Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 12

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 12

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 12: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 12. Tunawa da cewa ita fa yanzu mai ƴanci ce yasa ta…

3,356 words

Tunawa da cewa ita fa yanzu mai ƴanci ce yasa ta ɗan saki murmushi, har ta fara tunanin irin mugun kisan da za ta yi ma waɗanda su ka sadaukar da su, badajimawa ba ta soma Jin motsin tafiyar mutun a firgice ta buɗe idanuwanta lokaci ɗaya ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ganin Danish ne ya dawo hannun shi a ruƙe da Zomayen Daji da ya yo masu farautarsu, ya ruƙe ƙafafuwansu da hannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun ke aruƙe da gorar ruwan, mamaki ne ya kamata ganin zomaye, miƙa mata gorar ruwan yai da sauri tasa hannu ta kar6a, Acike take da ruwa, jera kafaɗa su ka yi suna tafiya suna satar kallon juna, abunda ya ɗaure mata kai yadda Danish yasan komai dangane da Daji mutumin da bai ta6a fita daga cikin kurkuku ba, Yanzu tadaina yi mashi kallon solo6iyo, A Namijinsa ta ke kallon shi.

Lokacin da su ka ƙaraso Gaban Kogon dutsen, Atare su ka shiga Ciki, Ya ajiye zomayen saman korayen ciyayin da ke shimfiɗe ƙasa, ya ɗago da ido ya kalle ta, zanje na haɗo itace yanzu zan dawo, Ta amsa mashi da toh,'

Bayan tafiyarshi ta ajiye gorar ruwan ƙasa, kafin ta nufi shimfiɗar su, ba ta yi mamakin ganin ba su farka ba saboda ta riga ta gane aikin Danishi, gaban akwatin kayansu ta zuƙunna ta buɗe ta curo tsoffin uniform ɗinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ta canza na jikinta da suka jiƙe ta shanya su daga wajen dutsen, dawowa tayi cikin kogon Agaban shimfiɗar ta zuƙunna tana ƙare masu kallo, idanuwanta akan Jemimah da Azeeza, daɗi kamar zai kasheta, a ƙagare ta ke da su farka su ga wurin da Allah ya kawosu tasan zasu sha mamaki da al'ajabi kuma zasu ji daɗin cika masu alƙawarin da ta yi.

Sam ba ta ji motsin shigowarshi ba, har sai da yai mata gyaran murya tukunna ta waiwayo su ka haɗa ido da shi

In zo in tayaka"? girgiza mata kai yai" a'a bana so ki wahala" miƙewa tayi tare da zuwa gabanshi ta zuƙunna tana ƙare mashi kallo, hankalin shi ya koma akan itacen da ya ke jerawa bayan ya kammala ya ɗauki duwatsun jiya da yai amfani wurin rura wuta, duk wani motsin shi akan idonta har ce mata yai "kije ki huta mana, ba kince kina jin sanyi ba? Ki ɗauko bargo" maƙe mashi kafaɗa tai alamar ba za ta je ba.

Bawan Allah shiya zauna zaman gasa masu naman, sai maiƙo yake yi kamar an soya shi da mai, Kitsan jikin zomayen ne ke narkewa, bayan ya kammala ya ɗaura gasasshen naman da ya tsira Jikin icce saman faffaɗan ganyan da ya shimfiɗa a ƙasa.

"Danish" ɗagowa yai tare da kallonta, bakomai ya gani acikin idanuwanta ba face Tsantsar tausayin shi

"Kada ki damu kanki am ok, idan zan shekara inayi maku bauta ba zan gaji ba" kalamanshi sun ƙara sanya mata ƙaunarshi acikin zuciyarta. "A ina ka samu wannan gorar ruwa"? Tai maganar tana nuna ta da yatsa

"A cikin Daji ba abunda ba zaki Iya samu ba, Hada kan mutun" murmushin gefen fuska ta saki, ga dukkan alamu zasu fara kafa nasu tarihin soyayyar tun acikin Daji.

Ɗagowa yai da lumsassun idanuwanshi ya ɗaura su kan fuskarta

"Can you eat by yourself? Or do I need to feed you?"

Girgiza mashi kai tai" ka wahala sosai, ni ya kamata in baka da hannuna" ya ji daɗin maganarta har ya buɗe baki da niyar mayar mata da martanin maganarta, kwatsam! muryar Jemimah ta katsesu da wani irin sautin mai amo take kwaɗawa Angel kira amatuƙar gigice take fadin"Genie wayyo Allah Genie Zafi Jikina ƙaiƙayi nake ji" Ahanzarce Danish da Angel suka miƙe da sauri suka nufi shimfiɗarsu atare suka zuƙunna agabansu, Hannu biyu Angel ta sanya ta ɗauko ta zuwa saman jikinta, ta ƙanƙameta, Duk tabi ta furgice sai kuka takeyi masu tana harba ƙafafuwanta, Sautin kukanta ne ya farfaɗo da sauran ƴan uwan nasu, Batul ce ta fara miƙewa kamar fatalwa idanuwanta luhu luhu sun kaɗa jawur, baiwar Allah har faɗawa tayi sai uban haske, gashin kanta kuwa a hargitse yake, Buɗe idonta keda wuya ta sauke su akan na Danish dake kallonta, Muryarshi na ɗan rawa ya furta sunanta"Ba..tul" ɗauke idonta tayi daga kan fuskarshi ta mayar dasu Kan kogon dutsen da suke aciki saƙo da lungu tabi da kallo, kukan farin cikine ya kubce mata, Da sauri Danish ya ruƙo hannunta acikin nashi ya kwanto da kanta saman ƙirjinshi, sosai ta ƙanƙameshi tana cigaba da yin kukan.

Farkawa Gabriel yai zumbur ya miƙe yana ambaton sunan Azeeza, da ita ya kwanta acikin ranshi, sai tsuma yake yi yana fitar da huci, Cikin shessheƙar Kuka Angel tace dashi"She's still alive! Azeezar mu bata mutu ba, suna araye,"

Karaf maganarta ta sauka akan kunnan sauran ƴan uwan su da suka farka, a zazzaune suka miƙe Tun daga kan Javed, Naufal da Hannah mutun uku ne basu motsa ba, parveen Azeeza da Haris, ga dukkan alamu sun farka daga bacci sai dai sun kasa motsawa, Jikinsu ba ƙoshin lafiya, ko yatsan su sun gaza ɗagawa.

Hankulansu gaba ɗaya ya koma kan su, kowan nan su fuskarshi akumbure take suntum, babu walwala ko annuri, dagaske Azeezana bata mutu ba? Gabriel ne yai tambayar yayin da idonshi ke fitar da hawaye, Danish ne ya bashi amsar tambayarshi, Tsabar farin Cikine ya bayyana akan fuskarshi, Rumfa yai ma azeeza da ƙirjinshi motsa la66anta da take yi ne ya tabbatar mashi da cewa tana araye sungumarta yai tare da ɗaurata saman laps ɗinshi, Danish Ya miƙa mashi gorar ruwa don ya bata tasha, Yatsun hannun shi na kerma ya kar6a ya kafa mata abaki, ruwan yana wucewa ta maƙoshinta sai dai ta gaza buɗe idonta, Farin Ciki duk ya cikasu, Naufal ne ya ɗauki Parveen Baiwar Allah anji jiki, miƙa mashi gorar ruwan Gabriel yai ya kar6a yabawa parveen kamar zata haɗa da gorar duka ta shanye, Sai lokacin Danish Ya raba jikin shi daga na Batul Ya rarrafa zuwa gaban Haris dake kwance kamar matacce ya ɗaura hannayenshi biyu wurin ɗago dashi ya kwantar da kansa saman kafaɗarshi, Cikin sanyin murya ya ke ambaton sunanshi"Haris! Haris!" shiru bai amsa mashi ba, jikin shi yai zafi sosai babu alamun lafiya atattare dashi, ɗaura tafin hannun shi yai saman ƙirjinshi bugun zuciyar haris a hargitse yake fita, hakan ba ƙaramin tada mashi hankali yai ba, Yana fargabar wani abu ya same shi. "Ɗan uwana Rabin raina nasan kana jin muryata pls kada ka bari damuwa tayi maka illa, ina atare da kai" jin muryar Danish acikin kunnanshi yasa shi ƙoƙarin motsa la66ansa sam sautin yaƙi fita, Fahimtar hakan yasa danish matsar da kunnanshi saitin bakin Haris

"Deeja ta mutu! Na rasa Deeja Danish! Bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, zuciyata nauyi take yi min, ka taimaka ma rayuwata" a hargitse yake magana, tsananin tausayin shi ne ya kama Danish, dama sai da ranshi ya bashi cewar akan Deeja ne ya shiga mawuyacin halin nan.

"Haris ka kwantar da hankalin ka, ba mu da tabbacin suna araye ko sun mutu, tun da har su Azeeza suka farka bayan munyi tunanin sun mutu ina saran suma za'a iya samun masu rai acikin su" cikin jin ƙunar rai Haris ya furta"Danish idan har hakane deejana tana araye azzuluman mutanancan zasu Iya kashe min ita, mun barsu fa a kurkuku, Danish ka koma ka ɗauko min ita, idan baso kake na mutu ba' sosai ya sanya mashi kuka, Rarrashin shi ya dinga yi yana lalla6a shi duk don ya samu ciwon nashi ya lafa.

Waɗanda suka fi jin jiki a cikinsu Jemimah ce da Azeeza sai Haris, Ita parveen tunda taji ta ajikin Naufal ta wartsake, har tana iya ambaton yunwa take ji, Jemimah kuwa taƙi daina yi masu kuka, Sautin kukanta ya karaɗe kogon dutsen kamar ana zare ranta, Hankalin Angel duk yabi ya tashi, Ta rasa ya zatayi da ita, Cikin muryar kuka take yiwa Danish magana akan yazo yataimaka mata, Har ƙwara Azeeza tun da ta ƙanƙame Gabriel bata ƙara motsawa ba, ta lafe mashi idanuwanta arufe suke gam.

Sun rasa ya za su yi dasu, kukan jamima ba ƙaramin tsuma zuciyarsu yake yi ba, taji jiki baiwar Allah, Sunga ƙoƙarinta da har ta iya yin kukan, azabar raɗaɗin gabanta ne ya addabeta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, fuskarta jaga jaga da hawaye, yarinyar da bata wuci shekara goma da watanni ba, ta rasa budurcinta, su kansu sunyi mamakin da ta iya rayuwa, lokacin mutuwarta ne baiyi ba, Tana kuka suna kuka, Babu wanda bai zubar mata da ƙwalla ba in ka cire Danish, kwantar da Haris yai saman shimfiɗar, jikinshi na tsuma ya nufi Angel Ya sanya hannu biyu ya kar6i jemimah daga hannunta, fucewa yai da ita daga Cikin kogon dutsen basu san Inda ya nufa da ita ba.

Tsawon mintuna sai gashi ya dawo rungume da ita a ƙirjinshi, ajiyar zuciya suka sauke Jin tayi shiru tadaina kukan, Akwatin kayansu ya buɗe ya ɗauko mata rigar sanyi, cikin waɗanɗa tsohuwa ta yi masu kyautarsu, Ya sanya mata a jikinta, ga dukkan alamu wanka ya yi mata, bayan ya kammala sanya mata rigar, ya curo mata hula ya zura mata akanta, ya kuma ɗauko Mayafin kayansu, Sai kallon shi suke yi, Danish ya basu mamaki, Asaman bayanta ya yafa mata mayafin ya miƙe tsaye yana lallashinta kamar yadda akeyi wa jarirai, jemimah ta natsu sai faman lumshe idanuwanta takeyi, Jikinta ya lafa sosai ta daina jin raɗaɗi ciwo nata, juyowa yai tare da nufar Angel ya miƙa mata jemimah,

"Zan tafi da Azeeza ki basu naman su fara ci" amsa mashi tayi da toh, ta kar6i jemimah tare da rungume ta a ƙirjinta, bayan Ya ɗauki Azeeza Ya fuce da ita, janyo masu naman tayi zuwa gabansu, duk da halin da suke aciki hakan bai hanasu Cin naman ba, Saboda matsiyaciyar yunwar da suke ji, Mutun ɗayane ya kasa cin naman, ko da Javed Ya tallabo shi ya zaunar dashi Yana tura mashi abaki, Amayar dashi ya dinga Yi, ruwa kaɗai ya iya sha, sun damu da rashin lafiyar Haris Ya galabaita sosai, Jemimah dai ta ɗanci naman Angel ce take bata abaki, har yanzu bata buɗe idanuwanta ba, balle ta san a ina suke.

Shigowa cikin Kogon Danish yai Hannunshi ɗauke da Azeeza, Ya wanke ta tass jikinta sai kakarwa yakeyi, tunkafin ya ƙaraso Gabriel Ya buɗe akwatin kayansu ya ɗauko mata rigar sanyi tare da mayafi, Bayan Danish Ya miƙa mashi ita, Ya sanya mata rigar asaman uniform ɗinta, Ya ɗaura mata mayafi saman kanta, kafin ya kwantar da ita saman ƙirjin shi, Abaki ya dinga gutsuro namanta yana tura mata abaki daƙyar take iya taune shi, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, duk fa wannan budurin da sukeyi Azeeza da Jamimah da Parveen basu san cewa sun bar kurkukun ƙaddara ba, Saboda basa acikin hayyacin su.

Danish bai samu damar cin nashi naman ba, Jira yai sai da suka kammala ɗaya bayan ɗaya ya raka su zuwa bakin ruwan nan suna yin wanka, da taimakon shi Haris ya samu yayi wanka jikin shi ya ɗanyi mashi daɗi, bayan sun kammala Ya ƙara haɗo wasu itacen Ya kunna masu wuta Kogon dutsen ya ɗumama sosai Sanyin da su ke ji ya washe, sun cinye namansu duka, Kaɗan Danish ya samu yaci, kamar masu zaman makoki haka su ka zauna kewaye da wutar da ke ci, Suna kallon junan su kowa da abunda ya ke saƙawa aran shi, jemimah tuni bacci ya ɗauketa kamar jinjira haka Angel ta matseta a ƙirjinta, haka azeezama bacci ne ya ɗauke ta, tana kwance saman jikin gabriel, Haris ya langwa6a kanshi saman kafaɗar Danish, Batul ta ɗaura kanta saman kafadar Angel, Parveen tana a kwance saman ƙirjin naufal, da hannu biyu ya tallabeta, haka zalika Hannah tana arungume jikin Javed, sun natsu suna sauraron kukan namun dawan dake hargowa acikin Dajin, ba zaka ta6a fahimtar yanayin da su ke a ciki ba, kowa da abunda yake saƙawa aranshi.

*OBIE STATE*

In Abuja🏙

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E8🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

*Obie Estate*Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi, Aljannar duniya da babu tamkarta a faɗin nahiyar Africa, Hamshaƙin Estate Ne Da ya haɗa tanƙama tanƙaman luxury Villas, da duk wani Ababen more rayuwa, Kayan alatun da ke a cikinsa kaɗai abun kallo ne, dollar ta yi kuka awurin ƙera ginin, yana da 6angarori da dama, kama daga katafaren Gate ɗin shiga Estate ɗin wanda Jami'ae ne ke tsaron shi Sojoji da ƴan sanda Ko sauro bai isa Ya ƙetara ƙofar shiga gidan ba saboda tsaron da ke gare shi, ba iya mutane ba hada na'urorin da ke sanya ido ga duk wani mai shige da fuce, kowace kusurwa ta villas ɗin tana maƙale da na'urorin cctv camera, daga bakin faffaɗan gate ɗin Santalelen titi ne zai isar da kai ga Interior ɗin daular, akwai Harabar ajiye motocinsu, Gardens da swimming pools area, Ga zoo wurin da ake kiwata dabbobin gidan. Kowani Villa na estate ɗin Yana da nashi kayan alatun na more rayuwa, parts ɗin da ke a cikin kowani gida ya haɗa da Haɗaɗɗun falullukansu waɗanda suka ji jigunannun furniture, Bedrooms, Dining rooms, Kitchens, Bathrooms, Laundry rooms, da sauransu, akwai Ƙayatattun dogayen benaye zubin twin stairs da U-shaped stairs, Idan ma mutun baida ra'ayin Hawa Benan Kowane Villa yana ɗauke da residential elevator wadda aka fi sani da lifter, tun daga Hawa na farko zata ɗauki mutun har izuwa hawa na Uku, dai dai da cokalin amfani na gidan babu wanda aka ƙera a ƙasa Nigeria, kaf kayansu daga ƙasar waje ake shigo dasu, mai karfin imani ne Kaɗai zai iya rayuwa acikin estate dinsu ba tare daya shagala daga yin ibadarshi ba, sai dai ta inda masu rayuwa cikin gidajen zasu burge ka Allah ya hore masu baiwar Ilmin duka na addini dana zamani, wayayyun mutanene masu daraja da ƙima a idon duniya, Sun Iya takun su ba zaka ta6a Iya aibatasu ba, saboda kyawawan ɗabi'unsu da halayansu, komai nasu is Extraordinary.

Tun da garin Allah ya waye masu aikin gidan su ke ta kai komo, kowaccensu ta yi dressing cikin chef's uniform launin farare, ƙwararru ne a 6angaren girke girke da gyaran gida, basu wasa da aikin su, Suna ba lokacin mahimmancin sa, kuma suna takatsantsan wurin kula da buƙatun mutanan gidan.

A tsastsaye su ke a Cikin Katafaren Kitchen ɗin gidan mai girman gaske, A shaƙe ya ke da kayan Amfani, ko'ina a tsaftacensa ya ke tamkar ba amfani su ke yi da shi ba, aiki su ke yi tuƙuri babu kama hannun yaro, Matasan Ƴan mata da manyan su, wasu suna aikin wanke nama wasu suna yanke yanken kayan lambu agaban cutting board, yayin da wasu su ke agaban manyan gass cooker suna kula da girkin da suka ɗaura, akwai waɗanda ke a tsaye in front of kitchen microwave suna aiki.

Ƙamshin girkinsu ya karaɗe ko'ina tun daga cikin kitchen ɗin har izuwa Babban falon gidan.

Babbar macace ta shigo kitchen ɗin domin duba masu aikin don ganin yadda komai ke gudana, A ƙalla za ta kai shekara 40 a duniya, Ta kasance ɗaya daga cikin Masu yi masu hidima a gidan, ita ce head maids shugaban ma'aikatan Cikin gidan, Macace mai yawan fara'a ga son mutane, ma'abociya son Shigar fararen Kaya, A yanzu haka pakistan ne a jikinta riga da wando farare ƙal anyi masu adon duwatsu launi daban daban, ƙafarta na sanye cikin flat shoes, bakowa bace wannan face *DIVYA* ba'indiyace amma sunfi kiranta da *HAJJATY* tun da ta shigo kitchen ɗin masu aikin suka fahimci itace tazo dubasu nan fa suka ƙara dage damtse suna aiki duk don su ku6uta daga faɗanta.

A hankali ta ke zagaye Kitchen ɗin, Hannayenta a goye saman ƙirjinta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, na ɗan wani lokaci kafin tayi masu gyaran murya, kusan atare su ka ɗago suna kallonta, Hannu ta tafa masu

"Aikin ku yana kyau, You ladies Are doing a fantastic job, everything smells delious, i'm sure ɗanɗanon girkin zaiyi daɗi kamar yadda ƙamshinsa ya ke da daɗin shaƙa, Ina ƙara jinjina ma ku," ta ƙarasa yi masu maganar tare da ɗaga masu babban yatsan hannunta na dama alamar Jinjina.

Murmushi ne Ya bayyana akan fuskokin su, ba ƙaramin daɗi suke ji ba, Idan hajjati ta yabe su, suna matuƙar sonta kuma suna girmamata saboda kyawun halayanta da ɗabi'unta.

"Dame dame aka kammala ne"? ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu, Abla ce ta soma Yi mata jawabi

"Kebab with chips, Beef shawarma, burger and pancakes,..." kusan abu goma ta lissafa mata, Jinjina kai Hajjaty ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa"Kada na katse maku aikin ku, lokaci Yana ƙurewa, Ku hanzata ku kammala, "

"An aikawa Hajiya saratu Breakfast ɗinta!"? da sauri Safa tace"yanzu nake shirin zuwa in kai mata, Nice nike duty part ɗinta" Gyaɗa kai Hajjaty ta yi.

"Okey, shirya min fresh fruit ki haɗa min da kakkauran tea," Wadda aka kira da Sarah ta amsa mata da toh, ba tare da 6ara lokaci ba ta shirya mata kayan marmari a cikin ƙayataccen wooden tray, tare da cup of tea, ta miƙa mata hannu biyu tasa ta kar6i tray din tare da juyawa ta fuce.

Bayan fitarta, Fira ta 6arke a tsakaninsu

"Safa ashe ke ce kike duty a part ɗin Aunty jarabatu zaki sha Masifa, " Abla ce tai mata maganar, murmushi suka saki, sophia tace"Ai hajiya saratu ba daga baya ba, In dai wurin Iya masifane, Last time fa da naje kai mata abinci cewa ta yi wai na gutsiri ƙafar kaza, hada cewa ita bata yarda damu ba, wama ya sani ko mun saka mata guba acikin abinci donta ci ta mutu," dariya suka saka

"Tana da wuyar sha'ani bata yarda da kowa ba, In ba wannan Mijin nata ba, Uban son banza suruki da zaman gidan surukai Ko kunya babu" sophia ce tai maganar, Safa tace"Ai koni na samu wurin zama agidan nan abunda zanyi kenan, waman taraka bati siddan, shiyasa a kullum nake roƙon Allah ya bani bugun zuciyar family ɗin, Wlh idan na Aure shi nadaina sakin baki ina bacci, nafilfili zanta yi akan Allah ya dawwamar da auran mu don nasan maƙiya da mahassada ba zasu bar mu mu zauna lafiya ba, Musamman Mahaifiyarshi uwar Ji da izza, kinga matar nan bata ɗaukar raini batason Mu'amala da bare...." tun da ta fara zuba suke binta da kallon rainin wayau saida takai aya tukunna Abla tace"you don't ave sense, Dama najima da zargin kwakwalwarki ba dai dai take aiki ba, Ko Jazz da muka raina wlh yafi ƙarfinki, Ni kaina ba zance bana son Owais ba, amma ance abunda yafi ƙarfinka ka haɗa shi da baka so" kwa6e fuska Safa tai"kiyi min fatan alkhairi kawai, Nima a hausa novels ni ke jin irin hakan na faruwa, mafi yawanci zaki ga ƴar aiki ta auri ɗan masu gida, wani sa'in ma mai gidan ta ke aurewa...." sautin dariyarsu ne Ya hana ta ƙarasa maganar, suna fira suna aiki,

"Safa kina atare da wahala, in dai ko zaki cigaba da tunanin zaki samu abunda ki ke so kamar yarda ki ke karantawa ahausa novels, Ni Bance baya faruwa ba amma Allah a zamanin da mu ke ciki zaiyi wuya, mai kuɗi sai ƴar mai kuɗi, talaka sai ɗan talaka, Ina jiye maki tsoron heart attack ya kama ki silar son wanda bai son Kina yi ba, a ƙarshe ki ƙare a emergency room"

Dariya suka saki gaba ɗayan su, kwata kwata firar da suke yi bata ɗauke masu hankali daga yin aikin su ba, manyan cikin su ne kadai basa magana sai dai idan sun faɗi abunda ya basu dariya su ɗan murmusa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull