Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 87
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 87: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 87. Angel ta ce masu Bacci ne mai nauyi…
1,017 words
Angel ta ce masu Bacci ne mai nauyi ya ɗauketa, gaba ɗaya sun yarda da maganarta, basu kawo komai aran su ba, Su Haris ba ƙaramin farin ciki su ka yi ba, ganin Angel musamman Gabriel don ba ƙaramin kewarta ya yi ba, jikin nasu babu wadatacciyar lafiya amma da ya ke mazane suna da ƙarfin hali da juriyar 6oye damuwar su, duk don kada su tayarwa ƴan uwansu da hankali, Ita kanta Angel ta lura da yanayin da suke aciki tabbas anyi masu wani mummunan abun da basu son sanar dasu, abunda yasa Angel bata matsa ma su akan su faɗa mata ba, saboda hankalinta ba a kwance ya ke ba, ta ƙwallafa rai akan son aiwatar da alƙawarin da ta ɗaukar wa Salsabeel, in har bata ci nasarar dawo da Danish a cikin su ba, ta kuma gano ƙofar nan to bazata ta6a samun natsuwa ba, ko su Deeja bata sanar dasu ainihin abunda ya faru da ita ba, ta yi hakanne saboda gudun kada murnar da za su yi ta yi silar janyo hankalin giants zuwa gare su, shiyasa ta ɗan jinkirta tana jiran su zo kawo masu abinci, saboda ta ɗauki ruwan zafin da za'a kawo masu, bayan giant ɗin sun tafi, zata ja su zuwa cikin sashen toilet ɗin saita sanar dasu komai, haka ta tsara acikin zuciyarta.
Kamar Giants sun san da shirinta ranar suka ƙi kawo masu Ganye da wuri, Ranta yai mugun 6aci, har sai da ta fara hasashen ko asirin su ya tonu ne shiyasa suka ƙi zuwa kawo masu ganyen, Wuraren marece sai gasu sun shigo ɗauke da farantan ganye da robobin ruwa mai zafin haske, Lamarin ya ɗaure wa su Haris kai ganin An kawo masu ganye amatsayin abincin su, Har tambayarsu Hanna su ka yi meyasa aka canza masu abinci? Nan suka kwashe duk abunda ya faru tsakanin Angel da tsohuwa zafreen suka sanar dasu, Ransu ya 6aci sosai, tsabar tausayin su da su ka ji har ƙwalla sai da su ka zubda masu.
Ko da Giant suka kawo masu ganyen bata bari su hanna sunci ba, duk don saboda Giant su yi saurin tafiya yasa ta kwashe masu ganyen da ke acikin wooden trays ɗin ta zuba su cikin kwandon batul, gaba ɗaya robobin ruwan zafin Angel ta tattarasu duka ta ajiyesu, Ganin sun gama kwashe Ganyen yasa Giants ɗaukar Farantan tare da fucewa daga Cikin ɗakin, kunnuwanta na jiyo mata ƙarar rufe ƙofa ta yi zumbur ta miƙe tare da ɗaukar robobin ruwan guda uku ta nufi sashen toilet ɗinsu Mamaki ya kama su batul ganin ta shiga da robobin ruwa cikin toilet, Hakan yasa suka bi bayanta da sauri don ganin me za ta yi da su.
Bayan sun shisshiga Ciki, tace da Azeeza ta kira su Haris su shigo gaba ɗayan su, da gudu Azeeza taje ta kirasu, bayan sun shigo daga Ciki, taja ƙopa ta datse ta da jamlock.
Atare suka haɗa baki wurin tambayarta"ANGEL WHY KIKA SHIGO TOILET DA BOTTLE WATERS A HANNUNKI? MEYASA KIKA SA AKA KIRA MU GABA ƊAYAN MU".
"BANA SO KUNA YIN MAGANA! KU YI SHIRU KU ZUBA IDO KU GA ABUNDA NAKE SON NUNA MAKU, AMMA KAFIN NAN INASO IN GARGAƊE KU, KOME IDANUWAN KU ZASU GANE MA KU KADA KU KUSKURA KU CE ZAKU YI MAGANA, " Amsa mata su ka yi da toh, zuƙunnawa tayi agaban tukunyar fulawan tare da ajiye robibin ruwan dake a hannunta ƙasa.
"Batul ke da Deeja ku kawar min da tukunyar nan" Da sauri suka sanya hannayensu tare da ɗaga tukunyar suka sauke ta gefe ɗaya.
Buɗe murfin robobin ruwan tayi har tiriri ya ke yi saboda zafin shi, ɗaya bayan ɗaya ta soma ɗaukarsu tana kwarara ruwan jikin bangon da tukunyar ta ke a jingine dashi, wurin yayi shaida saboda da daɗewar tukunyar.
Kowanan su Ya ƙura ido yana kallon ikon Allah, Shin me Angel ta ke son nuna masu ne? Ras gabansu ya faɗi, A matuƙar ruɗe su ka zazzare eyes ɗinsu akan bangon dake tsastsagewa Nan ta ke ginin dutsen da aka yi shafe dashi ya soma 6a66akowa, tamakar an sanya wuƙa an tsargashi haka ya dinga zazzagewa, gaba ɗaya ya rubzo ƙasa, Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu Tsantsar al'ajabi ne ya kamasu, lokacin da tsohon murfin ƙofar ya bayyana a suffar shi, Jikin ƙarfen duk yayi tsatsa.
"Angel menene wannan"? A matuƙar ruɗe suke tambayarta, Ɗagowa tayi tare da kallonsu wani ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarta mai nuni da tsantsar farin Cikin da ta ke a ciki, dimples ɗinta duka biyu sun lotsa sosai, Tunkafin ta motsa la66anta da niyar amsa masu tambayarsu, muryar batul ta katse mata hanzarin ta
"Kamar Ƙofar da mu ke nema"? jinjina masu kai tayi alamar eh ta ƙara da cewa"FINALLY MUN YI NASARAR GANO ƘOFAR DA ZA MU BI MU GUDU DAGA CIKIN KURKUKUN ƘADDARA SAI DAI KASH! BOSS TA ƊAUKE ALƘALAMINTA DOLE MU JIRA TAKUN TSAKIYA DOMIN JIN YADDA ZA TA YI DA RAYUWARMU IN ALLAH YA KAIMU DA RAI DA LAFIYA!"
ALHAMDULILLAH END OF TAKUN FARKO🥳🥳🥳🥳🥳
*Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za'ayi adding naka a paid group kuma za'a sanyaka a comment section, Sa'annan Ba'a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌*
*Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*
*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana*
*3196407426* Bature Hafsat Muhammad First bank
*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*