Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 11

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 11

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 11: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 11. "Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana…

3,240 words

"Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana iya gani da kyau, Naufal wai Ba mai ji na ne"? Shiru taji babu motsin mutun a kusa da ita, Jikinta yai mata tsami, ko yatsanta ta gaza motsawa, ga dukkan alamu dannau ne ya danneta, kware muryar tayi da ƙarfi ta furta Sunan Danish! Har cikin dodon kunnan shi ya ji sautin muryarta, slowly ya ɗan ware kyawawan idanuwanshi akan fuskarta, bargon da ya lullu6a mata a iya ƙirjinta ya tsaya hakan ya bashi damar kallon ta da kyau, duk da jinin da matsafa su ka yi mata wanka dashi ya koma mata tamkar fenti tayi muni sosai, cikin sanyin murya ya furta sunanta"My Angel" jin muryarshi yasa ta dakatawa da yin sambatun nata, ƙoƙari take wurin ganin ta motsa jikinta don ta samu damar zuwa gare shi, fahimtar hakan yasa shi matsawa dab da ita, kwanto da fuskarsa yai saitin fuskarta yai mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, numfashinsu har yana kokawa dana juna, kaɗan ta ke iya ganin fuskarshi, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, muryarta na ɗan rawa ta furta sunanshi"Da..Nish" fatanta Allah yasa ba mafarki bane.

Dogayen yatsun hannun shi ya ɗaura a gefen fuskarta ya shafa a hankali da sauri ta ɗaura nata hannun saman nashi dake akan face ɗinta, Sai yanzu ta samu damar motsa jikinta, zafafan hawaye ne su ka soma wanke mata fuskarta, Ɗago da ita yai zuwa saman ƙirjinshi Ya kwantar da ita, duka yatsun hannayen shi na acikin sumar kanta, sosai ya ƙanƙameta, yanayin yadda su ka rungume junansu zai tabbatar maka da irin kewar juna da su ka yi, ba ka jin komai sai sautin nunfashinsu, da bugun zuciyarsu dake harbawa da sauri da sauri,

"I can't explain how much I miss you. I'm sorry for what happened, it's all my fault. I'm sorry, Angel."

Cikin rauni na murya yai maganar, Cikin shessheƙar kuka ta soma yi mashi magana"ba laifinka bane Danish, ka daina faɗin hakan, ni abunda yafi damuna rashin ƴan uwan mu da suka rasu, na yi takaici Danish, ban cika masu alƙawarin da na ɗaukar masu ba, Jemimah da Azeeza sunci burin fita daga kurkuku don suje gidan daddyna, haka parveen burinta ta ci abincin gidan daddyna, baiwar Allah deejah ga sauran ƴan uwan mu da mu ka rasa" daƙyar ta ƙarasa maganar, zafin jikin su duk ya ɗumamasu, Yanayin weather ɗin dajin San yi sosai, daga inda suke suna iya jiyo sautin kukan Namun dawa.

Ɗaura tsinin hancinsa yai saman sumar kanta, shi kaɗai yasan raɗaɗin da ya ke ji acikin zuciyarshi, Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi ta ɗaura eye balls ɗinta akan fuskarshi, bacci ne bai ishe shi ba, sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, a tsanake su ke ƙarewa juna kallo tsawon mintuna goma sha biyar, '

"Bana so su Gabriel su farka su taras da gawawwakin su azeeza, abun zai ƙara ta6a zuciyarsu, ka taimaka min Danish mu binne su kafin farkawarsu," shiru bai tanka mata ba sai kallon ta ya ke yi kamar yau ya fara ganinta

"Danish! Am talking to u, bana jin daɗin jikina, maganar ma daƙyar nake iya furtata" Still bai motsa la66ansa ba' ta rasa meyasa ya ke kallonta yana lumshe ido Ya ƙi tanka mata," Gyaɗa kai tai"shikenan tun da bazaka taimaka min ba, Ni zan je na rufe su" tana ƙoƙarin miƙewa sexy voice ɗin shi ta ratsa kunnuwanta"Kin ta6a ganin an binne mutun da ranshi"!! ras taji gabanta ya faɗi a matuƙar ruɗe ta zazzaro idanuwanta waje tana kallon shi........

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E7🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

"ka na nufin ba su mutu ba suna a raye"? A ƙagare ta jefa mashi tambayar, jinjina mata kai yai ba tare da ya furta mata kalma ba, bugun zuciyarta ne ya qaru a sukwane ta juya baya don ta samu damar ƙare masu kallo, bargunan da ya lullu6e su da shi ya hana ta gan su da kyau, jikinta na 6ari ta ƙara sa gaban su ta zuƙunna tare da kai hannu ta ɗage saman bargon, duk wani motsin ta akan idon Danish.

Wani irin farin ciki ne Ya lullu6eta haƙiƙa ta yi al'ajabin wannan iko na Allah, kamar zautacciya haka ta dinga ɗaura kanta saman ƙirjinsu haɗi da jogana kunnanta saitin zuciyar su don ta ji idan tana bugawa, daga kan Jamimah ta fara tana ɗosa kunnanta bugun zuciyar jemimah ya daki dodon kunnan, nan ta ke ta fahimci cewa bacci su ke yi, Tambayoyi ta shiga jefawa kanta, Ta ya ya akai haka ta faru? Dama wanda ya mutu yana tashi? don ita dai a iya saninta idan an mutun ba adawowa, ɗaura kunnanta ta yi saman ƙirjin Azeeza lumshe idanuwanta ta yi wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, jin bugun zuciyar azeeza na har6awa, matsawa ta yi gaban Parveen tunkan ta ɗaura kanta saman ƙirjinta idanuwanta su ka sauka akan ƙaramin bakinta ganin yana motsi yasa ta fahimci tana araye, Lamarin yai matuƙar ɗaure mata kai, ta ya akai su ka rayu! Kuma Danish da kanshi ya tabbatar masu cewa Heart attack ne yai silar mutuwarsu, duk da bata da ƙoshin lafiya hakan bai hana smart brain ɗinta aiki ba, Zurfin tunani ta shiga idan har su Jemaimah su ka iya jure abunda ya faru dasu ya kenan ta 6angaren Sauran ƴan uwansu da su ka baro? Waro idanuwanta waje ta yi yayin da zuciyarta ka harbawa da sauri da sauri, a fujajen ta zabura ta miƙe kamar an zungure ta, ta juya ta nufi Danish dake a zaune Ya ɗan lumshe idanuwanshi, ƙoƙari ya ke ya hana kanshi yin bacci gudun kada yaja masu matsala, zuƙunnawa tai agabanshi

"Danish taya akai su Jamima su ka rayu? Bayan kai da kanka ne ka faɗa mana cewa zuciyarsu ce ta buga" ware idanuwanshi yai akan fuskarta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, damuwarta akan ƴan uwanta, bata damu da kanta ba, ƙarantar shekarunta yafi komai ɗaure mashi kai, yadda harta iya jure waɗannan wahalhalun rayuwar wanda yayi imanin ko wani babban ba zai Iya jurarsu ba.

"Danish bana so ina magana kana share ni, ka faɗa min ta ya ya akai su ka rayu? A iya sanina idan mutun ya mutu baya tashi, Sai gashi su Azeeza sun tashi, ko dai ka yi amfani da sihirinka ne wurin dawo masu da rayuwarsu..."? A ruɗe tai maganar babu kwanciyar hankali atattare da ita, a hankali ya ɗan motsa la66ansa.

"My Angel, u should stop talking about them, ba ki da lafiya u need a rest," damƙar wuyar best ɗin jikin tai sosai ta fashe mashi da kuka tana faɗin"Danish ka faɗa min dama kasan suna araye shi ne ba ka bari mun goyo su Deeja mun taho da su ba? Me yasa ka yi mana ƙaryar cewa zuciyarsu ce ta buga"? Tana magana tana ku ka, raunin gefen bakin ta tuni ya fara tsastsafo da jini.

Ranta yai mugun 6aci zuciyarta ta harzuƙa, A haukace ta miƙe tana faɗin"Zan koma na taho da su Deeeja, ban damu da in rasa raina ba," a hanzarce ya miƙe jin abunda tace, ido cikin ido su ke kallon juna"Am sorry Angel i don't mean to hurt u, kinsan bana ƙarya, sannan bani da amsar da zan baki that's why nayi shiru, hatta su Azeeza ban san suna araye ba, a daren jiya na yi ƙoƙarin binne su cos bana son ku farka ku taras da gawawwakinsu, hakan zai fama ma ku ciwon da ke a cikin zuciyarku, nayi amfani da sihirina wurin tsaga ƙasa har na fara sanyasu a ciki idona ya sauka akan yatsun ƙafafuwansu dake motsi, i was shocked cos ban yi expecting din zasu rayu ba, kin ji yadda akai nasan suna a raye"

kamar ta so ta fahimce shi sai dai wani sashe na zuciyarta yaƙi aminta dashi, girgiza mashi kai tai"Ni dai zan koma kurkuku in ɗauko su Deeja, Saboda ina ji araina cewa Suna araye"

Ya fahimci damuwace ke ƙoƙarin zautar da ita, Zaiyi wuya ta fahince shi, yasan halin kayansa da rigima ga kafiya da taurin kai, juyawa ta yi tare da nufar ƙofar fita daga kogon dutsen, da sauri Ya bi bayanta tare da ruƙo arm ɗinta ya janyota zuwa jikinshi, sosai ya matseta.

"Angel daji ne fa, ba mu a kusa da kurkukun ƙaddara, ta zarar awanni ce, A daren Jiya bayan mun fita ni ne na ɗauko ku na dawo da ku nan duk don na sauƙaƙa maku wahala" daƙyar ya ke magana, damuwace ƙarara akan fuskarsa, ƙoƙarin raba Jikinta tayi daga nashi.

Zuciyarta ce ke azalzalarta sam bata fahimtar kalamansa, idanuwanta sun makance

"Ka sake ni Danish, nasan ko nace kaje ka ɗauko min su Deeja ba za ka je ba, don haka ni zanje, saboda ina ji araina ƴan uwana suna araye basu mutu ba gashi mun baro su a hannun Azzaluman mutanancan....." cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar, duk yadda yaso ya hanata tafiya taƙiya, har kwatanta mata haɗarin da dajin gare shi amma ta kafe akan sai taje, sakinta yai idon shi akan bayanta, sam babu kuzari a jikinta ahaka ta fuce daga cikin kogon dutsen, Hasken ranane ya galle mata idonta da sauri ta lumshe su na ɗan sakanni kafin ta ware su tana ƙarewa ƙurmin Dajin kallo, Daddaɗar iskar dajin ce ta ratsa sassan jikinta ni'imtacciyar gaske, hatta sumar kanta sai kaɗawa take yi saboda ƙarfin iskar, saboda taurin kai irin na Angel da kasada, Ahaka ta soma tafiya tana nufar cikin dajin ita ala dole saita gano inda kurkukun ƙaddara ya ke, tun kan aje ko'ina ta fara tsorata da ganin ƙananun halittun da ke yawo Saman bishiyoyi, duk da haka bata sare ba taci gaba da tafiya hada ɗan saurinta da gudunta, ko takalma babu a ƙafarta.

Tun bayan fitarta Danish Ya fito daga cikin kogon dutsen, ya goya hannayenshi saman faffaɗan ƙirjinshi Yana kallon bayanta, Ta yi matuƙar bashi mamaki, duk da ya fahimci babu hankali atattare da ita, in ba haka ba ta ya ya wanda ya tsira yake ƙoƙarin komawa ga halaka. Yarinta ce ke damunta da kuma son ƴan uwanta.

Tana cikin yin tafiyar nan, kukan namun dawa Ya dakatar da ita cak ta tsaya tana ƙarewa wurin da take atsaye kallo, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Snake ɗin dake bin jikin bishiya yana ƙoƙarin saukowa ƙasa, zaro ido waje tai a gigice ta fasa ƙara tare da juyawa da gudun gaske tamkar zata tashi sama, majicin na ƙarasa saukowa yabi bayanta, tashin hankali duk ta bi ta rikice don ta fahimci ita yake bi, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a yin tozali da maciji ido da ido ba sai yau da Allah ya haɗosu, Tarasa gane ta wace hanya zata bi ta koma cikin kogon dutsen.

Danish ta dinga ƙwalawa kira kamar maƙoshinta zai 6allo, sai da ta gama galabaita cikin rashin sa'a tai tuntu6e da dutse gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa, ƙiris ya rage ta kife ƙasa a lokacin da ba ta yi tsammani ba taji Ya damƙo ta tare da kwantar da ita saman chest ɗinsa.

ƙanƙameshi tayi sosai ta fashe mashi da kuka tana zazzaga mashi masifa akan me zai barta ita kaɗai acikin daji? Idan ma don saboda ta yi mashi kafiya ne, bai ga ita yarinya bace, tun da fara mashi faɗa bai tanka mata ba, hannayen shi biyu suna tallabe da ita, sai da ta yi mai isarta, tukunna ta buɗe kumburarrun idanuwanta akan fuskarshi, tun daga kan tausasan red lips ɗinsa ta soma bi da kallo har izuwa ga dogon hancin sa kafin ta ɗauke idon nata ta ɗaura su kan sexy eyes ɗinshi masu matuƙar jan hankali.

ƙoƙarin shagala su ke yi da kallon Juna, tunawa da ƴan uwansu da su ka baro a kogon dutse ne yasa tayi saurin katse masu kallon ƙurullan da suke bin juna dashi"Danish mu koma kada wani abu ya same su" girgiza mata kai yai in a smoky voice ya furta mata"ba abunda zai same su, ina sane dasu, na rufe kogon dutsen babu wani abun cutarwa da zai Iya tunkarar su"Sam hankalin bai kwanta da kalaman shi ba

"Danish ni dai mu koma," ashagwa6e tayi mashi maganar, ita kanta batasan ta sanya shagwa6a ba'

"Zamu koma, but before that, Inaso ki raka ni cikin Dajin in nemo mana abunda zamu ci, ko kina so su farka suna Jin yunwa ne"?

Girgiza mashi kai tayi"a'a amma ni ba zan bi ka ba, Ka maida ni cikin kogon dutsen in ya so kai sai ka je nema mana abunda zamuci" kafe ta da ido yai, hakan yasa ta jefa mashi harara haɗi da murguɗa mashi baki, munin fuskarta bai hana shi ganin kyanta ba, musamman da ta yi mashi abunda ke jan hankalin shi gareta, Harara da murguɗe abun A jinin ta ya ke.

"Idan ba za ki bi ni ba, Ga hanya nan ki koma kogon dutsen ni kin ga tafiyana" yai maganar tare da nufar Cikin dajin, da ido tabi bayanshi da kallo, ranta a 6ace yasan ba zata iya kai kanta ba shiyasa yace ta koma, Tunawa da macijin da ya biyota ne yasa ta zabura da gudu tabi bayanshi, Yana cikin tafiya yaji ta zura hannunta cikin nashi, ƙayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi.

Ta yi tsammanin Iya abincin da zasu ci ne zasu nemo, ba ta san plan Ya shirya mata ba, Yanayin Iskar dajin ba ƙaramin ni'ima ta saukar masu ba, Suna tafiya suna kallon Juna, wani irin Sanyi ne ke ratsa zukatan su, dakatawa tai dayin tafiyar ta ɗan kalli fuskarshi"Na gaji Danish ƙafata ciwo ta ke yi min" ba tare da ya amsa mata ba, ya juya mata bayan shi, ta gane me yake nufi, da sauri ta haye Saman bayan Ya miƙe ɗauke da ita, ba ƙaramin daɗi taji ba, shin me yafi ranta gata ga garkuwar kurkuku, ta ƙanƙameshi sosai, lumshe idanuwanta tayi sai faman shaƙar mashi fatar wuyan shi take yi, bai sauke ta a ko'ina ba sai abakin wani tabkeken ruwa mai gudana, Ta jikin dutse ruwan ya ke gangarowa tsaftatacce fari ƙal dashi.

"Mun ƙaraso," Jin abunda yace ne yasa ta ɗago da kanta, tana ƙarewa wurin kallo, nan ta ke ta ji tana sha'awar shan ruwan, Zuƙunnawa yai ta sauko daga saman bayan nashi, a jere suka tsaya suna bin ruwan da kallo, ga dukkan alamu ya burgesu .

"Danish ƙishi na ke ji, nasan kaima kana ji, mu sha sai mu ɗebi wani mu kai ma su Parveen ko"? Ba tare da ya juyo ya kalli fuskarta ba ya soma magana"Wanka nake so nayi maki, saboda kinyi muni, jikin ki yayi datti"

Har saida gabanta ya faɗi jin abunda yace, juyowa yai da fuskarshi ya kalleta tare da kashe mata ido ɗaya

"za ki iya cire kayan ko in taimaka maki ne"? gabanta ne ya dinga faɗuwa sai ta ga kamar ya canza mata, babu alamun wasa akan fuskar shi yai maganar.

Ganin yana matsowa kusa da ita, yasa ta juya da niyar ta gudu, ko ta ku ɗaya bata kai ga yi ba taji Ya damƙi ƙugunta, ƙarfi ba ɗaya ba, Duk yadda taso ta kubce mashi ta kasa, matseta yai a ƙirjin shi, A hankali Yai amfani da hannun shi ɗaya wurin zame rigar Jikin shi, tare da wandon kakinsa na Giant, ya rage daga shi sai short fari, saman gungurumeman dutsen dake agefen ruwan, ya jefar da uniform ɗinshi.

kamar jinjira haka ya ɗauke ta, kaitsaye Ya nufi Cikin ruwan da ke gangarowa, ba yadda ta iya dashi, Tana kuka tana fadin bataso ya ƙyale ya rabu da ita, ahaka yayi mata wanka tass ya wanketa Kamar yayi amfani da sabulu ita kanta tayi mamikin yadda Jinin jikinta ke fita, Farar fatarta sol ta dawo har wani salƙi takeyi da ɗaukar ido, hatta uniform ɗin da ke ajikinta sun wanku sosai sun manne ma fatarta,

kwantar da kanta yai saman broad chest ɗinshi, Ya cusa yatsun hannunshi cikin sumar kanta yana cuccuɗata da ruwa, Jinin da ya danƙare mata a cikin kan ya dinga fita, gashin kanta ya dawo ainihin launin shi dark brown mai kyan gaske, ba ƙaramin taimakonta yai ba da yayi mata wanka, Ita kanta tasan bazata iya wanke najasar dake a jikinta ba, ƙanƙame jikinshi tayi sosai la66anta na kerma take faɗin"sanyi Danish san yi ni ke ji, tamkar ana ƙara gudun ruwan sun jiƙe sharkaf acikinsa, sai da ya kammala tsaftace mata jikinta tukunna ya ɗaukota saman kafaɗarshi ya dawo da ita Gefen dutsen da ya ɗaura uniform ɗinshi.

Tun da ya sauke ta ta faɗa ma faffaɗan ƙirjinshi, ta zagayo da hannayenta saman bayanshi, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, idanuwanta a lumshe, ita kaɗai tasan daɗin da ta ke ji, da farko taji haushi da ya yi mata wanka, amma yanzu ta fahimci Dalilin dayasa ya tursasa mata yin wanka, jikinta yayi mata daɗi wata irin ni'ima ke sauka, tamkar an yaye mata damuwar dake acikin zuciyarta, sun natsu suna sauraron bugun zuciyar junansu, irin yanayin da yafi son kasancewa tare da ita, yana son Angel dinsa fiye da yadda yake son kanshi, a shirye yake daya sadaukar da ranshi indai akanta ne"

Fatar wuyanta ya ƙurawa ido fara sol sai ƴan tabannin da ba arasa ba, na gurjewar da tayi, ɗaura tafin hannayensa yai asaman bayan nata,

"My Angel!" a kasalance ya furta sunanta shiru bata amsa mashi ba

"Are you feeling sleepy?" kamar yayi magana da bango shiru taƙi buɗe ba ki ta yi magana, ƙoƙarin rabata yayi daga ƙirjinsa, sai dai taƙi bari ya ɗago da ita, ta yi tighting ɗin shi tamkar zata koma cikin shi, baiwar Allah, Dama abuƙace take da ta samu inda zata sassauta raɗaɗin da ke acikin zuciyarta, abubuwan da suka faruwa a rayuwarta ta soma tariyowa tun daga lokacin da ta mallaki hankalin ta, har zuwa rayuwarta a hannun fulanin Daji da kuma faɗowarta gidan kurkukun ƙaddara, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta, jin shessheƙar kukanta ne yasa shi rikicewa ya shiga ambaton sunanta adabarbarce, daƙyar ya iya 6an6arota daga ƙirjinshi, eyes dinshi akan fuskarta ta runtse idonta

"My Angel I don't want you to dwell on what happened before, I know it hurts you, but please forget about the past. I don't like to see you cry.

tun da ya soma lallashinta bata buɗe idanuwanta ba, tsawon mintuna kafin a hankali ta ɗago da kanta tare da jingina bayanta jikin dutse.

Matsawa yayi jikin ƙaton dutsen ya miƙa hannu ya ruƙo uniform ɗin shi, A tsanake Ya sanyasu a jikin shi

"Zaki Iya jirana anan"? girgiza mashi kai tayi"tsoro nake ji, ka maida ni cikin ƴan uwana" yaso ta amince ko dan ya samu ya shiga cikin Dajin Ya nemo masu abunda zasu ci, kwantar mata da hankalinta yai"Yanzu zan dawo, bana so ƴan uwanmu su tashi da yunwa pls ki jirani anan, ba abunda zai same ki, kada kije ko'ina" bai jira amsarta ba, ya 6ace ma ganinta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull