Kenza eBookz

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 30

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 30

Kurkukun kaddara book 1 Chapter 30: Kurkukun kaddara book 1 Chapter 30. *_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN…

3,298 words

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

Sam bata ji komai ba, daya kwantar da kanshi saman kafadarta, sai taji tamkar ɗan uwanta ne na jini, ƙurawa sumar kanshi ido tayi, doguwa har saman bayan shi, kamar ta sanya hannu ta shafa sumar haka zuciyarta ke raya mata,

'Pls angel open the door for us, mun ƙagara mu ga ɗan uwanmu," muryar hannah ce take yi mata magiya, Hannu tasa ta dafa kafaɗar shi"danish suna son ganin ka, mu koma ɗaki," kusan minti biyar da yin maganar, ya ɗan dago da kan shi, still jikin shi ba kwari kerma yake yi,

Rarrafawa tayi ta ruƙo rigarshi ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ya zurata ajikin shi, Sai da ta taimaka ma shi wurin ruƙo shi tukunna ya samu ya miƙe, a haka suka soma tafiya har suka ƙaraso bakin ƙofar ta buɗe ta fito da shi, gaba ɗaya suka miƙe tsaye zasu rungumo shi,

Da sauri batool ta ware hannayenta wurin kare shi"Jikin shi ba ƙwari, danish yana buƙatar hutu," A jiyar zuciya kowa ya sauke, wuce wa angel ta yi Cikin ɗakin, Su Batool suka Bi bayan su, ya rurruƙeta ji yake kamar zai faɗi ƙasa, wani irin jiri jiri yake gani a Cikin idanuwanshi, a saman gadonshi ta tsaya tare da taimaka mashi ya kwanta sama,

"Sannu danish, Allah ya baka lafiya," batool ce ta yi maganar, su haris ma duk su kayi mashi ya jiki, sam ya kasa amsa masu amma duk yana jinsu,

Sunyi tsaitsaye cirko ciko a gefen da gefen gadonshi, hasken ɗakin ya yi duhu, alamar dare yayi lokacin bacci ne, da sauri Javed yaje gaban table ya kunna masu sauran fitilun, ɗakin yayi haske ya ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ya ajiye ta daga gefen gadon Danish,

Motsin buɗe ƙofa suka jiyo, da sauri kowannan su Ya juyo yana jiran ganin wanene zai 6ullo daga saman benan

Biyu ne daga Cikin Giants dake kawo masu abinci, Abun mamaki ɗaya daga Cikin su hannun shi na ɗauke da wooden tray, samanshi an rufe da jan ƙyalle, da alama kayan abinci ne, ɗayan Giant ɗin kuma Syringe ne a hannun shi, already an zuba ruwan allurar a ciki,

Me ruƙe da syringe ɗin ne ya yi masu nuni da hannunshi su matsa su basu wuri, da sauri suka ja baya, me ruƙe da tray ɗin ya sauke shi ƙasa gefen gadon danish, Kafin ya matsa zuwa saman gadon, wata irin zabura danish ya yi, ya daddafe kanshi yana faɗin baya so kada su matso kusa da shi, ya dinga ambaton sunayen su haris yana faɗin ba zasu taimake shi ba? Suna ganin za'a cutar da shi,

Tsananin tsauyin shi ne ya kama su batool, idanuwan kowannan su ya ciko tab da kwalla,

Ruƙe shi sosai Giant ɗin ya yi, shi kuma ɗayan Ya daddage ya caka mashi allurar a wuyanshi, nan take jikin shi ya saki, ya sulale saman katifar idanuwanshi a rufe,

Sakin shi su ka yi, a tare suka juya cikin takun nan nasu, suka fuce daga cikin ɗakin,

Fitar su keda wuya Su hannah suka yi mashi rumfa suna ambaton Sunanshi, danish danish

Haris yace subar shi ya huta zai ji sauƙi tunda anyi mashi allura,

Angel tace"Wai kun yadda allurar magani ce su kayi ma shi? Meyasa danish yake kuka yana faɗin bayaso sai kace ƙaramin yaro? Kuma har yana faɗin mu taimake shi, u ave to think about it, ni sam ban yarda da waɗannam mutanan ba, Allah kaɗai yasan me su kayi ma shi"

Yatsina fuska deeja tayi cike da jin haushin angel ta soma magana"babu abunda su ka yi ma shi, tun da muke dasu basu ta6a cutar da wani daga cikin mu, koma meye kece kike da alhakin ciwon da.......' Bata kai ƙarshen maganarta ba, sakamakon naushin da angel ta sakar mata a saman fuskarta, tsabar raɗadi yasa Deeja ta dafe kuncinta,

"Ni kika buga"? Harara angel ta jefa mata"kaɗan kika gani, in har kika ci gaba da faɗin cewa ni ce silar da danish yake a wannan halin saina zubar maki da haƙoran gaba, wawuya kawai, don kinga kwanakin nan nayi sanyi shiyasa har kika samu damar gaya mun magana"

Ganin sun harzuƙa yasa javed yin saurin shiga tsakaninsu, cikin sanyin mirya yace" kodan saboda danish, kuyi haƙuri kuyi shiru," jinjina kai deeja ta yi"na ƙyale ki a yanzu, amma wlh saina rama naushin da ki kayi mun" Tsoki angel taja"duk lokacin da kika shirya nima a shirye nake, mai rabon shan duka,"

Daga haka su ka yi shiru, Can Haris ya hango parveen zuƙunne gaban Kayan abincin da aka kawo, sai faman shinshina su take yi, hannu yakai tare da ruƙo wuyan rigarta, ya ɗago da ita tsaye ta maƙe wuya

"Abincin Mara lafiya ne, Kada ma mutun ya sanya rai," harara parveen ta ɗan jafe mashi"Amma ae muna jin yunwa sosai, wannan dama ce a gare mu, kuzo kawai mu zauna muci mu ƙoshi, in yaso sai mu rage mashi kaɗan, bama lallai ya iya cin abincin ba"

Wani kallo Hannah tayi mata" ke fa dama indai kan abinci ne, Ba imani kika cika ba, Kinsan dai sau ɗaya ake kawo mana abinci, wannan kuma da kika ga an kawo na danish ne, ina ma laifin kice idan yaci ya ƙoshi ya rage sai muci kingin"?

Murmushin yaƙe parveen ta saki"Ae naga bacci yake yi, zamuyi ta jiran shi ne har saiya farka yaci ya rage tukunna muci"? ta yi tambayar tana ƙyafƙyafta ido, yadda tayi ba ƙaramin dariya ya basu ba,

Mubeen yace"Ni kaina yunwa nake ji, Don ba yadda zanyi ne Allah," yana rufe baki naufal yace"ae ba kai kaɗai ba, ina ɗazu ɗinnan da muka dinga bugun ƙopa, to anan duka abincin da muka ci ya zube,"

Murmushi haris ya ɗan saki tare da cewa"duk bala'in ku dai bazaku ta6a abincin ɗan uwana ba, har saiya ci ya rage" dariya su kayi gaba ɗayansu, da alama suna farin cikin dawowar ɗan uwansu,

Dare fa ya yi sosai, yakamata kowa yaje ya kwanta, acewar yasmin, juyawa su kayi kowa ya nufi gadonshi, Banda mutun ɗaya Parveen ta yi tsaye agaban gadon danish

Dawowa Haris ya yi tare da kai hannu ya ruƙo wuyan rigarta" muje ki kwanta" bubbuga ƙafa ta yi tare da cewa"Mara lafiya ne fa shi, taya zamu barshi shi kaɗai, Ni inaso Inyi jinyarshi ne",

"Saboda shi kaɗai ne a ɗakin ko"? Ya yi tambayar yana kallonta, shiru tayi tana faman tur6une fuska,

"Oya muje ki kwanta, sarkin wayau" ya ambaci hakan tare da janta, sai da yakai ta har saman gadonta, tukunna shima ya wuce nashi gadon ya kwanta,

Gaba ɗaya sun kasa runtsawa, bakomai suke jira ba, face farfaɗowar Danish,

"Kinyi bacci"? Muryar haris ce, yana daga kwance yayi maganar yana kallon Parveen dake a kwance saman gadon ta dake a kusa da nashi "Taya zan iya bacci da ƙamshin abinci a hanci na," dariya haris yayi,

"Amma Haris baka ganin abincin zai iya lalace wa, tunda shi danish ba'asan lokacin da zai farka ba,"

"Calm down ur mind, tun da ki ka ga sun ajiye abincin nan, sunsan zai farka ne, Giants ne fa Sunsan me suke yi," sun jima suna tattaunawa, da haris before bacci yayi awon gaba da parveen,

Tsakiyar dare lokacin rabi da kwatarsu sunyi bacci, banda mutun ukun, Angel data ɗaurawa kanta alhakin ciwon danish, sai kuma Haris da yake na hannun damarshi, bayan su sai Batool, kowannansu yana kwance sunyi likimo tamkar masu yin bacci,

Ashe zuƙunne bata ƙare ba Kamar daga sama su ka ji danish ya fasa gigitacciyar ƙara mai matuƙar firgitarwa, farfaɗowarshi kenan, ya ta shi da wani sabon Ciwon, a matuƙar gigice angel ta yaye bargonta haris da batool duk suka cire bargunansu, hatta masu bacci sai da suka farka sakamakon Ƙarar danish data karaɗe Cikin ɗakin,

Gaba ɗaya hankalin su yae matuƙar tashi, ganin Danish Zaune saman gadonshi sai ƙara yake saki, ya daddafe kanshi da dukkan hannayenshi, tamkar wanda ake cikin zare ranshi saboda tsabar yarda yake fitar da sautin ƙarar har wani jijjiga muscles ɗin Jikin shi ke yi,

Durowa su ka yi daga saman gadajensu, jikinsu har kerma yake yi wurin tunkarar shi, Haris ne ya hau saman gadon, Javed da Mubeen hada naufal da sauran Ƴan matan duk Suna a tsaitsaye fuskokinsu da alamun ruɗu,

"Danish meya faru? meke damunka? dan Allah kayi mana bayani, " magana suke yi mashi amma sam baya sauraronsu ihu kawai yake yi, shi kaɗai yasan Raɗaɗin da yake ji bawan Allah,

"Bari naje na kira tsohuwa" Acewar Batool, juyawa ta yi da niyar taje ƙopar ɗakin tsohuwa, Angel tayi wuff ta ruƙo hannunta, tsayawa tayi tare da waigo wa ta kalli hannun angel da ta ruƙe ta, suka haɗa ido da juna"Ki jira akwai abunda nake so, in jaraba yi mashi idan bai ji sauƙi ba sai kije ki faɗa mata,". Rai a6ace haris yace"don me zaki hana ta zuwa ta kira ta? So kike mu rasa ɗan uwanmu? Baki ga halin da yake Ciki bane? Yana rufe baki Deeja tace"Da alama so take ta ƙarasa kashe shi, dama ni ban yarda da ita ba, ko me take da shi da zata iya taimakon shi?

angel bata tsaya sauraronsu ba. Kota kansu bata bi ba, batool ta kuma kallo tare da cewa"Ku bani dama," jinjina kai batool ta yi tare da kallon su haris tace"Tun da ta nemi alfarma, mu barta ta jaraba, amma kuma komai ya biyo baya, ke kija tun da kin hana a kira tsohuwa" gyaɗa kai angel ta yi, tare da matsawa ta haye saman gadon danish, ya kakkame Jikinshi sai kerma yake yi, yana sakin ihu ga zufa duk ta wanke jikin shi, duk da weather ɗin prison mai sanyi ce,

Miƙa hannu ta yi da niyar ta ruƙo shi, Ya buge hannun nata alamar baiso, duk yabi ya birkice masu,

Ganin yaƙi bata damar ruƙe shi yasa haris jan dogon tsoki tare da cewa"U just wanna waste our time, pls batool go and call her" tafiya batool ta soma yi ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa,

Rufe ido angel tayi, Cikin sanyin murya mai tattare da natsuwa da cikar kamala, ta soma raira qira'ar karatun alqur'ani mai girma,

Gaba ɗaya suka bita da kallo, sam basu san me take karantawa ba, amma tunda suke basu ta6a jin sautin abu mai daɗi ba, irin wanda angel take Rairawa ba, hatta batool dake ƙokarin kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa, tana fara jiyo sautin karatun da angel keyi nan take ta dakata, tamkar an dasa mata aya, da matuƙar mamaki ta juyo tana kallon inda suke.

Bakomai yafi ɗaure masu kai ba, Fa ce yadda danish ya yi shiru, yadaina ihun da yake yi, kuma jikin shi ya daina yin kerma,

A hankali angel ta buɗe idanuwanta, ta ɗaurasu akan fuskar Danish still bai buɗe idanuwanshi ba, matasawa ta ƙarayi kusa dashi sosai, ta sanya hannayenta biyu tare da ruƙo doguwar sumar kanshi, ta tattare ta zuwa bayanshi, moving lips ɗinta ta yi xuwa saitin kunnanshi na dama, sosai taci gaba da raira mashi karatun har cikin kanshi yake jin wani irin baƙon yanayi mara misaltuwa, zuciyarshi tayi sanyi, kasala ta baibaye shi, , Haƙiƙa Angel tabar ƴan kallo, Su haris sun saki baki kamar lehen sakarai sai kallonta suke yi, ta kawo masu wani baƙon abu da basu ta6a ji ba,

He slowly wrapped his arms around her waist and squeezed her tightly tamkar zai shige cikinta, sai faman nishi yake yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri, tana jin zafin jikin shi sosai ajikin nata, saboda matsewar da suka yi ajikin juna, tana jin yadda heart ɗinsa ke beating very fast, ƙasa ƙasa da murya yake furta mata, kada tadaina, taci gaba yi mashi yana samun sauƙi," kamar yadda ya buƙata haka taci gaba dayi mashi karatun, har sai da taji tempreture ɗin jikin shi ya dawo normal, numfashinsa da natsuwarshi sun daidaita tukunna ta dakata da yi mashi karatun acikin kunnuwanshi, zame jikinta ta yi daga nashi, tare da sanya hannayenta ta dafa shoulders ɗinshi, eyes ɗinta na kallon Fuskarshi, idanuwanshi tamkar na mashayin giya,

"Danish can u see my face" tayi maganar tana nuna mashi fuskarta, jinjina mata kai yayi alamar eh, ɗagowa ta yi tare da kallon su Haris dake a tsaitaye, Yadda kasan ƙerarrun gumaka, tsabar mamaki yasa sun kasa rufe bakunansu, Kowa zuciyarshi acike take fal da tunanin menene angel ta karantawa ɗan uwansu danish harya dawo cikin hayyacin shi,

"Angel kinyi matuƙar bamu mamaki" batool ce tayi maganar a lokacin ta dawo inda suke.

"Duk da bamusan menene kika karanta ma danish a kunnanshi ba, amma nayi matuƙar jin wani irin sanyi da daɗi acikin zuciyata, sai naji dama baki daina ba, kin cigaba da yi,"

Batool nakai ƙarshen maganarta, Javed yace"Nikaina naji wani irin daɗi mara misaltuwa, nayi mamaki kuma ganin yadda danish ya samu natsuwa yadaina haukan da yake yi," yakai ƙarshen maganar idonshi akan danish,

Hanna tace"i feel the same, zanso nasan menene angel kika karanta mashi me daɗi," tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,

"Zanyi maku bayani, amma yanzu danish yana buƙatar kulawarmu," tayi maganar tana kallonsu,

Haris dai yayi shiru shi da deeja kowa na tofa albarkacin bakinsa kan irin dadin da suka ji amma banda su, saboda tsabar kunyar da suka ji,

"Ga abincinsa kar ya lalace, aba shi yaci" parveen ce tayi maganar, tare da rankwafawa ta ɗauko tray din ta miƙa ma Angel, hannu biyu angel tasa ta ruƙe handle ɗin tray ɗin a tsakiyarsu ta sanya tray din, ta cire jan ƙyallen, waro ido parveen tayi ganin Roasted Chicken guda ɗaya sai maiƙo take yi ga wani irin ƙamshi, gefe kuma Milk ce a cikin bottle me sanyi, sai wooden bowl mai ɗauke da Fruits salad,'

"Zaka iya ci"? Ta yi tambayar tana kallon danish, wata irin narkakkiyar zufa ta gani tana gangarowa ta cikin yalwatacciyar suman kanshi, bai iya bata amsa ba, sai dai kallon ta da yake yi,

Sai lokacin harisun tsohuwa ya samu damar buɗe baki yace"Bari na taimaka ma shi ya watsa ruwa ajikin shi," yakai ƙarshen maganar, Tare da ruƙo danish, Javed ya taimaka shi suka yi mashi jagora zuwa Cikin toilet ɗinsu,

Bayan tafiyarsu batool ta kalli sauran ƴan uwan nasu"tun da jikin nashi da sauƙi, ku je ku kwanta," Yadda kasan ƴan gudun hijra haka suka tafi sharaf sharaf kowa Ya hau saman gadonshi Ya kwanta,

Ganin parveen taƙi tafiya yasa tace"ke fa" Hannu tasa tana ɗan sosa keyarta "Jira nake Su haris su dawo da danish yaci abincin shi, idan ya rage nima in samu in ɗan ci....." wani kallon rainin wayau batool tayi mata wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar,

"Sai kace kinfi kowa Jin yunwa, Allah yasa idan ya fito ya cinye abincin duka sai muga ya za ki yi" angel dake zaune saman gadon danish ta yi zurfi Cikin tunaninta, bakomai ya ɗaure mata kai ba, face yadda ta iya yin karatun qur'ani tiryan tiryan tun zuwanta gidan kurkukun tasha Yin attempting karatun qur'ani tana gazawa, sai ta dinga jin raɗaɗi a maƙoshinta, A yau dai kamar umarni aka bata tayi karatun haka tadinga ji, Kuma taji kwarin guiwar yin qira'ar, kenan nan gaba zata Iya samun damar yin ibada, mamaki take yi ya akai take samun nasara akan wasu abubuwan? Tabbas Allah yana atare da ita saboda kyakkyawar niyar dake gareta, kuma tana ji aranta cewa Akwai masu yi mata addu'a, fatanta Allah yasa dadynta idan yana araye ya kasance ɗaya daga Cikin masu Yi mata addu'a, Saboda ita addu'ar Iyaye kar6a66iyace akan ƴa'ƴansu kamar yadda hadisa ya tabbatar da hakan,

Shigowarsu haris Cikin ɗakin ne ya katse mata zancen zucin nata, ta ɗago tana kallonsu, Hannayensu ruƙe dana danish, jikin shi duk lemar ruwa, Hada sumar kanshi suka wanke mashi, duk ta manne mashi saman fatar wuyanshi, Lokacin da suka ƙaraso, Saman gadon ya haye ya ɗan kishingiɗa kan shi saman pillow, jikin shi duk ya saki babu ƙwari, idanuwanshi na a lumshe,

"Abincin fa"? Angel ce tayi ma shi maganar, slowly ya dan buɗe idonshi akan fuskarta, in a throaty voice ya furta mata"I can't eat anything now, u can share it," voice ɗinshi yayi low sosai, daƙyar ta iya jin me yake cewa,'

Cikin rashin jin ɗaɗin maganar shi haris yace"Ko madarar ce ka ɗaure ka sha, nasan kana jin yunwa," girgiza ma shi kai ya yi"bazan iya ba, kada ku damu kanku am ok,"

Babu wanda yaji daɗi Acikinsu, Sun so koda milk ɗin ce yasha, amma ya nuna masu cewa babu yunwa attare dashi, Su parveen abun nema ya samu, zama su kayi a kasa Kowa Ya shiga kai hannu yana yagar naman kazar yana Ci, Komai saida suka Bi suka lamushe, bayan sun kammala, Haris Ya zauna gefen gadon Danish, sauran suka wuce saman beds ɗinsu suka kwanta, Angel ma tuni ta koma nata gadon, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba, danish ya dawo Cikin su, sai da dare ya nutsa, tukunna haris yabar gefen gadon danish ya koma nashi gadon ya kwanta,

Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan ta juya ta saci kallon shimfiɗarshi, yayi bacci ko baiyi bacci ba?, kasa jurewa tayi a hankali ta dan mirgina ta juya ta 6angaren da yake fuskanta, bayan shi kaɗai take iya gani, jikinshi na lulu6e da bargon da haris ya rufa mashi har zuwa kafaɗarshi,

Chapter notes and social links

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull