaice zaki iya sarrafa tunanin shi amma fa sai kinci baƙar wahala domin kuwa baisan wacece ke ba a yanzu, Har kashe ki zai Iya yi, komai zai iya aikata maki, duk runtsi duk wuya karki bari tsoron shi yasa ki kasa watsa mashi ruwan a cikin bakin shi, ki tabbatar ya haɗiye shi.
Sannan Giant basa jin Bugu, Wuƙa bata iya tsaga jikinsu, haka zalika harsashin bindiga bai iya tsaga fatar su, Mutane ne masu hatsarin gaske, ƙarfin shaiɗanun aljanun da ke a jikin su ya rinjayi halittar su ta ɗan adam, Giant's heart ba irin zuciyar mutun bace, ta shaiɗanin aljani ce, Ko da ace kinyi nasarar sanya mashi ruwan abakin shi zai dawo hayyacin shi na ɗan lokaci ƙanƙani amma duk lokacin da Giant's heart ɗin shi ta motsa zaku ci baƙar wahala, Shiyasa ni ke so ki dage dayi mashi addu'a saboda ku samu ya fitar daku daga Cikin kurkukun nan, In yaso daga baya idan kuka faɗa cikin mutane zan baki Address ɗin gidan mu da mahaifiyata ta rubutamin don in baki, idan ku ka duba zaku iya samun sauran robobin ruwan zamzam na mahaifina daya ajiye a ƙarƙashin gadon shi, da shi zaku dinga yin amfani wurin shawo kan Danish a duk lokacin da Giant's heart ɗinshi ta motsa. Ki kula da rayuwar shi Angel Ki ɗauka cewa amanar Danish na baki, ki ruƙe mini shi hannu bibbiyu, kada ki kuskura ki bari yayi nesa dake, ku kasance atare domin mu samu muyi nasara agidan kurkukun nan, Danish yasan komai fiye da tunanin ki, mun riga shi zuwa kurkukun nan amma yafi mu sanin komai, shi kaɗai yasan hanyar da za'a iya ruguza su, Matsalar shi ɗaya mugun miskili ne kuma yana da taurin kai, zaku ci wahala kafin ku samu Ya baku haɗin kai.........." Yana kai ƙarshen maganar shi da sauri ya zura hannu cikin ajihun baƙin wandon dake ajikin shi ya zaro takardar dake a ninke ya miƙa mata, Address din gidanmu ne dake a Kaduna state, Daga yau ba zaki sake gani na ba, duk wani taimako daya dace inyi maku na riga nayi, yanzu saura ku ya rage ku fara naku, Zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo mana da kyakkyawan sakamako, Sai dai bamu da tabbacin zamu kai lokacin a raye nida mahaifiyata ko kuwa....." bai ƙarasa Maganar ba Angel ta faɗa jikin shi ta rungume shi sosai ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hannayen shi biyu ya ɗaura a saman bayanta ya ƙanƙame ta sosai tamkar ƴar cikin shi, Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna, kafin daga bisani taji kanta ya fara sara mata, nan ta ke idanuwan ta suka lumshe bacci mai nauyi yai awon gaba da ita.........
❤PRISONERS❤
Tsawon lokaci da su Batul su ke ta faman bubbuga ƙofar toilet, Angel tana aciki tana bacci kanta jingine da bango, Salsabeel ne Ya dawo da ita tun da jimawa, tasha uban baccin ta hankalinta akwance yayin da ƴan uwanta su ka shiga matsananciyar damuwa na rashinta.
Ba ta tashi farkawa ba, Sai da dare Ya tsala Lokacin Sun yi nisa acikin baccin su, A hankali ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta, Yayin da la66anta ke ambaton Sunan Allah, Wata irin kasala ta ke ji a jikinta sam babu kuzari, duk yinin yau bata ci abinci ba, Ko ruwa bai gifta maƙoshinta, azababbiyar yunwa ce ta addabe ta, daƙyar ta samu ta yunƙura ta miƙe tsaye Tana ƙarewa toilet ɗin nasu kallo, kamar ranar ta fara ganin shi, Hasken filitar da su ka ajiye acikin shi ce ta gaure ko'ina, Bakomai ne ya faɗo mata acikin ranta ba, Fa ce maganganun da Salsabeel Ya faɗa mata, tamkar a mafarki ta ke tariyo komai da ya faru a tsakanin su, kwokwanto ta soma yi a cikin zuciyarta Anya da gaske ne Haɗuwar su da shi? Gani ta ke yi kamar haduwarta mafarki ce, da sauri ta juya tare da ɗaura kyawawan idanuwanta kan tukunyar fulawar nan da ke ajiye saman floor, Walking slowly ta nufi tukunyar, zuƙunnawa ta yi agabanta idanuwanta akan furen Danish, A tsanake ta ke tariyo duk wani abu da Salsabeel Ya faɗa mata dangane da shi, ba za ta Iya misalta irin ƙaunarshi da ta ke ji ba, Taji takaicin mayar dashi Giant da su ka Yi, zuciyarta ba ƙaramin tafarfasa ta ke yi ba duk in ta tuna cewa yanzu Danish ɗinta Giant ne mai haɗarin gaske, Tayaya zata Iya tunkarar shi? Ba tare da ta samu matsala ba, ' runtse idanuwanta tayi sosai hawaye na cigaba da wanke fuskarta, idanuwanta sun canza launin, ciwon kanta ya tsananta sosai.
"GENIE!" Ras ta ji gabanta Ya faɗi jin muryar Jamimah, A hanzarce ta miƙe tare da sanya tafin hannunta ta share hawayen da ke tsastsafo mata saman kuncin ta, sai da ta fara zuwa gaban Fanfo ta wanke fuskarta sosai, har ta nufi ƙofa zata buɗe sai kuma ta fasa tunawa da Uniform ɗin Jamimah da bata wanke mata ba, kamar yarda tabar su saman Igiyar shanya haka tayi tozali da su, Matsawa tayi gaban Igiyar ta janyo uniform ɗin, kafin ta zame jam lock ɗin da ke a jikin ƙofar, zuciyarta acike fal da tunanin amsar da zata basu idan suka tambayeta Ina taje?
Slowly ta buɗe ƙofar, ba zato ba tsammani ta yi arba da mutun zaune ya jingina bayanshi jigin bangon sashen toilet ɗinsu, gabanta ba ƙaramin faɗuwa ya yi ba, ta ɗan tsorota kafin ta gane wacece, Ashe batul ce bacci ya ɗauke ta a wurin ita da Jamimah sunƙanƙame juna, yadda kasan ƴan gudun hijran da suka rasa wurin kwana, jamimah sai sambatu take yi tana ambaton sunan Genie, da alama bacci ne ya ɗauke su zaune awurin su kaɗai, ta kwanta da tunanin Angel shiyasa ta ke yin sambatun kiran sunanta, murmushi ta saki yayin da take ƙare masu kallo, Har zuwa ta yi gabansu ta zuƙunna tana ƙare masu kallo kamar zata lashe su saboda tsabar ƙaunar da ta ke yi masu, tunawa da Maganar Salsabeel Yasa tayi saurin miƙewa ba tare da ta tayar dasu daga baccin ba, ta nufi cikin ɗakin su, shigarta keda wuya Tayi arba da Su Deeja kwakkwance saman gadajen su, tsit ɗakin sautin minsharinsu Parveen ya cika ko'ina, mamaki ne ƙarara akan fuskarta, wai ashe dare ya yi bata sani ba? a iya sanin ta tsawon mintuna talatin su ka ɗauka suna yin magana da salsabeel, Kenan Baccin ne mai nauyi ya ɗauke ta A jikin shi? Kuma shine ya dawa da ita? Lamarin ya ɗaure mata kai sosai.
Allah ka ɗai yasan irin farin Cikin da ta ke aciki, Sai ta dinga ganin kamar suna a kwance ne saman Gadan daddynta dake a gidansu, Wani irin annuri ne ya bayyana akan fuskarta, kamar wadda aka yiwa albishir Da gidan Aljanna, Ji ta ke yi kamar ta Zuba ruwa ƙasa ta sha, A ƙalla ta ambaci Alhamdulillah ala Kulli Haal Yafi sau aƙirga, Ta gode ma Allah da wannan ranar domin tasan cewa shine silar komai, Allah maji roƙon bayinsa ne ya kar6i koken su Zai kawo masu ƙarshen Zaman Su A GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, Fatan ta Allah yasa Kada su ƙara rasa wani acikin su, tafi so dukansu su tsira atare kamar yarda su ka sha wahala atare, Zuƙunnawa tayi saman gwiwowinta tare da fuskantar gabas ta yi sujud shukr domin nuna godiyarta ga Allah, kafin ta ɗago kanta tuni hawaye sun wanke fuskarta, yau tasha kuka idanuwanta har kumbura sun ɗan yi, bayan ta kammala ta miƙe tsaye
Har zata nufi ɗakin tsohuwa tamira, ta wutsiyar idonta ta hango Haris kwance saman gadonshi, Da sauri ta Kai idonta gare shi, Abun mamaki sai taga Hada Naufal da javed Ga mubeen kwance saman gadonshi, Ga kuma Gabriel kwance ana shi gadon, Azeeza tana agefenshi, Nan bacci ya ɗauke ta, Waro Ido waje tayi bakinta a sake ta ke kallon su, farin Cikinta ya ƙara ninkuwa ɗaya bayan ɗaya ta ke binsu da kallo Agaban gadon haris ta tsaya tana kallon shi, Gwanin ban tausayi, Ya canza mata sosai, Zuƙunnawa tayi gaban gadon shi tsawon mintuna biyar tana bin shi da kallo kafin ta yunƙura ta miƙe ta nufi gadon Javed, bayan ta gama bin su da kallo ta tabbatar da jikinsu da sauƙi, sai taji sanyi aranta.
Ataƙaice daren ranar Angel Ta kashe hasken ɗakin su, Ta koma sashen makewayin su, ta ɗauko Fitila ɗaya, ta kashe haskenta, Cikin duhu ta dinga tafiya tana laluban Hanyar da zata kai ta ɗakin tsohuwa Tamira, cikin sa'a ta samu nasarar shafa jikin bangon da ƙopar ta ke a manne, nan ta ke ta buɗe.
Ajiyar zuciya ta sauke, ba tare da jin shakkar komai ba ta faɗa ciki, bakin ta ɗauke da bismillah, bayan ta shige taja ƙopar ta rufeta, kafin ta kunna Fitilar hannunta haskenta ya gauraye ɗakin sosai tamkar da rana, Mamaki ne ƙarara akan fuskarta, Ganin Gadon ƙarfe da wooden Book shelves Jikin bango, Jerin littattafaine tsoffi da suka daɗe a ajiye cikin shelves ɗin, daga can tsakiyar ɗakin kujeru ne guda biyu, A tsakankanin su madaidaicin teburi ne mai ɗauke da Tea pot da ƴan kofina.
A bun da ya ɗaure mata kai, Kwanakin baya da ta ta6a zuwa ɗakin Ba ta ga gadon ƙarfe da book shelves ɗin ba, sai dai Shufke shufken fulawowi da teburin nan mai ɗauke da teapot, Lallai tsohuwa Tamira ta ƙware wurin Iya Canza ma ɗaki suffar shi Ta hanyar yin amfani da sihirin ta.
Shiga ciki ta yi adai dai gaban teburin ta ɗaura fitilar hannunta, Ba tare da 6ata lokaci ba, ta bazama neman ruwan zam zam, Ko'ina ta shiga dubawa Har ƙarƙashin gado, ba ƙaramar wahala ta sha ba wurin neman shi, ta haɗa uban gumi a kan fuskarta, A ƙarshe ta gano ta a saƙon littattafan da ke a cikin shelf ɗin, (plastic vial) Ƴar Karamar roba kalar wadda ake zuba ruwan allura, wasu kuma suna amfani da ita wurin zuba ruwan turare, farace ƙal duk tsawon shekarun da ta ɗauke ajiye bata canza ba, kana iya hangen ruwan dake acikinta, bai wuci ka yi ma shi kur6a ɗaya ba Ya ƙare, A cikin aljihun wandonta ta zura robar, dama anan ta 6oye takardar adireshin da ya bata na gidan su.
Kafin ta baro Cikin ɗakin sai da ta kashe filitar, Tukunna ta ruƙo handle ɗinta, Cikin duhu ta fito ta nufi toilet dinsu Ta shiga ta ajiye fitilar, bayan ta fito ne, ta samu wuri daga gefen batul ta zauna tare da kai hannu ta janyo jamimah zuwa saman laps ɗinta sosai ta rungumeta a ƙirjinta, A saman kafaɗar batul ta ɗaura kanta, tamkar an wanke mata zuciyarta da ruwan farin ciki, Ba ta runtsa adaren ranar ba, saboda a ƙagare ta ke da gari yawaye, duk don ta samu damar cigaba da gudanar da aikin ta, gaba ɗaya daren idonta biyu ta yi shi, tunanin Danish da ƙofar nan sun tsaya mata aranta, sune abun harinta.
A washe garin ranar da su ka farka daga bacci, ba ƙaramin farin ciki su ka yi ba ganin Angel ɗinsu ta dawo acikinsu, ɗaya bayan ɗaya suka dinga rungumarta a ƙirjin su, haɗi da tambayarta meyasa taƙi buɗe masu ƙopar toilet? Meya faru da ita? Tsawon lokacin da ta shige cikin toilet.