Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 13

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 13

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 13: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 13. "Ni takaici na magadan gidan nan basu da yawa,…

3,317 words

"Ni takaici na magadan gidan nan basu da yawa, duk irin tarin dukiyar nan ace Iya mutun goma sha biyar ne ke da gadonsu" Abla ce tai maganar.

Abla tace"Nikaina abun na damu na, Yana yi mun ciwo a zuciya, na rasa gane meyasa basa son haihuwa, daga mai ƴa'ƴa biyu sai mai ƴa'ƴa uku, Allah ya hore masu wadatar arziƙi sai ƴa'ƴa ne zasu gagare su? Abun na ƙona mun rai, komai nasu na rayuwar turai, Mu da zasu taimaka su Aure mu, duk bayan ƴan watanni zamu dinga sakar masu ƴa'ƴa tuni zamu cika famiy ɗin"

Maganar Abla ba ƙaramin dariya ta basu ba, Sofiya tace"Sannu kaza suma ai suna son ƴa'ƴan, sannan bada son ransu bane ba su haihuwa, Ƙaddarar su ce ta zo masu ahaka, naji labari a bakin Hajjaty saboda tafi mu daɗewa a gidan, Suna haihuwa amma ƴa'ƴan basu zuwa da rai, A mace ake haihuwarsu yawanci da zarar sun yi haihuwar fari da ta biyu zaiyi wuya kiga sauran sun rayu a matattu su ke haihuwarsu, Allah ni tausayi suke bani, Musamman prime minister Hateem shifa Bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, shi da matarshi Gimbiya mujeedat, ƴa'ƴa biyu duka mata, rashin haihuwarsu ba ƙaramin gi6i yai masu ba arayuwarsu, Ki duba fa hateem shine yafi kowa arziƙi a family ɗinsu daga shi sai sharafudeen," mamakine akan fuskar Wasu daga cikinsu waɗanda basu daɗe da fara aiki ba

"Abun da ɗaure kai, Kuma an duba lafiyarsu? Ko dai wata lalurar ce da suka gada tun kaka da kakanni"?

"Ko ɗaya, Tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje an bincika lafiyar kowan nan su, Ba su da wata matsala da ta shafi ƙwayoyin haihuwarsu, lafiyar su ƙalau, har manyan malaman addini saida kakansu ya sanya don su bincika mashi meke faruwa a zuri'arshi, Sakamakon ɗaya ne dana asibiti, basu da wata lalura,"

Jikin su duk yai sanyi, Basu ta6a sanin zancen haihuwar da matansu keyi yara suna zuwa ba rai ba sai yau da sophia ta sanar da su.

"Allah mun tuba ka yafe mana, shiyasa akace zato zunibi koda ya kasance gaskiya, Gulma ba ta yi rana ba, Mune kullum tsegumin mu akan suna yin irin rayuwar turai ba su son haihuwa ashe ba laifin su bane, jarabtace daga Allah" murya asanyaye Safa Tayi maganar.

Abla tace "Na tausaya masu, kuma In sha Allah zamu ta ya su da addu'a, akan Allah ya yaye masu lalurar da ke damun su" shiru suka ɗanyi Na wani lokaci, daga bisani Safa ta shirya Kayan breakfast ɗin Hajiya saratu A Babban tray ta jera mata su, Bayan fitarta daga Cikin kitchen ɗin su ka ɗaura da wata firar, sam basa gajiya da firar Familyn Obinna.

"Muna fa da gagarumin bikin ranar zagayowar Haihuwar Obie, Nasan za'ae shagali na kece raini, za'a yi 6arin Dollar da pounds, Aranar zamu ga Zaratan ƴa'ƴan Obinna da Jikokinshi waɗanda basa a ƙasar, Ina da tabbacin Owais ma zai halarta"

Fuskar Sophia ɗauke da farin Ciki tayi maganar, Abla tace"Anya ko Owais zai zo? Kinsan fa halinshi, samun lokacin shi abune mai wuya"

"ai ko baiyi niya ba sai obinna Ya matsa mashi akan ya zo, Kinsan fa kaf cikin jikokinsa yafi ƙaunar Owais, kowa yasan da wannan zancen, Kinga ko ba zai so ayi shagalin nan ba tare da Owais Ya halatta ba," acewar Abla

Murmushi Sopy tayi "Can't wait to see Allah Ya nuna mana Lokacin, Dole naje ayi min wankin ido, don na samu damar ƙare Mashi kallo"

"Da rabon kisha mari, Owais baya son Kallo Idan Yana magana mutun bai isa Ya ɗaga ido ya kalle shi ba, Sannan ba'a katse shi, Sauƙin shi ɗaya Idan har kika karanci halayanshi da ɗabi'unsa tsaf zaku zauna lafiya, mutunne mai sauƙin kai baida girman kai, Yana da tausayi ga taimakon na ƙasa dashi....." tun da ta fara jera masu Kyawawan halayanshi bata tsagaita ba har saida Landline ɗin dake a bakin ƙofar fita kitchen ɗin ta yi ringing tukunna ta dakata da yin magana, da sauri Sophia ta fuce ta je ta ɗauki landline ɗin Ta ɗaga kiran daya shigo, Cikin girmamawa tayi sallama, Jikinta sai 6ari yake yi.

"Cofee...." Iya abunda Taji an furta mata acikin wayar, jin yayi rejecting yasa ta zame ta daga saman kunnanta ta ajiyeta saman table, Dawowa Cikin kitchren ɗin Tayi Hankalinsu gaba ɗaya ya dawo kanta.

Har suna haɗa baki wurin tambayar ta "Wanene Ya kira" kwa6e fuska tayi tare da cewa"Nakasa gane muryar wanene acikinsu, Zaid ne ko Zayn, Coffee su ke buƙata, wa zai kai masu"? Ta yi tambayar tana kallon sauran. Shiru babu wanda yace zai kai, saboda Mugun tsoron shiga part ɗinsu suke Yi, saboda masifarsu,"

"Kinga tun da ke kika ɗaga Kiran nan Ki lalla6a ki je kawai ki kai masu awuce wajen" Acewar Abla, Yamutsa fuska marwa ta yi, Ba yadda ta Iya don dole ta haɗa masu coffee acikin mugs guda biyu ta ɗaura saman Plate ta fuce daga cikin kitchen ɗin.

Tun lokacin da Able ta fita hannunta ɗauke da tray Na breakfast ɗin Hajiya Saratu, Kai tsaye ta nufi Part ɗinsu, Tun kan ta ƙara sa gaban ƙofar ɗakin ta daddaɗan ƙamshin turarenta Ya daki hancinta, macace mai son ƙamshi ga iya ɗaukar Wanka, A bakin door ɗin Ta tsaya tare da Yi mata sallama, daga cikin ɗakin tajiyo muryar Hajiya saratu

"U can come in" A hankali ta tura ƙofar ta shiga, Hajiya saratu tana azaune tsakiyar Katafaren gadonta, jikinta na asanye da jallabiya, Kanta babu Kallabi Kitson zanene all back Wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaɗarta, fararen idanuwanta suna a manne da farin glass medicated, tana da duhun fata mai kyan gaske, Hutu ya zauna mata, Hankalinta gaba ɗaya yana akan tsadaddar Apple Laptop ɗin da ta ke yin operating, ga dukkan alamu aiki ta ke yi.

"Once you're done looking at me, please put the food on the table and leave my room." Muryarta ce ta fargar da Safa daga kallon ƙurullan da ta ke bin ta da shi, Adabarbace ta gaishe da ita"Ina kwana Hajiya," Guntun tsoki taja ba tare da ta amsa mata ba, ko kallo ba ta ishe ta ba, asaman front table din bakin gadon, Safa ta ɗaura mata tray din

"ko akwai wani abu da ki ke buƙata "? cikin Jin shakkarta Safa ta yi mata tambayar don tasan halinta, in har bata ba mutun iznin tafiya ba, yai yunƙurin Juyawa zai tafi atsawace zata ce mashi da Iznin wa!

Safa har ta gaji da tsayuwa shiru bata tanka mata ba, tamkar bata san da mutun awurin ba, Halinta ne share mutane, sai da ta mula ta sha iska tukunna ta ba ta zinin tafiya, bayan fitar Safa daga ɗakin, Ta dakata da yin aikin laptop ɗin, Yunƙurawa tayi tare da kai hannu ta damƙo Burger Ta soma turata abakinta tana ci, Bata wasa da Cikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ta handameta, ta kuma janyo Chicken wings tana ci, baya tagama ta ɗauki bowl ɗin dake shaƙe da plaintain chips hannu baka hannu ƙurya kamar mai fama da cutar yunwa, Saida ta lamushe komai, a ƙarshe ta kora da ruwan lemu mai sanyi.

"Daɗina dake bakya wasa da Cikin ki," Jin muryar Mijin nata yasa ta ɗago da eye balls ɗinta akan fuskar shi, Daga cikin toilet ya fito waist ɗinshi ɗaure da towel, Ƙirarshi tamkar ɗan wrestling, Kakkarfan mutunne Jibgegen ƙato, Kyakkyawan ba'indiye Sumar kanshi akwance luf saman kanshi, Ga wani kwantaccen saje gefe da gefen doguwar fuskarshi, ' ta6e mashi baki Tayi"meye haka? Bana hanaka yawo da towel a qugunka ba? Yanzu da ace mai aikin nan tana acikin ɗaki ka fito fa? Fuskarta aɗaure tayi mashi maganar, Matsawa yai kusa da ita yaɗan ranƙwafa saitin fuskarta"yaushe zaki daina kishina? Murga mashi baki tayi"Bansani ba, Ni dai na faɗa maka, Karka kuskura ka ƙara fitowa ɗaure da guntun abu a qugunka bana son ta6ara" Ido cikin ido suke kallon Juna.

"Ƴa'ƴan mu Uku, kowan nan su Ya mallaki hankalin shi, Na yi tsammanin zaki rage kishi na da kike Yi" harara ta watsa mashi"pls Ka wuce ka je ka sanya suturarka, bana son ganin ka ahaka" Hannu ya kai yana ƙoƙarin warware towel ɗin gabanshi da sauri ta damƙi hannayenshi aɗan fadace tace"Pravin meye haka? Yarinta ce fa wannan"? Kashe mata ido ɗaya yayi fuskarshi ɗauke da murmushi yace"indai ina atare dake bazan ta6a girma ba, saboda tsantsar ƙaunar da kike nuna min" ta6e baki Saratu Tayi"naji yanzu kaje ka sanya suturarka, Sannan me kake son Ci insa akawo maka" Murmushin fuskarshi bai washe ba yace"abunda kika ci shi nake sonci abar ƙaunata, naga ma har kin kammala naki breakfast ɗin why ba ki bari na fito munci atare ba?" Ɗaure mashi fuska tayi "Pravin mu fa ba ƙananun yara bane da zaka tsaya kana gayamin kalaman Soyayya, ko da ya ke nafa tuna kufa indiyawan nan bautawa soyayya kuke yi har ku tsufa kuna abu ɗaya" cikin Zolaya ta ƙarasa maganar, gyaɗa kanshi yai"komi zaki ce bazanji haushin kalamanki ba, Amaryata kuma uwargidana, sannan uwar ƴa'ƴana abun alfaharina," lumshe ido ta ɗanyi idan zata biyewa pravin ba zai barta taci gaba da yin aikinta ba, gwanine a fagen Iya soyayya da daɗin baki, Ya ƙware wurin Iya jan hankalin mace.

"Romeo, now your Juliet is at work, I'm almost done, zansa a kawo maka breakfast ɗin ka, Ni da kaina ma zan baka abincin abaki" Amsa mata yai da Okey, Daƙyar ta lalla6a shi Ya miƙe ya nufi Cikin ɗakin Yana tafiya tana satar kallon Bayanshi, a gaban closet ɗin kayanshi Ya tsaya tare da kai hannu ya buɗe

"My Juliet ba ki faɗa min kayan da ki ke so In sanya ma"! Murmushi ta saki"Yau babu aiki, ka samu hutu don haka Nafi sha'awar ganinka Cikin shigarku ta al'ada, Ya gane me take nufi, riga da wando Ya curo kalar na mazan Indiya ya sanya su ajikinshi, sun bi shape din jikinshi yadda kasan matashin saurayi saboda haɗuwarshi.

Bayan ya kammala Shirya kanshi, Hajiya saratu tasa aka kawo mashi breakfast, Da kanta take bashi abaki Yana ci, mugun son shi ta ke yi, ta mutu akan pravin, kamar yadda shima yake ƙaunarta, Allah Ya hada jininsu. Babu mai cin moriyarta irin Mijinta, komai nata mallakin shi ne.

Lokacin Da Sophia ta ƙarasa Bedroom ɗin twins dake acan Upstairs Second floor, Jikinta na kakarwa ta yi knocking ƙofar, almost 3 times kafin tajiyo muryar ɗaya daga Cikinsu "you can come in" Numfashi taja kafin ta tura ƙofar Haɗaɗɗen bedroom ɗinsu, Sanyin A.c da ƙamshin Turarensu ne Ya daki hancinta har sai da ta lumshe idanuwanta saboda tsabar yadda ƙamshin Ya kurɗaɗa ta ƙofofin Hancinta, tunkan ta shiga ciki Ta hango Ɗaya daga Cikinsu A tsaye Gaban tanƙameman dressing mirror Daga shi Sai short a jikinsa launin ja, Yayin da twin brother ɗin shi yake a kwance saman gado rabin jikin shi lullu6e da duvet. Kyawun surarsu sak irin na mahaifinsu Pravin, tamkar yayi kakinsu.

Muryarta na ɗan rawa tace"Barka da safiya yalla6ai, Ga coffee ɗin Ina zan aje' ba tare da ya juya ya kalle ta ba yace "On my head" tuni tasha jinin jikinta, Batasan Ya zatayi ba, Zaid dake a kwance saman gadon Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya saman front table ɗin gaban gadon.

"Is that how your parent taught you to enter a room without saying 'Assalamu Alaikum ? Ɗakin kafurai kika shigo"?

Muryarshi tamkar ta mashayin giya

"Afwan yalla6ai, kafin in shigo saida na fara yin sallama, wata'ƙil baka jini ba ne" A sukwane Ya juya yana binta ɗan iskan kallo

"Am I deaf?" girgiza mashi kai tayi muryarta na kakarwa tace "That's not what I meant, sir..." bai bari takai ƙar ƙarshen maganarta ba, ya nuna mata ƙofar fita Aɗan tsawace ya furta "Oya Go back ki sake yin wata sallamar" fuskarshi a murtuke yayi maganar, Idanuwan sophia tuni sun ciko tab da ƙwalla, Jiki asanyaye ta juya ta koma waje.

Kware Murya tayi"Assalamu alaikum" shiru bai amsa mata ba, shiga ciki tayi"Sir nayi sallamar in shigo? Coffee ɗin Yana hucewa"

Kafin Ya bata amsa Zayn dake kwance saman gado ya furta "I didn't hear it. Go back and make another greeting"

Tayi mamakin Jin muryarshi duk a tunaninta bacci yake yi, ashe idonshi biyu, " Maƙoshinta tamkar zai 6allo ta ƙara kware murya wurin Yi masu Sallama, Tun tana yi da marmari har ta fara gajiya, idanuwanta sunyi luhu luhu, A ƙalla tayi masu sallama kusan sau Goma sha biyar ba tare da sun bata iznin shiga ɗakin ba, Har saida Coffeen hannunta Ya salafce, sai da suka tabbatar Ta jigata sosai tukunna Zaid yace da ita ta shigo ciki, hawaye nabin kuncinta ta shigo.

Kishingiɗe ta samu zayn ya ɗaura kanshi saman pillow, Ko kallon arziƙi bata ishe shi ba, jiki na 6ari ta nufi Table zata ɗaura plate ɗin, Kakkausar Murayar zayn ce ta dakatar da ita

"Don't you dare put that on the table! Ki koma ki canza wani coffee ɗin, wa zai sha abu ya salafce" juyawa marwa tayi tana kuka ta fuce daga Cikin ɗakin, ko a jikinsu, sun Iya rashin mutunci da mugunta idan suka so, duk rana ta Allah sai sun sanya ɗaya daga cikin masu aikin gidansu zubar da hawaye.

"Bro, when are we going back to America?" Zaid ne yai maganar while sitting on the dressing table chair.

Yatsina fuska Zayn yai "we have no way out, Zaid, seriously, naji takaicin tursasa mana dawowa Nigeria da obie yai, Ya hana rayuwarmu sakat, mu kaɗai mu ka tsone mashi ido, ga Owais can kamar tsuntsu Yana shawagi a ƙasashen waje sai mu da muka tsone mashi ido, nifa na gaji da halin dattijon nan, na rasa zaman me yake yi acikin duniyar nan, duk shekara sai na sayi sabon likafi da miski na mutuwarshi but yaƙi tafiya" Ranshi a6ace yake magana

Zaid dake kallon ɗan uwan nashi yana murmushi yace" I know what you're mad about" Yatsina fuska yai"Kai ma ɗin itace damuwarka, Ummin america ce silar komai, " Yana magana a harzuƙe ga dukkan alamu an fama mashi raunin dake acikin zuciyarshi.

"Everything about her is different. From the first day I saw her, I knew she was a classy woman with a magnetic personality that could captivate any man." lumshe ido zayn yayi, bakomai yake tariyowa ba face farkon haɗuwarsu da ita.

"Naso ace ta amince min, ba abunda zai hana in aureta, zan tattara dukiyata gaba ɗaya data mahaifiyata, da ta Dattijon can duka In bada a matsayin sadakinta, sai dai kash ta nuna bata buƙatar aure arayuwarta, Zaid ya zanyi da raina? Ta sanya min jarabar da bazan Iya gogeta ba" cikin jin shauƙi yake magana.

Harara zaid ya watsa mashi"nifa ban gane ba, Taya zaka dinga yi min magana akan macen da nake son in mallaka? Kasan dai haramun ne muyi sharing mace ɗaya a gidan aure ko?, awaje ne muke da ikon yin hakan duk da shima yin hakan haramun ɗinne" ta6e la66ansa yai"Zaid ni ba zan yi jayayya dakai ba, just Kada kamanta ni ne gidan kuɗi, na gaban goshin mommy, mata kuma saida kuɗi"

Dariyar shaƙiyanci zaid ya sakin kafin yace "Nima ina da daddy, kada ka manta komai na mommy mallakinsa ne" Sakin baki Zayn yai saida Zaid ya karasa maganar tukunna yace"Daddy ai ɗan koren mommy ne, mutumin da ke zaune agidan surukansa? Mommy ce fa silar arziƙinsa, tayaya zaka hada kan ka da Ni? baya kasan Mune ke da dukiyar Ku kuma Bayin mu ne, Sai mun ɗan watsa maku hatsi tukunna kuke samun wanda zaku tsastsaga....." Kallon al'ajabi Zaid yake bin ɗan uwansa dashi, yadda yake magana Yana kushe mahaifinsu yai matuƙar ɗaure mashi kai, da ace wani bare ne yai wannan maganar, hada shi za'a haɗu wurin cin ubansa, don sun tsani gorin da akeyiwa mahafinsu akan yana zaune gidan surukansu.

"Assalamu Alaikum" Muryar Sophia ce ta katse masu firar tasu, daga wajen bakin ƙofar ta tsaya"Yalla6ai ga coffee din na canza wani" har suna haɗa baki wurin furta"we don't need it!" ranta ya 6aci, duk wahala da tasha a ƙarshe sunce basu sha, gyaɗa kai ta yi tare da juyawa ta bar part ɗin nasu.

"Zayn ba ka da mutunci, daddyn namu ka ke yi wa gori? Yunƙurawa yai tare da mikewa zaune A harzuƙe yace"ƙarya nayi ne?ni ban ta6a ganin Mutun mai matattar zuciya irinta daddy ɗinmu ba, har yau in na tuna gorin da akeyi mana raina 6aci yake yi, Allah ya hore mana komai na rayuwa amma daddynmu yaja mana abun magana" Jinjina kai Zaid yai"Nima fa abun na ƙona min rai yana yi min ciwo a zuciya, amma ya zamuyi dole mu rungumi ƙaddararmu" saukowa Zayn yai daga saman gado Ya nufi toilet ya shige, ya rage saura Zaid a ɗakin ya tasa mirror gaba yana kallon fuskar shi, bakomai yake tunanowa ba face fuskar *UMMIN AMERICA*.

*MIDDLE STEP💋*

Daga alkalamin Boss✍️

Kishingiɗe yake saman lallausar Darduma, a Cikin Haɗaɗɗen Garden ɗin gidansa, jikinsa na asanye da Voile sky blue riga da wando, Kayan sun zauna mashi, Fari ne Ba irin sosai ɗinnan ba, dukkan wasu alamun tsufa sun bayyana akan fuskarshi da jikinshi, A ƙalla zai kai shakara tamanin a duniya, daga ganin fatarshi hutu ya zauna mashi, kan shi babu hula, tsufanshi bai 6oye mashi Kyawun fuskarshi ba, tsabar kyan Da Allah yayi mashi zaiyi wuya mutun yai mashi kallo ɗaya ya kauda kai, saboda haɗuwarshi da iya ɗaukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara hurhura duk ta lullu6e ainin launin gashin nasa, daga gaban goshin sa akwai siraran hurhura, da akayi gayu da ita, ba ƙaramin kyau ta yi mashi ba,Yana da tsayin fuska, da Manyan idanuwa, Launin gray mutunne shi ma'abocin son ƙamshi, tamkar Da ruwan turare ya ke yin wanka saboda tsabar yadda jikin shi ke fitar da daddaɗan fragrance mai kwantar da tarzoma, Dogon gemun shi fari fat ya sauko har saman ƙirjin shi, Yana da yalwatacciyar suma.

Dattijon Arziƙi kuma gwarzon Namiji mai ɗauke da suffofin Jagoranci, waɗanda su ke da Jan hankalin Jama'a, mutunne shi mai daraja, Wadatar Arziƙi, kaifin basira da bajinta, Jajircewa, Mai cikar kamala, ga iya mu'amala Da mutane, kaifi ɗaya ne kuma bai Sa6a alƙawari,Ta ko'ina Allah Ya hore mashi, Kuma duk mun tarin dukiyar da ya mallaka Hakan bai gusar dashi daga Yin ibadarshi ba, Hakokin Ubangiji kama daga fidda zakka, sadaka, Da kyautatawa al'umma, mutun ne mai jin ƙan talaka, Shi nashi arziƙin bai ɗaura mashi Girman kai da maƙo ba, Da kuma ƙyamar Talaka, kowa Nashi ne wannan kenan.

daga bayan shimfiɗar shi Sandar shi ce jingine da bishiya wadda aka ƙerata da zallar Gold kuɗin ta kaɗai sun ishi bawa yai maganin talaucinsa, Yayin da iskar Garden ɗin take ratsa sassan Jikin shi, A hankali ya ke ɗan lumshe idanuwanshi yana buɗesu haɗi da ƙarewa ƙayatattun kayan alatun da ke a garden ɗin kallo, a duk lokacin da kewar jikanshi ta addabe shi yakan ke6ance kanshi daga Cikin Jama'a, ba tare da sanin kowa ba, ya ke shigowa garden shan iska, yasan muddin masu kula da lafiyarshi suka gan shi shi kadai agarden sai sun kira ya'yanshi sun faɗa masu daga nan su kuma zasu rasa kwanciyar hankalinsu, har sai sunzo sun duba shi, sun tabbatar da lafiyarshi tukunna hankalinsu zai kwanta, shi kuma bayason ya katse masu aiyukansu, saboda suna ƙoƙari wurin zuwa ganinshi akai akai, Suna matuƙar ƙaunarshi, Babbar damuwarshi a yanzu Jikanshi daya mutu akan ƙaunarshi yayi nesa dashi, ya kwallafa rai akan son shi, ko ƴa'ƴanshi da ya haifa baya yi masu irin son da ya ke yi mashi, gaba ɗaya hankalin shi na akan, kyawawan furannin cikin garden ɗin, Da Halittun dake yawo acikinsa irinsu ɗawisu da filfilo Yana matuƙar son ganin su.

Shu'umin ƙamshin Humran Jikinta ne ya daki Hancinsa, tun kan ta ƙaraso Ya ɗago da idanuwanshi Ya kalle ta kafin Ya kawar da idon shi gefe ɗaya sam babu walwala akan fuskarshi

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull